Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mayar maka, kafin a gama gyaran"

Itama ta faɗa, tana mai nuna mashi makullin part ɗin da hannu.

Bai ce komai ba, ya shiga taka wa a hankali, yana mai ɗaukar keys ɗin sannan ya fice.

Ko da ya fito har Bilal yabar wurin, hakan ce ta sanya shi bai tsaya sauraran komai ba, ya wuce zuwa guest room ɗin kai tsaye, yana mai ɗan kallon sashen su Suhan ɗin, yana mai raya ma ranshi dama ace tana gidan yanzu ta fito ya ganta.

Daf da zai shiga part ɗinne ya hango fitowar Alhajin, kai tsaye shima wajen kayan y nufa yana masu magana, su kuma suna ta faman gaida shi.

Kai tsaye ya juya zuw aga Dad ɗin nashi.

"Kaje ka huta, zamuyi magana da daddare"

Abunda Dad ɗin ya faɗ a mashi kenan, domin yana iya hango tarin gajiya akan fuskar yaron nashi.

******


"kin tabbata da kammaluwar komai?, domin fa kinsan idan akwai Abunda na tsana a rayuwa ta bai wuce yarinyar da maman ta ba"

"Haba hajiya ta, ai baki da matsala, gani ga laila ma, tare muka sake komawa, kuma malam ɗin ya sake jaddada mana cewa indai aka bi sharuɗɗan da ya gindaya mana, aiki ziyi kyau fiye da yanda muke tsammani, kedai kawai kiyi ƙoƙarin ganin bai kusance ta ba, domin ana ɗaura auren nan fa, zaiji babu wadda ya tsana irin ta, ita dai Uwar ce malam yace muyi haƙurin ganin an gama da lamarin ɗiyar, saboda ita akwai wani al'amari mai girma tattare da ita"

Gyaɗa kia ta shiga yi cikin gamsuwa, "Ba matsala indai dan wannan ne, cin amanar da suka yi mani, ba zan taɓa kyale su su tafi hakanan ba, sai sunyi nadamar shiga rayuwa ta da sukayi"

Ta faɗa cikin kaushin murya, tana mai sauke wayar daga kunnen ta.

" Zasuyi danasani."


********


Kullum ya ganta babu Abunda ke faɗo mashi cikin rai, illa iyaka yaga cewa ya same ta.

Shifa Maree ce kaɗai wadda yake ganin dacewar shi da ita.

Ada kua baya jin hakan a ranshi, ko shi gani yake ya wuce da iyawar ta, Amman dai koma minene zai je ya samu alhaji da maganar akan cewa yana so a aura mashi maree, wallahi idan bai aure ta ba, yana jin za'a samu matsala, ya tabbata ba zata ƙi shi ba, masalan ma idna akayi la'akari da cewa shi ɗan aiki ne itama ƴar aiki ce.


*********


Sai bayan daya kammala komai ne, sannan ya kira ta, duk da bacci da yake ji, Amman yana tunanin idna ba muryar ta yaji ba, baccin ma gagarar shi zaiyi.

Sun daɗe kuwa suna waya, kalami yake zuba mata masu narkar da zuciya, shida baiƙi ma ace gobe a ɗaura auren nan ba , yana ganin wutar shi da cen baya, da ya tsaya ruwan ido, ashe ga wadda ta dace dashi ma tana rayuwa a cikin gidan ba tare da sanin shi ba.

Mun jima sosai a waya, kiran Umma da nagani yana shigowa wayar tawa ne ya sanya ni ce mashi yayi haƙuri zan sake kiran shi.

Shaida mani ta shiga yi, da zaran na kammala Jarabawa ta gobe, in shirya za'a zo a ɗauke ni, dukkan abubuwan da nasan zan buƙata in ɗauka, domin ba lallai in koma makarantar ba saida aure na akai.

Kunya Naji ta kama ni. Nan na kashe ina mai amsa mata, sannan na kira shi, nake faɗa mashi Amman Umman tace driver ne zai zo ya ɗaukeni da kanshi.

Faɗa ya kama yi, wia minene amfanin shi, shine zai zo da kanshi ya ɗaukeni, tinda ai yana gari.

Shifa ba zai lamunci yawan shiga motar driver ba, kai infact ma da munyi auren zai koya mani mota, yana matuƙar kishi na, ace kullum duk inda zani ina tare da wani ƙato, gara ya koya mani in dinga jan kaina.

Ya zuwa yanzu, na sakankance ma soyayyar da Ya Ameen ɗin yake yi mani, ashe dama haka yake, da nayi mashi gurguwar fahimta, sai nake ganin ko Afnan yanzu bata kaishi daɗin zama ba.

Har addu'a nake yi, bayan auren namu, in samu zaman lafiya, da kwatankwacin ƙaunar da yake nuna mani yanzu, domin ni kaina na sani, a yadda nake ba kowa ɗinnan ba, ace na samu miji kaman ya Ameen tabbas nayi ma mata zarra, bana kuma tunanin idan akwai wadda zata iya kamo ni nan kusa.

Haka mukayi sallama dashi, kaman kar mu rabu, kowa na begen juna, duk da har yanzu ina jin kunyar shi, domin wani abu ɗin idan ya faɗa sai na sauke kaina ƙasa tsabar kunya kaman yana gaba na.

Umman na sake kira na shaida mata yanda mukayi da ya Ameen ɗin.

Cewa tayi to ba damuwa, ai sai a gaya mashi inda zai kai ni, domin dai dama shi ɗin ba baƙon wurin bane.

Kai A ya ɗaure, tambayar ta na shiga yi akan cewa ban gane ba, kaman ya inda zai kai ni.

Cewa tayi in bari goben na gani.

Nidai haka na kashe wayar tawa, to me Umman ke nufi? Ni fa wannan hali na Umma na damu na, ita bata taɓa fitowa fili ta sanar da kai komai, tafi so komai ka gani da idon ka, inma ka tambaye ta, ba zata taɓa faɗa maka ba.


Haka na kwana cikin zulumi sosai, koda ya kira da daddare yaji kaman bana lafiya, ba irin tambayar da baiyi mani ba, Amman na shaida mashi cewa babu komai. Haka mukayi firar dai ba wani annashuwa, duk yanda yayi ya shawo kaina kasawa yayi, saidai ya haƙura ya ƙyale ni, shima ran nashi babu daɗi.

Washegari na shiga tattara kaya na, shaida ma su Raihana nayi komai da ake ciki, sunyi alƙawarin halartar biki na ɗin, da cewr idan lokacin yayi in turo masu da katin ko ta waya ne, zasu kira ni.

Cikin wata irin rantsattsar mota ya iso makarantar tamu, misalin ƙarfe sha biyu, shi kaina da kallon mamaki ya shiga bina, jin inda akace ya kai ni, kuma Dad ne ya shaida mashi da kanshi, duk da yace zasuyi magana jiya Dad ɗin bai dawo da wuri ba, yana cen harkoki sun riƙe shi, shirya ɗaurin aure yake yi mai cike da ƙawatarwa, saboda ko ba komai tuwon girma miyar shi nama.

Da kanshi ya dinga kwasar kaya na yana zubawa but, mutane sai mamaki suke yi, wasu na cewa Al'ameen Dambulan ne, wasu kuma na cewa bashi bane, saida Khadeeja ta shaida masu cewa shine, nan fa wasu suka fara ɗaukar shi hoto da waya ba tare da ya kula ma dasu ba.

Nidai da kallo nake binshi, yayi matuƙar kyau cikin manyan kaya, shadda ruwan ƙasa, da hula tangaran da takalma half cover sai kalli suke yi.

Khadeeja kasa tsayawa tayi wurin, haka ta juya zuwa ɗakin namu, zuciyar ta cike da ƙuna da suya, tabbas so daban ne, watau kuma son maso wani ƙoshin wahala ne, ita tana ganin son da Suhan keyi ma Al'ameen ko rabi rabin nata bata yi mashi, da ace ita ce Allah zai mallaka ma Al'ameen ɗin da ta kusa kashe shi da soyayyar ta.

Haka ya zagaya yana mai buɗe mani sit ɗin gaba, ba gaddamanna shiga, har yanzu ba walwala sosai a tare dani, saidai ganin shin da nayi ya mantar dani kusan komai.

Haka muka bar makarantar, tuƙi yake cikin gwanancewa, rabin hankalin shi duk yana kaina.

Hannun shi guda ɗaya ya sanya ya riƙe steary ɗin, yayin da gudan yayi amfani dashi wajen kamo nawa,

"Me ke damun ki ne dear? Ko zullumin auren ne har kin fara?"

Ya faɗa a hankali, cikin salon muryar shi, mai sanyaya mani jiki.

Ban ƙoƙarin ƙwace hannun nawa ba, saidai ina jin taushi da ɗumin hannun nashi har cikin kwalwa ta.

Ba ce dashi komai ba.

Shima bai sake cewa komai ba, sai ma tuƙin shi da yake hankali kwance, har yanzu bai saki hannun nawa ba.

Yatsan da zoben da ya saka mani yake murzawa a hankali.

"Thanks dear"

"For what?" na bashi amsa a hankali.

"Keeping my promise"

"Uhmm"

Na sake faɗa ina mai ɗan ƙoƙarin zare hannu na daga cikin nashi.

Sai kuma na ƙware da miyau ɗin da ya tsinke mani yana ta gudu cikin baki na.

Tari na fara yi, yayin da cikin ƴar ruɗewa ya saki kan motar yana mai tallafi dukkanin kaina, ya shiga hura mani iskar bakin shi a saman fuska ta.

Ganin kan motar ya fara yawo ne, ya sanya ni sake sakin ƙara, ganin gadan gadan motar ta nufi wani rami daki gefen titn.

Wata ƙarar na sake saki. Cike da firgita nake faɗin

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Yaya tuƙi fa kake yi."

Cikin gwanancewa ya riƙo kan motar, yan amai murza ta ya sauka daga kan titn ta ɓarayin da babu ramin yayi parking.

Cikin daji ne, hakan ya sanya ni sake kallon shi, idanuna har sun kaɗa sunyi ja.

Gorar Sona ya ɗauko daga cikin ɗan fridge ɗin motar, ya ɓalle murfin yana mai kara mani a baki.

"sha ruwa my matsoraciya , ashe haka kike da tsoro?

Ya faɗa yana mai kallo na da ɗan murmushi.

Ban musu ba na amsa ina mai tuttula ruwan a baki na, sai kuma na sauke ajiyar zuciya ina mai faɗin" huh" sannan na runtse idanuna, ina mai rufe fuska ta da tafukan hannaye na.

"Kina tsoron ki mutu baki ganki a ɗaki na ba ne?"

Ya faɗa a hankali yana mai ɗan keanto da fuskar shi saitin tawa, domin ya kalli cikin idanun nawa sosai.

Ba ce mashi komai ba, illa "Yaya Please mu bar wurin nan, Allah ina tsoron daji" na faɗa cikin tuno da Abunda ya faru dani ranar da zamu haɗu da Sir Salim.

Shima bai ce komai ba, ganin bana cikin natsuwa ya sanya shi sake tada motar ya hau titi.

Mu biyu muke ta tafiyar mu cikin mota a nutse, duk da uban gudun da yake shararawa, bamu tsaya ko ina ba, kasancewar Naji yana faɗin tafiyar da nisa.

Kaman in tambaye shi, sai kuma na ƙyale shi, so nake inga inda za'a kai in kaman yanda Umman ta faɗa.

Snacks ya ɗauko mani a bayan motar, haɗi da lemo, yace inci, saboda ba zamu tsaya ba.

Kaɗan naci na ajiye, duk Kunyar shi ta cika ni, gani nake ba zan iya sakin ciki in i wani abu a gaban shi ba.

Soyayya yake zuba mani mai tsabta, ji nake kaman ina a aljanna ne, ga sanyi dake ratsa ni a hankali a hankali, ga ƙamshi sosai cikin motar, da kuma wanda ke tasowa daga jikin mamallakin motar.

Ko salla bamu tsaya ba, a cewar shi ai ƙasau zamuyi.

Ba zan iya cewa ga sunan garin da muka isa ba, saboda ko a mafarki ban taɓa ganin garin ba, saidai abunda na kula dashi shine ƴan garin suna da matuƙar kyau, kuma kowa hidimar shi yakeyi ba ruwan shi da kowa.

Titin da muka ɗauka, shi yafi komai burge ni, da mamaki nake kallon Ya Ameen ɗin, shima ka faɗa ya ɗaga mani cikin wani salo yake cewa "Ohh nima haka akece mani in kawo ki nan"

Gate kusan nawa muka wuce, sai nake ganin kaman masarauta ce inda muke nufa, domin na fara ganin wasu mutane masu kama da dogara wa, kuma duk Gate ɗin da muka wuce sune ke tsaron Gate ɗin.

Na yarda shima Baisan komai a kai ba. Ban ƙara mamaki ba, saida naga mun shiga wata damfareriyar masarauta mai matuƙar kyau da ƙawatuwa tin daga waje.

Inda aka tanada wajen yin parking nan naga mun dosa.

Saida mukayi parking ne ya fito, ya zagayo yana mai ɓalle mani murfin motar.

Wasu gungun mata ne sanye da wani irin kaya iri guda mai kalar ruwan omo, sai maza masu sanye da kalar kayan suma.

Sannan dogarawa da kuma wasu gungun dattaw amasu ɗauke da rawani a saman kansu da babbar riga.

Tako wa muka fara yi a hankali muna nufar inda mutanen nan ke nufi mu suma.

Suna ƙarasowa naji an yafa mani wani abu tin daga kaina har ƙasa, ina dubawa naga Alkyabba ce, kallo na na maida kan Ya Ameen da yaje ta faman gaisawa da mutane, kaman dama cen ya sansu, ko ma ya sansu ɗinne oho?

"Ranki ta daɗe, barka da ƙarasowa"

Naji suna ta faɗa, lokaci guda kuma wata tana mai kamo hannuwa na ta nufi wani sashen na gidan dani.

Da kallo nake waiwayar Ya Ameen da naga suma mazan suna ta mashi biyayya, sun nufi wani sashe dashi na gidan.

Inda aka shigar dani dai kaman fada, a yanda na lura.

Wata mata ce dattijuwa ta taso da kanta ta tare ni, tana mai rungume ni tsam cikin jikin ta, mun daɗe a haka, sannan ya sake ji tana mai cewa "A kai ta ɗakin Gimbiya Merama domin ta huta tayi wanka"

Haka suka kuma hana zuwa wani ɗaki mai masifar kyau, an gaya ko ina sai ƙamshi yakeyi, tunani nake ta faman yi, nan ina ne aka kawo ni? Me ya Ameen da Umma suke nufi ne to?

Wasu haɗimai ne suka kuma shigowa da tulinbkaya a hannun su, sai kuma akwatuna na nakaya, suna fita wasu suka shigo ɗauke da wasu irin manya manyan ƙwarya cike da kayan marmari a cikin su.

Wata baiwa ce ta ƙara so inda nake zaune turus duk mamaki.

"Ranki ya daɗe, an kammala haɗa ruwan wankan, ki taso muje in nuna maki"

Ba ce ƙala ba, na miƙe ina mai nufar inda take bi, wani ɗan saƙo ne a cikin ɗakin.

Muna binshi muka isa wani haɗaɗɗen toilet, an haɗa ruwan wanka cikin baho sai tashin ƙamshi suke yi da tururi.

"Kiyi wanka Ranki ya daɗe, Fulani na nan shigowa da kanta zuwa gareki"

Da mamaki nake binta da kallo.

"Nan ina ne wai?"

Abunda na ita furta mata kenan.

"Masarutar Mai martaba Muhammadu Bello Barkindo Lamiɗo"

Abunda ta iya faɗa mani kenan ta juya tana mia russunawa gareni ta fice.

Na gaji sosai, haka na shiga kwaɓe kayan nayi wankan, sai tashin ƙamshi nakeyi, ina fitowa na tadda kaya ajiye saman gado, da kuma kayan shafa masu masifar kyau jere bisa mirror ɗin dake ɗakin.

Komai akwai a kayan da aka ajiye mani, hatta da eaner wears akwai.

Haka na koma banɗakin na saka kayan.

Kaya ne irin na sarauta sosai, sarauta ma kaman ta Fulani, domin kayan saƙi ne irin na kayan Fulani, saidai waɗannan an zamanantar dasu, sai walwali sukeyi.

Gaban mirror ɗin na koma ina mai shafa mai, sannan na koma bisa gado na zauna, ina mai ɗaukar Apple ɗaya na fara ci.

Wayata da ke ajiye gefe na ɗauko ina mai latsa number ɗin Ya Ameen.

Saida ta kusa katse wa ne ya ɗaga.

"Am sorry ina wanka ne wify"

"Yaya ina ne ka kawo ni nan?"

"Ina na kawo mu dai zaki ce?"

Ya faɗa shima da ɗan murmushi.

"Eh Yaya"

Kina Jihar Adamawa my Wife, ki kwantar da hankalin ki, zasuyi mana bayani, kina gidan girma ne anan"

Ya faɗa yana mai goge jikin shi da ƙaramin towel dake saman kanshi.

"Yaya Nifa tsoro nake ji"

Bai kia ga bani amsa ba, naga haɗimai na shigowa tare da wata mata, suna mai sunkuyawa gareta cike da girmamawa.

Nuni tayi masu da hannu akan su fita.

Ba musu suka fice sun amai nuna biyayya gareta.

Samun wajen zama tayi ta zauna.

"Maraba da Gimbiya mau Sunan mai babban ɗaki, ɗiya ga Gimbiya Gimbiya Merama hasken masarautar Adamawa"

Duk cikin kalaman ta ban iya tsintar ɗaya ba na fahimta.

Da kallo nake kuma binta, saidai na Gaza cewa komai sai "Ina yini?"

"Barka da wannan lokacin Gimbiya Suhan, nasan zakiyi mamakin ganin ki anan wajen, ki kwantar da hankalin ki, ke ba baƙuwa bace a nan gidan, duk da nasan ba lallai ki fahimci komai a sannu ba, Amman ina so ki sani, ya zama wajibi ki saki jikin ki damu, nan shine inda zaki zauna har zuwa lokacin ɗaurin auren naki"

Toh fa!

Nan zan zauna kuma?

A hankali na ɗaga kai ina mai kuma kallon ta.

"Nan shine gidan su Mahaifiyar ki Gimbiya Merama kaltingo"

Waro idanu na kuma yi.

Tau fa, sunan Umman tawa Maryama shine ta koma Merama kaltingo?

Ganin mamaki shimfiɗe a saman fuska ta, ya sanya ta sakin wani ɗan murmushi.

"Kada ki damu jiƙa ta, ki saki jiki ki huta, yanzu za'a shigo maki da abinci, kici sosai kafin mai martaba ya shirya ganawa daku, keda angon naki"

Abud ata faɗa kenan, ta miƙe a hankali, tana mai tattare Alkyabba sannan ta fice daga ɗakin.

Da kallo na shiga binta, kwanya ta gabaki ɗaya ta cushe.

Nan ne Gidan su Umma kuma?

Haba tayaya za'a ce haka? Bayan nasan Umma ta ƴar aiki ce a gidan su Suhan? Tayaya za'a ce ƴar sarki ce taje tana aikin bauta a wani gida, Ummata da gatan ta, ba zata taɓa iya tsallake wannan daular taje tayi zaman ƙas-ƙanci ba.

Wayata na jawo ina mai latsa number ɗin umman.

Biyu biyu ma nake gani, jin kaina nake kaman zai tarwatse, sai numfashi nake fiddawa akai akai, na ras ama tunanin da zanyi.

Na kira ya kai sau goma Amman bata ɗaga ba.

A hankali na miƙe daga zaunn, na fara safa da marwa cikin tanƙamemen ɗakin, wand a ake ta faman bi da kallo, hannuwa na goye bisa bayan nawa.

Wai wace irin rayuwa ce nakeyi haka NI Suhan? Da farko ƴar aiki? Sai ƴar makaranta? Sai wadda aka sama biki da namiji ɗaya tamkar da dubu? Sai kuma wai Gimbiya Suhan ɗiyar Gimbiya Merama?

Wasu mata ne nagani sun kuma shigowa ɗauke da kayan abinci.

Basu ce ƙala ba, illa sunkuya mani da sukayi, suka shiga her kayan abincin gabana.

Suna ficewa na sake ɗauko wayar na kira Layin yaya.

Yana ganin kiran ya saki murmushi yana mai amsawa.

Shi fa duk a zaton shi, Dad ne ya sanya a kawo ni nan, saboda wani dalili nashi.

"my Wife"

Abunda ya iya faɗa kenan.

"Yaya ban fahimce su ba Sam, suna faɗ aman wasu maganganu masu rikitarwa, kayi mani bayani yaya, me ka sani game d anan gidan?"

"Look sweet janam, ki kwantar da hankalin ki, yanzu zamu gana da mai martaba, shine zaiyi mana dukkanin cikakken bayani, ance yanzu za'a mana iso wajen shi,kici abinci please"

Yana gama faɗar haka ya datse kiran.

Bazan iya cin komai ba.

Jina nake kaman wata mahaikaciya.

Bayan kaman rabin awa ne, har na kammala salla ta, sai ga wasu bayi sun shigo, cike da girmamawa suke faɗin

"ran gimbiya ya daɗe, mai martaba na son ganin ki"

Ban masu musu ba na miƙe, ina mai yafa gyale na, dakatar dani suka yi, suna mai yafa mani Alkyabba.

Babban gida ne masha Allahu, ya gaji da haɗuwa, kaman ba masarauta ba da aka sani da ginin ƙasa.

Duk inda muka gitta kallo na ake tayi.

Oho masu, koma dai minene na ƙagara inje wajen mai martaba en domin ya fidda ni a duhu.

Wata ƙaramar fada ce aka shiga dani, jakadiya ce tayi mani iso har cikin faɗar, sannan ta kwashi gaisuwa tana mai juyawa.

A cen na tadda Ya Ameen zaune tankwashe da ƙafafu, jikin shi sanye da wata shaddar an mata ɗinki da aikin sarauta ko ina a jikin ta, yayi matuƙar kyau, Amman dayake hankali na ya kasu gida biyu, sai ban damu da kyaun da yayi ba.

Wuri na samu gefe ina mai zama, cike da girmamawa na ce ma mai martaba "ina yini?"

"Barka da wannan lokaci mai babban ɗaki"

Shima mai babban ɗakin ya kira ni.

A hankali na ɗaga kaina, ina mai duban shi, ya man kwarjini sosai. Sadda kaina ƙasa nayi, daidai lokacin da na tsinkayo muryar shi yana mai faɗin "Barka da dawowa gida Gimbiya Suhan ɗiya ga Gimbiya Merama hasken masarauta"

Cikin ɗan zaro idanu na kuma ɗagowa nima ina mai kallon shi.

Murmushi ya saki, sannan ya nisa ya cigaba da cewa

"Nasan baki sani ba, nasan mahaifiyar ki bata sanar dake komai ba, kaman yanda ta shaida mana, saidai muna so ki sani, nan da kika gani gidan su mahaifiyar ki ne, watau umman ki, kuma zaki cigaba da zama tare damu ne har zuwa lokacin ɗaurin auren naku"

Ai fitsari ne kawai ban saki ba, Amman shima kaɗan ya rage, a tare muka zaro idanu da ya Ameen ɗin da shima tinda mai martaba ya fara magana yake sauraron shi.

"Nan kuma gidan su Umma kuma? Dama Umma ƴar sarauta ce? Amman taje tana aiki a gidan nasu tsawon lokaci? Me yaja mata? Menene dalilin ta nayin hakan? Gimbiya Merama? Shine sunan da duk lokacin daya kawo ziyara masarautar yake ji suna yawan ambata, dayake duk idan zai je IDPs camp sai ya fara kawo gaisuwa masarautar kafin nan yake wucewa, wannan ce ta sanya sun sanshi sosai matuƙa, kuma masarauta tana yaba mashi haɗi da jinjina ma namijin ƙoƙarin shi.

"Tanka ya daɗe Ummata ta faɗa mani bama da kowa, bama da dangi duka sun mutu"

Ya tsinkayo muryar ta, tana faɗa cikin rawar murya, kaman zata saki kuka.

"Ta shaida maki haka ne, a bisa wani dalilin ta, wanda sai nan gaba ne zamu ji shi muma, Amman ki sani Umman ki kuwa ita ke da kowa, ita ke da gata, ita ke da asali, sannan kema kina da asali mai kyau, kuma mu nan da kika gani duk ƴan uwan ku ne, domin haka ki saki jikin ki damu, nan gidan ku ne"

Ba ni ba har Ya Ameen ya matuƙar kaɗuw ada jin wannan kalaman da suke fita daga bakin Mai Martaba, daga ni har shi ɗin kowa da abun da yake saƙawa a ranshi.

A hankali na ɗago ina mai maida kallo na saman fuskar Ya Ameen ɗin. Girgiza mani kai ya shiga yi kada inyi kuka , ganin kwallar da ta taru a idanun nawa, wanda na Gaza riƙe su,sia faman shatata sukeyi.

Ya ba zanyi kuka ba? Tsawon wannan lokaci ina tambayar Ummana akan asalin namu da dangin namu, bata taɓa shaida mani ba, sai yau kwatsam ace in tsinci kaina cikin su?

Wani irin kuka na ɓalle dashi, ko a haka ya Ameen ya barni ya gama mani komai, ya yarda zai aure ni ba tare da sanin ko ni ɗin wacece ba, ba tare da sanin cikakken asali na ba, ba tare da yarda da huɗubar mahaifiyar shi a kaina ba, ya tallafi rayuwa ta, ya tallafi ta mahaifiyar ta, ya tsaya akan karatu na, ya tsaya akan lafiyar Umma ta, yau sai gashi shine da kanshi ya ɗauko ni yana mai sada ni

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment