Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Uncle ɗina ya iya soyayya, ita fa har ta ƙagara ta ganta a ɗakin shi, ni kunya ma ta bani, na dinga kyalkyala mata dariya.

Ko da na kira Hafsat video ita mukayi, Munsha fira, har tana nuna mani samɓaleliyar yarinyar ta mai kyau, ga wayau kaman anyi suna, dayake an sallamo ta tana gida, suna kuma an ɗaga sai nan da sati biyu, Abunda ya sanya ƴan kankiyr tattara wa suka koma kenan, suna mai cewa idan an tashi sunan sun zaɓi wasu su wakilci su, ai ba sun tare anan ba, Kaka zuwaira ma ta tafi jiya bama nan, bamuyi sallama ba, banji daɗi ba, ina son tsohuwar ta shiga raina sosai, naso nayi mata abun alkhairi sosai.

Wannan ce ta sanya na rage kaɗaici, duk da nake zaune ni kaɗai kwallin kwal.


Wata ƴar matashiyar yarinya ce tayi sallama sashen namu, daga bedroom na fito ina mai amsa mata, ba zata wuce shekara sha biyu ba, itama ɗiyar wata sabuwar mai aiki ce da aka ɗauka, wai zata dinga taya Umma ta aikace aikace, duk da Ummata ta nuna bata ra'ayi, har yanzu dai shi Dad yana nan kan ba kanshi.

Bayan ta gaishe ni ne har ƙasa take sanar dani "wai inzo inji Aunty Nihal don Allah"

Nayi mamaki, Nihal kuma? To kiran me take mani? Yanzu fa ba da bane da zata kira ni naje, Amman koma menene ya kamata inje ɗin saboda inyi ma abun tufkar hanci.

Ce mata nayi tace mata ina zuwa, inda na ɗauko samosa guda biyu cikin wadda nayi ma Ya Ameen na bata, saboda na fita haƙƙin ta, ko ba komai nasan taji ƙamshi.

Fita tayi tana ta murna, inda na koma na ɗauko gyale na nabi bayan yarinyar.

Har bedroom ɗin Nihal ɗin na shiga, tana cikin bargo naɗe tana latsa waya.

Sallama kawai da nayi ta amsa da kyar, tana mai ɗagowa ta kalle ni cikin yamutsa fuska.

*"Banana shake nake so ki haɗo mani"*

Abunda ta iya cewa kenan ta maida kanta ga wayar tata tana cigaba da latsawa.

Tsaye nayi ina kallon ta, ta raina ni ma wallahi, kenan da yarinyar tace don Allah, ita ce ta tausasa kenan? Haba no wander Nidai nayi mamaki wai Nihal tace mani don Allah, saidai in da wata manufar.

Ɗagowa tayi tana mai watsa mani wani matsiyacin kallon.

"Bakiji me nace bane? Ko ba hali ne?"

Ga yara tsayuwa ta nayi, ina mai sakin wani killer smile. Lokaci guda na shiga cewa.

"Ke baki san inda kitchen ɗin yake bane? Ko na fiki sanin hanyar? Wannan na daga cikin Abunda yake son kashe maki aure, kada ki manta ni fa yanzu yayar ki ce, ba da bane, na ɗauka ma kin kira ni ne akan na taimaka na baki shawarar yanda ake zaman aure da kula da miji? to ki sani a yanzu saidai ni in sanya kiyi mani, idan kin ƙiya kuma in sanya Yayanki ya sanya kiyi don dole"

A zabura take kallo na, idan ranta yayi dubu to ya ɓaci, Suhan ce ke tsaye haka kanta tana watsa mata wannan kalaman masu kama da tafasasshen ruwan zafi? Ita har tayi ƙimar da zata iya koya mata zaman aure? Yaushe ma ta fara zaman aure?

Ganin zata buɗe baki ta sake gaya man wata maganar na dakatar da ita cikin ɗaga hannu "Enough is Enough malama, ki kiyaye ko dan gaba, idan ba haka ba Rayuwar ki zata iya ɓaci". Ina gama faɗin haka na sanya kai na fice, ina mai ƙutawa da kyaci. Ta bala'n ɓata man rai, Amman idan nayi la'akari da kalaman da na faɗa mata, sai inga ai gara ma da akayi hakan, ko ba komai zata dinga yin shakkar shiga gona ta

Ina ficewa ta sauko daga bisa gadon cike da bala'i. Dole ne ma wannan matsiyaci yar yarinyar ta fice ta bar masu gida, ita ce zata zo har ɗaki ta yaɓa mara magana kuma ta fice lafiya lau?

A karo na farko kenan da ta karya billen ta ta shiga kiran Layin Nureen ɗin.

Saida tayi mashi missed call goma kafin ya ɗauka. Murya cen ƙasa ya shiga ce mata. "Hello please who is on the line?"

Cikin kwallo idanu ta shiga cewa Baby baka gane mai magana bane? Kayi deleting ɗin number ɗita ne?

"Owh Nihal akwai matsala ne?"

Kuka ta fashe mashi dashi "Baby kazo ka ɗauke ni please, yanzu na iya komai kuma zan dinga yi maka komai please"

"Hold on Nihal, yanzu am very busy we'll talk later on" yana gama faɗin haka ya katse kiran.

Cikin kuka ta cire wayar a kunnen ta, tana bin wayar da kallo, kaman mai neman gano fuskar babyn nata. Sudat ta kira, ita ce abokiyar yinta, domin tasan ta kira Aunt Feena ƙaniyar ta zata ci sosai, to balle oga uban gayya Ya Ameen da baya ɗaukar wargi ko kaɗan.

Saida tayi kukan ta mai isar ta Saudat ɗin na bata haƙuri, sannan ta faɗa mata Abunda Suhan da Nureen suka yi mata, itama bata ji daɗi ba, Amman tace ta shirya tazo gidan ta same ta zasu san abun yi, ita tana tsoron tazo su haɗe da Dad.

"Aunt Saudat Mom fa bata nan, wai sun tafi gidan su Umman Suhan ita da su Dad da Uncle Alhaji"

Cikin tsananin mamaki da ɓacin rai Saudat ɗin ke cewa "Me suka je yi ne, ita mom me ya kai ta? Ta sani fa sarai mutanen nan ba ƙaunar mu suke yi ba, ki duba kiga yanda suka raba mu da Dad, Amman shine ta kama ta bisu" cewa saudat.

Cikin mamaki Nihal ɗin ke cewa "Ke Aunt Saudat baki san meke faruwa ba wai?"

"Me ya faru ne Nihal tell me now" itama ta faɗa cike da yatsina.

"Uhmm ke dai bari inzo kawai maganar bata yuwuwa a waya, Amman saidai nazo kawai, Mom na cikin wani hali ashe baki ji ba" saurin katse wayar tayi tana mai tashi ta zari yalolon gyalen ta, haɗi da ɗaukar makulli motar ta ta fice.

Ni kuwa jin zuciya ta sakayuu nake yi, ko ba komai nima na fara rama wani kaso daga cikin irin wulaƙancn da na fuskanta daga wajen Nihal, bana ƙullatar su, saidai ya zuwa yanzu ba zan iya jure wulaƙanci irin wanda na Ɗauka ada cen baya ba, lokacin da ina ƙarƙashin su.

******


Sun jima sosai suna aiki, sannan sai ga Baba Alhaji ya dawo, tun da yaga Al'ameen fuskar shi ta yalwanta da murmushi, yayi tsammanin ganin wani daga cikin gidan dama, saidai bai tsammaci ganin Al'ameen ba, ya ɗauka ko Alhaji Mustapha ɗin dama ko ita kanta Hajiya Kubra ɗin.

Bai ɓoye mamakin shi ba yake tambayar shi Dad ɗin nashi bayan sun gama gaisawa a mutumce.

Ba tare da kawo komai a ran shi ba, ya shiga shaida mashi inda suka tafi tare har da Mom ɗin tashi.

Ƴar fara'r dake kan fuskar shi ce ta ragu,yana gyaɗa kai a hankali, sai kuma ya gyara zama yana mai fuskantar a Al'ameen ɗin, tare da son jin dalilin zuwan nashi.

Bayan ya gama zayyana mashi komai, sannan ya buƙaci jin ƙarin bayanin wasu bayanai da kaf duniya daga wajen Baba Alhajin ne kawai yake sa ran jin su.

To saidai kalaman da Baba Alhajin ya faɗa mashi su ne suka sabbaba ɗaukewar numfashin shi, tare da bugawar zuciyar shi na wucin gadi. Da kyar ya lalubo numfashin nashi, yana mai ƙura ma Baba Alhaji idanun da ya zuwa yanzu idan ka kalle shi zaka iya cewa garwashin wuta ne aka ɗebo aka watsa mashi a ciki. Idanun nashi har sun fara tara kwalla, ji yake kaman kanshi zai tarwatse, me kalaman Baba Alhajin suke nufi?

*"Al'ameen ina so ka natsu ka saurare ni, kuma ka fuskanci inda na dosa, a zahirn gaskiya batun da kazo mani dashi na son sanin wasu muhimman bayanai da kake son sani daga gareni, dangane da harƙallolin mahaifiyarka da kuma ita kanta asalin dukiyar, duk da ka tabbatar da cewa gadarta tayi daga wajen mahaifin nata marigayi, abu ne mai wuyar gaske, da zaka ji shawara ta ma, da sai nace kabar batun nan kawai zaifi, kada kaje ka bankaɗo wani sirri, wani ƙulli, wani mugun dakwaye mai warin gaske, da zai yi silar tarwatsewar farin cikin ku gabaki ɗayan gidan ku, da kuka daɗe kuna ginawa kuma kuna rayuwa acikin shi tsawon shekara da shekaru"*







~Oum-Deedat ce~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~72~*


*Ina fatan za'ayi haƙuri da ji na shiru da akeyi kwana biyu, hakan ya faru ne sakamakon ayyuka da suka sha man kai, haɗi da hidindumun wannan rayuwar da basu ƙarewa. Allah yayi mana muwafaƙa, ina jin daɗin Addu'oin ku, Oum Deedat tana yi ku over. A cigaba da gashi...*



Falalar Salati Ga Annabi, Tsira da Amincin Allah Su Tabbata A gare shi
Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Wanda ya yi salati daya a gare ni, Allah zai yi salati goma a gare shi".

Kuma Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Ka da ku mai da kabarina idi, ku yi salati a gare ni ko ina kuke, domin salatinku yana isa zuwa gare ni ko a ina kuka kasance.

Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa amma bai yi mini salati ba.

Kuma Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce, Allah yana da wadansu Mala'iku matafiya a bayan kasa, suna isar mini da sallama daga al'ummata.


Kuma Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Babu wani wanda zai yi mini sallama face Allah ya dawo mini da raina na amsa masa sallamarsa".




°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°




Ya kai kusan minti biyar kanshi na a duke, jujjuya maganar Baba Alhaji yake yi a tsanake, ya gaza tsintar ma'anar ko kalma ɗaya, wannan wane irin ƙullin dakwaye ne haka mai mugun wari? Me Mom ɗinshi ta aikata ne har haka?

Jin kanshi yake kaman zai tarwatse, ni kaina da nake laɓe ina kallon su, ba zan iya tantance irin yanayin da ya shiga ba.

A hankali ya shiga ɗago kan nashi, yana mai ɗora idanun shi tsaf bisa fuskar Baba Alhajin da yake zaune, wani irin tausayin Al'ameen ɗin na kuma kama shi.

Baki ya buɗe da niyyar cewa wani abu, Baba Alhaji yayi saurin dakatar dashi, ta hanyar ɗaga mashi hannu.

"A'a Muhammadu Ameen, kada kace komai, na sani kai yaro ne mai biyayya, saboda haka ne ma tun haihuwar ka nake maka kallon Kabeeru gashi nan zaune, banso kaji wani abu daga baki na ba, sannan nayi murna da ka sanar dani cewa Alhaji Mustapha watau mahaifin ka, da Hajiya Kubra, mahaifiya gareka sun nufi garin Adamawa. Saidai zan so ka ƙkara sanya ma zuciyar ka hakuri da juriya kaman yanda na faɗa tun farko, abubuwa na ban mamaki da al'ajabi, ban haushi da tausayi zasu faru, Amman ina so ka sani har gobe ita ɗin mahaifiyarka ce, biyayya gareta dole ne kuma tilas ne, kaine kawai zaka zame mata ƙarshen ƙwarin guiwar ta, a yayin da kowa zai iya juya baya gareta, kada ka sake ka barta, kada ka sake ka nisance ta, ka kasance tare da ita a koda yaushe. Idan kuma har kaga na sanar dakai wani abu, to cikin ɗayan biyu, imma dai su mahaifan naka ne suka so ka san hakan, imma an kira wo mu ne ni dakai zuwa ga masarautar"

Baba Alhajin ya ƙkarashe maganar tashi yana mai nisawa, tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Tashin hankali!!!

Da sauri ya dafe kanshi dake jujjuya mashi, ji yake kaman ana hajijiya dashi, me Mom take aikatawa har haka da Baba Alhaji yake iƙirarin kowa zai iya juya mata baya???

Baisan lokacin da ya tashi tsaye ba, ba tare da yace da Baba Alhajin komai ba ya nufi ƙofa, cikin sauri Baba Alhaji yace ma Barrister Kabeer "Maza kaje ka kai shi gida Kabeeru, sannan ka ce ma da matarshi ta kula dashi sosai, dole ne nasan wannan ranar zata zo, saidai koma menene ina fatan yazo da sauƙi"

Da hanzari Barrister ya mike har yana sassarfa. Bayan Al'ameen yabi, ba tare da yace da Baba Alhajin komai ba shima.

Cen ya hango shi yana tafiya yana haɗa hanya, kaman zai kife, da saurin shi ya ƙara sa yana mai ce mashi "Yallaɓai kawo makullin motar ko?"

Miƙa mashi yayi ba tare da ya ce dashi uffan ba, yayin da ya kama shi yana mai zagayawa kujerar mai zaman banza, ya buɗe ya zaunar dashi, ya koma driver seat ya zauna, yana mai yi ma motar key.

Gudu yake sosai har kawo lokacin da ya isa ga ƙkofar gidan, da gudu Idi ya buɗe mashi gate ya shige.

Ya Ameen kasa fitowa yayi, gani yake kaman dama kowa yasan laifin mahaifiyar shi, kowa kallon su kawai yake a ɗage, zaune yake kawai kaman mutum mutumi.

Barrister wajen da Idi da Iro suke zaune ya nufa, yana mai cewa dasu suzo su taimaka mashi. Da hanzarin su suka taso, inda har Ya Ameen ya ɓalle murfin motar ya zuro ƙafafun shi.

Sallame Sallah ta kenan, ina zaune wurin dai kawai ina ta addu'oi na sosai na neman zaman lafiya da miji na, da sauran duk wanda Allah ya haɗa ni zama dashi.

Naji ana ta ƙiƙirniyar shigowa, da sauri na miƙe ina mai shafa addu'ar, hannu na ɗauke da casbaha ina ja.

Falo nayo, cikin salon tafiya ta, fuska ta ɗauke da maɗaukakin murmushi, so kawai nake nayi arba da gwarzon nawa, abun so na da alfahari na. Daga baƙin ƙofa ƙafa ta ta ƙage, na kasa cira ta in cigaba da tafiya, hangowa da nayi an shigo da Ya Ameen a rirriƙe, duk da yana iya takawa da ƙafafun shi.

Har kai lokacin da suka zaunar dashi bakin sofa, suna mai gaishe ni suka juya suka fice, in ka ɗauke Barrister shima da ya zauna wata kujera mai kallon ta Ya Ameen.

Da addu'a ta da komai na samu na cira ƙafa ta, ina mai takawa cikin sauri na nufi inda Ya Ameen yake zaune dafe da kai sosai. Gaban shi na zube ina mai cewa "Ya Ameen lafiya kuwa!? Me ya same ka!? Kayi man magana mana please,


" Barrister me ya samu Yayana don Allah!?" na faɗa ina mai maida akalar tambayar ga Barrister da yake zaune, idanu na har sun kawo ruwa, gab suke da zubowa.

Zaman shi Barrister ya gyara, yana mai fuskanta ta.

"Nooo Suhan, ba wani abu bane babba, kin dai san yanayin jikin nashi, so dole ne ki kula dashi sosai, kada ki tada hankalin ki, saboda muna so dole ne sai kin taimaka wajen kwantar mashi da hankali, yana tattare da damuwa ne, shine kawai, Amman kiyi ƙoƙarin ganin kin samo kanshi please" shima ya faɗa cikin son kauda mani zargin wani abu, saboda baya da masaniyar ko nasan abunda ke faruwa.

Ni kuwa har kwalla ta ta fara gangarowa, na juya ina mai kallon Ya Ameen da ya wara idanun shi a kaina, yana mai girgiza man kai a hankali, alamun kada nayi kuka.

Hannun shi ya miko gareni, alamun in taso kusa dashi, ba musu na kama hannun ina mai miƙewa zuwa bisa kujerar kusa dashi, ganin hakan da Barrister yayi, ya sanya shi miƙewa yana mai faɗin "Na barku lafiya amarya, idan da wani abu please kiyi gaggawar sanar dani, ko wani na kusa" ya faɗa yana mai takowa zuwa gaban Ya Ameen ya miƙa mashi hannu sukayi musabaha.

Da kyar Ya Ameen ya iya buɗe baki yana mai cewa dashi "Nagode Barrister, zamuyi magana zuwa anjima"

"Take care" Abunda Barrister kawai ya faɗa kenan yana mai juyawa ya fice.

Da yatsan shi yayi amfani wajen ɗauke man wani sabon kwallar da suka gangaro.

"Kukan na menene wify?"

Ya faɗa cikin ƙarfin hali, a ƙoƙarin shi na son kauda mani tawa damuwar

Kaina na kwantar zuwa bisa kafaɗar shi, ina mai sakin shagwaɓa a hankali nake cewa "to ba kai bane?" murmushi yayi shima kaɗan yana mai shafo gefen fuska ta.

"Nine me?" ya bani amsa shima, "Kaine mana, kasan baka lafiya ka fita a haka, gashi tun ɗazu nake jiran ka dawo kaci abinci, na kira ka kuma baka ɗauka ba, na maka massage ba reply, Haba dear" na kuma ƙarashewa cikin wata shagwaɓar.

Ƙoƙarin zare man hijab ɗin dake jiki na yayi, yana mai sakin murmushinƙkarfin hali a hankali a hankali.

"Ya isa hakanan to, ba gani na dawo ba? Dan dai salon shagwaɓa da sakata kawai, ga wata hijab da kika ƙaƙaba a cikin gida, kaman...." shima ya faɗa yana mai kashe man ido guda.

Taimaka mashi nayi wajen zare hijab ɗin, ina mai cewa "Tun da na gama salla ne ai dear sai ban cire ba" nima na faɗa cikin jin daɗin yanda naga ya ɗan saki jiki, alamun sauƙi na samuwa.

Shi kuwa Ya Ameen ta ɓangaren shi, ƙarfin hali kawai yake, gudun jefa ni cikin wata damuwar, tinda gashi har kwalla na fara, daga ganin shi cikin wani yanayi, ya kula ma dai kwallar bata yi mata wahala, kaman wata ruwa-ruwa.

"A taimaka man da ruwan wanka, daga nan sai inyi alwala, idan na gabatar da sallar sai...."

"Kaci abinci ko dear, nasan dai kana jin yunwa" na katse shi nima cikin murmushi, haɗi da jan dogon sirirn hancin shi, ina mai miƙewa na ɗauki hijab ɗita, na wuce kai tsaye zuwa bedroom, cikin murmushin da nasan yafi ƙauna daga gareni.

A bakin ƙofa na tsinci cesbaha ta, ashe nan na yarda ita. Duƙawa nayi na ɗauka ina mai murmusawa na wuce zuwa cikin ɗakin.

Ta bayan ta yake binta da kallo, komai nata a nutse yake, shi ya ma manta da wata aba wai ita yunwa, ƙalubalen da yake gaban shi, ya tabbata da baya da aure zai iya yin tsawon kwanaki, ba tare da ya kai ko spoon ɗaya a bakin nashi ba.

A hankali ya miƙe zuwa waje, ɗauko wayar shi yake so yayi, sai yanzu ne ya tuna da wayar na cikin mota ashe.

Da gudu su Iro suka taso suna masu yi mashi ya jiki,hannu kawai ya iya ɗaga masu ya buɗe murfin motar ya zura kanshi ciki da niyyar ɗauko wayar.

Har ya ɗauko ya fito ya kulle motar, sai a lokacin ne ya kula da Iro da yake tsaye ta bayan shi.

"Lafiya dai ko? Malam Iro?" Abunda ya Ameen ɗin ya iya cewa dashi kenan kawai.

Shi kuwa Iro duƙar da kai yayo yana mai sosa ƙyeya da hannu, alamun kunya.

Murmushi Ya Ameen ya saki, cikin kulawa ya shiga ce mashi.

"Malam Iro kayi magana mana, daga ni fa sai kai ne a wurin, kunya ta kake ji? Ina fatan ba dai wata matsala ko? Idan da matsala, kayi haƙuri idan zan fito anjima sai in ganka"

Sake duƙar da kai Iro yayi yana murmushi "Ranka ya daɗe ba wata matsala bace, kawai dai ina so ne muyi maganar Maree ne dakai, gaskiya ina neman da a bani auren ta, kaf duk duniyar nan babu wadda nake so da aure in ba ita ba"

Maganar Iron ta bashi mamaki, har saida ya bayyana a fuskar shi, lokaci guda kuma ya shiga murmusawa.

Ya Ameen kenan, mutum mai farin hali, farar zuciya, da farar fata. Komai nashi shi daban ne.

"Malam Iro kenan, to ai ina ganin ba ni ne ya kamata ka samu da wannan maganar ba, ita yarinyar da mahaifiyar ta zaka samu, idan sun amince ne, sai ka neme mu daga baya, abu yayi kyau ina taya ka murna sosai fa"

Ya ƙarashe yana mai dafo kafaɗar Iron, sannan ya ja shi suka fara takawa.

Abunda ke burge kaf ma'aikatan gidan kenan dangane da Ya Ameen ɗin, shi mutum ne mai sauƙin halin da yake zaune da kowa lafiya, idan har Kaga fushin shi, to fa ka aikata abunda yake ba daidai bane.

Cikin jin kunya Iron ya shiga cewa "To Yallaɓai, insha Allah zan tuntuɓe ta, wallahi na kasa ne tun tuni, Kunyar ta nake ji Shiyasa" Dariya sosai yaba Ya Ameen, har saida fararen haƙoran shi suka bayyana.

Ikon Allah kenan, wai Maree da take hauka kanshi, ita ce yau Iro shi kuma ke cewa yana so.

"Ya kamata ka ƙoƙarta malam Iro" ya faɗa shima yana mai zaro kuɗi daga cikin aljihun shi, ya damƙa su ga hannun Iron, kuɗi ne masu yawa "Ga wannan ba yawa kuyi haƙuri, kaje ku raba kai da Idi ko?" ya faɗa yana mai sakin hannun.

Cikin tsantsar murna da farin ciki Iron ya shiga godiya, kaman zai duƙa ma, Ya Ameen ɗinne yayi saurin taro shi. "Ba damuwa kaji ka ƙoƙarta dai, ina sauraren ka" shima ya faɗa yana mai jufar cikin sashen nasu.

Ni kau ina fitowa falon na tadda ba kowa ciki, kitchen na leƙa nan ma bai nan, ƙofar sashen namu na nufa, aiko na hango shi cen tsaye da Iro bakin mota, sai kuma naga ya saƙalo kafaɗar Iron sun shiga takowa. Murmushi nake sosai, watau Ya Ameen baya ƙyamar talaka, baya ƙyamatar masu aiki, jibi yanda ya haɗo jiki da Iro don Allah kaman wani abokin shi.

Tun kafin ya ƙaraso inda nake tsaye, yake sakar man wani irin killer smile, nima murmushin nake mashi, inda ya shiga wara man hannayen shi alamun in taho.

Ganin ana iya hangen mu, sai na shiga noƙe mashi kafaɗa alamun a'ah, turus yayi inda yake tsaye, shima yana mai noƙe man kafaɗar alamun a'ah shima sai na taho.

Wayar shi ce dake hannun shi ta ɗauki ringing. Bilal ne. A hankali ya ɗaga, yana mai cigaba da takowa suka fara magana da Bilal ɗin.

Sanar mashi yake ya iso yaje ya ɗauko shi. Inda shi kuma ya shiga sanar mashi cewa wanka zaiyi yanzu, idan zai iya jira. Bilal ɗinne yace bari ya hawo taxi kawai.

Yana ƙarasowa inda nake tsaye ya damƙo hannu na yana mai jana, haɗi da ce man "Muje ki taya ni wankan Mrs Al'ameen Dambulan"

Bance mashi ƙala ba, na shiga bin shi, har saida muka isa wajen hanyar kutchen, na zare hannun nawa, na kwasa da gudu zuwa cikin kitchen ɗin ina mashi gwalo. Biyo ni yayi da gudu shima, saidai kafin ya ƙaraso na maida ƙofar na kulle, na jingina baya na da ƙofar ina mai sulalewa nake sakin dariya sosai.

Shima dariya take sosai, watau so take ta mantar dashi damuwarshi, abunda bata sani ba, damuwa ce wadda ba yanda zaiyi ya iya mantawa da ita, har sai komai ya warware. Shi abunda yafi komai ɗaga mashi hankali ma shine, kalaman Baba Alhaji da yake cewa wai tafiyar Mom da Dad ɗin nashi, zasuyi sababin faruwar abubuwan ban haushi ɗana al'ajabi.

To meye alaƙar Mom da masarautar Adamawan? Wanda zai iya iƙirarin cewa Mom ɗin tashi bata taɓa taka garin ba? Duk yawa ce yawancen ta bata taɓa yin cen ba, duk kuwa da cewa tasha faɗa mashi cewa tana so taje, lokutta da dama idan yana bata kabarin ƴan gudun hijiran dake wurin.

Murya sosai ya ɗaga yana mai ce mani "Kina nufin wayau kika yi mani ko? Zamu haɗu ne ai" ya faɗa yana mai wucewa kai tsaye zuwa ɗakin.

Ya daɗe yana cuɗa jikin shi, ba don komai ba sai don tunani da ya

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment