Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da umma ta ta ɗauki hannu ta bigeni ba, saboda ita mace ce mai san yin hali, Sam bata da zafi;

kuka na fashe dashi lokaci guda ina mai ƙanƙame jikina, yanda naga ta hassala kaman zata rufe ni da suka.

"Ashe ke shashasha ce hauwau ban sani ba?, ina tarbiyyar da na baki? Ina kika kaita, nan ɗin da kike ganin ana wulaƙanta mu, ya fiye mana cen, in kika koma kashe ki zasu yi, nace kashe ki zasu yi! Ni ma ba zasu barni ba, saboda ke nake zaune nan, dan ki tsira da mutuncin ki, ki tsira da rayuwarki yasa nake zaune nan, nima abun yana man zafi, Amman ko me zasu yi mana ba zasu iya kashe mu ba, zaki mutu ne muddin kika yarda kika koma cen" kwalla ce ke shata ta a idanun umman tawa, abun da ya ƙara matuƙar firgita ni kenan, rarrafawa na shiga yi ina mai zuwa inda take na rungume ta, ture ni ta shiga yi, jeki, je ki nemi mahaifin ki, ƙila zakiyi sa'ar ganin kabarin nashi, ƙila zai iya tashi ya faɗa maki komai, Hauwa'u ban tsammanin akwai ranar da har ke zaki iya zuwa ki sanya ni a gaba ba, ki titsiye ni sai na faɗa maki wacece ke ba, na ɗauka na gama maki komai, na ɗauka na ishe ki komai, ban tsammanin zaki gaji da zama a inda na zaɓa mana rayuwa ba, nace kashe ki zasu yi, muddin kika yarda suka san kina nan da ranki, jeki jeki ki nemo dangin mahaifin ki, ki nemo dangi na, Amman ni kar ki ƙara tambaya ta game da su, kar kuma ki sake ki dawo inda nake, kuma duk Abunda ya same ku ke ce kika siya da kuɗin ki, kar ki ƙara tambaya ta abunda ya shafe su; Ta shiga ƙara ture ni daga jikin ta tana mai share kwallar da take ta ambaliya a fuskar ta.

Ƙara ƙwaƙume ta nayi, ina mai sakin gunjin kuka lokaci guda ina mai faɗin "Umma kiyi haƙuri ki yafe man, ki gafarce ni umma, nayi maki laifi, na aikata maki ba daidai ba umma, na cutar da zuciyoyinmu umma, bansan haka ba, bansan komai ba umma ki yafe man" shiru naji lokaci daƴa kaman ma bata numfashi, A firgice na ɗago, domin in ga me ke faruwa, abunda idanunwa na suka gani ne ya sani sakin razananiyar ƙara da sai da ta cika ilahirin sashen namu. Jikin ta gaba ɗaya ya saki, kaman wadda ta mutu bata numfashi Sam, "umma ki tashi" na shiga faɗi lokaci ɗaya ina mai jijjiga ta "umma ki tashi don Allah na bari, umma ki yafe man, umma kar ki mutu ki barni don Allah, umma ban da kowa sai ke, ke ce uwa ta ke ce uba na umma, ke ce komai nawa umma, kar ki mutu ki barni a cikin gidan nan umma, zan mutu nima in biki wallahi muddin kika barni, umma basa son mu basa ƙaunarmu, kar ki barni ni ɗaya a cikin gidannan" kuka ne gami da majina suka bi suka haɗe a yalwataciyar fuskar tawa, bama ta su nake yi ba, balle in mai da kai wajen share wa, gunjin kuka na nake yi mai cike da ruɗani kala kala, yayin da umman tawa take sharaf a jikina babu alamar numfashi tattare da ita, kwantar da ita na shiga yi lokaci guda ina mai girgiza kaina "umma ta bazata mutu ta barni nan ni kaɗai ba, bansan kowa ba umma sai ke" haka nake faɗa yayin da na tashi na fice da matsanancin gudu zuwa nemo wanda zai duba man ita, a tsakar gida muka haɗu da sauran ƴan aikin gidan da duk sun jiyo kuka na sun fito hankali tashe, hannun uwani na shiga ja ko sauraren ta banyi ba ina faɗin "mama uwani Kuzo ku duba man umma ta kar kuce man ta mutu, kar kuce man bata da rai, kar ku kashe man ita" mama Talatu Kuzo" na saki hannun mama uwani da nufi mama Talatu da gudu itama na shiga jan ta, ina mai sake sakin kuka mai tsuma rai, "me ya samu maman Suhana ɗin ne wai? " mama uwani take tambaya ta, ban iya bata amsa ba, domin naga sun yi tsaye sun ma ƙi shiga ɗakin, hanyar waje na nufa da gudu cikin kuka ina kwala ma baba idi kira, yazo ya duba ban umman tawa.


Tin daga nesa ya hango ta, Ya Ameen ne da ya fito daga part ɗin nashi cikin shirin zuwa wajen aiki, suit ce sanye jikin shi kalar royal blue, ya matuƙar yin kyau cikin sanyin shi yake takawa da niyya zuwa ɗaukar motar tashi, ya hango ta tayi hanyar fita waje cikin matsanancin gudu, kuka ma take yi, duk ta cukuikuye hijabin tata kaman mahaukaciya, lelleƙawa nayi banga kowa ba, ga dukkan alamu ma basu baro sashen nasu na maza ba da yake cen gefe guda da namu Amman da tazara sosai, juyowa nayi da gudu zan koma sashen namu wajen umman tawa, kuka nake bil haƙƙi da gaskiya ni a tunani na umman tawa ta mutu ne, karo naci da mutum ba tare da sanin ko wanene ba na shiga jan hannun shi, idona ya kulle, bana ganin kowa bana ganin komai, umma ta kawai nake kira, lokaci guda Naji an kama man hannuwa duka an riƙe aka shiga girgiza ni, "ke ki natsu, natsu nace, ki faɗa man me ya sami umman taki? Tana ina ne?" amon murya shi ta bugi dodon kunne na lokaci guda na wara idanuna akan shi, shi dai ne, Ya Ameen ne riƙe dani ni suhan, yana girgiza ni, hannuwa na duka cikin nashi, duk da firici da halin kuka da damuwa da nake ciki, bai hanani jiyo ƙamshin turaren shi ba da kuma taushin hannuwan nashi da suke cike da wani sanyi mai ratsa zuciya, "umma ta, ba zata mutu ba, Ya Ameen kaje ka duba man ita don Allah, bata numfashi, bansan haka ba da ban mata maganar ba, kada ta mutu ta bar ni ni ɗaya cikin gidan nan bansan kowa ba sai ita duk duniyar nan"

Na faɗa cikin kuka ina mai durƙushe wa kan ƙafafu na, gami da sake sakin wani marayan kuka mai ban tausayi ga mai sauraro, durƙusa wa yayi shima gami da kamo dukkanin damatsan hannuwa na ya miƙar dani "is ok, ya isa hakanan, ba zata mutu ba insha Allah muje in ganta" ikon Allah, maimakon ni da ke jan hannuwan waɗanda nake son su taimaka man, wannan karin wanda yake son taimaka man ɗin ne ya shiga jan hannuwa na, kaman makaho da ɗan jagora haka yake janye da hannuwa na, duk da nasan babu kyau hakan, ina jin babu daɗi a jikina duk kuwa da halin da nake ciki, Amman banyi yunƙurin janye hannun nawa ba, saboda da taimakon shi ne nake tafiya, jikina babu kwari Sam, kukan da nayi ya sanya har wata juwa-juwa nake gani, ƙala bance ba, na shiga bin shi kaman wadda bata san hanyar ba, har muka iso bakin ƙofar ɗakin da yake danƙam da ƴan kallon umma ta, dukkan su ma'aikata ne, Amman babu wadda tayi yunƙurin zuwa kusa da umman tawa ma da take yashe a tsakar ɗakin, duk sun tokare wasu daga ciki, wasu kuma daga bakin ƙofar dakin, wannan ƙiyayya har ina?


To fa! Turƙashi, Alhaji ƙarami ne riƙe da hannuwan Suhana yana janye da ita? Me hakan ke nufi? Ita har ta kai ma tsayin wadda Al'Ameen ɗin zai ruƙo ya shigo da ita har cikin ɗakin ta? Take redio masu amfani da jini suka fara naɗar ƙarya da gaskiya, darewa suka shiga yi suna bashi hanya tare da ƙoƙarin gaidashi, ko kallon inda suke baiyi ba, domin shima sun bashi matuƙar mamaki, sai dai Al'Ameen ɗin ba irin mutanen da ke shiga sabgar da babu ruwan shi bace, hannuwan nawa ya saki yayin da yake kamo na umman tawa yana mai ƙoƙarin jin pulse ɗinta.

Miƙewa yayi tare da maida kallon shi kan mama talatin dake tsaye tana recording ɗin duk wani motsi namu a ɗakin ko babu komai yau Hajiya Babba da labari kenan.

"Mama ku kamo ta a sanya ta a mota muje asibiti, bari in fiddo motar" ya faɗa cikin sanyi halin shi mai cike da miskilanci, maganar ma kaman baya son yi, sannan ya juya inda nake tsaye yana faɗin "Muje" a taƙaice, lokaci guda ya shiga takawa da niyya barin ɗakin.

Har yanzu kuma kuka nake, sai dai sauti kukan ya ragu sai dai kwalla da taƙi ta tsaya, bin shi na shiga yi a baya har zuwa parking lot da yake cike da motoci na alfarma; motar shi da tafi kowacce haɗuwa a wurin ya shiga tare da juyo ta daidai saitin da nake tsaye, sannan ya sanya hannu ta ciki ya buɗe man ƙofar gaba ta mai zaman banza, ganin da yayi ina ƙoƙarin shiga baya, banyi musu ba na shiga na zauna ina mai share kwalla ta akai akai, daidai lokacin da mama Talatu da mama uwani suka kamo umma tawa kaman matatta suka buɗe baya suka sanya ta, ya fita ya gyara masu sannan ya umarci mama Talatu da take shugaba ta shiga mu tafi tare da ita, yayin da mama uwani ta juya zuwa sashen namu tana mai taɓe bakin an mata buƙulun shiga haɗaɗɗiyar motar da take ɗauke hankalin duk wani dake zama sashen masu aikin.

Horn yayi mai gadi da fitowarshi kenan daga makewayi, ya rugo da gudu ya shiga wangale tangaman gate ɗin, lokaci guda yana mai ɗaga ma uban ɗakin nashi hannu, ( da yake Al'Ameen ɗin mutumin shi ne sosai da sosai) shima mamaki fal cikin ranshi, ganin suhan ɗin a gaban motar Alhaji ƙarami da mama Talatu a baya sai wata mata da take kwance da bai iya tantance wacece ba bayan motar kaman matatta, Allah dai yasa lafiya ya faɗa yana mai furzar da dattin asuwaki daga bakin shi sannan ya shiga rufe ƙyauren gate ɗin da take turawa da ƙarfi saboda nauyin shi.

Motar ya harba bisa titi, yayin da ya ƙara speed ɗin motar, mu da muke cikin motar gani muke tamkar baya gudu, Amman a zahiri gaskiya gudu yake wanda ya wuce ƙa'ida ma, hakan ce tasa nake ganin nawar tashi kaman in ƙwace tuƙin nake ji.

Lokaci lokaci yakan juyo ya ɗan kalle ni da nake ta sharar kwalla gami da jan majina a hankali, tin kafin mu isa asibiti yayi masu waya gashi da patien emergency, aikuwa muna isa aka turo ɗan gadon ɗaukar marasa lafiya tare da gungura ta zuwa emergency ward, ɗaga ƙafa nayi da niyyar bin bayan su suka dakatar dani ta hanyar ɗaga man hannu, wannan ne ya sanya hankali na ya ƙara tashi fiye na da baya, ganin umman tawa kaman gawa sai yanda aka yi da ita, sake durƙushe wa nayi wurin ina mai sakin wani tsumammen kuka da ya karaɗe ilahirin reception ɗin, Ya ilahi, na shiga furta wa a fili ina faɗin "Ya Rab sa'idnee ya Allah" mama Talatu bata yi yunƙurin zuwa inda nake ba, kaman yanda shi ma gogan naku bai yi yunƙurin hana ni ba, sai ma waje da ya samu ya zauna ya tsura man idanu yana mai ƙara nazari na, lokaci guda ya miƙe tare da nufi inda nake durƙushen cikin sakon tafiyar shi mai kama da ta saraki.....




*Fans Kuzo kuci cake ɗin deedat, fa u are All invited*


~_Oum-Deedat ce_~
[8/5, 8:24 PM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹*BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

*Page ~11~*

**********'*********************


Kusan yini afnan tayi mana ita dasu Ayan, tafiya tayi wajen ƙarfe shidda saura, bayan ta sake bani haƙuri, na nuna mata haba ya wuce ai babu komai.

Ya Ameen bai dawo ba har misalin ƙarfe shidda da wani abu kuma umma ta bata farfaɗo ba, hankali na ne ya tashi, office ɗin likitan na koma ya ƙara kwantar man da hankali, cewa yayi lafiya lau idan ta farka zata samu ƙarfi sosai, da wannan ne na samu naji ɗan sauƙi, babu abin da ke tadani kusa da umman tawa sai salla, ko abincin da afnan ta sanya ni inci, kaɗan na ɗan tsakura, ita ma da taga ba zan iya ci bane sai ta haƙura ta ƙyale ni.


Ƙarfe bakwai daidai ya shigo bakin shi ɗauke da siririyar sallama da ni ƙaɗai na jiyo shi, kaina da yake duƙe bisa gadon umman tawa na ɗago a hankali na ɗora idanu na akan shi, idanun mu ne suka sarƙe cikin na juna nayi sauri janye nawa, kujerar da nake zaune kai na miƙe gami da tura mashi domin ya zauna.

Dakatar dani yayi ta hanyar ɗaga man hannu da na lura sana'ar shi ce, watau maganar ma wahala take bashi, da ido nake bin shi har ya zauna kan sofar dake ɗakin ƙwara ɗaya tal doguwa 3seater, "ya jikin umman? Har yanzu bata farka ba?" na tsinkayi muryarshi yana jefo man tambaya cikin muryarshi mai daɗin saurare, ɗaga mashi kai kawai nayi, domin har ga Allah kwarjinn shi na hana ni sukuni, ƙamshin turaren shi duk yabi ya cika man hanci." OK" ya faɗa cen iya leaɓɓa, zaro wayar shi yayi ya cigaba da latsawa kaman ma baya cikin ɗakin.


Sallama aka yi, gami da shigowa baki ɗaya, Alhaji Mustapha ne da iyalanshi baki ɗaya suka iso ta ƙarƙashin jagorancin Afnan da tace ta san ɗakin, miƙewa nayi cikin hanzari tare da masu barka da zuwa na ba Alhaji Mustapha kujerar da nake zaune, Gaishe su na shiga yi su da Hajiya kubra da take tsaye gefen Alhaji cikin isa da taƙama, "lafiya" Hajiyar ta amsa mani tana mai nufar kujerar da Ya Ameen yake kai ta zauna, tana mai sakar mashi murmushi yaƙeda wani irin kallo mai cike da ma'ano ni daban daban;

Shi kau Alhajin amsawa yayi cikin sarkin fuska, yana mai tambaya ta jikin umman tawa, amsa mashi nayi ina mai ɗan murmushi iya fuska ta.

Aunty feena ce ta ja kujerar da na bama Alhaji domin ya zauna sai bai zauna ɗin ba, gaishe ta nayi itama ina mai sa hannu na ɗauki Nasreem da take saɓe a kafaɗarta, ta ko wangale man baki tana wasa da hijabin jikina, Amsawa tayi cikin sakin fuska da har saida ta bani mamaki, (Lallai mai ɗa wawa inji Hausawa) jikin umman tawa ta tambaya na amsa mata kaina duƙe ina ɗan yaƙe, Allah ya bata lafiya, da Allah ya kyauta ta shiga yi man, Ameen mun gode na shiga jerawa

Afnan da Ayan ne suka nufi wajen Yayan nasu tin shigowar su, dama ita ta hannun daman shi ce, Nihal ce ta dire wata ƙatuwar ledar da suka shigo da ita a hannu suna ta cin magani ko tanka man ba suyi ba, balle kuma in samu arziƙi tambayar jikin umman tawa,

Angode na shiga faɗi lokacin da Alhajin ya ke faɗa man su zasu wuce Allah ya bata sauƙi. Da ameen na bishi ina mai masu rakiya har bakin ƙofar motar da suka zo da ita, wata danƙareriyar mota ce duk yawan su ta kwashe su tsaf, gaskiya motar ta haɗu iya haɗuwa, Nidai ba zance ga sunan motar ba, Amman Alhajin ne da kanshi ke tuƙawa.

Hajiya Kubra ce ta kalli ɗan nata cikin wani yanayi na ɓacin rai Amman tana ƙoƙarin dannewa ne saboda kada Alhaji ya gane "Son ko zaka zo muje ne? Zamu yi ma su Hajiya siyayya ne gobe insha Allah zamu tafi cen mu duka muyi masu week end" ta faɗa tana mai gyara zama ta cikin motar,

"No mom ina da uziri yanzu gaskiya, akwai inda zanje mai muhimmanci, zamu haɗu gida wajen dinner kawai" ya faɗa a dake cikin miskalancin shi, lokaci guda yana latsa wayar shi kaman ma ba da mom ɗin tashi yake magana ba; saboda ya kula da hajiyar ko jikin umman tawa bata tambaya ba, hakan bai mashi daɗi ba kuma ya kula ko Alhajin nasu ma hankalin shi bai kai wajen ba.

"OK Al'ameen kayi ƙoƙari dai ka dawo kafin diner ɗin saboda zamu tattauna yanda tafiyar zata kaya" aAbban nashi ya faɗa cikin murmushi yana mai tada motar tashi, Saboda ya ji daɗin yanda ya iske Al'ameen ɗin a asibitn, ko babu komai ya san zasu samu kulawa da ta dace, kuma ya san tausaya war ɗanɗan nashi ga na ƙasa dashi.

Juyawa muka yi ni da Ya Ameen ɗin muka shige asibiti n akan idon Hajiya Kubran,

Cikin ɓacin rai da hajiyar ta kasa dannewa ta shiga faɗa tana faɗin "Amman Ahaji hakan ya dace ace kaman Al'ameen yana zaune suna jinyar ƴar aiki tare wannan yarinyar? Haba Alhaji, ya kake maida mu baya ne? Gaskiya Sam banji daɗi ba, iske shi fa nayi zaune hankalin shi kwance, shi ko iskar da take tasowa daga jikin su ma bai ji gurɓatacciya ce" Alhajin ne ya Dakatar da ita cikin ɗan ɓacin rai da yake ɗan taso mashi na halin Hajiyar "Ya isa Hajiya, kibar wannan maganar, wannan shine abun da ya dace kowanne shugaba yayi, na tsayawa tsayin daka ya tabbatar da lafiyar duk wani da yake aiki ƙarƙashin shi, ina Alfahri da Ameenun yana abunda yake dacewa" ƙutawa tayi cikin ɓacin rai da ƙudurce ɗaukar mataki akan al'amarin.

Afnan da take cen baya sai zumɓura baki take yi tana ƙunƙuni, Saudat ɗin ce ta hamɓare ta gami da cewa "village gal, ai dama ke kullum kina bayansu kullum" Aunty Feena ce ta dalla mata harara gami da cewa a hankali "kedai kin cika baƙin hali Saudat"

Shigarmu ɗakin yayi daidai da farfaɗowar umman tawa ta shiga motsa hannun ta gami da ƙoƙarin buɗe idanun ta.

Cikin hanzari muka isa bakin gadon a tare, gami da furta sannu umma, lafiyar ki ƙlau? "Jiddah! Jiddah, kina ina? Matso nan Suhan, hannuna na saka cikin nata ina mai murmushin farin ciki da ke taho wa da ƴar kwalla ta," Gani umma, gani kusa da ke" na shiga faɗi ina mai durƙusa wa na ranƙwafa daidai kan ta ina mai rungumo ta cikin jikina

"Hauwa'u ki yafe man kinji, na hana ki cikar burin ki, ki kira Alhaji ƙarami ki ce mashi na yarda da karatun ki, kiyi haƙuri da sannu kuma zaki san su wanene dangina, ahalina kuma, kiyi ma su Hajiya biyayya su ɗin iyayen ki ne, amanar ki na hannun su ko da bani da rai" ta ke faɗa cikin zafin ciwo idanu ta na a kulle har yanzu

Kuka na fashe dashi ina mai furta "umma ni zaki yafe mawa, nice sanadin tashin ciwon nan naki umma, kiyi haƙuri umma, na dena tambayar ki komai wallahi insha Allah"

Runtse hannuwa na tayi cikin nata tayi shiru a hankali tana mai sauke numfashi a hankali a hankali da gani bacci ne ta samu.


Kasaƙe yayi yana ta kallon uwa da ɗiyar tata cikin tausaya wa ta ɓangare guda kuma yana mai sakin Sirrin murmushi har dimple ɗinshi ya loɓa, Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da yaga umman ta samu bacci, ko ba komai zai samu sauƙi da zuciyar shi take yi mashi na kukan da afnan ɗin take yi, ya tsani kuka, ya tsani kuka masalan na mace mai rauni, yanzu zai ruɗe ya rasa inda zai sanya kanshi.

Tasowa yayi a hankali,, ya tako har zuwa gaban gadon da ya koma ya zauna bayan da yaga ɗiya da uwa suna magana cikin shauƙin so, ledar da Nihal ta ajiye ce ƙasa gaban gadon umman tawa ya shiga buɗewa, kayan ciki ya shiga fiddowa a hankali a hankali, yana jera su bisa kyakkyawa locar da take ajiye gefen gadon, kayan tea ne, sai ruwan gora, da plax sai mug na shan tea, sai kayan marmari da su cake da sauran kayan ciye ciye da marar lafiyar zai iya buƙata.

Da gani dai wannan siyayyar ta abban shi ce, dan ko kusa ya san halin mom ɗin tashi ba zata iya tsayawa yima ƴan aiki soyayya ba.

Sai da ya tabbatar da ba zasu buƙaci komai ba sannan yayi mata sallama a gajarce ya fice yana mai ja masu ƙofar, da idanu na bishi har ya wuce, tabɗi Ya Ameen Matarka zata sha miskilanci na raya a rai na ina mai miƙewa domin komawa inda ya tashi dan in samu in miƙe ƙafa ta, da kallo na shiga bin wajen da ya tashin, kaman yana wajen zaune, ƙamshin turaren shi yana nan liƙe kaman nan ya fesa shi, ajiyar zuciya na shiga sauke wa a hankali a hankali ina mai furta Alhamdulillahi!


******************************

Bai shiga babban part ɗin ba saida ya koma nashi yayi wanka ya kintsa sannan ya nufi part ɗin hajiyar cikin takon shi kaman na saraki; Sallama yayi ya shiga, duk sun hallara a dining table suna cin abincin da sai dai aka yi ma mama Talatu umarni da ta girka shi ita da mama uwani, kujera ya ja guda ɗaya ya zauna saitin abban nashi, Mug ya ɗauka gami da haɗa cofee, domin bai jin zai iya cin komai a wajen, tsaftar umman Suhan ɗin ce kawai ya yarda da ita.

A hankali ya ke shan cofee ɗin yayin da Alhaji yayi gyaran murya duk suka maida hankali su akan shi, " Gobe idan Allah ya kai mu zamu tafi kankiya, kaman yanda muka saba in mun yi haɗuwa irin wannan, Hajiya ki rubuta list ɗin abubuwan da za'a buƙata da wanda za'a kai ma su Baba ɗin, sannan ku Saudat da Nihal sanin kanku ne cewa idan muka je sai anyi maku maganar fidda mazaje, idan kuna da tsayayyu ku tura su cen kankiya su gaida kakannin naku kafin mu taho, zan yi ma yaya Auwalu magana sai yazo su gaishe su tare, sannan kai kuma Al'ameen idan an amshi list ɗin ka tabbatar ka haɗa komai cikin daren nan dan ina kyautata zaton da safe zamu wuce don na riga nasa anyi booking flight. Ina fatan babu mai magana ko?" ya faɗa yana mai maida kallon shi kan Hajiya Kubran da take zaune tana ta cika tana batsewa,"

Alhaji shi Al'ameen ɗin baka ce ya fidda mata ba, don na gaji da ganin shi zaune haka nan, tsararrakin shi har sun yi aure, wasu ma harda ƴaƴa, don haka shima yayi gaggawa fidda wadda yake so, in mun duba munga cancantar ta, sai a haɗa bikin da na su Saudat kawai"

Ɗan murmushi Alhajin yayi yana mai maida kallon shi kan Al'ameen ɗin da ya kafe mom ɗin tashi da idanu yana ɗan murmusawa, shi da ya gano ta, watau tana gudun ya so yarinyar cen dake asibiti tare da maman ta, humm Hajiya kenan, yana fatan Allah ya shirya da mom ɗin tashi ta gane annabi ya faku, koma dai minene shi dai ai ba za'ayi mashi auren dole ba, ba kuma za'a ƙayyade mashi lokacin auren shi ba, duk tsiya dai sai ya samu wadda tayi mashi, kuma har yanzu baya tinanin ya dace, duk cikin ƴan matan da suke cewa suna so shi, shi fa ba suyi mashi ba, bai yarda da natsuwa da inganci shi ba, don duk irin ƴaƴan hamshaƙan masu kuɗi ne, masu ɗabi'a irin ta mom ɗin tashi watau wulaƙanta na ƙasa dasu, Sam basu san babu ba basu kuma san daraja ɗan adam ba, abin da umman tashi bata sani ba shine, duk wacce ya auro cikin su ya kawo mata ba zasu taɓa daidaitawa ba, saboda halin su ɗaya ne, isa, taƙama, izza da son mulki, wa zai bi wani? Murmushi ya ƙara saki daidai lokacin da yaji Dad ɗin nashi na faɗin


"Tau kaji fa Son, Mom ɗin ka na nuƙatar suruka" "Amman sai inga ai shi namiji ne ya kwantar da hankalin shi ya

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment