Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shawara Amman kana neman gaya man magana?" Nureen ɗin ya faɗa shima a zuciye.

"To Man na faɗa maka yanda zakayi kaƙi ji, kawai ka tura mata text cewa nan da sati biyu ne bikin naka, an ɗaga Amman zaka bata zaɓi, kodai cikin sati biyun ko makaranta ce zata nema ta shiga, inda zata iya duk wasu aikace aikace na matar gida, ko kuma kayi auren ka kawai, ka tura mata da takadda, sai ta zaɓa, kana jiran amsar ta. Wallahi zaka ga reply nata cikin sauri. Kuma ka jaraba"

"Ko?" Nureen ɗin ya tambaye shi.

"Just try it Bro" cewar Khalifa.

Ba musu Nureen ya jawo waya yana mai lallatsa keybord nata ya tura mata da saƙon waya.


Ba ɓata lokaci sosai sai ga saƙon nata ya dawo.

"Am happy Baby, One week ma is enough for me. I missed u dear Husby. I kissed u"

Murmushi ya saki sosai, yana mai cewa "Bro look at her reply, itama tayi missing ɗina sosai, nagode maka, dan haka zanje kawai sai in sanya a fara gyara mata gidan zuwa nan da sati ɗayan.

" Yanzu naji batu shege. Abokina, ai na gode ma Nihal ɗin nan, ta kusa zata man aboki" cewa Khalifa yana mai miƙa mashi hannu suka tafa, sannan Nureen ɗin yayi ma motar key suka bar wurin.


*****

Da gudu ta shiga sashen nawa da murnar ihun ta. A zabure na fito daga cikin bedroom ɗin nawa domin ganin ko menene.

Aikuwa ina fitowa ta rungume ni tana mai cewa Aunty Suhan ya amince, zan koma gida na, Aunty Suhan please ki fara man classes daga yau, wallahi ki nawa kike so zan baki, nidai ina so in iya. Please amaryar Yaya"

Sai yanzu na fahimci inda zancen ta ya dosa. Ɗan janye ta a jikina nayi, nima ina mai sakar mata murmushi, cikin aji nace "Zaki iya biyana kin tabbata?"

Gyaɗa man kai tayi da sauri cikin zaƙuwa da jin ko nawane zance ta biya.

Ni mamaki ma ta bani, yau Nihal mai sanya ni inyi mata abu, babu gode balle na gode, yau ita ce ke cewa zata biya ni? Oh duniya kenan mai juyi juyi rawar ƴan mata, na gaba ya koma baya.

A hankali na shiga takawa zuwa tsakiyar falon nawa, saida na daidaita zamana bisa Sofar, sannan na buɗe baki cikin wata irin magana mai cike da ƙwarin guiwar hankalin da nasha alwashn koya mata, nace zaki bada ten million!? (10m)

Cikin zaro idanu da kaɗuwa take kallona, bata taɓa tunanin jin hakan daga bakina ba, yanda taga na amshe ta, na sakar mata fuska, na jata a jiki cikin kwana biyu nan, ta ɗauka ma kyauta zance zan koya mata, Amman sai taji saɓanin haka


Ni kuwa a nawa ɓangaren, izza, tutiya da alfaharin dukiyar da tasha yiman a baya, sune suka sabbaba wannan abun da nake niyyar yi mata. Ko ba komai dole ne in fahimtar da ita kuskuren da tasha tafkawa a rayuwar tata.

Baki a buɗe tace "Aunty Suhan Ten Million fa kika ce! ?"

nima cikin san tabbatar mata da abunda nace ɗin na shiga gyaɗa mata kai

*"Yes Ten Million Nihal"*













~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~79~*






°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°






Kusan zamu iya cewa sanyi ƙafafun nata sukayi. Da wani irin kallo Nihal ɗin ke bin Suhan, yanayin ta kaf ya cenza zuwa kalar tausayi.

Duk da taɓa Suhan ɗin tausayi, Amman wannan ba shine zai hanata ta nun ambata matuƙar kuskurenta ba, masalan idan ta tuno irin yanda taci bala'in wahalar Nihal ɗin a rayuwa.

Gyara tsayuwarta tayi, tana mai bin Nihal ɗin da kallo, cike da wani irin yanayi, gabaki ɗaya Suhan ɗin ta cenza, ta murje, fatar ta sai wani irin kalli da sheƙi takeyi, kai idan ka ganta ma zaka ɗauka dama cen cikin gata ta taso. Ta zama matar manya, hatta da jikin nata ya sake cikowa, duk da dama cen ita ɗin ba ramamma bace.

"Kije kiyi shawara Nihal, duk abunda kika yanke zan saurare ki, and payment ɗin zaki iya yi throug Bank ko kuma cash, duk dai wanda yafi maki sauƙi, and i promise u sai kunzo kin mani godiya" tana gama faɗin hakan ta zagaye Nihal ɗin da take tsaye kaman an dasa ta.

Kai tsaye cikin falon ta isa, tana mai zama saman Sofa, sannan ta jawo remote ta kunna tashar Zee world ta cigaba da kallon Saraƙat zaujen da take kallo a daidai lokacin.

Murna ai sai ta koma ciki, tuni idanun Nihal suka kawo ruwa, ita yanzu ko yanka ta za'ayi ina zata samu waɗannan kuɗin? Ta tabbata ko Mom ɗinta ta tambaya ba lalle ta samu ba, masalan ma yanzu da take cikin irin wannan situation ɗin, na damfarar da Alhaji Yaro yayi mata. Dad kam dama ba'a maganar shi, shi ko kallon ta ma bayayi, toh balle uwa uba Ya Ameen, ta ina ma zata fara tambayar shi? indai ba sarƙoƙinta zata saida ba da motar ta? Amman kuma ai abun kunya ne ƙawayen ta suga tana siyar da ƙadarori, kuma aganta bata da mota, yanzu idan tayi saken rasa motar ta wanene zai siya mata wata? Ta tabbata ko da Nureen zai sai mata wata ba yanzu ba, sannan bama zata iya tunkarar Ya Ameen da zancen ba.

Nisawa tayi, tana mai ɗan murmusawa, ga motocin Mom? Ai ko cikinsu sai ta ɗauki ɗaya kafin ta samu ta shawo kan Nureen ya sai mata wata, tunda duk abunda Zatayi danshi ne zatayi.

Juyawa tayi, tana mai komawa cikin falon.kujerar dake kallon ta Suhan ɗin ta zauna.

"Aunty naji na yarda zan bayar insha Allahu, dan Allah mu fara lesson ɗin kafin in haɗa kuɗin"

Kallon ta Suhan tayi, tana mai murmusawa kaɗan.

"Nihal pay before serve" Abunda ta iya ce mata kenan, tana mai maida hankalinta kan Tv ɗin.

Jiki a sanyaye Nihal ɗin ta miƙe tana mai cewa "To Aunty insha Allahu zan kawo" Juyawa tayi tana mai ficewa daga falon.

Dariya Suhan tayi bayan idasa ficewarta, "Humm Nihal kenan, ina so ne ki ɗauki darasi, ba komai ne kuɗi ke sama maka ba a rayuwa, kuma dan ka tsinci kanka a cikin waɗanda Allah yayi ma nasibi, ba shike nuna cewa kowanne talaka banza ne wulaƙantacce a wajenka ba, kuma shi ɗan adam daraja ne gareshi, dole ne watarana ka nemi wani abu wajen shi, idan ka riga ka mashi wulaƙanci tun farko fa? Kayi yaya?"

Ɗan nisawa tayi tana mai cewa "Allah shi kyauta, ko kuɗin kika bayar zanyi maki ne kawai domin mijina, kuma ba wai wani amfani zanyi da kuɗin ba, aa darasi rayuwa kawai nake so ki ɗauka. Amman da ko kallo baki isheni ba, kije cen kiji da matsalar ki"



*************

Suna sauka filin jirgin, hayar taxi suka ɗauka kawai, gami da shaida mashi inda zai kaisu. An kuwa ci sa'a tafiya ba nisa sai gasu cikin area ɗin.

Unguwa ce da take tsit, baka jin komai sai kukan tsuntsaye, akwai yalwar itace, da wasu irin duwatsu masu tsawo, bayan duwatsun ruwa ne makeke, tsuntsaye sai shawagi suke sama, da manyan jirage da ƙanana na shaƙatawa. Ga wani irin sanyi, gabaki ɗaya ma area ɗin snow ce ke sauka a hankali.

Bayan sun sallami taxi ɗin ne Ya Ameen ya sake duba number ɗin gidan.

Da hannu yayi ma Bilal nuni, dama sun riga da sun tsara yanda komai zai tafi.


A hankali suka shiga gangarawa zuwa gidan da ke maƙautaka da gidan, makulli Al'ameen yasa, gami da buɗe gidan suka shiga, dama tun jiya da daddare ya kammala komai na booking gidan, sannan suna sauka aka miƙa mashi ɗan makullun gidan.

Gida ne ɗan madaidaici. Safe content ne, mai ɗauke da ɗan madaidaici falo, sai ɗakunan bacci guda biyu, da kuma
Kitchen gefe, kowanne ɗaki yana da toilet da gadon barci, sai mirror ɗan madaidaici da kuma wardroop ta bango.

Babu abunda babu a gidan, komai tsaf yake, kaman dai gidaje ne na haya, wanda ake bama baƙi da suka sauka ƙasar, kuma basa son zauna Hotel.

Wasu irin manyan barguna ne cikin wardroop ɗin ɗakunan, saboda irin sanyin da ake tsalawa garin.


Faɗawa bisa luntsuma luntsuman kujeru Bilal yayi, yana mai sauke ajiyar zuciya ta gajiya, lokaci guda kuma yana mai sakin miƙa gami da hamma.

Ɗan guntun tsoki Ya Ameen yayi, yana mai wucewa kai tsaye zuwa cikin ɗakin, ba tare da yace mashi komai ba.

Shima Bilal ɗin dariya ya sheƙe da ita, "Mutumena miskilancin ne ya tashi ko? Ka ji dashi kuwa, dan wallahi ni nan bakaji yanda na gaji ba" Al'ameen ɗin na jiyo shi, yayi mashi banza, yana mai idasa shigewa ɗakin.

Kusan tsawon awa guda, sai ga Al'ameen ɗin ya fito, jikinshi ɗanye da kayan jeans set, kalar ruwan samaniya mai turuwa, ya ɗora baƙar rigar sanyi mai hula a bisa kai, ƙafafun nashi ƙunshe cikin sneckers suma kalar kayan, sai baƙar safa daya sanya ciki,ya ƙunshe fuskar shi cikin baƙin face mask saboda sanyi, kai idan ba mugun sani kayi mashi ba, ba zaka iya shaida shi ba.

Dayake farar fata ne, sai kayan suka amshi jikinshi, kyaun shi ya sake fitowa fili, kwarjini da haibar shi suka sake bayyana.

Hannayen shi soke cikin aljihun wandon nashi yake yima Bilal magana, wanda gajiya ta sanya har ya fara bacci.


"Ka tashi ka shirya zamu fita"

Cewar Ya Ameen ɗin, wanda yake tsaye har yanzu. A hankali Bilal ya shiga buɗe idanun nashi, saman fuskar Ya Ameen ya sauke idanun nashi, sai kuma ya tashi zaune yana mai fashewa da dariya.

"Me zan gani haka Friend? Duk ɓadda kamar ce? Kaida har yanzu bamu da tabbacin suna cikin gidan ko basa nan?"

Takawa Ya Ameen ɗin ya fara yi a hankali zuwa wajen ƙofar fita. Saida ya kusa ida ficewa ne, sannan ya dakata yana mai cema Bilal ɗin

"Idan baka iya kama ɓarawo ba, ai shi sai ya kama ka, kuma tsuntsu mai wayau a wuya ake kama shi"

Bai jira Cewar Bilal ɗin ba, ya idasa ficewa abunshi.

Dariya Bilal ɗin ya saki, "Hoo mutumen gaskiya kam bahaushe ne kai gangaran, ko ina ya iya hausa har haka?" ya faɗa yana mai sakin dariya sosai, sannan ya miƙe zuwa cikin ɗakin.


Yayi tafiya mai ɗan nisa, zuwa bayan manyan duwatsun. Bakin ruwan yayi ma kanshi wuri, har yanzu hannayen nashi suna cikin aljihun nashi.

A hankali ya ciro hannayen, yana mai sauke hular rigar sanyin dake kan nashi. Sai kuma ya ɗaga ƙafa yana mai bin gefe da gefen ruwan. Wayar dake cikin aljihun shi ce ya zaro.

Vedio Call ya danna mata, sa'a aka ci kuwa wayar tata na kusa da ita, haka kuma datar tata a kunne take.

Ina zaune nayi nisa cikin kallon da nake yi, ya zuwa yanzu Kunal ya fara bani haushi, irin cin amanar da yake yima Mouli, abun har ya fara fita raina, ji nake idan dani ce fa? Ba zan taɓa iya sakakin barin mijina da wata wai ita ƙawata ba, kaman yanda Mouli tayi ma Nandini ba, sai gashi daga ƙarshe ya ci amanar ta, ya koma kuma yana neman Ƙawar tata.

Ringing ɗin da yake mallaki Ya Ameen mai sanyin tashi ne naji yana kaɗawa a wayar tawa.

Cikin zaƙuwa na kai hannu na ɗauka, tashin farko na haske shi da wani irin ƙayataccen murmushi, kafin in sake mashi sallama cikin wata irin murya, da ni kaina bansan lokacin da nake yinta ba.

"Mrs Al'ameen Dambulan" Abunda ya furta kenan shima, fuskar shi ta wadata da murmushi, idanun nashi cike da kewata.

Nima dariya na saki mai cike da wasu irin ma'anoni da dama, ina mai cewa "Yallaɓai barka da rana"

"Barka dai Yallaɓiya ta, ya kewa, ya kuma kaɗaici? Ana nan ana kewa ta ko?"

Sunne kaina nayi ƙasa, sai naji kunya ta kama ni. "Kaman ka sani Hubby, kewarka ita ce komai nawa, tun lokacin da ka tafi kabar amaryar taka"

"Ɗan matse baki yayi a hankali, sai kuma ya shiga ɗan kaɗa kai a hankali a hankali," Na sani wify, nima nan hakan take gareni, sai nake ji dama tare dake na taho, Amman kada ki samu damuwa, da komai ya koma normal ba zan sake barinki ba, a koda yaushe zan ɗauko ki anan ɗina" ya faɗa yana mai nuni da ƙirjin nashi


Wani irin daɗi naji ya ratsa ni, sai na sake murmushi,ina mai ƙure shi da kallo, ya zuwa yanzu ya ɗaga kanshi yana mai kallon ruwan da yake gefe, wanda igiyar ruwa keta kaɗawa, gashin kanshi sai iska ke kaɗa shi, sai naga ma ya cenza gabaki ɗaya, ya sake kyau, ga wurin da yake wajen gwanin ban sha'awa, ya saje, kaman dama ɗan cen ne.

A hankali muka shiga fira mai kwantar da hankali, Saima na sanya hannu ina mai rage volume ɗin Tv ɗin sosai, nunnuna man ko ina ya shiga yi, hatta da irin yanda tsuntsaye ke shawagi, kaman dai ina wurin ne.

Mun ɗan jima a haka, kowa kewar kowa yake, kalamai masu kwantar da hankali muke aike ma junan namu, ji nake kaman in tsuntsuwa in iske shi inda yake. Ashe na daɗe ina wauta? Ashe na daɗe ina jin son Ya Ameen a cikin raina? Sai yanzu dana kasance dashi ne, sai nake gane ashe ma tuni wannan shi ake kira da so , duk wani motsi nashi ina son kasancewa dashi, banƙi ba ace kullum numfashin shi, saman fuska ta yake sauke shi.


Daga cen baya Bilal ke tahowa yana kwala mashi kira "Mr Fafarawo! Mrs Fafarawo!"

Da ɗan sassarfa ya ƙarasa inda Ya ameen ɗin yake tsaye, sai haki yake saukewa.

"Nasha neman ka, ashe kai kana ta nan kana cin soyayya?" ya faɗa yana mai manne ido guda, alamun zaulaya.

"Baby zamuyi magana anjima, yanzu zamu je mu samu abunda zamu ci ne, ina jin yunwa, gashi ina kewar abincin ki"

Ɗan zaro idanu nayi, "Dear yanzu fa ƙarfe huɗu anan, na kuma tabbata ku anan yanzu kusan bakwai tayi, please ka dena zama da yunwa, kuje ku samu wani abu kuci, kaci dani Baby, kasha man ice-cream kaji?"

Murmushi ya saki, "OK Done wify, bye i love u" ya faɗa yana mai sakar man wani irin Kiss.

Ina dariya na kashe wayar, so nake ma in tashi in tafi gidan su Hafsat, gobe suna gashi kuma har yanzu ban tafi ba, na ƙagara ma in fita, domin ya zuwa yanzu nasan ƴan Kankiya ma sun isa isowa.

A hankali na sauke wayar ƙasa, wata irin kewar mijina nake yi, ba na gajiya da faɗar irin dacen miji da nayi, komai ya zama gwanin ban sha'awa. Ya Ameen namiji ne harma ya zarta, komai nashi a nutse, komai nashi daban ne, ina jin Bilal nata yi mashi tsiya, wai yaushe ya fara iya soyayya haka? Bai dai tanka shi ba, balle yace mashi wani abu.

A haka na miƙe, ina mai isa bedroom ɗin, na ɗauko hijab da makulli, sai ƴar jikkata. Ƙasimu Driver ne na sanya ya kaini, wanda muka rabu da zummar cewa bayan isha'i yaje ya ɗauko ni zuwa gida.



*******


Baba Alhaji ne ya sake russunawa gaban mai martaba, "Haƙiƙa ranka ya daɗe haka akayi, sannan duk ina da wasu hujjoji da zasu sake tabbatar ma mai martaba da abunda na faɗa ɗin, saboda haka ne nake so da a bani tsawon kwanaki bakwai, insha Allahu zan tattara sauran bayanan, kuma duk abunda ake buƙata za'a samu da izinin Allah"

Gyaɗa kai mai martaba keyi cikin gamsuwa da bayanin Baba Alhajin.

Cikin isa, da magana irin tasu ta saraki ya maida kallon shi kan Alhaji Mustapha da yake zaune bisa wata irin Sofa mai kyau, shi da Alhaji Auwalu ne bisa Sofar, yayin da gefe kuma Mama Fulani ce da Umma, sai kuma sauran matan sarkin bisa wata kujerar suma, sai Mom dake zaune bisa kujera mai cin mutum biyu.

Yau babu irin tashin hankalin dake saman fuskar ta irin na jiya, saidai har yanzu fuskar babu koda ɗishin annuri ne a saman fuskar. Bana tunanin idan Hajiya Kubra zata iya bada haɗin kai irin yanda ake da buƙata.

Maganar mai martaba sarki ce ta katse shirun da ya biyo baya, tun kammala jawabin Baba Alhaji.

"Ah Alhaji Mustapha kaji abunda lauya ya faɗi, saboda haka ne mu ba zamu riƙe ku ba, zaka iya ɗaukar su matan naka ku koma gida, alabasshi zuwa sati guda ɗin da shi Barrister ya ɗiba, nasan zuwa lokacin shi Al'ameen ya samo shi Wancen mayaudarin Alhaji Yaro, saboda haka ne zamu san abun yi, masarauta tana yi maku fatan sauka gida lafiya"

Abunda Mai martaba ya faɗi kenan, yana mai miƙewa, da kanshi ya tako har zuwa gaban Alhaji Mustapha da Alhaji Auwalu ya basu hannu sukayi musabaha. Kai tsaye cikin gidan ya nufa yana mai gyara alkyabbar dake jikin shi, wanda take ta faman ɗaukar ido da walwali.


Kai Umma ta sauke ƙasa, a hankali Mama Fulani ta kamo hannuwan ta, gyaɗa mata kia take a hankali, haƙiƙa ita kanta tasan irin dattakon da Umman tayi, wanda wanna ba abun mamaki bane, duk wani jinin sarauta na asali, zai iya ma yin abunda yafi haka,masalan ita data kasance jinin mai martaba kai rasuwa. Wanda kowa ya sanshi wajen kawaici, dattako da halin girma.


Idan ka kalli Hajiya Kubra kuwa, tabbas ba sai na faɗa maka ba, tana cikin wani irin yanayi na kaɗuwa, ga yanda take ganin Fuskar mai martaba zaiyi wuya ace yabar mata dukiyar nan, gashi da gani irin mutanen nan ne masu tsaida gaskiya, gashi dukkan hujjoji sun tabbatar da cewa lallai dukiyar ta, dukiya ce da take mallakin Suhan yanzu halak malak, idan ka cire wadda Umma tace ta yafe mata, kenan ba zata tsira da ko rabi ne a cikin dukiyar dake hannun nata ba kenan?

Lallai ba zata iya bari wannan al'amari ya tafi a haka ba, zata san duk yanda zatayi ta mallaki dukiyar ta ita kaɗai, idan ma ta kama a kauda wani ne, tabbas zata kauda duk wanda yake neman shiga hurumin dukiyar tata, yanzu ita faɗan nata, ba da Umma Zatayi ba, da Masarauta Zatayi, wanda take iƙirarin yima kowa adalci, mai laifi kuma ya amshi hukunci.

Cikin gida suka shiga, saida suka gama kintsa komai, sannan akayi masu rakiya zuwa bakin mota. Dole saida masarauta ta haɗa umma da kuyangi uku amuntattun dattijai, wanda zasu dinga tayata zama, da kuma kula da duk wani motsin ta, sannan ta haɗa ta da fadawa guda biyu, wanda idan ta kama koda driving ne zasu dinga yi mata.

Sun baro masarauta cike da farin ciki, in ka ɗauke Mom, wanda zaune kawai take, har yanzu ta gagara cema kowa komai.

Ta fannin Umma kuwa, wani irin annashuwa take ji tana shigar ta, ko ba komai yanzu komai ya bayyana, Hajiya kubran ta gane ko wacece ita, sannan ta gane matsayin ta a gareta yanzu, ko yanzu kasuwa ta watse ɗan koli yaci Riba, ba sauran taƙama ko ɗaga kai, sannan idan yanzu Suhan tace bata yarda ba, bata da yanda Zatayi da ita, dole ta miƙa mata haƙƙin ta, saidai bata fatan ace ankai ga hakan, saboda ko ba komai yanzu matsayin Uwa take gareta, na farko gata surukar ta, sannan gata abokiyar zaman Umman ta, sannan mata ga mijin Umman tata, ko dan haka za'a ɗaga ma Hajiya Kubran ƙafa, sannan tasan duk wani abu da tayiyyi mata a baya, sheri ne irin nasu Mama Talatu, wanda ko ita Umman a yanzu bata jin idan zata daure suci gaba da zama a cikin gidan nasu, bata son duk wani abu da zai shafi zaman gidan, saboda yanzu rayuwa take so su gudanar mai cike da tsafta, mai cike da addini, mai cike da soyayya da ƙaunar juna, tana fatan ace tayi sanadin kulluwar duk wata ɓaraka da ta riga ta shigo gidan, saboda haka, duk wani shige da fice, da motsin kowa a gidan tana ankare dashi, lokaci ne da zata fito ta shaida ma kowa da kuma duniya cewa itama fa mata ce kaman kowa, saboda haka duk wanda tasan zai iya zama barazana ga zaman lafiyar gidan, to fa a shirye take data ɗauki mataki akai, wana tana da tabbacin samun goyon baya, daga mai gidan har magajin gidan.



Sun share awanni kafin su iso gidan. Kaman yanda suka zata ɗin dai ne, gidan tsit, in ka ɗauke mai gadi , sai iro da yake cen gefe yana yankar Flowers, sai masu aiki mata jefi jefi da sukan gitta.


A harabar gidan sukayi parking, dukansu fitowa sukayi suna masu ɗauke da salati ga bakunan su, jin ƙarasowar su ne ya sanya sauran ma'aikatan firfitowa cike da farin ciki suna masu yi masu sannu da zuwa.

Mom dai wucewa tayi kai tsaye zuwa sashe nata, yayin da take aike ma sashen Suhan da harara, kai kace Suhan ɗin ce a wajen.

Ita ko Umma tsayawa tayi suna gaggaisawa da ma'aikatan gidan, masalan ma data kwana biyu bata cikin gidan, ya zuwa yanzu dai labari ya iske kowa na irin matsayin Umman, saboda haka ne, kowa sai yake kallon ta cike da kwarjini da haiba, gashi duk ta wani cenza, hutu da jin daɗi sun sake huda jikin ta, ta zama wata ƴar gayu, kaman ba Umma mai aiki da kuka sani cen baya ba.

Mama Saude sai taɓo Mama Talatu take yi, inda ita kuma sai ta buge mata hannu, duk Umman na an kare dasu, murmushi ta saki tana mai cewa "Bari in ƙara sa ciki in ɗan watsa ruwa, ke GAJE muje ko sai a samu a ɗan gyaggyara man sashen" ta faɗa tana maida kallon ta kan haɗiman da ta taho dasu.

Juyawa tayi zuwa sashen nata, ko ɓangaren sashen Suhan bata kalla ba, duk kuwa da yanda idanun nata ke son kaiwa wajen sai tayi maza ta janye kanta daga kallon sashen. Tana fatan ace ɗiyar tata tana ciki hankalinta a kwance, saidai tasan da kamar wuya kam, ko ba komai wannan issue ɗin kawai daya ɓullo ya isa ya wargaza dukkan wani farin ciki na Suhan ɗin. Shiyasa ma bata shaida mata ba da bakinta, ta ƙyale shi Al'ameen ɗin yayi amfani da baiwa da dubarar da Allah ya bashi wajen fayyace mata komai. Bata so ta saka kanta cikin rayuwar auren Suhan ɗin, masalan da ya kasance gida ɗaya suke zaman aure da ɗiyar tata.



********


Sun sha yawo sosai, dama shi Bilal wannan ne karon shi na farkon zuwa ƙasar, ƙasar ta matuƙar burge shi, Larabawa ne sosai, saidai al'adar su da ɗabi'ar su, suturar su tasha bamban da sauran Larabawa, idan Kaga yanda suke gudanar da al'amurran su, kai kace turawa ne. Saboda haka ne saida sukayi mai isar su yawon, sannan suka nemi abunda zasu ci suka koma gida.

Bayan Sallar isha'i ne sosai, saboda haka suna gama abunda duk zasuyi, naga Ya Ameen ya fiddo waya yana magana cikin halshen turanci mai cike da gwanancewa,kai kace ba bahaushe bane.


Wasu irin jibga jibgan riguna naga sun ɗora saman nasu kayan, sannan sukayi amfani da face mask baƙa, wadda ta rufe ko ina na fuskar su, in ka ɗauke idanun su, shi ya Ameen ma saida yayi amfani da baƙin Google ya rufe ƙwayar idanun nashi.

Ƙarar motar da suka jiyo ce daga ƙofar gidan, ya sanya su hanzari ficewa cikin sanɗa, kaman wasu munafukai, cikin motar sukayi ma kansu mazauni, yayin da ɗaya daga cikin motar ya fice

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment