Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi amfani wajen buɗe ɗakin da haska shi, duk da ba wani haske ne ya wadata ba, ga dukkan amu ma dai basa da wata fitila da tafi wannan Aci balbal ɗin.

Kayanmu muka fara kwasa muna kaiwa zuwa cikin ɗakin da sai mun duƙa zamu iya shiga, masalan ma ni da nake da ɗan tsawo.

Har yanzu dai bata tanka mana ba, da gani dai a tsorace take damu.

Ɗakin kam yayi ƙura, a haka ta koma ta ɗauko mana tsintsiya ta kakkaɓe mana muna tsaye gefe ni da ummata da har yanzu bata wani kula ni.

Ƴar yalolon tabarmar kaba ce shimfiɗe a ɗakin dagani dai ana nufin a bisa ita zamu kwana, gashi ba wani girman kirki ne da ita ba, sai ɗan yalolon filon da ta shigo mana dashi guda ɗaya a hannun ta riƙe da ƙwarya mai kyau da fura ciki wadda tasha nono kindirmo.

Zama mukayi muna bismilla, cikin mu ma babu wanda yabi ta kan furar, daf da zata fita ne ummata tace mata "Hajjo muna so muyi salla ne"

Da to tabi umman tawa tana fita, bata daɗe ba ta miƙo mana ƙatuwar buta ta tasa cike da ruwa, amsa umman tawa tayi tana mai ficewa daga ɗakin.

Zurut na tashi ina mai biye bayan ta, domin Nidai harga Allah tsoro nake ji, bata ko kalle ni ba, da yake ta san kan yanda gidan yake bayan ɗakin kawai ta nufa ta kamo ruwa gami da fitowa ta ɗaura Alwala, bayan ta gama ne ta miƙa man da niyyar nima inyi.

Amsa nayi ina mai cewa "Umma Don Allah ki jiran in gama, wallahi tsoro nakeji" bata ceman ƙala ba sai ma ja da tayi gefe ta tsaya tana mai bin ko ina na gidan da kallo da dukkan alamu dai tana fahimtar ba'a samu kowanne sauyi ba acikin gidan illa ma ƙara ruɓewa da gidan yayi.

Koda na shiga bayin, rasa inda zan zuƙunna inyi fitsarin nayi, domin ko ina ƙasa ce kwance, a haka dai na samu na raɓa nahau wani shimfiɗaɗɗen dutsi mai ɗan tudu da aga alamar wanda ake zama ne bisa in za'ayi wanka.

A kanshi na hau na tsula fitsari na, na gama na fito tare da ɗaura Alwalar sannan muka ranka ya zuwa cikin ɗakin.

Har muka gama salla babu wanda ya kuma shigowa, ganin hakan da mukayi ne ya sanya muka gane ba zasu dawo ba, sakaya ɗakin mukayi saboda sauro gashi babu maganin sauro, mu kuma namu dake cikin kaya yana cen ƙasa bama mu san ta inda zamu fara neman shi ba.

Hakanan dai muke zaune, cikin mu babu wanda yake da niyyar kwanciya, ganin hakane umman tawa ta miƙe gami da zaro wani zaninta cikin Ghana must Go ɗin tamu ta shinfiɗa mani gami da cewa idan ba zan sha furar ba in kwanta in huta.

Allah sarki mahaifiya, duk duniya babu yake, haka nan kasa kwanciya, itama ta kasa kwanciya, tana ta ƙare ma ɗakin kallo.

Cen kaman an buɗe mata baki an zaro maganar Naji tace


" *Anan fa aka Haifeki* "

Ai bansan na zabura ba na tashi tsaye, har saida Naji tace "to miye na tashi tsaye? Ni kar ku faɗo mani"

Sannan ne fa na koma na zauna, tinani fal cikin raina da tarin tambayoyi.

Ban ce mata ƙala ba, sanin halin ta da nayi, yanzu ina iya tambayar ta cibi ya zama ƙari, koma ta fasa faɗa man Abunda tayi niyya.

An kusa awa bata ƙara ceman komai ba, sai nice nayi shahadar fitowa in mata maganar karatuna ganin mun samu lokaci mu da ita.

"Umma ya maganar makaranta ta? Ki taimaka mani umma kada wannan damar ta kucce mani, bani da kowa sai Allah sai kuma ke, wannan karatun da zanyi zai taimaki Rayuwar mu ya tallamu ta ni dake baki ɗaya"

Shiru tayi tana mai nazarn kalaman nawa, cikin tausaya wa irin na uwa ta buɗe bakin ta ta shiga cewa


"Mamana, nice nan na yarda kiyi karatu, saidai kuma yanzu bana buƙatar karatun ki a waccen makarantar da suka sanya ki, dukkan Abunda ya shafe su ma bana buƙatar shi atare damu, kuma inaso kiyi mani Alfarma da alƙawalin cewa zaki manta dasu duk kansu, kuma ki binne labarin su da babinsu a Rayuwar ki"

Gabana ne ya tsananta bugu, me umma ke nufi, Amman dai koma minene tinda Naji tace zata barni inyi, ai ina tinanin zai zo mani da sauƙi

"To umma hidimar karatun fa waye zai yi mani? Kada ki manta fa, nan ba aiki mukeyi ba, ba kuma albashi ake bamu ba, umma Meyasa kika zaɓi mu baro cen gidan dukkan irin muzguna mana da akeyi, kika zaɓi muzo nan muyi Rayuwar mu?"

Na faɗa ina mai saddar da kaina ƙasa domin bansan da irin ɗauka da fassarar da zata yi ma maganar ba.

" Hauwa'u ke yarinya ce har yanzu, ba zaki gane ba, ba zaki fahimta ba, Hajiya Kubra bata da zuciyar imani, ta sanya su Hajiya Sa'a suyi dukkan yanda zasuyi mubar gidan nan, har Rayuwar mu ma zata iya Sanyawa a hallaka saboda tana tunanin ke ɗinnan zaki mallake mata yaro ne, a yayin da take kallon shi ɗin yafi ƙarfin ki ba sa'an yinki bane, ni kuma na kwammace mu bar gidan tin kafin mu nemi rasa Rayuwar mu a karo na barkatai, ki bar maganar su, dasu da Abunda ya shafe su gabaki ɗaya yanzu bana son maganar su, Alkhairin da Alhaji da Shi Ameenullahin yayi mana Mungode Allah ya saka, Amman bana kyautata zaton akwai Abunda zai ƙara haɗa mu dasu"

Tinda ta fara magana bata tsaya ba, haka kuma bani take kallo ba, hasali ma idanun ta a kulle suke gam, nikau da kwalla take shatata da zuraro mani sai faman ajiyar zuciya nake sauke wa,

Ban aune ba naji ta sake cewa

"Karatun ki Allah ne zai yi mana, Allah ne zai bamu iko da Abunda zakiyi karatun dashi, Mamana inaso ƙibar sanya ma ranki cewa dole sai dasu ne zamu iya, inaso ki sani su ɗin da Allah ya basu kuma ba zai manta damu ba, kiyi ta addu'a komai zai zo da sauƙi insha Allah, wannan halin da muke ciki zai zama tarihi da izinin wanda ya halicce mu"

"Ameen Umma"

Shi kaɗai ne Abunda bakina ya samu ya iya furta wa, duk kuwa da tarin kaman da suke cikin shi.

Kusan a haka muka kwana zaune, kowa da Abunda yake saƙawa, saidai daf da asuba ne wani nannauyan barci ya kwashe ni, cike da mafarkai masu ban tsoro kuma duk Al'ameen ne nake hangowa a ciki, koda na tashi na tadda har gari ya fara wayewa, sanin da ummata tayi cewa baccin na gajiya ne ya sanya bata tadani ba, ta bari idan na tashi nayi sallar.


****************** To kusan muce yanda su Suhan ɗin suka kwana zaune cikin ƙututun ɗaki, haka suma su Umman suka kwana, duk da ga gado ga Ac Amman hakan bisa ɗaya daga cikin su ya runtsa ba, gashi kuma Al'ameen ɗin fa har yanzu bai motsa ba, haka umma ta kwana a tsaye jikin glass, Allah ya isa dai Suhan tasha ta, domin ita a gani ta duk itace sila ko ince sanadin da ya sanya Al'ameen ɗin yabar ƙasar tashi, gashi yazo ya haɗu da mahassada masu neman ganin bayan shi, ai gara ma da ta tafi cen daga cen ayi cen insha Allahu ba dai yaron nata da wannan matsiyaciyar yarinyar ba ƴar matsiyata.

Saidai likitocibsu shiga su dudduba shi, gami da gyara mashi kwanciya su fita, Abunda ya ƙara ɗaga hankalin su shine ganin da sukayi wasu gungun likitocin kusan su biyar sun rugu a kanshi, dagani ma manyan likitocin ne da ba'a asibitin suke aiki ba kiran su aka yi.

Bayan sun gama ne suka fito su duka, fuskar su babu walwala suka ce su Mom ɗin su biyo bayan su zuwa office ɗin.

Hajiya Kubra ce da bilal ɗin suka bisu, yayin da aka bar abie nan zaune yana hango Al'ameen ɗin.

Bayanin komai sukayi masu, ai tini Hajiya Kubra ta rushe da kuka, tana cewa "wai ina Alhaji ne? Yazo yaji, yazo yaga yaron nan kada ya mutu, me ke damun Al'ameen haka da har ciwon zuciya ya kama shi har ta kumbura? Tunanin me yake yi haka? Me ya nema ya rasa? Bilal kira man alhajin kace don Allah yazo yaji Abunda likitocin nan ke faɗi.

Ai cikin hanzari shima jikin shi na rawa ya latsa number ɗin Alhajin, koda ya gaya mashi shima salati ya sanya yana mai cewa yana nan tahowa yau-yau ɗin nan kuwa insha Allahu, zai bar dukkanin Abunda yake yi yazo ya iske su a american.

Faɗa ma Mom ɗin yayi yanda sukayi da alhajin, taɓe baki tayi cikin kuka take faɗin


"ai ga irin ta nan, yaushe za'a ce maka yaron ka yana kwance rai hannun Allah kace sai ka tsaya neman wasu matsiyata marasa galihu cen, Rayuwar yaron namu batafi rayuwar su ba su duka?"

Runtse idanu bilal ɗin kawai yayi yana mai girgiza kai ya tashi ya fice daga office ɗin ma baki ɗaya, kalaman na hajiya kubra sun rasa shi, sun girgiza shi matuƙa, ko wannan kaɗai ya isa ya sanya Al'ameen ɗin ciwon zuciya, samun wannan irin uwa haka ai ba abun daɗin ne ba. Ganin yanda ranshi ma ya ɓaci ya sanya shi fita cen harabr asibitin ƙarƙashin wata bishiyar umbrella ya zauna yana mai nanata kalaman hajiyar a zuciya.



********************

Koko da ƙosai aka miƙo mana masu zafi, bamuyi ƙwaron baki ba muka sha, duk da ba wani sugan kirki ne a ciki ba, har yanzu dai tinda malam da Hajjo ɗin suka leƙo muka gaisa bamu sake ganin kowa ba, sai cen wajen ƙarfe goma ne a kintata ta, saboda waya ta ta ɗauke ba chaji, gashi kuma banga alamun wuta ba a ɗan tsukukun ƙauyen.

Ruwan wanka Hajjo ɗin tace in fito in ɗiba a cikin waccen tukunyar, irin ƙatuwar tukunyar nan ce ta ƙasa, hakan yasa na fiddo bokitin robar mu na wanka da soso da sabulu, sai dai fa da naje ɗibar ruwan na kai minti goma ina kallon ruwan nazari nake yi ta yaya ma mai rai zai iya wanka da waɗannan ruwan?

Hajjo da take tsaye daga cen ƙofar ɗakin ta ce ta ce mani. "Ki ɗiba mana, ko ba yanzu zakiyi wankan ba?"

Ban ƙasa a guiwa ba wajen juyawa nace mata "Mama waɗannan sune ruwan wankan?"

"Yo Eah mana sune, dasu mukeyin komai a nan ƙauyen mu, ko rijiya bamu da ita, sai rafi shima safko nayi naje na ɗebo, har girki dashi mukeyi, ke ko kokon da kika sha yau dashi na dama, ƙosan ne kawai aka siyo a cen bayan layi"

Baya naja da dukkanin sauri da ƙarfi na ina mai dafe ƙirji, cen kuma sai ga amai kwarara ya taho man, duƙawa nayi da sauri kada in ɓata jikina, ban tashi ba saida na amaye dukkanin abincin dake cikina, ɗan kokon da ƙosan kuwa sun dame babu kyau gani.

Nasha Wahala domin ni da kaina na dinga ƙaƙalo shi, bansan sanda hawayen wahala da tausayn kaina suka wanke mani fuska ba, ummata dake tsaye bakin ƙofa jin maganar mu da hajjon ne ya sanya ta fitowa.

A hankali ta tako har inda nake durƙushe ina mai idasa ƙaƙalo sauran kokon

"Kinga Mamana, dole fa zakiyi haƙuri, haka Rayuwar su take ciki anan ƙauyen, gwamnati ma bata san da zaman su ba duk tsawon wannan lokacin, in ma ta sani to babu Abunda take aiwatar masu, illa iyaka idan zaɓe ya tashi kiga annkawo rimfuna da sabullai ana raba masu su zaɓi wanda ya basu. Amman ruwa da wuta kam saidai in kin bar garin nan, ko ruwan rijiya basu dashi saboda suna kan tudu ne, ba'a samun damshi a ƙasan, haƙuri zakiyi ki daure har Allah ya iyakance, domin ko ɗazu ma dasu mukayi Alwalar salla, yanzun ma dasu zaki ɗauraye bakinki ki tashi hakanan ki ɗiba kiyi wankan"

Bansan lokacin da na kalle ta ba kwalla na zuraro mani, raina fa duk a dagule yake, mamadin inyi shiru sai a sake ɓarkewa da kuka da nayi, ashe cen inda muka baro muna cikin rahma ne, ashe bawa ya gode ma Allah a duk inda ya samu kanshi, hakan ma wata baiwar ce? Me yasa ya ummata jawo mu nan wurin? Me hakan ke nufi da rabo mu cikin rufin asirin mu? Duk da ada kallon muna cikin wahala mukeyi?

Sake dafa kfaɗa ta tayi cikin tausaya wa irin ta uwa, sannan ta shiga goge man hawayen tana mai cewa kinga maza ki ɗibi ruwa kije kiyi wanka kizo ki tafi makarantar taku ki gano ya zakuyi?"

Dasauri na kalle ta," Umma nan fa bansan sunan garin da muke ciki ba, bansan a wane state ma muke ba tukunna, tayaya ma zan gano hanyar da zata fidda ni daga nan surƙuƙin?

"Zaki ita Suhan, zaki iya, ke ɗin mai ƙoƙari ce akan Abunda kike so, akwai masu babura acen ƴar yara da zaki hau su fidda ki babban titi, sannan nan muna ƙauyen sunkui kenan dake cikin jihar Jigawa. (Na sanya sunan littafin ne gudun kada wasu suce na faɗo sunan ƙauyen su na aibata shi).

Ɗan murmushi nayi ina mai matsawa na ɗauko moɗar gami da zuba ruwan a cikin bokitin na wanke wurin duk da ƙasa ce, sannan na ɗauraye bakina ina yi ina runtse idanuna jin ruwan a bakina.

Sannan na zuba ruwan na shiga bayin, aiko bisa ɗan dutsen nan na haye nayi wankan, sannan har na gama ban miƙe ba, jikina kam sai ƙaiƙayi nake yi, ina zuwa ɗakin na tadda umma ta fiddo mani mantheletor na zafi wai in shafe dukkan jikina.

Haka kuwa aka yi ina shafawa Naji sauƙin ƙaiƙayin, haka umman tawa ta fice itama domin yin wankan, ina gamawa na sanya kaya na gami da shan nutri milk ɗin da umman ta ajiye mani da ragowar bredin jiya, aiko naji dam, duk da har yanzu zuciya ta tashi take yi kaman zan sake wani aman.

Saida nabari umman tawa ta gama wankan ne ta shirya ta sanya kaya, sannan nace mata zan wuce, kuɗi ta ɗauko masu ƴar dama ta bani tana mai cewa Allah ya kiyaye hanya, duk runtsi kada in bari dare yayi mani a hanya batare da na dawo ba, in kuma har ban gama ba da wuri in kwana a hostel ɗin da aka riga aka bamu Alabasshi gobe in yo sauko in dawo.

Da addu'a ta bini har ƙofar ɗakin, saida nayi ma Hajjo sallama da take zaune tana tsintar shinkafa ƴar hausa, itama cikin ƴar fara'a ta amsa mani, sannan na tambayeta kwatancen inda zai hau babur ɗin.

Wani yaro ta ƙwala ma kira da yake cen waje yana wasan ƙasa shi da ƙanen shi, dukkanin yaran jikin su gaja gaja yake da datti ga majina a hancin shi, saurin kauda kaina nayi, ina jin zuciya ta na sake tashi.

"Isa maza je ka raka wannan yayar taka ƴar yara ta hau babur ya fidda ta a hanya" da to ya bita ya ruga da gudu yana mai kaɗa ƴar tayar shi, sallama nayi masu nabi bayan yaron, yayin da umman tawa ta kai zaune bisa ƴar tabarmar kabar dake shimfiɗe ƙasa tana mai cewa "Hajjo kawo tsintar mana in tayaki"

Ba musu ta miƙa mata, sunayi suna cigaba da ƴar firar su ta yaushe gami, dagani dai yanzu ta ɗan saki jiki da umman tawa, jira kawai take yi mijin nata ya dawo daga cin kasuwa da yayi sammakon tafiya suji ta bakin Maryamar.

Nikau bamuyi wata tafiya mai nisa ba muka hango ƴar yarar, masu babur ukku ne rak a wurin kwance bisa machinan su suna ta fira, hango mu da sukayi ne ya sanya su zabura suka bukako mashin ɗin zuwa gabanmu suna cewa "Hajiya Tafiya ne?"

Ganin ɗaya daga cikin su ya fisu zaƙalƙalewa ya sanya sauran biyun haƙura suka koma suna ƙunƙuni, nikau ya juya man nahau ina mai cewa "bakin babban titi zaka fidda ni inda zan samu mota"

"To hajiya saidai fa akwai nisa, gashi hanyar bata da kyau yashi yayi yawa, sai kin riƙe mashin ɗin sosai"

Aiko na kama mashin ɗin na maƙalƙale ina mai juyawa nace ma yaron ya koma gida sai na dawo nagode

Yaron ya juya da gudu ba tare da ya jira wani ihisani daga gareni ba, saɓaninnyaran mu na yanzu ƴan cikin birni ko mun ƙanƙantar Abunda sukayi maki sai suyi maki ƙerere suna jiran ki basu kuɗi, Allah shi kyauta mana da wannan zamani.

Hanya muka ɗauka ɗoɗar, kusan tafiyar awa guda mukayi sannan muka fito bakin hanya, titi ne samɓal, nan na sauka ina mai ce mashi nawa ne?

"Jikka biyu" ya faɗa yana mai ɗaure fuska, banyi musu ba saidai na tambaye shi ƙarin bayani nawa ne jikka biyun da Hausa?

"To ai malama hausar nayi maki, saidai in baki gane ba sai ince ɗari huɗu kenan"

To nace mashi gami da ɗauko ɗari biyar na bashi, saidai bayada ko sisi a aljihun, cewa nayi ya bar shi kawai, godiya ya shiga zabga mani yana cewa "Allah ya kiyaye a dawo lafiya, ai bana tafi ba banga shigar ki mota ba hajiya"

Muna tsaye kuwa sai ga mota golf ta shararo da gudun tsiya, tsaida mani yayi na shiga ina faɗin sunan garin da zani.

Na kuwa ci sa'a suma cen suka nufa, mai mashin ɗinnan yana ta ɗaga mana hannu har muka ɓace ma ganin shi sannan ya juya, ga dukkan alamu dai yaji daɗin kuɗin nan da ya samu daga gareni.


*_Allah ka yafe mana kura kuranmu, ya sanya mu gama da duniya da iyayen mu lafiya Ameen_*



~Oum-Deedat ce~
[9/21, 12:27 PM] Aminatu Hassan: https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~33~*


°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°


Ƙarfe uku daidai muka isa garin na Zaria, Nidai bana ce ga sunan garuruwan da muke ta wucewa ba, har Allah yayi mana isowa.

Muna sauka ne na gane inda zan dosa, mai a daidaita sahu na tare har zuwa cikin makarantar ina saɓe da ƴar jikka ta.

Bayan na sallame shi ne kai tsaye na wuce zuwa admin block na foculty ɗinmu, saidai abun da har yanzu yake ɗaure mani kai tin shigowa ta makarantar, ƴan tsirarun mutane ne suke ta kai komo, wasunsu kuma a zazzaune.

Saida na isa ne zuwa Office ɗin HOD ɗin namu ne na ganshi a kulle, kaina ya ƙara kulle wa, dole na juyo zuwa inda na hango wasu zaune ƙarƙashin bishiya, maza da mata ne zaune abun su suna ta fira da raha, duk da sun bani mamaki yanda suka saki jiki da waɗanda ba jinsin su ba, sallama nayi masu gami da tambayar su ko lafiya makarantar ba kowa har malaman?

Ƴar dariya suka saki, lokaci guda ɗaya daga cikin su ya fara bani amsa.

"Haba baiwar Allah, yanzu ke fisabilillahi duk yajin aikin da aka shiga baki sani ba? Hala ke sabuwar zuwa ce?"

Ya jefa man tambaya a ƙarshen maganar tashi, ban samu damar bashi amsa ba, saboda yanda Naji jikina yayi sanyi ko ƙafa ta ma nema take ta gaza ɗauka ta, gyaɗa mashi kai kawai na samu damar yi, sannan nace masu nagode.

Juyawa nayi a matuƙar gajiye, ga yunwa ga tashin hankalin komawa gida a yanzu, ga tashin hankalin ban samu Abunda nake so ba, ga kuma waya ta babu chagi.

A haka har na fito bakin gate duk tsawon tafiyar nan, na matuƙar galabaita jikina har ƴar kyarma yake yi.

Cen nesa kaɗan na hango mai ɗan shago yana saida provision da su lemuna, sai dougnut ɗana hango cikin bokiti. Da ɗan sauri na na isa ga inda yake zaune na fiddo kuɗi gami da cewa "A bani a haɗa mani da lemo."

Alfarma na roƙa wurin da yake zaune, akan ya tsira mani chaji na wayar ta ɗan kawo, duk da ba wai don in kira wani ba, aiko sai gashi kafin in gama cin dougnut ɗin da na shige hijab ina ta faman turawa, wayar ta samu kusan 20% da yake chargre ɗin tana da kyau.

Godiya nayi mashi gami da karɓa na wuce, shawara kawai nake yi ta yanda zan nemi komawa a yau ɗinnan gashi har la'asar tayi, kuma ban hango wurin da zanyi salla ba ma, dole a haka na nufi tasha, na tadda mota na lodi, a haka nima nabi su wurin zaman jiran sauran passingers ɗin bayan na gaya masu inda zani.

Saida dreban yace mani "Amman kinsan inda zaki cen cikin lungu ne ko? Saboda dole a hanya zamu sauke ki"

Ce mashi nayi na sani, a haka har motar ta cika muka ɗauki hanyar komawa gida.


***********************



Alhaji Mustapha sai cikin dare ya isa, har yanzu dai babu wani cigaba, duk da Bilal ya fita yayo masu take away ɗin abunda zasu ci, har yanzu babu wanda ya iya cin wani abu, saidai ruwa kawai da hajiya kubran ke kurɓa, idanun ta sunyi mata luhu luhu,ko buɗe su bata iya yi, ya zuwa yanzu kowa dake nigerian ya san da rashin lafiyar ta Al'ameen.

Isar shi ce tayi daidai da isar su Aunty Feener da Afnan, aiko suka dasa wani sabon kukan, duk da ba'a bari a shiga inda yake saidai suna hango shi ta cikin glass, duk da yanda Alhajn ke lallashin su Akan suyi shiru, kasawa sukayi, gani suke kaman sunyi bankwana da ɗan uwan nasu ne.

Tini dai Alhaji Mustaphan ya nemi da a cenza mashi asibiti mai zaman kanta inda mafi ƙwarewar likitocin suke, ba musu kasancewar sunsan yadda su Alhajn suke a ƙasar ta amurkan.

Asibiti mai kyau da tsaruwa aka maida shi, nan ɗinma kimlace shi aka sake yi wuri na musamman, saidai yanzu kam basa iya hango ta inda ma yake kwance, har yanzu bai san wake kanshi ba, hakan ya ƙara tada hankalin Hajiyna, gani take yi kaman za'a fito ace mata ya mutu, shi kau Alhaji Mustapha bai ma bi ta kan hajiyar ba, saidai afnan da take maƙalƙale dashi tana kuka, sai faman lallashinta yake yi.

Da yake an basu ɗaki na musamman akace suyi amfani dashi, duk da asibitn ba'a zaman jinya, saidai Alfarmar Alhaji Mustaphan da ya daɗe cikin ƙasar ya sanya aka basu, a haka suka kwana zaune, Bilal ne kawai ya tafi gida ganin Alhajn ya iso ga kuma su Aunty Feenar.

Tin da safe washegari sai ga Saudat da Nihal gabaki ɗayansu da mazajen su, ai fa nan sani sabon babin kukan ya buɗe, Alhaji Mustaphan har ya gaji da lallashinsu ya sanya masu idanu.

Ya san dole suyi kuka, Al'ameen ɗin ɗan uwa ne nagari, duk da kasancewar shi ba mai yawan fara'a ba ko shiga hidimar mutun, shi ɗin mai tausayi ne, mai jin ƙan na ƙasa dashi ne. Ana haka sai ga kira daga mataimakin shugaban ƙasa da sauran sarakunan sun zo ganin Al'ameen ɗin.

Kusan

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment