Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɗanɗan ta ba, dan Allah ina mai roƙon ki da ki kwantar da hankalin ki, kinsan kina fama da lalura ta ciwon zuciya, kada ki sanya damuwa mai yawa a cikin ranki, wanda hakan zai iya shafar lafiyar ki Umma. Insha Allahu wannan al'amarn zai warware cikin sauƙi, kinsha faɗa mun cewa *watarana sai labari* Umma gashi yau labarin yazo wanda yazo mana cike da ɗin in kunya da danasani a gareki, a karo na biyu ina mai sake jaddada ban haƙuri a gareki, a madadin mahaifiyar tawa, da kuma kakana wanda yake kwance cikin ƙasa a halin yanzu, ba wai nace ki yafe masu bane, saidai bana so kina dinga tuna abunda ya faru a baya, Abunda ya faru ya riga ya wuce amma, don Allah ki sake kwantar da hankalin ki, kinji Ummanmu"

Murmushi Umma ta sakar mashi a hankali, cike da so da ƙauna, itama ta runtse hannayen nashi cikin nata, jinshi takeyi kaman Suhan, soyayya da kulawar da yake ba ɗiyar tata kaɗai ta isheta a rayuwar ta, ko ba komai tasan indai Suhan na tare da Al'ameen bata da sauran damuwa ko fargabar hakan, saboda hakan ne ma ya sanya ta furta yafiya ga mahaifiyar tashi, bata fatan wannan al'amari ya shafi rayuwar auren yarinyar tata.

"Allah yayi maka albarka ɗana, ya baka Abunda kake so duniya da lahira, Suhan kuma amana ce a gareka, ina mai alfahari nima da samun suruki kaman kai, hakan kuma ina mai jinjina ma ƙoƙarin ka, dauriyar ka, da kuma taimakonka ga na ƙasa dakai da biyayyar ka, hakan kaɗai ya isa ya sanya ka cimma dukkan ƙudurorinka, babu wata uwa da zata same ka a matsayi ɗa, ta gaza gode ma Allah a bisa baiwar da yayi mata, Allah nake roƙo kaima da ya baka masu yi maka, ya baka zuri'a ta gari.

Cikin jin daɗi, karo na farko kenan da haƙoran nashi suka washe, fuskar shi ta cika da murmushi mai ƙayatarwa , wanda hakan yayi sanadiyyar loɓawar gefe da gefen fuskar tashi, wushiryar shi ta bayyana, inda kyawon fuskar tashi ya daɗa bayyana a fili.

Addu'o in nata da maganganun nata, sun sake sama mata wani matsayi a cikin zuciyar shi, ina ma mahaifiyar tashi Zatayi koyi da irin halayen Umman? Ina ma... To saidai kash, izza, taƙama da isa, wanda zamu iya cewa tayi gadon hakan ne a wajen mahaifin ta, ba zasu iya bari ta zama irin Umman ba, wanda babu komai a cikin zuciyar ta, daga addini sai soyayya, jin ƙai da tausayi a ciki, Sam bata jin kanta a matsayin wata, da tuni ba zatayi ma mahaifiyarshi bautar da tayi mata ba.

Baisan lokacin da ya wara hannu ba, yana mai rungumo Umman, soyayyar ta yake ji har cikin zuciyar shi, ta maye mashi gurbin rashin dacen uwa da yayi, hakan kuma sai yake jinta kaman Mom ɗin tashi wadda ta tsugunna ta haife shi,

Wani irin ƙayataccen murmushi Alhaji Mustapha Dambulan ya saki, yana mai godiya ga Allah, ko Al'ameen kaɗai Allah ya bashi, ya tabbata ya gama dacen haihuwa, cikin tsantsar shauƙi yake kallon yaron nashi da yake durƙushe bisa guiwoyin nashi, yana mai rungume da surukar tashi, wadda yake jinta kaman mahaifiyar shi. Ji yake ina ma Umma ce ya fara haɗuwa da ita a zahiri, da babu abunda zai sanya shi ƙara wani auren, saidai ina ƙaddara ta riga fata, da bai auri Hajiya Kubran ba kuma da ba zai samu yaro Kaman Al'ameen ba, wanda bama shi ba, hatta da ƙasar baki ɗaya take ji dashi, da kuma alfahari dashi.

Sakin Umman yayi yana mai sake bata kyautar murmushin nan nashi mai tsada, yana mai miƙewa ya isa inda iyayen nashi maza suke zaune, suma duƙawa yayi cike da girmamawa da ladabi ya gaishe su, albarka sosai suka saka mashi, inda yake sanar da Dad ɗin nashi cewa shi da Bilal ɗin yau zasu koma, Amman zuwa gobe yake son wucewa zuwa ga neman Alhaji Yaron. Addu'a sosai sukayi mashi, suna masu ƙara bashi ƙwarin guiwa. A hakan ya miƙe yana mai ficewa daga falon, abun mamaki ko inda Hajiya Kubran take bai kalla ba, baya ma son ko kallon nata yayi, domin baisan da wanne irin idanu zai kalleta ɗin ba, so yake ta gane kuskuren ta, so yake ta nemi yafiyar Umma, so yake ta nemi yafiya a madadin mahaifin nata, na halin da ya jefa rayuwar Umman da kuma Suhan ɗin tashi tun ma tana cikin ciki, amman yasan ba zata iya ba, Mom ɗin tashi ba irin mutanen da suke saduda lokaci guda bane su yarda makaman yaƙin su, shi kuma yasha alwashi cewa ba zai taɓa goyon bayan rashin gaskiya ba, ba zai taɓa sanya son zuciya ko son kai a cikin wannan al'amari ba, Mom ɗinshi tayi kuskure, wanda kuma dole ne ta gane cewa tayi ɗin. Har kai lokacin da yabar falon ya kula duk kukan da takeyi ba kukan nadama da danasani bane, kuka ne na son zuciya son kai, kukan za'a rabata da dukiyar ta, wanda take jin kaman za'a rabata da rayuwarta ne. Addu'a kan yanayi kuma zai cigaba da yi mata, yana so ta gyara rayuwar tata, ta daidaita akan hanya madaidaiciya, ta zama kaman kowacce uwa ta kirki akan ƴaƴan nata, ta zama kaman kowacce mata ta kirki a wajen mijin nata, ta zama kaman ko wacce suruka ta kirki a wajen dangin Dad ɗin nashi, idan tayi haka saɓon Allah ne kawai ba zaiyi ba akan ya kyautata mata, idan tayi hakan ko wuta tace ya faɗa, shi yana da yaƙinin faɗawa cikin ta, indai hakan zai faranta ran shi, saboda sanin kanshi ne cewa Mom ɗin tashi tana sonshi da ƙaunar shi, saidai wani lokaci son zuciyar tata ne yake danne dukkan wani abu na daidai daya kamata ace ta aikata, kuma ba wai dan bata sani bane.


Bilal yayi mamakin sake ganin shi ya fito cikin ƙanƙanin lokaci, sannan yayi mamakin daya shaida mashi cewa yanzu yanzu ne zasu juya.

Mamakin shi guda yanzu cikin wannan sanyin marecen zasu ɗauki hanyar Abuja? Saidai yanda yaga yanayin abokin nashi, sai bai tsaya gaddama mashi ba, ya shiga motar yana mai yi mata key, shima zagayawa yayi ya shiga ya zauna. Inda Bilal ɗin ya juya kan mitar suna masu ficewa daga harabar tamfatsetsiyar masarautar.


A hanya ne ya shaida ma Bilal ɗin ƙudirin shi na zuwa neman Alhaji Yaro, Bilal ɗin baiyi mamaki ba, dan dama yasan issue ɗin, saidai ya jaddada ma Al'ameen cewa wannan tafiyar tasu ce baki ɗaya, kuma insha Allahu duk yanda zasuyi, zasuyi domin ganin cewa mai laifin yazo hannun su. Domin ba ƙaramar cin amana bace ta maƙudan kuɗaɗe da yayi ma Hajiya Kubran ba.

Kamo hannun shi Al'ameen ɗin yayi, karo na farko da Al'ameen ya buɗe baki yana zuba ma Bilal ɗin godiya, gami da alfahari da kasancewar shi amini na amana a gareshi, ya daɗa tabbatar ma kanshi cewa samun Aboki kuma amini kaman Bilal ɗin a wannan lokacin da amana da yarda tayi wahala abu ne mai wuya.

Bilal ɗin bai barshi hakanan ba, ya cigaba da jan shi da fira,har saida ya tabbatar ya ɗan saki jiki, a ƙoƙarin shi na son kauda duk wani tunani daga zuciyar abokin nashi, har lokacin da yaga Al'ameen ɗin ya jawo waya yana mai shaida ma Suhan ɗin cewa insha Allah komin dare yau zasu iso, ɗin haka ta shirya masu abubuwan buƙata.




*******************'


Ni kau ta ɓangaren na yini nayi yau babu daɗi, jikina nake ji kaman ba nawa ba, ga yawan faɗuwar gaba, wadda yau yini nayi da ita, dalili kenan da ya sanya nayi kira ga Mijin nawa, farin ciki na kuma saidai bai amsa ba, hakan ne ya daɗa tayar man da hankali na rubuta mashi saƙo, saidai saƙon bai daɗe da shiga ba sai ga reply nashi, inda sai lokacin na ɗan samu sauƙin zuciya ta.

Miƙewa nayi ina mai harhaɗa kaya na, so nake zuwa dare in kira Ya Ameen ɗin na shaida mashi maganar komawa ta makaranta, tun da sanyin safiya Khadeeja ta kirani a waya tana shaida man lallai in dawo school in ba so nake in samu matsa ba, masalan ma yanzu da muka shiga aji na huɗun, inda karatun ya ɗauko zafi, sa'a ake nema tsakanin ɗaliban da malaman.



***************



Ina kwance ne falon nawa, wanda na gyara shi tsaf na ƙalƙale shi, sanye nake da ƙananan kaya riga da wando iya guiwa, sai gashin kaina dana gyara, na tufke shi tsakiyar kaina, na bar sauran nata reto da lilo a baya. Kaina babu ɗan kwali, sai wata vandaner mai kyau wanda iya kaina kawai ta zagaye man, littafin *Menene Riba ta?* nake karantawa, inda nake jin irin zallar fasahar da marubutan suke zubawa cikin labarin, wanda yanzu yake faruwa sosai, wasu marubutan sun ɗauka rubuta batsa a littafi, ko fayyace rayuwar daren na'aurata shine ilimantarwa da faɗakantarwa. Na jinjina masu, kuma littafin yayi ma'ana, inda suka fiddo da aibun da kuma kuskuren aikata hakan a fili. Na natsu tsaf ina kwashe duk wani saƙo na littafin naji ƙugin mota da ƙarfi.

Da sauri na miƙe har ina neman zamewa zuwa ƙasa, yanda naji an banki wani abu da ƙarfi. Ta taga na leƙa zuwa farfajiyar gidan, Nihal ce na hango da mugun gudu ta shige sashen su, tana mai rusa kuka, ƙafarta ko takalmi babu, haka jikin ta ko gyale ma babu.

Ƙarar da naji kuwa ashe motar Ya Ameen ce da take fake gefe ta kaima karo, har bayan motar ya taɓu sosai, glassan motar ta baya sun farfashe suma.

Hankali na ne ya tashi sosai, me ke faruwa ne? Gashi munyi waya da ya Ameen ya shaida man yana hanya.

Ai da gudu na koma bisa sofa inda wayata take ajiye, na ɗauko ta da sauri gami da danna kiran Ya Ameen.

Har ta gama ringing bai ɗaga ba, sai hankalina ya kuma tashi, yanzu duniyar nan babu gaskiya cikin ta, haka hanyar ma ana fama da wannan mamuguntan ƴan kidnapping ɗin.

Ban tsaya wata wata ba, na ruga ɗaki na zura doguwar hijab ɗita ta sallah har ƙasa.

Ban ko tsaya kulle sashen nawa ba, yanayin yanda hankalina yake tashe. Kai tsaye sashen Mom ɗin na nufa, har ina ɗan haɗawa da gudu.

Kai tsaye ɗakin Nihal ɗin na ma tsinke.

Cen bisa gado na hango ta lafe sai shesshekar kuka take yi, wajen gadon na matsa ina mai cewa "Nihal Lafiya kuwa? Me ya faru ne? Pls kiyi man bayani mana" nima cikin tashin hankali nake maganar.

Da sauri ta taso zuwa gareni, sai kuma naji ta rungume ni tsam a ƙirjinta, tana mai sake fasa kukan.

"Aunty Suhan ki taimake ni don Allah, ba wanda zai tsaya saurara ta yanzu nasan sai ke, kiyi ma Ya Ameen magana ya kira baby, wai aure zai ƙara please aunty Suhan"

Maganar tata ta bani mamaki kwarai da gaske, yai ni Nihal ke kira da aunty? Ni take cewa inma Ya Ameen magana akan wata buƙata tata? Ashe ma tasan ina da wani matsayi a wajen shi, dama su baki ɗaya.

A hankali nayi ƙoƙarin raba jikina da nata, abun ma da rainin hankali ciki. Jin ƙoƙarin da nake yine ya sanyata saurin sake ƙanƙame ni. "Please Aunty Suhan ki taimakeni, kada ku bari Baby ya ƙara aure, wallahi zan iya mutuwa in na ganshi da wata macen"

Sai kuma naji jikina yayi sanyi, ko ba komai zata iya cin darajar Ya Ameen, ko ba komai ita ɗin ƙanwa ce gareshi, kuma ɗiya ga Alhaji Mustapha, ba zan taɓa iya ganin jinin Ya Ameen cikin wani hali ba, ba tare da na taimaka ɗin ba, muddin ina da yanda zanyi. Taci daraja ta Ya Ameen da Dad. Da ko kallo Nihal bata isheni ba, tom dandai babu kyau rama sharri da sharri.

Bakin gadon na samu ina mai zaunar da ita. A hankali na shiga kwantar mata da hankali, ina nunnuna mata illolinta a wayance, da kuma dalilin halin data shiga, yau sai ga Nihal tayi kasaƙe tana saurare na, har ma da gyaɗa man kai, alamun maganganun nawa suna ratsa ta. Ni da kaina nace mata nayi alƙawarn koya mata dukkan wani abu datasan cewa bata iya ba, ba tare da ƙyara ko hantara ba.

Nasha mamakin yanda Nihal ta sauke girman kai, izza da isa tana bani haƙuri har naji kunya, gashi dai a girme zata ɗan girme mani, sai ga Nihal yau Aunty sama Aunty ƙasa, harda rungume ni tana sabon kuka tana bani haƙuri, cewa wai tayi nadama, ashe fahimta ta ne batayi ba, ni ɗin ko a cikin mutane daban nake, kuma insha Allah ba zata sake hawa turbar Mom ɗinta ba, ita kanta ta sani ko Mom ba zata tsaya ta saurare ta ba, ta kuma fahimce ta kaman yanda nayi.

Na daɗe sashen har kusan ƙarfe shiddan marece, ina ta kwantar mata da hankali, a ƴar firar da mukayi ne na fahimci gaskiya dole Nureen ya ɗaukar ma kanshi mataki, duk da ba wai yau nasan Nihal ba, Amman tare na da ita ban iya fahimtar yanda al'amurranta suke a dagule ba sai tau, kawai dai nasan komai bata iya yi da kanta sai nayi mata, ashe ni hakan gata ne a gareni, ashe ni hakan zai zame mani alkhairi a gaba, duk da a lokacin ina mai kallon wahala ne kawai nakeyi.

Faɗa mata nayi cewa zanje sashe na inyi ma yayanta girkin tarba. Nacewa tayi akan sai ta bini, lallai ta hakan ne zata tabbatar da cewa na yafe mata, kuma a shirye nake da in taimaka mata.

Sam batayi man maganar Saudat ba, duk da ita bansan irin rayuwar da take yi ba, Amman na tabbata kanwar duk ja ce, abunda yaci doma ba zai bar awai ba.

Sai gashi mun zage a kitchen muna ta aikace aikace da Nihal, ni kallon ta ma nake tayi, wani lokaci har dariya ce take neman suɓuce man, ni kaina ban zata zan iya yafe ma Nihal haka cikin sauƙi ba, sai na fahimci hada tausayi data bani ne, da kuma darajar Yayanta data ci.

Ni ke nunnuna mata komai, lallai Nihal za'a sha fama, a yanda na fahimta ruwan zafi kawai ta iya dafawa, sai kuma indomie, itama tsurar ta, daga mai sai magi sai kwai.
Cikin lokaci ƙanƙai muka gama dukkan Abunda zamu gama.

Ceman tayi zata koma ɗaki, saboda tasan bata iya haɗa ido da Ya Ameen, ita kanta tasan haushinta yake ji, sannan ta ƙara roƙo na da in sake ba Ya Ameen baki, akan ya duba al'amarn ta, ita kanta tasan muddin Ya Ameen ya sauko, to Dad ma zai saurare ta.

Har bakin ƙofa na raka ta, inda saida ta sake bani haƙuri sannan tabar sashen nawa. Na lura cewa laushin nata na dole ne, duk da har cikin ranta ina ganin kaman tayi nadamar. To koma dai menene zan iya aiwatarwa ko domin Ya Ameen, idan nayi haka nasan ran shi zaiyi fari, duk da yana jin haushin ta, Amman ɗan uwa daban yake.


Wanka na shige ina mai durje jikina sosai, ko bayan na fito daga wankan, na daɗe gaban dressing mirror ina ƙalƙale kaina sosai. Ni kaina nasan nayi kyau, doguwar riga ƴar kanti na saka, launin Ja mai haske, tsawon ta iya guiwa ne, anyi mata ado sosai, saidai hannun shimi gareta, hakan ya sanya ni ɗaukar ƴar falmara fara nai adon jajayen duwatsu na ɗora kai, sai fasion ƴan kunne dana manna ma kunnena na barima suma farare da ɗigon farin dutsi a tsakiya ja.

Nayi matuƙar kyau sai tashin ƙamshi nakeyi, fata ta ta daɗa murjewa da kyau, haske na ya kuma fitowa. Fuskar sai tayi cas, sai walwali takeyi.

Na ɓata lokaci sosai, inda Allah ya taimakeni na haɗo da alwala ta. Saboda haka zane kawai na ɗaura kai na tayar da sallah ta.

Ina gamawa na kwance zanen na link gami da hijabin da sallayar. Gaban mirror na koma ina mai sake feshe jikina da turare mai sanyin ƙamshi.

Ko kwalbar ban ajiye ba, na jiyo dirin mota. Ai da sauri na yaye labulen ɗakin ina hango farfajiyar.

Motar ya Ameen ce, inda ina hango shi ya fito, haɗi da sakin wata ƴar ƙaramar miƙa alamun gajiya.

Murmushi na saki, lokacin da na hango shi ya fara ta kowa cikin salon tafiyar shi mai ban sha'awa yana doso sashen namu.

Sai na samu kaina da cenza tafiya, zuwa falon domin buɗe mashi.

Aikuwa ina buɗewar na ganshi tsaye bakin ƙofa, dukkan hannuwan shi soke cikin aljihun wandon shi, ya wani karya kai alamun shagwaɓa da gajiya.

Daga inda nake tsaye na haske shi da murmushi. hakan ce ta sanya shi takowa zuwa gareni, ja baya nayi kaɗan zan bashi hanya, naji wani irin sulɓi ya kwasheni, ai sai nayi baya suuuu zan faɗi, ban idasa kai ƙasa ba Naji ya fizgo ni zuwa jikinshi. Ai sai na maƙalƙale shi ina mai zare idanuwa.

Mun kusan second ashirin a haka, idanu na cikin nashi, lokaci guda kuma na fara ƙoƙarin ɗago kaina inga abunda ya jani har haka, bayan nasan babu wani abu dana ajiye, ko kafin in shiga wanka, saida na daɗa gyara wurin.

Ɓawon Ayaba ne barbaje a wajen. Cikin zaro idanu nake kallon wurin, tayaya akayi ɓawon ayabar da na zuba a dustbin, bayan na gama haɗa mashi banana shake ya fito yazo wajen? To wanene ya shigo man sashe bayan na shiga wanka?.

Shima da alamu mamakin hakan yake yi, ɓawon Ayaba a bakin ƙofa? Me hakan ke nufi?

Buɗe baki nayi da niyyar yin magana ya ɗora man hannu a baki, alamun inyi shiru, sannan ya raɗa man a kunne. Je ki sanya hijab, tare muke da Bilal, zan gyara wajen.

Jikina a sanyaye na raba jikina da nashi, ina mai tsattsallakewa zuwa ɗakin namu cikin sauri, yayinda shi kuma ya wuce kai tsaye zuwa kitchen, ya ɗauko tsintsiya da abun kwashe sharar ya shiga tattara wurin.

Daidai lokacin da Bilal yayi sallama yana mai turo ƙofar Falon. Dariya ya fashe dashi, yana mai cewa "Omo look at you Bro, kaine yau da shara? Daga isowar ka? Hahaha wani abun sai mata"

Ganin yana neman yi mashi shaƙiyyanci ya sanya shi cemashi "ka tsaya gulma malam, idan ba zaka je kaci abinci ba"

Wucewa Bilal ɗin yayi zuwa dining kai tsaye, yana ƙunshe dariya. Har ya gama yayi mopping ɗin wurin ban fito ba, ina cen ɗaki zaune bakin gado, tsoro fal a cikin raina, iko sai Allah, wanene yake neman ma ƙasa ta a cikin gidan nan? Wa na tsare ma wani abu? Mom bata nan, balle ince ko ita ce ta sanya wani, saboda ƙiyayyar da take man, kaina fa ya kulle, idanun na har sun kaɗa sun kawo ruwa. Gashi nidai ba zance Nihal bace tunda mun rabu lafiya da ita ta tafi...


Katse man tunanin yayi, inda naji hannun shi cikin nawa yana mai cewa "Madam ya gida? Ya kaɗaici?"

Murmushi na sakar mashi, wanda har saida ya sanya shi zama, yana mai zame hular dake kaina ya fara shafo sumar kaina, jin hakan sai na lafe bisa jikin shi, ina mai shafa gefen hannun nashi da nake kai a hankali.

Yasan dole hankalina ya tashi, saboda haka ne ya shiga jana da fira da wasanni har na saki jiki, hijab na zura, ina mai bin bayan shi zuwa falon, inda dining yake.

Bilal ya saki jiki ya kwashi girki son ranshi, sai zuba santi yake, ko bayan da muka isa wajen muka zauna, bai kulamu ba, har saida ya gama cin abincin shi, yana mai zuba ma matan da suka iya girki godiya, sannan ya miƙe gami da dafe ciki yayi hamdala yana mai cema Al'ameen sai zuwa safen sa haɗu.

Sai lokacin ne muka gaisa, Ya Ameen dai cewa yayi ba inda zai raka shi, haka shima yace bai ce yana buƙata ba. Yana fita yaja mana ƙofar, inda duk muka bishi da kallo, muna masu taya shi dariyar.

Nasha kula sosai a ranar, Ya Ameen daban yake ba zan gaji da faɗa ba, komai nashi cikin salo yake yinshi, saida yayi wanka ya gargama duk ayyukan shi, sannan muka kwanta. Kula da tattali ranar nasha su, sai nake jin ma duniyar kaman babu kowa cikunta sai mu kaɗai.

Duk abun nan da akeyi ya kasa faɗa man komai na dangane da halin da ake ciki sai kallona yake da abun, ya gaza ta yanda zai ɓullo man da maganar. Yanke shawara yayi akan cewa zai bari sai ya nemo Alhaji Yaro, sannan zai sanar dani halin da ake ciki ɗin.

Maganar makaranta nayi mashi, ce mani yayi yana sane, dan a halin da ake ciki ma wai ya nema mani transfer, kawai takadda yake jira, nan da kwana biyu zata iso, inda ya maidoni nan Abuja, anan ne zan idasa karatun nawa, wai a cewar shi baya son yin nisa dani.

Naji daɗin hakan, lokaci yayi nima da zan roƙe shi ya koya man mota, Tunda ina da motar da na samu kyauta lokacin biki na, sai in dinga yin day kawai a kullun, ba sai na zauna Hostel ba da aure na.

Cikin wayau na sako mashi maganar Nihal, ƙoƙarin dakatar dani yake yi, ban ƙara cewa komai ba, har saida ya kammala faɗace faɗacen shi, kunsan muskili bai iya zuciya ba, sai a lokacin ne nikuma cikin siyasa da kissa irin tamu ta mata na sanar dashi yanda mukayi da Nihal ɗin, harma ayyukan da ta tayani yau mukayi.

Shiru yayi mani, kaman yayi bacci, har yanzu dai yana naniƙe dani, wani irin so na ne yake ji yana ratsa shi, yana mai ƙara gode ma Allah da mallaka ta a matsayin mata da yayi. In ba haka ba, inda wata ce yanda nasha wahalar Nihal, zan so ne ma ace rayuwar gidan tata ta lalace, sai gashi nice ma ke roƙon shi, akan cewa ya sanya baki a gyara komai.

Saida ya rungume ni yana mai sanya mani albarka, sannan yace mani, in bari yaga kamun ludayin nata, idan yaga dagaske ta cenza, insha Allahu zai san yadda Zatayi ta koma gidan nata, Amman maganar ya hana Nureen ƙarin aure ma bata taso ba, tunda shi aure lokaci ne, kuma raine dashi, dan haka koma menene ya same ta ita ce ta ja ma kanta.


Lamo nayi ina sauraren shi, inda yake sanar mani tafiyar da zaiyi goben shi da Bilal. Addu'a na dinga kwararo mashi, ina mai jaddada mashi matsayin Mom a gareshi, kwarai ya yaba a gareni, kuma ya ƙara tabbatar ma kanshi cewa koda abunda yake ta ɓoyo ya fallasa, shi yasan ba zan taɓa juya mashi baya ba.


*******


Tun tana sa ran taji an fasa ihu daga sashen namu har dai taji tsit, kenan ɓawon ayabar da ta sanya bai yi amfani ba, duk wahalar da tasha kafin taga ta samu shiga kitchen ɗin nawa ta ɗebo ɓawon ayabar har ta kai da zuba mani, ba tare da kowa ya ganta ba, a duk tunanin ta, muddin santsin nan ya kwashe ni, ƙila ma ba karaya ɗaya ba, idan ta kai goma ƙila sai nayi ta.

Saidai saɓanin yanda ta zata, sai ji tayi shiru, kuma a kan idanun ta Ya Ameen da Bilal suka dawo. Me hakan ke nufi kenan? Suna nufin sunga ɓawon ayabar ne, ko kuma ta faɗin ihun dai ne Allah bai sa taji ba? Koma dai menene zata bari zuwa safiya, domin taji abunda ya faru, Amman tana da tabbacin zuwa safiyar zata ga an cicciɓo Suhan ɗin zuwa asibitin ƙashi...


Kaman yanda ta kwana sauraren farin saƙo a gareta, haka Ya Ameen ya kwana tunanin halin da yake fuskanta, da kuma dalilin zuwan ɓawon Ayaba sashen nashi, ya tabbata Suhan aka ƙulla ma hakan, sannan yayi imanin cewa koma wanene yayi hakan yana cikin gidan, sannan yasha alwashin koma wanene gamuwar tasu ba zatayi daɗi ba.









~Oum-Deedat ce~
[1/24, 10:00 PM] GOLDEN

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment