Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yanayi a jikin shi, dalilin da ya sanya na idasa cusa gashin nawa cikin hular, ina mai taka wa a hankali na isa gaban gadon.

Sai nake ganin kaman yana da ƴar damuwa, kawai yana ɓoye man ne.

Hannayen shi duka na kamo cikin tafukan nawa hannayen, ina mai murza su a hankali. Sai ajiyar zuciya yake saukewa a hankali, inda ya sake janyo ni zuwa jikin nashi, na faɗa bisa gadon.

Ban musa ba na lafe, kaman wata mage, shima sake gyarawa yayi sosai yanda zan ji daɗi, yana mai zame ƴar yalolon hular da take cike da sumar kan tawa. Shafawa yake a hankali a hankali.

Mu duka munyi laƙwas, kowa na shaƙar ƙamshin kowa, wani irin yanayi ne a tattare damu. Samun Ya Ameen a gareni ba ƙaramin abu bane, gashi yau ni Suhan wai har da cikin Yayan namu a jiki na.

"Kin yi kyau Baby na! Faɗa man menene Sirrin wai? Naga har wani shining kike yi" ya faɗa a hankali cikin kunne na.

Ƴar naj i jiki na yayi man, lokaci guda ina mai sakin murmushi, na sunne kaina cikin ƙirjin nashi.

"ko sirri ne? Ba za'a faɗa ma Yaya ba?" ya sake faɗa shima, cikin jin wani irin sauƙin kasancewar tamu haka.

Ɗan girgiza kai nayi a hankali.

"To a faɗa man, Sirrin Suhan ai na Al'ameen ne" ya jaddada man a cikin kunne.

Naji daɗin kalaman shi, ko a mafarki ban taɓa tunanin zan samu daraja da ɗaukakar haɗa kaina da Ya Ameen ba. Sai gashi yau da bakin nashi ma yana haɗawa.

A hankali na kamo hannayen nashi, ina mai ɗora su bisa shafaffen cikin nawa, wanda kai kace ma babu ƴan hanji a ciki.

Shafawa ya shiga yi a hankali, yana mai wara idanun shi sosai a saman fuskar tawa.

Soke kaina nayi cikin blanket, ina mai ɗan ɗaga kaina a hankali.

Zumbur yayi daga bisa gadon, yana mai tallafo ni sosai.

"What Suhan? Baby! Kina da baby nan ciki? Ciki na? Are u pregnant baby?" duk ya jero man waɗannan maganganun a lokaci guda.

Gyaɗa kai nayi a hankali, har yanzu na gagara ɗora idanu na a kanshi, wata irin kunyar shi nake ji.

Ai da ƙarfi naji ya sauke ajiyar zuciya, yana mai furta *"Alhamdulillah ya Allah"*

*"Thanks you aloot aloot Baby, kin biya ni, kin gama man komai, am so proud of you Baby, you mean kina ɗauke da ciki na? My Kid? My happiness?"*

Saukowa yayi sosai daga bisa gadon, ya shiga kai komo yana shafa kai, har yanzu fuskar shi a wasashe take sosai. Sai kuma na ga ya dawo da sauri zuwa bisa gadon ya ɗago ni sosai, yana mai rungume ni sosai, kaman zai mayar dani cikin ciki.

Mun kai minti biyar a haka, sai numfashi nake ji yana saukewa a hankali a hankali

*"Zan zama Dad very soon dear, me kike so? Me kike so in maki? Dama na faɗa maki ina da ajiya nan ciki, Dad zaiyi grandson haka ma Umma"*

Ya faɗa cikin sauƙi sosai. Ni sai na zama ma kaman wata sauna, duk murnar cikin ce haka? Hada surutai?

Da kallo nake binshi, nima murmushi kwance a saman fuska ta.

Caraf! Naji ya ɗage ni zuwa sama, sai kuma ya fara juyi dani a hankali a hankali, maƙalƙale shi nayi sosai, ina mai sakin dariya mai sauti, bai damu da a jiyo mu ba, duk kuwa da cewa dare yayi.

Saida ya kula da na fara jin juwa, sannan ya dire ni bakin gadon yana mai faɗin "Zauna a hankali Baby"

Zama nayi, har yanzu hannaye na cikin nashi. Zamowa yayi zuwa ƙasa ya durƙusa sosai, yana mai kuma tallafo fuskar tawa.

"Thank aloot dear, ban san kuma ne zance maki ba, kin gama bani komai a rayuwa ta, please ki kula man da kanki, ki kula man da baby na please and please Suhan"

Gyaɗa mashi kai nake yi sosai, nima wani irin daɗi nake ji, zan so ace yaron ma yayi kama dashi, Ya Ameen komai da komai nashi burge ni yake yi, watau wannan miskilanci, rashin son hayaniyar da ada ya kan bani haushi, sai gashi yanzu su ne suka dawo suna burge ni, kusanta ta gare shi, sai na gane, ashe duk wani kallo da nake mashi a da, da kuma irin fassarar da na mashi, ashe duk ba haka yake ba, shi mutum ne dai da Allah yayi shi mara son hayaniya, ashe ba ɗagawa ko izza bace ke sanya shi hakan, shi mutum ne mai tausayin na ƙasa dashi, ko kuma wanda bai kaishi ba, shi mutum ne mai yawan kyauta, mai iya zama da mutane, mutum ne wanda babu ruwan shi da sha'anin wasu, mutum ne ba mai yawan abokai ba, balle yayi jaye jayen mutanen da ba su dace da rayuwar shi ba.

Ɗan nisawa nayi, lokacin da naji laɓɓan shi saman baki na, har wata ajiyar zuciya na sauke, kafin in fara maida mashi da dukkanin saƙunan da yake aika man.

Mun nutsa ne wayar shi ta ɗauki ruri. Duk da kasancewr dare ne, sai banyi mamaki ba, in nayi la'akari da cewa suna ƙoƙarin komawa bakin aiki ne, saboda a haka kusan zan iya cewa kullum a cikin amsa waya yake.

Bilal ne, dan haka ya ɗan miƙe cikin dariya sosai, yana mai amsawa yake faɗin

"Sai ka bani goro kafin na faɗa maka friend"

Ta ɗaya ɓangaren Bilal cikin mamaki yace "Faɗi me kake so? I promise to give u friend"

Dayake wayar a handsfree ya saka ta, ina iya jiyo abunda yake faɗa, juyowa yayi zuwa gareni, yana mai ɗan man alamu da waya akan me zaice? Me nake so? ɗan murmusawa nayi, ina mai son gyara wanciya ta, idanu na a kanshi. Da sauri ya maƙale wayar a kunnen shi da kafaɗa, yana mai matsowa inda nake cikin sauri ya shiga gyara man kwanciyar.

Alamu ya kuma man da hannu, bayan ya miƙe tsaye, yana mai kashe man idanu.

"Agwaluma" na furta a hankali, cikin jin kunya, duk da bansan lokacin da baki na ya faɗi hakan ba.

*"Agwaguma"* ya faɗa shima cikin sauri.

A lokaci guda muka tun tsire da dariya ni da Bilal ɗin.

Watau agwalumar ma bai iya faɗa ba, ikon Allah.

Ɗan ɗaure fuska yayi, lokacin da yaji Bilal na faɗin "Shege ai ba ma sai ka faɗa ba, to na gane, congrat friend, ashe girma kuma yazo? Yanzu zakayi hankali dan ubanka"

Ɗan kallo na ya sata, ni kuma sai na ɗauke kai kaman banji ba, dai cen na ji ya bushe da dariya yana faɗin "Yanzu zaka kawo ta kuwa tunda kunyi mani wayau"

Shima cikin farin ciki sosai Bilal ɗin ke ma Ya Ameen murna, saidai ya roƙi alfarmar a bari sai da safe zai kawo, yanzu kam dare yayi, har sha ɗaya ta wuce.

Ina jin su suna waya, duk abunda Bilal ɗin ya faɗa, amsa mashi kawai yake yi, saboda a irin tsananin farin cikin da take ciki.

Naga gata a cikin daren, komai nake kafa kafa yake dani, yanda kasan wata jariri ya, sai riritani yake yi. Hatta da sallr asuba da muka tashi, har toilet ɗin ya kaini. Kai ko bacci bai yarda inyi ni kaɗai ba, ba tare da ina cikin jikin shi ba, yana shafa cikin a hankali a hankali.

Kafin kwana biyu kaf labarin cikin ya buɗe ko ina, nace ina ruwan ba sabun ba. Ni da ganɗoki mu je biki

Sai kuma me, tun da maganar cikin ta fasu, sai jiki na ya fara ciwo, yau wannan gobe wancen, laulayi dai irin na masu yaron ciki, ina son Wancen, banson Wancen, duk abunda na ce ina so ya siyo mun shi mai yawa ya kawo, har asibiti muka je akace ba wata matsala bace, saidai in ɗan dinga hutawa.

Umma na ba ƙaramin farin ciki tayi ba, saidai ta ɓoye ne saboda kawaici.

Ƴan dubiya akai akai sukan zo, hatta da wasu daga cikin ƴan Kankiya saida suka zo.

Kaka zuwaira kuwa kusan kullum sai ta kira ni, haka aunty Feena, haɗa ƙara bani wasu shawarwari.

Dad ma sai gashi da kanshi sashe na, karon farko da ya tako sashen namu, kunya duk sai ta lulluɓe ni, dayake tare da Mom suka shigo, saidai na kula ta ɗan yi sanyi, tana son ba ni kulawa, saidai ban sani ba ko kunya ce ke hana ta.

Labarin cikin ya yi ma wasu daɗi, saɓanin wasu kuma, saidai koma dai menene hakan mu a gare mu alkhairi ne.

Abokan Ya Ameen wasu tun biki rabo na dasu, sai gasu suna tururuwar zuwa, oh ni Suhan, kenan duka binsu yayi yana shelanta ni, ciki kaman kanshi farau.

Classes da zamu fara da Nihal ma, cewa yayi a dakata aga yanayin jikin, saidai ba ƙarya ba, wallahi ina ɗan shan wahala, ni kaɗai nasan yanda nake sha. Har Ammi ma saida ta kira ni, dayake Afnan ta tsegunta ma Sir Salim, shine shima fa ya kira ni.

Ina ganin abubuwa iri iri, motsin kirki da nayi akan idanun shi ne, kullum sai an ba cikin nan Kiss ya kai sau ashirin, butsu butsu, ko fita yayi sai kiga ya dawo da wuri.

Afnan kullum kusan tana sashen, ita da Nihal suke haɗuwa suna mna wasu aikace aikacen, da yace a kawo man masu taya ni, ni ce nace a'a bana so.

Sai gashi Nihal da ada ni ce nake shiga in share mata ko ina a ɗakin ta, in dafa mata abunda take so, yau gashi har ɗaki har toilet Nihal ke gyara mun, the same wahalar da na kasance ina mata a da, ita take yi man, ko so take ta ƙara kakkaɓe laifin ta a gareni ne? Oho?


Na kusan sati biyu a haka sannan na fara jin dama dama. Shima makaranta ne da zamu rubuta final exam, ya sanya na daure, na ƙarfafa jiki na na miƙe. Sai gashi kuma nan take dole, karatu muke yi sosai, at the same time kuma in na samu chance, mukan yi class da Nihal da Afnan, sai gashi Nihal na mamaki, da ta tambayi Afnan wai nawa na amsa, tace ko naira, ban ma yi maganar ta biya ni ba, jikin ta ya sake yin sanyi, kenan dai ta kula da biyu na karɓi kuɗin ta, to koma dai menene ta gode, tunda duk abunda muke yi tana ganewa sosai, sai gashi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci komai nata ya fara cenza wa, ta fara komawa ainahin Nihal ɗinta a baya, mace mai son gayu da kwalliya, gashi kuma Nureen akai akai ya kan kira ta a waya, ya ji daɗi da ta tabbatar mashi da cewa ta fara iya abubuwa da dama.

Saudat ko tazo bata leƙowa, ko a sashen Mom muka haɗu da ita, saidai ta bini da wani kallon banza, haushin Nihal take ji, wai kaman Nihal ace ta saki kambun ta, tana bina sau da ƙafa, gashi ni kuma sai wani jansu a jiki nake yi, ina nuna kaman su ƙannai na ne na gaske.

Zamu iya cewa Hajiya Kubra ta ji matuƙar daɗin hakan, ta ɗauka aure na da ɗan nata zai kawo cikas, ko naƙasu a zamantakewar gidan nata, ta ɗauka ci baya ne ace yaron nata ya auri yarinya ƴar aiki mara gata da galihu kama ta. Saidai bata nuna ba ko alama, kuma har yanzu ta kan ɗan fita ga harkokin ta, duk da har yanzu taji shiru daga masarauta, duk kuwa da cewa an kamo Hajiya Laila da Alhaji Yaro.

So take Sa'a taji kunya, har lailan ma, tunda su dai mayaudara ne, maciya amana, ko da za'a raba ta da dukiyar, Amman ya kasance ta ga Hajiya Laila, Hajiya Sa'a da Alhaji yaro sun wulaƙanta, sun muzanta a duniya.



*************


Kaman kullum, mun kammala duk girkin da muka yi a ranar, Nihal na kitchen tana gyarawa, Afnan kuma na zaune bisa Sofa kusa da ni, tana mammatsa man hannaye na, da ƙafafu na da suka ɗan yi fushi, saboda tsayuwa.

Ya Ameen yayi sallama shi da wani Likitan shi mai suna Dr Aleeyu, Wanda ya kasance shi ke duba ni. sai Bilal da suke tare.

Ɗan janye ƙafa ta nayi, da niyyar tashi, ina mai gyara zaman ɗan kwali na a bisa kaina.

Itama Afnan niƙewa tayi. Da sauri ya sanya hannu yana mai dakatar da ita.

"Noo Lil Sis, cigaba da matsa mata ƙafafun, hala aiki tayi mai yawa ko? Bata jin magana, Dr yace ta dinga samun hutu, Amman ta matsa ma kanta, sauƙin ma ɗaya da ta samu ta kammala jarabawar. Dr gata nan ka duba ta, sannan ka sake yi mata faɗa, ni bata jin magana ta"

Zama Dr ɗin yayi gefe, yana mai murmushi yake faɗin "Madam ya gida? Ya je ya tattago ni, wai nazo na duba mashi ke, baki ɗan jin daɗi, gashi kin ƙi ki zauna ki huta, wai haka ne?"

Ina kallon Ya Ameen da yake tsaye ta kusan bisa kaina , nake girgiza kai "Dr zaman ne ya isheni, shi yasa banson in zauna ɗin"

Ɗan hararar wasa ya sakar mani, yana mai tarar numfashi na "Aleeyu kada ka yarda da maganar ta, ka duba ta sosai please"

Cewar shi, yana mai komawa kusa da Bilal ya zauna. Sosai muka gaisa da Bilal, ina tambayar Umme, wanda har ta dawo, har ni ma tazo ta duba, da yaron ta danƙwalele kyakkyawa sosai mai sunan Ya Ameen.

BP ɗina ya fara ɗauka, sannan nauyi na, sai kuma sauran aune aune.

Ɗagowa yayi yana mai kallon Ya Ameen cikin ido. "Watau yallaɓai, akwai buƙatar a sake kula fa sosai, ita da baby duk lafiyar su lau, nan da wata guda ma zata iya fara zuwa awo, sai ka kai mana ita cen wajen mu, akwai ƙwararrun likitocin da zan sanya su bata kulawa ta musamman, wanda suke fannin masu ciki"

Gyaɗa kai yayi sosai cikin gamsuwa, inda sai da ya sake kafa wasu dokokin sannan ya tafi.

Tun da likita ya sake bada doka, sai ya kasance ko ƙwai baya shan kula da riritar da nake sha. Hatta da ruwan zafi a flaks shi ke dafawa yana zuba wa. Abinci kuma daga cikin gida, sashen Mom ake kawo man, shima Afnan ce ke yi. Sai Umma idan ta dafa abun marmari na gargajiya tana aiko Afnan ɗin dashi. Shima sai da Ya Ameen yayi ma Dad complain ɗin Mom yanzu bata kula ni sosai, sannan yayi mata magana, sai a lokacin ne ma aka samu ta shigo ta duba ni, duk da cewa cikin ranta tana tausaya man, domin ta san irin wahalar da nasha lokacin ina ciki, kuma tana fata ace ciki na, ba zaiyi daɗewar da ni nayi ba, duk da nima sherri ne irin na mahassada.


Ya Ameen ya kan ɗauke ni wani lokaci mu zaga gari, wajejen shaƙatawa muke zuwa, idan ka gammu sai mun burge ka, duk hassadar ka, komai kaf kaf yake yi dani, gashi cikin ya fara ɗan tasawa kaɗan, ina ɗan jin motsi a hankali a hankali, wani lokaci idan yana motsi, Ya Ameen ɗinne kan ɗora hannun shi bisa cikin, yana yi yana murmushi, yana ma cikin magana, kaman yana sauraren shi.

Wannan ciki fa ya ga gata over, komai nake so shi ake man, komai nake son ci shi ake bani. Aunty Feena ce kan kira akai akai tana ja mashi kunne, duk da ya kula Mom kawaici ne take mashi, ko kunya ce? Ko kuma ƙiyayyar tawa ce ta shafi cikin, saidai shi bai damu ba, a haka yake ci gaba da kulawa dani, tare da bani dukkanin wani jin daɗi na rayuwa.

Kusan zan iya cewa yanzu bana da matsala, ta kowanne fanni lafiya lau, Afnan da Nihal sun maida hankali, duk abunda nake koya masu ɗauke wa suke yi.




**********


Ranar wata Asabar ne, muna falo muna kallo, saidai rabin hankalin mu, yana ga kan yanke man farce da Ya Ameen ke yi, yana faɗin ya kamata a jira mai lalle tazo ta yi mani, ni dai sai dariya nake yi.

Wayar shi ce tayi ƙara kaɗan, alamun saƙo ya shigo.

Bai dakata daga yi man abunda yake yi ba, komai a nutse, cikin salon shauƙin ƙauna, motsi kaɗan nayi sai yace "Ya dai baby? Akwai wani abu ne? Ko baby na ne?" sai in girgiza mashi kai. Har sai da ya kammala, sannan ya ɗauko wayar yana dubawa.

Da sauri naga ya miƙe, yana mai faɗin "Tafiya Adamawa ya kama mu yanzu, harda Umma da Mom da Dad, ina fatan zaki kula da kanki sosai har in dawo, zan turo Lil wajen ki Baby, please ki kula fa"

Jinjina mashi kai nayi, hankali na ya tashi sosai da sosai, hakanan sai naji ba daɗi jiki na, kira daga masarauta kuma? Harda Mom kuma da Dad? To me ke faruwa?

Cikin salon takun shi, da ɗan sauri ya nufi bed room. Sai gashi ya fito saɓe da ƴar jikka.

Inda nake zaune ta dawo ya iske ni. Durƙusa wa yayi sosai, yana mai bani peck a goshi, sannan ya maida akalar Kiss ɗin zuwa ga cikin, yana mai shafawa yake faɗin "Baby na sai na dawo kaji? Kada kayi ma Mummyn ka rigima, Allah yayi maka albarka"

Kaman cikin yaji abunda Ya Ameen ɗin ya faɗa, sai naji ya motsa yayi ɓul! Murmushin mu ne ya faɗaɗa, yana mai cewa "Kin gani ko baby? Yaji abunda na faɗa, sai na dawo kuyi mana addu'a"

"Allah ya tsare, ya kiyaye hanya, ya sanya a dawo lafiya, a gaida mana kowa da kowa, har da Mama Fulani, da mai martaba" na samu kaina da faɗa a hankali cikin wani salo. Saida ya rungumo ni cikin jikin shi sosai na wani lokaci, sannan ya sake ni, yana mai matsawa jikin stool ya zari makullin mota, sannan ya juya ya fice.

Har sai da ya kai bakin ƙofar fita, sannan na samu kaina da cewa "Ya Ameen"

Cak ya ja ya tsaya, yana mai juyowa a hankali gareni.

Tashi nayi a hankali, ina mai dafe da ƙugu, sannan na taka har kusa da inda yake tsaye. Sannan na kamo hannayen shi ina mai cewa "Ya Ameen ina so in tambaye ka, Amman please kayi alƙawarin faɗa man gaskiya"

Kallo na yake da mamaki, sai jikin shi yayi sanyi kuma.

Tallafo fuska ta yayi, yana mai cewa "Ask me dear"

Sai dana ɗan yi jim, nauyi da girman maganar nake aunawa, saidai ya zama dole nayi mashi ita,

"Uhm..." ya faɗa shima, yana mai bin fuska ta da waɗannan shanyayyun idanun nashi.

"Ya Ameen please me ke faruwa ne? Menene alaƙar dake tsakanin Mom da Umma? Me yasa masarauta ke neman ku? Jiki na yayi sanyi, sai nake ji kaman ba lafiya ba, Ya Ameen zuciya ta na halbawa, bana son duk wata matsala da zata iya shiga yanzu tsakanin mu, sai nake ji kaman ban iya jurewa, Ya Ameen zuciya ta zafi take man, tsoro ne fal a cikin ta.. "

Da idanu yake kallo na. Sai yaji kaman ƙasa ta tsage ya shige, sai yaji wata irin kasala ta lulluɓe shi, tausayi na ya tsira mashi sosai, me zai ce ma Suhan? Da wanne ido zaiyi nata bayanin halin da ake ciki?

Kama ni yayi sosai, har zuwa bakin Sofa, sannan ya zaunar dani. Shima kusa dani ya zauna, yana mai kwantar man da kai na bisa kafaɗar shi.

Hannaye na cikin nashi yana murzawa.

"Suhan!" ya kira sunana a hankali cikin wani sauti.

"Ba lafiya ba", haka zuciyata ke raya man, na daɗe rabon da naji irin wannan kiran daga bakin Ya Ameen.

Ƙoƙarin ɗagawa nayi in kalle shi.

Ya sake mayar man da kan bisa kafaɗar

"Zan faɗa maki Baby, Amman sai mun dawo, and ki kwantar da hankalin ki please, no matter how ina tare dake, da unburn namu, i will never leave u in my entire Life. Ke ce rayuwa ta, ke ce farin cikin Al'ameen, wannan kuma shi ne burin Al'ameen"

Ya faɗa daƙyar kuma a hankali, yana mai shafi saman cikin nawa.

Maimakon inji hankali na ya kwanta da maganganun shi, sai naji hankali na ya kuma tashi, wai me ke faruwa ne? Gashi Umma bata faɗa man komai, ba kullun nake ganin ta ba ma, in dai ba ni na shiga sashen ba.

Baki na buɗe da niyyar zan magana, ya sanya hannun shi, yana mai toshe man bakin, tare da ɗan girgiza man kai. "Kiyi mana addu'a mu is lafiya, da na dawo zaki ji komai ƙanwata"

Ɗan Murmushin yaƙe na saki, ina mai ɗagawa daga bisa jikin shi.

"Shikenan Yaya, sai kun dawo, Allah ya kiyaye mana ku a duk inda kuke" ya ji daɗin addu'ar, Shiyasa ya ɗaga yana mai sakar man murmushi mai kyau, tare da lakace man hanci "To kuma ko ke fa baby na? AMEEN Ameen to, ki kula man da kanki, da ajiya ta kuma" ya faɗa yana mai miƙewa.

Har bakin ƙofa na raka shi. Saida ya fice sannan na koma ɗaki na kwanta, tunani fal a cikin zuciya ta, sai na samu kaina da zurarar da ruwan hawaye masu ɗumi, ban shirya duk wata matsala da zata ɓarko a tsakanina da miji na ba, ina mashi son da bazan iya kwatanta wa ba, ba zan iya rabuwa dashi ba, ko da kuwa za'a yanka ni ne. Balle ace matsala daga ɓangaren Umma. To ko dai faɗa suka yi? Shine ake neman sasanta su? Kai ai kuma da naji labari, ko na ga wata alama dake nuna hakan, kuma nasan Umma ta, ba mace bace mai irin halin faɗa ba.

Kaman yanda yace, sai ga Afnan tazo man taya ni fira.nan fa muka shantake, muna kallo muna labari, zuwa cen kuma sai ga Nihal ita ma, nan fa labari ya sake ɓarkewa. Agwaluma ta nake sha a hankali, wadda akai akai Bulla ke kawo man ita. Na ja su sosai a jiki na, su ma sun saki jiki dani sosai, Nihal ko da yaushe so take tayi wani abu, da zai sa ta gane cewa na yafe mata har cikin raina.




Haka na kwana tunane tunane da juye juye, kaman marar lafiya, sauƙi na ma butsu butsu ya kan kira ni a waya, duk da sai dare suka isa, amman mun raba dare muna fira, yana tambaya ta unborn nashi. Saidai na ce lafiya lau, yana mai ƙara ja man kunne da na kula, domin wannan cikin shi ne rayuwar shi a yanzu, sannan ya sanar da ni cewa duk abunda nake so, na kira Bilal, in ya kasance bana da ɗan aike, bai yarda in fita in yi driving da kaina ba (Dayake ya koya man mota cikin tsakanin, saboda zuwa makaranta)




*************




A hankali sawun takon mutum ke bayyana, har zuwa lokacin da ƙafafun suka daidaita tsayuwar su cikin ƙayataccen falon.

Ko numfashin kirki baya yi, yayin da aka duƙa a hankali a hankali, aka ajiye wani abu dake cikin baƙar keda, wanda ba zaka iya tantance ko menene ba.

Ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin akayi a hankali, lokaci guda kuma, ana mai ɗaga ƙafafu cikin sauri aka fita daga sashen.

Cikin bacci mai daɗi naji ana Ƙwanƙwasa man ƙofar ɗaki. A'ah me ke faruwa ne? Ashe ban rufe ƙofa ta ba jiya? Kai anya kuwa? Ni ce fa na rufe ta da hannu na, kafin na kwanta, lokacin da na raka su Afnan bakin ƙofa. To ko dai Ya Ameen ne ya dawo? Shi kaɗai ke da makullin sashen namu, sai kuma Mom wanda take dashi tun tuni.

Gaba na ne ya tsananta faɗuwa, bansan dalili ba, saidai ya ta'allaƙa da jin ƙila ƙofa ta a buɗe ne.

Doguwar rigar bacci ce jiki na, mai taushi da kuma haske, fara ce ƙar da ita, har wani santsi santsi take yi.

Plat shoes ɗina na soso mai taushi na zura, ina mai jawo ƴar hula ta da ta zame saboda daɗin bacci. Kafa ta nayi a kaina sosai, na sauko daga bisa gadon, baki na ɗauke da salati.

Nayi mamakin ganin har gari ya fara wayewa, kenan har anyi sallar asuba? Ikon

1 Comments On BAN FI KARFIN TA BA
avatar
zakari-4

10 months ago

Reply

I really love the novel

Please Login or Register in order to submit comment