Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah, wayyo! Daɗin ya Ameen kenan, da ba zai bari in dinga baccin Lalaci haka ba, duk da yake lallaɓa ni sosai a yanzu. Saboda haka ne na nufi ƙofa da ɗan hanzari na, zuciya ta wanke fes, tuno firar mu da ya Ameen da nayi jiya, wanda har saida bacci ya ɗauke ni muna fira dashi, kafin wayar ta sulale ya kashe daga cen ɓangaren.

A hankali na murza handle ɗin ƙofar, bayan na sanya makullin na buɗe.

Kai kawai na saka zuwa falo, sai faman murza idanu nake yi. Daga cen gefe na hangi wata baƙar leda a dunƙule, in ba idanu na bane suke man gizo, sai naga ledar kaman tana motsi.

Ɗan murmushi na saki, ina mai cewa "Oh ko me ya kawo leda kuma nan? Ko dai ledar agwaluma ta ce na manta ban ɗauke ba? Gadan gadan na nufi wajen da ledar take, a hankali na zuƙunna ina mai kai hannu bisa ledar na yayo ta kai tsaye.

Wani irin taushi da sulɓi da wani irin yanayi na ji cikin ledar, lokaci guda kuma abunda ke motsi a cikin ledar yayi ƙoƙarin fitowa da gudu.

Wani irin razananne ihu na saki, ganin wani irin danƙareren ɓera, baƙi wuluk yayi tsallen burgu, har yana bige mani ƙafa ya nufi bedroom ɗina da gudun masifa.

Ihuuu na sake kurmawa, cikin wata irin gigita, domin har faratan ƙafar shi sun yakushe ni a ƙafa, lokaci da kuma na sulale ƙasa a sume, a lokaci guda kuma cikin nawa yayi wani irin juyi da hautsinawa, sannan ya dunƙule waje guda ya cure, sai kuma naji ya wani irin saki, sakamakon razana da nayi, sai ga jini shaaa yana biyo tsakanin cinyoyi na da gudu wani na korar wani.

Daidai lokacin da idanu na suka kai kan jini ne, wata irin gigita ta sake kama ni, saidai duk yanda naso inyi controlling kaina kasa iyawa nayi.

Ruf! Idanun nawa suka idasa rufewa, daidai sa'ilin da Afnan da Nihal suke rige rigen shigowa sashen nawa...








~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

*Page ~83~*

*************************

Rige rigen kaiwa gare ta suka shiga yi, hankalin su idan yayi dubu ya tashi.

Basu ƙara gigice wa ba, sai da suka ga yanda jini yake malala daga ƙarƙashin Suhan ɗin.

Ihu sosai Afnan ta saki; "Innalillahi Aunty Suhan lafiya dai ko? Me ya faru?" take ta jero ma Suhan ɗin tambayoyi cikin kuka, ko kula ma bata yi ba, da yanda Suhan ɗin take kwance samɓal ba numfashi.

"Kira Yaya, Afnan yi sauri" Cewar Nihal ɗin itama, da duk ta gigice, zube take kawai ƙasa kusa da kan Suhan ɗin, ta tallafo kan nata zuwa bisa cinyar tata, sai fiffita take yi mata da ƴar fingilar rigar baccin tata.

"Aunty Nihal na baro waya ta ɗaki" Afnan ɗin ta faɗa da ƙarfi tana goge ƙwalla.

"Nemo wayar ta maza Afnan bata numfashi fa..." Cewar Nihal ɗin.

Ko bari Nihal ɗin ta ƙarasa maganar Afnan batayi ba, ta bazama da gudu bedroom na Suhan ɗin.

Cen bisa gado ƙarƙashin fillow ta hango wayar, ai da sauri ta latsa tana mai kiran Yayan nata.

Saidai duk kiran da tayi ta mashi ƙin shiga wayar tayi, da gudu ta fito falon tana faɗa ma Nihal ɗin taƙi shiga, kuka take yi sosai, ganin Suhan ɗin kwance kaman gawa.

"Ɗauko ruwa Afnan, ɗauko ku zuba mata please"

Da gudu Afnan ɗin ta juya zuwa kitchen. Bottle water ta ɗauko na Faro, tun kafin ta ƙara so ta ɓalle murfin.

Sheƙa mata ruwana suka shiga yi, Amman ko gezau bata yi ba, gashi har kawo yanzu jinin da yake malala bai tsaya ba.

Nan fa suka sake ruɗewa, sai koke koke suke cikin falon, har yanzu Suhan samɓal take, alamun babu rai a tattare da ita.

Afnan ta kai gwauro ta kai kari, sun rasa me zasu yi, wayar Suhan na hannun ta, tana ta faman danna mashi kira, Amman taƙi shiga.

Girgiza ta Nihal ɗin keyi, tana mai faɗin; "Aunty Suhan ki tashi DAN Allah, mun bani, ki tashi kar ki mutu, me ya faru dake? Wa yayi maki haka? Ki tashi..."

"yauwa ta shiga" Cewar Afnan da ƙarfi, ai da sauri Nihal ɗin ta miƙe, tana mai matsawa da gudu gaban Afnan ta fizge wayar.

"Assalamu Alaiki Ya Habibty, Good morning Sweet Janam, how is your night? missing me?" duk ya faɗa lokaci guda, yana mai sakin murmushi, dan ya shirya ma jin daɗaɗan amsar ta.

Kukan da yaji an rushe dashi ne a cikin wayar, ya sanya shi hantsilowa daga bisa gadon ba shiri, yana mai cewa" What happened Suhan? Tell me now, ki dena kula, me akayi maki ne?"

Saboda tsabar ruɗewa, ya ma kasa tsayawa ya tantance ba muryar Suhan ɗin bace.

" Yaya Nihal ce! Aunty Suhan ɗin.." sai kuma ta kasa idasa wa.

" Look Nihal tell me me ya faru? Ina Suhan ɗin? Me ya same ta? Ki faɗa man mana, ina sauraren ki ɗan Allah Nihal kiyi magana, me ya samu Matata? Ina take?"

Ya jero mata tambayoyin lokaci guda, yana mai buɗe ƙofar ya fice zuwa falo da sauri

"Yaya Aunty Suhan ce, bamu san me ya same ta ba, mun dai jiyo ihun ta, kafin muzo, sai muka tadda ta kwance ƙasa cikin falo jini na zuba a jikin ta, kuma bata numfashi tun ɗazu muke kiran....."

"Enough! Ya isa nace Nihal, wa ya taɓa man mata? Me kuka yi mata? Tun ɗazu uban me kuke baku kaita asibiti ba? Sai ta mutu? Sai kun kashe man ita? Garin yaya ma akayi hakan ta faru? Bayan jiya lafiya lau muka kwanta, Nihal kiyi magana, tun kafin in saɓa maki"

Jin tashin hankalin da take ciki, sai ya hana ta magana, kuka ne mai ƙarfi ya ƙwace mata, dasa guiwoyin ta tayi ƙasa, tana mai sakin tsumammen kuka. Shi kau gogan sai surfa bala'i yake yi, har ma ya buɗe falon ya fice harabar gidan bai sani ba.

Da sauri Nihal ta ɗauki wayar daga ƙasa da Nihal ta sake ta.

"Hello Yaya!"

"Lil zaman me kuke yi da ita a gida haka? A cikin wannan situation ɗin? Sai ta mutu? Jini fa kuka ce yana zuba a jikin ta, saboda baku da hankali, shine kuka sanya mata ido, Afnan! Nace ku kira mudi ku kaita asibiti yanzu, bansan jin komai ku wuce nace!" ya ƙarshe cikin ƙaraji da ɗaga murya, barorin da ke kai komo cikin harabar gidan, suna ta kallon shi, saidai sanin ko shi ɗin wanene, saidai kawai su russunar da kansu zuwa ƙasa, cikin girmamawa da ladabi, sannan su wuce, bai ko kula su, bai ma san suna yi ba, inda motar shi kawai take ajiye ya zarce.

Da gudu ya isa ga motar, yana mai zura makulli ya buɗe ya shiga, sai da yayi mata key ne, sannan ya tuna a inda yake, da kuma dalilin zuwan, bayan hakan ma, babu wanda yasan halin da ake ciki, balle ma asan tafiyar tashi.

Zai iya tuƙi a haka kuwa? Cikin wannan halin da yake ciki?

Kashe motar yayi, yana mai fitowa da sauri, ya nufi sashen da su Dad da Alhaji Auwalu suke ciki.

Da ƙarfi yake knocking kaman wani zarrare, gani yake Dad ɗin nashi yayi nawar buɗewa, kaman ya ɓalle murfin sashen yake ji, sai sauke ajiyar zuciya da numfashi yake yi.

"Ba dai ɓari Suhan tayi ba? Baby na! Shikenan na rasa baby na? Unborn ɗina? Meyasa na taho? Ƙila da ina nan, hakan ba zata faru da ita ba, zan bata cikakkiyar kulawa, kaman yanda ya dace. Wanene yayi maki haka Suhan? Me ya faru dake? Wa ke bibiyar rayuwar ki? Tabbas wanda ya saka ɓawon Ayaba a sahen nasu rana, shi ne ya sake harar Suhan ɗin, bayan anga baya nan, in ko haka ne, lallai ya taka babban kuskure, cikin nashi da yake ji dashi, kaman tsoka a miya? "

Duk cikin zuciya yake wannan tunanin, yayin da ya goya dukkanin hannuwa nashi a baya, yake takawa daga kusurwa zuwa wata kusurwar dake harabar wajen

Ƙarar buɗe ƙofa ne, ya sanya shi zabura, da sauri ya nufi ƙofar

"Dad!" ya furta da ƙarfi, cikin wata irin murya, daga ji zaka iya fahimtar halin da yake ciki na tashin hankali

"Son what happened lafiya dai ko? Irin wannan bubbuga ƙofa haka? Baka koma ka kwanta ba?"

Cewar Dad ɗin, wanda yake tsaye da Jallabiya fara sol da kuma casbaha a hannu.

"Dady Suhan ce, Suhan Dady, baby na Dady, Suhan bata lafiya, Dady tafiya zanyi yanzu please Dady allow me"

Ya furta, zuciyar shi na mashi wani irin suya, idanun nashi kuwa kaman garwashin wuta.

A hankali Dad ɗin ya kama mashi hannu, zuwa cikin sashen nasu, duk da shima hankalin shi yayi ƙololuwar tashi, irin wahalar da Suhan ɗin tasha, yanzu ace ba cikin, ai akwai damuwa, ba ga Suhan da Al'ameen kaɗai ba, ga kowa ma dake cikin gidan.

Bakin kujera ya shiga zaunar dashi, kaman ba zai zauna ba, sai kuma ya zauna, yana mai kai hannu zuwa kwarmin idanun nashi, ya shiga goge wasu siraran ƙwalla.

Da kallo Dad ke binshi, lallai Al'ameen ya ƙwallafa rai ga Suhan da abunda yake cikin ta.

"Son ka natsu kayi bayani, me yake faruwa ne a cen gidan? Dama bata lafiya ne?"

Girgiza kai ya shiga yi "Dad lafiyar ta lau, akwai dai abunda ke faruwa, ga su Nihal cen sun nufi kaita asibiti, Dad zan tafi, ba zan iya zama ba, bansan a halin da take ciki ba..."

"Assalamu Alaikum" sallamar Alhaji Auwalu, ita tayi sanadiyyar maida kallon su gabaki ɗaya gareshi.

Amsa mashi sallamar sukayi su duka, yayin da ya ƙara so ga ƙanen nashi, yana mai bashi hannu suka yi musabaha, sannan ya miƙa ma Al'ameen shima, yayin da shi kuma ya ƙara da gaishe shi.

Murmushi yake yi mashi, tare da amsawa, duk da zai iya jiyo maganganun su, kafin ya ƙara sa fitowa.

"Me ya faru ne Mustapha?" cewar alhaji Auwalun

"Yarinyar nan ce Suhan ce bata da lafiya, bata jin daɗi, shine ya tada hankalin shi, akan lallai sai ya tafi, ni da gani nake, kaman ya haƙura kawai, tunda Bilal na cen, sai ya aiwatar da komai, a dai samu a ƙarƙare zancen nan yau.

Girgiza kai Alhaji Auwalu ya shiga yi.

"a'a ba za'a yi haka ba, kai Ameenu tashi kaje, Allah ya tsare hanya, je ka wajen matar ka, ya fi wannan muhimmanci, lafiyar ta ita ce, akan gaba, Allah ya tsare hanya" ya faɗa shima, cikin jimami da alhini.

Zumbur ya miƙe, yana mai ɗaga ƙafa da sauri ya shiga takawa da niyyar barin ɗakin, ya manta ko sallama ma bai yi masu ba, har ya dakata, sai kuma ya shiga cusa kai zuwa ficewa waje.

Wannan karon ma da gudu ya isa ga motar tashi, wanda ko parking daidai baiyi ba, ya faɗa yana mai yi mata key.

Shi in ma ba dan Alhaji Auwalu da ya ambaci Bilal ba, ya ma manta dashi.

Kira ya shiga jera ma su Nihal ɗin, yayin da su kuma suke cen suna taga tagar sanya ta mota, komai na jikin ta ya saki, ba numfashi a tattare da ita. Kuka kawai Nihal ke yi, tana faɗin ki tashi Suhan, na bani da Yaya idan kika mutu, dan Allah ki tashi.

Kowa na gidan ya firfito, harda Mudin suka kakkama aka saka ta haka a motar, jini na yarara, tun daga sashen Suhan ɗin, har zuwa parking lots ɗin.

Gudu suke sharara wa su biyu, yayin da mudi ya nufi asibiti, shi kuma Ya Ameen ya nufo Abuja.

A kan hanyar shi ne ya latsa lambar Bilal, tayi ta ringing bai ɗaga ba, saboda haka ya tura mashi saƙo.

Akwai akai ya kan daki kan motar; "Suhan, wa yayi maki haka ne? Wanene shi? Wanene ya ja man asarar ciki?"

Babu mai bashi amsa, dalili kenan da ya sake take kan motar, wasu da yake wucewa a hanya, har sukan saki tsaki, ko ma su ambata zagi a gareshi, shi dai ba tasu yake yi ba, hankalin shi na kan ya isa yaga halin da matar tashi ke ciki.

**********

Da gudu aka gungura ta bisa keken marasa lafiya, yayin da wasu likitocin suke aikin maƙala mata oxygen, wasu kuma suna ƙoƙarin ɗaura mata ruwa,sai dai ruwan ma baya shiga jikin nata.

Kuka sosai suke yi su Afnan, duk sun fita hayyacin su. Tun dai da aka shiga da ita A&E Sam hankalin su bai kwanta ba, gani suke kaman za'a fito ace masu ba ta.

Wayar Suhan ɗin ce ta ɗauki ruri

Da sauri Afnan ɗin ta ɗaga, muryar Bilal ce, shima hankali tashe yake tambayar suna ina?

Kwatancen asibitin Afnan ɗin tayi masu, ita Nihal ma ko magana baya iya yi tashin hankalin da za'a fuskanta kawai take zullumi, muddin Ya Ameen ya iso. Domin daga tasowar shi, kawo yanzu, yayi kira ya kusa hamsin.

Ko minti goma cikakke ba'a yi ba, sai ga Bilal a ruɗe, saɓe da babyn shi a kafaɗa, Ummi na gefen shi, suna ta zuba uban sauri.

Da Nihal suka fara cin karo, ta ci kuka ta ƙoshi, idanun nan sunyi luhu luhu, abun ka da fara.

Kasa amsa masu tayi, sai cen ne suka hango Afnan, tana kai gwauro ta kai mari.

Kusa da ita suka ƙara sa, ita ɗin ma dai hakan ce, fuskar nan zawur, kaman wadda aka daddala ma maruka.

"Garin ya haka Afnan?" Cewar Bilal

"Yaya wallahi muma. Bamu sani ba, a haka muka iske ta, Amman dai da gani wani abu ne ya razana ta, tunda sai da tayi ihu sosai, jikin nata kuma, ba alamun cewa faɗuwa tayi.

Da sauri Bulla ɗin ya miƙa ma Umme da take tsaye gefe Lil Ameen, yana mai wucewa da sauri zuwa Office ɗin Dr ɗin direct.

Ya ɗan jima Dr ɗin bai fito ba, sai daga baya ne ya fito, zufa sharkaf a jikin shi.

Sai da ya cire hand gloves nashi, ya sanya sanitizer ya ɗauraye hannun shi, sannan ya koma ya zauna, yana mai kallon Bilal.

"Ranka ya daɗe barka da zuwa, ya masu jiki kuma?" cewr Dr ɗin.

"Lafiya lau Dr. Ya condition na Suhan Dr?" cewar Bilal ɗin.

Ɗan girgiza kai Dr yayi, yana mai tattara natsuwar shi duka ga Bilal ɗin.

"Haƙiƙanin gaskiya Yallaɓai ba zamu iya cewa komai ba tukunna, abokan aiki na, suna iya ƙoƙarin su, wajen ganin an ceto rayuwar ta, da ta abunda yake cikin cikinta, Amman dai maganar gaskiya, da akwai kamar wuya, idan zamu iya bada tabbacin zata tashi, domin kuwa ta samu heart attack ne lokaci guda, abunda kuma ba'a so ga mai ciki, wannan shi ne yayi sanadiyyar suman ta, wanda har kawo yanzu da nake maka magana bata farfaɗo ba"

Idan hankalin Bilal ya kai million ya tashi, har baisan lokacin da ya miƙe ba, yana mai haɗa zufa.

"Dr please, ku taimaka ku ceto rayuwar ta, kada ta mutu Dr. Dan Allah! Na san kuna iya ƙoƙarin ku, Amman ku ƙara"

Cewar Bilal, wanda yake tsaye kan ƙafafun shi, ya ɗan ranƙwafa, zuwa ga Dr ɗin, ko zama ya gagare shi.

"Ɗan murmushi Dr ɗin yayi; "Zamuyi iya ƙoƙarin mu insha Allahu kada ku samu damuwa, insha Allahu zata miƙe, Amman cikin biyu sai anyi ɗaya, ko dai ita, ko kuma abunda yake cikin cikin ta!"

Da hanzari Bilal ya sauke kai ƙasa, yana mai hangen wayar shi dake cikin hannun shi tana sakin haske, alamun ana kira, kuma ya san Al'ameen ne, a yanda ya san halin shi, ba zai taɓa ita ɗauka ba, balle har ya sanar dashi halin da ake ciki, tuƙi yake yi, komai zai iya faruwa.

Hannu Bilal ya miƙa ma Dr yana mai yi mashi godiya, tare da sake roƙon shi.

A reception ya tadda su duka, hadda Umme da ke ta famn jinjiga Lil Ameen dake bisa kafaɗar ta, yayin da Nihal take zaune ta zuba uban tagumi, sai Afnan da take tsaye ita kuma ta haɗa kai da bango, sai shesshekar kuka take yi.

Babu madadin Suhan a garesu, ba zasu taɓa samu ba, Suhan macen kirki ce, Ya Ameen na masifar ƙaunar ta, ta ina zasu fara rasa ta? Ya zasuyi? Wanne hali Umma da Yaa Ameen zasu shiga? Balle a gangaro zuwa kansu? Kukan nata ne ya cigaba da tsananta, yayin da Umme ta matsa kusa da ita, tana bata baki.

A sanyaye Bilal ya wuce zuwa cen gefe ya samu kujera ya zauna, da idanu Umme ke tambayar shi, ɗan girgiza mata kai ya shiga yi, wanda karaf sai a idanun Nihal.

Ai wani kuka ta kuma fasawa, tana mai cewa "Shikenan Suhan, kaddai ace kin tafi kin barmu, ya zanyi da Yaya? Taya zan fara sanar mashi babu hannu na a ciki?"

Gabaki ɗaya mutanen da suke wajen suma zazzauna, sai suka kuma shiga kallon su, wasu na tausaya masu, wanda sun gane ga dukkan alamu, wadda ke cikin halin rashin lafiyar tana da muhimmanci a garesu.

**************

Karaf! Gam! Ƙiiiiiiii...... Wata irin mahaukaciyar ƙara ce ta karaɗe ilahirin wurin. Da hanzarin tsiya ya take burki, yana mai fitowa a zuciye, a sukwane kuma yayo kan motar Ya Ameen ɗin, wanda shima dan dole ya ja burki ya take.

"Malam kai mahaukacin ina ne haka? Lahira zaka ne da kake ta wannan uban gudun? Wai ku mutane Meyasa baku da hankali ne? Kenan da ka kashe mu fa? Kace ma iyalan mu me? Ko ɗan baka da iyalan kuma baka san darajar su ba? In baka da su ai na tabbata akwai iyaye ko? Ko suma asara suka yi ne na haihuwar ka? Tunda har zaka iya aikata abunda zaka ja masu zagi, yanzu gashi da ka bugar man mota ta lalace, wallahi sai ka biya ni, ba zan taɓa ɗaukar asara ba.

Mutumen da ake ta rirriƙe shi, yana fuzgewa, tare da sakin baƙaƙen maganganu ga Ya Ameen ɗin, wanda ya haɗa kanshi da jikin motar ya lumshe idanun shi, ya san shi ke da laifi, shi ya buga ma wancen mutumen motar shi, saboda haka ne ya zauna cikin motar bai fita ba, yana mai sauraren kalaman mutumen nan, wanda yake ta danƙara mashi zagi, ba ma shi kaɗai ba, har da iyayen nashi.

Sai rirriƙe mutumen ake yi, yana mai fuzgewa, gami da cewa "Wallahi ku sake ni, sai ya biya ni asara ta, in ba haka ba, in bugi kuɗi na wallahi, tun ɗazu yake mana overtaking, mun ƙyale shi, shine bai ishe shi ba, sai da yazo ya buga man mota, banza dashi kaman wani makaho, ya bar ganin yana cikin wannan motar, wallahi yanzu haka ma aro ta yayi, baisan darajar ta ba, shiyasa baya lallaɓa wa yake wulaƙantawa"

Wani daga gefe ne yace mashi, "Haba kai kuwa Malam, ka duba duk zagin da kayi mashi, bai fito ba, saboda kada hayaniyar tayi yawa, ya dakata a cikin tashi motar, Amman kai sai zagin shi kake harda ma iyayen shi, wanda hakan ba shine masalaha ba"

"Kai malam dakata, ba ruwanka, dan ba motar ka bace? Kasan ko nawa na siya mota ta? Hakanan wani banza yazo ya lalata mun? Nace ko ka cikasa man ne da zan siya motar? Balle kazo kana gaya man ƙarya da gaskiya? Irin ku ne masu neman na adawa a baki, ƙanzagi kake mashi dan ya ɗebi wani abu ya baka ko? Ku daga kunga mutum a jibgegiyar mota, sai kuyi tunanin duka kenan, yanzu haka ma holoƙo ne." yana yi yan fiffizgewa, tare da kunfar baka, kaman Zaizo kan motar Ya Ameen, ana rirriƙe shi.

*"Ku ƙyale shi, yazo yayi abunda zaiyi, duk abunda yake ganin zai iya yazo yayi"*

Cewar Ya Ameen, wanda ya fito a hankali, yana mai rufe motar tashi ya jingina da jikin motar, yana mai harɗe hannuwa a ƙirji.

Duk da jallabiya ce a jikin nashi, kuma fuskar nan Sam babu annuri, gashi ta cenza kala zuwa ja, hakan bai hana shi yin wani irin kwarjini ba.

Dafe baki wanda suka sanshi suka fara yi, daga ciki ma, har akwai ma'aikatan da suke ƙarƙashin kamfanin shi, wanda sun sanshi farin sani, yana masu alkhairai, tare da kyautatawa iyakar iyawar shi. Yanzu ma suna kan hanyar su ne ta komawa bakin aikin su.

A hankali mutumen nan yayi shiru, yana mai fizge hannun shi daga cikin na waɗanda suka riƙe shi, sai kuma ya saddar da kai ƙasa, yana mai cewa "Yallaɓai dan Allah kayi haƙuri, wallahi ban san kai bane, wallahi tallahi, dan Allah kayi haƙuri"

Ɗan murmushi Al'ameen ya saki, sai yanzu ne ma ya gane mutumen, ya taɓa zuwa ya same shi, akan ya taimaka ya bashi aiki, kaf gidan su, a ƙarƙashin shi suke, Amman maimakon Ya Ameen ya bashi aiki, sai ya bashi maƙudan kuɗi, yace yaje ya ja jari, wanda zai riƙe kanshi da iyayen shi da ma iyalan shi, da duk wani dake ƙarƙashin shi, dalili kuwa shine ;idan aiki ya ɗauke shi, sai ƙarshen wata ne za'a biya shi, kafin nan matsaltsalun sun sake lunkuwa, Amman idan kasuwanci kake yi, kullum kana cikin juya kuɗi ne.

A hankali ta shiga takawa zuwa gaban motar Ya Ameen ɗin. Mutane dai sai suka koma kallon su kuma, suna masu sakin maganganu ƙasa ƙasa, ai ga irin ta nan, wanda yaso wulaƙantawar ma, ya fishi a komai.

Ƙoƙarin duƙawa yake yi, Ya Ameen ya dakatar dashi, yana mai cewa "Allah ya kiyaye gaba, nawa ne kuɗin gyaran ɓarnar da nayi ɗin?"

Girgiza kai mutumen yayi, kanshi a ƙasa "Allah ya sauwaƙe Yallaɓai, Allah ya kyauta in karɓi ramuwa daga gareka, nayi danasani, saurin fushi shine sila, wallahi bansan kai bane, da ban fara ba ma, ko da kuwa damaged motar nan tayi, ba zan iya amsar ko sisin kwabo ba, daga hannun ka, dan Allah ka yafe man, na roƙe ka"

Sake girgiza kai Ya Ameen yayi.

"Ba komai na yafe maka, kaima kayi haƙuri, ina cikin wani uziri ne, Shiyasa na kasa controlling kaina. Amman komai ya wuce, Allah ya kiyaye hanya"

Yana gama faɗar haka, ya miƙa mashi hannu suka yi musabaha, sannan ya faɗa motar tashi, yana mai yi mata key, dan dole ya shiga lallaɓawa a yanzu, saboda gudun sake samun wata matsalar, wadda har ta kan zama barazana ga saurin da yake yi.

Bayan tafiyar shi ne, mutumen ya ba mutane dake wurin labarin Ya Ameen ɗin.

Nan fa aka shiga shi mashi albarka, hadda waɗannan ma'aikatan nashi, suma suna sake faɗin kyawawan halayen nashi, da Alkhairin shi garesu, wanda shi baima gane su ba.

Jiki a mace cike da kunya mutumen yaja motar shi, yana mai barin wajen, nadama cike da zuciyar shi, yasha alwashn nan gaba, ko da kashe shi za'a yi, ba zai ƙara gigin yanke hukunci cikin fushi ba.

*********

Babu wanda ya san halin da cen gida ake ciki, dangane da Suhan, kuma su Alhaji Auwalu sun yanke shawarar ba zasu faɗa ma kowa ba, har sai an gama abunda ya kaisu, gudun sake ɗaga lokacin zaman. Sannan sunsan Umman Suhan ɗin ba zata iya jurewa ta zauna a wajen ba.

Falon yayi tsit, baka jin komai sai ƙarar na'urar sanyaya ɗaki, kowa ya natsu, ya bada hankalin shi ga mai martaba.

Wannan karon hada Baba Waziri aka zo, wanda ko haɗa idanu da Umma ya kasa, haka itama Hajiya Kubra, Amman akai akai, ta kan ɗaga idanu ta kalli baba waziri, wanda take ji, kaman hada shi cikin ummul'aba'isin jefa rayuwar ta, da ma dukiyar tata cikin garari., sannan sai Alhaji yaro

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment