Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abun shi, kaman ba shi ba, ga jiki irin na turawa, ko ina ɓul-ɓul.

Saida Bilal ya bashi hannu suka yi musabaha ne, sannan ya koma bisa Sofa ya baje yana faɗin "wash friend, wlh akwai tafiya kam sosai, kusan awa 12 a jirgi"

Ɗan hararar shi Al'ameen yayi yana mai faɗin "Kaji shi kaman yau ka fara tafiya america"

Mudi ya ba saƙon yayo masu take away. Sannan ya maida kallon shi kan tilon ƙanen nashi "Ya Abie, how far? Ya gajiya?"

Cike da shagwaɓa irin na ƴaƴan masu kuɗin abie & in ke cewa "Wallahi Big bros akwai ta, ni fa na ƙagara naga Su Dad da Mom, anya ba wucewa zamuyi da Mudi ba, idan kun gama kun same ni a gida"

Kafaɗa Al'ameen ya sauke, yana mai faɗin "To ka kira Mudin ka faɗa mashi ban da kai zaiyo, nima banda ni, sai ko dai Bilal"

Da harara Bilal ɗin ke binshi, sai kuma yace "Kajika, kana gauro ɗinne zaka ce band kai, sai dai ko ni? Ka manta ina da mata ne?"

"To ina matar take?" cewar Al'ameen yana mai maida kanshi bisa makarin kujerar ya kwantas, lokaci guda yana mai jujjuya kujerar a hankali a hankali.

"Oooh haka ne fa, mtseww wlh friend har na fara gajiya da rashin ta a gidan"

"Kai ka sani, ka ƙara mana"

"aidai gara ni, kai kuwa da ko ɓalli baka da ita fa?"

"Me kake tauna na baka na zuba, ƙila dai baka lissafi, nima saura kwanaki ne ai"

Da mamaki Abie ke kallon shi, ɗan wari idanu yayi.

"Wow yaya ne kake cewa? Kana nufin you are on a date?"

Ɗan murmushi ya sakar ma Abie ɗin yana faɗin "Yeah Lil Bro, ka kusa yin aunty, Amman ita bata son hayaniya da surutu fa"

"Bro nima ai bana da surutu, ko kuwa Yaya?"

Ya maida tambayar kan Bilal.

"Really my Bro, ai shi ya ma fika surutu"

Ɗan harara wasa Al'ameen yayi, "zama da kai ne shegen kaya"


"ko kuma soyayya ba" cewar Bilal ɗin.

Su duka murmushi suka sanya, yayin da shi kuma gogan naka ya murmusa, ko ba komai sun tuno mashi da sahibil ƙalbin shi.

"wao wat a suprise Yaya? Wacece wannan a ina kuma take?"

A hankali ya ɗago yana mai kallon Abie ɗin.

"zaka ganta soon bros, me kake ma sauri ne?"

Ɗan murmushi Bilal ɗin ya saki.

"Lallai ta ciri tura yaya, ashe a ƙasar nan matar taka take, ni da na ɗauka baka son ƴar nigeria ne"

Bai tanka mashi ba, sai ma sake sakin murmushi da yayi, da ido Bilal ɗin yayi ma Abie nuni da ya bar maganar.

Ɗan ɗaga gira yayi, yana mai ɓame bakin shi, da yin alamu za hannu (Zip).

Dariya suka sake saki su biyun, daidai shigowar mudi ɗin ɗauke da take away.

Yana ajiye ma Bilal ɗin, Abie ya miƙe yana mai yi masu sallama, yabi mudi ɗin a baya,


***********


Zama sukayi Umman na mai sake gaida su, cikin fara'a suka shiga amsa mata, ko ba komai tayi abun da Kubra bata taɓa yi ba tinda mustapha ya aure ta, sun dawo daga tafiya su tadda abinci ready? Wanda kuma ita ce ta girka masu shi?

Cikin nuna farin cikin su ALHAJI Auwalun ya shiga yi mata godiyar abinci, ita ma har ya bata kunya.

Hajiya zainab ɗin ce ta shiga shaida masu dalilin shigowar su wajen nasu.

Dumansu natsuwr su suka maida kan Umman.

A hankali ta fara magana, bayan ta sauke kanta ƙasa.

"Alhaji nima nace ina da magana, Suhan yarinya ce da tun da ta taso take mani maganar mahaifin ta, da maganar dangin mahaifin ta, da maganar ni kaina dangi na, Amman ko sau ɗaya ban taɓa faɗa mata wani abu ba, daya dangance mu, tayi magiyar har ta gaji, tasha gorin cewa bata da mahaifi, to yanzu lokaci yayi da bama ita kaɗai ba, ku dukan ku zaku san labarin namu, kuma ba yanzu ne zan faɗa ba, har sai munyi wata tafiya mun dawo, ina SO alhaji tafiyar nan ta zama sirri tsakanin iya mu nan, ko su yaran bana so su sani, nayi hakan ne ba domin komai ba, sai don ba yadda za'ayi in iya aurar da Suhan ba tare da sanin mahaifa na ba, ba tare da amincewar su ba, duk da nasan ba wai zasu hana bane, shi kanshi yaron (Al'ameen) domin shi da mahaifiyar shi su samu natsuwar cewa Suhan na da mahaifi, kuma tana da usili mai kyau, kaman yanda nima nake dashi"

Ba Alhaji Mustapha ba, har Hajiya Zainab da Alhaji Auwalu ba wanda biyo mamaki ba, dukan su zuba mata idanu sukayi.

Ikon Allah, ashe akwai ranar da zata zo Maryamar tayi maganar mahaifarta da kanta.

Kusan zamu iya cewa Alhaji mustapha yafi kowa murna da zancen.

Cikin mamaki suka shiga jera mata tambayoyi, saidai babu wadda ta amsa, kawai dai ta nemi da su sanya lokaci wanda zata yi masu jagora zuwa ga mahaifar tata, wadda ita da kanta ne ta sanya ƙafar ta tabar ta, shekara ashirin da huɗu da suka wuce.

Su ji daɗi, sun yi matuƙar godiya gareta, hankalin su ya kuma kwanciya da auren, sun sanya ranar Juma'a mai zuwa za'ayi tafiyar, don haka Alhaji Mustapha ɗinne zai shirya komai kafin zuwan lokacin.

A haka su Alhaji Auwalu sukabmiƙe, gami da yi masu sallama suka nufi nasu gidan, to ko dai a mota tattaunawr da suka shiga yi kenan, Alhaji Auwalun ne ke cewa, shi yana ji a jikin shi, Maryamar duk inda ta fito, ta fito ne daga babban gida, natsuwar ta, da kuma yanayin yanda take mu'ammala da mutane ne ya nuna hakan.


Shima Alhaji Mustapha ɗin bai kuma tada mata maganar ba, sai ma waya daya ɗauko yana neman Layin Al'ameen gami da shaida mashi ya same shi gida.

Nan ne ya kuma cigaba da lala shin Umman, gami da bata baki, akan ta daure ta jure taba yaran goyon baya su samu Abunda suke so, sharuɗɗan Hajiya Kubran ba abun dubawa bane, muddin dai aka ɗaura auren.

Ita kuma tayi hakan ne domin ta tseratar da yarinyar tata daga gorin dangin mijin nata, ko ba komai gorin asali ba ƙaramn gori bane, lokaci ne yazo da zasu gane cewa Suhan ɗin ba abar wulaƙanta wa bace, itama da kalar nata asalin.


***********


Saida Bilal ya gama cin abincin, sannan Ya Ameen ɗin ya ɗauko shi zuwa gidan nashi, domin yayi wanka ya huta.

Sun rabu akan cewa da ya tashi daga bacci zai neme shi, domin su fara shirye shiryen wucewar Al'ameen ɗin zuwa gobe.

Gida yayi ma tsinke, zuciyar shi na daɗa bugawa, domin baisan abunda zai je ya taras ba, masalan wannan tafiyar da sukayi, zuciyar shi na raya mashi cewa ta shafe shi, gashi tin ranar da suka haɗu da Mom ta ɓalla mashi harara rabon da ya sanya ta a idon shi kenan.


Part ɗin Dad ɗin nashi yayi ma tsinke.

A perlour ya tadda shi, zaune yake bisa Sofa yana kallon tashar aljazeera, shi kaɗai a Falon sai tulin jaridun da suka fito yau wanda bai gama dubawa ba, dama haka akeyi mashi, kullum sai an kawo mashi jaridun da suka fita a ranar ta duba su.

A ladabce ya ida ga Dad ɗin nashi dake zaune, ƙafafun shi gabaki ɗaya bisa doguwar kujerar ya kishingiɗa.

Dad ɗin nashi mutum ne dake cike da kamala da kwarjini, ƙasa ya samu gefen shi ya zauna, yana mai tanƙwashe ƙafafun shi yake faɗin

"Dad barka da rana, an dawo lafiya ya hanya?"

