Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hawaye na zirarowa daga cikin idanuwanta,
tunanin kaninta takeyi dan shekara 6 a duniya wanda ta zamo gata a gareshi gaba da baya,
ko a wani hali yake yanzu Allah masani,
ludayi uku tayi ta miko ma ma'u..
Amsar kwaryar tayi tana fadin "hai har kin koshi, da kin kara kadan ta fadi tana miko mata, Girgiza kai tayi saboda ta fahimci nufinta tace "Alhamdillah, Jazakumullah khairan"
yashe hakori Ma'u tayi tana dariya har can cikinta tana kyakyato shi,
dariyar murnan jin yaren larabci, da kuma ganin ita kanta balarabiyar makkan a gidanta takeyi,
saida ta gama dariyarta tace "hai Baffan Boddo an je gidan kawu suwidi in fadowa su inna wuro munyi bakuwa mai tsarki yar Makkah,
takalmin robarta ta janyo me ruwan bula tasa a kafarta, ta yayo dankwalin saka ta rufe kanta ta fara tafiya,
ta kusa taba kofar Baffa yayi saurin tareta yace "A wala hakkilo na" ("baki da hankali ne?)
Kinsan irin halin da zaki samu a ciki in kika gayyato mana mutanen gidan Kawu Suwidi?, kince bazata bar gidan nan ba na hakura ta zauna amma ki sani babu me shigo min gida bare ya ganta ya jaza min masifa,
tana nan zaune nasan za'a zo cigiyarta a lokacin sai in mikata gurin iyayenta,,
kalonshi ma'u tayi fuskar nan cike da gamsuwa tayi kamar ta yarda din da gaske,
yaye dankwalin kanta tayi tace "Haka ne, na manta ne ina ta zumudin kai rahoto dan kawai in burge su inna wuro,
yanzu bari inje in sata tayi wanka sai ta canza kaya a wanke na jikinta, gyada kai Baffa yayi cikin jin dadi ya koma daki kusa da yaranshi ya zauna yana shafa kan karamar dake kokarin tashi..



Murdaddiyar sarkar murjanin gwal din da ta cire kafin ta shiga wanka ma'u tayi ta juyawa a hannunta tana dariyar farin ciki, "Aiya Ya Allahn Hard'ejo,
(sunan yayan mijinta kenan malamin da ya fara kawo musu musulunci kauyen),
ji wani "kuje ndade' (sarka) kamar ba hannun mutum bane ya kerashi, sashi tayi a wuyanta tace "wannan ko matar Ardo Laminu bata da irinshi,
kaii ya zame min dole in je gidan su inna wuro dan bazan bar wannan daddadan labari ya wuce ban basu shi ba,
ai ni ko da wannan maka wuyar aka barni na tsira,
daki tayi da sauri tana magana kamar zararra,

kayanta dake cikin wani akwatin katako ta dauko sababbi na fulani tace " Baffa zan bata wannan kayan nawa tasa saboda a wanke wadancan,
gyada mata kai kawai yayi dan mamakinta bai barshi ya bude baki yayi magana ba,
ma'u da ko dankwalinta bata iya bawa wani aro shine har ta dauko kayanta da bata taba sasu ba zata bawa wata tasa, lallai yar makkah ta ciri tuta..


Sosai kayan fulanin suka mata kyau a jiki saboda tsabar kyawunta,
lallausan gashinta ma'u ta shiga kitsashi da kyar tana yi yana warwarewa,
haka dai tayi mata irin nasu na fulani ta dauko mata su sarka da abun hannu duk dan ta mantar da ita sarkar gwal dinta...



Mrs Tijjani Shattima...
[07/03 6:31 AM] fareedah: •• ZUMUNCINMU A YAU •• 2⃣1⃣
By Aysha Ya'u Kurah





Hanyar sama Badariyya tayi da gudu tana shashshekar kuka kamar ranta zai fita,

kofar dakin Daddy ta shiga bugawa kamar zata ballata,
da gudu mummy ta fito daga bayi jiki na rawa ta bude kofar,
Daddy kuwa zaune yayi yana jiran ganin me mishi irin wannan bugun kofar da safiyyar nan,

jikin mummy Badar ta fado ta sake kecewa da wani kukan,
waigawa tayi ta kalli Daddy da ya rike kanshi yana tsaki,

waje ta jata ta rufo mishi kofar, ta kama hannunta sukayi dakin ta,

zaunar da ita tayi a kan gado ta shiga rarrashinta,
saida ta tabbatar ta fara samun nutusuwa sannan ta tambayeta abinda ya faru,

karya ta shiga rerowa mummy cikin wani sabon kukan,
"Ya Hilal ne yayi min dukan tsiya,
wai saboda Nadeeyah taje tana wanke wanke kunama ta harbeta,
shine yaje ya taso ni ina bacci wai tace mishi ni nasa ta,
kuma tace mishi wai na hana a bata abinci jiya har tayi bacci,
sannan a gabana Ya Musaddiq ya dauketa ya sata a mota suka kaita asibiti wai kafin su dawo in tabbatar na gama wanke wanken da ya rage------- ,

Wani irin kunci da tukuki mummy taji a ranta,
"Hilal din ne ya dake ki?
gyada kai Badar tayi wasu zafafan hawaye na sake bin kuncin ta,
'irin kallon da Musaddiq ke ma Nadeeyah shi ya fi komai taba zuciyarta,
kwanciya tayi jikin mummy ta runtse idanuwanta saboda ganin hanun Musaddiq da takeyi cikin na Nadeeyah,


"Hello Reemah,
daga daya bangaren Anty Reemah ta bude idonta hankali tashe cikin muryar bacci tace "Na'am, ina kwana Mummy,
''lfy kadai mummý tace, ta cigaba, "kizo gida yanzu ina nemanki, bata jira amsarta ba ta kashe wayar..

Mikewa Anty Reemah tayi jiki a sanyaye,
tasan akan matsalar Hilal akayi kiranta da safen nan,

cikin zafi tace "wai wannan wani irin yaro ne da yakeson kashe ni tun lokaci na baiyi ba,
wallhy yau, ko gobe zamu bar kasar nan kar ya jaza min bala'i,
ina kokarin gamawa da mahaifiyata lafiya yana neman janyo min tsinuwa,

Papa tashi plss ka fara mana shirye shiryen tafiya bari inje gida in dawo,

Ajiyar zuciya kawai Papa yayi ya juya ya kara jan bargo,
samm bayason abinda zai matsawa matarshi da ta zamo jigo kuma garkuwa cikin rayuwarshi,
"Papa kara rufe kanka kayi?
ta fadi kamar zatayi kuka,
yayewa yayi da sauri yana murmushi yace "its too early my omri,
kije ki dawo sai muyi shirye shiryen tare, gyada kanta tayi tasa hijab har kasa ta dauki mukullin mota ta fita...


********

"Waye ya sa ki aiki da wannan safiyar?
Tambayar da Hilal ya jefo mata kenan idonshi na kallon titi,

Tana zaune a kaikaice a baya, saboda kar ta bata musu mota,
cike da jin tsoronshi tace "babu kowa,
naga kayan sunyi datti ne,

Are u an au pair girl??
Musaddiq ya kara jefo mata wata tambayar,
shuru tayi idonta yayi narai narai zai fara zubar hawaye,
juyowa baya yayi ya kalli yadda ta zauna yace "to ruwa ruwa,
zauna dakyau sai kiji dadin yin kukan,
kara kaikaicewa tayi ta kife kanta jikin sit din da yake zaune,

"hey wasa nake miki zauna yadda kike so,
ya fadi hade da maida fuskarshi gaba,

Daidai wani babban shago dake bakin layin Hilal yayi parking,

kallonshi Musaddiq yayi yace "me zaka siya,
hannu Hilal yasa a aljihunshi yaji ba kudi, bai amsa musaddiq ba yace "akwai kudi a jikinka,
taba aljihunshi yayi yace i don't think akwai,
ko akwai ma basu da yawa,

dauko wallet dinshi da ya bari cikin motar yayi ya cire atm din da PAPA ya bashi ya shige shagon,

"Kunada pos?
ya tambayi wani yaron shagon,

eh akwai sir, yaron ya amsa shi cikin girmamawa,
wucewa ciki yayi ya dauko "pad" guda uku,
"Tunda suka isa Asibiti ya lura ta kasa zama har aka gama yi mata allurori,
kuma yaga alamar digon jini a jikin rigarta,
babu inda bai karewa kallo a jikinta ba,
hatta yatsun kafarta wadanda suka fi tafiya da imanin zuciyarshi,

siyayya yayi mata na turaruka da mayuka da sabulai masu kyau da dan tsada,
yadda ya barta haka ya fito ya sameta,

Hira musaddiq ke janta dashi tana amsa wasu, wasu kuma tayi shuru tana murmushi ba tare da ta dago kanta ba,
gefen da take zaune Hilal ya bude,
a tsorace ta dago saboda ta kusa fadi dan ta jingina da kofar,


Ganin Hilal ne ya sanya ta gyara zama ta nutsu sosai,
wani sanyayyen kallo yayi wa nutsuwar da tayi, sannan ya mika mata kayan ya rufe kofar ya shiga suka wuce..

Rike kayan tayi a darare,
ta gefen idonta ta hango pad,
gabanta ne ya yanke ya fadi a zuciyarta tace Allah yasa ba staining tayi ba,
tsoro da kunya duk suka kara dagula lissafinta a cikin motar,

suna isa cikin gidan tayi saurin bude motar ta fita ba tare da ta dauki kayan ba,

kashe motar yayi ya bita da shagalallen kallo har ta kusa shiga cikin gidan,

"yarinyar nan bata dauki kayan nan ba,
musaddiq ya fadi hade da bude baya ya dauko su,

motar Anty Reemah ya gani yace
"ur momma is here,
kallonshi Hilal yayi yace "a haba,
ina take?

"Tayarta na gani ba ita ba ya karashe yana murmushi hade da nuna mishi motar,
fitowa yayi suka karasa cikin gidan a tare...



"Ga munafukar nan ma ta shigo, Mummy ta fadi a kausashe tana kallon Nadeeyah,

tsayawa Nadeeyah tayi a bakin kofar ta kasa daga kafarta, nan take jikinta ya fara rawa,

karaso ciki algunguma,
daga zuwanki jiya zaki yi min setting gida on fire da farar safiya,
to walhy bazan dauka ba,

Nadeeyah saboda tsoro hakoranta suka fara kara kainin haduwa da junansu,
har lokacin bata iya karasowa ba dan kafarta ta gaza dagawa,

ba dake nake magana ba?
Mummy ta kara fadi cikin daga murya,

kuka mai karfi ne ya kufce ma Nadeeyah,

"laaaa ha ila ha illahu!!
uban me aka miki zaki tsaya a bakin kofa ki sake ma mutane kuka,

kaii nikam na bani,
na dauko makirar yarinya da hannuna na kawo cikin gida na,

Mikewa Badariyya tayi ta kamo hannunta out of anger, ta fara janta tana fadin zo ki wuce munafuka dangin tsiya,
yau sai kin bar gidannan tunda ba gidan ubanki bane, tayi wurgi da ita a tsakiyar parlon tana maida numfashi kamar bakin kumurci,
zuciyarta mugun zafi take yi na ganin Musaddiq na petting Nadeeyah kuma harda rike hannunta..


Antyn Reemah dai bata ce uffan tana zaune idonta yayi jawur saboda irin tashin hankalin da mummy ta sata na furucinta a kanta,
tana tsoron sake magana kar ta kara harzuka mummy,

Hannu Badar tasa zata fisge karamin hijab din jikin Nadeeyah,
Hilal ya rike hannun ya dauketa da mari kwarara guda biyu,

ke din gidan ubanki ne?
Nace gidan ubanki ne?
Yanda kike a gidan nan haka take!

Ihunta ne ya gauraye gidan ta shiga zaginshi tana fadin Allah ya isa mugu azzalumi kawai,

wani dukan zai sake kai mata Anty Reemah ta rike hannunshi ta kwada mishi mari,

wani irin kallo yayi mata na mamaki yace "Mum------ shut up ta katseshi rai a bace,
kana hauka ne,
wace irin zuciya gareka da zata dinga saka dukan mace,
ko ka sami jakar ka ne?
tun safe kake jibgarta,
Koma me tayi maka ai da sai ka fadawa mummy ba wai kai ka yanke hukunci da kanka ba,
beside ma ina ruwanka dan tasa Nadeeyah wanke wanke,
meye naka a ciki,

kullum ni kenan in nazo gida bani da kwanciyar hankali saboda kai,
duk sona da yin zumunci haka nake hakura saboda bakar zuciya irin taka,
yanzu rashin kunyar taka akan mahaifiyata ya kai har ka kusa zaginta, saboda dai ka nuna wa duniya mu bamu baka tarbiyar girmama na gaba da kai ba,

To bari kaji, yadda na haifeka itama haka ta haifeni,
walhy duk ranar da ka yarda tayi min baki akanka babu ni babu k------- da sauri Musaddiq ya rufe mata baki,

subhanallah!!!
Anty me ya kawo wadannan magangannun?
Me yayi zafi haka?

Kallonshi Anty Reemah tayi tace "barni da yaron nan little,
so yake yi ya kashe ni,
baya san zaman lafiya ko kadan,
tun jiya da daddare mummy ta fada min irin rashin kunyar da yayi mata, sannan yau da safe ya sauke dukkan fushinshi kan Badariyya,

me tayi mishi har takai ga duka sai kace " *SHAGON MADA* "
in ma da gaske Badar tasa Nadeeyah wanke wanke wat is the big deal in it?
ai mace ce, kuma kowace mace da aikin gida aka santa,
most he sai ya nuna karfinshi jikin 'ya mace sai kace ya samu jaka,

Rage sautin kuka Badariyya tayi saboda taji asirinta na gab da tonuwa,

zatayi magana Musaddiq yayi saurin cewa waitt Anty,
waye ya fada miki Hilal ya daki Badariyya?

Hararshi Mummy tayi tace
"Nice!
Ko karya nayi, bai daketa din bane, fada mishi da bakinki Badar,
ya daketa saboda wannan munafukar ta hada tuggu da karya saboda kawai ta shiga tsakanin ya'yana suyi ta fada kamar karnunka,
to ta Allah ba taki ba walhy. .

Ni fa ban gane ba?
Musaddiq ya fadi hade da kai idonshi kan Badariyya dake rike da kuncinta,

Me Nadeeyah tace game da ke,
kuma da yaushe Hilal ya dake ki?

"Uhmmm uhmm--- uhmn--- ka fita lokacin yace in-- in ya dawo zai min dukan tsiya,
ina tsoron kar ya dake ni shiyasa na fadi ma mummy ya dake ni dan ayi wa tufkar hanci,
kallon Mummy Musaddiq yayi yace "kinji abinda tace ko in maimaita miki?

A kunyace mummy tace "to meye nashi na mata barazana,
ai dole in gasgata saboda nasan bashi da aiki sai duka da zagin na kasa dashi,

Anty Reemah kuwa idonta na kan Hilal dake rike da kunci har lokacin, shi din ma ita yake kallo idonshi jajur,
karyar da kanta tayi zata mishi magana yayi hanyar dakin Musaddiq da sauri,
ajiyar zuciya tayi ta kalli Musaddiq dake ta ma Mummy magana cikin fada,

"Nadeeyah da kika kira munafuka babu abinda tace game da kowa, hasali ma wannan bakar dagar bata san meke faruwa ba har saida muka zo kaita asibiti,
ita ce ma tayi ma Hilal rashin kunya ina jinta bai tanka ba,
walhy in dai baki daina biyewa yarinyar nan ba wata rana sai kinyi dana sani marar amfani,
haba dan Allah ya karashe rai a bace hade da gallawa Badar harara,


Durkusawa yayi kusa da Nadeeyah dake kuka yace "tashi kije daki kisha magani ki kwanta,
mikewa tayi tana share hawaye ta fara tafiya,
kayan da Hilal ya sai mata ya dauko ya bi bayanta,

Dakin Delu yaga tana kokarin shiga yace "ba nan bane dakin gashi nan,
ya nuna dakin su Badar,

Husnah da tun ihun Badar ta farka, tayi hamma tace "a dakin Delu ta kwana kayanta na can,

jinginar da kanshi yayi jigin bango yace "Hasbunallah,
dakin ya bita ya mika mata kayan ya fito da sauri yayi hanyar Sama,

A tsaye yaga Daddy yayi folding arms dinshi fuskar nan tashi a murtuke, asalin Kanuri ya bayyana a tare dashi,

"Daddy kana gan----- naga komai *Saaaaaadiq* " haka yake kiranshi har sai yaja sunan!

kasa ya sauko ya kalli Mummy da duk ta sukurkurce yace
"bana san jin komai,
anjima karfe biyu na rana bayan jumm'a duk mu hallara a gidan Baffa,

"i want to clear all my mystifications, dole ne ku fitar dani cikin duhu,
dan alamu sun nuna min ba Goggo bace ta haifi SUWAIBA,
sannan ba talaucin su bane ya sanya ku tsanarsu a matsayinsu na jininku, akwai dai wani abun a kasa,

*WALLAHI*
Daddy ya fadi da muryar da ta ba Mummy tsoro,
"in har baku fitar dani cikin wannan duhun ba aurenmu dake zai kare,
saboda na gaji sosai da irin halinku da ya shafi zuri'ata,
bazan dauka ba..!
ya mike a zafafe ya haye sama..

Jikin Mummy babu inda bai rawa, ta mike ta haye saman ita ma ta bar Musaddiq da Reemah da Husnah a falon sunyi jugum jugum.....!!!!


Mrs Tijjani Shattima.....
[07/03 6:31 AM] fareedah: ••ZUMUNCINMU A YAU•• 2⃣0⃣
By Aysha Ya'u kurah



"Wai ina zaku tafi ne? bakwa ganin dare yayi!
hannunta ta nuna saitin agogo ta cigaba da fadin pass 10 fa,
bansan yawon banza ku koma dakinku,

Ja da baya Musaddiq yayi yace "wallahi Anty Reemah haka na fada mishi wai shi yau a gidan mummy zai kwana, bansan sanda ya fara shiri da compound din gidan ba, ni da ya kyaleni ma bacci nake ji,

Harara Hilal ya watsawa Musaddiq hade da tsaki, yace "plss mum, air con din dakina ba gas and u knw dat,
Kuma tun isowarmu na fadawa Papa,

ajiye kopin coffee Papa yayi ya kalli Hilal yace "wane Papan?
  "kai mana, Hilal ya fadi hade karyar da kanshi a shagwabe yace "plss papa don't prolong dis issue, dare na dada yi,
mukullin motar papa ya dauka yaja hannun Musaddiq yace "Gud nyt Honey stars,
girgiza kai Anty Reemah tayi tace "Allah ya shirya,
Ameen!! Papa yace hade janyota jikinshi,
hab'arta ya dago ya kalli kwayar idonta wacce ya hango damuwa sosai a cikin ta,
me akayi ma first lady?
Wa ya taba min ke?
tun dawowarki na lura da yanayin ki, sannan kiran da Raliya tayi miki naga ya kara sanya ki cikin damuwa,
fada min matsalarki ko tafi karfina inyi kokarin magance miki ita,

Ajiyar zuciya tayi tace "as usual Papa, sai matsala ta dauko kamar zata warware sai ta kara dagulewa,
nasan duk family ana samun crisis, amma sai inga namu na daban ne,
san zuciya shine ke haddasa komai cikin gurbacewar zumuncin zuriarmu,

labarin abin da ya faru a gidan su Nadeeyah ta bashi ta daura da abin da Raliya ta fada mata a waya,
sannan ta cigaba da cewa "tun ina karama in naga yadda suke treating mama suwaiba sai inyi ta tunanin anya kuwa Goggo ce ta haifeta,
abin da Goggo kema Mummy da Anty Leemah sam yasha banban da wanda take ma mama Suwaiba,
a kuruciyata sai nayi tunanin ko dan ta auri talaka ne,
furucin Goggo na yau ya sanyani cikin tunani sosai na son sanin wacece ATIKA, meye alakarmu da ita.....

Tambayar da Anty Reemah keyi wa zuciyarta a wannan lokacin ita Daddy keyi a zaune a balcony din dakinshi,

Isowar mummy gurin ne ya katse tunaninshi,
cikin taushin murya tace "in kawo maka ruwan zafin? black or green tea? Wanne zan kawo,

Mikewa yayi yace "ko wanne ki kawo, da fatan yaran nan sun kwanta, kuma babu wata matsala,?
gyada kai mummy tayi tace "eh Nadeeyah ma tayi bacci ita kuma zainab tana gidan Reemah,
Good Daddy yace hade da cewa ki ja ma Badariyya kunne,
bana son fitina, suyi zamansu guri daya tunda duk sa'anni ne,
zama cikin nasu shine zai kara musu dankon zumunci,
dan Allah ki kula sosai dan duk ya'yanki ne banason nuna banbanci,

murmushin yake mummy tayi tace "ba sai ka tuna min ba,
na riga na fada musu, kuma in shaa Allah komai zai tafi normal,

kafin yayi magana yaji Hon din mota ya cika gidan,
gate din ya kallo daga sama dan ganin mai shigowa a wannan daren,
hasken dake gidan ne ya haska cikin motar,
ganin Musaddiq kadai yakan sanya Alhj Mukhtar manta duk wata damuwa,
Ajiyar zuciya yayi yace "su kuma daga ina,
cike da jin dadin yadda fuskar Daddy ta canza mummy tace "Gidan Reemah,
ni duk tunanina a can zai kwana,
tafiya ya fara yi yana fadin "gara dai ya dawo gida,
tunda ya dawo ma bamu zauna ba, bare mu tattauna akan sakamakon makarantarshi,

Sakkowarshi kasa tayi daidai da shigowar su Musaddiq cikin parlon,

Remote Daddy ya dauka fuskarshi cike da annashuwar ganin zaratan mazan familyn shi, kuma ababen kaunarshi yace "ABOKI KANGIWA, kai ne a daren nan? yau anan zaka kwana kenan,

kusa dashi Hilal yaje ya rungumeshi yace "yes ABOKI DADDY,
a dakinka ma zan kwana, mu raba dare muna hira,
mun dade bamu hadu ba,

dariya Daddy yayi ya zauna yana kallon Musaddiq dake tsaye yana murmushi,
"zo ka zauna auta na, kar kafarka ta sage,

AUTA fa Daddy? 
To in shi auta ne ni kuma fa?
Husna da ta fito daga kitchen rike da plate din indomie ta fadi tana turo baki,

Dariya Daddy yayi yace "haka ne my baby, 
na manta ne, ba auta bane, kafi auta ne, kece auta,,
Kumbura baki tayi tace "ni ce duka biyun, dariya sukayi dukkansu, mummy ta mika ma Daddy kofin tea,

shan kunu Hilal yayi yace "ni fa,
ina nawa tea din,?
hararar shi mummy tayi tace "kai asu wa?
a mijinki Hilal ya fadi yana gyara zama,
  ko bakya auren?

Tuni na sake ka, ka riga ka gama rainani,
na barwa "Yalwan Kangiwa" kuje can ku karata,
dariya Hilal yayi ya mike ya dauko kopi ya zauna a kasa ya tsiyayi ruwan zafin,

"Zo ki zauna muci tare auta, Musaddiq ya cewa Husna da ke kokarin shigewa dakinsu,

"wayyo Yaya tare da Badar zamuci! Husnah ta bashi amsa tana kallonshi cike da damuwar taga yana san abu ba halin bashi,,

"Muje muci dukkan mu mana,
ai zai ishemu,,
cewar Badariyya da tun shigowar Su musaddiq take tsaye a jikin kofar dakinsu,
jin da tayi zaici abincinsu ya bata damar murda kofar dan a ganinta ta samu damar da zata sanyashi a idonta, 

gefe ya juyar da kanshi ya dauki kopin da ya rage ya tsiyayi ruwan zafin,

kallon shi mummy tayi zuciyarta ba dadi,
tasan yana fushi da Badar, amma batayi tunanin fushin har ya kai haka ba,

"My little yau kuma kai da kanka zaka sha Lipton,
i knw u are nt a fan of it,
in indomie kakeso kaje kuci da yan uwanka ko kuma Badariyya ta dafa maka wata,

mikewa yayi yace "mummy ba Lipton zan sha ba, hot chocolate zan hada, wasa nake ma Husnah,
its too late for me in ci indomie,
gara dai ruwan zafin,

kafin ya kai gurin dinning har Badar ta dauko gwangwanin
"Cadbury hot chocolate,

Ya ilahi!!
ya fadi hade da dafe kanshi,
juyawa yayi dan komawa ya zauna, tayi saurin cewa,
am sorry gashi!,
bai saurareta ba ya koma ya zauna,

kallonshi Mummy tayi ranta ya fara baci da irin tsanar da yake nunawa Badariyya,
"miko min nan in hada mishi!

cike da tsanar kanta taja kafarta ta mikawa mummy gwangwanin ta wuce daki da sauri,

Soyayyar Musaddiq ita ce weak point dinta,
wen it comes to Musaddiq zuciyarta mai taushi ce matuka,
shi kadai take iya daukar wulakancin shi,
soyayyarshi tayi ma zuciyarta illa tun bata san mecece kalmar so ba,

*****Tun tana yar yarinyarta ba ta yarda kowa ya rabe shi, koda kuwa Husnah ce,
ko da yaushe tana tare dashi,
sunyi matukar shakuwa da juna,

shi a nashi bangaren tausayinta yake ji na rashin iyaye tun tana jarinta,
yawanci rainonta shi yayi,
in yana gida bata taba barinshi sukuni,

Tun da ta shiga school shakuwar tasu ta fara raguwa saboda halayyarta,
tun tana nursery take ma yan ajinsu mugunta musamman in taga yarinya ta fita kyau ko gashi,
ko kuma ta ga wanda ya fita a komai, ( zamu iya sanya Badariyya a cikin jerin irin halittun dake da hassada, wadanda basa san kowa ya fisu)..

Musaddiq kullum in yazo class dinsu sai ya tarar da ita tana duka da jan gashin yara,
karfi da yaji ta zama boss a class, kowani yaro tsoronta yake ji,

haka a gida in suna wasa da Husnah ta dinga kyararta kenan tana sata kuka,

wannan halin shi ya farraqa shakuwar Musaddiq da Badariyya,

shareta da yake yi da sanyin hali irin nashi yasa ta rainashi sosai,

kullum sai ta tsokaneshi hankalinta yake kwanciya,
dariyarshi da bacin ranshi duk suna da ma'anoninsu a zuciyarta..

Hey Badar, "baza kici abincin bane, tun dazu nake miki magana kina jina,
sai cika kikeyi kina batsewa,
plss zo muci kinga 11 ta wuce,
tashi muje pls, Husnah ta karashe hade da kamo hannunta,

kwacewa Badar tayi ta maida kanta jikin gado tace "na koshi,
je ki cinye,

Husnah ta bata fuska tace "haba nw sis, karki sauke fushink---- plsss Ma'u lv me alone,
ko dole ne sai naci, Badar ta katseta a kausashe,

fita tayi a dakin tana kunkuni a ranta, da kinsan bazaki ci ba da baki wahalar dani ba,
kuma da baki barta ta fara sanyi ba,
da mitar ta karasa parlor ta zauna a kasa kusa da Musaddiq da Mummy ta mikawa kofin tea ya karba ya ajiye,

Fada ta fara mishi sosai iya karfin ta,
tun Daddy na kawaicin saurarenta har hakurinshi ya kusa karewa,

kallon da yayi wa Musaddiq yaga idonshi ya ciko da kwalla ne ya karar da hakurinshi,
kafin yayi magana Hilal ya rigashi,

"Haba Mummy, irin wannan fadan sai kace yayi wani mugun laifi,
haba dan Allah, is not fair walhy, shiyasa yaran nan duk suka raina shi,

Duka mummy ta kaiwa Hilal ya goce,
cike da masifa tace "wallahi Hilal ka fita idona,
bana son rashin kunya,
dan uwarka ina ruwanka,
walhy zanyi mugun bata maka rai in ka sake shiga sabgata, tunda ni ba sa'arka bace,

"ai gaskiya na fada, akan wannan fitsararriyar yarin----- daga hannu tayi ta kwada mishi mari,

Daddy baice komai ba idonshi na kan tv.,
zuciyarshi sai kai kawo takeyi, ranshi in yayi dubu ya baci,
muryar mummy ce ta kara cika kunnenshi,

Please Login or Register in order to submit comment