Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

indo ta faďi tana dariya,

"Whatt?
Mijinta?


"Kwarai kuwa,
mijinta nake, ko kinada matsala da wannan me?


Wani irin sarawa taji kanta nayi tayi saurin zama akan kujera,

"Ni zaka ciwa Amana Shamsu?

"Auren ne cin amana? Inna indo ta tambaya tana zama a gefen Radiya,


"Ke dallah can rufe min baki,
ina magana ne da mijina ba dake gayyar na aiya gayyar tsiya ba..



"Aheeee yayanki ma gayyar tsiyace tunda abun da yayi ni hi yayi su,



"Shamsu kayi warning matar nan,
kasani sarai bani da mutunci,


"Rashin mutuncinki ya tsaya akanki,
kinga na samu nutsuwa a gidana,
karki zo ki nemi tarwatsa min,


Fatima shiga da yara ciki,
ki sirka min ruwan wanka kuma ki jirani a bayin..


A fusace Raudha ta mike ta fisgo hannun Adeel haďe da kwada ma Fatima mari,
nuna ta da yatsa tayi tace
"in baki fita a cikin gidannan yanzu ba, wallahi sai na kasheki, zo ki wuce, munafukai maciya amana,


Marin da tayi mata shamsu ya mayar kan fuskarta yace

"saidai ke ki fita,
in har bazaki yarda da fatima a matsayin matata ba saidai ki fita ki barmin gida,


"Wallahi shamsu kai baka isa ka haďa ni kishi da wannan kucakar ba,
wallahi kayi kaďan,



Rungumo Fatima yayi sosai yace
"wannan kucakar ta shayar dani kaunar da wayayya ta kasa shayar dani,
ta kula da mahaifiyata cikin kankanin lokaci,
mai rabani da ita saidai mutuwa...



"To ko saidai ka zaba koni ko ita... Radiya ta faďi tana huci..


"A bayyane yake Radiya,
na zabi Fatima,
saboda ta haďa abubuwa da dama,
wayewa ce bata da ita,
zan siyo mata a kanti tunda akwai su da dama kantin wayayyu,
zan maida ita first class lady wacce zakiyi mamakinta,
ban ce zan sake ki ba,
amma in kina bukata ina iyawa,


"Aiko dole ka sakeni,
me zanci da kai,
kaje can ka karata da yar talakawa yar mai min hidima, kazami kawai..




"Nagode mai tsafta ya fadi yana dariya,
"Kije na sakeki,
amma duk ranar da kikaji kina muradina kafin ki gama idda ina iya maida ki saboda darajar 'yayanki da mahaifinki,
yana kaiwa nan yaja Fatima suka wuce daki..


Yana jiyo ihunta tana zaginshi da mahaifiyarshi,
babu wanda a cikinsu ya tanka ta dan anyi mata mai kankat....



Dakinta ta shiga ta tattare kayanta da gwalagwalanta ta fice ta bar mishi gidanshi....




*********

Saida Musaddiq ya kwana uku a asibiti, lokacin ya farfaďo yana gane duk wanda ke kanshi,
babu abinda yakeyi daga kallon su Daddy sai bacci in allurai sun ratsashi,
tunda ya farfaďo kamar an tafi da hawayen da yakeyi,
magana ba ya yinta ko kadan sai dai in sunyi ya bisu da ido,


Da support yake zuwa yayi alwala da wanka saboda jikinshi samm babu kwari,
a wannan lokacin ne aka yarda kowa yazo ya ganshi dan jikinshi yayi kyau matuka,
abinci da ya zamo aminin Musaddiq yanzu ya maidashi babban makiyinshi domin sai anyi bacin rai kafin ya yarda yayi cokali daya,
kowa burinshi ya farantawa Musaddiq dan dai kawai su samu ya saki jikinshi ya cigaba da Mu'amala kamar yadda ya saba,


Zainab da Ruwaida ne samm ba'a yarda suje inda yake ba saboda har yanzu bakinsu bai bar tambayar inda Nadeeyah take ba...






A cikin kwanan shi na bakwai aka sallameshi,
har wannan lokacin babu wanda yayi mishi maganar inda Nadeeyah take,
shidai yafi bada an binneta shiyasa ma baiyi yunkurin tambaya ba, dan kar ya sake tayar wa da hankalin su Daddy,


Suma kuma har lokacin basu bar neman Nadeeyah ba,
dan har police station suka kai,
tunda Allah baiyi sunga gawarta ba sunsan tabbas tana raye,
in da rai wata rana dole su haďu in shaa Allah....






****
"Karka damu Daddy,
i will take care of myself,


Kallon Zubair Daddy yayi yace "Dan Allah ka kula dashi,
karka barshi ya dinga tunani, ka----

"Nace i will take care of myself,
i'm nt a kid,

yadda yayi maganar da tsawa ya sanya Anty Reemah matsowa kusa dashi,

Dafa kafaďunshi tayi tace
"Laifi ne dan ance a kula dakai,
tafiyar nan ance ka hakura da yinta,
baka da lafiya, ka dage sai kayi ta,
dole a nemi mai kula da kai..


Hannunta ya cire a kafadunshi ya dauki brief case haďe da kallon Daddy yace
"kayi min addu'a in shaa Allah babu abinda zai sameni,
tunani shi ke yin kanshi,
with ur Du'a komai zai daidaita,

Murmushi Daddy yayi yace
"In shaa Allah son,
Allah ya tsare ku ya bada sa'ar abinda aka je nema...




Gurin da Hilal ya ke tsaye Musaddiq ya kalla,
suna haďa ido ya karaso inda yake ya rungumeshi,
rashin walwalar Musaddiq na matukar damunshi,
babu abinda yake sanya shi farin ciki,
dariya kanta ya manta yadda akeyinta, domin wani sashi na yin dariyarshi ya mutu a ranar da ya rasa Nadeeyah,



"Take care kaji,
in na gama project zanzo Singapore inyi keeping dinka company,

gyaďa kai kawai Musaddiq yayi suka fita,
dukkansu yan parlon kowa na mishi fatan alkhairi haďe da adduar Allah ya kara sanya farin ciki a cikin zuciyarshi......




Mutum kamar Musaddiq wanda baisan menene bacin rai ko fushi ba a ganshi a haka dole hankalin makusantanshi ya tashi dan sun san ba karamin abu bane yake sanya Musaddiq fushi,

Daddy yaso yayi quiting aikin da yakeyi amma Musaddiq sam yaki, saboda shi kadai ne yake ganin zai dabe mishi kewa,
badan Daddy yaso ba haka nan ya yarda dan yaso ya zauna tare dashi har ya samu sassauci a zuciyarshi...






Duk wani shiri na barin gidan su Badariyya sunyi domin abun kawai da ya rage musu shine su tarwatsa kuttun tsafin Bokan gaba daya,

layar dake bakinsu suka matsa dan bacewa suka ji su har lokacin a gurin,
cike da tashin hankali suka kalli juna haďe da sake latsata,

hankalinsu bai kara tashi ba sai da sukaji damka a bayansu,

waigowa sukayi dan ganin mai ganinsu a wannan lokacin da suka san sunyi komai dan bacewa ganin mutanen gidan,


Yareemah Suhail suka gani gefenshi kuma duk wasu kulli da sukayi ne wanda ya warwaresu ya sanya musu wuta,


Dariya sosai yayi yace


"kun taba jin labarin wanda ya shigo gidannan ya fita shi kadai,

shafa kanshi yayi ya cigaba da cewa

"Badariyya nasan da hatsabibancinki kika zo,
sai kuma kika kara da na Marakisiyya,
da nice ke zanyi biyayya domin cikin biyayyar wata rana in da rabo ina iya kaiki gida ki ga yan uwanki har kiyi musu sati in kinaso,
amma tunda kin biyewa wannan hatsabibiyar sai kuyi ta zama da taurin kanku,
duk ranar da kuka ga kun amince da zaman gidan nan sai kuyi biyayya, in kuna da rabo sai kuga na kaiku gida dan ziyara,
yana kaiwa nan yayi wurgi dasu cikin wani dakin da basu san da zamanshi a gidan ba..




Kukan jini ne kadai Badariyya batayi ba dan ta ga koshi ya rikide ya zame mata kwanan yunwa,
tayi shirin komawa ta shiga Musaddiq sosai har ta kai ga aurenshi hankali kwance ba tare da kowa ya zargeta ba...

Taci kuka sosai har saida faďa mai karfi ya kacame musu ita da Marakisiyya,
faďan da ya sanya zubewar hakoran Badariyya na gaba, dan Sosai Marakisiyya tafi karfinta.....






*6months later...*



*******

Radiya..
bani dubu biyu zan baki gobe in Reemah ta turo min,


Buďe baki Radiya tayi tace
"ina na gansu Mummy,
nawa nake binki?
kusan 30k fa,
ina zanga dubu biyu yanzu,



Raudha dake kwance akan kujera tace
"Ki bata mana,
jiya fa kika siyar da zobenki,
meye a ciki dan kin bata,
kika san abunda zatayi dashi...


To munafuka,
da na siyar da zoben baki faďa mata abun da nayi dashi ba,
saida zoben kaďai kika iya faďa mata,
ni fa na gaji da wannan rayuwar,
duk wani abu nawa ya kare,
kullum ni kenan cikin bada kudi sai kace wata banki,
na gaji wallahi ta mike fuuuu tayi cikin daki....



Share zufa Mummy tayi haďe ficewa daga dakin tana mamakin hali irin na Radiya,
kwallar da ta fito a idanunta ta share haďe da yin tagumi tana tunanin a wani hali Musaddiq yake yanzu,
rabon ta da ta sashi a ido tun daren da suka fita nemo Nadeeyah,
ko sau ďaya bai taba tunanin nemanta ba,
ta sani ta bata mishi matuka,
a yanzu dana sani takeyi sosai na biye wa san zuciyarta da tayi,

kawayenta da a da suke like mata kaff dinsu sun guje ta saboda halin da take ciki,

Nairah dari yanzu mugun sha'awa take bata,
ga Baffa ya dauke Anni ya maida ita gidan da Papy ya siya saboda ya dinga sauka in yazo,
ko ganinshi basa yi a gidan saboda a cewarshi basa girmama matarshi,



Daddy kuwa ko ta kirashi bata samu dan ya sanyata a black list,
samm bata samunshi, koda text tayi mishi saidai ya dawo mata dan ko kusa baya isa gurinshi...



Shigowar Rilwanu da kayan abinci shi ya katse mata tunanin da takeyi,
da murnarta ta mike tace

"Wadannan kayan daga ina?


"Alhj karami ne ya zo shi ya sauke su, yana waje nasan yanzu zai shigo,



Hijab ta dauko da sauri jiki na rawa ta fita tarbo Papy...



Kuka wiwi ta dinga mishi tana neman gafararshi,
rike mata hannu yayi yace

"Haba,
wallahi ban taba rike ki ba,
we are all humans, we make mistakes,
ni waye da bazan yafe miki ba,
komai ya wuce wallahi,
ina Goggo?



Hmmm ta tafi kauye tun shekaran jiya,

"Nace ya labarin Musaddiq,
kana ji daga gareshi kuwa?


Bai zo bane?
Papy ya tambaya cike mamaki haďe da fito wayarshi,


kuka Mummy ta fashe dashi tace
"Rabona da Musaddiq wata shida kenan da kwanaki..


"Ya salam,
ai ban sani ba,
jiya da ya kirani nake tambayarshi yazo gida yake cemin yazo duk kuna nan lafiya,



Hawaye Mummy ta share tace

"Nasan nayi deserving more than this,
tunda har Daddy yace in har aka sake mishi maganata zai cike ukun, shiyasa nake lallabawa ina hakuri har lokacin da Allah zai yanke min wannan punishment din...




Cike da tausayin dan uwa Papy yace

"karki damu,
wata rana zai sakko,
yanzu ya hau dokin zuciya ne,


Gashi ya auri zaman lagos,
gaba daya yayi ma kaduna kaura,
in shaa Allahu komai zai wuce,

ke dai kici gaba da addu'a da kyakykyawar niyya,
zakiga kamar ba'ayi ba...


Hira sosai sukayi ya bata dubu ashirin, sannan ya tashi ya nufi gidan su Anni.....







*Memories are always special, sometimes we laugh by remembering the day we cried, nd sometimes we cry by remembering the day we laughed That's life*...



"Na dade da manta yadda ake dariya,
rabin rayuwata ya mutu ranar da kika tafi kika barni,
"
Kin manta alkawarin da kikayi min?

we promise to live together duk rintsi duk wuya,

Why did u live ur other half..
Why,
Why did u go nd live me alone,
Why Nadeeyah,
Why..

hakan ya dinga maimaitawa yana yayyaga hotunanta haďe yin wurgi da laptop din da ya manna hotonta kan screen din,


Da sauri Daddy ya hawo sama ya sameshi yana tattaka laptop din yana huci kamar mayuwancin zaki,


Rikeshi Daddy yayi hade da janye shi da kyar daga kan laptop din,


Idonshi da yayi jawur Daddy ya kalla yace

"Meyasa kake yima rayuwarka haka,
kafi Allah sanin abun da ya dace da kai ne,
tunda kaga ya ďauketa yasan dalilinshi na yin hakan,

Allah nasan masu tawakkali,



"Tawakkali wanne kuke son inyi? Ya tambaya a harzuke,

Ka taba ganin nayi kuka,
ko na tambayeku inda take?

Nasan ta tafi kuma bazata dawo ba,
shiyasa nakeson yadda ta tafi ba tare tunanin halin da zan shiga ba,
nima ta fita a raina..


I want to cry her love out of my life,
i want to hate her so much,


Nasan nayi mata laifi,
amma laifina bai kai tayi min irin wannan hukuncin ba,

ya zata tafi ta barni bayan tayi min alkawarin bazata rabu dani ba,
in ta tafi dan bata sona meyasa zata bar min nata son a cikin zuciyata,
da sai ta tafi dashi gaba ďaya,

Plss Daddy help me,
ka faďa min yadda zanyi ta fita a raina,
bata bari na sukuni,
komai nakeyi ita ke yawo cikin kaina da jinin jikina,
dan Allah ka taimakeni ka cire min ita a cikin raina,

plsss....



Rungumeshi Daddy yayi yana kuka sosai haďe da cewa

"Cry Musaddiq,
kayi kuka may be ka samu sassauci,

*So*
Allah ke sanya shi,
baka isa ka cireshi ba,
u have to move on,
in Allah yasa zakayi wani farin cikin nan gaba to zaizo ba tare da shawara ba,
sai kaga Allah ya baka wacce tafi Nadeeyah...



Sakin Daddy yayi yace

"Samun mace irin Nadeeyah abu ne mai wahala,


Cikin hikima Daddy yace

"Allah,
har tafi Antynka Reemah?


"Ita ba wacce za'a kwatanta da kowa bace,
she is very nice..

Yadda ya bawa Daddy amsa cikin sakin jiki ya sanyashi zaunar dashi yana tambayarshi labarai akan Nadeeyah,
labarinta ya shiga bashi wanda ya sanya mishi kaunarta marar adadi cikin kwana taran da sukayi tare,


"Nadeeyah is so special Daddy, she is so sweet..
ya karashe haďe da yin wata yar dariya wacce bata kai ko'ina ba.......





Mrs Tijjani Shattimah......
[30/04 4:57 PM] +234 807 161 1811: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣6⃣
By *Aysha Ya'u kurah*





*A square Turkey constructing company*....


Ya rasulullah...
dattijon ya faďi haďe da dafe kanshi,
coffee din dake gabanshi ya ture gefe yana mai sake duba cikin system dinsa,
ya dade bai duba ayyukan gidajen shi ba saboda yadda ya yarda da ingancin masu yi mishi aiki musamman mai mishi zane da engineern dake tsaye gurin ganin an tsara ginin yadda ya kamata,

"kusan watanni shida kenan da gama aikin wasu gini amma har yanzu mutane biyar kaďai suka siya wasu bangare daga gidan,
tun yana Egypt yake damuwa da outcome din business dinshi dake turkey,
yau dai ya shirya zuwa dan ganin dalilin da ya sanya companynshi ya fara zama koma baya wurin ciniki a kasar instanbul,
ganin yanayin tsarin ginin da ya kashe makudai kudi yayi su ya sanya hankalinshi tashi matuka,
sam zubin tsarin baiyi ba,
komai anyi shi a gaggauce,
kama daga zanen har ginin,
sam bai iya bacin rai ba domin shi mutum ne wanda ya yarda da kaddara mai kyau da marar kyau,
asarar da yayi bata kananan kudade bace,
haka ya bar gurin yana istigfari haďe da adduar Allah ya sanya asarar da yake shirin yi ta zame mishi alkhairi....



Yana komawa office ya bukaci sanin a inda matsalar take, engineern ya fara kira,
nan ya gabatar mishi da zanen da aka bashi domin yin aikin sannan ya ďora da cewa

"kanin manager ne yayi zanen,
wanda ya saba yin zanen ya bar aiki damu kamar yadda manager ya faďa min..

Sheik na ganin zanen ya gane a inda matsalar take,
bai bukaci jin wani karin bayani ba yayi zaune hankali duk a tashe yana hango dakushewar kasuwancinshi kwana kusa,


Rufe system din yayi ya mike ya danna wata kararrawa dan yin taro na gaggawa da ma'aikatanshi,
nan fa suka shiga tururuwar shigowa cike da ladabi suka tsaytsaya a muhallinsu.....



Bayan ya gama musu bayanai na abun da ya tarasu sannan ya dora da irin barazanar da companynshi yake fuskanta ya kuma yi umurni da kar a sake baiwa wanda yayi zanen gidajen da sukayi musu bandaro aiki,

Bayan nan ya bukaci duk wani wanda yasan mai zane wanda ya kware a zane ya je ya kawo shi ya kuma sashi ya taho da aikin da yayi,
rabin yan gurin wadanda suka san Hilal suka fara ihun sunan

*M H K*...

wasunsu kuma suka fita domin kiran makusantansu suzo ga aiki ya samu,

Cikin awanni uku aka haďa masu zane kusan su 15,
nan duk suka gabatar da ayyukansu wanda ko rabin na Hilal basu kamo ba,
cike da kosawa ya kalli zanen na karshen haďe da mikawa engineern,

"Call for another meeting plss,
ina son sanin dalilin da yasa Hilal ya bar aiki anan gurin..
cike da girmamawa engineern ya amsa shi ya fita da sauri ya sake kiran wani meeting din..




"Da harcen turancin dattijon da bai wuce shekaru hamsin da doriya ba yake magana,

"Nasan akwai masu zanen gidaje da yawa,
amma companyn nan kowa yasan "Hilal Kangiwa" ne yake zanen gidajen da muke ginawa masu daukar hankalin jama'a,
duk wadannan masu zanen da kuka tara min dan Allah ku basu hakuri,
a je a nemo min Hilal muyi eye to eye dashi inji nawa yake son a kara mishi,

Cikin girmamawa manajan kamfanin yace

"Ba kudin bane sukayi mishi kadan,
matsala suka samu da IRFAN,
shine yace ya bar aiki,

Ya salam...
dattijon ya fadi yana mai dafe kanshi,
wato Irfan sai ya kori duk wani wanda suke kasuwanci tare,

a kausashe yace
"bani number wayarshi zan kirashi yanzu yazo office ya sameni...



******

"Duk tashoshin cartoon din yau basu yi zee,
kin gani? ta tsaida kan Mbc 1,
tana yunkurin canzawa wayarta ta dau kara,
mikewa tayi da sauri ta zare wayar a charge,
daki ta wuce tana waya da Jamal cike da so da qauna,


Lamoo Zainab tayi cikin lallausar kujerar parlon tana kallo haďe da lumshe ido alamun bacci nason yin gaba da ita, 
bata dauke idonta a kan tvn ba dan tasan in suka gama tallan drama's dinsu zasu sako cartoon,

hannu tasa a baki tana sha a boye dan kar Hilal ya kamata,
yadda ta naďe hannun da hula zaka rantse wani abun take sha daban,

Kamar cikin mafarki ta tsinkayi kukan yar budurwa cikin wani tallan arabic drama,
sanye take cikin jallabiya baka kanta yane da ďankwali,

Mikewa zainab tayi ta isa gaban tvn dan kalolin hotunan budurwar ake nunowa,
daga wanda take kuka sai wanda take dariya,

*Adda*

ta furta a hankali tana shafa fuskarta a screen....

" *Hey everyone i'm _MALEEKA SAHEEB SAIF_.... SAHEEBUL QALBEE will be in cinema's on the 3rd may in shaa Allah, don't miss the unconditional love story of NAINAH AND SAMIR, dos in Egypt will see ya on the 5th, nd Istanbul on the dday, love yhu oll my fans.. muahhhh..*




Ya Hilal...
Ya Hilal...

A ruďe ya rufe laptop dinshi ya buďe kofa saboda irin kiran da Zainab take mishi,
duk tunaninshi wani abun ne ya sameta,
haki ya ga tana yi tana nuna mishi tv,

"Adda na gani a cikin tv,
wallahi itace,

ajiyar zuciya Hilal yayi ya kwace naďin da tayi ma hannunta da hula yace

"wannan abun da kikayi shi ya sanya tayi miki gizo,
amma muje in ga ko itace,
bin bayanshi tayi suka zauna a parlon lokacin an wuce tallan har an fara cartoon,
a hankali tace
"an gama, amma ka zauna a sake yin talla zaka ganta,

janyota jikinshi yayi yace
"Bacci kikeji my baby,
kwanta kinji,
anjima in kin tashi sai mu fita yawo,

rufe idonta tayi tana hango fuskar Maleekah wacce tayi ma lakabi da Nadeeyah,
babu abinda ya banbanta su sai tsayi da wayewa,

Maleeka ta ďan dara Nadeeyah tsayi sannan wayewarsu da gogewarsu ma sam ba daya bace,
amma kamannin fuska babu inda suka banbanta,
da tunanin bacci yayi gaba da Zainab,

kwantar da ita yayi a gurin ya mike dan karasa research din da yakeyi akan aikin da gwamnati ke son bayarwa,
yana son Applying aikin amma yasan yafi karfin Papa ma bashi ba...


Cike da confidence yayi Applying haďe da ayyukan da yayi a baya,
tunanin yadda zaiyi ya haďu da mai
*A square TCC*
ya keyi,
yasan zaiyi aikin domin kuwa karuwarsa ce da shi baki daya,
dan in ya yarda sukayi aikin nan ba karamin kuďi zasu samu ba,

Wayarshi ya dauko da niyyar kiran manajan companyn,
tunawa da halinshi da yayi ya sanyashi ajiye wayar ya cigaba da tunanin yadda zaiyi ya hadu da CEO din cikin sauki,,
har ya mike zai  shiga bayi yaji karar waya,
da kamar kar ya dauka dan yaga bakuwar number,
wani sashi na zuciyarshi ya bashi umarnin dagawa yaji ko alheri ne,

Aiko Hilal yayi farin ciki matuka da jin mai kiran nashi dan abun da ya dade yana nema kenan,

nan yayi alwala yayi sallah haďe da yin addu'ar Allah ya bashi karfin gwiwar fada mishi abun da ke ranshi,
ya kuma sanya haduwar tasu ta zamto alkhairi.....





"Shiryawa yayi tsaff cikin kaftan riga da wando ash,
ya dade yana son haduwa da Ceo din companyn da yake wa zane  *SHEIK ATIKU SAHEEB SAIFUDDEEN*
Saboda wadannan  ayyukan zanen gwannati da yake son nuna mishi,
kuma yana son yi mishi gargadi akan macutan dake gudanar da ayyukansu a companyn shi...



Sanyin A.c. hade da kamshi mai dadi ke tashi a cikin office din,


Makeken Hoton jikin bangon idonshi ya sauka a kai gabanshi yayi mugun faduwa,

su hudu ne a jikin Hoton,

Irfan kadai ya gane saboda yayi mishi sanayya marar dadi,


Hoton yar budurwar da mahaifinta su suka fi tayar da hankalinshi,

bai gama shiga dimuwa ba sai da yaji muryar mutumin ya fito yana mishi MARHABAN ya Hilal,

suman tsaye yayi da suka hada ido saboda tsabar firgici,
tabbas yasan mama suwaiba bata da wani dan uwa namiji,

to wannan mutumin me irin fuskarta daga ina ya fito...


Hasbunallahu wa ni'imal wakeel ya fadi jiki na rawa,
a zatonshi gamo yayi da aljani.....


Karasowa kusa da Hilal yayi ya miko mishi hannu dan su gaisa,

kasa daurewa Hilal yayi yayi saurin tsugunawa dan yi mishi irin gaisuwarmu ta hausawa,
nan fa Sheik ya sake jin kaunar Hilal na yawo a cikin jininshi,

dagoshi yayi ya haďe jikinshi da nashi haďe da sumbutar kumatunshi irin dai yadda larabawa ke gaisuwarsu,
hoton dake kan makeken table dinshi kuwa saida ya kusa tsaida numfashin Hilal,

Hotone kato black nd white, fuskar nan bata da maraba da ta su Mama Suwaiba, Sheik, Nadeeyah da yar budurwar dake cikin hoto,
bai kara samun kanshi cikin ruďani ba sai da idonshi yayi tozali da sarkar wuyar tsohon hoton,
wannan karan Hilal ya riga ya gama fita hayyacinshi,
kar dai son da yakewa Nadeeyah ne ke neman kaishi wata duniyar daban,
hannun dattijon da yaji cikin nashi ne yasa shi saurin matsawa baya,
da karfi yake furta kalmar
"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel,
cikin rashin fahimta dattijon ya nufoshi yace

"Lafiya?
Menene yake faruwa?

"Dan Allah karka cutar dani, Innalillahi,

"wa inna ilaihir rajiun sheik ya karasa cike da zullumi haďe da cewa "Subhanallah,

jin ya ambaci sunan Allah ne ya sanya Hilal nutsuwa haďe da nemo duk wata jarumtakarshi,
ganin ya samu nutsuwa ya sanyashi cewa
"su shiga cikin parlon office din,
bayanshi Hilal yabi yana ambaton sunan Allah...



Kallon Hilal Sheik yayi yana tambayarshi damuwarshi,

Murmushi kawai Hilal yayi yace

"Babu komai kawai yayi mishi kama da wasu relatives dinshi ne nd they are no more,

hoto ya kuma gani a kan centre table din cikin parlon an haďa pixmix da na Maleekah,
dauka Hilal yayi ya fito da wayarshi yayi scrolling hoton Nadeeyah ya nuna ma sheik,

second goma yayi yana kallon fuskar Nadeeyah,
tabbas wannan tayi kama da yayarshi wacce ya rasa tun da kananun shekaru,
katse mishi tunani Hilal yayi dan a lokacin tsoro ya fita a ranshi, yana da tabbacin wannan dan uwan Mama suwaiba ne bangaren uwa,

"Wannan sarkar ya nuna sarkar wuyar tsohon hoton,
da sauri Sheik yace "Ehem kasan sarkar ne,
gyaďa kai Hilal yayi yace
"Sosai, tana gurin grandfather dina,
gaba ďaya sun manta zaman da suka zo yi,
ko wannensu ya shiga shaukin son jin labarin juna,

"A ina ya samu sarkar,

yadda muryarshi ke rawa ya sanya Hilal dafashi,

"calm down sir,
farin cikin da nake ciki bazai barni in baka amsa ba,
sunanta kaďai zanji ya sanya ni fita gurin nan cikin gaggawa dan bayyanawa yan uwana abun farin cikin da ke tunkaro mu,

a gaggauce Sheik yace
*At---*

*ATIKA*

Hilal ya karashe cike da kaguwa domin ya kasa jiranshi ya karasa,

"Yesss,
she is my sister Atika,
my only sister,
my everything ya karashe cikin matsanancin kuka haďe da rungumar hotonta wanda ya zame mishi kullum...


"Ya Allah...
Hilal ya faďi yana zubar hawaye,

Nadeeyah were are uuu,
Asalinki ya fara bayyana,
ya ilahi,
tsatso mai kyau,
i knew it,
nan gaba abubuwan shahara zasu bayyana gareku,
Ina kika shige Nadeeyah,

kuka sosai sukeyi,
shi Sheik yana yi ne dan duk a tunaninshi zai sake sanya yar uwarshi a ido,

shi kuma Hilal kukan biyu ya haďe mishi,
na farin ciki da kuma na bakin ciki domin duk wanda ya kamata ya ga wannan farin cikin baya tare dasu,

" *Is this a scene or reality?*

Zazzakar muryarta ta karaďe dakin,
a tare suka kalleta tana tsaye sanye da bakin dogon wando wanda kasanshi yake a buďe sosai sai milk riga mai dogon hannu,
kanta yane da da bakin gyale wanda ya bayyana gashinta har gadon bayanta,

karasowa tayi hankali a tashe

Please Login or Register in order to submit comment