Da murmushi Alhaji Mustapha ɗin ya miƙe zaune, yana mai zuro ƙafafun shi daga bisa kujerar, ya daidaita zaman nashi, yana mai shafo kwantaccen sumar kan yaron nashi yake cewa "lafiya Lau Son, ya aiki? Ya rana kuma?"

"Duk lafiya lau Dad, ya kuka baro su Alhaji da Hajiya?"

"Duk suna gaida ku Son"

"To masha Allahu Dad, Allah ya huta gajiya"

"Ameen Son, na kira ka ne nan saboda ina so ne mu tattauna wata muhimmiyar magana, nasan kasan munyi tafiya, kuma wata ƙila ka iya gane dalilin maganar auren ka ce ta kaimu cen kankiya ɗin, to Alhamdulillah munje lafiya mun dawo lafiya, kuma na dawo maka ɗauke da magana a bakina, saidai ina so ka natsu tsaf ka fahimta, nasan kana son yarinyar nan Suhan ko ba haka ba?"

Gyaɗa kai Al'ameen ɗin yayi, yana mai sake sun ne kai ƙasa, wai yau shine Dad ɗinshi ke cewa yana son wata da bakin shi.

Katse mashi tunanin yayi ta hanyar cigaba da cewa." Abunda ya kaimu kankiya kenan, su Alhaji suka buƙaci ganin mu, to cikin ikon Allah ita mahaifiyar taka ta amince da auren naka"

Cikin tsanann mamakin farin ciki ya ɗago yana mai kallon Dad ɗin nashi, sai kuma ya saki murmushi, har kumatun shi suka loɓa.

Sai kuma ya sake sauke kai ƙasa, zuciyar shi na ƙara hur a mashi wutar son Suhan ɗin, yanzu ne ma da Dad ɗin nashi ke sanar dashi amincewar Mom ɗin, sai yaji ya sake samun natsuwa da soyayyar, wai dama she Abunda ke dakushe mashi kafin soyayyar tashi ga Suhan ɗin, rashin amincewar Mom ɗinne.

"Saidai kuma fa, akwai wani hanzari ba gudu ba, ita ma Mom ɗin taka, ta kafa sharuɗɗan guda biyu, a bisa amincewar tata"

Cikin mamaki ya kuma ɗagowa ya kai duban shi kan fuskar Dad & in, da take ba yabo ba fallasa.

"Dady sharaɗi kuma?"

Ya faɗa annurn dake fuskar shi na ƙoƙarin gushewa.

"Kwantar da hankalin ka Son, ni a gani na, a ɗaura auren shine mafi muhimmanci kafin wannan. Sharaɗi na farko shine, zaka zauna da matar cikin gidan nan, ina nufin ba zaku bar gidan nan ba kauda a Suhan ɗin ko bayan anyi auren, sharaɗi na biyu kuma shine, duk lokacin da taga wata wadda ta kwanta mata arai zata kawo maka ita ka aura, waɗannan sune sharuɗɗan Mom ɗin taka a gareka, idan ka amince to.. "

Baisan lokacin da ya miƙe tsaye ba, sai kuma ya koma ya zauna" Dad zama da mata ta acikin gidan nan? Matar ma wadda kowa yayi yaƙi in mom bata sonta? Aure kuma Dad? Mata biyu ni a shekarun nan nawa Dad?"

Duk ya shiga jera ma Dad ɗin tambayoyi, fuskar shi a matuƙar haɗe, wadda ke bayyana tarin rikici da ɓacin ran da suka same shi a nan take.

Hannun shi Dad & in ya kamo, yana mai ɗago shi ya zaunar dashi bisa kujerar da yake zaune, kaman wani abokin shi.

A ƙoƙarin shi na kwantar mashi da hankali ya shiga cewa "Son kwantar da hankalin ka, babu abun ɗaga hankali ciki, sanin kanka ne cewa idna har baka yarda ba, ba zaka taɓa samun kwanciyar hankali ba a gidan nan naka, muddin matar taka zata haɗu da mom ɗinka, mafi a'ala dai ka yarda da dukkan sharuɗɗan nata. Zam dai ka zauna na wani ɗan lokaci, kafin komai ya daidaita, Amman maganar auren ne nima har yanzu nake nazari akai, Amman dai ka fara ce mata ka amince ɗin, daga baya ko me kenan sai ayi shi"

Sai yanzu ya samu kwanciyar hankali, koma minene zai ce ya amince ne kawai ko domin ƙiyayyar mom ga Suhan ɗin ta ragu, sannan ko domin kada wata fitinar ta kuma ɓullowa.

Gyaɗa kai ya shiga yi, yana mai cewa "To Dady ba damuwa, insha Allahu hakan za'ayi, zan same ta da maganar dady, nagode Allah ya ƙara girma"

Ba damuwa Son, insha Allahu zan tsaya tsayin daka akan ganin komai ya yuwu, tinda ka amince zuwa gobe za'a fara gyaran sashen naka, sai ka bada plan ɗin yanda kake so a tsara maka, kuma maganar kaya duk ni ne zan zuba maku da kaina, babu Abunda nake buƙata daga gare ku, saidai cen tsakanin ka da yarinyar, ina nufin lefe da abun da ba'a rasa ba, sadaki kuma babanka yace shine zai bada"

Cikin farin ciki ya kuma shiga gyaɗa kai, ko ba komai mahaifin nashi, na ƙoƙari wajen ganin ya faranta mashi rai, yana sonshi yana ƙaunar shi, haka kuma yana girmama duk wani ra'ayi nashi da bai saɓa ma shari'a ba.

Shiru ne ya biyo baya, sai kuma suka shiga tattauna harkokin kasuwancin su, anan ne yake shaida mashi cewa zaiyi tafiya ma zuwa New York ɗin zuwa gobe idan Allah ya kaimu, saboda zasu tattauna da wasu kanfanoni akan zuba hannun jari.

Al'ameen ɗinne ya kuma gyara zama.

"Dad maganar Nihal, na kira shi mijin nata jiya, to mun tattauna dai......."

Ya kashe duk yanda sukayi da Nureen ɗin ya faɗa ma Dad ɗin.

"Na sani Al'ameen, ban yi maganar bane saboda ina so ne su gane kuskuren su, kuma na gansu da duk hukuncin daka yanke kuma ina mai goyon bayan ka, zuwa anjima ma zan shiga in jaddada masu hukuncin naka, dole ne su gane kuskure nasu, Amman tinda kai ka riga ka kira shi kunyi magana shikenan hakan yayi, kada ka kuma tanka masu akan maganar har sai lokacin da ka lura ita ɗin ta cenza ta gyara, saboda don tana ɗiyar mu, ba shi ke nuna cewa zamu goyon ma rashin gaskiya baya ba"

Jinjina kai Al'ameen ɗin ya shiga yi, yana mai faɗin "Haka ne Dad, bari inje in samu Mom ɗin, insha Allahu duk yanda mukayi da ita, zanzo in sanar maka"

Da kallo ya bishi yana ta faman murmushi har ya fice.

Samun natsuwar yaron nashi shine auren, insha Allahu duk yanda zaiyi yaga anyi auren zai bi, domin ganin yaron nashi ya samu natsuwa...







~Our-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*Addu'a Idan Ya yi Buda Baki a Gidan Mutane*

أَفْطَرَ عِنْدَكُمْ الصَّائِمُونَ وَأَكَلَ طَعَامَكُمُ اْلأَبْرَارِ، وَصَلَّتْ عَلَيْكُمُ الْمَلاَئِكَةِ.

*Aftara 'indakumus-sa-imoon, wa-akala ta'amakumul-abrar, wasallat 'alaykumul-mala-ikah.*

*Allah Ya sa masu azumi su yi buda baki a wajenku, kuma Allah ya s anagartattun bayi su ci abincinku, kuma Allah Ya sa Mala'iku su yi muku addu'a.*


>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~57~*

*Godiya mai ɗinbin yawa zuwa gareki ƙawata _Salamatu_ haƙiƙa kin nuna mani ƙauna, kin nuna kuna tare dani da kuma ~SuhAmeen~ godiya marar adadi, wannan Page ɗin naki ne, kyauta halak malak, na gode da wannan ƙauna da kike nuna mani, Allah ya barmu tare.*

*Jinjina gareki ƴar uwa ta, Jiddon Dady, kina ƙara ƙarfafa mani guiwa da kuma shawarwarn ki, haƙiƙa nafi kowa dace da samun ƴar uwa kuma ƙanwa a duk faɗin duniyar nan, ba zan iya misalta ƙauna ta gareki ba, har kullum kina cikin zuciyar tilon ƴar uwan ki Oum-Deedat. Fatan zaki dawwama cikin aminci, da ƙauna daga angon ki, mai gidan ki Yusuf Tijjani Baffa (Dady) gaisuwa zuwa gareku baki ɗaya*


_@One lurv marubuciyar ( *Ƙareenaty* ) da Fatima batula marubuciyar ( *Ni da Malama ta*) gaisuwa zuwa gareku. in kuka ɗauke Umar babu wanda ke nuna ma littafi na ƙauna, duk cikin forum ɗinmu kaman ku, ina yinku irin over ɗinnan, a cigaba da zazzaga mana zallah fasaha._

~Hehehe @Batula ina so ki sani, yanzu ne ma na fara karanta *Ni da malama ta* yanda kike zazzaga fasaha ai ba zan taɓa son in dena karantawa ba, kada a shani masilla~


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


A falo ya tada ta zaune, Abie na kwance gefen ta, kanshi bisa dukkanin cinyoyin ta.

Da sallama ya ƙarasa ɗauke a bakin shi, zuwa kujerar da take kusa da su.

Zama yayi, yana mai gaida ta, da dukkanin kulawa da fara'a sosai ɗauke a fuskar ta, ta shiga amsawa.

Gama wayar ta kenan da Hajiya Sa'a, ta tabbatar mata da an kammala komai, duk da sharaɗin da boka ya gindaya masu mai matuƙar ƙarfi, cewa an kammala komai da zaran an ɗaura auren zaiji duk duniya ba wadda ya tsana irin matar tashi, to saidai fa, muddin suka yadda ya santa a ɗiya mace, lokacin ne fa komai zai warware. Son da yake mata ma zai daɗa linka na da.

A haka suka amince, masalan Hajiya Kubran da idon ta ya riga ya makance, ƙiyayyar da tsanar ce kawai ke cin ta, ita a ganin ta, tinda kusa da ita zasu zauna, zata yi duk yanda zata yi ta hana shi tarawa da Suhan ɗin, masalan ma gashi ance zai tsane ta, dama dalilin ta kenan na cewa a zauna gidan kenan, saboda ta sanya ma duk wani motsi nasu idanu, ita fa ba zata taɓa sake jiki tana ji tana kallo ta haɗa iri da waɗannan baƙaƙen talakawan ba.

"Son an dawo lafiya? Ya gajiya?"

Ta faɗa, tana mai kallon yaron nata cike da annashuwa, gani takeyi kaman burin ta ya gama kammala, ita har ta ƙagara ma a ɗaura auren, ko zai fara tsanar tata, kuma lokaci ne yanzu da zata sauya salo, zata nuna ma kowa ta amince da auren, kuma tana ƙaunar Suhan ɗin 100%.

Yayi mamakin sakewar ta gareshi, dukda haka dai sai ya basar, yana mai cewa "yes Mom, gajiya akwai ta"

Ya faɗa yana ɗan zamewa bisa kujerar.

"Ko zaka ci abinci ne? Sai Nihal ta kawo maka"

"wa yayi girkin?" ya faɗa yana mai ɗagowa ya dubeta.

"Eh to wai Nihal tace ita ce tayi, ai kai ne kace ta dinga yi"

"Uhmm" kawai yace, domin yasan ƙarya Nihal ɗin takeyi, ba zata iya cika sharuɗɗan shi ba.

"No Mom, ta bar shi kawai, kinsan ba iyawa tayi ba, zan samu abun da zan ci a ɗaki na"

Ya faɗa yana mai ɗan gyara zama ya fuskance ta.

Ɗan ɗaure fuska tayi, domin Nihal ɗin ta faɗa mata komai, to ita ma ɗin duk da bata ji daɗin hukuncin Al'ameen ɗin ba, zata so ace Nihal ɗin ta koma gidan mijin nata, kaman ita Hajiya Kubra bai kyautu ace an koro mata ɗiyar tata gida ba, Amman yanzu ba ta Nihal ɗin takeyi ba, so take ta gama da matsalar Al'ameen ɗin tukunna.

"Kai malam sai ka ɗaga man Mom ko? Kazo ka wani hahhaye ta"

Ya faɗa a hankali, cikin salon maganar shi, mai cike da sanyi.

"A'a ƙyale mani auta na, yaushe rabon da in ganshi?"

"ita Afnan ɗin kin bada ta ne? Da kike kiran shi auta, wannan gotai gotai ɗin dashi, kalle shi fa, ya kusa tsawo na"

"Mom ƙyale shi, na dawo fa kenan ai, so yake ya takura ni" Abie ɗin ya faɗa cike da shagwaɓa.

Murmushi ya saki, yayin da shi kuma gogan ya ɗan lumshe ido yana mai kauda kai gefe.

Saida ya tattaro dukkan natsuwa da dakiya ya ɗora ma kanshi sannan ya fara cewa "Mom daga wajen Dad nake, munyi magana dashi sosai, ya faɗa man dukkanin sharuɗɗan ki, insha Allahu na amince, kuma zaki sameni mai yi maki biyayya a koda yaushe"

"Dama zaka ce haka mana, Soyayya ta rufe maka ido, to ai ni ba zan zuba maka idanu ba haka kaman baka da gata, ka rasa wadda zaka aura sai takalan masu aiki na" ta faɗa cikin zuciyar ta, a zahiri kuma murmushi tayi sannan tace.

"Ba damuwa Son, feel free, nice na amince maka da kaina, da fatan dokokn basuyi maka tsari ba, bana so ne kayi nisa kusa dani, Shiyasa nace a taimaka a zauna kusa dani ɗin, na gane cewa yarinyar tana da natsuwa kuma kan sonta, ni kuma kasan ina ƙaunar dukkanin abubuwan da kake so"

Da matuƙar mamaki yake kallon ta.

Anya kuwa mom ce? What bring this suddent change?

Shima ɗan zura mata idanu yayi, Un blievable, ace kaman mom ce yau ta tausasa murya tana mashi magana haka akan auren nashi, bai ƙara shan mamaki ba, saida tace mashi "ya inlaw ɗin tawa? Fatan dai tana lafiya?"

"Lafiya Lau Mom, tana gaida ku"

Ya faɗa a hankali cen Ƙasan maƙoshin, na farko kenan a tarihn rayuwar shi, tin tasowar shi daya ji tana tambayar lafiyar Suhan ɗin.

Abie ne da yake kwance, Baisan wainar da ake toyawa ba, tashi zaune yayi yana mai cewa "Mom yaya yaƙi faɗa man wacece groom ɗin tashi har yanzu fa"


Kallon ta ta maida kan Abie, "Kada ka damu Son ai ka santa ma, Suhan ce ta gidan nan"

"what? Mom Suhan wadda na sani? Ita yaya zai aura?"

Ya faɗa yana mai ɗan zaro idanu cikin kaɗuwa.

Hankalin shi Al'ameen ɗin ya maida kan Abie, kada dai ace shima baya goyon bayan abun kaman saudat da Nihal.

"Yes for Sure Son, kaga tuwon mu manmu"

Ga mamakin Al'ameen wani irin ƙayataccen murmushi ya saki, yana mai tashi ya koma bisa kujerar da Ya Ameen ɗin yake kai, rungumo shi yayi yana mai cewa "Congrat Yaya, Allah ya sanya alkhairi, ai Suhan tayi, tana da kirki da natsuwa, ta cencenci a aure ta"

Su duka da kallon mamaki suke binshi, daga mom ɗin har Al'ameen ɗin.

Shima murmushi Al'ameen ɗin ya saki jin abinda yace, sai kuma ya maida kallon shi kan Hajiya Kubran da take hakimce, fuskar ba yabo ba fallasa.

Miƙewa yayi yana mai cewa "Thanks Bro, bari in wuce daƙi, ina so ne in huta, gobe insha Allahu da wuri nake so in wuce, alabasshi kai ka tafi daga baya"

"Ina zuwa ne Son?" Mom ɗin ta faɗa, har yanzu fuskar ta ba yabo ba fallasa.

"Mom New York nake so naje zuwa gobe akwai ayyukan da suka taso mana ne acen, kuma dole sai nine zan yi su, maganar zuba hannun jari ne a cen kamfanonin nasu"

"OK to babu damuwa, inda ka dawo sai muyi maganar yanda abubuwa zasu kasance Son, kada ka damu ni na amince Allah ya baku zaman lafiya mai ɗorewa, sannan nima ina so ne muyi maganar ƙara share ɗin da zanyi a nnpc tower, ko zuwa bayan hidimar ne"

"OK Mom see u later"

Ya faɗa yana mai wucewa zuwa sashen nashi, bai san me ke damun mom ɗin tashi ba, da take ta ɗaukar maƙudan kuɗaɗen ta tana zuba hannun jari a kamfanin man fetur da iskar gas ɗin ba, duk dai da cewa lafiya lau tana ganin profit nata, saidai fa shi ba wai ya natsu bane sosai da har kar, kasancewr haka take abun wani lokaci ba lauyoyi, duk da dai shi yana rubuta komai da sanya hannun waɗanda kuɗin nata ke shiga hannun

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment