Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su. yayin da Abie ma ya miƙe ya nufi ɗakin shi, yana mai faɗin "Mom bari inje in watsa ruwa nima"

Da kallo ta bisu dukan su, har suka ɓace ma ganin ta. Zuciyar ta na ayyana mata abubuwa iri iri, watau yanzu aka fara wasan.


********


Umma ce zaune bakin gadon nata.

Tunani ne kala kala cikin ran nata, saidai ita tana ganin wannan ne kawai abun da ya dace tayi, a tsawon shekarn da ta ɗauka, daidai da rana ɗaya bata taɓa tunanin komawa mahaifar tata ba, saidai bata da zaɓi ne, wannan karon ta shirya tsab, koda kuwa cewa daidai yake da rasa rayuwar ta, ba zata taɓa bari yarinyar tata tayi zaman ƙunci a gidan miji ba, ta dalilin rashin sanin asalin ta.

Saidai ta ina zata fara?

Ita ɗin da kowa yake tunanin ta mutu, ita ɗin da kowa yake ma kallon maragayiya tsawon shekaru masu yawa.

"Hmm" ta faɗa tana mai nisa wa, sannan ta zakuɗa zaman nata, tana mai cewa "komai yazo ƙarshe, Mamana lokaci yayi da kema zaki dara, cikin dangin ki da ƴan uwan ki"

Wayar ta dake gefe ajiye ce ta ɗauki tsuwwa, alamun kira ya shigo.

Ganin baƙuwar number sai baisa tayi saurin ɗagawa ba, har ta katse, kiran ya kuma shigowa.

A hankali ta ɗaga, cikin manyance da dattako take amsa sallamar da akayi mata.

Muryar mace ce, cike take da annashuwa da fara'a.

A haka suka shiga gaisawa, saidai tin kafin ma Umman ta tambaya matar tayi saurin cewa "nasan baki gane ni ba, nice Hajiya Khaltum, Ammin Salim, malamin su Suhan"

Fara'a umman ta faɗaɗa, kunya na mai kama ta "Allah sarki Ammi, ya gida ya kwana biyu, nima ina ta so ince Suhan ta bani number ɗin in kira wallahi na shafa'a, da fatan dai kowa na lafiya?"

"Lafiya Lau Umma, dama cewa nayi bari in kira mu gaisa, tin bayan da abun nan ya faru bamu sake jin juna ba, Salim ne ke sanar dani an sanya ranar Suhan ɗin, shine nace bari in sanar dake, Suhan har yanzu ɗiya ta ce, saboda haka nake so ki amince ko zuwa sati guda ne kafin bikin in aiko da mai yi mata gyaran jiki irin namu na nan barno, sannan don Allah ki sanya ta, ta lissafo mani dukkanin abubuwan da take buƙata, da suka danganci kayan kitchen, insha Allahu duk na ɗauki nauyi, bana so kice a'a don Allah, alkhairi ne nayi niyyar yi, ko da ace ba Salim zata aura ba, ai shima namiji ne, nasan in nace tayo da kaina ba zata yo ba, kuma nasan idan na sanya Salim yayi mata maganar ba yi zaiyi ba, yace Kunyar yi mata magana yake ji, Shiyasa nace bari in biyo ta ɓangaren ki Umma, don Allah ki taimaka"

Mamaki ma ya hana Umma magana, iko sai Allah, har cikin zuciyar ta, tana jin ciwon rashin suruka da Suhan tayi irin Ammi ɗin, lallai wannan ƙauna daga Allah ne, babu Abunda zata iya cewa saidai godiya, da fatan Allah ya ƙara yalwata masu Arziƙi su.

Ta ɗaure ta da dukkanin jijiyoyin jikin ta, don haka ne ta shiga zuba mata godiya, "Ah haba ba wani abun godiya a ciki, ai har yanzu Suhan ɗiya ta ce" Ammin ta faɗa har yanzu cikin fara'a take.

Kaman Umman tace mata zasu shigo garin nasu, sai kuma ta share, tinda tafiyar ba tata bace ita ɗaya ai bai kamata ta ɓata masu lokaci ba, alabasshi bayan biki zata shirya da kanta zuwa wajen Ammi ɗin, takanas domin godiya da ƙauna da ɗawainiya, ko ba komai duk wanda yaso ɗanka ai kai yake so.

Haka sukayi sallama cikin mutun ta juna, kowa na girmama kowa, lallai Ammi ɗin ta cika mace, har ma tafi, duk wadda ya samu Ammi a matsayin Uwa, ko kuma a suruka, ya cencenci jinjina, Ammi ɗin irin matan nan ce da za'a iya cewa basu ɗauki duniya da zafi ba, kuɗi ilimi duk basu isa su sanya ta jin kanta a matsayin ita ɗin wata bace.

Number ta Umman ta kira, bayan mun gaisa ne take sanar dani yan da sukayi da Ammi.

Nima kunya ma sai ta kama ni, rabona da Ammin tin ranar rabuwar mu da Sir Salim ɗin.

Allah sarki Ammi, kenan ita bata yi fushi ba? Kenan ta fahimce mu? Gyaɗa kai kawai na shiga yi, ina yi ma Umman godiya, sannan ta gargaɗe ni da in lissafa kaɗan, domin anan Alhaji ne yace zaiyi komai, kada yaga kaman mun raina abunda yayi mana ne ɗin.

Taso tayi mani maganar zama na gidan tare dasu sai ta share, koma miye Hajiya Kubran ke shiryawa, da izinin Allah zai koma alkhairi ne, in ma domin ta ƙuntata mani ne, Allah yana kallon zukatan kowa, bama nufin su da sharri, insha Allahu ba zasu iya cutar damu ɗin ba.


Kiran na Umma na katse wa kiran Ya Ameen ya shigo.

Bansan na saki murmushi ba, har saida ta kusa katse wa sannan na ɗaga, wai ni irin jan ajin nan na mata.

Duk da yanzu na yarda ma kaina cewa ashe tsundum na faɗa soyayyar Ya Ameen ɗin, ashe da cen wauta nakeyi ba soyayya nakeyi da Sir Salim ba? Wasan yara ne nake mashi.

Ashe haka soyayyar take? Akai akai ni kaɗai na kan saki murmushi, wani lokacin har ƴar dariya nakeyi, idan na dinga tunano lokutta mabanbanta, lokacin da na suma a lambu ya ɗauko ni, da lokacin da naji wani abu na bina a bayan gida na faɗa mashi, da lokacin da ya shigo ɗakin ya tadda ni ina neman warin ɗan kunne na. Da lokacin da Umma bata lafiya naje na ruƙunƙume shi.

To dama wai cen ina sonshi ne? Ko kuma yanzu ne na fara, yanda nake ji a kanshi zuwa yanzu kaman na shekaru ina sonshi.

Na saki jiki dashi, dan dai ina jin kunyar shi yanzu sosai, wasu kalmomn da yake faɗa lokutta da dama, sai inga kaman ba shine ba, sai inga kaman ba daga bakin shi maganar ke futowa ba.

Sallama yakeyi, yayin da ni kuma na faɗa shauƙin tunanin soyayya.

"My wife kina ji na kuwa?"

Ya faɗa a hankali.

Kaman ince ka kira ni video yaya, sai kuma na share, ya zuwa yanzu ba abunda nake marari da muradin gani kaman Fuskar Yayan nawa, kuma mai shirin zama miji na nan gaba, zuwa lokaci ƙanƙani.

"Eh yaya, ina jinka, ina yini ya gida?"

"Lafiya lau ya karatu my sweet?" ya faɗa, yana mai mirginawa ya kuma matse filon dake hannun shi rungume.

"Alhamdulillah, gashi zamu fara exam, nan da sati mai zamu iya gamawa" na faɗa nima a hankali, cikin muryar da budurwa kan yi ga saurayin ta, ni kaina har mamakin kaina nakeyi, yanda na cenza lokaci guda, nice wai har nake sirara murya ta, ga ya Ameen ɗin, harda kashe murya duk domin yaji daɗi, lallai ma ni Suhan.

"Wow my hrt, Allah ya bada Sa'a, kiyi karatu sosai kinji dear"

"OK dear insha Allah"

Ɗan murmushi ya saki, jin har ta fara cenza mashi suna, hmm Suhan ma kenan, nan gaba yana da tabbacin sai ta rasa sunan ma da zata kira shi dashi, domin duk ta riga ta faɗe su a gareshi.

"Albishir na kira ki in maki my Janam"

Ɗan murmushi na saki, ina mai cewa "To Yaya ina sauraren ka"

"Menene tukuici na?". Ya faɗa kai tsaye, cikin sake sakin murmushi.

"Me kake so?"

"a'a dear kada ki ce haka, ba zaki iya bani ba"

"ka wuce komai a wuri na yaya" na faɗa ina mai kallon zoben da shine ya saka mani da kanshi a ɗan yasan nawa.

"OK shikenan tinda kince haka, I want deep Kiss"

Ɗan zaro ido nayi, ina mai ɗauke wayar daga kunne na.

Ƙit naji ya katse, sai gashi kuma ya sake kira ta video.

Duk da ina son ganin nashi, Amman Kunyar shi ta baibaye ni, haka na ɗaga a hankali ina mai sanya hannu na na rufe fuskar tawa.

" Look at ne dear, ke kika ce fa zaki iya, oya ina sauraren ki kiyi mani"

Ya faɗa yana mai lumshe idon shi da suke ɗauke da Zara zaran gashin ido.

Maimakon Kiss ɗin da yace in mashi, sai ma ƙura ma fuskar tashi idanu da nayi. Lips ɗinnan nashi pink mai duhu duhu kaman maroon, sai walƙiya suke kaman ya shafa masu lip balm, gashi bakin nashi ɗan tsut dashi. Wanda kwantaccen gashin baki ya zagaye, sai ya ƙara ma fuskar kyau.

Masha Allah, gaskiya Ya Ameen ƙarshe ne, komai nashi daban yake, jibi don Allah kaman shi ya halitta kanshi, ina da tabbacin cewa duk gidan shine ya ɗebo kyaun Alhaji Mustapha da Hajiya Kubra.

Bai ce komai ba, har yanzu kuma idanun nashi a lumshe suke, sai ɗan murmushin gefen baki da yake saki akai akai, ya sani sarai kallon shi nake, Amman da zai buɗe idon, sai fa in basar ko? Harma ina iya cewa meye abun kallo a ciki ko?

A hankali ya buɗe idanun nashi, aiko ta kama ni, idanu na ƙur akan fuskar tashi.

Maimakon in janye idanun nawa, sai na gyara zama.

Bansan lokacin da nace "yaya u are so much handsome"

"like u my beautefull wife"

Ya faɗa shima yana mai wani ƙanƙan ce idanu.

"Hmm more than me Yaya"

"Ban son wayau, ina jiran alƙawari na kafin na faɗa"

Ɗan murmushi na saki, ina mai cewa "OK dear later"

"promise?"

"Yeah promise"

"ok" ya faɗa yana mai tashi zaune, ya tattara dukkan natsuwar shi a kaina.

"Mom fa ta yarda da auren mu" bansan lokacin da na ɗago daga jinginn da nake ba, ina mai zaro idanu.

"wow are u sure Yaya?"

"Yep dear, don haka sai ki shirya zama surukar Mom, da na dawo daga tafiya zanzo mu tsara yadda komai zai kasance"

Wani murmushi na saki, ina mai sauke ajiyar zuciya a hankali a hankali.

Shima ya kula da yanda nake murna, Allah sarki Suhan, ashe dama tana sonshi, tsoron Mom ne ya cika mata zuciya.

Mamaki nakeyi yanda akayi ta amince lokaci guda, ko me ya faru kuma? Gashi Umma bata sanar dani komi dake faruwa a gidan, iyaka dai kawai fira ce tsakanin mu, da Abunda ya dangance mu.

"To Allah ya kaimu yaya" na faɗa nima ina mai sauke kai ƙasa, sai yanzu Kunyar murnar da nayi ta shiga kama ni, kaddai ace yayi tunanin dama cen ina sonshi.

Aiko abun da nake gudu ne ya faru.

"Yaushe kika fara sona har haka?"

Tambayar da ya jefa mani kenan.

Saurin kauda kaina nayi gefe, ina mai ɗan firgita hka, yanda maganar ta dakar mani zuciya.

"kwana uku da suka wuce" na faɗa ina mai ƙara sauke kai ƙasa cikin kunya.

Sai kuma na kife kan wayar a cinya ta.
"Banson ƙarya, wannan soyayyar tafi shekaru" na jiyo shi ta cikin earpiece yana faɗa, duk da bana kallon shi
Murmushi nake saki, lallai soyayya daban ce, masalan da ya Ameen ɗin.

Ba zan kuma cutar kaina ba, kaman yanda Raihana ta bani shawara, ni ɗin wadda Allah ya zaɓa ya mallaka mani zuciyar Ya Ameen ce cikin mata fiye da dubu, ba buƙatar in tsaya ɓata lokaci, ya Ameen ba irin mazan da ake sake dasu bane, Soyayya nake fatan mu shimfiɗa fiye da tunanin kowa, wani abun ma sai munyi aure, domin yanzu haka na shiga wani group na WhatsApp na matan aure ne zalla, ni kaina basu san bana da aure ba, a matar aure na shiga, suna koyar da abubuwa iri iri, ina ta ɗaukar darasi kuma, da burin dukkanin abubuwan da ake faɗa zan jaraba su akan Ya Ameen ɗin, domin na lura shi salon tashi soyayyar ta miskilai daban take da kowacce, gashi komai zaiyi cikin jan aji da ya ga yake yin shi, na daga abubuwan dake ƙara ma mata sonshi kenan, bayan kyawu da kuɗi da nasaba da Allah ya mallaka mashi.

Haka muka cigaba da waya tsawon lokaci, bana so ko network yayi rawa, shima ta ɓangaren shi, zamewa yayi yana mai kwantawa, rigingine, ya tada kanshi da hannun shi guda ɗaya, yana ta zuba mani kalamai, wasu ma ban taɓa tunanin zai iya furta mani su ba, masalan ma yau da yaga nafi sakin jiki dashi a kn kowacce rana, yana da tabbacin cewa ya dasa soyayyar shi mai girma a cikin zuciyar tawa, to nima yanzu bana da haufin son da yake yi mani ɗin, idan nayi la'akari da yanda kowa ke faɗar yanda nake da kyau da natsuwa, na cencenci a soni ɗin fiye da kima.

A haka har Bilal yayi sallama ɗakin.

Kai tsaye bisa gadon da Ya Ameen ɗin yake kwance yayi ma tsinke, ɗan duka ya kai mashi ta baya yana faɗin "to fafarawo baban soyayya"

Ɗan juyowa yayi ya kalle shi, shi fa bai ma ko ji shigowar tashi ba.

Sallama yayi mani yana mai katse wayar cikin dan tsoki, yasan yazo kenan zai fara takura mashi, kaman shi wani ne yaje ya takura mashi lokacin soyayyar tashi da Ummin.

Duk da bilal ɗin ya kula yaji haushi katse mashi firar tashi da yayi, saidai ya sani ba wai zai tanka mashi bane, to mutumen da magana ke ma wahala, shi yana ma mamakin yanda suke kwashe tsawon awanni suna magana da Suhanan a wayar, ko me yake faɗa mata? Oho wa ma ya sani ko ita ce keyi mashi firar? Domin dai shi yasan abokin nashi bai kware ba ta wannan fannin.

Haka ya samu daƙyar suka shiga aikin da ya kawo shi, so yake ya bashi komai in details, ta yadda ba zai kuma neman shi ba, koda ya isa cen ɗin. Yana kula dashi kuma wani lokacin sai yayi ɗan kasaƙe, sai kuma ya saki murmushi yana mai sosai gefen girar nashi da biron dake hannun shi. Kaman wanda ya zauce a soyayya.


**********


Haka rayuwa ta cigaba da juyawa, daƙiƙu na shuɗewa, awanni da kuma kwanaki, cikin kwana uku ne muka fara Jarabawa, haka kuma cikin kwana ukun ne ya kasance kwanan ya Ameen ɗin biyu ke nan cur da tafiya, saidai ya lura abun mai yawa ne, zai iya ma ɗaukar shi kusan sati ba tare da ya juyo ba. Shiyasa yanzu ko waya bamu cika yi ba, wani lokacin ma sai rana ta ƙare bamuyi waya ba, tinda awannin daren mu, sune awannin ranar su su acen

A haka ne kuma ranar tafiyar su Umman tazo.

Tafiya ce da aka shirya ta cikin sirri, su huɗu ne zasuyi tafiyar, sai driver da yake cikon na biyar.

Tin a daren ranar Umman ta sanar ma da Dad ɗin garin da zasu je, nan yake tambayar ta zadai ta iya gane wurin ko? A hankali ta shiga jinjina mashi kai, zuciyar ta cike da tarabbabi da wasi wasi.

Hajiya Kubra bata wani damu ba, duk da ba wai tasan da tafiyar bane, hasali ma tana cen hulɗoɗin ta, tin dai da su Hajiya Sa'ar suka tabbatar mata cewa komai zai tafi yanda aka tsara. Koda taga ana gyaran sashen Ya Ameen ɗin, bata damu ba, bata kuma tambayi Alhajin ba, kawai dai tasan cewa kurkuku ne ake gina ma Suhan ɗin ba tare da sanin kowa ba in banda ita.

Ba'a rushe tsarin gidan ba, saboda yace a bar shi haka, shima ai ba zaman shi ne dindindin a gidan ba, kawai zai biyayya ne ya zauna, kaman yanda Mom ɗin ta buƙata, shima na wani lokaci ne.

*******


Tafiya miƙaƙƙa.

Alhaji Auwalu, Alhaji Mustapha, Hajiya Zainab da Umman.

Firar su suke gwanin ban shawa'awa, Amman banda Umman, da kaf hankalin ta ya riga ya tafi a kan yadda zata je ta tadda wurin.

Wace irin tarba zasu samu? A matsayin ta na matatta a wajen su?


Salla kawai suka tsaya sukayi, dayake lafiyayyar mota ce, kuma ta samu tuƙin driver ɗin Alhajin sai gasu dan danan sun isa zuwa jihar ta Adamawa.

Da kallo Umman ke bin garin, an samu ci gaba iri daban daban, komai ya cenza, saidai hanyar zuwa gidan nasu har yanzu tana nan yanda take, saidai ƙara faɗaɗa ta ne da akayi da titi mai matuƙar kyau da ban sha'awa.

Sun wuce ya kai gate uku, ko wanne gate sai na tsaida su, lura da irin motar, da kuma manyan mutanen da ke cikin ta, ya sanya ko binciken su sosai ba'a tsayawa yi, kasancewr an san baƙi ne daga wani garin.

Gate na huɗu, shine ya sada su da ainahin harabar masarautr.

Babbar masarauta ce, mai daɗaɗɗen tarihi.

Inda aka tanada musamman domin ajiye mitoci, nan driver ɗin yayi parking, kowa mamaki ya cika mashi zuciya, saidai babu wanda ya tanka cikin su.

Haka Umman ta wuce gaba suna biye da ita, kowa kallon mamaki takeyi.

Babbar masarauta ce, mai haɗe da gini irin na da, saidai an ƙawata shi da zamani, ma'ana an zamanantar dashi, ta hanyar abubuwan ƙawa irin na gine gine.

Fadawa ne birjik ke kai da komo a cikin gidan, suna hango shigowar motar wasu daga cikin su duka rugo zuwa inda su Alhaji Mustaphan suke.

*"Hayya dai Hayya dai, ranku ya daɗe, baƙin sarki, barkan ku da zuwa masarautar mai martaba sarki Muhammadu Bello Barkindo lamiɗo, muna maku maraba da zuwa a madadin sarki"*

Wani bafade da yake ta muzurai, hannun shi riƙe da wata zabgegiyar Bulalar dorina, irin ta bugun dawakai.

Wani tanƙamemen falo ne aka shigar dasu, sarkin zagi ne yazo ya kwashi gaisuwa, duk da dai ba wai an shaida su bane, Amman yanda aka gansu cike da kwarjini da kamala, ya sanya aka san baƙin sarki ne, gashi kuma sarki baya so ana banzatar mashi da baƙo koda baya nan.

"Hutawar ku lafiya ranku shi daɗe, yanzun nan za'a nemo maku iso wajen sarki mai ɗinbin daraja da alfarma, an gaida baƙin sarki da suke tafe da tarin albarka da alkhairi"

Su dai sai faman murmushi suke yi, har yanzu dai suna tare da ɗinbin mamaki, gashi kuma Umman ta ƙi cewa komai.

Nan da nan aka ciccika masu gaban su da kayan itatuwa.

Falo ne mai matuƙar girma da kyawu, ba kowa cikin shi, sai kilisai da aka shisshinfiɗa, da kuma tumtum irin na tada hannuwa dashi, sai mafitai masu kyau da ban sha'awa da aka ajiye gefe gefen falon, duk da akwai yalwar central Ac dake ta faman yin aiki.

Mamakin su ɗaya, meye haɗin Umman Suhan ɗin da masarautar? Gashi kuma ga dukkan alamu ba wanda ya ko gane ta cikin fadawan, da ma ma'aikatan bayin gidan da aka aiko suka ajiye abubuwan ci ɗin.

Basu fi minti sha biyar ba, sai ga wannan bafaden ya dawo cikin sauri, yana ta faman saɓa babbar riga.

"Barkanku da hutawa baƙin sarki, sarki ya ce a yi maki iso zuwa fadar tashi yana mai fitowa ba da jimawa ba"

A hankali suka miƙe, suna mai bin bayan shi, ta wani ɗan cirridor suka bi, sai gasu sun bayyana a wani tafkeken fili da babu Abunda ke cikin shi banda rairayi mai kyau, da kuma itatuwa tsanwaye shar shar dasu.

Fada ce babba, wadda ta amsa sunan ta fada, kai lallai sarauta daban ce, masalan ma yadda wannan masarautar da kai da ga ganin ta, kasan ana shimfiɗa mulki mai cike da kyawu ta tsafta.

Komai na fadar kalar jaaa ne sosai mai cizawa, kujeru ne irin na sarauta masu ado da ruwan gold suka zagaye faɗar dashi, anyi ma faɗar ado kala kala, har ma kusan muce sunyi yawa, duk da fadar ta matuƙar ƙayatar da su dukan su.

Kai daga ganin faɗar ka tabbatar da an narkar da dukiya wurin.

Babban sarki ne, da dukkanin faɗin nahiyar tamu ake ji dashi sosai.

Su dai sai bin Umma da kallo suke, wadda ta sadda kanta ƙasa, ba zaka ma iya tantance halin da take ciki ba.

Zaman su keda wuya, suka jiyo tahowar sarki, tare da masu yi mashi kirayi, da kuma gyara mashi alkyabba da hanya.

*"Gaba salamun baya salamun sarki ɗan sarki, ƙanen sarki jikan sarki, iyayen sarakunan mu masu daraja na nan gaba, an gaida ɗan gidan mai martaba Barkindo lamiɗo, sarari, gyara kintsi, hadari sa gaban ka inda kake so, ɗan toron giwa, kai sarki jikan sarki, kakan ka sarki, an gaishe ka, gyara kintsi, gaba dai gaba dai"*

Su Dad suna gani haka suka miƙe tsaye cikin girmamawa, komi kuɗin ka, komi matsayin ka, sarauta daban ce, sarki daban ne, masalan ma sarki kaman wannan da yake da ɗinbin daraja da kuma wuƙar yanka.

Sai bayan da suka gyara mashi zama ne, ya zauna sosai, cike da izzar mulki da taƙama. Sannan suka matsa cike da girmamawa, suna mai naɗe hannayen babbar rigar su, suka koma gefe suka zauna. Suna mai duƙawa sosai suka shiga kai gaisuwa

Yayin da ya daidaita zaman shi bisa kujerar shi yake kallon su Alhaji Mustapha Dambulan ɗin.

Murmushi irin na sarakai ya saki, lokacin da suke miƙa mashi gaisuwa, cike da girmamwawa, sarkin zagi ne ke amsawa "Sarkii Yaaaaa Amssaaa maku" kaman yanda yafi kowa halshe a faɗar, itama Hajiya Zainab gaisuwar ta kai har ƙasa, tana mai girmamawa ga sarkin.

"An gaishe ku baƙin ariziƙi baƙin alkhairi, sarki ya amsa baƙuncin ku, maraba da zuwa babbar mmasarauta mai tarihi da ɗinbin daraja"

Mai makon Umman ta zuƙunna ta kai gaisuwar itama, sai ta wuce kai tsaye zuwa inda sarkin yake zaune, ya zuƙunna tana mai sakin wani irin kuka.

"Hattara dai Hajiya, Sarki baya ɗaukar wargi da wasa, Hattara ya ke wannan baƙuwa"

Da mamaki mai martaba sarki Bello ke kallon ta, har yanzu bata ɗago fuskar ta ba, ta sanya hannuwan ta dukan su tana mai kamo dukkanin kafaɗun shi, take faɗin "BAFFAAA" sannan ta ɗago fuskar ta cike da hawaye wasu na korar wasu.

Cikin kaɗuwa da furgici mai martaba ke kallon ta, sai kuma ya miƙe cike da mamaki da al'ajabi yake mai faɗin

*MARYAMA???*

_Waih Allah kuyi haƙuri da wannan, gaskiya typing akwai wahala._

Masu son suga auren Ya Ameen da Suhan su bini a hankali, komai ɗan a hankali ne











~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*Addu'a Yayin Da Aka ga Tumu,(Hurai-Sabon Amfanin Gona*

اَللَّهُمَّ بَارِكْ لَنَا فِي ثَمَرِنَا، وَبَارِكْ لَنَا فِي مَدِينَتِنَا، وَبَارِكْ لَنَا فِي صَاعِنَا، وَبَارِكْ لَنَا فِي مُدِّنَا.

*Allahumma barik lana fee thamarina, wabarik lana fee madeenatina, wabarik lana fee sa'ina wabarik lana fee muddina.*

*Ya Allah! Ka albarka ce mu a cikin kayan gonarmu, ka albarkan ce mu a garinmu, Ka albarkance mu a kwanon awonmu, Ka albarkan ce mua mudun awonmu.*



>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*---

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment