Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai kin ce ba, zaki ga abunda zai faru da ita. Ita dai Maryama mun ƙyale ta. Ba ta ita muke ba yanzu, Alhaji ƙaramin nake so yazo hannun mu, domin shine kan gidan a yanzu.. "

Cewar Mama talatun, wanda take magana tana ɗan waige waige, gudun ace wani ya jisu.

"Kutumar Ubaaa, ni kika buga haka Innarmu?" cewar Maree ɗin, tana mai hayayyaƙowa kaman zata rama.

Dariyar shaiɗan ci Mama talatun tayi.

" Ke shashasha ce, ni ba bugun ki nayi ba, bakin ki na buga, saboda baya da linzami, har yanzu baki biyo hali na ba, ai ta ƙarƙashin ƙasa ake komai, ke dai ki zuba mani ido, Amman Alhaji Ƙarami gaki cen a ɗakin shi, kinji na gaya maki"

Sai yanzu ne Mareen ta saki dariya. Lokaci guda kuma suna masu taɓawa kaman wasu ƙawaye.

Turo ƙofar da akayi gami da sallama, shi ya sanya suka ja bakin su suka ɗinke.

Mama Uwani ce, take shaida ma Maree tazo tayo cefane inji Hajiya Babba.

Ba musu ta miƙe, tana mai gyara kwalliyar fuskar ta, abun dariya sosai. Sannan ta yafa ɗan fingilin gyale, tana tafiya tana gantsaro gaba.

A bakin gare ta haɗu dashi, jingine yake da mota, hannun shi wata ƴar jikka ce haka ta kwali mai kyau, shi da wani ne suna magana.

"Ina yininku?" ta furta cikin shaƙe murya, sai wani karairaya take yi, dan ma babu ƙugun.

Bai ko kalle ta ba, balle ta sanya ran zai amsa, sai wanda suke tare ne ya amsa mata, yana mai cewa "Oga ana gaishe ka" "Lafiya" kawai ya iya furta wa, yana mai ɗauke kanshi, ya zuwa buɗe motar ya ɗauko wani abu.

Ƙafafu a sanyaye taka ta wuce, tana ji su Iro suna yi mata dariya da suke zaune bakin gate. Shi kanshi iron haushin yanda take nuna shige ma Alhaji ƙaramin yake ji. To koma dai kishi ne hakan? Oho!

Gashi shi kuma ko kula shi bata yi. Yana nan dai yana sauraren Al'ameen ɗin, akan maganar Maree ɗin.


Ƙutawa tayi a cikin zuciyar ta. Za kayi magana ne, sai ma an ganni a gaban motar taka, inji ta ƙaryar nuna ɗagin kai. Ko wa ma zai ɗaga ma kai? Shi da yake auren ƴar aikin gidan, wadda ko ni na fita gata, dan dai kawai tana da ɗan haske, wata ƙila ma mai ne take shafawa, Amman yana wani wulaƙanta mutum. Daga kai har ita zaku sani ne.

A haka ta wuce su har tayi masu nisa, daidai lokacin da ya sallama mutumen, yana mai binta da kallo, haɗi da sakin wani guntun tsoki. Yarinyar Sam bata burge shi, zubin ƴan duniya gareta, gashi tana tafiya tana wani girgiza, haɗi da ban ƙaro ƙirji wai ita mace, wanda ko shi da yake namiji ya fita fasali mai kyau.



*******


"Ammi na ji ki shiru ne da maganar tamu, Ammi ki taimaka man, nima ina son in ganni cikin iyali na Ammi, yarinyar nan tana sona fa, Ammi kada kiyi saken da zan sake rasa ta ita ma"

Sir Saleem ɗin ya furta cikin marairaicewa, Shiyasa ma wannan karon sai bai dawo ba, yayi zaman shi a cen zariyan, saboda ko ya dawo gidan baya jinshi da daɗi, ga kuma ƴan uwan Ma'u dake karakaina gidan, kuma cikin salon cin mutumci. Wanda ya zuwa yanzu so suke yaje yayo bikon Ma'un kuma.

Yaƙi zuwa ne, domin yana so ya nuna masu kuskuren su, sannan yana so Ma'un ta sake ƙara hankali, duk da har yanzu zuciyar shi na raya mashi cewa Ma'aun ba wai tayi sanyi bane.

"Kayi haƙuri Son, insha Allahu komai yana tafiya daidai. Mai martaba ne da kanshi yace abar batun a hannun shi, daga kai har Afnan duk ƴaƴan shi ne, dan haka duk yanda za'ayi insha Allahu babu matsala, Shiyasa Kaga mun saurara tukunna, amman muna sane da kai Son"

Ajiyar zuciya ya sauke, sai yanzu yaji sauƙi, ai tunda dai magana ta kai ƙoli, yasan ya samu Afnan ya gama. Jiki na ɓari ya katse kiran Ammin bayan sunyi sallama, yana mai kiran Afnan ɗin.



*********


Ƙarar blander dake aiki ce na ji ta tsaya lokaci guda. Da sauri na waiwaya, har ina ɗan razana kaɗan. Sai kuma na saki murmushi, ganin gogan nawa tsaye, yana juye man markaɗaɗɗun kayan miyan cikin man da nake soyawa na miyar.

Ɗan jingina nayi da cabinet, ina mai harɗe hannaye na, gami da langaɓar da kai cikin sigar shagwaɓa.

"Allah kuwa ni yaya ka bani tsoro wallahi" na faɗa cikin sigar shagwaɓa.

Saida ya tabbatar da ya gama juye wa, sannan ya wanke hannun shi jikin sinc, yana mai gogewa da kitchen napkin, sannan ya matso sosai zuwa inda naken, yana mai tallafo fuskar tawa.

"Sorry my lolipop, taya ki zanyi fa" ya faɗa yana mai lalubar baki na a hankali.

Kauda kai nayi gefe, ina ɗan dukan ƙirjin shi.

Hannu ya sanya, yana mai lafar mani kai na bisa faffaɗan ƙirjin nashi. Mun natsu a haka, kowa na amsar saƙon juna. Babu abunda ke yawan saurin saukar mashi da natsuwa, irin jin Suhan ɗin a cikin ƙirjinshi, yana mai shaƙar daɗaɗɗen ƙamshin mayukan gashin nata.

Ɗan ƙauri ƙarin da muka jiyo ne, ya sanya mu saurin raba jikin namu. Muna mai kai kallon mu wajen girkin namu. Dashishin farar shinkafar dake cikin stummer ɗinne ruwan ya ƙone, saurin saukewa nayi, yana mai taro man ruwa a famfo na sinc na ƙara zubawa. Shi ya cigaba da taimaka man, hatta da yanke yanken su Cabbage shi yayi mani. Muna girkin hana bani labaru daɗi, wasu har sia na dafe ciki saboda dariya, yayin da ya kan zuba mani ido wani lokaci yana kallo na ina dariya. Har cikin zuciyarshi yake jin daɗi hakan. Ya tabbatar ma kanshi cewa ina jin daɗin zaman nawa tare dashi.


Na dafe ciki ina dariya, harda ƙyaƙyatawa ne, sai jin ya kamo mani duka hannuwa yayi.

Ƙure ni da idanu yayi, ƙasa daure ma kallon nashi nayi na sadda kaina zuwa ƙasa. Idanun nashi na mani nauyi a kullum. Wani irin kallo yake yi mani, mai cike da tsantsar ƙauna. Ban taɓa tunanin Ya Ameen zai iya sakin jiki dani haka ba, na ɗauka ko da na aure shi, zamuyi zama ne kaman na ubangida da yaron sa, ban ɗauka soyayya ta ta kai har haka ba a cikin zuciyar shi.

Katse mani tunanin yayi, yana mai nufar hannayen nawa dake cikin nashi hannuwn zuwa bisa ƙirjin shi, saitin zuciyar shi.

*"I Love u Suhan... No words can explain how much u mean to me, please and please i beg u Suhan, for my sake, don ever leave me for any reason, u always means alot to me wife and always keep firgiven me ,please dear"*

Ya furta cike da wani irin shauƙi. Ni kaina jiki na ya mace duka.

A hankali na kai baki na bisa hannun nashi da ke dunƙule da nawa. Ina mai manna mashi wani irin peck mai sauti. Lokaci guda kuma na wara duka hannuwn nawa, ina mai shige wa cikin jikin shi tsaf. Ba wata wata shima ya maida hannuwan nawa cikin nashi, yana mai sake manne jikin nawa da nashi.

A hankali ya shiga saddo da kanshi zuwa gareni, yana mai lalubar laɓɓan nawa.

Wannan karon ban hana shi ba, kaman yanda sai lokacin da yaji ya gamasu, sannan ya sake ni, ya na mai maida numfashi, har yanzu idanun shi a lumshe suke.


Saida muka kammala komai, sannan ya taya ni muka jera a saman dining, har yanzu komai take man a lallaɓe, cike da wata irin salon soyayya da ke ƙara ruɗa ni. Gani nake kaman ni kaɗai ce nayi Sa'ar miji a duniyar nan, gani nake kaman ni kaɗai ce macen da tayi saura a faɗin duniyar.




A falo ta iske mu, zaune yake bisa sofa yana amsa wayar manager ɗinshi. Yayin da ni kuma nake kwance kusa dashi, kaina bisa cinyar tashi, ya zame hular dake bisa kaina, yana mai yamutsa dogon gashin kan nawa. Ni kuma hannu na riƙe da waya ina karanta mana wani littafi *Saif ko Maleek* kiran wayar manager ɗin ta shigo wayar shi.


Gefe ta samu ta zauna, hannun ta ɗauke da wata leda. yayin da ni kuma ganin tan bai sanya na tashi ba. Duniya kenan, wai yau Nihal ce a ɗarare a sashe nawa. Wanda ada zanje ɗakin ta in ta sallama Amman sai taga daman amsawa, shima a gadarance, ko magana Zatayi man cikin isa da tsawa, ni kuma jiki na na ɓari, kaman zanyi mata sujjada.


Saida ya kammala tsaf, shima akan komawar su aiki ne. Sannan ya juya ga Nihal ɗin, yana mai maida hankalin shi kanta.

"Uhm Nihal kin dawo ne?" ya furta ciki ciki, kaman baya son maganar.

"Um Yaya" ta furta itama a hankali.

A hankali na zame kaina daga bisa cinyar tashi, ina mai miƙewa da niyyar wuce wa, domin dia ban nuna mashi naji maganganun su na ɗazu ba.

Hannu ya sanya yana mai kamo nawa hannun cikin nashi, gami da maida ni ya zaunar gefen shi.

"Zauna wife, maganar ta shafe ki ai, ko ma bata shafe ki ba, dani dake duk ɗaya ne, sit!" ya faɗa shima idanun shi cikin nawa. Ba musu na koma ma zauna nima, ina mai ɗan sakar mashi murmushi, gami da ɗan yin fari da idanu. Murmushin shima yayi, yana mai lakato man Kumatu.


Gyara zaman nashi yayi, yana mai ɗaukar remote ya latse tv ɗin dake aiki, wanda ta kusa lamushe rabin bangon.

Hankalin shi ya maido kaina. "Wife maganar ku ne ke da Nihal, akan koya mata abubuwan da zakiyi, na farko ina son sanar dake cewa, Naji daɗi, lallai zuciyar ki mai kyau ce wife, ina alfahari da samun ki a matsayin mata ta. Na biyu kuma ina mai neman alfarma a gareki, muddin kika ga bata maida hankali kan abunda zaki koya mata kada kiji nauyin sanar mani, sannan idan ba zata kwantar da hankalinta ta koya ba, gara tun wuri a barta kawai, sannan ina so ki sani, wannan kuɗi da kika nema naji daɗin hakan, wannan ke nuna mani cewa komai na duniyar nan yana da daraja, abunda su suka kasa fahimta kenan. Saboda haka ga kuɗin zata baki da hannunta" duk yana maganar ne a hankali cikin natsuwa mai tattare da haiba da kwarjini.

Ya ƙara she yana mai yi ma Nihal ɗin nuni da gefen stool akan ta haɗo da sauran cikon da zai bata ɗin.

Duka ta har haɗa su, sai ga uban tulun kuɗi a gaba na. Wanda hakan har saida ta sanya na kusa ruɗewa, ban taɓa gani ba, ko a mafarki. Saurin saisaita kaina nayi. Ina mai gyaɗa kai a hankali cikin basarwa na shiga cewa "Ba komai Yaya, komai nayi ma Nihal ban faɗi ba, domin ita ɗin kai ne, saboda haka kada ka samu damuwa, insha Allahu zuwa gobe zamu fara class da ita. Cikin lokaci ƙanƙani zan tabbatar da ta iya. Kuma wannan kuɗi da ta bayar, ina so ku sani ba ni ce zan amfani dasu ba. Ko naira bana so, bana da sha'awa a ciki. Dan haka na sadaukar ma da gidan Marayun da muka je dakai kwanaki, Naji kana son tallafa masu, dan haka nima wannan gudunmuwa ta ce zuwa gareka. Allah kuma ya taimaka, ya baka sa'a, sannan ya ci gaba da dafa maka akan dukkanin al'amurran ka ameen"


Da sauri Nihal ɗin ta maida kallon ta zuwa gareni, cike da tsantsar mamaki da al'ajabi sosai take kallo na. Ikon Allah, wacece ma Suhan ne wai? Dama haka take? Dama mace mai ɗinbin alkhairi tattare da ita, suka dinga wulaƙanta ta ada cen baya?

Saurin tasowa tayi zuwa garenin, tana mai rungume ni kai tsaye ta saki kuka.

"Aunty ki yafe man, nayi nadama Yaya ka taya ni bata haƙuri, insha Allahu na ɗauke ta tamkar ƴar uwa ta a yanzu, Yaya Aunty Suhan mace ce ta gari kaman Umman ta, dan Allah Aunty ina mai roƙon ki da ki sake yafe mani a karo na barkatai"


Nima rungume ta nayi sosai cikin jiki na. Ina mai goge ƙwallar da ta zubo mani. Ko a mafarki ban taɓa tunanin kaiwa haka ba, ko a mafarki ban taɓa tunanin zama yanda na zama ba a yanzu. Dole na gode ma Allah da wannan baiwa da yayi mani.

A hankali na zame ta daga jikin nawa. Ina mai cewa "Ba komai Nihal, ke ɗin kaman ƴar uwa kike a gareni, insha Allahu babu abunda zai gagara inyi maki, ko domin miji na, ko domin uban ƴaƴa na, ko domin wanda ya bani farin ciki fiye da yanda na tsammata"

Cike da so da sha'awa yake kallo na. Baima san me zaice mani ba. He's speachless dai a Yanzu.

Har dare yayi Ya Ameen na yaba mani, yana mai faɗa man kalamai masu matuƙar daɗi, wanda saboda hakan ne ma naci alwashin sanar mashi da labarin cikin nawa, ko domin yanda naga yana cikin farin ciki da annashuwa.



*_Oum-Deedat ce_*











https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


🌹 *BAN FI ƘARFIN TA BA* 🌹

🌺🌺🌺🌺🌺


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._


*Page ~81~*



Daf da zasu idasa taka ƴar matattakalar da zata sada su da cikin gidan ne yaja ya toge.

A hankali Mom ɗin tashi ta juyo tana mai binshi da idanu, shima idanun nashi ƙyam cikin nata, sai yanzu ne ranshi ke raya mashi menene hakan kenan?

Juyawa yayi a sukwane, yana mai nufar sashen nashi, inda yake iya hango Suhan ɗin ta ƙarasa shige wa da gudu.


Ta bayan ta ya rungomo ta. Tana tsaye cikin kitchen, jikin cabinet ta juya ma ƙofa baya.

Bata san lokacin da ta sauke wata bayyanannar ajiyar zuciya ba, lokaci Guda kuma tana ƙoƙarin goge ruwan hawayen da suka ziraro mata. Bata so ya gani kada ya kawo ma ranshi wani abu, Amman har ga Allah yanda mom ɗin tayi, sai ya sanya ta ƙara tsorata da al'amarin mom ɗin.

Ta bisa kafaɗar ta ya saƙalo kanshi, yana mai shaƙo daɗaɗɗen ƙamshin nata mai idasa rikita mashi ƙwalwa.

Sun Kai kusan minti biyu a hakan, idanun su a lumshe. Har yanzu tana matse cikin jikin nashi, hannayen nashi kuma suna zagaye bisa ɗan shafaffen cikinta, wata irin kewar juna suke ji tana taso masu, daga cen ƙasan zukatan nasu.

A hankali ya juyo da ita sasai zuwa cikin ƙirjin shi, yana mai sanya hannu ya kwantar da kan ta saman faffaɗan ƙirjin nashi,har numfashin su na gauraya. Lamo tayi, tana mai jiyo sautin bugawar zuciyar tashi da sauri da sauri.

Jin motsi a falo shi ya fargar dasu daga duniyar soyayyar da suka lula. Ɗan ja baya tayi kaɗan, tana mai sake mashi kyakkyawan murmushi. Lakato mata hanci yayi, yana mai murmusawa shima. Sai kuma ya gyara tsayuwar shi, har yanzu hannayenta cikin nashi.

"I missed you Sweet Janam" ya furta murya cen ƙasa ƙasa, cikin wani irin shauƙi.

"I missed u too Yayana" ita ma ta furta cike da ɗan zaulaya haka. Sannan ta zame hannayen nata daga cikin nashi, tana mai matsawa jikin fridge ta fiddo gorar ruwa da cup.

Tana tsiyaya mashi yana amsa, saida ya ƙwalƙwale ne, sannan ya saki ajiyar zuciya mai ƙarfi. Yana mai sake jawo ta zuwa jikin nashi, bayan ya ajiye cup ɗin bisa cabinet.

Ƙoƙarin raba jikin ta da nashi take yi, jin yanda yake jagula ta, gami da sarrafa ta son ranshi. Ta sani sunyi kewar juna, amman sai zuciyar ta ke bata akwai wani a falon nasu.

Shi kuma gogan da Sam ya manta ma da Bilal suke tare, har saida ta raɗa mashi a kunne "Ya Bilal fa?" sannan ne ya sake ta, yana maida numfashi, gami da gyara zaman necktail dake wuyan nashi.

Hannun ta ya kama zuwa falon nasu. Su duka sororai sukayi, duk kunya kuma sai ta lulluɓe su, ganin Bilal ɗin zaune bisa sofa, sai latsa waya yake yi, yana murmushi.

A kunyace na juya zuwa cikin kitchen ɗin. Kenan duk abunda muke yi yana jinmu, wata ƙila ma yana kallon mu. Saboda kitchen ɗin da falon farin glass ne kawai akayi amfani dashi wajen raba tsakani, saidai kuma golden cotton ɗin dake ta ciki, wanda idan aka zuge shi, tsaf za'a iya hangen tsarin kitchen ɗin.

Ruwa na ɗauko, haɗi da lemo, sai snacks wanda bama rabuwa dashi kullum a fridge, microwaving nashi nayi masu, sannan na haɗa da kayan marmari, ina mai nufar falon.

Ɗan tattaunawa suke a hankali a hankali. Ganin fitowa ta ne, ya sanya su yin shiru, tare da cenza akalar firar.

"ƙanwa ta duk kin bi kin zauta man aboki, gashi har sambatun ki yake in yana bacci" Bilal ɗin ya faɗa, fuskar shi cike da murmushi, daidai lokacin da nake ajiye masu plates ɗin bisa stool.

Nima faɗaɗa murmushi na nayi, tare da cewa "Ayya Yayana, nima ai har ƴar rashin lafiya nayi da baya nan" cike da jin kunya.

Hannu ya sanya, tare da jawo ni zuwa jikin nashi sosai. Ban musa mashi ba na zauna gefen shi nima sosai. Duk Kunyar Bilal ta cika ni.

Sai naga su dukan su basu wani damu da hakan ba, to an saba da ɗabi'ar turawa, su a garesu hakan wayewa ce sosai.


"Baby naga kin ƙara wani irin haske da fresh! Uhm, faɗa man Sirrin" Ya Ameen ɗin ya faɗa a hankali, fuskar shi daidai kunne na. Ɗan zabura nayi, ina mai ɓoye fuska ta cikin jikin nashi.

Shi dai Bilal sai dariya kawai yake yi, yanda yaga Al'ameen na cin soyayya, bai taɓa tunani ba, sai yake ganin kaman ba shi bane, kaman abokin nashi ba zai iya haka ba.

Sun ɗan jima anan, har saida na sama masu abu mai sauƙi na daga abinci suka ci. Sannan Bilal yabar gidan.

Cikin kwana biyun da ya share a gida, babu inda yake zuwa, daga masallaci sai sashen Mom da Umma. Komai a gida yake kammala abun shi. Da daddare na kan bi shi sashen Mom ɗinshi mu gaisa, gami da ƴar fira. Sai nake ganin kaman Mom ɗin na bina da wani irin kallo. Har yanzu dai ban saki jiki da ita ba sosai, idan muka je tare da Ya Ameen sashen, sai ta dinga janye shi da fira, dan ma Allah yasa Afnan na nan, wani lokaci kuma Nihal kan ɗan tsoma baki. Duk da shima sai na kula kaman akwai abunda yake tsakanin su, baya sakin jiki da ita kaman da. Amman banso hakan ba, sai nake ganin kaman nice na shiga tsakani, sai nake ganin kaman laifi na ne. Amman har yanzu na kasa yi ma Ya Ameen maganar.

Har yanzu tsakani na da Umma ba wani sakin jiki sosai, bata so ma nake cika shiga sashen nata. Nima sai ban takura ɗin ba, nasan bata so wani abu ya faru ne, a ce da saka hannun ta ciki.

Irin kulawar da Ya Ameen ke bani har ta wuce misali. Ya zuwa yanzu har makaranta munje an kammala komai, har na fara shiga aji. Dayake nuna shekarar ƙarshe ne, sai naga abun kaman wasa, gashi har mun fara shirye shiryen fita.



*******


Zaune yake falo bisa sofa, gaban shi laptop ce tashi, sai kuma gefen shi ɗan dambun kaji ne cikin bowl fari, tare da ɗan cokali. Sai gorar ruwa da cup da suke gefen nashi. A hankali a hankali ya kan ɗan ɗago gami da ɗibar dambun ya kai bakin shi. Dambun ya mashi matuƙar daɗi, duk lokacin da bana nan, ina makaranta, dambun ne yake ɗebe mashi kewa, hakan ce ta sanya, bana yarda ya katse mun. Wani lokaci har Bilal ya kan zo yayi guzuri. Dayake Ummin shi ta kusa dawowa.


Murɗa ƙofar falon aka yi tare da shigowa. Jin hakan ne ya sanya ni ajiye jera mana kaya cikin wardrooop tamu da nake yi, nayo falon domin ganin ko wanene.

Tun dai da ya ɗago sau ɗaya ya kalle ta, sai ya maida kanshi ƙasa, ya zuwa aikin da yake yi mai muhimmanci. Wanda yake saka ran kamfanonin nashi zasu koma bakin aikin su cikin satin. Hakan ne ya sanya abubuwa yi mashi yawa, kusan zan iya cewa tare da Bilal suke yi. To Amman yau kasancewar Ummin Bilal ɗin zata dawo, sai kawai ya bashi hutu, tare da yi mashi tsiyar cewa wai yaje ya kula da sauran abubuwa. Dayake ana gyara gidan ne, tare da cenza fenti da sauran kayan dake cikin gidan.


Jiki a sanyaye ta ƙarasa cikin falon ta zauna ɗan nesa kaɗan da Yayan nata.

Fuska ta a sake kaman kullum, saidai babu alamun wasa a cikin ta, na ƙara so ina mai cewa "A'ah Nihal ce?". Ɗan gyaɗa kai tayi a hankali tana mai cewa "Eah nice Aunty"

Ɗan ɗagowa ya sake yi yana mai kallon ta haka, sai kuma ya cigaba da abun da yake yi.

"To sannu da zuwa, ya gida?" na tambaye ta, ina daga tsaye bayan kujerar Ya Ameen ɗin.

"Lafiya lau" ta furta, har yanzu jikin ta a mace yake, zan iya karanto irin halin damuwar da ta shiga. Domin kuwa yanzu Nihal ta zama abun tausayi.

"Yaya wurin ka nazo" ta furta a hankali, tana mai maida kallon ta bisa kan Ya Ameen ɗin.

Da hannu yayi mata alama da ta cigaba yana jin ta.

Ganin hakan ni kuma sai na juya zuwa bedroom ɗin, domin ƙara sa aikin da na fara.

Saidai abunda kunne na yaji ta faɗa ne, ya sanya ni, ina shigewa ɗakin, na ɗan turo ƙofar a hankali. Saidai bana iya hangen ta, saidai Ya Ameen shima ya ɗan juya baya haka kaɗan, gefen fuskar shi kawai nake iya gani.

"Yaya akan maganar Baby ne.. " sau kuma ta kasa idasa faɗar abunda tayi niyya.

"Uhum ina jinki" ya faɗa shima, yana mai ɗan jawo wata ƴar joter da take ajiye gefen shi ya fara joting.

Ɗan shiru ne ya biyo baya. Sai kuma cen tayi ƙarfin halin cewa.

"Yaya ina son komawa gida na ne, Amman akwai matsala wallahi, dan Allah ka taimaka man." Ajiye abunda yake yi yayi gefe, yana mai ɗagowa sosai ya shiga kallon Nihal ɗin.

Fuskar shi ɗaure tam, babu alamun wasa

"Uhm ina jinki dai, matsala kaman ta me kenan?"


Sauke kai tayi zuwa ƙasa, idanun Ya Ameen ɗin sun mata nauyi, dama tun cen, tun da daɗewa su kansu sunsan Ya Ameen ba irin wanda ake kawo ma wargi bane, sam baya ɗaukar wasa ko raini.

"Eh Yaya! Naje na samu Mom da maganar, ta nuna mani cewa in rabu da batun komawa gidan Baby, tana jira ne ya kawo man takadda ta, gashi kuma Dad ko kallo na baya yi, bansan laifin da nayi mashi ba.."


"Ya isa hakanan Nihal! Tunda ga abunda Mom tace, yanzu ni me kike so inyi maki? Duk abunda zan iya yi na riga nayi, sai Allah yasa ke ba mai jin magana bace, Mom ita ce duk abunda ta faɗa shine daidai, ita ke ɗaure maku gindin yin duk abunda kuka ga dama, to ba shikenan ba, sai kije kibi abunda tace maki ai, mahaifiyar ki ce, ta isa ta sanya ki kiyi, and tasan abunda yake daidai dake ai"

Ya katse mata maganar tata a zafafe, yana mai maida kanshi bisa aikin shi.

"Am really sorry Yaya, wallahi na gane nayi kuskure, Shiyasa ma na samu Aunty Suhan..."

"What? Kika same ta akan me? Me zata iya yi maki? Look Nihal, dont deare involve my wife a cikin lamarin ki, babu abunda zata iya yi, bana son another

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment