Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wurin zuwa gida, ba yanda ba'a yi da ita ba, tace da safe zata koma gidan, shima saboda tana da sauran baƙi ne.

Ko a motar ma da hannu ɗaya yake driving, ɗayan yana cikin nawa yana murza shi a hankali. Afnan dake baya tana lura da hakan, saidai bata ce komai ba, sai murmushi da take saki, ita dama ai ta daɗe da hango tarin Ƙaunar Suhan ɗin a idanun yayan nata, to saidai ganin bai furta ba ya sanya ta ɗauka ko haukan yarintar ta ne.

Bilal ma gida ya wuce, yana mai danna ma cen ɓangaren su Ummin tashi waya domin jin ya jikin. Shaida mashi sukayi da sauƙi, har yanzu dai ba'a sauka ɗin ba. Yayi niyyar tafiya gobe da safe suka dakatar dashi da cewa jikin ai da sauƙi sosai, idan akwai buƙatar su kira shi ɗin zasu kira shi.

Afnan da su khadee sashen su suka nufa kai tsaye, inda ni da Ya Ameen kuma muka shiga sashen Kaka zuwaira, domin sanar da ita halin da ake ciki.

Itama tayi murna da jin jikin da sauƙi, nan ta ƙara jan hankalin mu akan mu zauna lafiya mu mugunta juna, san na tayi mana adduo'i sosai, tare da fatan samun zuria ɗayyiba.

Tin a gaban kaka zuwaira ɗin ya kamo hannu na da zamu fice, daƙuwa ta Di ga dunƙula mashi, shi kau yana ta murmushi yake cewa "To kin gani dai ni ita na zaɓa, ke kuwa ki koma ma tsohon mijin ki, kinyi kwantai" ba ita ba har ni saida nayi murmushi cikin jin kunya. Haka na shiga bin shi har zuwa sahen namu.




Yana buɗe ƙofar muka shiga, kawai sai Naji caraf ya ɗage ni zuwa sama ya shiga juyi dani sosai, kaman masu rawa.

Dariya nake ƙyalƙyala wa cikin jin kunya da murna. Shi kanshi ya lura da yanda nake cikin annashuwa, kuma ko raba ɗayan biyu baya yi akan cewa labarin samun Rayuwar Hafsat ne da nayi.

Bai dire ni ko ina ba sai saman gado.

A hakan ma bai kyale ni ba, sai kawai Naji ya zare hijab ɗin yana mai bina bisa ga don ya danne, nauyin shi kaf ya sakar mani. Ni kau sai nishi nake ina mutsu mutsu. Wai dam a haka Ya Ameen ɗin yake? To menene dalilin da ya sanya da ake kiran shi miskili ne?

Ganin na gaji har na fara tsuwwar wahala ne ya sanya ni ɗaga ni, yana mai gyara rigar shi ya shiga kashe mani ido ɗaya da na kula kaman al'adar shi ce ta zaulaya.

Toilet ya wuce kai tsaye, yayin da ni kuma na miƙe zaune ina ta maida numfashin wahala.

Ɗakin ya dawo hannun shi duk ruwa, kallon shi nake ƙasa ƙasa, sai kawai naji ya yarda mani sauran ruwan dake hannun shi. Ajiyar zuciya na sauke ina mai ɗan zabura, ba tare da wata damuwa ba ya shiga kwaɓe kayan dake jikin shi.

Ganin haka na zabura zan fice zuwa falo ga sanya hannun shi suka ya maida ni kan gadon.

"Ba inda zaki baby zauna nan, ni fa mijin ki ne" Abunda ya faɗa kenan, yana mai zame dogon wandon dake jikin shi, ya rage daga shi sai boxer, tunowa da nayi abunda yayi mani jiya ne ya sanya ni sauke kaina ƙasa cikin tsabar tsorata,

Ganin hakan da yayi ne ya sanya shi takowa zuwa gaban gadon. Durƙusawa yayi guiwoyin shi ƙasa, ya ranƙwafo sosai ta yadda zan iya ganin shi.

"Ni dake mun zama ɗaya Hayateee tin jiya, na yarda kece rabin rayuwa ta, idan babu ke bansan irin halin da zan iya shiga ba, kiyi mani alƙawarin ƙauna da kulawa fiye da yanda zan baki dear promise me" ya faɗa yana mai miƙo mani hannun shi alamun idan na yarda in kama.

Kaina a ƙasa still na miƙa mashi hannun, runtse su yayi wuri guda, zan iya jiyo tashin dake shimfiɗa a tafin nashi hannun, nan ma ajiyar zuciya na sauke a hankali. Lokacin da ya miƙe zuwa zaune bisa gadon, yayi amfani da dukkanin hannayn shi wajen kwanto da kaina zuwa bisa cinyar tashi.

Baya da riga, illa kwantaccen gashin ƙurjin shi da yake Zara Zara baƙi siɗik bisa murzazzar farar fatar da gani hutu ya daɗe da ratsa ta.

Ru tae idanu na nayi gam, Kunyar shi nake ji har zuwa tafin ƙafar tawa, ba zan iya jurar kallon shi a haka ba, wani irin kwarjini yake yi mani, har yanzu ina iya jiyo wannan abun dake tunatas dani Ya Ameen ba sa'an aure na bane, duk kuwa da cewa yanzu na gane ko ni ɗin wacece.

Hannuwa na duka ya kamo tana mai ɗora su bisa ƙurjin nashi daidai saitin zuciyar shi.

Fatar hannu na, da fatar ƙurjin suka haɗu suka bani wani irin shork. Kaman yau ne rana ta farko da na fara taɓa jikin nashi.

"tin ranar da na fara sonki Suhan, tin ra ar ɗana buɗi ido na ganki, nan ɗina bai dena bugawa ba, da sonki nake kwana dashi nake tashi, hankali natsuwa tarbiyyar ki, kawaici haƙuri da kuma kamala sune suka haɗu suka yi tasiri a kaina, *Ina SONKI Suhana ki daure ki soni ki ƙaunci Muhammad Al'ameen ko zai samu salama a cikin zuciyar shi*

Kalaman shi sun mani nauyi, sunyi matuƙar tasiri a cikin zuciya ta, lallai dole in sauke kunya dole ne in ba mijina dukka in kulawa ta, Ya Ameen ya cencenci fiye da haka a wuri na, har ina jiyo tarin ƙaunar da nake mashi kaman tafi ma wadda yake mani.

Wayar shi ce tayi ruri. Bai tashi ba ya sanya hannu ya ɗauko ta. Sunan friend ya gani yana yawo a scream ɗin. Ɗagawa yayi yana mai mamaki, duka yanzu fa suka rabu.

"Bello Friend how far?"

Sai kuma Naji yayi shiru, cen kuma sai Naji yace "Kai A big congrat to you Friend kace mun zama Dad, to Allah ya raya Allah ya ɗayyaba, ina maka murna, ga Wife nan ma tace ayi maka murna, sai ka shigo ɗin" yana gama faɗar haka ya datse kiran, ko bai sanar dani ba, kalaman shi sun shaida mani cewa Ummin Ya Bilal ɗince ta haihu.

Da murmushi yake shaida mani.

Nima cikin jin daɗi nake mashi barka, ko ba komai yau zamu kwana cikin farin ciki marasa misaltuwa. Komai yai ji shi nake daidai zam.

Kalaman ya Ameen ɗinne suka saka kunya kama ni, shaida mani da yake yi cewa "Mu zamu fi su ƙoƙari Sweet heart, mu ƴan uku zaki haifa mana kinji?" ya faɗa yana mai kashe mani ido guda kaman yanda ya saba.

Bansan na ru gume shi ba, na shiga cusa kaina cikin jikin nashi, shima murmushi ya saki, yana mai miƙewa a hankali ya jawo filo yayi mani matashi dashi kaman yanda nake a bisa cinyar tashi.

Wanka ya shiga, ya daɗe a ciki, sannan ya fito ɗaure da towel a ƙugu. Nidai sai kallon rashin Kunyar Ya Ameen nake yi. Ikon Allah, wai ashe shi ɗin miji na ne,namiji mai kyau asali tare da cikar haiba.

Katse mani tunanin yayi da cewa ga ruwan wanka na cen, bam cire kayan ba haka na tashi na nufi Toilet ɗin, da kallo ya bita, yana sakin murmushi a hankali. Kunyar ta na ƙara burge shi, ko ba komai hakan na nuna mashi cewa bata rayu da maza ba hakan ne ya sanya bata saba dasu ba.

Ko da na fito wankan baya cikin ɗakin, sai nayi tunanin ko yana falo.

Mai da turaruka masu taushi na shafa, haka na sake yin using wannan turaren, ba tare da na san ma wai menene amfanin shi ba.

Ina zura doguwar rigar bacci iya cinya be ya shigo. Saurin ida Sanyawa nayi, ina mai juyowa ta inda yake tsaye da ƙaton tray cike da kayan ciye ciye.

Takawa nayi zuwa inda yake tsaye haɗi da karɓar tray ɗin, ina mashi sannu. Cen gaban gado bisa chinese carpet na ajiye. Ina ɗagowa Najini bisa ƙurjin mutum.

"Kin yi kyau Wife, dole in bada tukuicin wannan kyau ɗin."

Sunsunar jiki na ya shiga yi ta ko ina yana kai hancin shi, yamutsa ni yake sosai, daƙyar na kwaci kaina ina maida numfashi, idanun shi har sun kaɗa sunyi ɗan ja, zama yayi gefen gadon shima yana mai bina da mayataccen kallo. Ganin hakan da nayi ne gabana ya shiga faɗuwa, ba dai yanda yayi mani jiya haka zai maimaita yau ba?

Ai sai tsoro ya shige ni, jikina ya fara rawa, ganin hakan da yayi ne ya sanya shi sauka ƙasa yana mai faɗin "Dear yi wa nake ji sosai, serve me please"

Nima haka na zauna jiki babu kwari, na shiga zuba mashi fresh milk da naman gasassun kaji da tsiren da na gani, daga gani yanzu ya fita yaje ya siyo su. Sai chips da na zuba mashi kaɗan, ni kaina yunwr nake ji, Amman kunya ba zata barni in wani ci abincin ba sosai, shi yake bani da kanshi, yayin da kaina yake bisa ƙurjin shi lafe, duk yanda naso in kwaci kaina ya hana, duk yabo ya kanainaye ni, na kasa koda kwakkwaran motsi.

Da kanshi ya kashe kayan zuwa kitchen. Ya dawo ya same ni kwance bisa gado na duƙunƙune sai muzurai nake.

Murmushi kawai yayi, yana mai ƙudurta cewa ba abunda zaiyi mata, ai sai kuma ta warke sosai. Saida ya kashe ko ina ya kulle. Sannan ya dawo yana mai zare jallabiyar ya rataya ta cikin sip, sannan ya zare singlet ɗin itama, ya rage daga shi sai boxer, a haka ya hauro bisa gadon ya same ni, zuciya ta kaman zata tsaho ƙirji na ta fito.

Ga mamaki na, rungume ni yayi yana mai faɗa mani wasu kalamai masu nauyi da suka girmi kwalwa ta, saida ya gama yamutsa ni sosai son ranshi, sannan ya kuma rungume ji yana mai tofa mana addu'ar barci. Daren ranar dai haka nayi shi cike da jin daɗi, bacci na nake cikin natsuwa kwanciyar hankali da annashuwa, kusan ma zan iya cewa tin da uwata ta haife ni a duniya, yau ne ranar farko da nayi bacci mai daɗin wannan. Har bana so ko alama inji jiki na zai rabu da nashi jikin da nake iya jiyo wani irin ɗumi da ƙamshi mai daɗi yana tasowa daga cikin fatar tashi......






°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°



~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


Addu'ar Kin shu'umci

اَللَّهُمَّ لاَ طَيْرَ إِلاَّ طَيْرُكَ، وَلاَ خَيْرَ إِلاَّ خَيْرُكَ، وَلاَ إِلَهَ غَيْرُكَ.
Allahumma la tayra illa tayruk, wala khayra illa khayruk, wala ilaha ghayruk.

Ya Allah! Babu shu'umci sai abin da Ka halitta, kuma babu alheri sai alherinka, kuma babu abin bautawa da gaskiya ba Kai ba.


>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~67~*

*Congatulation Sis Batula na kammala littafin ki _Ni da Malama ta_ Allah ubangiji yasa an kammala a sa'a. Saƙon da yake ciki muna fatan ya amfanar, kura kuran dake ciki kuma Allah ya yafe mana baki ɗaya. Allah ya baki ikon fara wani a sa'a. Ya kuma baki ikon rubuta mai amfani Batula. Ina yinki Over, ke da ɗaukacin Sisters na Golden Pen, Allah ya ƙara haɗa kawunan mu, ya tsole idanun maƙiya a kanmu. Ya ɗaukaka mu ya bamu ikon rubuta abu mai amfani, ba abunda zuciyar mu ta raya mana ba, wanda zai sanadin ɓata tarbiyyar wasu. Ameen Thumma Ameen*
°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


Haka muka kwana tare dashi yana nuna mani zallar ƙauna, duk da babu Abunda yayi mani, Amman hakan bai hana shi yamutsa ni ba, son ran shi.

Kunya yake sakar mani, hakan ce ta sanya saidai in sun ne kaina cikin jikin nashi, inda wata irin wutar ƙaunar junan mu ke ruruwa a zukatan namu.

Godiya ga Allah na sha ta kuwa, saboda sai yanzun ne nake gane cewa ashe Abunda Ya Ameen ɗin yayi mani ba'a kiran shi da komai sai ƙauna. Nayi imani da irin son da take mani, ko kwayar idanun shi na kalla ina iya hango tsantsar ƙaunar tawa tana yawo.

Shi yayi mana komai da safe, ko abincin cikin gida bai jira aka kawo mana ba, shi ya shiga kitchen da kanshi ya sama mana Abunda zamu ci, sannan ya koma bedroom ɗin yana mai taso ni bayan ya haɗa mani ruwan wanka.

Komai yake cikin natsuwa da aji yake yi, Ya Ameen daban yake a ko yaushe ba zan gaji da faɗa ba, saidai har yanzu zan iya hango jini na miskilanci yana yawo a cikin jinin jikin sa. Domin idan yana abu shi kaɗai, sai kaga kaman bai taɓa rayuwa da wani ba a rayuwar shi, saidai in ya tuno some moment ya kan saki murmushi sosai.

Nayi mamakin dana fito daga wankan na tadda ya ajiye mani kayan da zan saka, oho, kenan shi ne ya zaɓa mani da kanshi.

Yana zaune bakin gadon da system a gaban shi, hannun shi riƙe da waya yana amsa kiran Bilal da yake sanar mashi shi fa yanzu jirgin nasu zai ɗaga, zai je ya duba mai jego ne da baby Boy ɗin da aka haifa mashi.

Jikin nashi sanye da baƙar body hug wadda ta dace da kalar fatar jikin nashi.sai dogon wando har ƙasa na blue ɗin jeans. Ƙafar shi ba takalmi saidai baƙar safa. Yayi masifar kyau, ga gashin nan nashi da yasha gyara yayi kwance luf abun shi sai sheƙi da salƙi yake yi.

A hankali na kai zaune bisa stool ɗin ina mai idasa goge kaina dana wanke da wani irin shampoo mai ƙanshi da ni ban ma taɓa ganin shi ba. Lokaci guda ina mai satar kallon shi ta ƙasa ƙasa, domin yayi mani masifar kyau.

Peck naji an kai mani ta side ɗin kumatu na nadama. Da mamaki cike da kunya na ɗan waiwaya ina kallon shi cikin ido, sai kuma na sauke kaina ƙasa ina mai sakin wani irin ƙayataccen murmushi. Bansan lokacin da ya taso ba

Abunda ya ƙara burge shi dani kenan, ya idasa takowa zuwa gareni yana mai datse kiran, sannan ya ɗora wayar zuwa bisa mirror ɗin a hankali.

Miƙewa tsaye nayi, domin duk na takura, ina ma tunanin yanda zan iya cenza kaya, sannan in shafa mai a gaban shi.

Bansan lokacin da ya zauna bisa stool ɗin da na tashi kai ba, sai ji nayi kawai ya jawo ni zuwa bisa cinyar shi.

Banyi musu ba, domin ni kaina ya zuwa yanzu na tabbatar ma kaina cewa bana gajiya da shaƙar ƙamshin jikin shi mai daɗi, sannan da fatar shi mai ɗauke da wani irin sinadarin taushi.

A hankali ya shiga warware mani towel ɗin da yake ɗaure a ƙirjin nawa.

Saurin kai hannu nayi na kare, bai ce komai ba, sai a murmushn gefen baki daya saki, irin wanda yake yi idan abu ya burge shi.

Bai nuna ma ya kula da abunda nayi ba, ya kai hannu yana mai jawo man da zan shafa ya shiga matsawa a hannu. Da kanshi ya shiga bin ko'ina na jiki na da man yana shafa mani, lokaci guda kuma yana matsa turaren jiki shima yana cakuɗawa,cikin tafukan hannun nashi masu matuƙar taushi.

Kunya duk ta gama kashe ni, haka nake ta sunne kai yana bin ko ina da hannun nashi yana ɗan shasshafa wa da mammatsawa.

Ganin zai kama wata tashar ya sanya ni Miƙewa da sauri na zari kayan, wuf na faɗa toilet.

Miƙewa yayi yana mai sakin murmushi har fararen haƙoranshi na bayyana. Ɗan rungume hannun shi yayi yana daga tsaye, inda nabi na wuce yake kallo. sai kuma ya taka yana mai isa ga gadon ya ɗaukai system tashi da Phone tashi dake kan mirror ya fice zuwa falo.

Sai da na leƙo na tabbatar baya ɗakin sannan na fito. Ina mai idasa shafar, sannan na ƙara gyaggyara ɗakin.

Baisan lokacin da ya miƙe yana mai wara mani dukkanin hannun shi ba. A hankali nake takawa, cike da kwarkwasa da wata irin tafiyar da bansan lokacin da na koye ta ba,zuwa cikin ƙirjin nashi, bai wata wata ba ya maida hannun ya rungume ni tsam cikin jikin nashi, yana mai sunsunar kaina da na maƙale gashin sannan na ɗaura bandaner.

Munkai minti biyu a haka muna mai amsa saƙon zukatan namu.

Ƙarar kwankwaso ƙofa ne ya farkar damu daga duniyar soyayyar da muka Lula.

Sai da ya kaini bisa dining ya zaunar dani sannan ya isa zuwa ga ƙofar yana mai buɗewa a hankali.

Da kallo na raka shi. Hatta da tafiyar Ya Ameen abar kallo ce, ba tin yanzu na gane hakan ba. Kayan jikin shi sun amshe shi, su ne ma suka taimaka wajen fiddo da asalin kyawun halittar shi

Nihal ce ɗauke da wani ƙaton kwando, daƙyar take ɗauke dashi, sai nishi take saki, da gani dai yayi mata nauyi.

Fuskar shi ba wata walwala sosai yake amsa gaisuwar da tayi mashi.

Ƙoƙarin shiga take ya dakatar da ita da cewa "Menene nan?"

"Yaya break fast ɗinku ne, Mom ce tace a kawo maku"

"Wanene ya dafa?"

"Ni ce Yaya"

Ɗan murmushi ya saki, yana mai gyara tsayuwar shi.

"Ba zata ci wannan jagwalgwalon naki ba, ki ajiye ki shiga ki gaida ta, ki mayar da abincin na sama mana Abunda zamu ci"

Cikin kwalalo idanu take kallon shi, jim kalaman da ya yaɓa mata, to saidai wargi ma wuri yakeyi.

Jiki a sanyaye, zuciyar ta na azalzala tace "To yaya" tana mai ajiye basket ɗin ta raɓe shi ta shige ciki.

Sakin ƙofar yayi ya biyo bayan ta, sanin ko wacece Nihal ɗin, tsaye ya tadda ta nesa kaɗan dani, tana mai cewa "Good Morning"

Murmushi na saki, ina mai Miƙewa a hankali na shiga taka wa zuwa inda take. Batayi tsammani ba sai ji kawai tayi na rungumo ta zuwa jikin nawa ina mai cewa "Morning Sis Nihal ya gajiya?" ɗan sansaraƙwai tayi tana mai sakin dariyar yake.

A hankali na raba jikin namu ina mai cewa "Ki zauna mana"

Ya Ameen ɗinne ya katse mana maganar da cewa "No taje ta mayar da wancen abincin, zamu ci abinci ne" ya faɗa yana mai jawo mani kujera. Murmushi na saki wanda nasan sai ya tafasa mata zuciya sannan nace "Ayya Sis Nihal ai da baki wahalar da kanki ba, Yayan naki ai ya sama mana Abunda zamu ci, kinsan he's caring husband"

Maganar tawa tayi mashi daɗi kuwa, hakan ya sanya shi kamo ni yana mai zaunar dani bisa kujerar, sannan shima yaja ya zauna, yana mai ce mata "ki kulle ƙofar idan kin fita" ya faɗa yana mai haɗe fuska alamun baya son wargi.

Jiki a sanyaye ta juya tana mai nufar ƙofa tanayi tana waiwayen mu, har tana tuntuɓe da room Base. Shi kau Gogan har ya ja plate ya fara zuba mani abincin.

Har ta fice kaman zata saka kuka, dole ne ta faɗa ma Mom Abunda ke faruwa, idan ba suyi sa'a ba wannan ƴar duniyar yarinyar zata raba su da ɗan uwan nasu, dubi fa yanda yake faɗa mata magana, wai harma da sanar da ita ba zata ci jagwalgwalo ba, kenan ma ita ce mai yin jagwalgwalon. Bata san sanda kwalla ta shiga ziraro mata ba, tayi saurin gogewa saboda wurin masu aiki duk sun fito birjik kowa na aikin gaban shi. Sannan bata son a raina ta ko misƙala zarratin


Yana bani abincin yana mani fira, ba yanda banyi ba dashi ko loma ɗaya ce ya kai bakin shi Amman ya ƙiya, ni fa nayi mamakin da irin wannan ƙauna da Ya Ameen ke nuna mani, sai tarairaya ta yake yi kaman kwai, kaman wata jaririya. Wanda kuwa idan wani yaji a waje zai iya buga ƙasa yace ba Ya Ameen bane, wannan miskilin.

"Bilal ya wuce yanzun nan" Ya faɗa daidai lokacin da na ɗebo abinci ina mai nufar bakin nashi.

Bai musu ba ya sanya hannu ya riƙe nawa, yana mai idasa kai cokaln baki.

Murmushi na saki ina mai cewa "Ah su Dad Bilal sarkin azarɓaɓi, kenan har ya wuce, to Allah ya raya, ina son a bani number ɗin Ummin ma inyi mata barka kafin muje"

Ɗan haɗe fuska yayi kaɗan yana mai kallo na cikin ido "Kije ina?" ya tambaye ni sound so serious.

"cen ƙasar mana dear, ko ba zanje ba?" gyaɗa kai ya shiga yi, sannan yace "thanks God tinda gashi kin ba kanki amsa. Duka kwanan ki nawa sweet heart?"

A hankali na ajiye cokali ina mai sauke kaina ƙasa.

Sai kuma na ɗago ina mai sakin fuska ta. "Shikenan Dear, Allah ya bata lafiya, idan ta dawo naje, Amman please ka sanya a turo mana pic ɗin baby" ɗan murmushi ya sake saki "Done Baby, zaki ganshi yau kuwa insha Allah" ya faɗa yana mai zaro tissue ya goge bakin shi, sannan ya miƙe yana mai ranƙwafowa ya sakar mani side peck. "Take care baby, zanje hospital wajen Hafsat"

Nima Miƙewa nayi ina mai ce mashi "Ba tare zamu je ba baby?" ɗan dakata wa yayi daga niyyar wucewa da yayi, sai kuma ya juyo yana kallo na.

"Ya Salam Suhan, yaushe duka yau kwanan ki uku fa, jiya ma ai bansan zaki fitan ba, kinga tinda ta samu sauƙi ko me kenan idan na isa zan kira ki video sai kiga jikin nata, baby ɗinma zan sake ɗauko maki pic ɗin nata ki sake ganin ta da kyau" ya faɗa a tausashe, jin hakan da nayi ya sanya ni matsawa kusa dashi sosai, ina mai ɗan ɗaga ƙafa ta nima na mayar mashi da peck ɗin, sannan nace "OK dear a dawo lafiya, a gaida masu jikin, sannan na manta in sanar maka su khadeeja yau ne zasu koma school fa"

Da dukkanin hannuwan shi yayi using wajen Kamo ƙugu na, "Thanks for your understanding baby, akwai kuɗi cikin drower, ki sallame su baby, ba zan samu ganin su ba, may be kafin in dawo sun wuce, ki gaishe mani dasu please"

Har bakin ƙofa na raka shi ina mai mashi a dawo lafiya, cikin salo da kwarkwasa, wadda ta tafi da imanin shi har yana tuƙi yana sakin murmushi a hankali a hankali, bayan ya shiga sashen Mom ɗin tashi ya gaishe ta. Dayake tin da safe ta dawo gidan saboda sauran baƙi da ƴan uwanta dake cikin gidan.

Komawa nayi bakin taga na tsaye, duka hannaye na a rungume. Abubuwa da dama ne ke kai komo a zuciyar tawa, oh ni Suhan yau gani a gidan Alhaji Almustapha Dambulan, a matsayin surukar shi, surukar Mom sannan mata Ga Muhammad Al'ameen Almustapha Dambulan. Rayuwa kenan, Allah mai juya al'amura, a hankali na maida kallo na kan sashen Umma da yake kulle, nan shine inda Ummata zata rayuwa har ƙarshen Rayuwar tata a matsayin matar gidan, kallo na ma ɗauke ina mai maida shi kan hanyar da zata sada ni da sashen namu na masu aiki ada. Ƙure

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment