Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kufce mata ta nuna dakinsu tace Badariyya zata kashe Nadee----

kafin ta karasa fadi Hilal ya murda kofar da karfi har yana cire handle din kofar,

lokacin da ya shiga kiriss ya rage Nadeeyah ta suma,
dan idonta da ya jike da hawaye ya fara lumshewa,

ita kanta Badar din kukan takeyi, amma zuciyarta ta ki bari ta saketa,
dama wannan damar take jira,
tsanar da tayi ma Nadeeyah mara misaltuwa ce,
gara ta kasheta kowa ya huta,
tasan hukuncinta kadan ne tunda bata kai 18yrs ba "a karancin iliminta na addini",


Iya karfinshi ya sa ya janye Badar, yayi wurgi da ita jikin drawer dakin har saida mudubin drawer ya fashe,

da gudu Musaddiq yayi kan Nadeeyah da ta durkushe tana tari dakyar,
rungumota yayi jikinshi yana jijjigata,
yana kiran sunanta da karfi saboda firgici......




Mrs Tijjani Shattimah......
[24/03 9:36 PM] Ummu Abdul 2: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣2⃣
By *Aysha Ya'u kurah*




Ganin yadda take lumshe ido ya sa Daddy cewa
"kawo ruwa da sauri Husnah,

rige rigen dauko ruwa sukayi ita da Anty Raly,


A kidime Musaddiq ya bude bakinta yana hura mata iskar bakinshi saboda yadda jikinta ya fara saki,

babu wanda a cikinsu ya ji, ko ya saurari irin dukan da Hilal yakewa Badariyya kamar Allah ya aikoshi,

Tun tana ihu anaji har muryarta ta dashe,
da gudu ta rarrafa ta rike kafar Daddy tace

"dan Allah Daddy kace yayi hakuri bazan kara ba wallahi,

finciko Hilal yayi yace "kin san Allah dama,
belt din hannunshi har ya tattare saboda azabar duka,

Badan tausayi ba,
sai dan saboda muryarta ta ishi Daddy yasashi cewa
"kyaleta Muktar!

Badan yaso ba ya kyaleta yana yi mata kallon ban gama dake ba,

a guje ta bar dakin tana ihun azabar haurin da yayi mata a baya,
a kofar shigowa palon taci karo da Su Mummy,

rungumarta tayi a tsorace tace "ke lafiya,
meya faru?

Kankameta Badar tayi tace

"zasu kasheni Mummy,
wayyo Allah bayana,

kallon su Mami da Anni tayi tace "ku shigo ciki ku zauna,

shigowa sukayi suka zauna,

Mummy taja hannun Badar suka shiga dakin,

Tsaye ta samesu dukkansu akan Nadeeyah da ta bude idonta tana maida numfashi,

Belt din hannun Hilal ta kalla rai a bace tace

"uban me tayi maka kayi mata dukan ficewar hayyaci,
abin da ya kawoka gidan nan kenan,

ya ilahi kayi min maganin yaron nan da duk in yazo gidana sai ya tayar min da husuma,
wannan wace irin mas----


dakata min!!


Daddy ya katseta fuskarshi a murtuke babu alamun wasa,

Naji alamar zuwan baki,
muje in samesu,
da kaina zanyi maganin matsalar gidana,
naji duk abin da ke faruwa tun zuwan Nadeeyah gidannan har kawo yau da idona ya gane min,

"Nadeeyah,

Mummy ta fadi a hankali,
ta kalli Nadeeyar dake kwance har lokacin a jikin Musaddiq,

Saida Daddy ya bar dakin ta tambayi Husnah abun da ya faru,

yadda abin ya faru ta fada mata, ta sakaya mata ainihin abun da ya tunzura Badar,

jiki a sanyaye ta fita a daki dan bata da mafita sai jiran hukuncin da Daddy zai yanke....




Ya Musaddiq..
Daddy yana kiranka,
Husnah ta fadi tana ajiye wayar da Daddy yayi kiranta,
maida kan Nadeeyah kan pillo yayi,
ya sauka suka fita a dakin tare da Anty Raly domin kaiwa baki abin ci da sha...



"Baki da karfi dama kika fara *Soyayya*
dagowa tayi ta kalleshi,

tsareta yayi da ido kamar bashi yayi maganar ba,

"ni bana soyayya, ta fadi hade da rufe fuskarta da hijab dinta,
faduwar gabanta ya karu sosai,

nade belt din hannunshi yayi yace
"in ma kinada niyyar farawa gara in tuna miki,
kije ki koyi fada,

dan in baki da karfi zaki cutu a soyayya,

ko tsoron maza bakya ji kin wani tsaya gab dashi,

to da bamu zo gurin ba me zai faru kenan?

Shi---
runtse idonshi yayi maganar ta makale a makoshinshi,
a zuciyarshi yana neman tsari da shedan dake kawata mishi abubuwa marasa kyau,


canza maganar yayi da cewa
"wuyan baya miki zafi,
in yana miki zafi kiyi magana a kaiki asibiti,

"Murya can kasan makoshi tace "zai daina in shaa Allah,
yana yi kadan kadan,

Dauko waya yayi a aljihunshi ya danna number Hinad,
tayi ringing sau biyu, a na uku ta dauka,

"ina Zee,?

jin ya ambaci sunan Zainab yasa ta mikewa zaune,

"bata nan ya Hilal,
sun fita da *Anty Mee*,

kashe wayar yayi ya kira Meerah taki dagawa,

wayar na katsewa tata ta shigo,
video call,
tsaki yaja ya dauka,

"Hi dear,

ta fadi tana daga mishi hannu,

"Hello Meerah kina lafiya?

Kamar yadda ka gani am very ok, but am missing yha, ta fadi a shagwabe,

kauda zancen yayi ta hanyar tambayarta

"where is Zee?


Juya wayar tayi zuwa gurin Su Adeel cikin muryarta mai dadi tace
"say Hi to Ya Hilal,
fitowa tayi a cikin motar wasan yara ta bude hannu hade da cewa "oyoyo!

Murmushi yayi yace

"yawo,

kika fita yawo baki fada min ba, nt good baby,

karbar wayar tayi ta bata fuska tace

"wayau zaka min ko,
dan kaga na hakura bana kuka har yanzu,
ka gudu ka barni baka kaini gurin Adda na ba,

Tun Nadeeyah na rike murnarta najin muryar gudan jininta,
har ta kasa tayi saurin zuwa gurinshi zata karbi wayar,

hada ido sukayi tayi saurin maida hannunta,

dariyar da bata fito fili ba yayi, sannan ya mika mata wayar,

da sauri ta karba sukayi ido da ido da abar kaunarta,

safa da marwa ta shiga yi suna hira cikin farin ciki harda yar kwallarsu,

murnar ganin yadda zainab ta koma ya hanata sukuni ta dinga yi mata tambayoyi,

sun fi minti bakwai suna hira sannan tace "ga Anty Mee ku gaisa,
tana kula damu sosai ni da Ya Hilal,


kallon juna suka yi na seconds kafin Nadeeyah ta saki murmushi tace "ina wuni,
amsawa tayi itama tana mata musayar murmushi,

yadda take jin sunan Nadeeyah a bakin Hilal ya tabbatar mata da lallai ganin da tayi mata yafi jinta,

domin duk kushen mai kushe bai isa ya nemo aibun Nadeeyah ba,

kyawunta na musamman ne,
gashin da yayi kwance a gefen farar fuskarta su sukara kara kawata kyawunta,

gashi in tayi murmushi ko dariya gefen kumatunta daya ke lotsawa can ciki,

haka nan Meerah taji wani abu ya darsu a cikin zuciyarta,

ita kanta Nadeeyah da bata cika lura da abu ko sanyashi a ranta ba taji wani abu kadan game da Meerah,

kallon farko da sukayi wa juna dukkansu suka fahimci jininsu yayi nisa gurin haduwa,

shurun da sukayi suna kallon juna ya sanya Zainab karbar wayar suka cigaba da hira,


Tunanin inda ta taba ganin Nadeeyah meerah ta shiga yi,

dakyar ta iya tunano sketch din da yayi a school as assignment,

duk da wancan da dan yarinta sosai amma ta gane ita ce,

lokacin duk wanda ya tambayeshi sai ya amsa cikin shakiyanci yace

"My dream girl,

a mafarki na na hadu da ita shine kamanninta suka mannu a zuciyata,

nan da nan kamannin Meerah suka canza,
zufa ta fara karyo mata tace "Zee bani wayar nan,

mika mata tayi ta zauna kusa da ita,

"Bani Hilal pls, tace ma Nadeeyah fuskar ta babu yabo babu fallasa,

sai a lokacin Nadeeyah ta waigo ta kalleshi dan ta manta ma yana dakin,

juyar da wayar tayi inda ake iya ganinshi ba tare da ta sani ba ta sunkui da kanta kasa,

wani irin kallo Meerah ta hangoshi yana yi ma Nadeeyah wanda bata taba sanin ya iyashi ba,

lokacin da ta mika mishi wayar bai kalleta ba ya fara kokarin kasheta,

da sauri Meerah tace

"Kangiwa kana ji na?

"Yes Meerah Turaki ina jinki,

yadda ya kirata ya tabbatar mata yana cikin shauki,

"ina kabar Musaddiq,
ta fada tana jin wani mugun kishi a cikin zuciyarta,

sai a lokacin ma ya tuna da Musaddiq yace

"auchh yana daki may be, ko Daddy ya aikeshi,
bari in dubo shi will call u,
ya katse wayar kafin ma ta sake magana,


Yana kashe wayar Husnah ta shigo dakin da gudu tana kiran Sunan Nadeeyah,


Hijab ta mika mata tace "yi sauri kisa,

kallon Hilal tayi tace "my PP,

zo muje kaga wani abun al'ajabi,


Maida wayarshi cikin aljihu yayi ya bi bayansu dan ganin abun da zata nuna mishi...



Ga Nadeeyahn nan....

Daddy ya fadi yana murmushin jin dadi,

Allah kadai yasan irin farin cikin da yake ciki,
gani yakeyi kamar da ita kanta Suwaibar yake zaune,

gefe Nadeeyah ta tsuguna tace "ina wuni,

Hannu Papy ya bude mata alamar ta iso gareshi,

kalle kalle ta shiga yi suka hada ido da Hafeez ya gyada mata kai yana murmushi,

mikewa tayi ta isa gabanshi tana mai mamakin kamannin,

tsugunawa tazo yi yayi saurin dagota ya rungumeta,

kukan da yake kokarin boyewa yaki boyuwa saida ya zubda su,


Damke Hannun Hilal dake yunkurin zuwa gurin Husnah tayi tace "Babanta ne fa,
twins din Mama Suwaiba,

cikin rashin fahimta yace "what, ba Baffa yace ya mutu ba,


Baffa dake zaune ya jiyo Hilal yace
"muma duk haka muka dauka Muntari,
ashe yana nan da ranshi,

kaddarar da ta boye mana shi ita ta sake hadamu dashi,

kallon Nadeeyah da ta kasa sakin jiki har lokacin Baffa yayi yace

"saki jikinki,
wannan uwa yake a gurinki, haka uba,
domin tare suka zo duniya da Mahaifiyarki,

kallonshi tayi sosai dan ta gasgata maganarshi,

tun daga hannayenshi har kafarshi saida ta kare musu kallon,

kyawawan yatsun kafarshi da ya zamto irin na Mamma da nata shi ya tabbatar mata da maganar Baffa,


wata irin runguma ta sake yi mishi tana kuka sosai a zuciyarta tana jero alhamdulillah,

ta kusa minti uku a jikinshi tana tunano rayuwar da sukayi da Mamma,

ji takeyi kamar dawo da ita Allah yayi cikin wata suffar,

saukowa a jikin Mami Ruwaidah tayi ta kama hijab din Nadeeyah tace

"let my Papy be,

karki bata mishi kaya da hawayenki,

Papy na baya son kuka,

dagashi tayi ta fara shafa fuskar Ruwaidah hade da rungumeta,

duk rashin son mutanen Ruwaidah ta kasa nuna shi ga Nadeeyah,

sai ma ce mata da tayi, "ki daina kuka mana,
na fada miki Papy baya son kuka,

ko so kikeyi yasa Yaya Jamal ya daura ki a bayan *OBENIZA*


Dariya Hafeez da Jamal suka saki dan sunsan ta da mugun tsoron obeniza,


share hawaye Nadeeyah tayi tace "nayi shuru,

hannu Ruwaida tasa a gefen kumatunta ta share mata wasu hawayen tace

"you are very beautifull,

Yaya Jamal batayi kama da *MALEEKA SAHEEB* ba,

kaga har one dimple din,

kallon ta yayi yaga tabbas akwai kamanni saidai Maleeka akwai wayewar larabawa yan drama sosai a tare da ita,

kaunar da sukeyi wa films dinta ya sanya kowa a gidan saninta...




Masallaci suka tafi dan yin sallar Magriba,


matan kuma duk sukayi a cikin daki,

Badar kuwa dakin mummy taje ta kwanta dan jikinta yayi tsami sosai,

har lokacin zubar hawaye takeyi tana kara jin tsanar Nadeeyah wacce take jin kamar da tsanar aka haifeta..

fada sosai Mummy tayi mata dan ta tsorata sosai bata san hukuncin da Daddy zai yanke a kanta ba...





Magana ce a bakin Papy amma kunya ta hanashi furta ta,

a yadda yake ji yanzu baijin zai iya koda kwana daya baisa duk su ukun a ido ba,

harda Zainab da ya ga hotonta tamkar shi ya haifeta dan babu inda ta barshi,


kallon Daddy yayi yace

"Alhaji mun gode fa,
gaskiya samun mutum irinka a wannan zamanin sai an tona,

ni inaga jibi zan koma Gombe,

nace --- ko --am ko---

dariya sosai Daddy yayi dan ya gano manufarshi,

kace ko zaka iya tafiya Nadeeyah ko?

Cike da jin kunya Papy yayi dariya yace

"kunya ta hana ni fadi,

Daddy yayi saurin cewa "na lura da hakan,

amma fa bazan baka ba ya fadi cike da zolaya,

Dariya Papy yayi yace

"ai yarka ce, ka fini iko da ita,

amma dan Allah ina rokon alfarmar tazo mana hutun wata daya,

cike da farin cikin girmamashi da akayi Daddy yace

"watanni ma Proff,

kar ka damu sun kusa zana jarabawar waec,
daga ta zana zata zo tayi maka hutu har sai ka kaji da ita,

"inaa bazamu gaji ba Anni ta fadi tana dariya,
tace "Allah ya kaimu lokacin,


Da sauri Hilal yace
"Daddy ayi mata transfer kawai tayi waec din acan,
gara ta dan zauna a can ta samu nutusuwar zana jarabawa,

"Bata da nutsuwa ne anan?
Baffa ya jeho mishi tambayar,

"a'a ina nufin zata ji dadin ganin su,
kuma zata fi yin karatu sosai acan,


Anty Raly da harbo jirginshi tace "babu inda zata,
bamu gaji da ganinta ba,
tayi zamanta har sanda Daddy yace,

badan Raliya ta girmeshi ba,
da babu abinda zai hana bai zageta ba,

murmushi tayi hade da mishi gwalon babu yadda zaiyi da ita,

ba yadda zaiyi haka ya hakura,
yasa ma ranshi zai tsoratar da ita sosai akan kula samari musamman Taheer da yayi mishi muguwar tsana a ganin farko...



Sai gurin tara da rabi su Papy suka bar gidan,

babu yadda ba'ayi Ruwaidah ta zauna ba taki,
duk da dan zaman da sukayi ta fara sabawa da Nadeeyah da Husna...

Nadeeyah ta kira wannan ranar da ranar farin ciki,

tabbas ta yarda in alheri zai doso ka sai ka hadu da bacin rai mai tarin yawa,

kwana tayi tana hamdala tana godewa Allah......





A daren Daddy ya yanke hukucin bazai cigaba da zama da Badariyya a gidanshi ba,

domin kuwa zata bata mishi zuciyar ya',

babu irin hakurin da Mummy bata bashi ba ya kekashe kasa yaki hakura kuma ya hada yi ma Badariyya gori sosai badan baya santa ba, sai dan ta hankalta ta dawo cikin hankalinta,



Wannan gori na rashin asali da yayi ma Badariyya,
ba karamin tsayawa a ran Mummy da Badar din yayi ba,

Ranar da Nadeeyah tayi kwanan farin ciki,
a ranar Badariyya kwana tayi kuka tana saka mugayen abubuwan da zatayi ma Nadeeyah......



Mrs Tijjani Shattima....
[24/03 9:36 PM] Ummu Abdul 2: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣3⃣
By *Aysha Ya'u kurah*






Da sassafe Mummy ta sa Husnah da Nadeeyah suje su roki Daddy akan ya bar Badar ta zauna a gidan,

ko da suka je dakin a bakin gado suka sameshi yana duba laptop dinshi,

gaisheshi sukayi suka hada baki suka ce

"Daddy dan Allah kayi hakuri ka kyale Badariyya,

Nadeeyah tace "sharrin shaidan ne Daddy,
baya wuce kan kowa,
in shaa Allahu zata canza,
kayi hakuri dan Allah,


glass din idonshi ya cire yace

"zanyi hakuri saboda darajar ki,

ke aka batawa kuma ke kika bada hakuri,

babu yadda zanyi tunda kin hakura ni ma dole in hakura,

amma sai na karya rantsuwata,
taje gidan Goggo tayi wata daya,


Mikewa sukayi suna godiya suka fita daga dakin,


Mummy da ta gama jinsu ta wuce dakin su Badar tace ta shirya zata kaita gidan Goggo tayi kwana biyu har Daddy ya huce,


kwallar da ta ciko idonta tayi saurin mayarwa,
ta mike sukuku ta fara fito da kayanta,

fita Mummy tayi dan bazata iya Kallon kayan tausayin nan ba,


karfe goma daidai bayan sun gama karyawa ta fito da akwatinta ta fitar waje,


shi kanshi Daddy saida ya dan tausaya mata saboda ta zama kamar jininshi,

halayyarta ce sam baya so tun tana karama,
shiyasa ko kadan baya bi ta kanta,


Har mota Husnah ta rakata itama tausayinta ya cika ta dan bata saba zaman ko ina ba sai gida,

ko gidajen su Anty Radiya bata zuwa da kwana saidai da yini,

bare gidan Goggo, ko toilet kadai ya ishi Badar....




A hanya Badar ta kalli mummy dake tuki tace "Mummy alfarma nake so kiyi min,


"ina jinki,

ta amsa idonta na kallon titi,


juyowa tayi tana kallon Mummy sosai tace

"Mummy aure nake son ayi min?

Kirrrrrr.....


Mummy ta taka birki ta kalleta tace
"aure?

Wani irin aure kuma,?


kukan munafurci ta fara kirkirowa tace

"Aure dai Mummy wanda akeyi,

dan Allah kuyi min aure,

sake tada motar Mummy tayi tace "to sai ki turo mijin da zaki aura tunda ke kika zabi hakan da kanki,


Abun da take jira dama kenan tayi saurin cewa
"ni bana tsayawa da saurayi,

ke zaki samo min Mummy,

dariya Mummy tayi tace
"yarinta hoo,

to karki damu bari in nutsu zan duba cikin ya'yan kawayena,


cikin sauri ta tari hanzarinta tace
"a'a Mummy,

gara dai ki nemo min a family,

kinga a gida ne kadai zanyi aure hankalin kowa ya kwanta,


Tsayar dasu traffic yayi Mummy tace "to Badariyya ina muke da aukin maza a family,

ko Hafeez kike so?

Allah ya kyauta tayi saurin fadi tana tofar da miyau waje,

to shi kadai ne sai Hilal da yake danki,

sai kuma
*MUSADDIQ*
Badar ta karshe da sauri,


Mummy ina son yaya Musaddiq, dan Allah ayi mana aure cikin gaggawa plsss,

faduwar gabar da tashin hankalin da Mummy ta shiga ba mai misaltuwa bane,

bata kara kallon Badar ba ta cigaba da tukinta,

magiya sosai Badar takeyi mata amma Mummy ko kallonta batayi ba bare tasan tana yi,

suna shiga gidan Mummy tasa Rilwanu daukar akwatin Badar..


Bayan Mummy tabi tana tambayarta dalilin da yasa bata san Musaddiq ya aureta,

a daidai gurin da zai sadasu da tsakar gidan Mummy tace

"kar in sake jin kin maimata maganar nan, bare har wani yaji!!

Tana kaiwa nan tayi Sallama ta fada cikin gidan,


Da gudu Badar tabi bayanta kamar zatayi kuka,

Mummy ta san sarai Badariyya naci gareta,

bata gama tunanin ba taji Badar na cewa pls Mummy,

a harzuke Mummy ta juya ta kalleta tace

"bani hankalinki nan,
aure ya haramta tsakaninki da Musaddiq,


Dariyar takaici Badar tayi tace "Haramta?

Menene ya haramta shi,
naga we are cousins saidai in baki son farin ciki na,


Buge bakinta Mummy tayi da karfi hade da cewa "bance karki kara min maganar nan ba,



Zafin buge bakin da zafin ganin zata rasa masoyinta yasata sakin wani irin Kuka,


Inda take Goggo tayo tana tambayar dalilin kukanta,

bata amsa ta ba ta cigaba da kukanta,


Mummy ce ta tsuguna a gabanta zata fara rarrashi,


kafin tayi magana ta katseta...

"Cikin kuka mai cin rai tace menene ya haramta aurena da Yaya Musaddiq Mummy,
menene shi,

a iya sanina bake kika haifeni ba,

nasan babu abin da zai haramta aurena dashi saidai in kema so kikeyi ki min gori akan asalina kamar yadda Daddy yayi m----

tassss..

mummy ta dauke ta da mari,
itama kukan ne ya subuce mata ta rungumota tace


"Allah ne ya haramta shi Badar,

Asalinki bazai taba zame min abin gori ba saboda ke din makwafi biyu gareki a gurina,


na diya da kuma kanwa,


ke kadai ce jinin yar uwata wacce nake gani inji dadi,

ban damu da ya kikazo duniya ba nidai nasan ina ganinki a matsayin LEEMAH,



Cike da shashsheka Badar tace "to mummy ki yarda ya aureni, walhy in na rasa shi zan iya mutuwa,


*Badariyya*


*NONO*
daya kuka sha da Musaddiq,
babu aure a tsakaninku......



Wani irin zaman dirshan Badariyya tayi wanda ya tafi da duk wani ganinta na dan lokaci kadan,

" *NONO DAYA KUKA SHA*

Kalmar ke ta mata yawo a kwakwalwarta,

duk da bata zuwa islamiyya sosai tasan haramcin auren,


wasu zafafan Hawaye ne suka dinga ambaliyar fitowa a idonta, "NA MUTU,
BANI DA SAURAN AMFANI,

kalaman da ta dinga fada kenan kamar zautacciya,

rungumeta Goggo tayi tace "bazaki mutu ba indai ina raye,


Musaddiq ne ki kwantar da hankalinki zan san yadda zakiyi ki aureshi,

anjima zanje gurin liman BADARU ya nemo wani hadisin da ya halasta aurenku,

tashi kije maza ki wanke fuskarki,


Tashi tayi kamar wacce kwai ya fashewa a ciki ta wuce bayin Goggo,

Tashin hankalin da ta tarar a ciki ya sanya ta fitowa da gudu tana haki,

"lafiya Suka hada baki suka tambaya,

ina fa Lafiya bayi yayi kaca kaca,

haba Goggo,
dan Allah bakya yin flushing ne?


Tabe baki Goggo tayi ta mikawa Zulai mai tayata aikin gida farar shinkafar tuwo dan ta gyara,

ta waigo ta kalli Badar tace "tunda kinzo sai ki gyara ai,

da tsufa na zanyi ta hakilon wankin bayi,

"ay da sai zulai ta wanke ta fadi kamar zatayi kuka,


murmushi Goggo tayi tace "kin sani sarai Zulai bata shiga min dakin miji bare bayi,

matse fitsarin mararta tayi tace "gaskiya Goggo bazan iya ba,
bazan iya zama har wata daya a nan gidan ba,

"to ya zakiyi,

haka nan zaki hakura,
kije can dakin zulai ta tayaki gyarawa dan duk yayi kura,

gani tayi kamar laughing stock suka maida ita ta nemi guri ta zauna kamar zatayi kuka tace

"Mummy dan Allah ki kaini gidan Aunty Raudha ko Anty Radiya,

"Lagos zaki bi Raudha,

Radiya kuma kinsan halinta,

duk yadda kuke shiri bazata raga miki gurin hidimar gida ba,

kiyi zamanki anan na lokaci ne,
Mummy ta fadi tana mikewa zata koma gida,


Sallama tayi ma Goggo wacce ke amsata da kyar saboda laifukan da tayi mata ciki harda korar Badariyya da mijinta Yayi...



Da kyar Goggo ta yarda Zulai ta wanke mata bayi,

sai a sannan Badar ta shiga a kyankyame tayi fitsari ta fito da sauri,

kan gadon Goggo ta kwanta tana maida numfashi....



"Fito kici Abinci,

Goggo ta fadi tana fiffita tuwon a cikin faranti,


badan taso ba sai dan tana jin yunwa ta sakko a gado ta fito waje,

yadda yaukin miyar ke bin hannun Goggo da zulai yasa komawa daki da sauri,

da karfi tace

"Tuwo da rana tsaka Goggo,
kuma miyar yauki kamar majina ta karashe fadi kar zatayi amai,

wannan wace irin jarabawa ce,

kudi ta fito dashi a jakarta ta kira Rilwanu ya siyo mata Abinci a restaurant mai kyau....


ko kallonta Goggo batayi ba ta cigaba da kai lomar tuwonta...


Tunanin Musaddiq kwanta takeyi,
ta ya za'ace babu aure a tsakaninsu,

dan kawai sun sa nono daya,

Allah yasa Liman ya gano wani hadisin da ya halasta hakan,
in ba haka ba walalhi daga ita har shi saidai su mutu ba aure,

dan duk wacce yayi yunkurin aura sai ta kasheta.....




********

Danna wayarshi yayi ya kira layin wayar da ya ba Nadeeyah a karo na ba adadi,
har lokacin ba'a kunna wayar ba,

juyi kawai yakeyi a kan makeken gadonshi,

gaba daya ya rasa abinda yake mishi dadi,

tun dawowarshi daga gidan su Nadeeyah ya kasa sukuni,

ko abinci kwakwkwara bai iya kaiwa bakinshi ba,

bacci kuwa sai dai dan barawo ne ya saceshi bayan ya idar da Sallar asuba,


Ya gama sawa ranshi sha biyu nayi in yaji ba'a kunna wayar ba zai koma gidan koma me zai faru ya faru,

Soyayyar Nadeeyah na neman yi ma zuciyarshi illa,

yama za'ayi ya iya rayuwa babu ita,

kallon kofar da aka murda yayi yaga Momma ta shigo dauke da kayan break fast,


"Gud morning my Tee,

Morning Momma, kin tashi lafiya?


Lafiya kalau nd u?


Nt bad ya fadi hade da mikewa zauna,



'Tee me yake damunka,
yau baka fito ba kwata kwata,
sannan jiya ina lura dakai dakyar ka tsakuri abinci,

yar hirar da muka saba ma baka zauna munyi ba,
tell me,
meye matsalarka,


Bazai iya boye komai na daga dangin farin cikinshi ko akasin haka daga gareta ba,

gyara zama yayi ya rike hannuwanta,
raunanannun idanuwanshi suka tara ruwa yace

"Zan rasa ta Momma,

Nadeeyah zatayi ma rayuwata nisa,

Zan rasa farin cikin da ya ziyarceni a lokacin da na fidda ran zuwanshi,


Fuskarshi ta tallaba da hannayenta biyu cike da tausayin shi tace

"bazaka rasa ta ba,

baka taba neman abu ka rasa ba Tee baza'a fara akan wannan ba da yardar Allah,

ka kwantar da hankalinka kaci abincinka kamar ka sameta ka gama,

Anjima da yamma zan kira *Kawu Tidjani* in fada mishi ya taho muje nema maka aure,


Murmushin farin ciki yayi yace thank u Momma,
Allah yayi miki sakayya da aljanna firdaus,

Ameen my Boy,
tashi maza kayi wanka ka shirya ka tafi gym wannan tumbin da ka fara ajiyewa ka gyarashi kafin ranar aurenka,

shafa tumbin yayi yana dariya yace "ina tumbi anan Momma,

sai dai in so kikeyi ya shafe da bayana,

dariya tayi hade da mikewa tace "in kayi wanka kazo zan aikeka,

gyada kai yayi yace "to

Please Login or Register in order to submit comment