Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


sannan tasa aka karbo mata kwadon zogale a gurin Laure matar Hardejo ta biyu,

zogalen kadai ta iya ci, tasha ruwa, ta dan kwanta a inda take zaune,
bacci ne mai karfi da dadi yayi gaba da ita,
gyara mata kwanciya Aisha tayi cike da tausayawa,
kyakykyawar fuskarta ta kalla ta sa hannu ta share mata hawayen dake gangarowa ta gefen idonta,
a zuciyarta tana Hailala ga ubangijin da yake da ikon mayar da mai gata bawa,
Allah ka ďaura mana jarabawa mai sauki wacce zamu iya daukarta,
da waďannan adduoin mai babban suna ta tashi ta fita tsakar gidan dan samowa Atika naman da zata gasa mata,

kicibus tayi da yaro ya shigo da zabuwa an yanka ta,
dariya tayi tace "ko baka fada ba nasan Bala ne ya aiko ka,
gyada kai yaron yayi ya fita da gudu,
albarka ta shiga shi mishi saboda kullum sai ya kawo musu halastacciyar dabba gidan sunci,
maryam ta mikawa zabon tace "maza tayi amfani da ruwan zafin ta gyara shi,
amsa tayi cikin ladabi ta gyara shi hade da bankareshi yadda zaiyi kyaun gashi,
kafin Mamanta ta fito har ta fara gasashi cike da kwarewa,
saida ta gama tass sannan ta sa a karamin bangaji ta wuce ta kaima Aisha....




Saboda dadewa bata huta ba,
da kuma karancin bacci da take samu yasata ta kai har bayan isha'i bata tashi ba,
babu wanda ya tasheta saboda yanayin da take ciki, saida tayi bacci mai isarta sannan ta tashi tana mika hade da salati,
ganin duhun dakin ya sanyata mikewa zubur ta fara lulube,
dan hasken dake tsakar gidan ta hango ta tsagin tagar dakin,
ajiyar zuciya tayi ta dauki mayafinta ta rufe kanta sannan ta fito waje,
kamar jiranta yaran sukeyi ta fito suka kewaya ta suna kallonta,
magana Aisha tayi mata tace "kije kiyi alwala kiyi salloli sai kici abinci kiyi wanka..

Tana idar da sallah suka kewaye ta da abinci da fura da kuma gasashshen zabo,
tuwon taci sosai tana hamdalla a zuciyarta,
rabon ta da taci irinshi tunda kaddara ta kaita auren Baffa,
saida taci tayi katt sannan ta kora da ruwa,
naman ne kadai bata ci ba saboda sam batason jin kamshin gashi, Ba karamin horata Ma'u tayi ba da gashinta na kullum,
wanka tayi da ruwan zafi mai dadi sannan ta dawo inda suke ta zauna,
rokon Allah ta shiga yi da ya barta a cikin su har Allah ya kawo sanadiyyar da zai hadata da Abbunta da kaninta Ateek,

kallon irin zaman da sukeyi takeyi mai cike da tsafta da kaunar juna,
yaran gidan duk suna kaunar junansu haka basa yi ma wacce ba uwarsu ba rashin kunya,
matan kuwa kullum cikin hira suke da karatun al kur'ani, wani lokacin kuma mai babban suna ta tarasu dukkansu harda makota ta basu tarihin Annabawan Allah da iyalensu, da irin gwagwarmayar da suka sha,
shiyasa a ko da yaushe gidan yake a cike da mata da maza,
koda yaushe gidan baya rabo da abin ci da kuma sha saboda yawan sadaukarwar da sukeyi.....




Shigowa gidan yayi fuska dauke da murmushi ya kalli ahalin gidanshi ya kara samun nutsuwa a cikin ranshi,
a kullum kara godewa Allah yakeyi da ya hada shi da Aisha da kuma sauran matanshi masu fahimta da lura,
Zama yayi a tsakiyarsu ya kalli Atika yace "Barka da zuwa cikin Ahali na,
nayi matukar farin cikin jin zamu samu jininki a cikin zuri'ata,
ina miki fatan Allah ya sauke ki lafiya, daga nan sai mu tafi can kasarku da dan da zaki haifa..
Ameen matan shi suka ce cike da farin cikin addu'ar,

kallon Maryam yayi yace "Malama Maryama ku koma can gefe ke da kannenki zamuyi magana da iyayenki,
mikewa sukayi cike da ladabi suka koma wata tabarmar a kusurwar dakin Saude matar Hardejo ta uku,
Aisha ya kalla yace "mun kusa samun siriki,
cike da farin ciki laure tace " Alhamdulillah, wanene ke son Maryama?
Bala,
Bala ne ke sonta, dazu ya turo mahaifinshi, na kuma ce na bashi,
cike da farin ciki dukka matan suka ce mashaa Allahu,
Allah yasa alkhairi, Allah ya basu zuri'a dayyaba,
Ameen Hardejo ya fadi ya kalli Aisha da taki amsawa saidai murmushi kawai takeyi, ita a dole kunyar diyar fari,
nan fa suka shiga tsokanarta cike da nishadi kamar ba kishiyoyi ba.....





*BAYAN WATA BIYAR*

●●●●●●
*Mummunar Kaddara*


Har lokacin Baffa bai waiwayi gida ba, yana can yana neman kudi saboda ya tsira mutuncinsa da na iyalinsa,
kullum cikin tunaninsu yake, ciki harda Atika da sam bashi da masaniyar tana dauke da cikinshi,
cikin kudirar ubangiji neman da yakeyi Allah na sa mishi albarka a cikinsa dan har ya samu ya siya dan gida mai daki uku ginin siminti na jaka biyar da rabi a cikin jalingo,
a wannan lokacin ne ya yi niyyar zuwa gida dan ya tattaro iyalinshi ya fara sabon zama dasu mai cike da jin dadi..



A cikin watanin da suka shude aka daura auren Maryam Da Bala Shaho,
murna a gurin shaho ba'a cewa komai saboda yadda ya dauki malam da ahalinsa, bauta ce kadai bazai iya masa ba,
domin kuwa ya taimaka mishi gurin samun rayuwa mai inganci da tsafta...



Atika ma tayi bul bul, cikinta yayi girma sosai har yayi mata nauyi,
gaf take da shiga lokacin haihuwarta,
kula ta musamman take samu a gurin Hardejo da matanshi,
ba irin kayan da basu sak'a ma jaririn ba tun kafin
Zuwanshi duniya,
a wannan lokacin Atika ta dan fara jin fillanci kadan kadan, dan in aka mata magana zata ji amma mayarwa ke mata wahala....



Ita kuwa Ma'u tun da ta tafi can garinsu ukari bata dawo ba sai dai aiken mugun abu da take ta yo wa Atika da cikin jikinta,
haka duk juma'a sai ta bi motar katako taje garin dan taga ko mijinta abin kaunar ta ya dawo sannan ta shiga gurin Haire ta bata sakon magungunan da take kaiwa Atika dan cikin ya zube,
bata san Haire watsi takeyi da maganin ba, domin ita mace ce mai tsananin tsoro,
tunda ta amshi musulunci ta daina duk wani aikin sabon Allah, dama wani lokaci ma'u ke zugata suyi tare,
yanzu ko da ba ta nan, kullum tana gidan Hardejo daukar karatu...




Yau ma kamar kowace jumma'a ta gama shirye shiryenta na mugun kullinta, ta dauko su Bingel ta shiryasu dan yau in ta tafi bazata dawo ba,
tasan da tana garin babu abin da zai hana ta kashe dan dake cikin Atika,
yanzu kuwa ta dauki alwashin kashe har Atikan saboda in ta barta to fa Hardejo sai yasan yadda yayi ya sake sata cikin rayuwarsu,
gara kawai ta kashesu gaba daya..



A daidai kwanar da zata sadasu da hanyar kauyen suka hango cincirindon yan ta'adda, babu kaya a jikinsu sai wukake rataye a kafadunsu da kugunsu,
tsayar da motar sukayi suna ta wasa wuka a kasa,
fitsari Bingel ta saki ta fara ihu tana kuka,
sakko dasu mutanen sukayi suna mazurai,
cikin wani irin yare suke tambayarsu ko su musulmai ne, drivern da yake yana yawon safara, Kuma yasan musulmai sun fara yawa yace "eh shi musulmi ne,
nan take suka farďeshi sukayi wurgi da gawar,
Ma'u jiki na rawa tace "Dama kai musulmi ne ka dauko mu?
Ta fara tambayar karen motar, girgiza kai karen motar yayi yace ni cikakken mabiyin Addinin sarki *HAWAIZU NA UKARI* ne, Dariyar keta mutanen sukayi suka ce "ina za ku?

Ma'u da ta gama samun mafita tace "Gembu,
kauyen da Malam Hardejo ya cika shi da musulmai,
zamuje ne domin yi musu magana akan abin da sukeyi mara kyau,
sun yarda bautar iyaye da kakanni sun dauki wani addini da Hardejo ya kawo,
cike da farin cikin samun Nama ogan yace "dama mun dade muna son kai farmaki kauyen,
mai girma *SADUN* ya dade yana bamu labari akan malamin da yayi wa kauyen kawanya da musulmai,
ku shiga mota ku jagorance mu dan mu aikata abin kirkin da za'a dade ana tunamu dashi har duniya ta dade.....




A kofar Gidan jauro Ma'u ta sauka da ya'yanta,
tayi musu nuni da gidan Hardejo, tace musu zata dubo dayan malamin ko yana nan zata zo ta samesu,
wucewa sukayi; ita ma ta kama ya'yanta ta ruga da gudu ta shige gidanta ta turo,
babban fatanta shine su fara yin layyarsu da Atika,
can kuryar daki ta shige ta kwantar da ya'yanta hade da tsoratar dasu dan kar su tashi suce zasu fita,
saida ta tabbatar bacci ya daukesu sannan ta fito ta tsaya a tsakar gida tana kasa kunne,
ita dai in bukatarta zata biya Kowa ma ya mutu,
yanda taci alwashi a kauyensu na cewar Baffa bai isa ya mata kishiya ba,
kuma kawai sai gashi banda kishiyar har 'yan uba gare ya'yanta,
inaa sam in ta bari hakan ya faru to bata cika jinin *MANASIR* ba....





Kamar yadda suka saba taruwa a kofar gidan ranar jumma'a maza da mata yau ma hakan ne ta kasance,

Kamar daga sama sukaji tsayuwar motar katako a kansu,
babu wanda yayi yunkurin katse sallar saboda a iya saninsu kauyen nasu lafiya lau yake domin musulmai sun danyi rinjaye a garin yanzu,
tun ba ma komawar shaho cikin musulunci tsundum ba,
a sujjadar karshe suke sukaji an fara kai musu farmaki,
basu sallame ba har lokacin saida suka gama zaman tahiyar karshe,
suna sallemawa kowa ya fara neman hanyar tsira,
kewaye su yan ta'addan sukayi suka dinga sarar jikinsu,

"Allahu Akbar
Malam Hardejo ya fadi nan take gurin ya dauka, a nan fa Shaho da mutanenshi suka tuno da dabanci suka tube kaya suna fadin Allahu Akbaar,
suka nufi yan daban,
Rashin makamai ne ya cucesu shiyasa duk fadan da sukeyi aka sassari su shaho,
cike da karfi Shaho yayi kokarin fusge katuwar wukar jikin ogan,
nan fa yasa ihu ya fara sararsu iya karfinshi,
a take samarin garin suka shiga gidajen kusa suka dauko makamai,
ciki harda Barde mahaifin shaho,

shi kuwa Hardejo sallah ya koma ya cigaba dayi yana rokon Allah ya kareshi da dukkan jama'ar musulmi,
(idan Ajali yazo)
babu makawa sai an tafi,
babu addu'ar dake dauke ajali a jikin mutum,

kamar hadin baki arnan kauyen suma suka fito da makamansu,
"in ka san farkon rigima to fa baka san karshenta ba,
Rigimar da Ma'u ta hada saboda san zuciyarta ya haifar mutuwar rayuka da dama,
Ma'u bala'i ce a cikin alummar musulmi....



Shaho ya jigata iya jigata,
shi kadai ne mai karfin dake yakarsu,
sauran arnan garin abin da yasa sukaci galaba akansu saboda daga cikin gidan suka fara gurin matan,
saida suka karkashe matansu da ya'yansu sannan suka fito suka hada hannu akan mazan,
dama ba karamar tsana sukayi wa Hardejo ba,

wani a cikinsu mai siyar da barasa yayi kan Hardejo da gatari saboda shi tuni yake hakonshi dan hani da yayi da shanta ga daukacin musulman kauyen yasa shi ya daina ciniki,

Shaho na ganin haka yayi saurin tareshi hade da kai mishi wuka kirjinshi,
ta baya wani ya lallabo ya sari gefen kafadun Hardejo,
sannan ya sake luma mishi wukar,
salatin da ya fara yi ne ya dawo da hankalin shaho kanshi,
tuni jikinshi ya mutu ya saki wukar hannunshi ya durkushe a gurin yana rusa kuka,
Ya Allah ga hardejonka nan,
Ya Allah me yasa baka turo mana da kariya ba a lokacin da muke da bukata,
Ni kadai bazan iya ba ya Allah,
gawarwakin mutanen ya kalla harda na babanshi ya sake rusa kuka,
cikin sanďa wani sumameshi ya luma mishi wuk'a a bayanshi saitin da zuciya take,
nan take ruwa mai karfi ya kece a cikin kauyen,
wani irin ihun murna arnan suka fara yi dan duk sunbi musulman sun musu kisan gilla,
harda matansu da ya'yansu,
cikin murna suka nufi cikin gidan suka fara kwaso shanaye suna bi takan gawarwakin....



Ma'u kuwa tun tana jiyo ihu har ta daina ji,
anan ne jikinta ya bata an gama komai,,
cike da murna ta fito gida da niyyar zuwa gidan Haire,
a kofar gidan taci karo da Baffa da kaya niki niki a hannu,
karbar kayan tayi ta fara murna suka shiga cikin gidan,
a tsakar gida ya baje kayan yana bata labarin irin abubuwan alkhairin da ya samo,
"Ta ina ka shigo garin nan? Ta jefo mishi tambayar tana kallonshi hade jiran amsa,
" Ta bayan gari, saboda bana sann kowa ya rigani fada muku isowa ta,
yanzu wanka zanyi in wuce gidan Malam,
naga garin ma ba kowa nasan duk suna can maza da mata ana sallar juma'a da wa'azin Hardejo,
cike da kissa tace "nima ko sai muje dan bacci ne ya daukeni ban samu zuwa ba,
dube dube taga ya fara yi tasan tabbas Atika yake nema,
murmushi tayi tace "Amarya tana can gidan Hardejo,
ka tafi kabar amarya da nauyinka,
nace su Baffa ba'a cika min alkawari ba,
cikin rashin fahimta yace "me kike nufi?
murmushi tayi a ranta na mugunta ne amma a fili ta nuna na soyayya ne tace "matarka dai ciki gareta, tama kusa haihuwa,
a daburce yace "ma'u ban karya miki alk---- katseshi tayi da sauri tace "babu komai ai matarka ce,
ni fatana ma mu samu dan namiji tunda naga dukkanku baku da namiji,
kaga sai mu samu magaji, murmushin farin ciki Baffa yayi ya mike yace "dauko mayafi mu tafi,
zunde tayi mishi ta baya sannan tace " har ka fara zumudi,
nima bakaga yadda na kosa ba,
komai a gidan nan bana barinta tayi,
ganin cikin nema yasa hankalina ya kwanta dan ina tunanin namiji zata haifa mana,
rungumeta Baffa yayi cikin farin ciki yace "Ma'u shiyasa nake kara kaunarki,
tun farkon haduwar mu kike min halacci har kawo yanzu,
nagode nagode,
gwalo tayi ma bayanshi tace "Ai mun zama Daya Baffa....




Tun a bakin gidan jauro suke karo da gawa har suka isa kwanar gidan Hardejo,

wani irin ihu Baffa ya saka da yaga Hardejo kwance cikin jini ruwan da akayi ya dama gurin, girgizashi ya fara yi ya dinga rusar ihu yana fadin waye ya aikata haka a gareka,
waye ni, wayyo ni Allahn Hardejo,
Dafa shi wani dattijo yayi a cikin wadanda suka gudu yace "Tashi Muhammadu, yanzu ba lokacin wannan bane muyi gaggawar haka rami a cikin gidan hardejo mu tattarasu duka musasu a ciki domin kuwa yanzu makasan sun tafi hada walimar murna kafin su dawo su mamaye gidajen,
kuma kaima muna gamawa ina umartarka da ka gudu da kai da iyalinka,
mikewa Baffa yayi a tsorace yana kuka suka shige gidan su biyar da wasu samari,
a cikin gidan ma ya daburce ya dinga kuka yana kiraye kirayen suna,
ita kuwa Ma'u rashin ganin Atika cikin gawar wakin ne ya fi daga mata hankali,
kar dai ta samu ta tsere,
dube dube ta fara yi har ta kai ga bayin gefen dakin saudatu,
Atika ta gani tana kuka tana nishin nakuda,
da sauri ta tufe bayin ta koma gurin su Baffa,
duk wanda a cikinsu taga zaiyi gurin sai tayi maza ta hanashi,
hak'a rami sukayi mai zurfin gaske da tsaho,
suka fara dibo gawarwakin suna turawa a ciki, saida suka gama tsaff ta Hardejo ta zama ta karshen sawa, fuskarnan tashi dauke da murmushi,
wani kukan Baffa ya saki yana zuba kasa a kanshi yana rusa kuka,
saida suka gama komai sannan hankalinshi ya dawo kan Atika da bai ganta ba,
Ma'u in dai ba idona bane yake min gizo banga Atika ba,,
kafin Ma'u ta bashi amsa sukaji kukan jariri da karfin gaske,
runtse ido Ma'u tayi tace shikenan yazo duniyar,
da sauri Baffa yabi ta inda yake jin kukan,
kofar bayin ya tura da karfi,
a durkushe ya sameta tana dada dafe cikin alamun akwai wani a ciki,
daukar jinjirar yayi sannan ya taimaketa ta fito suka wuce dakin Aisha,
bin su Ma'u tayi tace bari in taimaka mata,
Kamar zautacciya ta dinga maimata yan biyu kyautar Allahn Hardejo,
tsaye yayi akansu ya rufe ma jinjirar hannunshi jiki da zanin mai babban suna,
saida ta kara awa daya sannan ta haifo Danta kato namiji,

cike da yake Ma'u tace "tafi ka nemo abin da zamu yanke cibi,
wani abu mai kaifi Atika ta sanya a hannun Ma'u,
harararta tayi ta yanke cibiyar,
kallon jinjirar hannunshi tayi tace "dame aka daure cibiyar, zanin jikinta ne ta yaga ta daure dashi,
kallon ta ma'u tayi a zuciyarta tace duk a ina ta koyo wadannan abubuwan,
wani tsumman ta kuma yaga ta katsewa ma'u tunanin da takeyi,
amsa tayi ta daureshi sama sama, ta kuma dukunkuneshi ta hana Baffa ya daukeshi,

saboda rashin imani Ma'u na ganin jini na ambaliyar fitowa daga jikin yaron tayi banza da alamarin,
kuka sosai yaron keyi amma saboda kawaici Baffa yaki yunkurin karbarshi,
a ganinshi ma'u ma uwa ce a gareshi,
kuka Atika ta fara yi ta yafito Baffa da hannunta,

tsugunawa yayi a gefenta shima cikin kuka yace "bana gane abinda kike cewa,
cikin yaren fulani wanda ta fara fahimta kadan kadan tace " *SUWAIBA* Shine sunanta,,
sunan ummuna,,,
shi kuma *SAIFULLAH* in har ya kasance cikin rayayyu,
Ka kularmin dasu,
Amanarka ne su,
Dan Allah ka Nemi *Ateek* da Abbuna dan Allah..

kuka Baffa ya cigaba da yi sosai yana fadin bazaki mutu ba, ki yafemin dan Allah,
share mishi hawaye tayi tace "Inda zan tafi ya fiye min nan,
son samu ma in tafi da 'yarana,
Allah yayi bazan rayu dasu ba,

Muryar samarin sukaji a waje suna fadin ku fito mu tafi Muhammadu gasu nan dawowa,
da sauri ya mikawa ma'u jaririyar ya dauki Atika a kafadunshi suka bar gidan da sauri...



Tun a hanya ma'u ta gane namijin ya cika,
nan fa hankalinta ya kwanta sosai,
suna shiga gidan yayi saurin shimfidar da Atika ya dauko ruwa yana shafa mata,
salati ta farayi idonta ya fara kafewa,
ta kara cigaba da kiran sunan Allah,
ga jini har lokacin zuba yakeyi kamar famfo,
cikin tashin hankali yace ma Ma'u ta taimaka ta kawo maganin da take sha idan ta haihu,

kwantar da yaran tayi taje ta dauko MANDA mai tsinka jini ta jikata da yawa ta kawo mata,

dago kanta tayi tasa a bakinta ta dure mata shi tasss,

wani jinin ne ya kuma tsinkewa shaaaaaa,
nan da nan ganin Atika ya dauke, hannuwanta suka saki gaba daya,
babu abin da kake iya jiyowa sai sautin kukan jinjirar da maganar Atika,
*SUWAIBA* Sunan da take ta maimaitawa kenan hade da kalmar shahada.....



Mrs Tijjani Shattima.....
[04/03 11:57 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 2⃣7⃣
By *Aysha Ya'u Kurah*



*KADDARA*


_Ba wanda ke shigowa cikin rayuwarmu ba tare da wani dalili ba, tun daga ranar da aka haifemu har izuwa ranar mutuwar mu, da kowa muka hadu a wannan rayuwar, akwai wani zare da ya hadamu wanda bama gani,shi wannan zare da bama gani shi ake kira da *KADDARA*_





A gaban kabarin da ya binne Atika da Saif ya tsuguna yana kuka kamar ranshi zai fita,
Bingel ce zaune a gabanshi tana share mishi hawaye itama tana tayashi kukan,
"Baffa kayi hakuri, kaga ka rufeta tana bacci, ta huta da wahala da duka,
sannan ga yarinya ta haifa mana mai kyau sosai,
ka daina kuka ka barta ta huta, "Duka?
Wanene yake dukanta Zainabu, kafin Bingel tayi magana Ma'u ta fito tace "shirmen ta ne, wai dan ina mata tausa in kafarta ta kumbura shine take dauka dukanta nakeyi,
kallon Ma'u yayi yana son karyata maganarta, ya gasgata ta yarshi, nan take wata zuciyar ta kwabe shi da cewar Ma'u ba muguwa bace..



Saida ta gama tattaro kayanta gaba daya da na ya'yanta,
daga lungun gadonta ta dauko akushin dake dauke da sarkar Atika,
majina ta fara ja ta fito gurin Baffa cikin kukan munafurci tace "Allah sarki, ga sarkar Atika, yanzu sai na ajiye wa yarta, dan nasan yanzu mallakinta ce,
share hawayenshi yayi yace "nagode Ma'u, nasan *Suwaiba* baza tayi maraicin uwa ba, nagode sosai ya karashe cikin kuka hade da rungume jinjirar......




*MARAICI*



Tafi awa daya a zaune a kan pou, ga zafin rana, ga kuda sun baibayeta,, tun tana kuka ana jinta har ya daina fita,
Ma'u na can zaune a daki tana shan rake ita da Boddo da a lokacin take shekara biyu ciff,

dama pou din da kanta ta hau shi, dan tasan irin azabar da take sha a karancin shekarunta in tayi kashin a kasa..

Kamar an tsikareta ta mike a islamiyya cikin kawayenta tace zata je gida tasha ruwa,
Nafisa makociyarsu ce tace jirani in karasa rubutu a allon nan sai mu tafi,
zama tayi ta jirata har ta gama sannan suka wuce,
a kofar gida suka rabu kowa ya shige gidansu,
tana shiga tayi karo da suwaiba fuska kaca kaca da zufa da hawaye,
gyangyadawa takeyi, in tayi kamar zata fadi sai ta bude idonta ta cigaba da kukan,
cikin kunan rai Bingel ta isa gurinta ta dagata sukayi gurin rijiya, ta janyo ruwa ta wanke mata dukka jikinta,
tana yi tana kunkuni dan kar Ma'u taji,
tana gama wanke mata jiki ta goyata ta shiga daki ta samu Ma'u na kankarewa Boddo kai tana bacci,

Haba Goggo (sunan da yaran makota ke kiranta dashi) yanzu kina ganin yarinyar nan tafi awa zaune a kan pou baki wanke mata ba,
wallahi kiji tsoron Allah,
kullum a islamiyya ana fada mana muhimmancin rikon maraya,
nawa Suwaiba take da ta cancanci wannan azabar,
bakya t---- katseta tayi ta hanyar bige bakinta,
sai kizo ki dukeni,
nace kizo ki dukeni uwata,
sauke ta a bayanki dan ubanki,
fita Bingel tayi ta dauki hijab dinta ta koma islamiyya da suwaiba a bayanta tana share hawaye,
ta rasa irin wannan tsanar da take nunawa Suwaiba in suna kebe su hudu,
amma a gaban mutane da Baffansu bata da yar lele kamar suwaiba..

A kullum nunawa Baffa takeyi ita fa Suwaiba ta fiye mata ya'yanta, kuma koda wasa bata san kowa yasan ba ita ta haifeta ba,
shiyasa Baffa ke tafiya neman kudinshi a duk fadin nigeria hankali kwance,
ko ya dawo gidan baya samun damar daukarta saboda yadda Goggo ke makale ta a bayanta, saidai daddare in suna kwance ya shafa mata kanta yayi yar kwallar tausayin maraicinta da tunanin uwarta....


●●●●●●●●

Shekaru masu yawa sun shude cikin dadi ga masu sa'ar samun dadin,
sannan cikin radadin azaba ga marasa galihun rayuwa,
cikin wadannan shekarun Baffa ya samu cigaba sosai a rayuwarshi,
dan sana'arshi ta maidashi Kaduna inda yake tsara atamfofi a kamfanin yar masaka,
a lokacin yakan kasance da iyalinshi duk dare,
a nan ne ya dan fara dan fahimtar zaman da Ma'u ke yi da suwaiba,
a ko yaushe in ya fara wannan tunanin sai ya kauda shi saboda baisan sanya wasi wasi a zamanshi da Ma'u,
in ya ga suwaiba tayi shuru sai yayita kallonta ya rasa bakin da zai tambayeta,
wani lokaci in Ma'u ta lura da hakan sai ta sameshi ta fashe mishi da kuka tace "yarinyar nan bansan meyasa take yawon zama shuru ba, ni kaina inason a koda yaushe ta sake kamar yadda Halima take yi,
na rasa me ke damunta,
Baffa yakan yi murmushi yace "yanayinta kenan, haka Allah yayi ta shuru shuru,
mu bamu isa mu canzata ba...






*HADUWAR ALKHAIRI*


_Muna Haduwa da mutane ta hanyoyi daban daban, to kenan ta yaya muke haduwa da waďanda zamu gudanar da rayuwarmu tare dasu ma'ana *MASOYA*_



"Leemah Muhammad",
meye position dinki?,
harararsu tayi tace "meye naku a ciki, kowa yaji da kanshi,
dariya suka kece mata dashi hade da cewa bench warmer, daga ke babu wani,
Suwaiba dake tahowa da Akwatinsu na gwangwaro tace "Haba Amina Sa'ad, babu kyau fa, ilimi Allah ne ke bada shi kuma yayi hani da gori akanshi,
basu fasa dariyar ba suka ce barmu mu ci ma yar rainin wayan nan mutunci,
ita a ganinta tafi kowa,
sai anzo jarabawa ido ya raina fata ta fito da ziro me katon kanta,

Wasu gungun mata dake bayansu a karkashin bishiya suma suka kece da dariya hade da cewa su Leemah gayu ba brain,
sai ki dawo first term da juniors dinki, muko ay sai candy,
kukan takaici ta fashe dashi ta ruga bakin gate din makarantar, bin bayanta Suwaiba tayi da kayan niki niki masu masifar nauyi,
hakuri ta fara bata tace "karki

Please Login or Register in order to submit comment