Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta da idanu nayi ina mai sakin ɗan murmushi, sai naji ina mai son ziyartar wajen domin ganin yanda ya koma, ko su wanene kuma yanzu a ciki ɗakin namu ni da Umma ta?

Ma'aikata kowa sai aikin gaban shi yake yi, gidan ya wani cenza, kullum sake sabunta shi akeyi, ga wasu kayan gyara da ake daɗa sassanyawa.

Hango zugar ƴan mata na nayi suna mai nufo sashen nawa. Ƙure Khadee da idanu nayi, har yanzu jikin ta a sanyaye yake, yau gata a gidan su Dambulan ɗin, wanda ko a mafarki bata taɓa tunani ba, saidai ba'a matsayin ta na matar gida ba, a matsayin ta na Ƙawar matar gida.

A haka suka iso bakin ƙofar ɗakin, ko kafin su kwankwaso na buɗe masu, ina mai maƙalƙake raihana, haɗi da sakin uhun murnar ganin su.

Toshe mani baki sukayi suma suna dariya, raihanan ce mai cewa "hala dai kin manta ke ɗin amarya ce, ko har yanzu ba'a girma bane?" Ta faɗa cikin zaulaya. Harda Afnan suke, dan haka na janye su zuwa cikin falon.abincin da ya ragu nake ƙoƙarin sauko masu dashi ƙasa, suka dakatar dani tare da sanar dani sunci abinci. Afnan ce ta toshe baki tana mai cewa "Aikau yau kunci daɗi, dan abincin su Aunt Nihal ba kaman shi a daɗi nan gidan, wai dan ma ba ita kaɗai tayi ba, har Su Aunt Feena saida suka sanya masu hannu"

Da harara nake kallon ta ta wasa, domin nasan sharri ne take ma Nihal ɗin da take a yayar ta.

Nan muka taɓa fira, har na miƙe na ɗauki masu kuɗi masu yawa cikin kuɗin da suke ajiye cikin locker ɗin da bansan lokacin da ya zuba su ba, na dai ga suna da yawa sosai.

Godiya suka shiga yi, suna kai tambayar ango, nake shaida masu ya fice zuwa asibiti gano jikin Hafsat. Saida suka sanar dani ai Afnan zata raka su su sake ganin jikin nata kafin su wuce. Bansan dalili ba sai Naji banji daɗi ba, naso su wuce, domin ya zuwa yanzu fa wlh na fara jin kishin Ya Ameen a cikin zuciyar tawa, Sam bana ma ko son su haɗu da khadeejan, Shiyasa ma ko da ya faɗa man ba zasu haɗu ba, banji komai ba.

Afnan ce ta katse mana firar da cewa "amm Aunty Suhameen please nace wannan yayan naku faaa."

Ɗan ƙanƙance idanu nayi ina kallon ta, sai kuma nace "Yayan mu da, Afnan wane yayan kenan?"

Raihana ɗince tayi hanzarin tarar numfashi na da cewa "Sir Salim mana, ai jiya kwana mukayi ana mana firar shi, ke har waya fa naji suna yi" murmushi na saki mai sauti. Ina mai cewa "Ah ƙanwata, har ƙwallo ta faɗa cikin raga kenan?"

Rufe gefen fuskar ta tayi wai ita kunya, sai kuma ta buɗe da sauri tana mai cewa "Ah dama cewa nayi Ammin shi da ƙanwar shi naga suna da kirki, Asiyar ma fa har kira na tayi jiya tana mani ban gajiya, while nice ma ya kamata inyi mata"

Cinyar ta na dafa ina mai ce mata "Kinga Afnan, Sir Salim is a nice man, na maki sha'awar shi, and AMMIN shi bata da wata matsalar kome, idan har kun daidaita kanku, babu Abunda zance sai Allah ya sanya alkhairi, ki bari hidimar bikin nan ta kwaranye zan ma Umma magana, and shi ba Yayana bane ba ma, Uncle ɗina ne. Saidai ina fatan dai kinsan yana da mata ɗaya da yara biyu. U deserved each other Afnan Congratulation"

Sai kuma maganar tawa ta bata kunya, ta shiga rufe fuska tana kyalkyala dariya. Afnan yarinya ce mai hankali da kunya, na tabbata zata iya daure duk wata matsala da zata iya samu da Ma'u, tinda har tana son Sir Salim ɗin.

Basu wani daɗe ba suka miƙe, gami da yi mani sallama. Har bakin ƙofa na raka su, tinda ba zan iya fita ba a yanzu. Afnan ce ke sanar dani cewa Mudi driver ne zai je ya kaisu asibitin daga nan su wuce inda zasu hau mota.

Sashen ya rage tsit, sai ni ɗaya, saidai waɗanda idan zasu wuce su sake biyo wa suga amarya, inda nake zaune cen ƙuryar ɗaki kada kuma ace nayi rashin kunya an tadda ni falo.

Yinin ranar Nihal a ƙuntace tayi shi, ko da ta sanar da Aunt Feena Abunda Yayan nasu yayi mata, dariya ta dinga yi mata tana mai ce mata indai bata son ta dinga kwasar wannan haushin to lallai saidai ta laluba Nureen domin yazo a gyara auren nan nata, Amman idan ba haka ba, wlh ta bani da Al' Ameen a cikin gidan, masalan ma yanzu da gidan yake zaune dindindin.

Butsu Butsu ya kan kira ni a waya, yana mai bani haƙuri wai yasan gidan da mata, Shiyasa bai dawo ba, Amman soon zan ganshi insha Allahu. Addu'a nayi mashi ina mai tuna mashi da alƙawari na na kira mun Hafsat, ce mani yayi in bari yayi alƙawarn da marece idan ya koma ba zai manta ba.


********


Kwance yake shame shame bisa gadon, ɗakin yayi ƙura matuƙa, Amman gajiyar da ya kwaso sai bata bar shi ya ko iya kakkaɓe gadon ba, hakanan ya raɓa ya kwanta.

Cen cikin bacci yaji ana ta daga mashi tsawa, a hankali ya buɗe idon nashi yana mai ɗora su saman fuskar ta.

"Ma'u" Ya furta a hankali. Sai kuma ya tashi zaune, jikin shi Sam babu ƙarfi ko kuzari duk ya bi ya gaji.

"Salim ka tashi magana zamuyi dakai, wacece wannan yarinyar da naga kana kallo a cikin video ɗin bikin nan? Kuma naga kaine ka kai ta wajen dinner ɗin, sannan na ganku tare da ita"

Ta faɗa muryar ta a sama, ta fanni guda kuma hannun ta ɗauke da ludayin miya sai yayyarfa shi take yi cikin ɗakin.

A hankali ya sanya hannu yana mai kare fuskar shi, gudun kada ta watso mashi man miya.

"Ma'u wace yarinya kenan kike nufi haka?" shima ya faɗa yana mai miƙewa tsaye.

"Ban sani ba Abban Eesher, kana nufin ka ce mani baka gane me nake nufi ba? To kalli nan" ta faɗa tana mai haska mashi fuskar wayar shi dake hannun ta. Photon Afnan ne tsaye tana murmushi cikin garden ɗin gidan su.

"Eh na gani menene kuma?"

"So nake nasan ita ɗin wacece?"

"Afnan" ya bata amsa kai tsaye. Ya fara gajiya da halin ma'u, ko ba komai shima lokaci yayi da ya kamata ya nuna mata cewa shine ke auren ta fa, ba ita ce ke auren shi ba, kuma ko ba komai shine namiji, shine sama da ita.

"Oho koma wacece, ba sunan ta nake son ji ba,tinda an riga an sanar dani sunan nata. menene alaƙar ka da ita?"

"Ƙanwar Al'ameen mijin Suhan, kuma ita ce wadda nake so yanzu zan aura, su wanda suka sanar dake sunan basu sanar maki da alaƙar tamu ba?"

Sai kuma ta saki shewa tana kai bubbuga baki "ehooo ka daiji kunya wallahi, watau ka bibiyi ita Suhan ɗin ka gane ba ajinka bace, yaudarar ka kawai tayi, tuni tana da wanda ya fika, shine yanzu ka koma ma wata cen wai ita ƙanwar shi, to wallahi ka sani, kayi kaɗan Abban Essher, wlh mu zuba mu gani cikin gidan nan shelege ka fasa ɗan halak sai yanka"

Da idanu kawai yake binta, jin Abunda ta faɗa ne ya shiga gyara tsayuwar shi yana mai faɗin "To wanene shegen Ma'u? Ina ce dai ba dani kike ba? Ki shiga hankalin ki wlh kada ki kuskura ki kai ni ƙarshe, don zan saɓa maki ne, dama Ammi ce ke dakatar dani daga yi maki wasu abubuwan, to yanzu ko sani ma ba zata yi ba, sai na aikata sannan taji labari, Haba na gaji hakanan, ki rabu dani in sarara mana Ma'u, yanzu don Allah dubeki, yanzu ƙarfe kusan biyar Amman har yanzu kayan bacci ne jikin ki, kanki ba ko ɗan kwali, dubi ɗakin mijin ki? Yanzu tsakani da Allah sai kuma kice in zauna dake ke kaɗai a haka? Da yarinta ta da ƙuruciya ta?"

" Oho maka ka auro ɗari ma in zaka iya, Amman wlh ka sani ka siya tashin hankali da tijara da kuɗin ka, shanyayye kawai , komai kace Ammi, eh ita Ammi ai dangin mijin ta basu sako ta gaba ba, shine take neman ni ta sako ni gaba ta shiga rayuwa ta da ƙudundune, dama nasan duk Abunda kake yi wlh ita ce ke zuga ka. Amman ka sani....... " kalaman ta ne suka maƙake jin gaggauran marin da ya sake nata a fuska tafi biyu. Ba arzuƙi ta idasa maƙale sauran kalaman bakin nata. Sai kuma ta durƙushe tana mai sakin kuka, inda ta saki ludayin miyar saman gadon.

Girgiza kanshi kawai yayi yana mai zarrar rigar shi ya sanya ya bar mata gidan. Kai tsaye gidan Ammi ya nufa, ɗakin da yake mallakn shi tuni shi ya shiga, ruwan sanyi kawai ya sakar ma kanshi, yana mai fitowa ya zura Jallabiya, sannan ya nufi sashen Ammin. Kafin ya idasa shiga wayar shi da ya fizge hannun Ma'u ta ɗauki ruri. Sunan Afnan ya gani jikin wayar yana yawo.

Dakatawa yayi daga shiga, inda ya samu wata kujerar rober inda malamin su Esher yake zama in zai masu lesson

Waya yake yi da ita cikin kwanciyar hankali da annashuwa, kafin kace me ta matar dashi damuwar shi, inda take labarta mashi haihuwa biyu da akayi masu masu muhimmanci. Yana cikin wayar da ita ne yaran nashi suka dawo daga islamiyya. Nan ya haɗa ta dasu cikin waya suna ta mata soki burutsu, daga ƙarshe ya ɗauki excuse nata akan zai shiga ya gana da Ammin shi, inda take bashi sallahun gaisuwa.

Koda suka shiga yaran ne suka fara labarta ma Ammin labarin New aunty ɗinsu. Da kallon tuhuma Ammin ke bin yaron nata. Baiyi ƙasa guiwa ba, wajen fesa ma Ammi tsakanin shi da Afnan ɗin, taji daɗi matuƙa, ko ba komai ta tabbata samun suriki daga tsatsn Alhaji Mustapha abun alfahari ne, kuma ko ba komai tin wajen bikin ta kula da hankali da natsuwar yarinya, kuma dama tayi ma Salim sha'awar ta, to saidai rashin sanin takamaimai ko tana da tsayayye ya sanya ta share. Kuma bata da ra'ayin nema ma Salim aure, tafi son ya gani da kanshi yace yana so sannan

Cikin jin daɗi take gyaɗa mashi kai, daga baya ta bishi da addu'ar nasara da dacewa, sannan ta sanar mashi zata smau Umman Suhan da maganar kafin ta koma, saidai tana mai roƙon shi da ya dakata har sai an warware wata dambarwa da take neman kunno kai ga zuri'ar tata.

Ta kula yana cikin wani yanayi, auren yake so ruwa a jallo. To saidai shi komai ɗan a hankali ne, har kullum tana ma yaron nata addu'ar zaɓin alkhairi a Rayuwar shi, da kuma tsaro da kariya daga wajen mahaliccinmu baki ɗaya. Nan ya kai har dare suna ta wasanni da yaran nashi, Abunda ke ƙara ɗebe masu kewa kenan, har zuwa lokacin da Abban nashi ya dawo. Sun daɗe suna tattauna abubuwa masu mihimmanci, kafin daga bisani yayi masu sallama yana mai nufar gidan nashi zuciyar shi cike da ɗarɗar da zullumi.

Kaman yanda ya tsammata haka ya taras, maimakon gyara ɗakin, sai a idasa tarwatsa shi da tayi, duk ta barbazo mashi da kaya masu amfani ta farfasa mashi bed lamp da sauran kwayayen dake cikin ɗakin nashi. Kayan shi masu muhimmanci duk tabi ta yayyaga su.

Gefen gadon ya zauna yana mai dafe kai. MA'U kenan, shi ya rasa me ke damun ma'u, Sam bata cencenci irin matar da ya dace ya zauna da ita ba.

Miƙe wa yayi a hankali yana mai lelleƙa sauran ɗakunan, duk bata nan, kuma suma duk tayi mashi ɓannar da tasan sai ya kashe kuɗi sosai kafin ya samu ya gyara. Ɗakin nashi ya koma yana mai girgiza kai, watau bata gidan ma kenan, saboda ta zagar Mashi ammi ya mare ta shine tayi yaji. Ko ma menene kanta tayi mawa, aure dai sai ya ƙara, bai ga abun zama da ita ba, tana kuɗɗar mace. Saida ya gyara ɗakin sosai sannan ya samu ya iya kwanciya. Ya daɗe yana juye juye, sai daga bisani ne ya kira Afnan, inda ya ɗan samu sauƙi, daren dai da ƙyar ya samu bacci yayi awon gaba dashi, shima ɗin dan dai ɓarawo ne.

*******


Ya Ameen ya kira ni video, inda na ga jikin Hafsat yayi sauƙi sosai, har ma tana iya dariya, ga babyn ta rungume a hannun ta tana bata nono. Abun sai yayi mani daɗi ya ƙayatar dani kuma, Allah ya sani ina son Hafsat, ko ba komai yanayin yanda take ƙauna ta itama ba duka kowa ba, bayan mun gama ne Ya Ameen ɗin ya amsa yana mai ficewa mota ya koma ya zauna, yana mai sanar dani cewa wai gashi nan tafe gidan, me na tanadar mashi.

Kai tsaye nace "soyayya ta My hubby, bayan ita ko kana neman wani abu ne bayan ita?" shima murmushi ya saki yana mai ce mani "Promise?" ɗan sadda kaina nayi ƙasa ina mai cewa "Yeah promise dear"

"Me zan taho maki dashi?"

"Anything dear Janam" saida ya ɗan ƙura mani idanu, jin na kira shi da sunan da shima yake kira na.

"Kisha kurumin ki, abu mai daɗi zan taho maki dashi, har sai kin manta kanki, zan kawo maki sweet heart"

Ɗan waro idanu nayi, "Dear in manta kaina fa kace? As how?". Saida ya kashe mani ido ɗaya , sannan ya juya fuskar wayar zuwa wani wuri yana mai kai hannu da niyyar shafawa, ai ganin inda ya dosa ne ya sanya ni saurin datse kiran, ina mai kyalkyala dariya. Hoo Ya Ameen wai ina yake kai Kunyar shi ne irin haka? Wallahi idan wani a waje ka faɗamawa ba zai ce Ya Ameen zai iya aikata hakan ba. Duk da na kashe wayar kunya bata barni ba, ina kallon kiran shi na kasa ɗagawa, sai kuma jikina yayi sanyi, kenan yana nufin yau ba zai barni in zauna lafiya ba?

Shima ta cen ɓangaren shi, dariyar ya saki yana mai cewa "Baby magana zakiyi" sai kuma ya saki murmushi mai burgewa, yana mai tada motar ya nufo gidan kai tsaye.....


~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


Addu'ar Shiga Wata Karkara ko Wani Gari

أَللَّهُمَّ رَبَّ السَّمَوَاتِ السَّبْعِ وَمَا أَظْلَلَنَ، وَرَبَّ اْلأَرَاضِينَ السَّبْعِ وَمَا أقْلَلْنَ، وَرَبَّ الشَّيَاطِينِ وَمَا أَضْلَلْنَ، وَرَبَّ الرِّيَاحِ وَمَا ذَرَيْنَ، أَسْأَلُكَ خَيْرَ هَذِهِ الْقَرْيَةِ وَخَيْرَ أَهْلِهَا، وَخَيْرَ مَا فِيهَا، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهاَ وَشَرِّ أَهْلِهَا، وَشَرِّ مَا فِيهَا.
Allahumma rabbas-samawatis-sab'i wama azlaln, warabbal-aradeenas-sab'i wama aklaln, warabbash-shayateeni wama adlaln, warabbar-riyahi wama zarayn, as-aluka khayra hathihil-qaryah, wakhayra ahlilha wakhayra ma feeha, wa-a'oozu bika min sharriha washarri ahliha, washarri ma feeha.

Ya Allah! Ubangijin sammai bakwai da abin da suka rufe, kuma Ubangijin kassai bakwai da abin da suke duake da shi, kuma Ubangijin shaidanu da wadanda suka batar, kuma Ubangijin iska da abin da ta yayyada! Ina rokon Ka alherin wannan alkarya, da alherin mutanen da ke cikinta, da alherin abin da ke cikinta. Kuma ina neman tsari da Kai daga sharrinta, da sharrin mutanenta, da sharrin abin da ke cikinta.

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

*Page sadaukarwa ga duk masoyan Oum-Deedat. Na gode da adduo'i, da waɗanda suka iso gareni da wanda ma ban sansu ba, Oum-Deedat tace tana amsawa, kuma tace Ameen, sannan tace Allah ya bar ƙauna da zumunci. Jiki yayi sauƙi sai ƙarashe. Saboda jin daɗin adduo'in ne ma ya sanya na ƙoƙarta na baku wannan Page ɗin, gashi nan kuyi dumu dumu a cikin sa Nogede Allah yabar zaman amana*


*Page ~68~*



°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°



Bai iso gidan ba, saida ya biya ta wani babban super market yayo mana siyayya sosai.

Har ƙofar part ɗin namu yayi parking, dirin mota kawai naji na miƙe daga zaunen da nake da littafin ishmawi a hannu na, wanda nake karantawa, ina mai ƙara missing Ummata, domin ita ce mai ƙara mani karatun a koda yaushe.

Ni na buɗe mashi ƙofar da yake ta faman kiciniya da ledojin dake hannun shi.

Yana shigowa kuwa ya dire ledojin yana mai cafe ni ya fara juyi dani. Ɗage ƙafa ta nayi ina mai wara hannuwa na nake kyalkyala dariya cikin sauƙin soyayya.

Direni yayi yana mai tallafo kaina da dukkan hannuwan shi.

"Sweet Heart ya gidan ya kaɗaici?"

Murmushi nayi ina mai cewa "Dear ina tare da tunanin ka a zuciya bana tare da kaɗaici" shima murmushin ya mayar mani, yana mai shafo gefen fuska ta. Yake cewa "I missed u aloot wify, muje mu jera kayan nan ko?, sai kiga abubuwan da za'a sake nemowa"

"Done dear" Abunda na faɗa kenan, ina mai sunkuyawa na sunkuci wasu ledojin, yayin da shima ya kwashi wasu a hannun shi. Ina gaba yana biye dani a baya har zuwa cikin kitchen ɗin.

Nayi mamakin yanda akayi har ya iya wannan soyayyar kaman mace, duk abubuwan da yasan za'a buƙata ya siyo shi saidai Abunda babu. Hatta da kaji da dangin su kifi da jan nama, wanda akayi packaging nashi cikin farar santana, saida ya siyo. Shi ne ya koma motar yana kwaso sauran kayan ina jera su inda ya dace. Hatta da lemuna wanda ma ban taɓa gani ba, duk da dai dama akwai wasu a cikin fridge ɗin dana tadda.

Muna gamawa ya kamo hannuwa na zuwa falo. Saman cinyar shi yake ƙoƙarin zaunar dani na ƙiya, ina mai sulalewa ƙasa na shiga zare mashi takalman da safar. Sai kuma na kwashe su zan wuce dasu ma'ajin su a bedroom.

Caraf Naji ya sake ɗauke nj, ga alamu dai Ya Ameen yana jin ƙarfi a jikin shi, in ba haka ba, duk da nake ba siririya ba, hakan baisa yaji wahalar ɗaga ni. Har cikin bedroom ɗin ya ajiye ni jikin shoes rag ɗin.

Da kanshi ya zari takalman yana mai jawo rag ɗin ya saka su ciki ya maida ya rufe. Sai kuma naji ya shiga jana zuwa bakin gadon.

Zama yayi yana mai langwaɓe kai. "Sauran kayan baby" ɗan waro idanu nayi. Kayan ma nice zan cire mashi?

Langwaɓe kai ya kuma yi, yana mai yamutsa fuska wai shi nan shagwaɓa. Kallon shi kawai nakeyi, mamaki nake cikin zuciya ta, anya kuwa ya Ameen ne?

A hankali na duƙa ina mai tallafo fuskar shi da tafukan hannayn nawa, wani irin abu na fizga ta zuwa gareshi, gani nake kaman almara, wai Ya Ameen ne nan zaune gabana yana zuba mani shagwaɓa, ya ajiye girman kan, sarautar, kuɗi da izzar.

"Dear ya gajiya?" Abunda na samu kaina da cewa kenan.

"Akwai ta kam wify, ina son massage please"

Gyaɗa mashi kai nayi, ina mai zare hannun daga fuskar tashi zuwa ƙirjin shi na shiga ɓalle mashi maɓallan rigar.

Sannan ya ɗaga hannun na shiga zare mashi bady Hug ɗin. Kwantawa yayi plat, ƙafafn shi na ƙasa, na haye bisa gadon na fara mammatsa mashi jikin kanshi na bisa cinya ta.

Lumshe idanu yake cikin wani irin yanayi. Har barci ya fara fizgar shi, gashi kuma ga alama yana buƙatar watsa ruwa. A hankali na shiga sauke kanshi saman fillow ɗin dana jawo. Yana ji na baiyi yunƙurin hana ni ba. Saidai murmushi da yake saki. Har na idasa sauka na nufi hanyar toilet.

Sai da na haɗa ruwan sannan na dawo ina mai tada shi a hankali. Fizgata yayi na faɗa bisa gadon, inda ya birki ta ni zuwa ƙasa ya shiga nuna mani ƙauna. Daƙyar na kwaci kaina ina mai maida numfashi. Shima a hankali ya miƙe, yana mai cusa hannayn shi cikin sumar dake kwance luf saman kanshi, har yanzu idanun shi a lumshe suke. Ganin ya fara ƙoƙarin zame dogon wandon ne ya sanya ni saurin ficewa.

Cikin abubuwan daya shigo dasu masu sauƙin sarrafawa na ɗauko gami da sama mashi abu mai sauƙi da nasan ba zai ƙi ci ba.

Ya daɗe yana cuɗa jikin shi, da yake jin ƙamshin ruwan daban. Ga alamu ta zuba turarukan wanka da baisan da irin su ba.

Ina kitchen har ya fito ya dawo ɗakin, saida ya gama muttsuka mai mai sauƙin zafi, sannan ya zuro gajeren wando mai ruwan na sojoji, sai amless fara mara nauyi sosai.

Fitowar shi tayi daidai da gama ɗora abincin bisa dining.

Tsaye nayi ina mai ƙare mashi kallo, cikin jin nauyi. Ya kula da hakan. Shiyasa ya nufi inda nake direct, yana kai cewa "Wife Sannu da aiki, me kike haka naji ki shiru, ina cen ina ta jiran kizo ki cuɗa ni" ya faɗa yana mai kashe ido ɗaya.

Sauke kaina ƙasa nayi ina mai cewa "Yaya abinci na sama maka, nasan maybe baka ci komai ba"

"Kaman kuwa kin sani, sauko mani dashi ƙasa, zanfi jin daɗin zama, u know i missed your food sosai"

Sai ma ya bani kunya, mutumen da ina kallon shi ko abincin na girka bai cika ci ba sosai, yafi cin na Umma ko da cen ma.

Tsakiyar falon na jera mashi abincin inda yake zaune da remote na Ac yana daidaita sanyin.

Sai da na kammala ajiye mashi komai na zuba mashi sannan nima na koma gefe inda zai iya gani na na zauna.

Ƙura mani idanu yayi.

"ba zan iya ci da kaina ba fa" ya faɗa still yana wani lanƙwashe wuya irin na ɗazu. Dariya ma ya bani, murmusawa nayi ina mai cewa "Baby as u wish"

Ba musu ya shiga amsar abincin da nake bashi a baki har ya ƙoshi, yaci abincin sosai har ya fara bani tausayi, ganin yanda yaji yunwa har haka. Shima haka ya shiga cida ni bayan na gama bashi, cikin kunya nake amsa. Har muka kammala cin abincin.

Miƙewa yayi yana mai nufar ɗaki ya ɗauko wayar shi da system tashi.

Sai da ya daidaita zaman shi bisa sofa, sannan ya jawo ni kusa dashi, ban musu ba na lafe, dama kuma na riga na maida kayan abincin kitchen.

"Baby ina so ne muyi wata shawara dama, tin ɗazu sai kuma na bari mu natsu sana"

Ɗan ɗago wa nayi ina mai kallon fuskar shi, bakin nan gum kaman gidan tsutsa, gashi da haske kaman ya shafa

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment