Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

damu, kisa ma ranki zaki iya next term din,
dan an miki repeating ba yana nufin bazaki iya bane,
zan tayaki addu--- katseta tayi cikin kuka tace "rike nasihar ki da adduar ki,
ba na ja miki kunne akan babu ruwanki dani ba?, wai ma ban hanaki jerawa tare dani ba,
ni sa'arki ce da zaki dinga jerawa dani har kiji abinda ake cewa a kaina,
wallahi bari muje gida,
sai na miki dukan tsiya,
yar iska matsiyaciya kawai,
Ajiye kayan suwaiba tayi tace "kiyi hakuri dan Allah, wallahi bazan kara ba, kinga in zaki min hukunci kiyi min anan, amma dan Allah karki bari Goggo taji,
tsaki taja mata tayi gaba a zuciyarta tace "wallahi bazan sake dawowa makarantar nan ba, tunda karatun ba dole bane...



Abokina!!
irin wannan kallo haka, ai sai kasa ta fadi, ji yadda ka kafeta da ido,
in dai wadancan biyun ne, to sun saba,
kullum leemah cikin masifa take ita kuma suwaiba tayi ta tausarta,
i think immediate ne,
dan uwa daya uba daya suke, dalili kenan da yasa na daina sa musu baki,
karka shiga fadan yan uwa,
and kasan me ke yawan sasu fada,
ita waccen,, ya nuna suwaiba, tana da masifar kokari, ita kuma dayar in kana neman dakiki ajin farko in ka sameta to ka rufe kofa,
ja motar muje na dauko takardun,
tada motar yayi har lokacin idonshi nakan Suwaiba,
yana isowa saitin da take ya kashe motar ya fito,
kallonshi abokin wanda ya kasance malamin makarantar yayi yace "Lafiya ina zaka,
bai saurare shi ba ya zagaya gurin Suwaiba dake tsaye a gurin kamar an kafeta,
tana tunanin irin hukuncin da zasu yanke mata a gida,
addua takeyi a zuciyarta na Allah yasa yayarta na gidan, ita kadaice zata iya taimkonta daga ukubar da zasu mata,

kamar daga sama ta jiyo sallamarshi,
kallonshi tayi ta kauda kai tace "Ameen wa alaikum salam, ina yini,
wani sanyi ne yaji ya ratsashi na jin daddadar muryarta,
Amsawa yayi yace "lafiya kalau malama Suwaiba,
dago kai tayi cike da mamaki tace "laaa sunana,
a ina ka san sunana?, daga kanshi sama yayi yace "wahayi akayi min da sunan,
kuma aka ce inzo nan in sameki, rike baki tayi ta daga kai sama tace "a can sararin samaniya?
Gyada kai yayi yana murmushi yace "kwarai kuwa, ko kina tantama ne,
cike da nutsuwa tace "kwarai ba tantama nakeyi ba,
yarda ce banyi ba saboda na karanta a littafi,
manzanni kadai ake wa wahayi, kuma nasan a cikin duniyar nan da azzalumai sukayi yawa babu tabbacin samun wani annabi,
kuma ai annabin Allah shine karshen annabawa,
dan Allah in ma gatse kakeyi to ka daina domin ina tsoron wani ya samu zunubi ko yayi shirka domin ni,
"Ya ilahi ya fadi a zuciyarshi ya kalli Abokinshi dake cikin mota yace "kaji Kalamai daga bakin fasihiyya ko Abbakar,
kallon motar tayi tace "laa uncle Abu ina wuni,
fitowa yayi a motar yana dariya yace "lafiya kalau Suwaiba,
anyi hutu ana jin dadi za'a koma gida ko,
murmushi kawai tayi a zuciyarta tace wani hutu, ita da za'a barta ta kare rayuwarta a makaranta ai da taji dadi,
katse mata tunani Abbakar yayi yace "wannan abokina ne, sunanshi *MUKHTAR KYARI* ganin irin masifar da yar uwarki take miki ne yasa shi tsayawa ya baki shawarar ki dage ki dinga ramawa,
kyawawan mata da tsiwa aka sansu, ke kuma hakurin naki yayi yawa,
kallonshi Mukhtar yayi yace "to sannu koma mota,
nagode da ka tayani fada,
dariya sosai Abbakar yayi ya wuce cikin mota yana fadin 5mins na baka,
kasan we have alot to dzoo,
a gaugauce ya tambayeta ko zai iya sauke su a gida daga nan sai yaga gidan nasu,
kallon Leemah tayi da ta waigo tana hararar su tace "bari in tambayi yar uwata,
ajiye akwatin tayi a kasa yayi saurin daukarsu ya zuba a boot, ya shiga motar yace "abokina kai zaka musu magana su shiga dan dakyar waccan masifaffiyar ta yarda su bimu,
magana daya Uncle Abu yayi musu suka shiga motar,
a kofar gidansu yayi parking,
da sauri Leemah ta bude motar ta shige gida gudu,
jiki na rawa Suwaiba ta bude motar tace "ina akwatinan mu? Bude boot din yayi ya fito da akwatinan yace "muje in rakaki, nauyinsu yayi yawa,
a'a tayi saurin cewa, hade da mika hannu,
Dan Allah ka rufa min asiri, fada za'a min a gida,
"let her go kyari,
bakasan condition din da take ciki ba,
sakin akwatinan yayi tayi saurin dauka ta ruga cikin gidan da gudu,
bin ta yayi da ido har ta kure cikin gidan sannan ya shiga motar ya tada suka wuce....




Mrs Tijjani Shattima.....
[04/03 12:44 PM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 2⃣8⃣
By *Aysha Ya'u Kurah*





Tun daga zauren gidan take jiyo masifar Ma'u hade da kukan Leemah,
sharri kala kala tayi mata sannan tace "ta hadu da saurayi tanata shige mishi har ta rokeshi ya kawo su gida,

innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai suwaiba ke furtawa a cikin ranta,
da sallama ta shigo gidan ta ajiye akwatinnan ta tsuguna har kasa ta gaida Ma'u,
matsowa kusa da ita tayi ta daga hannu ta kwada mata mari,

Halima sa'arki ce da zaku hadu da kawayenki kuyi ta cin mutuncinta,
ke dan uwarki ke kika bawa kanki kokarin,
au dan na yarda kun shiga makaranta daya,
shine zaki nuna zakewa ki nuna kinfi ta iya komai,
bulala Leemah ta miko ma Goggo tace "ga yaren da tafi ganewa nan Goggo,
karbar bulalar tayi ta fara zuba mata tana cewa uban waye ya saukeku a kofar gida,
yanzu dan rashin kunya kina ganin yayunki basuyi aure ba ke har kina da tsaurin idon tsayawa da saurayi,
to wallhi in na kara ji da ganin kin tsaya da saurayi tun yanzu sai na miki illah,
banason rashin ido a gurin y'a mace wallahi,
bulalar da zata kai mata na karshe ne ya sauka a jikin yaya zainab (Bingel) da ta shigo gidan a lokacin,
dago suwaiba tayi tana share mata hawaye itama hawayen take tace "haba Goggo, kowa ba rabonshi yake samu ba,
yanzu wannan abun da kikeyi shine Allah zaisa mu samu miji ko me,
ki duba kiga yadda na girma na rika a gida babu mashinshini, haka Halima babu wanda ya taba furta mata kalmar so duk ko da irin kyan da muke dashi,
a cikin mu Allah ya sanya suwaiba nada farin jinin da duk ta fita sai ta samu mai cewa yana sonta, ai sai mu godewa Allah,

wani kukan ne ya kufce mata na tuno saurayin da tayi arangama dashi a bikin Nafisa jiya mai cike da barkwanci da halin kirki,
a zuciyarta tana takaicin yadda yayi mata nisa ta ko wani irin bangare saboda matsayin shi,
daki taja suwaiba suka shige ta bar Goggo nata banbamin bala'inta,
itama tana takaicin bakin jinin da yaranta suke dashi,
babu irin maganin da batayi musu ba dan su samu mashin shini amma a banza,
to ita kuwa ta yaya zata yarda ta bar suwaiba ta kula samari alhali yaranta duk ba mashin shini, masifar ta cigaba dayi kamar zautacciya zuciyarta na mata zafin balbalin wuta.....





Albishirinki Ma'u!!!
Kai yau cikin farin ciki nake wallahi,
Goro ta fadi tana zuba mishi ruwa a kofi,
baibi takan ruwan ba ya kwala kiran suwaiba,
da sauri ta fito yace "akwai bako a waje kira Yayarki kuje ta rakaki, kuma kar ku dade,

cike da faduwar gaba Ma'u tace "baka ce min komai ba kuma kace yara su fita,
yanzu sai aga yara sun fita zance kai ba abin kunyar ka bane,
"shiyasa nace Zainabu ta raka ta ai, saboda idon mutane,
zuciyar ma'u kamar zata fito tace "to meye albishir din,
gyara zama yayi yace "kinajin labarin Alhaji Garba Kyari mai fata ko?, gyada kai Ma'u tayi kirjinta na tsananta bugawa,
yace "to danshi ne yaga suwaiba yake so,
kuma da aure, nace yaje ya turo magabatanshi mu tsayar da maganar aure,
wallahi Ma'u bakiji dadin da nakeji ba,
ko ba komai zan fara aurar wa, mutanen unguwa zasu bar zundena,
yake ma'u ta shiga yi tana fadin madallah Allah ya sanya alheri, Ameen.. Baffa yace ya mike ya wuce daki zuciyarshi wasai bai ko lura da yanayin ma'u ba,
shidai a yadda yakeji a ranshi, yasan suwaiba ta gama samun gatan duniya saidai kuma ta roki lahira....



Tun da suka fito Bingel tayi tozali da Mukhtar cikin kayanshi riga da wando fela,
gashin nan Afro ya tajeshi ya mike sosai, hankalinta yayi kololuwar tashi,
shine,
shine wanda ta ganshi a gidan Nafisa,
karasowa yayi gurin kafin su iso yace "barka da fitowa sahibar ruhina,

ya ilahi, suwaiba kamar zata nutse ta damki hannun yayarta hade da rufe fuskarta cikin hijab,

no, no, no,
wannan kunyar cutar dani zatayi,
kiyi hakuri ki dago kanki ki kalleni,
sakin hannun Bingel tayi ta ruga cikin gida da gudu ta barsu a waje da Bingel da tayi tsaye tana kallonshi kamar mutum mutumi,
Hannu yasa yayi kasss a fuskarta yace "ina wuni yar uwarmu,
firgigit tayi tace "ni ya kamata in fara gaisar dakai,
murmushi yayi yace "kuma sai kika barta ta gudu baki rike ta ba,
dariya tayi tace "kasan yarinya ce, kunya gareta,
amma bari in tayata tadin,
cikin nutsuwa ta dinga tambayarshi halayarshi da abubuwan daya kamata ta sani,
sun dade suna hira yana fada mata yadda yake ji a cikin rashi game da kanwarta,
da zai tafi ya bukaci ta kira mishi ita su yi sallama,
sallama tayi mishi ta wuce gida ta iske suwaiba a zaure tace "jeki kiyi sallama dashi, ko so kikeyi yayi fushi,
dakyar ta fito ta tsaya nesa dashi tace "ina wuni,
jingina yayi jikin stalet dinshi yace "bazan amsa ba,
ashe ma dai ni dodo ne ban sani ba,
rufe fuskarta ta sakeyi tace a'a kayi hakuri,
murmushi yayi yace to nayi, ya bude gaban motar ya dauko leda yace "gashi inji mamanki tace wai a kawo wa yarta,
dakyar ta karbi ledar ta ruga cikin gida da gudu,
murmushin shaukin samun farar mace kamila yayi sannan ya shiga mota ya tada ya wuce....



Bayan zuwan magabatan Mukhtar aka saka ranar aure sati biyu,
babu irin hidimar da baya ma Baffa saboda so da kaunar da yake yi ma suwaiba,
ita kuwa Bingel ramewa ta soma yi saboda tunanin mukhtar da ta sanya kanta ciki,
bangaren Ma'u kuma sai hada tuggunta takeyi wanda zai hana auren,
gori kuwa babu wanda bata sha daga makota,
da abun ya isheta ta zauna wani dare ta dinga rusar kuka, Halima da itama kishin suwaiba ya dameta ta zauna tana tayata kukan,
a haka suwaiba da ta dawo gurin mukhtar ta samesu,
kudin da ya bata ta fito dashi ta mikawa Ma'u tace "Goggo gashi yace in kawo miki kudin walima,
amsa tayi ta ajiye a gefe,
cike da fargaba tace "Goggo me ya sameki,
rungumar munafurci Ma'u tayi mata tace "Suwaiba ya zanyi da raina,
ya zanyi da gorin mutane,
yanzu kina karamar kanwar yayarki ace kinyi aure ita bata yi ba,
kinsan dole abun ya dameni,
dole ne in shiga cikin kunci da takaici saboda nasan babu wanda zai aureta yanzu, matso da ita ta kuma yi tace
"kinsan dai ni na haifeku dukkanku ko? Gyada kai Suwaiba tayi tace "eh, to yar albarka ina umurtarki da ki janye auren nan akanki ki barwa yayarki,
nasan Allah zai dubi abin alherin da kikayi ya baki wanda ya fishi,

jiki na rawa suwaiba tace "Goggo, dan Allah kiyi hakuri,
wallahi ina sonshi,
kuma shim--- ya isheni,
yanzu duk halaccin da Bingel tayi miki tun kina yarinya har kawo yanzu baki gani ba,
duk irin kaunar da ta nuna miki bazaki dubashi ki sadaukar mata da mijin da zaki aura ba,
kuka ne ya kufcewa suwaiba tace "hakkinta ne Goggo,
Hakkinta ne a matsayinta na yayata ta kula dani kuma ta sadaukar da komai nata a gareni,
wallahi da zan iya da na rabu dashi na bar mata shi amma bazan iya---- wani wawan mari Ma'u ta kai mata,
tace "lallai rashin kunyarki ta tumbatsa,
a gabana kike cewa kina son namiji,
lallai ďan da baka haifa ba dole ya nuna shi ba naka bane,

dammmmm....

suwaiba taji a kirjinta,
kalaman Goggo suka sa zuciyarta ta fara yawo a cikin ma'ajiyinta........




Mrs Tijjani Shattima
[05/03 11:10 PM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* 2⃣9⃣
By *Aysha Ya'u Kurah*




*_Duniya kurkukun mu'imuni, kuma Aljannar kafiri, akwai mutanen da Allah swt yake Halittarsu a cikin duniyar nan ba domin suji dadi ba, sai dai domin rayuwakansu su zamto izina ga wadanda sukazo domin zamanta na din din, mai hankali shi kadai yasan duniya ba gurin jin dadi bane, lahira itace matabbata, sannan akwai tarin tanadi da Allah yayi wa bayinshi masu hakuri, tanadin Allah shine tanadi Allah ya sa mu dace,_*


*RABUWA DA MASOYI*


Mikewa tayi ta isa gabanta tace "Goggo, dan Allah karki ce bake kika haifeni ba,

Kukan Munafurci Ma'u ta saki tace "Suwaiba yau kin sani na fada miki abinda ban taba tunanin fadin shi ba,
yau kin kaini makura har na fito miki da *SIRRIN BOYE*
kuka ne ya kufce ma Suwaiba tace "wacece mahaifiyata?
, a ina take?,
nan take shaukin son taga mahaifiyarta yazo cikin zuciyarta,
rungemeta Ma'u tayi sosai tace "Tambayar bata da amfani tunda bata raye,
ni nan ni na raine ki tun kina jarinta da taimakon yayarki,
munsha gwargwarmayar rayuwa gurin baki tarbiyya,
musamman yayar taki da kike yunkurin k'in sadaukar mata da soyayyarki,

cikin kuka suwaiba tace "innalillahi wa inna ilaihir rajiun, kara kankameta Ma'u tayi tace "duk abin da kika ga na miki a baya bawai dan bana sanki bane, nayi shi ne dan samar miki tarbiyya mai kyau da amfani,
kiyi hakuri,
kiyi hakuri ki bar mata,
"labarin karya ta shirya mata akan mahaifiyarta sannan ta karashe da fadin irin kular da zainab din tayi mata,
kukan bai fasa zubowa a idonta ba tace "Allah ya jikan mahaifiyata Goggo, Ameen Ma'u ta fadi sannan tace "nasan zaki bar ma yar uwarki mijin da zaki aura ko? Nasan zuciyar zinari gareki,
girgiza kai Suwaiba tayi tace a'a Goggo,
yaudara ce wannan,
bazan iya hakuri da shi ba,
domin kuwa Allah sai ya tambayeni,
yasa rai da aurena kuma kawai sai in ce mishi ya auri yayata,
hakan bazai yiwu ba,
tana karashe fadi hade da tashi ta fita zuciyarta na tariyo mata irin ukubar da tasha a hannun Goggo,
ba tun yau take tunanin cewa ba Goggo bace ta haifeta,
gashi yau sanadiyyar Mukhtar an warware mata komai,
hawayen idonta ta share dan tasan in shaa Allahu ta kusa daina zubda su,
tasan Mukhtar zai zame mata komai da ta rasa a rayuwa..

Dakinsu ta shiga jiki a sanyaye,
a zaune ta tarar da zainab da ta gama sauraron duk abinda suke cewa,
tafarfasa zuciyarta takeyi saboda yadda ta dauka Suwaiba zata iya barin mata komai take bukata a rayuwa,
lallai a yanzu ne ta fahimci cewa uwa daya ya wuce wasa,
tayi imanin da Leemah ce zata yarda ta barta Mukhtar dan kar ta kunyata,
wata irin tsanar Suwaiba ce ta darsu a zuciyar zainab wacce dama ta dade ana mata aikenta, sai yanzu shaidan ya samar mata mazauni a zuciyarta,
barka da hutawa yaya, suwaiba ta fadi tana cire hijab dinta,
uhmmm!!
kawai taji tace sannan ta mike kafarta a kan gado,
gabanta ne ya fadi dan bata saba ganin hakan a gurin yar uwarta ba,
gefen gadon taje ta tsuguna tace "yaya ko na miki wani abu ne,
juya mata baya tayi tace "karki dameni suwaiba,
kaina ke ciwo,
nan take idonta ya ciko da kwalla ta mike ta fita kofar dakin,

kuka sosai ta zauna tana yi, zuciyarta sai kai kawo takeyi akan maganar da Goggo tayi mata,
sam bata damu da sanin cewa ba ita ta haifeta ba, dan ta dade da sanin uwar da ta haifeka baza tayi maka irin wannan tsanar ba,
abin kawai da ya daga hankalinta shine rashin sanin uwarta da kuma rashin adduar da bata samu daga gareta a matsayin sadaka a kabarinta..
yanzu kuma babban tashin hankalinta bai wuce na rashin walwalar da ta gani a gurin yar uwarta mai kaunarta ba,
tana wannan tunanin taji Ma'u tazo ta wuce cikin dakin...



Yanzu dai kinga halin wacce kika fifita akan yar uwarki,
kindai gani da idonki,
kuka zainab ta fashe dashi tace "Wallahi Goggo ina mutuwar kaunar muntari,
na dauka zan iya hakuri in bar mata shi,
amma yanzu da naga aski yazo gaban goshi walhy bazan iya hakura ba,
duk abinda da kika ga ya dace kiyi Goggo, nima ko meye zan yi walhy,
murmushi Goggo tayi a zuciyarta tace "wuya makarantar kare, waya fada miki borno a gabas take,
kwantar mata da hankali tayi tace gobe zatayi komai da tasan zatayi ta rabasu,,,

wani sabon kuka ne ya kufcewa Suwaiba da ta gama sauraren kalaman Goggo,
mikewa tayi ta je bakin pampo tayi alwala ta dawo dakin,
a zaune ta samu Leemah da yaya zainab suna magana kuskus,
darduma ta dauka ta fito waje tayi raka'a biyu ta zauna a gurin tana kai kukanta gurin ubangiji....





Baffa na fasa auren muntari! Wata iriyar faduwar gaba Baffa yaji wacce zata iya sanya zuciyar bawa tsayuwa,
hade rai yayi kamar bai taba dariya ba yace "wace irin magana ce kin fasa aure?, dama yardar aurenki da rashinshi duk a hannunki suke,?
dama ke kike da ikon zabawa kanki miji bani ba,
dan Allah ya kawo miki miji shine har kike da bakin butulce mishi,
lallai suwaiba ban taba tunanin baki da hankali ba sai yau,
idan kika sake furta min wannan kalmar walhi sai na lahira yafi ki jin dadi,
tashi ki bani guri sakarya kawai..
tashi tayi ta fita tana kuka a ranta tana fadin nima ba asan raina bane Baffa,
ina gudun a sabauta rayuwata da ta muntari ne,
ya zanyi in fahimtar dakai akwai matsalar dake shirin bullowa,
ya zanyi ka fahimci matarka wacce na dauka uwa marar kaunata Guba ce a cikin rayuwarka,
da wadannan tunanin ta isa zauren gidansu ta zauna akan dakali ta cigaba da kuka,
saida ta dauki kamar minti talatin a gurin sannan ta tashi ta wuce makaranta...



A dimauce ya dago kai ya kalleta sosai yace "maimaita abin da kika fadi,
cike da dakiya tace "kayi hakuri dan Allah ka janye batun auren mu da kai,
wallahi zuciyata ta kasa aminta da yin rayuwar aure dakai,
share zufar da ta keto mishi yayi yace "karyane! Wadannan kalaman ba naki bane,
ko kina da ciwon aljanu ne ban sani ba?
Hawaye ne ya fara zuba a idonta tace "Gaskiyar magana nake fada maka daga cikin zuciyat---- karya kikeyi! Ya daka mata tsawar da sake sanya ruwan idonta ambaliya,
sauke muryarshi yayi yace " baki da lafiya suwaiba,
kin gane ko, jeki gida ki kwanta,

"lafiyata kalau ta fadi murya na rawa,
ka fahimceni, rayuwar aure bazata yiwu da zuciyoyin da basu gama yarda da junansu ba,
nayi duk iya kokarin da zanyi in tusa sonka a raina na kasa,

kallonta yakeyi da manyan idanuwanshi da suka rine zuwa jajaye,
"me yasa kike kuka?
Karki damu share hawayenki,
share hawaye tayi da sauri, yauwa ya fadi hade da cewa kar in sake ganin kukan nan kinji ko?
Gyada mishi kai tayi tace "na daina,
"kin min alkawari?
Eh "Nayi!

Yauwa matar Muntari, kin gane ko,
dama ni bana son ki soni,
son da nake miki ya isa,
ni fa ina sonki ne badan ki soni ba,
so karki damu zanyi maneji,
ko ba komai in na dawo gidana nasan da abin da nake so zan fara tozali, gyara tsayuwa yayi yace "baki san ke din sarauniyata bace, in kina gurina a killace to bani da wata damuwa,
dan haka bana san jin komai je ki gida ni zan tafi,
ko kina son wani abu?
Wani kukan take kokarin sake yi yace "mutum dai yasan hukuncin mai saba alkawari! Nidai ba ruwana, kamun Allah bana mutum bane,
share hawayen tayi da sauri ta ruga gida..

Kwantar da kanshi yayi akan sitiyarin motar zuciyarshi na azalzala da kalamanta,
ya zaiyi in da gaske ya rasa Suwaiba,
da wace mace zai iya rayuwa in ba ita ba,
sake kallon kofar gidan yayi sannan ya tada motarshi ya wuce gida jikinshi duk a sanyaye....




Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba,
Suwaiba ta daina fita gurin Mukhtar,
ko yazo saidai ya karaci tsayuwarshi saboda rashin baffa a gari,

Ana jibi daurin aure ne ta fito ta sameshi,
a wannan ranar saida ya nuna mata irin nashi bacin ran kafin ya tafi ranshi a bace,
yana mata uzurin yarinta da kuma bata san meye kalmar so ba,
gidan su Abbakar ya wuce direct,

cikin bacin rai yake magana yana fada mishi yadda al'amura suka sauya cikin kankanin lokacin,
"Abbakar kai kadai zaka mata magana,
wallhi ina shiga cikin matsanancin hali in naji tace "bazata aureni ba,
yarintar ta bata gaya mata gaskiya, in ba haka ba sai ka kalli mutun kace baka kaunarshi,

Shiryawa Abbakar yayi suka wuce gidan su suwaiba,
dakyar ta sake fitowa, har saida ma'u tace ta fita,
ita duk tunaninta asirinta ne ya kama Suwaiba,
bata san kauna ce ta sanyata hakura dashi ba,
tasani tunda sukayi alwashi zasu iya rabasu kuma ta zauna a gidan su gasa mata aya a hannu,
gara ta hakura dashi ya auri yar uwarta ko zasu samu maslaha da ita,
dan a yan kwanakin nan ta jigata da rashin kulawar da Zainab take bata..




"Abokina yayi laifi ko?
Rufe fuskarta tayi murya na rawa tace "A'a,
to meya faru?,
fada min a matsayina na uncle dinki,
kuka ta fara yi kamar yarinya karama tace "nidai kawai bana sanshi ne, kuma yaki ya taimakeni yace ma Baffa bazai aureni ba,
runtse ido Mukhtar yayi kirjinshi kamar zai fado kasa,
matsowa kusa da ita yayi kamar zaiyi kuka yace "nasan bakya sona,
kiyi hakuri ki bani amanar rayuwarki,
nayi alkawarin koya miki sona,

wani abu taji tun daga kanta har tafin kafarta,
"meyasa Ya Allah,
meyasa na samu gatan da zaisa in zama lele kuma yanzu gatan zai subuce min,
meyasa,
wannan shi ake kira da Dandani haukaci,
a fili kuma kukan dai ta cigaba dayi tace "ni bazan iya jure zama dakai bane,
uncle Abu dan Allah kace yayi hakuri ya nemi wata,
"bazanyi hakurin ba,
Abbakar yarinyar nan bata da hankali,
rabu da ita kazo mu tafi,
in an daura auren ta mutu,

kafadunshi Abbakar ya dafa yace "calm down kyari,
hannun ya ture kafadun shi yace "dan taga ina lallaba ta ne, wallahi abinda zai hanani aurenki saidai mutuwa,
ko kuma dama bani da rabon zama dake har mu samu 'ya'ya, amma in har inada jini a jikinki sai kin aureni (Rabon yayi muku wannan farraqun),
yana kaiwa nan ya fita yana huci kamar zaki,

Duk irin lallashin da uncle Abu yayi mata ta kafe akan ita bata sanshi,
har yaji haushi sukayi sallama,
kafin yakai kofar fita yaji ta rushe da kuka mai ratsa zuciya, tsayawa yayi yana kallonta a ranshi yace tabbas akwai matsala, haka nan bazata ce bata son kyari ba,
koma menene Allah ya kawo mata mafita....




*RANAR AURE*


Tun da suka idar da asuba Suwaiba ta wuce islamiyyarsu ta zauna can wani lungu da babu mai zuwa gurin,
kuka takeyi sosai hade da karatun qurani,
tasan in har ba'a ganta ba to tabbas baza'a daura mata auren ba...



Zufa Baffa ke sharewa yana fadin "ina tace miki zata,
kukan munafurci Ma'u ta kirkiro tace "bata fada min ba,
nidai naji Leemah na cewa Suwaiba tace "in aka mata aure saita kashe kanta,
salati Baffa ya saki yana fadin yarinyar nan so takeyi ta kunyata ni,
duk irin mutanen da muka tara a kofar gidannan so takeyi lallai sai na kunyata,
Matsowa kusa dashi ma'u tayi tace "tunda tace bata sanshi a hakura mana,
Wani kallo baffa yayi mata yace "so kikeyi in zama karamin mutum,
kinsan adadin manyan masu kudin dake zaune a kofar gidannan suna jiran a daura auren nan,
kawai kuma sai inje ince musu amarya ta gudu,
Sake matsowa tayi

Please Login or Register in order to submit comment