Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



Gyaɗa kanshi yayi, yan mai maida hankalin shi kan tuƙin da yake yi.

Mu yo tafiya mai nisa, yayin da shiru ya ziyarci motar, sai ƙira'a da ya sanya tana tashi a hankali, har bansan lokacin da na jingina kaina da makarin kujerar ba ina mai bin karatun a hankali a hankali.

Shima ta gefen ido yake daɗa kallo na, na masifar burge shi, bansan yanda akayi ba, sai gani nayi munyi parking.

"Muje ko?" ya faɗa mani, yana mai sanya hannu ya buɗe man murfin motar ta ciki.

Hakan ya sanya hannun shi shafar jikin nawa, tsikar jikina ce ta tashi, ba Arziƙi nayi saurin ficewa ina rufo ƙofar.

Shima fita yayi yana mai rufe ƙofar.


"Wow masha Allah" Abunda na faɗa kenan a cikin zuciya ta, wurin ya matuƙar ƙawata ni, ciyawa ta fito tayi shar kaman grass carfet, sai korayen flowers da ja, masu matuƙar kyau da ƙamshi, wurin akwai ni'ima sosai, daga gefe wani ɗan rafi ne cike da ruwa, bado da kainuwa sun fito su yi fafut, harda wata farar flower mai adon yellow a jikin ta.

"Here we can go"

Ya faɗa yana mai juna mani cen gefe ƙarƙashin wasu irin flowers masu tsawo, suna zubo da wasu irin ƴan ƙananan flawowi.

Kujeru ne guda biyu, irin na gida wanda akayi da zallar cement da duwatsu.

A baya na shiga binshi har muka isa inda suke.

Shine ya nuna mani inda zan zauna, Nifa kaina ya kulle, na mamaki nake bi shi da kallo.

A zamanin nan da babu tsaro, shine zamu zo wurin nan mu kaɗai mu zauna? Duk da dai wurin yana da matuƙar kyau, kaman wurin shaƙatawa yake.

Saida na zauna sannan shima ya zauna, yana mai faɗin "Huhhh Finaly gani ga Madam ɗita"

Sauke kaina nayi ƙasa, wata irin kunya ce ta kama ni.

"Kinyi matuƙar kyau my Suhan, kaman muyi ta zama a haka nake ji"

Ya faɗa cikin wani yanayi na sauƙi da dakewa.

"Uhmmm" Abunda na iya cewa kenan ina mai wasa da yatsun hannuwan nawa.

"Ki saki jikin ki Suhan, babu Abunda zanyi maki, kawai dai ina so mu saba ne, nan da wata ɗaya ne"

Ya faɗa sosai cikin son haɗa ido dani.

A hankali na ɗago idanun na ina mai kallon shi. Sai kuma yaga ina ɗan waiwayawa alamun a tsorace nake.

Baice komai ba, naga ya jawo wayar shi, bansan me yake yi ba sai naga yana magana, kaman video call yake yi.

Sai kuma ya nuni mani fuskar wayar.

Wasu mutane nagani tsaitsaye riƙe da bindigogi,alamun masu tsaron lafiyar mu ne.

To yaushe suka zo nan?

"kada ki damu, duka nan akwai tsaro sosai, fiye da yanda kike tunani.

Sai a lokacin na sauke ajiyar zuciya.

Ko ba komai na samu natsuwa.

Ƙureni ya cigaba da yi da kallo.

A hankali naji ya sanya hannuwan shi duka ya kamo nawa.

Ɗan firgita nayi ina mai son janye hannun.

Bai bani damar haka ba, sai ma ƙara matse hannuwan da naji yayi.

Da kallo nake mashi alamu da babu kyau fa.

Shima kallon na sani ya shiga bina dashi, yana mai ɗan haɗe fuska kaɗan.

"Kinsan me?" ya faɗa yana mai sakin hannuwan nawa.

Girgiza mashi kai na shiga yi, ikon Allah yau nake kallo, wai wannan Ya Ameen ne da kanshi?

Katse mani tunani yayi da cewa


"Shekarun cen baya, wata ƴar yarinya ce kyakkyawa, bana gajiya da ɗaukar ta, bana gajiya da wasa da ita, haka bana gajiya da kallon ta, itama bata gajiya da zama a tare dani, har barci takeyi a ɗaki na, muna zuwa da ita unguwa, har wajen wasanni ina kai ta, a hankali ta fara girma, sai kuma Maman ta ta fara hanani ɗaukar ta bansan dalili ba, duk da haka bana gajiya da siyo mata sweet da biscuit, haka yasa idan ban siya mata ba a rana tana kuka sosai, kwatsam tafiya ta kama mu zuwa wata ƙasa, nan na barta cike da kewa, cike da tsantsar ƙauna, cike da muradn dama ace da ita muka tafi, cike da alhinin rabuwa da ita. Saidai ko kafin in dawo ta girma, ko kafin in dawo ta zama budurwa hakan yasa na fara ja baya da ita, hakan ya sanya na fara jin ina ma ace bata girma ba, na cigaba da wasa da ita, kyakkyawa mai gashi, ga wayau, ga yarinta a tattare da ita. Hmmmm. Kinsan wacece wannan?"

A ƙasa ƙasa nake kallon shi, labarin ya ƙayatar dani, a take Naji ina mai son yarinyar yanda yake fasalta ta, sai kuma na ɗna ji wani abu, ashe ma ya taɓa son wata acen baya?dukda yarinya ce, amman shaƙuwar tasu ta ɗan taɓa mani zuciya.

Girgiza kai na shiga yi a hankali a hankali.

Da ɗan yatsan shi manuni ya shiga nuna ni, sai kuma ya sake kamo hannuwa na dukan su, yan mai ɗora su zuwa saitin inda zuciyar shi take.

"kece Suhan, kece wannan yarinyar, na raineki da hannuna Suhan, nayi bacci tare dake, munyi wasa tare dake, kin man fitsari a bisa jikina Suhan, na maki wanki na kaiki makaranta na ɗauko ki suna, kinyi bacci bisa ka faɗa ta, kinyi bacci bisa ƙirjina Suhan, kinyi bacci bisa cinya ta. A karo na biyu ina fatan ace wannan rayuwar ta dawo, kin mani kina yarinya, ki taimaka kiyi mani ina babba, wanda na mallaki hankalin kaina, wanda zaki samu lada Suhan"

Dukan da zuciya ta keyi bai musaltuwa, da zai kula zai fahimci ma kaman nayi suman zaune ne, na kasa cire hannuna daga cikin nashi, haka kuma ina iya jiyo bugawr zuciyar tashi.

A hankali ya saki hannuna yana mai miƙewa.

Da kallo na shiga binshi har ya isa zuwa ga motar tashi.

Wani abu ya ɗauko cikin mota ya dawo ya zauna.

Hak dama ya Ameen ɗin yake? Hak Soyayyar take wai? Ni kaina yanzu ba zan iya fasalta yanda nake ji ba, wani irin yanayi nake ciki, ga sanyi da ƙamshin wurin na baibaya ta, ga kuma wata irin kunya dake addaba ta, har na kasa ma haɗa idanu dani.

Zobe da sarƙa ya fiddo daga cikin ƴar cover ɗin tasu.

Sai ya ajiye sauran bisa cinyar shi.

A hankali ya ɗago su cikin haɗin hannun shi mai matuƙar kyau, Nidai haka nake zaune kaman mutum mutumi, na kasa taɓuka komai, saidai in saki ɓoyayyar ajiyar zuciya.

Sarƙa ce da zobe na Gold masu masifar kyau da tsada.

Tunani na ya katse, daidai lokacin da naji yananmai cewa


"Idan har kin yarda da Soyayya ta Suhan ki bani dama in sanya maki sarƙa da zoben nan da hannuwa na, ba zan takura maki ba, saidai zanyi matuƙar farin ciki idan har na sameki a matsayin abokiyar rayuwar tawa"

A hankali na ɗago fararen idanu na, ina mai ɗora su bisa kyakkayawar fuskar tashi dake mani kwarjini a koda yyaushe.

Shi ɗinne dai, Ya Ameen ne kaman yand ana sani.

Fuskar shi cike da annuri dake fidda zallar soyayya, idanun nan nashi har wani walƙiya sukeyi kaman wanda aka ɗiga ma zaiba.

A hankali na shiga ɗaga hannun nawa ina mai miƙa mashi cikin wani irin yanayi da ni kaina ba zan iya cewa gashi ba.. ......




_Hadda na gobe_








~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*Addu'ar zama tsakanin sujadar farko da ta biyu.*

رَبِّ اغْفِـرْ لِي ، رَبِّ اغْفِـرْ لِي .


*Rabbigh-fir lee, rabbigh-fir lee.*

*Ya Ubangijina! Ka gafarta mini, Ya Ubangijina! Ka gafarta mini.*


اللّهُـمَّ اغْفِـرْ لِي، وَارْحَمْنِي، وَاهْدِنِي، وَاجْبُرْنِي، وَعَافِنِي وَارْزُقْنِي وَارْفَعْنِي .


*Allahummagh-fir lee, warhamnee, wahdinee, wajburnee, wa'afinee, warzuknee warfa'nee.*

*Ya Allah! Ka gafarta mini, ka ji kai na, ka shirye ni, ka wadata ni, ka ba ni lafiya da tsira daga musifu, ka azurta ni, ka daukaka ni.*


>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~53~*


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°

Har ya kawo hannun shi cikin wani irin yanayi dake nuna zallar shauƙi a saman fuskar shi, sai kuma na janye nawa a hankali ina mai cewa

"Yaya ina jin tsoro fa"

Ajiyar zuciya ya saki a hankali yana mai faɗin "Tsoron me wify?"

"Mom" na faɗa a hankali

Huh.

Ya sake dauke ajiyar zuciya a hankali, yana mai rumtse zoben da sarƙar a cikin tafukan hannayen shi.

Tsaf ya taso a hankali daga inda yake zaune yana fuskanta ta.

Sai kuma ya dawo bisa kujerar da nake zaune, dayake tana da ɗan tsawo da faɗi, hakan ce ta sanya ni ja baya a hankali ina mai lumshe idanu na, jin ƙamshin turaren shi a kusa dani.

"Suhan tsoron me kike ji? Bayan gani a tare dake?"

Sauke kaina ƙasa nayi, ina mai fara wasa da Zara zaran yatsun hannun nawa.

Har yanzu idanun shi a bisa kaina suke, ya gaza koda ɗauke wa.

Kallon ne yayi mani yawa, hakan ne ta sanya ni ɗagowa a hankali, ina mai ɗora idanun nawa a saman tashi fuskar.

"Yaya Mom ba zata yarda ba, ina tsoron hukuncin ta..."


"Common Suhan, kin faye tsoro, zanyi mata bayani, insha Allahu zata fahimta, beside ki ƙyale maganar mom komai yana a hannun Dad, he'll handle the issue"

Ya faɗa cikin ɗan marairaice fuska.

Sai naga ya sake yi mani kyau a idanu na, a hankali na sauke idanun nawa bisa hannun, sai kuma na fara murza yatsu na, hannuwan suna a dunƙule, ina mai ɗago su na wara mashi yatsun hannun.

Wata irin ɓoyayyar ajiyar zuciya ya saki, zamowa yayi daga inda yake zaune, ya zuƙunna bisa ƙafafun shi, yana mai kamo ɗan yatsa na na kusa da ƙaramin ya shiga zura mani zoben da yake da matuƙar kyau da walwali.

Sai kuma ya riƙe hannun sosai, bayan ya gama sanya zoben ya ƙure shi da kallo.

Ji yake kaman ya sunbace shi, saidai yana gudun Abunda ka iya jeea ya dawo.

Ko ba komai yardar da yarinyar tayi mashi, akan cewa ba zai iya cutar da ita ba, bai kamata ace ya dasa wani tsoro ko shakku acikin ranta ba.

A hankali ya miƙe, yana mai tallafo damatsan hannuwa na duka ya shiga miƙar dani tsaye.

Ba musu na miƙe nima, har gyalena yana zamewa daga jikina.

Ɗan durƙusawa nayi da niyyar ɗaukowa, ya riga ni kai hannu, sai kuma ya tattara shi ya ajiye bisa kujerar, yana mai warware sarƙar dake cikin hannuwan shi.

Nidai da idanu kawai nake bin shi, wai Ya Ameen ne haka tsaye gabana, yana mai marmari da muradin soyayyar tawa, wani irin yanayi ne na tsinci kaina ciki, masalan yanda da muka kaɗai ce daga ni sai shi a wurin.

Ban aune ba sai ji nayi ya wara duka hannuwan nashi gabaki ɗaya, yana mai zagaye ni dasu, ya shiga ɗaura mani kwaɗon sarƙar a dogon wuyan nawa da yake fari tas cike da gashi ya kwakkwanta.

A hankali ya sakeni, sai kuma ya ja baya yana mai ƙare mani kallo, ba Arziƙi na kuma sunkuyar da kai ƙasa.

"Wow my beautifull wife"

Nisawa yayi yana mai yin taku biyu inda nake tsaye, sai jinai ya tallafo duka fuska ta, daf da tashi.

*"You are highly Welcome in to my life Mrs Al'ameen Almustapha Dambulan"*

Ya faɗa cikin wata irin murna, mai nuni da tsantar jin daɗi wadda take cike da wani irin sauƙi na soyayya.

Duk abun nan fuskar tashi na maƙale da ɗan murmushi da gefen fuskar, da har saida kumatun shi suka loɓa.

Sakin fuskar tawa yayi, jan hannu na ya shiga yi a hankali, bayan ya ɗauko gyalen ya yafa mani.

Inda ɗan ƙaramin rafin nan yake ya shiga jana.

Haka na shiga bin shi, ina mai ƙare ma ƙeya da bayan shi kallo, wanda ko salon takun tafiyar tashi ma abun kallo ne.

Daf da ruwan yaja ya tsaya, yana mai sakin hannun nawa.

Sai kuma naga ya zuƙunna ya zaro wata irin flower mai ban sha'awa da ƙamshi guda uku, ya haɗe su wuri guda.

Miƙewa yayi yana mai ɗan kai ta zuwa hancin shi ya sun suna, yana mai wani lumshe kyawawan idanun nashi, masu ɗauke da Zara-zaran gashin ido. Sai kuma naga yayo saitin hancin nawa da ita.

Ɗan kautar da kaina nayi gefe, nifa duk kunya ta cika ni, gani nakeyi kaman a mafarki.

Masalan ma yanda wurin ya ƙawatu da furanni da kuma shi kanshi ya Ameen ɗin da ya kusa kasheni da mamaki.

Wane irin salon soyayya ne haka? Wannan ai sai yasa in tsaya wasa da karatun nawa.

"Bana son wannan Kunyar fa, Shiyasa nake ce maki baƙauya"

Ya faɗa yana mai yawatawa da idanun shi bisa fuskar tawa.

Ɗan murmushi na saki, ina mai ɗan ja baya, saboda yanda muke tsaye dashi daf da daf, kusa da kusa, har hucin numfashin shi ina ji, sai jikina yake ƙara yin sanyi ga kuma yawan faɗuwar gaba da nakeyi.

Lallai matuƙa Ya Ameen ɗin ya shayar dani matuƙar mamaki, mutumen da ada ko gaida shi nayi, sai dai ya amsa kawai a gajarce ya wuce, ko kuma ya ɗaga maka hannu, duk ranar da baya jin ƴan magana?

"Say something mana, bana son shirun nan Suhan, sai inga kaman baki yadda dani ba"

"A'a Yaya"

Na faɗa a hankali.

Duk kunya ta cika ni.

"To muje in zagaya dake"

Ya faɗa yana mai wucewa gaba, cikin salon takun tafiyar shi.

A hankali na shiga bin shi, ashe wajen yana da girma da faɗi har haka?

Gaskiya wurin ya bani sha'awa matuƙa, wani wurin ma ko ciyawun babu, saidai flowers da suka zuzzubo suka rufe ƙasar dake shimfiɗe wurin.

Ya Ameen ya zage fa surutu, saidai duk Abunda zai faɗa cikin irin halin shi yake faɗa, kai da gani kasan surutu ba halin shi bane, illa iyaka ƙoƙarin da yakeyi na in saki jikina dashi.

Mun ɗan yi yawo ba laifi, har na fara gajiya.

Lura da yayi na fara gajiya ne ya sanya shi cewa mu zauna in huta.

Bisa koren ciyawa muka zauna, ina mai tattare ƙafafu na duka, shima kusa dani ya zauna yana mai faɗin.

"Ko kin gaji ne mu tafi?"

Da kai na ɗan amsa mashi, ina mai faɗin "Ina gudu ne dare yayi, gashi munyi nisa da makaranta"

"Kada ki damu, insha Allahu makaranta zaki kwana"

Ban fahimci me yake nufi ba, illa iyaka dai naga yayi shiru, yana mai jawo wayar shi ya shiga lallatsawa.

Sai kuma naga ya ɗaga ta yana ta ɗaukar mu hotuna da muke zaune kusa da juna haka.

Hannuwa na duka na sanya ina mai kare fuska ta, cikin shagwaɓa nake cewa "Kai Yaya?"

Ɗan murmushi ya saka yana mai faɗin "Bacci zai dinga taya ni, kafin kizo"

Da sauri na kalle shi, sai kuma na kauda kai cike da kunya, Amman shi naga ma ko a jikin shi, hidimar shi kawai yakeyi, saida yayi mai isar shi, sana Naji yana faɗin

"To tashi muje ko? Na fara jin yunwa, gashi kuma wife ɗin tawa bata iya tarbar baƙi ba, koda kuwa da abun sha ne"

Sai a lokacin kuma Naji wata Kunyar ta sake kama ni, a haka na shiga bi shi har gaban motar, saida ya buɗe mani na shiga na zauna, sannan naga shima ya zagaya ya shiga.

Kaman kar na bar wurin haka nake ji.

Da kallo na dinga bin wurin, har muka ɓace daga wurin muka hau titi.

Ba zan iya fassara halin da nake ciki ba a yanzu, kasancewa ta atare da ya Ameen na ɗan wani lokaci ya mantr dani wasu damuwoyi na, ashe haka Ya Ameen ɗin yake? Rashin sani ya sanya nake mashi fassara kala kala a cikin zuciyar tawa.

Na mai girman kai, mai ji da kanshi, mai ɗagawa da miskilanci.

Ashe sai in baka zauna dashi bane yake haka.

A hankali na shiga wara idanun nawa, ganin mun dawo cikin garin zariyn.

Amma ga mamaki na, maimakon mu nufi makaranta, sai naga mun wuce cikin gari.

Wani irin restaurant ne naga munyi parking a gaban shi.

Wannan karon ma shine ya buɗe mani, Nidai har yanzu da mamaki nake kallon shi, kaman wata sarauniya haka ya maida ni.

A hankali na shiga bin bayan shi, wata ƙofa mai kyau naga mun nufa, a saman ta an rubuta VIP.

Ɗamin ya matuƙar ƙayatuwa, kaman kana gidan ka, kai wani ko a gidan shi ba zai samu haka ba.

Fali ne babba, yana ɗauke da set ɗin kujeru masu kyau, irin na gidan alfarma.

Tsakiyar su da wani irin centre table.

Suna da Stools guda huɗu gefe da gefen kujern.

Tiles ne malale a tsakiyar falon, sai wani irin chinese carpet da ya kusa cinye rabin falon.

Ƙatuwar tv na bisa tv stand da akayi da POP akayi ma wani irin ado da fitilu masu haske sosai kowanne launi.

Sai daga cen gefe ne dining table ne mai kyau, na zallar glass mai ɗaukar idanu, saman shi cike yake da abinciccika kala kala.

Wurin dai daga i shirya shi akayi na musamman.

Gefen dining table ɗin sink ne na wanke hannu, da towels na tsane hannu.

Kai tsaye kujera yaja mani yana mai faɗin "Have a sit wife" haka na zauna ina mai ɗan bin shi da kallo.

Yaushe duk yasanya aka harhaɗa waɗannan abubuwan?

Dare fa nayi, Amman hankalin shi kwance kaman ma ba yau zai tafi ba.

Shima kujera yaja yan mai zama inda zai iya fuskanta ta.

"who will serve us?" ya faɗa cikin ƴar zaulaya, yana mai sakin wani ɗan guntun murmushi.

A hankali na miƙe ina mai kai hannu saman serving spoon ɗin, cikin rashin sa'a shima ya kai hannu, hannuna ne ya sauka bisan nashi, kaman wadda aka jona ma shork haka nayi maza na janye hannun.

"Ni na isa? Zauna princess ne kike so in zuba maki"

A hankali na koma na zauna, ina mai cewa "Abunda zaka ci yaya, ni bana jin yunwa sosai"

"Sure?" ya faɗa yana mai ɗan kanne mani idanu ɗaya.

Ɗaga mashi kai na shiga yi, nima ina mai ɗan kallon shi da murmushi, duk na takura, wallahi ji nake kaman ba Suhan ɗin Umma ba.

Abincin ya shiga zuba mani, ɗan daidai daidai, sai kuma shima ya zuba ma kanshi.

"Ko in haɗa mana?"

Ya faɗa cikin wani irin salo na tambaya.

Girgiza kai na shiga yi a hankali, ina mia jawo gefen gyalena na rufe fuska ta.

"Hmm alright" ya faɗa cikin wani irin yanayi mia nuni da watarana ma a baki zan baki.

Lemon 5alive shima ya zuba mani cikin wani cup dogo mai garai garai.

Duk na takura, yayin da shima ya shiga cin abincin shi, hankalin shi kwance.

Akwai akai yana mai duba agogon hannun nashi.

Tsam ya miƙe yana goge baki da tissue, yana mai faɗin "Kici abincin nan kafin inyo salla in dawo, in ba haka ba, ɗura zan mani"

Ya faɗa yana mai zagaye ni ya fice daga falon, cikin sauri, kaman ya soma makara masallacin.

Da ɗan kallo na shiga binshi, wannan kuwa anya ba zanyi fama dashi ba? Duk lokacin da akace an ɗaura mani aure dashi.

Ganin ya fita ne, ya sanya ni fara cin abincin, yayi mani daɗi, saidai duk da haka ba zan iya sakin jiki inci abinci ba, a rana ta uku da sanin shi a matsayin masoyi.

Har ya dawo ina mai ɗan jujjuya cokali.

Da kallon bakiciba ko? Ya shiga bina.

Da sauri nace "Allah kuwa Yaya naci sosai"

"Ok" Ya faɗa yana mai zama, sai kuma ya ɗauki ruwa ya ɗan kurɓa haka yana mai faɗin "Muje ko?"

Da kallo nabi kayan abincin, nan fa duk ya biya, gashi sun zama wastage, in banda abun Ya Ameen wannan kayan abincin ai ko mutum goma zasu iya ci su ƙoshi har su rage.

A mota ne yake tambaya ta wai ko akwai Abunda nake buƙata?

Ɗan girgiza mashi kai nayi, ina mai cewa "Babu yaya"

Duk da haka saida ya tsaya wani shopping complex, saidai naga ana jijjibga abubuwa a mota.

Bamu sha wahala ba wajen shiga makarantar, tin dai daya nuna ma masu gadi Id card ɗinshi, sai naga ma har wani sara mashi suke yi.

Hankali na ya ɗan tashi ganin irin kayan da ya jijjibgo mani,to duka ma yaushe ne zamu samun hutun semester? Bai wuce sati uku nan gaba fa.

Godiya yai mashi sosai, har saida ya nuna mani ɓacin rai, sannan yace "Akwai biscuit da Sweet a ciki, harda springles ma, irin waɗanda kike ci da kina kid"

Dariya ya bani har saida na dara.

Jingina yayi jikin motar, yana mai harɗe hanjuwa duka a ƙirji, cikin hasken soler ɗin dake yi hake iya kallon fuskar shi.

"Suhan zan koma masauki na, amman insha Allahu zuwa gobe zan wuce. Kada dai ki manta zuwa jibi ne ƙa'idar lokaci na ta cika"

Ya faɗa yana mai tsattsare ni da idanu.

"Himm" kawai nace ina mai sauke kaina ƙasa.

Sai kuma naga ya sake buɗe motar ya cire wata farar leda ya ya miƙo mani.

Wannan kyauta ce daga hannun Mijin ki, bana so kuna kallo na a wani mutum daban, Suhan ni ne mijinki da izinin Allah, don haka duk Abunda kike buƙata feel free ki tambaye ni. insha Allahu babu Abunda zai gagara, maganar Mom ki ajiye ta gefe, kada ki sake damuwar kanki akan al'amarin, insha Allahu komai mai zuwa ne dasauƙi"

Nidai a ƙasa ƙasa nake kallon shi.

Yau ɗin ta daban ce a tsarin rayuwar tawa.

Godiya na shiga yi mashi a sanyaye cikin jin kunya.

"Ki kira frienss ɗinki su tayaki ɗibar kayan. And Bilal yace in gaida mashi ke, yayi wata ƴar tafiya ne, da tare zamu zo"

"Ina amsawa". Na faɗa cikin sakin murmushi, ko ba komai Bilal ɗin ya kula damu sosai lokacin da babu Ya Ameen ɗin, har ma munyi sabon da ko Ya Ameen ban saki jiki dashi haka ba, bansan kuma dalili ba.

Komawa yayi cikin mota yana mai faɗin "I am going to miss u Wify, zamuyi waya"

Ina ji ina kallo yaja motar yayi ribos ya fice.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi na saki, ina maida kallo na bisa kayan daya jibge mani harda su Lemuna na kwali manya manya, da kayan ƙwalama irin na ƴan makaranta.

Number ɗin Raihana na kira, ai kuwa sai gasu ita da khadee.

Cikin mamakin yawan kayan suka shiga taya ni kwasa, har muka shige dasu duka ɗaki.

Kowa mamakin kayan yakeyi, masalan ɗana faɗa masu Ya Ameen ne ya siya mani, kuma tare muka fita.

Sun tayani murna matuƙa, masalan Raihana, domin khadee na lura har yanzu akwai wani miki dake yawo cikin ranta, duk kuwa da tana ƙoƙarin karewa kada in gani.

Ina kallon raihana na zungurar ta,

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment