Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa ƙofar gidan da Alhaji yaron yake ciki, hannun shi ɗauke da wani kwali.


A cikin motar ne Al'ameen yabi dukkan hanyar da zai bi wajen ganin ya ɗauke ganin CCTV camera ɗin da take yankin, ta cikin Computer ɗinshi, ta yanda koda Anzo binciken wani abu ba lallai a gane ba.

Sau biyu yana knocking, kaman babu kowa ciki, har ya haƙura zai juya, yaji alamun tafiya.

Kwalin da yake ɗauke a hannun shi ne ya turo zuwa gaba.

A hankali ta ɗaga ɗan abunda zata iya hango ko wanene a wajen, ganin mutum da kwalin burger a hannun shine ya sanya ta ja baya ta buɗe gidan.

Shiga yayi ciki bai ce mata komai ba, yayin da ta saki kyauren tana mai binshi a baya.

Saman dining tayi mashi nuni daya aza mata, sannan tace ya jira ta zuwa ga kawo mashi kuɗin.

Tana fitowa kuwa ya buɗe wani ƙaton hanky yana mai rufe mata fuska, ƴar ƙara tayi kaɗan ta sulale a wajen, ƙarar dataja hankalin Alhaji Yaro kenan ya fito da sauri daga bedroom ɗin domin ganin ko me ke faruwa. Shima yana fitowa Irkan dake tsaye bayan kyaure ya rufe mashi hanci da wannan hancarchip ɗin.

Ba ɓata lokaci shima ya sulale a wajen, da sauri Irkan ya latsa wani abu dake hannun shi, sai gasu duk sun shisshigo da sauri.

Alhaji yaro ne ma yaso basu wahalar ɗauka, saboda irin yanda yake da tsayi da girma, bayan babbar motar duk suka kwakkwantar dasu, suna mai rufo masu gidan, sannan suka ja motar da matsananci gudu suka bar wajen...







~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~80~*



*A cigaba da yi mani haƙuri dan Allah, uzirori ne ke riƙe ni, Amman insha Allahu mun dasa kenan, har sai mun ƙarƙare*

***********


Ba ƙaramin mamaki Alhaji yaro yayi ba. Tun bayan daya fardaɗo yake bin ɗakin da suke ciki da kallo. Gefen shi Hajiya Laila ce tayi wurjan-jan, kuka kawai take yi. Tun ɗazu take dukan Alhaji Yaron da hannuwanta da aka ɗaure su, saidai ba'a matse su ba yanda zasu wahala.

Da idanu yake binta, yana mata wani irin kallon wahala, da kuma tuhuma.

"Nima ban sani ba, ban sansu ba, fuskokinsu duk a kulle, tun ɗazu suke shigowa su gani ko ka farfaɗo, ka tashi hakanan, kada su kashe mu"
Ta faɗa cikin wani irin kuka.

Ƙoƙarin tashi zaune yayi, amma ya kasa. Baisan ko awanni nawa ya kwashe cikin wannan halin na ɓacewar hankali ba.

"Laila wanene yayi mana haka? Me mukayi ma wani? Su wanene su? " Ya maida mata shima, cikin wani irin kaɗuwa. Su dukansu sun girgiza da ganin halin da suke ciki. Ɗakin da aka ajiye su kanshi ma abun kallo ne. Domin kuwa yayi datti sosai, ga ƙura ko ina, sannan babu wani abu dake cikin ɗakin, koda kuwa tsinke ne, kaman ma a bayan gari suke.

A hankali ya buɗe murfin ɗakin, yana mai shigowa, hannun shi ɗauke da wata ƴar roba ta take-away. Sai leda fara sol, zaka iya hango gorar ruwa ciki, da kuma lemon roba.

Har yanzu fuskar tashi a rufe take, in ka ɗauke sumar kanshi da take kwance luf, iskar ƙofar da ya buɗe tana shigowa, tana ƙaɗa gashin nashi.

Gefen su ya ajiye kayan dake hannun nashi, yana mai matsawa kusa da Alhaji yaron ya sanya hannu ya ɗago shi.

Zaune sosai ya taimaka mashi ya tashi. Sannan ya koma bayan Hajiya Laila yana mai kwance mata ɗaurin da akayi ma hannun nata.

Har yanzu kuka take yi. Saidai babu sauti, sai hawaye da majina da take sha akai akai. Ko kaɗan tausayin su bai kama shi ba, ba wai dan sun ma mahaifiyar shi haka ba, sai dan irin cin amana, da ha'incin da suka sanya a rayuwar tasu. Irin su ne ke ja ma ƙasar tashi ta nigeria zagi. Irin su ne ke sanyawa amana ko taimako yayi kaɗan.

Robar abincin ɗaya ya matsar mata da ita zuwa gabanta. Aiko ba wata wata ta jawo abincin ta fara ci, kaman tsohuwar mayunwaciya.

Miƙewa yayi tsaye, yana mai zura hannayen shi duka cikin aljihun wandon shi.

Ƙissima yanda zaiyi masu kawai yake yi. Sai wata zuciyar take shawartar shi kawai da ya miƙa su ga hukumar ƙasar, ya zuwa yanzu babu abunda yake ji cikin zuciyar tashi, illa wani mugun tsanar su.

Da hannu yayi alama. Sai ga wani murgujejen mutum fari sol dashi, ga alama shima ɗan ƙasar ne. Ya shigo ɗauke da wata irin kyakkyawar madaidaiciyar kujera. Gudan hannun nashi kuma bindiga ce, ƙirar pistol.

Saida yayi alamun girmamawa gareshi, sannan ya ajiye kujerar, yana mai komawa gefe ya tsaya.

Da hannu ya kuma yi mashi alama da ya kwance Alhaji Yaron.

Kwance shi yayi, sannan ya matsar mashi da abincin gaban shi.

Duk kansu zaune suke ƙasa gabanshi, suna masu cin abincin cikin ƙasƙanci. Zuciyar imani ce ma kawai ta sanya shi basu abincin. Dan da ya biye ma Bilal, da har su koma ƙasar tasu ba zasu basu abinci ba, saidai ruwa.

Har yanzu basu tantance ko wanene ba, basu kuma san laifin su gareshi ba. Saidai ganin farar fatar tashi, sai basu ɗauka ma ɗan tasu ƙasar bane. Sun ɗauka ɗan ƙasar Turkey ɗin ne.

"Bawan Allah dan Allah laifin ke mukayi maka haka? Ka tausaya mana, ka sake mu, ƴan uwanmu na cen na jiran mu" cewar Hajiya Lailan.

Jin kalaman nata, baisan lokacin da ya murmusa ba, har sautin shi na ɗan fita. Lallai ma Hajiya Laila da rainin wayau take, kenan ma ya gane Sam har yanzu basu fahimci halin da ake ciki ba.

A hankali ya sanya hannun shi, yana mai yaye lulluɓin fuskar tashi.

Ai tuni Hajiya Laila ta kuma zaro idanu, tana mai ja da baya da baya. Bakin ta har rawa yake. Ba Hajiya Laila ba, har shi kanshi Alhaji yaron da yake namiji saida ya kaɗu, ganin ko wanene zaune a gaban su.

"Al'aaammm.." Cikin rawar baki take son faɗar sunan nashi, Amman ta kasa, saboda irin yanda jikin ta ke rawa, bakin nata na karkarwa.

Da hannu ta shiga nuna shi.

"Son...!" ta sake ƙoƙarta wa ta faɗa, cikin matsanancin tashin hankali.

Kallon da yake yi nata, shi ya sa baba wata irin kunya, haɗe da nadama ce suka taru suka lulluɓe ta a lokaci guda. Sai ta sadda kanta zuwa ƙasa kawai. Bata taɓa tunanin wannan ranar na zuwa ba. Bata taɓa hararo wai ita Laila akwai ranar da zata muzanta haka ba.

Idanun nashi jawur, sai ya haɗu da farar fuskar tashi, suka bada wata irin kala. Ba sai na faɗa maka ba, ran shi a matuƙar ɓace yake. Da idanu kawai yake bin su da kallo. Tuni ai Alhaji yaro ya ture robar abincin daga gabanshi.

Ji yake kaman ya tashi ya zura da gudu, saidai ina za shi? Ko waɗannan murtuka murtukan mutanen da suke tsaye suna gadin su, fuskar nan tasu ba alamun imani, sun isa su sanya su suyi biyayya.

Kaɗa ƙafar shi yake yi a hankali. Na daga cikin al'adar shi, idan ran shi ya ɓacin irin haka, zai dinga girgiza ƙafa a hankali a hankali.

Rasa ma me zai ce masu yayi, saidai kawai ya miƙe, yana mai dosar ƙofar fita.

"You have to be ready, we must go back to nigeria" Abunda ya iya faɗa kenan, yana mai daf da ficewr.sannan ya sanya kai yana mai idasa ficewar.

Kuka Hajiya Laila ta kuma saki..

"Duk laifinka ne Alhaji, kai ka kawo shawarar mu taho da kuɗin mutanen nan, na faɗa maka tana da hatsabibin yaro, kuma kaima ka sani, Amman kai ta zura ni cewa mu gudu kawai, duk yanda yake ba ko ina ya sani ba ai, yanzu gashi nan ka jawo mani abun kunya, abun faɗa, ace kaman yanda nake da Kubra naci amanar ta, sai gashi tun ba'aje ko ina ba, tun bamu mori kuɗin ba, yaron nan yazo ya kama mu, cikin ƙasƙanci da abun kunya, yanzu ka dubi halin da muke ciki dan Allah, could you imagine?.. "

Cikin tsawa Alhaji Yaro ya dakatar da ita.

" Is enough Laila, ya isa nace, bangane ni na zuga ki ba, tun yaushe muke neman wannan damar dake? Tun yaushe in da na biye maki zamuyi hakan? Sai kuma nace ki bari dukiyar tata ta ƙara yawa a hannun mu, ke kaɗai kika sha Kunyar ne? Nace ke kaɗai kike cikin halin? Malama in zaki man shiru kiyi kawai, mu nemi mafita, amman ba zan taɓa lamuntar cin zarafi da ƙanƙanci daga gurin yaron ciki na ba.. "

" Kai kake ganin shi yaro, Al'ameen ya wuce inda duk kake tunani, na sani kuma kaima kanka nasan ka sani, wace irin mafita ke garemu? Ka duba fa waɗannan jibga jibgan mutanen? Kai in baka tsoron su, wallahi ni ina ji, idan kuma kaima ka kuskure, wallahi ɗauke ka zasuyi nan take, dan Allah Alhaji kada kayi wani gigi, na roƙeka" ta idasa cikin wani irin gunjin kukan.

Dayake su masu tsaron nasu ba jin hausa suke yi ba, su dai kawai aikin su suke yi. Sai faman kaiwa da komowa suke yi.

Duk da haka Alhaji yaron bai ji shawarar Lailan ba. Miƙewa yayi a sukwane, da niyyar ficewa. Bakin bindiga kawai suka sanya mashi a ƙyeya, sai gashi ya kuma sake baje wa nan gaban Hajiya Laila ɗin a some.

Wani ihun kukan ta sake saki; "Na bani Alhaji, ka gani ko? Ka ga abunda nace maka ko? Basu da imani, sai su kashe ka, dan Allah Al'ameen kayi haƙuri ka sake mu, ka ƙyale mu, wallahi zamu mayar maku da dukiyar ku hankali kwance.." nan fa tayi ta sambatu, tana mai jawo gorar ruwan, ya shiga tuttula ma Alhaji Yaro, Amman inaaa. Ko motsawa ma baya yi...


*************


Ina cen na shige cikin ƴan hidimar suna, aka sanar mana da isowar su Umma nawa.

Ƙai tsaye gidan Alhaji Auwalun suka nufa. Bayan sun sun huta sunci abinci. Gida fa ya kacame kaman a ranar ake sunan, duk ƴan Kankiya sun iso, harda su Huda, har kaka zuwaira ma tace ba za'a barta a baya ba.

Nan fa gida ya kuma rincaɓewa. Masalan ma yanzu da labari ya zaga ko ina cewa Umman tawa gimbiya ce. Sai kowa yake ƙoƙarin ya ganta su gaisa.

Kai tsaye ɗakin Hajiya Zainab aka nufa dasu. Sai kowa ya kasance Umman tawa yake mararin gani. Irin yanda ake yi ma Hajiya Kubra ada, a matsayin ta na matar Alhaji Mustapha ɗin, kuma kasancewa ta mai kuɗi. Wannan karon duk sai taga ba haka ba.

Suna zaune a ɗakin ne ana ta faman gaisa wa na shiga. Kai tsaye kusa da umma ta na nufa, ina mai rungume ta na yaushe gamo. Sai kuma naji kaman wani kuka yana neman taho mani, duk sai aka saka dariya, mun burge kowa, muma yanzu mun zama mutane, irin yanda Umman tawa ta saki jiki da kowa. Sai abun ya ƙara burge su. Ita kanta Hajiya Kubran sai ta koma tana yaƙe, mutane kaɗan kaɗan ne suke ta ita.

Ɗan tureni Ummana tayi dgaa jikin ta, tana mai cewa "Ah ke me zan gani haka? Allah na tuba, gotai gotai ɗin me?" sai aka kuma saka dariyar. Har Kaka zuwairan na cewa; "Ah to kema kin faɗa gimbiya Maryam, gashi ta ƙwace man miji, yanzu kuma za tazo tana wata shagwaɓa, kaman ƴar jariri ya"

Ƙasa na zame, kunya na mai lulkuɓeni, lokaci guda kuma ina maida kallon na ɓangaren da Hajiya Kubra ke hakimce gefe.

"Ina yini Mom, ya hanya?" na faɗa cikin girmamawa. Sai ta ɗan saki fuska, ba yabo ba fallasa ta shiga amsa man, kowa yayi mamakin yanda tayi ɗin, tunda kowa ya san yanda take da al'amarin namu.

Har tambaya ta takeyi, wai "Ya gida ya zaman kaɗai ci?"

Ƙasa nayi da kai ina mai cewa "Lafiya lau Mom"

Da kallo ta shiga bina. Sosai tayi mamakin cenzawar tawa. Sai yanzu ne take ta hango tsabar kamanceceniya ta da Mahaifin nawa Yayanta Muhammadu. Ko ba komai ni kaɗai ce a yanzu take kallo, wadda na fito daga ɓangaren mahaifin nata.

Sauƙin tsanar tawa sai ya ragu a cikin zuciyar ta, duk dai da cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba. Akwai takun saƙa tsakani.

Sun jima sosai a gidan. Kafin Hajiya Kubran ta buƙaci tafiya, a cewarta zata je ta kwanta ta huta, sai kuma zuwa goben.

Kaman tace in taho mu tafi, sai tayi wani tunani. Yanzu fa idan kowa yaji dukiyar mu ce a hannun ta, kowa zaice ba dan Allah tayi ba. Share wa tayi kawai, nan aka samu wanda suka raka ta mota ta tafi. Nidai ban gigin raka ta ba.

Har yanzu bansan a halin da muke ciki ba, gashi kuma nasan cewa umma ta ba zata taɓa faɗa man halin da ake ciki ɗin ba.

Isowar su Afnan ne ya ƙara ruɗa gidan, ka dangin Sadeeq ɗin da suke ta ɓulɓulowa ko ta ina. Bikin suna fa an shirya shi sosai, in baku manta ba, dangin sadeeq, dashi kanshi sadeeq ɗin masu hali ne sosai, Shiyasa a wannan karon ma sunyi bajinta, sunyi matuƙar ƙoƙari. Ko shanaye manya gida biyu suka kawo, da tulƙa tulƙan ragunan su guda biyu. Sai akwatuna na kayan barka set mai guda shidda. Biyu na mai jego, huɗu na jaririya. Babu abunda babu ciki. Komai yaji masha Allahu.

Komai ake ciki, ni Hafsat ɗin ke sanyawa gaba gaba. Na zama wata *Cele* kasancewa ta mata a gurin ya Ameen ɗin. Wanda kowa ke matuƙar sonshi da ji dashi. Alkhairin nashi a cikin ahalin nashi, sai ya siya man soyayya fiye da tunani na. Na ɗauka idan akayi bikin namu, zan zama wata bare a cikin su. Sai gashi duk inda na gitta, Aunty Suhan kake ji kawai ana ambata.

Ni kaina nasan na cenza, na ƙara wani irin haske, nayi mulmul, fata ta sai sheƙi take yi, ga wani irin kwarjini na ƙara yi.

Ko Afnan saidai ta dinga bina da kallo tana zaulaya ta. Aunty Feena ma ta saki jiki dani sosai, Ayan da Nasreem sun ƙara girma. Dama Ayan ɗan wuri na, duk inda na gitta hannun shi na cikin nawa. Sai hakan ya ƙara yi masu daɗi, kunsan ance mai ɗa wawa.

Umma ta ta ba Hajiya Zainab gudunmuwa sosai, yayi da ta keɓe gefe dani tana mai tambaya ta ni me zan bada?

Dama na kwaso kuɗi wanda na samu gudunmuwar biki, Ya Ameen ɗin yace in ajiye waje na, ko zan buƙace su. Ba ma yanda banyi akan ya amsa ya ƙiya, saidai cewa yayi inshi bai ƙara man ba, ba zai amsa nawa ba.

Shiyasa nace mata su zan bata, bansan ne zan siya mata ba. Taji daɗin hakan, inda tace ko Al'ameen ɗin kada in ma magana, kuma duk abunda nake so, kada in sake in tambayi mijin nawa, in tuntuɓe ta kai tsaye.

Kusan dubu ɗari biyu na ware, kuɗin suna da yawa, dan haka nasan wannan ma sun isa, dama yau nayi niyyar bata.

Sai kusan ƙarfe takwas na dare, Mudi driver yaje ya kwaso mu, ba yanda Hafsat batayi ba in kwana, ai nan ma duk gida be. Amman na ƙiya, na dai ce mata zan yi sammakon komawa gidan sunna, washegari.


Ko a mota fira ake jefi jefi, Afnan kan saka ni, yayin da Aunty Feena saidai tayi murmushi. Nihal ma da ɗan dama, Amman tunda nace mata sai ta biyai kafin in koya mata wasu abubuwa, duk sai jikin ta yayi sanyi. Gashi inda Allah ya taimake ta, Nureen ɗin ya ɗan turo mata wani abu, wai tayi buƙatoci. Amman fa ta sani, ita da komawa, sai ta cika sharuɗɗan da ya gindaya mata.
Dama ta ƙagara Mom ɗin tasu ta dawo taje ta same ta akan batun. Shiyasa ko Saudat bata faɗa mawa ba, tasan ba shawarar arziƙi zata bata ba. Ita duk sai taji ma Saudat ɗin ta sure mata. Irin manyan laifulan da idanun ta suka gane mata Saudat ɗin na aikatawa.

Saida aka kai Saudat gida. Sama sama sukayi Sallama. Ita kanta Aunty Feena ta lura akwai abunda ke faruwa. Amman ta zura masu idanu ne, taga iya gudun ruwan su, dama tasan lokaci na zuwa, da kowaccen su zatayi nadamar abubuwan da ta aikata ɗin.

Janye Afnan nayi zuwa sashen nawa, ita da Ayan. Munsha firar mu sosai. Nan fa aka zage ana bani labarin Sir Saleem. Tabbas naji matuƙar daɗi, daga Afnan ɗin, har Sir Saleem ɗin sun dace da juna. Tsoro na ɗaya cikin al'amarin watau Ma'u, domin na kula ita ɗin mahaukaciya ce a fannin Kishi.

Sai dai ga alamu Saleem ɗin bai yi ma Afnan maganar ma'u ba. Dan duk cikin labarin banji tayi ma Suhan maganar Ma'un ba.

Washegari da wuri wuri muka sake shiryawa, saidai kafin mu wuce, saida na leƙa sashen Mom ɗita.

Ganin tare muke da Afnan, sai naga kaman bata saki jiki sosai ba, kuma gashi Alhaji Mustapha a sashen nata yake. Cewa tayi kawai mu wuce sai ta iso.

Dan haka, ko da na isa bamu zauna ba. Mu kenan shige da fice. Yarinya taci Sunan Zainab. Ana ce mata Khairi. Suna ya ƙawatar.Hafsat taji daɗin kyautar da nayi mata ta kuɗi, duk da tasan cewa kyautar daga gareni take, tasan ta Ya Ameen sai ta wuce hakan.

Hajiya Kubra ma tayi bazata. Itama ta kawo turamenta masu kyau sosai manya, da kayan jariri. Sai ɗan kunne Ƙarami na gwal wa jaririya. Nan fa aka shiga faɗa, da ƴan maganganu, dan a tarihi ba'a taɓa ganin tayi hakan ba, sai kowa ke ganin ko dan taga Alhajinbya ƙara aure ne, Shiyasa take son shiga dangi itama.

Alhaji Mustapha ma yayi ƙoƙari sosai. Iyayen kaya da ya bada da duk wani abu da ake buƙata. Ya ɗauke masu shi na sunan. Suna fa yayi kyau ya ƙayatar. Kaya kala uku na sanya nima a ranar, duk inda na gitta saidai a bini da kallo, wanda basu idasa sani na ba a dangi, suka ƙara waye wa dani.

Ita kanta Hajiya Kubran idanun ta na bisa ni. Mamaki take yi, wai nice na zama haka? Dama ita bata kushe ni ba ta hanyar kyau, Amman talauci da ƙanƙancin da nake ciki a lokacin su ta guda. Amman ko yanzu ai tasan tayi suruka, ga wata irin wayewa da na sake yi. Har su Khadeeja sun yi man kara sosai, suma sunzo sunan, duk da basu daɗe ba suka koma, tunda sun ji cewa na samu trnsfer. Sun matuƙar ji babu daɗi, har yanzu Khadeeja na tare da abokin Ya Ameen, wanda suka haɗu da bikin nawa.


Taro ya tashi lafiya sai sam barka, Khairi tazo da goshi. Tayi matuƙar mutane, Hafsat ta samu alkhairi sosai, kasancewar ta mai zaune da mutane lafiya. Kowa nata ne, bata taɓa wulaƙanta ka dan baka dashi.

Taro na watsewa muma muka tattara muka koma gida. Da niyyar zamuje mu huta kuma, sai an kwana biyu. Saboda aikin nama dai akwai ma'aikatan da zasu yi mata shi.

Munsha albarka a wajen Kaka Zuwaira da Hajiya Zainab. Masalan ma ni, yanda suka ga inyi nan inyi nan, duk da nake ji na bana da lafiya, haka nayi ta daurewa, har dai Allah yasa aka gama lafiya.


Duk inda nayi dama Kaka Zuwairan na hankalce sani. Inma taga na cika zirga zirga, ta kan ce wai inyi a hankali, gashi ni ba ni kaɗai ba. Abun na bani mamaki, saidai inyi murmushi kawai. To duka ma yaushe akayi auren? Auren da ko wata baiyi ba, Amman ace har na samu ciki? Kawai dai gajiya ce, saidai inyi murmushi cikin jin kunya kawai in wuce sum-sum.


Kwana biyun nan da mukayi muna zirga zirga, sai na samu ƙarancin ganawa da Yayan nawa. Wani lokaci saidai in tadda missed call. Da na kira kuma zai hau ƙorafin bana da lokacin shi, ina cen tare da su Hafsat, muna ta luguden laɓɓa. Saidai inyi dariya.

To sai ma nazo in na kira bana samu, saidai wani lokaci inga text ɗinshi, cewa yana lafiya.

Bansan lokacin da zai dawo ba. Hakan yasa bayan na samu natsuwa na kira shi. Saidai bata shiga ba, saƙo na tura mashi. Amman shima sai na lura kaman bai shiga ba.

Haka dai har aka kwana. Nan fa hankali na ya fara tashi, akai akai na kan kira, Amman dai a kashe.

Kasa daurewa nayi na cenza akalar kiran zuwa ga lambar Bilal. Shima dai duk maganar ɗaya ce. Afnan ce ke kwantar mani da hankali, kan cewa insha Allahu ba abunda zai same sh, yana cikin ƙoshin lafiya. Duk da ita ma hankalin nata ya fara tashi.


********

Ta ɓangaren Ya Ameen kuwa, kwana uku ya ɗauka, kanshi yayi matuƙar zafi. Shirya yanda zasu fita da Alhaji Yaro, da Hajiya laila yake ta faman yi, ba tare da sun bashi wata matsala ba. Kuma gashi bugun da Erkan yayi ma Alhaji Yaro a ƙyeya, har ya samu rauni, saida ya kaishi asibiti aka duba shi, dalili da ya sanya kenan bai sake yunƙurin gudu ba.

Suna cikin wani hali, dan ma babu wata izaya da ya ke yi masu. A inda suke dai, akwai toilet, zasu iya shiga su biya buƙata. Sannan ya sanya an kawo masu manyan barguna, kuma abinci ma yana basu.

Saidai fa, nan da cen basa da damar motsawa. Ya amshe wayoyin su, basa da wata hanyar sadarwa. Sannan duk kuɗaɗen da suke Wancen gidan, ya sanya an kwaso mashi su. Haka kuma ya maida ma hukumar ƙasar makullan gidan. A cewarshi wanda suka amshi gidan sun koma ƙasar su, bayan ya sanya an kwaso masu kayan sanyawar su.

Sai a kwana na huɗu ne abunda yake ysarawa ya kammala. Ko ya shiga ɗakin da suke ma, iyakar shi dasu kallo ne. Babu alamun tausayawa tattare da Ya Ameen ɗin wannan karon. Saboda haka ne, har suka samu suka nufi gida tare dasu, inda ya biya su Erkan kuɗi, zasu rako su har ƙasar ta Nigeria. Ko dan gudun yin gaddamar su.

Suna zuwa gidan Nigeria kuma. Manyan motocin masarauta ne, cike da fadawa suka isa tarar su. Sun sha ɗinbin mamaki. Me kuma ya kawo masarauta ciki? Ai tuni Hajiya Laila ta sake tsurewa, ko ba komai tasan ƙarfi da ikon masarauta. Tuni ta sallama, ta tabbatar da cewa kashin su ma ya gama bushe wa. Amman tunda take bata taɓa ganin shegen yaro mai tauri kai, haɗi da fasahar Al'ameen ba. Kai shi kanshi ma ta daɗe tana ma Hajiya Kubra baƙin cikin kasancewar shi ɗan ta. Taso ina ma ace Al'ameen ɗin yaron ta ne. Da babu abunda zai hana ta sake buɗawa, haɗi da fantamawa.


Ko da suka isa masarauta. Wata tarbar suka samu ta daban, kuma ta musamman. Sun sha matuƙar wahala. Amman sai mai Martaba yace masu, su koma gida, zai nemesu su duka.

Saboda haka suna hutawa suka ci abinci, haɗi da cenza kaya suka ɗauko hanyar gida Abuja.

Babu wanda yasan da zuwan su. Kawai sai dai dirin motar su akaji. Lokacin ina cikin ɗaki na kwance, bansan me ke man daɗi ba. Na kasa faɗa ma Umma ta, kunya ma nake ji. Gashi Afnan ce kawai da Nihal nake gani wani lokaci, tunda su Aunty Feena sun koma, wannan karon ba'a koma da Afnan ba, kasancewar zata fara service nata a nan Nigeria. Sai kuma Maree, wanda wani lokaci idan muka haɗu ko a hanya ne, sai tayi kaman ta bangaje ni, tana tafiya tana wani taunan chewing gum, haɗi da bubbuɗawa.

Saidai in kauce in bata hanya, ni dariya ma take bani, har

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment