Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gari aka ɗaura aure muka gane kan yaron nan, gashi ya ɗaga maki hankali kema duk kin ruɗe, mai kyakkyawar fahimta dole ya gane bakya cikin natsuwa.

Hajiya Kubra ce ta sake nisawa, cikin wata irin jin kunya, da zamu ce bata taɓa jin irin ta ba.

"Ni fa ban san abun nan haka yake ba, duk son zuciya ta ne yaja mani, saboda bana so Sam ace ana yayata ni a cikin ƙawaye cewa yaro na ya auri ƴar aikin mu, shine kawai dalili, Amman ko ita Maryama ina cike da kunya da nadamar duk ranar da zata dawo gidan nan, domin a rayuwa na cutar dasu, na wulaƙanta su, kuma wlh duk ina sane, saboda son zuciya ta, Amman yanzu ba wannan ba, duk ma Abunda zai faru daga baya ne. Ku bani shawarar ya zanyi da Al'ameen, kun sanshi sarai wani irin murɗaɗɗen mutum ne, shine ma dalili na na cewa yazo ya same ni nan. Kunga kuma har yanzu bai kira ba.

"Ni fa dama ina mamakin yanda kika ɗauki karan tsana kika ɗora ma matar na da yarinyar tata, naga ba sashen kike zuwa ba, Amman duk wani motsin su akan idon ki yake, nayi mamaki da bakiyi ma sauran ma'aikatan sai su..." Hajiya Sa'a ta faɗa itama

"Sa'a kema dai kin faɗa, hakanan na ji na tsane su wlh, kuma tabbas bana zuwa sashen masu aiki, saidai ina da masu kawo mani dukkanin rahoto, Talatu da Sayde, saidai Talatu ita ce kan gaba, saboda ita ce shugaba, ban sani bama dukkanin abubuwan da take zuwa tana faɗa man ɗin, ko don inji na tsane su ne? Mu bar wannan maganar ba lokacin ta bane Sa'a ku bani shawara, duk yanda za'ayi ina so yaron nan ya tara da yarinyar nan cikin daren nan, ta yanda komai zia warware cikin sauƙi, daga yanzu ba zan kuma cutar Suhan ba, saboda nasan idan nayi haka ko ma sarautar ma ba zata ƙyale ni ba. Nayi nadama da wuri Laila ku bani shawara."

" Al'ameen da take tsaye ta bayan su, duk Abunda suke faɗa ya gama ji, a hankali a hankali ya shiga takawa cikin wani irin rawar jiki, wurin yake ƙoƙarin bari, ko don kada ya faɗi a wajen.

Baisan lokacin da ya kai kanshi bakin mota ba. Jikin shi kyarma kawai yake yi, tuni fuskar tashi ta rine da kwanciyar jini, haka idanun shi, baisan halin da yake ciki ba, a haka ya shiga jan motar cikin tuƙin ganganci. Har yanzu zuciyar shi ta kasa gasgata Abunda yaji, to da wani ne yazo ya faɗa mashi wannan maganar, Allah ne kaɗai zai iya raba su dashi a ranar nan.

Haka ya shiga cikin gidan yana mai haɗa hanya, kaman wanda tasha giya kwalba goma.

Da sauri Bilal ya miƙe yana mai taro shi suka zube kan kujera.

"Friend gaya mani me ya faru kuma? Kaje gidan ne? Me ya faru ko in kira Mom ɗin?"

Bai iya cewa ƙala ba, sai wasu irin hawaye masu ɗumi dake shatata a idanun nashi.

Dakatar da Bilal yayi da hannu, da ya zaro waya yana mai ƙoƙarin kiran Mom.

*"Dont call her"*

Ya faɗa a tsawace, wani irin miyau na feshi daga bakin shi, mai kumfa kumfa.

Ruɗewa Bilal & in yayi, zai iya cewa bai taɓa ganin abokin nashi cikin wannan halin ba.

To me yake faruwa ne?

"To ka faɗ aman Friend lafiya? Ka tada mani hankali fa, idan ba zaka faɗa ba, i'll call her defenetly"

Shima ya faɗa cikin fushi, kukan da yaga Al'ameen ɗin nayi ya ɗaga mashi hankali.

Tun hawaye na zuba, har ya fara sakin sauti, yana mai dafe da kanshi da yake ji kaman zai tsage mashi biyu.

Da dukkanin hannuwan shi yayi amfani wajen kamo Al'ameen ɗin da ya kuma sake miƙewa ya nufi zuwa bedroom ɗin.

Fizgewa yayi, yana mai wucewa yana haɗa hanya.

Baiyi fushi ba, a zafafe shima ya miƙe ya bishi

"Please Friend kada ka ɓata mana wannan ranar, ka sanar dani me ke faruwa don Allah, tin kafin nima ka sanya ni kukan, ba tare da sanin me ke faruwa ba"

Ya faɗa yana mai zaunawa shima Ƙasan carpet, kaman yanda yaga Al'ameen ɗin yayi.

A hankali ya fara rage sautin kukan nashi.

"Bilal dukkan abunda ke faruwa dani Mom ce sila, Mom tana da masani ya, Mom ce dalilin tsanar Suhan da nayi, Mom ce da ƙawayen ta, Dalilin barin Su Suhan gidan namu Wancen karon, Mom ta azabar da su Suhan da Umma, a lokacin zaman su gidan namu, duk ba tare da ni ko Dad mun sani ba, Bilal ka faɗa man wace irin uwa ce Allah ya bani? Wane irin hali Mom ta jefa kanta na bin bokaye da sunan malamai? Me Mom zata tsinta a yin hakan da tayi? Me Mom ta nema ta rasa a rayuwar ta? Me su Suhan da Umman ta suka tsare ma Mom? Sai gashi yau da bakin ta duk tana faɗar waɗannan abubuwan. Da wanne ido zan kalli Suhan da Umman ta duk ranar da suka ji hakan? Shin bata tunanin su samu saɓani da ƙawayen nata su fita waje su tona mata asiri.? Bilal ka faɗa mani ya zanyi? Bilal ba abunda na nema na rasa wanda Allah bai mallaka mani ba, Amman ya jarabce ni da samun Uwa mai halin Mom. Bilal ina nadamar tsanar da na nuna ma Suhan a yau. Duk da ba wai ina jin son ta ya dawo mani bane ɗari bisa ɗari. Dole in danne zuciya ta, Bilal ka bani shawar wai ya zanyi ne?"

Ya faɗa yana mai sake sakin wnai kukan.

Shi kanshi Bilal idanun nashi sun kaɗa sunyi jawur. Dole dama zuciyar shi na raya mashi cewa harda sa hannun Mom a duk Abunda take faruwa, ya sakankance da lamarin Mom tin wata rana da ya same ta tana waya akan irin hakan, saidai bai fahimci komai ba, haka ya juya ya fita, ba tare da ya bata damar ganin shi ba, balle ta kawo ma ranta cewa ko yaji Abunda take faɗa a wayar. To ya zasuyi, uwa uwa ce, dole su jure, dole su danne, saidai suna gudun ranar jin kunya, kuma sun sani dole ne tana nan zuwa.

Miƙewa Bilal yayi ya nufi fridge yana mai ɗauko gorar ruwa ya sake dawowa, inda Al'ameen ɗin yake zaune.

Miƙa mashi yayi, bai wata wata ba ya sanya hannu ya amsa, yana mai ɓalle murfin ya sake kafa kai.

Cikin matuƙar rausayawa yake kallon abokin nashi, ikon Allah kenan, yanzu dai gashi babu Abunda Allah bai mallaka ma Al'ameen ɗin ba kaman yanda yace kuɗi, gidaje, motoci, kmafanoni, ilimi, kyau, asali, nasaba, farin jini da sarauta, Amman shi kuma ta nan tashi jarabawar take, kowa dole ne Allah ya jarabce shi, wallahi kabar ganin mutum a cikin sutura, wani mai kuɗin ma da zai buɗe maka cikin shi, to tabbas sai ka fahimci ashe kai ne Allah yake so, kai ne Allah ke ma sutura, ashe shi kura ce lulluɓe da fatar akuya, Abunda da yawa mu Talakawa bama kawo ma ranmu kenan, muna ɗuaka idan Allah ya bamu kuɗi shikenan ba wata Jarabawa da zata iya biyowa baya.

Gefe ya koma ya zauna yana mai kallon abokin nashi da ya haɗa kai da guiwa yana mai sakin ajiyar zuciya a hankali a hankali.

Suna haka ne kiran Mom ya sake shigowa wayar tashi.

Kai hannu yayi da niyyar latse kiran, Bilal yayi saurin ɗauke wayar ya amsa.

"Mom Al'ameen yana wanka ne, kuma mun fara shiri, please kiyi haƙuri ko zuwa gobe ne sai kuyi maganar, saboda ya faɗa mani cewa kina neman sa, bama so ne mu makara" ya faɗa mata haka, yana mai katse kiran ba tare ma daya jira cewr ta ba, yasan hakan da suka yi mata bai kyautu ba, saidai basa da zaɓi ne baya ga hakan, dole duk wani abu da zai haɗa Al'ameen da Mom ɗin a yanzu su kauce mashi, ko don halin da Aminun nashi ke ciki. Kai gidan ma baya fatan ace ya taka yau, so yake ace har sai kowa ya watse, domin baya so zuciya ta kwashi abokin nashi ya aikata ba daidai ba cikin mutane yanda zuciyar na tashi take haka.

Yana katse wayar, Al'ameen ya miƙa mashi hannu alamun ya bashi, ba musu ya miƙa mashi. Kashe ta yayi gabaki ɗaya, inda ya wurga ta cen bisa gado, domin ko alamu ma baya fata da burin sauraren Mom ɗin tashi a yau.

Ita kuwa ta ɓangaren ta mamaki take yi, duka yaushe yace mata yana wanka, kuma har ya sake komawa wani? Wai me ke faruwa ne? "Hidima ce tayi mashi yawa Hajiya kibi a hankali"

Cewr Hajiya Sa'a.

Ajiyar zuciya ta sauke, dole akwai buƙatar ta kira alhaji, domin ta faɗ ama shi buƙatar masarautr, shi sai ya kira shi da kanshi yayi mashi bayani, tinda dai shi yake namiji, ba kaman ita ba da take mace.

Ko da ta kira Alhajin yana cikin mutane, sai dai ya bata uzirin zai kira ta daga baya.

Dole jiki ba kwari ta miƙe tana mai komawa ciki, inda ta sanya aka ƙra haɗa wasu kayan ciye ciyen zuwa wajensu Mama Fulani. Tare da guest Pass ɗinsu, kaman yanda Bilal ya kawo mata.

Ai tuni gida ta ƙara harmutsewa ƴan zuwa dinner. Inda har motocin kwasar Mutane sun fara yin oarking a harabr gidan, domin basa fatan ace anyi African time saboda an gaji kowa ya kwanta da wuri ya huta.

********

Ni kau tin magariba aka sanya nayi wanka, sai bin ko'ina na ɗakin da kallo nake yi a sace, hatta da ruwan wankan da aka sanya nayi wankan dasu daban suke, wani irin ƙamshin daɗi ne yake fita daga cikin su. Sannan aka sake turara ni, har da na tsugunne. Domin Mama Fulani ta aiko da mai gyaran jikin, kuma ta faɗa mata cewa yau ne ango zai shiga ɗaki, ba kowa ya sani ba, Shiyasa take ta sake haɗe ni da wasu irin sirruka, tana yi tana sakin dariyar da ita ce kaɗai ta san ma'anr ta.

Hatta da gashin kaina ba'a bar shi ba. Gashi kuwa indai ba na kaina ba, duk jiki na babu inda yake. Haka aka dinga bani wasu irin turaruka ina murje ma jikin, har da na matsawa, duk da ba wai shiga yake ba, haka ake sanya ni ina shafawa gefe gefe. Kai har dai na gaji, dan dai bana da yadda zanyi ne, tunani nake tinda ba yau ne ango zai shigo ɗaki ba, menene na yi mani wannan fi'ilin.

Nan fa ko ina ya ɗau ƙamshi, har falo kana iya jiyo ƙamshin. Dama sashen bama da yawa ciki. Su Afnan ne da Jidda sai Asiya, Hafsat, khadeeja Raihana da Huda, sauran duk sun koma sashen su. Sai haɗimai guda biyu da suke zaune falo suna jiran ace suyi wani abu.

Ƙamshin jikin nawa duk da yana da yawa sosai, amman hakan baisa yake hawan kai ba. Tana gama gyara ni, sai ta miƙa mani wani turare, tace in tabbata yau da gobe idan zan kwanta na shafa a jiki na. Wannan wani sirri ne da sai nayi mata godiya.

Haka ta fice, inda mai kwalliyr da Afnan ta ɗauko tazo ta fara aikin ta.

Cikin ƙanƙanen lokaci kamanni na suka cenza, na koma kaman wadda aka ɓanɓaro daga inji. Tuni na ɗau sheƙi da walwali. Wata irin doguwar wedding gown ce mai kakar Royal blue akan kawo mani har ƙasa tana jan ƙasa, sai wani irin head da mai kwalliyr ta tsaya ta zubda zallar fasaha ta wajen ɗaura mani shi, shi kuma fari ne tar, har yana ɗaukar idanu. Sai wasu irin flowers da zan riƙe a hannu na, da ƴar post ɗin takalman mai kalar fara tar da duwatsun bula sai walwali take.

Hatta da sarƙar wuya na abun kallo ce. Tuni suka ɗau sowa da tafi. Inda su kuma suka shirya cikin riga da skirt na english wears kalar baƙin skirt da ruwan miyon goro ta riga, sai hula da suka kakkafa pecing cap itama baƙa, inda kowacce ta saki gashi ta hudar bayan hular. Sunyi kyau sosai suma kaman zasu bar ƙasar.

Muna cikin wannan shirin ne, inda har yanzu an ƙi bari na hakanan in huta, sai ƙalailaicewa ake yi. Saƙon anguna ya iske mu akan cewa ƴan matan amarya su fito, Amman banda amarya, ango ne da kanshi zai zo ya tafi da ita. A barta ita da wata Ƙawar ta guda.

Nan aka fara muhawarar da wa za'a barta.

Hafsat dai ita aka zaɓa akan ta zauna jiran yayan nasu.

Inda kowacce Ƙawar amarya da abokin ango guda cikin motar shi.

Nan fa duk motar da ka buɗe ka shiga, ita ce ta abokin angon da zaku zauna wuri guda gashi har a gama dinner ɗin.

Hafsat wadda bata sanya irin kayan sauran ƙawayen ba, wata doguwar riga ce jikin ta, kalar Orange da baƙin head, sai rigar taba cikin damar zama daram. Ita dama ai tana mamakin ace wai wani naƙuda take yi, gashi har zata je pherty ɗin hankali kwance, inda Sadeq ya shaida mata tare da Al'ameen zasu zo da Bilal.

Cikin sa'a Jidda na buɗe motar da taji zuciyar ta ta aminta da Yusuf (Dady) ɗinta na ciki. Tana shiga ta sakar mashi murmushi, inda ya kashe mata ido guda shima yana mai faɗin, "Ai ni wata budurwa nake jira ta faɗo nan my jiddo, kinga ƙawa ce sai yayi daɗi ko?"

Ɗan haɗe fuska tayi, itama cikin wata irin shagwaɓa tace "ai nice budurwar ko kuwa baby?"

Jinjina mata kai ya shiga yi, cikin wata irin ƙauna da sauƙi, to dama su ɗin har yanzu amare ne, hakan ya sanya na bar su, ina mai nufar motar da naga Afnan ta buɗe ta shiga.

Cikin sa'a ya ɗago kanshi, domin ganin wacece ta shigo.

Hasken fatar tata, na ɗaya daga cikin Abunda ya shaida mashi ita.

Ko ba'a faɗa ba, tabbas wannan jinin su Al'ameen ce, watau gayen da ya ƙwace mashi Suhan. Sai yaji ba daɗi sosai, yanzu ba komai ne da ya shafi Al'ameen take so ya ganshi kusa dashi ba, dan dai baya da yadda zaiyi ne, har yanzu kishin Suhan ɗin na sukar mashi zuciya. Saidai gaida shin da tayi ne cikin fara'a ya sanya ya ɗan kalle ta kaɗan yana mai amsawa, sai kuma ya sanya hannu yana kunna ƙira'a a motar, inda motar ta ɗauki shiru banda tashin ƙira'a, yana jiran a basu umurnn fara tafiya.

Tini dangin Dad da Mom sunyi gaba, inda har sun zazzauna ana jiran ƙarasowar kowa.

A haka aka bada umurnn fara tafiya, key suka fara yi ma motar suna mai fara barin harabr gidan, a hankali, inda suka saki fitilu ɗaiɗai na gefen bayan motar.

Abun dai gwanin ban sha'awa. Inda ko da suka ƙarasa, bayan sun firfito daga motocin nasu ba'a bari sun shiga ba, aka tsaida su a wani reception cewa su jira ƙarasowar ango da amarya, inda zasu samu masu masu rakiya.


***********


Da ƙyar Bilal ya shawo kanshi wajen shiryawa, Afnan ita ce ta zaɓa ma Yayan nata kayan Sanyawa, hakan ce ta sanya shi sawa ba tare da musun komai ba, Afnan ɗin daban take cikin ƴan uwan Ya Ameen, kusan ma zamu iya cewa yafi shaƙuwa da ita akan kowa dake cikin gidan.

Ango yasha kyau, kaman ba shine yake kuka ba ɗazu, inda da ƙyal Bilal ya lallashe shi akan ya saki fuskar shi ko yaya ne.

Motar da suka taho cikin ta ɗaukar amarya, yau ne aka fara hawan ta, renge rover 2020 inda ake jira ayi lunching ɗinta, Amman saboda wannan ranar Ya Ameen ya siyo ta, sai gashi cewa ranar bata zo mashi a yanda ya zata ba. Da gani Ya Ameen bai da wata motar da yake matuƙar so da ta wuce ƙirar kamfanin.

Bai fito daga cikin motar ba. Inda Sadeeq yayi ma Hafsat waya akan cewa amarya ta fito.

Yana mai komawa cikin motar shi da take fake gefe guda, inda a cikin ta ne zasu tafi shi da Hafsat ɗin, domin yan so ya kasance duk wani motsin ta a kan idon shi ne.

Tana tafe Hafsat ɗin na gyara mata rigar ta dake sharar ƙasa, don ma interluck ne.

Idanu ya zuba mata, yana ta gaban mota zaune. Ba Al'ameen ba, hatta Bilal ta burge shi. Kwakkwaran motsi ba mai yi, tunowa da yayi ko wacece Suhan ɗin a yanzu ya sanya shi ɗauke ido, yana mai sauke su bisa steary.

Tayi mashi matuƙar kyau, wani irin mikin shauƙin sonta ne ke taso mashi cen Ƙasan rai, inda wani gululun abu ke tasowa yana danne wannan shauƙin.

Bilal ne ya buɗe baki zai ce wani abu, yaga ya ɓalle marfin motar a hankali yake takawa zuwa gare ta.

Ganin hakan da Hafsat tayi sai ya sanya ta cenza akalar tafiyar ta, itama tana mai nufar motar mijin nata dakyal inda yake zaman jiran ta.

Hannu kawai naga ya miƙe mani, alamun in kama, ba wata wata na sanya hannu ina mai maƙale nashi.

Wani irin shork ne ya fizge mu mu duka, saida muka ɗan zabura, inda a hankali na ɗaga fuska ta zuwa saman tashi.

Fuskar shi ba yabo ba fallasa, saidai irin fara'a da murmushn da na zaci samu ban same shi ba.

Sauke kaina ƙasa nayi, ina mai fara takawa, kaman yanda naga shima yayi.

Saida ya buɗe mani ƙofar bayan motar na zauna, sannan ya gyara mani rigar, yana mai zagayawa shima ya buɗe ya shigo.

Bilal yayi gyaran murya, dake ma Al'ameen nuni da kada ya saida hali, sannan yayi ma mota key, inda su sadeeq ɗin suka shiga binsu a baya.

Muna hanya ne wayar Dad & in ta shigo.

Ba tare da ya kawo komai a ranahi ba ya ɗaga, yana mai gaida Dad ɗin. Shima saboda yasan yana cikin hidima sai a gaggauce yace mashi idan sun gama komin dare ya same shi sashen nashi..

Da to ya amsa, yana mai yin shutdown ɗin wayar baki ɗaya.

Saidai har yanzu bai ɗago idanu ya kalle ni ba, nima kuma irin Kunyar nan ta hana ni kallon nashi har zuwa lokacin da muka ƙarasa.

Motar amarya na tsayawa, ƙawayen ta suka yi caaaa, inda suka kama tasu, suma anguna suka kama nasu.

Saida aka daidaita ma kowa tsayuwar shi, sannan aka bada izinin mu fara takawa a hankali zuwa cikin hall ɗin, inda aka sakar mana waƙa a hankali take tashi cike da nishaɗantarwa.

Hannu na yana cikin nashi maƙale, kai idan ka gan mu zaka ce ba'a taɓa yin masoya kaman mu ba.

Saidai yanzu saɓanin ɗazu, murmushi yake saki a hankali a ƙoƙarin shi na kawar da duk wata damuwa dake ranshi, kaman yanda Bilal ɗin ya shawarce shi.

Hakan sai ya ƙawatar da kowa. Kowa ya miƙe yana mai sakin tafi, inda sauran ƙawayen nawa suke rausayawa a hankali su da abokan angon.

Kai tsaye wajen da ka tanadar mana domin zaman namu aka nufa damu. Har yanzu dai ina maƙale a jikin shi, kaman wani zai ƙwace mashi ni. Sai ma yaba iyayen nashi dake zaune wurin kunya, masalan Kaka zuwaira da ta matsa sai taje wurin saboda tsufa. Daƙuwa ta dunƙula tana mai sakar shi. "Kuji ja'iri, yana ta mamutse ta tin kafin ya shiga ɗakin, o'kho yaran yanzu ba kuna garesu ba"

Dariya ta ba kowa, inda suka lura ma Al'ameen ɗin bai san tana yi ba. Duk da wajen zama na musamman aka tanadar mata itama.

Bamu daɗe da zama ba, sauran abokai da ƙawayen suma suka koma inda aka tanadar masu suka zazzauna.


Sir Salim baya da yanda zaiyi, dole hakanan ya zauna tare da Afnan, inda itama duk ta takura, gani take kaman baya da sakin jiki da mutane, ita kuwa Asiya sai daɗi take ji tana sakar mashi signal da ido, akan ga kamu nan tayi mashi. Dama ita ce ta tura Afnan ɗin zuwa ga motar Sir Salim ɗin tin da ta gane ta. Ba tare da Afnan ɗin ta sani ba.

Wata waƙar aka kuma saki, sannan ne malam Ibrahim shahrukhan Mc ɗin da tayi masu jiya, nan ma shine zaiyi masu. Ya fara gabatar da shirye shirye, inda aka fara jejjera kayan ciye ciye bisa teburan da suke gaban kowa.

Kirari ne muka ji an ɗauka, inda wasu fadawa da haɗimai ke tafe suna zubga guɗa, sai Mama Fulani da Ammi da suke take ma baya. Suma haka aka shigo dasu zuwa wajen da aka tanada masu domin zaman nasu.

Nan fa shagali ya kankama, inda aka shiga gunguro wani irin ƙaton cake da yake ɗauke da photon amarya da ango cikin shigar dinner ɗin. Har an samu mai photon da ya ɗauka ya kai aka maƙala.

Da na kalli ya Ameen sai yayi mani wata ƴar dariya da na Gaza tantancewa, mai kama da yaƙe.

Ba haka na zaci gani ba ayau tattare dashi, to me ke faruwa ne? Kada dai ace nayi garaje nayi shisshigi. Irin rawar ƙafar da nago kan nuna ma amaryar shi wajen irin wannan pherty ɗin, ni sai ban ganta ba Sam.

Inda Bilal da kallo yake bin Aminun nashi, hakan ne ma ya sanya wani abun yake maintaining nashi.

Nan fa aka buƙaci amarya da ango da suzo su yanka cake, sannan su ci da kansu a gaban bainar jama'a.

A hankali muka miƙe, har ina mai kusan faɗuwa, shine ma ya taro ni, yana mai ƙure ni da idanu. A wajen mutane sai hakan ya burge su, suna tunanin zallar ƙauna ce, Amman tsakani na dashi sai ma ɗaure fuska da yayi.

Haka ya sake gyara roƙon da yayi mani muka nufi wajen cake ɗin.

Sai da aka ƙilga uku, sannan wuƙar da take riƙe a hannu na, shi kuma hannun Ya Ameen yake bisan nawa, ta lume cikin cake ɗin, inda aka saki tafi da sowa, ana mai sake sakin wani kuɗi daban na waƙar auren tamu, wadda bansan lokacin da akayi ta ba, ban kuma san wanene ya bada ayi ɗin ba.

A hankali na fara ɗebowa ina mai nufar bakin shi.

Riƙe hannu na yayi, ƴan ami yi mani wani irin kallo, inda ya taimaka mani wajen Sanyawa a wabkin nashi, sai kuma ya sake riƙe hannun nawa ya nufo baki na dashi.

Hakan ya sake burge mutane. Inda aka bada damar a sanya ma amarya da ango kiɗa su ɗan tattaka. An ba masu liƙo dama.

Waiyo Allah na. Ai sai ga ruwan kuɗi har da daloli na tashi. Mama Fulani ma saida ta fito ta sakar mana ruwan kuɗi, kai hatta da kaka zuwaira saida ta tako a hankali zuwa wajen namu, ita kam ƴan naira biyar biyar da ba'a san inda ta samo su ba ta liƙa mana. Hakan yayi ma mutane daɗi, ko ba komai ya nuna tsohuwar bata da wani abu dake nuni da fahari ko ɗagawar cewa yaran nata su ɗin wasu ne, tinda kowa ya sani ko daloli taso liƙawa, za'a kawo mata su ta liƙa.

Ana cikin shagali ne, sia ga wani group ya shigo hall ɗin, inda yaja hankalin kowa dake wurin. Dukan su mata ne inda ɗaya ne kawai cikin su yake namiji. Sanye suke da wata irin doguwar riga kaman za'a ƙulke su ciki sai ɗamarar rigar, inda ta bayyana matuƙa da kyawun rigar.

Ko wacce ɗamara an rubuta *Banfi ƙarfin ta ba fans* inda aka sakar masu sautin su daban, kaman dai sai da suka zaɓo waƙar, domin waƙar taken ƙungiyar tasu ne, da kuma ambatar suna yen nasu da ɗaiɗai da ɗaiɗai.

Nan fa suma suka ƙaraso cikin fili suna mai takawa a hankali cikin wani salo. Ruwan liƙo suka fara saki suna mai takawa sosai. Ah cen na hango su Salamatu mrs Daura, khaddeja, ummi zainab naja'atu da

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment