Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kowa ya huta da mutum marar amfani iri na...


Cikin kuka yan uwanshin ke kiran sunanshi suna hanashi ji ma kanshi ciwo,
duk suna tsoron matsawa kusa ya illata su,

Mummy kuwa da tasan duk itace silar hakan zama tayi a bakin kofa tana kuka ririsss,

Cikin zafin nama Daddy ya karaso cikin ďakin ya isa gaban mudubin ya juyo dashi da karfi ya daukeshi da kyawawan mari har guda uku,
yana shirin sake yin na hudu Baffa da Papy suka hanashi..



Cire hannun Papy Musaddiq yayi a jikin Daddy ya kai hannun fuskarshi ya cigaba da marin kanshi,

"Slap me to death Daddy,
Dan Allah ka mareni har sai mutuwa ta riskeni,
i'm dead already,
numfashin ne kadai ya rage,
wallahi ko baka kasheni ba,
ni zan kashe kaina....




Da karfi ya janyo gudan jininshi cikin kirjinshi ya rungumeshi tsamm yana kuka mai taba zuciya,

Sai a lokacin zuciyar Musaddiq ta karye ya soma rero kuka mai cike da sambatu.....




Mrs Tijjani Shattima.......
[22/06 10:21 PM] +234 807 161 1811: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 7⃣5⃣
By *Aysha Ya'u kurah*





Jugummm jugummm..
sukayi a parlon kowa da abun da yake sak'awa a cikin ransa,
fitowar likitan da Hilal ne ya sanya su nufarsu da sauri,

"Doctor yaya?
Hope all is well?
Daddy ya tambaya cike da damuwa,
Guri likitan ya samu ya zauna haďe da ajiye akwatin taimakon gaggawarshi,

"Ka kwantar da hankalinka Alhaji,
komai lafiya kalau,
jinin da ya zubar ne kaďai ya sanyashi zama weak,
amma ya farfaďo, saidai ya samu bacci, yana bukatar hutawa da kulawa sosai..
yana kaiwa nan ya kalli mutanen dake zaune a parlon,
ganin rabinsu duk mata ne yasa shi mikewa yace
"Alhaji anjima ka sameni a office, akwai abin da zamu tattauna, Allah ya bashi lafiya ya karashe yana dafa kafadun Daddy haďe da yin hanyar waje....
Kasa zama Daddy yayi ya bi bayanshi da sauri dan baijin zai iya kaiwa anjima baiji abinda yake son su tattauna ba wanda ya tabbatar akan ciwon ďanshi ne....

Hilal kuwa zama yayi a can gefe, hawayen dake zarya a idanuwanshi sun kafe saboda tsananin tashin hankali
"Ta ina zai fara,
wace hanya zai bi dan ganin ya samar wa Musaddiq abun da yakeso ba tare da hankalin kowa ya tashi ba,
yafi karfin awa ďaya yana tufka da warwara amma bai samo mafita ba,
runtse idonshi yayi saboda yadda yake jin nauyi a kan kirjinshi, dakyar ya iya mikewa da taimakon Maleekah suka koma can dakin da Musaddiq yake....


Cikin kalaman hikima irin na likita, Doctor Lawal yake wa Daddy magana,

"Ya taba samun attack a yanda na lura,
saboda halin da na riskeshi a yau ban taba tunanin zai rayu ba..

Alhaji Mukhtar,
ďanka na cikin critical condition, zuciyarshi na iya bugawa at any time,
dan Allah ku kula a daina sanyashi cikin damuwa sannan a taimaka a samo mishi abinda yake so,

Cike da damuwa Daddy ya dubi Doc Lawal bayan ya gama mishi jawabi yace
"Samun abin da yake so wannan na Allah ne,
nidai zanyi kokarin ganin ya daina shiga damuwa da bacin rai...

Shawarwari Dr Lawal ya bashi kafin suyi Sallama....


Parlon ya koma jiki a sanyaye yana tunanin kalaman Doctor, yadda ya barsu a parlon haka ya dawo ya samesu saidai wannan karan suna dan tattaunawa da su Papy...

Bayan ya zauna ne  suka shiga kum kum wannan na cewa wannan tayi magana suna ki,
a tare suka daure dan suna ganin hakan shine kaďai mafita ga rayuwar Musaddiq domin zaifi samun kula daga gurin uwa..

"Daddy dan Allah kayi ma Mummy afuwa,
ta gane kuskurenta,
dan Allah kayi hakuri ka sassauta mata...

Kallon 'ya'yan nashi yayi fuskar nan babu walwala zaiyi magana muryar Baffa ta katseshi....

"Me ya faru Rilwanu?

Me ya samu gidan nawa?

To to to gamu nan zuwa yanzu da yardar Allah ya karashe haďe da mikewa,
mikewa su Daddy sukayi suna tambayarshi ko lafiya?

"To nima dai ban sani ba,
Rilwanu yace inzo gida ba lafiya, a hanzarce suka fita dan zuwa gidan suga abinda ke faruwa..

Mummy dake can sama gurin Musaddiq itama tayi saurin mikewa ta biyo bayan Radiya da ta kawo mata rahoto...


Da sauri Malam Mato mahaifin Rilwanu ya debo ruwa ya mikawa matarshi dake tsaye kan Goggo tana taimaka mata,

wani irin ihu takeyi tana fisgar gashin jikinta haďe da firzar da ruwan da ake zuba mata a baki,

"Gishiri,
Gishiri,
hakan ta dinga faďi tana zaro harcenta da yayi fari tass kamar mayya,

Gishirin rilwanu ya debo a cikin buhu ya kawo musu dan a tunaninsu ciwukan jikinta zata sawa,
yana kawo mata ta yafa kusan rabin kofin a bakinta,

A firgice suka fara kokarin kwace kofin suka kasa saboda a wannan lokacin karfin ba ďaya bane,
ko jariri ne wanda bashi da zunubin komai sai ya fuskanci barazanar wannan rana bare mutum irin Goggo wacce ta naďi kayayyakin bil adama marasa adadi...

Sarketa gishirin yayi ta shiga tari kirjinta na ďagawa sama kamar zai rabu da jikinta,
yaye zanin jikinta tayi saboda tsabar azaba ta mike ta fara zubar da kayan dakinta tana ihu sosai..

Halacci da iyayen Rilwanu suke ganin an yiwa dansu shi ya hanasu barin dakin duk ko da irin warin dake fita a jikin Goggo...

Wasu gungun hotuna ta zubo har gaban malam mato, saura kiris glass din da ya fashe ya taba kafarshi,
da sauri ya matsa baya ya tsuguna ya fara tattara hotunan ya umurci Rilwanu da matarshi da su riketa,
yana gama tattara hotunan ya ajiyesu a kan table zai komo gurinta..

Tsayawa yayi cakk ya waigo da sauri ya sake duban hoton saman wanda bashi da kala samm, dauko hoton yayi jiki na rawa yace "Ma'un Ukari,
*Nankwat Manasir*
shigowar su Baffa ne yasashi mayar da hoton da bazai taba manta ranar da akayi shi ba,

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun..
shi kawai yake maimaitawa cikin ranshi tare da tunanin inda mutanen nan masu matukar karamci suka san mace marar imani irin Ma'u...

Mummy ce ta karaso ciki ta dauko zani dan rufe mata tsiraicin jikinta tana kuka sosai,

Baffa kuwa hannunta ya rike yana faďin
"Ma'u zauna kiyi ta salati,
a yanzu ihu ba naki bane,
da karfinta ta fisge tayi hanyar waje tana ihun da ko gida uku ne tsakaninku zakaji ta,
da azama suka bita suka rikota suka maidata daki suka garkameshi dan yadda take jiyar da mutane ciwo....


Malam Mato kasa rike abun yayi a ranshi yace

"Marar lafiyar nan itace Ma'u wacce naga hotonta da kananan yara biyu?

Da sauri Baffa yace "Eh itace, ka santa ne?

Juyayi Malam Mato ya shiga yana tunanin ta yanda zai fara sanar dasu abubuwan da ya sani shekaru da dama wanda babu wanda yasan dasu sai ubangijin talikai sai shi da ita kanta Ma'un,

Nufar inda yake Baffa yayi zaiyi magana sukaji ihun Goggo tana faďin
"Na shiga uku,
ku kira min Bokan Ukari yazo ya tamaikeni,
yagar naman jikina akeyi,
wayyo,
wayyo,
ku kirashi yazo ya taimakeni,
yayi min alkawarin bazan mutu  ba,
yayi min alkawarin karashe rayuwata har kowa ya mutu ya barni..

"Mai kashewa shi ke tsoron mutuwa,
shin akwai adalci a cikin wannan?
Malam ya Mato yayi tambayar ba tare da jiran amsar kowa ba,
da sauri ya nufi dakin ya buďeshi domin a yanzu samm ya daina tausaya mata...

"Ai bai kamata wanda yake da karfin zuciyar sanadiyyar rayukan mu'imunai da dama tsoron mutuwa ba,

*JUMMA'ATU BABBAN RANA*

Ranar yin katako daga kauyen ukari zuwa Gembu,

*Ma'u yar gidan Manasir*...

Tunaninki zai iya tafiya shekaru hamsin da doriya suka wuce,
in kin manta ni bazan manta ba,
zan fara tuna miki in yaso sai ki karasa da bakinki..

Tunda ya fara maganar azababben jikin Goggo ya saki,
maganarshi tafi ciwon azaba...

"Harďejo,
Musulman kauyen Gembu,
suna Sallar Jumma'a...
ko zaki iya tuna abun da faru a ranar,
cikin dabara yace

"Faďin ainihin abin da ya faru shine kadai zai taimaki rayuwarki ki dawo kamar yadda kike da, sannan babu zancen mutuwa har sai dan kanki kinji duniyar ta isheki...

Saboda jahilci da kuma tsabar son duniya, Goggo ta fara faďin dukkan labaran da suka faru a baya,
har kawo mutuwar Atika da yunkurin kashe Papy da kuma irin ukubar da ta bawa Mamma Suwaiba, har yadda tayi ta raba Daddy da Mamma suwaiba ta hanyar asiri,
wannan confession din tayi shi ne cike da sa ran ciwon zai barta sannan bazata mutu ba,
ta sa rai bayan ta rayu zata yi asirin da zai mantar dasu komai...

*Goggo dai tazo duniya zama ne, tazo ne kawai ta karaci rayuwarta cikin asarar da lokacinta gurin yiwa wasu sihiri domin kawai gamsar da zuciyarta*....


Ajiyar Zuciya Malam Mato yayi ya kalli duk mutanen gurin da suka mutu a tsaye saboda jin rashin imanin Goggo,

"Alhamdulillah da Allah ya taimakeni ta faďi da bakinta domin inata tunanin yadda zan gamsar daku,
a lokacin da Ma'u ta sanar da yan ta'addan nan cewa akwai Musulmai a kauyen Gembu, bani da bakin magana domin na riga na ce musu ni ba musulmi bane, bayan mun shiga garin na saukesu sai na nufi can wani guri na samu maboya,
ganin irin kisan gillar da sukayi ma musulman kauyen yasani barin garin Taraba gaba dayanta saboda tsabar tsoron wata rana wannan abun zai faru dani ko wani nawa,
a kullum kwanan duniya cikin shekarun nan sai na tuno da wannan al'amarin,
rashin sanin inda zanga mai aika aikar yasani barin wa cikina komai,
da nasan a gidan nan take wallahi da kaina zan mikata ga hukuma su hukunta ta tun da sauran karfinta,
amma yanzu ko an mikata ga hukuma babu amfani domin hukuncin ubangiji ya fara tun anan duniya kafin ta riskeshi a lahira....

Wani irin kuka Baffa ya durkushe a gurin ya fara yi cikin kunan rai, shekara da shekaru yana tare da wacce ta rabashi da ahalinshi,

a harzuke bayan kukan ya lafa ya mike ya nufi inda take zaune tana yakushin jikinta ya kaiwa wuyanta shaka..


A gaggauce su Papy suka share hawayensu suka nufi gurin Baffa, dakyar suka iya rabashi da Goggo wacce take ihun ceton rai..

"Karka zama irinta Baffa,
sai ka kwashe dukkan zunubbanta,
ka barta da abunta ta girbe abun da ta shuka da hannunta..

Daddy ne ke magana cike da takaicin haďa iri da wannan zuri'a karo na ba adadi,
dole ya dinga fuskantar kalubale kala kala a cikin tashi zuri'ar...



Mummy samm ta kasa motsawa daga inda take,
juya maganganun ta dingayi a cikin kwakwalawarta,
rashin imanin mahaifiyarta har ya kai haka,
tabbas dole ta dinga ganin jarabawa kala kala,
Allah bai bata uwa ba,
wannan wacce irin uwa ce wacce sam babu kwayar halittar imani a cikin zuciyarta...


Zaburar da Goggo ta sakeyi ita ta dawo dasu daga duniyar sake saken da suka tafi,
babu wanda yayi yunkurin bin ta sai Papy da Anni,
kafin su kai inda take har ta kusa kofar gida....

Da gudu wani mai baro wanda ya lodo karafe da langar kwanon aluminum tsofaffi ya taho dan wucewa yana jin wakarshi,
tsayawa yayi a gefen gidan su Baffa dan siyan rake ya parka baron a gurin,

Fitowar Goggo keda wuya wata langa mai tsini ta kama yaďuwar fatar cikinta,
da yake gurin gangare ne nan fa sukayi kasa ita da baron kaifin langar yayi fata fata naman cikin Goggo,


Innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai mutanen gurin suka fara faďi haďe da yin kanta da gudu,

Dakyar aka samu aka zare wasu parts din langar a jikinta,
har lokacin tana da rai sai ihun azaba kawai takeyi cikin sarkewar murya,
da sauri Papy da me baron suka dauketa suka yi gurin mota da ita, jinin dake zuba a jikinta ba jinin wasa bane,
ga tsagu da cikinta ya samu can ciki ana iya hango wasu daga cikin kayan cikin,
suna isa gurin motar Papy ya kalli Daddy da suka fito gaba dayansu yace

"Bude motar Alhaji muje,

Ďauke kai Daddy yayi yace
"Ba'a mota ta ba,
kallon Raliya yayi dan ita kadai ce tazo da mota yace
"Kema in kika dauka ban yafe miki ba,
yana kaiwa nan ya shiga motarshi yayi gaba ba tare da ya kalli kowa a cikinsu ba,
samm babu digon tausayinta a ranshi bare har ya kai ga taimakonta,

Papy ya rasa yadda zaiyi dan tashi motar na gurin Hafeez, motoci suka fara tsayarwa na haya,
duk motar da ta tsaya in taga yanayin Goggo sai tayi gaba dan kar a bata musu mota,

Cikin tsananin tashin hankali mai baron yace
"Ko zamu dauketa cikin baro na, ni zanyi tukin sai ku biyomu a mota,
da wannan shawarar aka dauki Goggo aka sata a cikin baron bayan an shimfida bargo aka rufe mata jiki,
tausayin rai da matsawar Anni su suka sa Baffa bin bayansu,
gudu sosai mai baron yakeyi dan yana tsoron mutuwarta a sanadiyarshi,
go slown da suka tarar shi ya sanya shi yin yanke ta wani lungu dan su isa asibitin da wuri,

Yana shiga kwanar yayi tuntunbe da katon dutse wanda hakan yayi sanadiyyar subucewar baron yayi wani kwaron kudiddifi da Goggo,
ihuu ya saka yabi bayan su,
yana isa yaga baron makale  jikin wani dutse ita kuma Goggo kwance kan wani katon dutse kanta yayi fata fata,
cike da tsoro yaron yaja baronshi jiki na rawa ya bar gurin dan kar hakan yayi sanadiyyar shiganshi wani hali...



Motar da suka hawo na biyowa lungun sukaga mutane sunyi dafifi a gurin kudiddifin,
da sauri Papy ya dakatar da mai motar ya sauka yana tambayar abun da ke faruwa,
labarta mishi wani yaro yayi sannan yace sunbi mai baron basu ga inda ya shiga ba..


Cikin tashin hankali Papy ya biya wasu yara majiya karfi yace su cirota,
koda suka cirota har lokacin bata mutu ba saidai ta jikkata iya jikkatuwa,
babu ta inda jini bai zuba a jikinta,
fashewar da kanta yayi ya sauya halittar fuskarta,
azabar da take sha a lokacin har gara ta gwammaci mutuwa da rayuwa,
to saidai inda matsalar take bata san me zata tarar bayan mutuwar ba..

*(Allah a'alamu, shi kadai yasan hukuncin da zaiwa bayinsa masu mugun hali iri ko kuma kwatankwacin na Ma'u, Bawa bai isa ya yanke ba domin shi Allah mai gafara ne a lokacin da yaso, ta yiwu mutum ya sha iya wahalarshi a nan duniya a ranar da zai koma ga Allah, ta yiwu kuma sai anje can, wannan Allah buwayi gagara misali shi kadai yasan daidai.... Allah ka datar damu da aljanna firdausi, ka tsarkake zuciyarmu kasa mufi karfinta)*



Kudi mai yawa Papy ya bawa mai motar sannan ya yarda zai dauki Goggo a boot,
asibiti mafi kusa suka isa saboda jinin dake zuba a jikinta,
kin karbarta sukayi dan acewarsu yafi karfinsu a wuce general hospital,
Mummy dai kuka kawai takeyi tana fadin
*Astagfirullah ya Allah*,
mai motar da aka sake roka ya wuce dasu General hospital,

koda suka isa emergencyn kanshi a cike yake da marasa,
dakyar aka samu aka shiga da Goggo wacce babu abunda bakinta ke furtawa sai wayyo na shiga uku,
Boka Garbuji kazo ka taimakeni,
duk yadda likitoci suka kai da kokarin tsaida jinin abin yaci tura domin zuba yakeyi kamar ana kara wani a jikinta,
allurar bacci sukayi mata dan ta samu tayi bacci suyi mata aiki,
itama allurar sam taki aiki a jikinta,
sai ihu kawai takeyi,
a haka sukayi mata aikin azaba na karaďe dukkan sassa na jikinta,
bayan sun gama suka barta a gurin suka bada alluran da za'a siyo ko zata samu bacci,

Anyi mata allurai uku amma samm taki rissinawa bare tayi bacci,
ga fusge fusgen azaba da takeyi tana kiran sunan bokayenta ko zata samu taimakonsu...

*A wannan ranar Goggo bata san ko waye bazai tseratar da mutum daga abinda dake rubuce ba, domin in har ganyenka na zaman duniya ya bushe har ya kai ga faďuwa kasa to fa babu wani tsumi ko dabarar da zai hanaka faduwa kasan nan kaima*...




Har karfe goma na dare Goggo na abu daya,
ita bata rintsa ba ita bata bar na kusa da ita sun runtsa ba,
duk yadda ahalinta suka so tayi salati abin yaci tura domin suna diga aya zata dura musu ashar tace basu san abun da take ji ba..

*Kwatan kwacin hakan bayin Allah da kika sa aka kashe suka ji, su da basu dauki zunubin kowa ba ma kenan kin wahalar dasu, bare ke da kika kwashi na mutane marasa adadi...*




Karfe 2:40 na dare jikin Goggo ya kara tsamari,
domin a yanzu samm ta kasa kwanciya,
jikinta kuwa babu komai sai rigar da aka saka mata,
ihuu kawai takeyi wanda yake ratsa ko ina na asibitin,

Mummy da ta rage ita kadai ta dinga zubar da hawaye haďe da ambaton Allah..


Wata zabura da Goggo tayi babu wanda ya ankara sai ganinta akayi a can waje asibiti domin ita Mummy mai jinyarta ta tafi makewayi..

Ihuu kawai takeyi tana tsallen azaba tana kiran sunaye kala kala,
dinkin da akayi mata a ciki nan take ya warware saboda rashin kwarin jikinta da kuma sabontakar dinkin,

Warwarar dinkin tayi daidai da tahowar motar wasu gayu wadanda suka sha giya sukayi tatil,
saboda yanayin duhun garin da kuma yanayin buguwarsu sai jin wani kara sukayi wanda yasasu taka birki,
shurun da sukaji babu wanda yayi magana yasa drivern yin ihu haďe da sake kara volume din motar fiye da da ya takata suka wuce,

securityn dake dutyn dare ne ya fito yana ihun neman taimako, ihun da yakeyi shi ya janyo hankalin Mummy da attendance din dare wadanda suke yawon nemanta a harabar asibitin,
da gudu suka nufi gurin shi suna tambaya ko lafiya,
ganin ya nufi wata katangar dake tsallaken asibitin yasasu binshi a baya suna daďa tambayar ko lafiya,
suna isa gurin tambayarsu ta makale a makoshi domin Goggo suka gani hange jikin tsinin karfen katangar wanda ya burma cikinta har baya,

Kuka sosai Mummy ta sanya tana kiran sunanta domin har lokacin da sauran ranta tana ta gumshekar azaba wacce tafi kama da ta mutuwa,
Da kyar security's din ciki da suka fito suka zarota suka nufi ciki da ita,

Karasawarsu ciki keda wuya ta damki cikin inda ciwukan suke haďe ciza harcenta da karfi har saida jini ya fito,
ihun karshe da ta saki yayi daidai da daina motsa kafarta da kuma sakin dukkan jikinta,

Ajiyar zuciya wata nurse tayi taja zani ta rufeta ta kalli Mummy tace

"Saidai hakuri,
ta mutu!!

Bazan mutu ba Goggo ta faďi a wahalce haďe da yayewa ta damki hannun nurse din,
irin jinin da ya zuba a jikin Goggo ya isa dukkan karfinta ya kare,

A tsorace Nurse din ta fincike hannunta taja da baya da sauri, dan minti ďaya baya tabbas taga mutuwa a tare da Goggo..



Sunan Mummy ta fara kira a hankali saboda duhu ya fara ziyartar ganinta,
daga nesa Mummy ta amsa dan tsabar tsoron irin rayuwar da Goggo ta ďibo,
gaba ďaya yanayinta ya canza daga farar bafulatana wacce tsufa ya tattare fatanta zuwa wani irin yanayi na ban tsoro,
jinin dake zuba a jikinta gaba ďaya ya kafe dan babu ragowarshi a jikinta,
karfaffiyar zuciyarta wacce rashin imani ya kesashar ita kadai ke aiki a jikinta...

Babu wanda a dakin bai bata mutuwa ba saboda irin ukubar da tasha kuma take kan sha,
a lokacin nan mutane da dama sun sake tsorata da Allah domin shine ke da ikon yin wannan abun al'ajabi,,

Sake kiran sunan Mummy Goggo tayi a karo na uku,
a ďarare ta matso kusa da ita tace "Gani,

"Yanzu duk wannan azabar da nake ciki bazaki iya zuwa ki kiramin wani bokan ya fidda ni ba,
duk abubuwan da nayi a baya saboda ku nayi shi,
amma ni yanzu abu ďaya da zaki min in fita daga wannan azabar bazaki iya ba.... 
babu wanda ya fahimci abinda Goggon ke faďa sai Mummy domin ita kadai ce a gefenta,

Cike da damuwa Mummy tace "Shin har yanzu baki saduda kin san Allah daya bane?
Har yanzu kina tunanin akwai wanda ya isa ya hanaka yin aure bare ya hanaka mutuwa,
lallai kuwa in dai wannan azabar da kika sha ta tsayin watanni bata nunar miki hanyar Allah ba babu wata azaba da zata maidaki daidai,
Mutuwarki itace alheri ga dukkan yan uwa musulmi,
domin ke ďin anno-----

wata damka Goggo ta kai mata wacce idonta bai nunar mata gefen da ta kaita ba saboda duhun da ya fara rufesu,
a hanzarce Mummy ta mike haďe da fincikewa wanda hakan yayi sanadiyyar kai Goggo kasa,
zafin faďuwar ya sanyata sakin ihun karshe wanda daga shi bata sake cewa komai ba sai fisga da jikinta yakeyi yana dukan gadon..

A wannan lokacin mai daukar rai ya ziyarci tsohuwa Goggo wacce tayi kisan ban mamaki kuma take tsoron mutuwar kanta,
a lokacin Goggo ta dandanin azabar da matattun da suka mutu a sanadinta suka dandana,
babu rayuwar da bata tunano ba kafin ganinta ya dauke baki ďaya....

*(Kullu nafsin za'ikatul maut,, Duk mai rai sai ya dandani mutuwa)*...


*Anzo a banza an koma a wofi...*

Furucin wata tsohuwa ne doki kunnen Mummy dake zaune tana kuka tana jiran azo daukar gawar Goggo,

Wani sabon kukan ne yazo mata tanata adduar nemawa mahaifiyarta sassaucin ubangiji,

*(Allah ghafuru raheem*)....



Mutuwar Goggo ta taba makusantanta,
domin ko babu komai rai daraja gareshi duk ko irin bakin halin wannan ran..


A ranar da akayi sadakar uku Baffa yasa aka kwashe kayan Goggo aka kaiwa tsofaffin mabaratan bakin titi,
kayan kudinta ne kadai ya bawa Goggo domin itace magajiyarta shi kuwa a bangarenshi yace baya bukatar komai nata domin ta fita a sahun matarshi kafin rai yayi halinsa...





***********

Har gurin mota Daddy ya raka su Anty Saude domin hirar da ta jashi da shi ba wacce zasu katseta bace,
Cike da damuwa  ita ta katse hirar bayan ta ajiye jakarta a bayan mota,

"Ya jikin Musaddiq?
Hope da sauki,
Hafeez ke faďa mana jiya ashe bai ji dadi ba kwana biyu,

Cike da basarwa Daddy yace "Alhamdulillah, jiki kam da sauki sosai,
dan har ya fita ma yau..

"To mashaa Allah Anty Saude tace cike da farin ciki,
jikanka dai yana neman haddasa min fitina, daga yaga zamu fita zai fara kuka saidai a barshi a gida,
yanzu dai na barsu da Taheer zasu zo zuwa anjima suyi muku gaisuwa sai yayi dabara ya barshi can gurin Nadeeyah,

"Murmushin dattaku Daddy yayi wanda ya tuno mata da samartakarshi yace
"Babu komai,
nasan rashin sabo ne,
wata rana ba zaiso ya bar gidana ba,


"In shaa Allah Anty Saude ta faďi tana dariya,
motar ta shiga tana faďin
"Kyan alkawari dai Kyari, ina nan ina jiranka,,

Baki da matsala, in shaa Allahu gobe zanzo ai ni na faďa.. ya faďi cike da jaddadawa...

"To saika zo bari mu wuce Allah ya kara hakuri,

Ameen Daddy ya faďi haďe da rufe kofar motar...





A tare motar su shigo cikin katafaren gidan,
sai da kowacce tayi parking a mazauninta sannan suka fito rike da kaya niki niki..

Cike da ladabi Kamal ya gaisheta bayan ta sakko daga cikin motar,

Amsawa tayi hannunta nakan kayan tace
"Har kun dawo?
Allah yasa dai bakuyi shirme a list dinnan ba,

Girgiza kai Taheer yayi cike da gajiya yace
"komai muyi momma,
muje ciki ki gani,
My dear kawo ledar nan ya karashe yana duban Junior dake rike da leda yana ja,

"Noo Daddy,
muje kaima naka akwai nauyi,

daya daga cikin mai musu aiki ne ya karaso ya karbi dukkan kayan harda na hannun junior,

sai a lokacin suka saki ajiyar zuciya suka wuce ciki ko wanne na dauke da gajiyar kasuwa data zaban kaya..




Buďe kayayyakin Shareefah takeyi tana duban Anty Saude dake cire warwarayen hannunta tana kallon kanta a mudubi,

"Kaya Machaa Allah Saude, yanzu abu kadan ya rage a gama, sai kuma su *plaķiù'oòl..*

Nasa Raahilar masu gari ta siyo ta taho dasu,
naso ayi bikin nan a can Agadez saboda a nuna su ga dangi kuma ayi biki kashi biyu,
na Yareemah mai jiran gado da kuma daurin auren tunda abun duk phàmèè ne,
to Taheer ya hana yace dole ayi shi anan,
amma ki faďa mishi daga an daura zamu wuce can sai ayi biki domin bazai yiwu bikin yazo min a yar karo ba alhali dukkansu nawa ne,
dole a buga tambura agadez ta dauki bikin jinina,
shakikai na wadanda zan bugi kirji ince su din nawa ne... 



Warwaron karshe Anty Saude ta zare ta dawo kusa da Shareefah,

"Karki damu yar uwa,
yin bikin a nan ya zama dole, bayan an daura sai kiyi yadda kike so babu wanda zai hana, kwana nawa ya rage,
kedai kisa a fara shirye shirye a can kafin isowarmu..

Wannan ba matsala bane,
biki kam za'ayi shi wanda ba'a taba yin irinshi ba a tarihi.. Shareefah ta faďi zuciyarta cike fal da murna...




**********

Tsakurar indomien dake gabanta takeyi a hankali tana kaita baki,
tunanin abubuwa da dama sun cika zuciyarta,
ga tausayin halin da Musaddiq

Please Login or Register in order to submit comment