Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kyau?

Wani irin karaaa ta saki mai karfi tana bubbuga kafarta a kasa,
Da gudu Mamy ta fito daga dakin Anni tace "waye? lafiya,
motsin kofar Jamal ta gani ya tabbatar mata da shine ya taba ta, "bude kofar nan Jay,
ta window ya leko yace "Mamy babu abin da na mata fa,
kawai dan nace mata Anni bata da lafiya yau karta damu mutane shine fa ta fara kuka,
daukarta mamy tayi tace "Sorry my love, Anni will get well soon in shaa Allah kinji,
muje ki ganta,

gefen Anni ta zauna tana fadin Anni wanene ya saki ciwo,
hannunta Anni ta rike tace "bana ciwo takwara,
lafiyata kalau,
tashi kije kici abinci kizo kiyi min fira kinji,
mikewa tayi tabi bayan mamy hade da cewa "to Anni na ni kadai banda Wicked yaya Jay...

Suna fita Alh Abdallah ya shigo dakin ya zauna a kusa da ita,
Anni likita yace "idan baki daina tunani ba zamu iya rasaki,
zuciyarki ta kusa shiga matakin Karshe,
me kike so wanda Allah bai miki ba,
duk irin tsanar da akayi miki a gida saboda ni yanzu bai zame miki alkhairi ba,
babu abinda na rasa Anni, dukiya, mace, 'yaya, ga kuma ke da kika zamo jigo a rayuwata,
kece mafarin komai Anni, hawayen da ya zubo a idonta ta share tace "Uba" Abdallah,
ka rasa uba,
tun kana ciki ake min kallon fasika,
har fitowarka duniya ban huta ba saboda kiranka shege da akeyi,
nasani kayi min kawaici na rashin ganin laifina akan rashin sanin inda ubanka yake,
A yau ma abun da na saba fada maka shi zan fada maka,
wallahi tallahi Abdallah kai dan Aure ne,
sunnar manzon Allah ita ta samar dakai,
amma babban abin takaicin shine har yanzu bazan ce ga inda mahaifinka yake ba.... ta karashe da kuka mai hade da tari......

(Twist) karku rude ku biyoni da muje komai zai warware....




Daddy nayi magana da papa akan ina so a bani daya daga cikin yaran mama suwaiba mu rike,
yardarshi tasa nace bari in tambayeka ko za'a bani,
ajiye cup din hannunshi yayi yace "banajin ki Reemah,
na yarje miki ki dauki zainab domin itace karama,
ita take bukatar uwa irinki,
ita kuwa Nadeeya yanzu ta girma gara ta zauna anan ta cigaba da makarantarta,
Allah yayi miki albarka, ya kara miki soyayyar yan uwanki a cikin zuciyarki,
Ameen Anty Reemah tace hade da janyo abin cire farce ta cire mishi wata kumba da ta dago a kafarshi..
yaushe zaku koma ne? Daddy ya tambayeta yana taba gurin da ta cire farce,,
jibi in shaa Allahu Daddy,
to Allah ya kaimu....
ta amsa da Ameen sannan suka cigaba da hirar ya da mahaifi...



Mrs Tijjani shattima
[09/03 6:50 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣2⃣
By *Aysha Ya'u kurah*





Karar da wayarshi keyi ne ya sanya shi jan tsaki hade da mik'a hannu ya dauka,
kara ta yayi a kunnen shi,
"uhmm *Meerah* Hw u, ya fadi kamar mai cin magani,

daga daya bangaren tace "nt good kangiwa!
Cire wayar yayi a kunnenshi ya kalli screen din yayi tsaki a hankali hade da mikawa Musaddiq,
deal with her pls,
inada abun yi,
murmushi Musaddiq yayi ya karbi wayar cike da barkwanci yace "Meeran Kangiwa,
kin ma manta da Allah yayi ruwan Musaddiq a doron duniya ko,
bude baki tayi tace "laaaa small uncle kayi hakuri,
kana raina kullum,
in na kira kangiwa bai cika picking ba, kuma bani da contact dinka, am so sorry plss,
"a'a haba bakomai, ba gashi yanzu mun gaisa ba, just pulling ur legs ne dama, ya karashe cike da zolaya,
So ya gida nd su Adeel?
Lafiyarsu kalau we missed u alot ta fadi murya cike da farin ciki, ummm really ya fadi hade da cewa "i missed u guys more more, barin ma su Adeel,
plss my regards to them,

"zasuji in shaa Allah Small uncle,

Hira sosai suka cigaba dayi,
duk ta gaji tana son tambayarshi Hilal,
da ya fahimci haka yace "sorry fa, bari in baki mutumin, duk na cika ki da surutu,
murmushi tayi tace "ba komai naji dadin hirar ai,
mikawa Hilal wayar yayi hade da dauke kai saboda irin hararar da yake watso mishi,
kara wayar yayi a karo na biyu, bai barta tayi magana ba yace " sorry Meerah, will call if am chance, bai bata damar sake yin magana ba ya katse wayar...

"Bakyau,
wannan wulakanci ne,
ba kai ka kirata ba kuma ta kira sai ka kashe mata waya,
is nt fair wallahi, Musaddiq ne ke magana rai a bace,
Meerah na matukar bashi tausayi yadda take bin Hilal shi kuma yana wulakanta ta,

"Na taba rokonta nace ta dinga kirana Mr Soft? Hilal ya jefo mishi tambayar yana mishi kallon jiran amsa,
Tsaki Musaddiq yayi yace "its pointless talking to u, bazaka gane ba sai ka tsinci kanka a shoes dinta,

Da sauri Hilal yace "i pray not to in shaa Allah,
ka gane ne ko,
mace da kamun kai aka santa,
ya zata dinga kiran namiji every nw nd then,
haba, ita bata ko jin kunya,
nawa nake da mace zata fara min kwainanen soyayya,
komai yana da lokaci,
lokacin da zan sa kaina a cikin soyayya yana nan zuwa,
runtse idonshi yayi yana siffanto Nadeeya ya cigaba da cewa, Soyayyar ma wacce babu irinta a fadin duniya...

banza dashi musaddiq yayi ya ja takalmanshi yasa ya fita,
Dariya Hilal yayi hade da daukar jakar laptop dinshi yabi bayan Musaddiq...




A zaune suka samu Mummy tayi tagumi tana tunani,
gefenta Musaddiq ya zauna ya cire mata tagumin yace "Mummy na menene?
Kallonshi tayi zuciyarta duk ba dadi tace "babu komai Diku, har kun tashi?,
ina Hilal?
Kafin Musaddiq ya bata amsa Hilal ya zauna kusa da ita yace "an tashi lafiya Hajiya,
shafa kanshi tayi tace "lafiya kalau, har ka shirya, naji ance gobe zaku tafi,
cike da mamakinta Hilal yace "eh Mum ta fada min,
mikewa tayi tace "bari in hado muku break fast,
gyada kai sukayi hade da binta da kallo suna mamakin sabon canjin da suka gani tare da ita,
gab da zata shiga kitchen suka kusa karo da Nadeeyah,
da sauri taja baya ta tsuguna har kasa ta gaisheta,
murmushi tayi ta dago ta tace "Lafiya kalau Nadeeyah, har kin tashi, gyada kai tayi tace "eh na tashi,
hannunta Mummy ta kama suka wuce dakin mai aikinsu tace "ina kayanki suka,
can lungu ta janyo jakar kayanta tace "gasu nan,
kiran mai aikin mummy tayi tace ta dauko kayan ta biyosu dashi,
da sauri ta dauki kayan ta bi bayansu,
dakin su Badar Mummy ta bude suka shiga ciki,
bacci ta samesu sunayi dukkansu, basa ko motsi kamar matattu,
kallon Nadeeyah mummy tayi tace "nan ne dakin da zaki dawo,
ga drawer nan, akwai wacce babu kaya a ciki, sai ki saka kayanki,
a darare tace "Mummy dan Allah ki barni a can dakin, shima yayi sosai,,
kafadunta mummy ta dafa tace "dake da su Husna duk daya ne a gurina,
in har zan barki a dakin masu aiki, to tabbas zan bar su Husna ma a can,
ki saki jikinki nan ma gida ne kinji ko,
share kwalla tayi tace "Eh mummy, nagode sosai,
kara share mata hawayen tayi tace "babu godiya tsakanin 'ya da uwa,
jeki maza ki fara shirya kayanki kizo mu karya,
saida Mummy ta fita tafara jan jakarta jiki a sanyaye,
bude drawers din tayi tagansu cike da tsala tsalan kayan su Badar,
drawer can karshe ta bude, babu komai a ciki sai zanin gado da towels,
fito dasu tayi ta maidasu kasa, sannan ta fara fito da kayanta tana jerasu a ciki,
tana gab da gamawa taji an saki ashar mai wuyar fadi a bayanta,
juyowa tayi taga Badariyya tsaye rike da kugu,

"keeee,
uban waye yasa ki shigo mana daki har ki bude drawer ki zuba wadannan tsummokaran naki?

Nadeeyah bata kula ta ba ta juya ta cigaba da fito da kodaddun kayanta tana cigaba da jerawa,
a harzuke Badar ta fincikota tayi wurgi da ita,
"ke har kin isa ina miki magana kiyi banza dani,
leda ta dauko tasa a hannunta ta fara fito da kayan tana fadin "bazan iya taba dirty kayan nan da hannuna ba,
ke in banda ma shegen tsaurin ido har kina da confidence din shigo mana daki ki fara jera kayanki,
baki ma da hankali tunda har baki iya bijirewa kice dakin yafi karfinki ba,
rufe drawer tayi bayan ta gama fito da kayan tace "oya oya maza hada tsummar roba robarki ki kara gaba, nan dakin yafi karfin kazamai irinki,
Nadeeyah bata amsata ba ta tattara kayanta cikin jaka ta sa a can wani lungu ta yi hanya fita parlor,
da karfi Badar ta janyo mata hijab har yana shaketa,
harararta tayi tace "uban wa kika barwa kayanki?
dalla wuce ki dauke mana su ko dakin mu zai samu saukin wari,

cikin sanyin Murya Nadeeya tace "Badariyya sake min Hijab kin kama min wuya,

"bazan sake ki ba, Badar ta fadi tana girgiza jiki,
Kwacewa Nadeeyah tayi da kyar, ta dauko jakarta ta bude kofar palon,
dankwalinta da ya fado kasa Badar ta dauko tayi saurin binta dashi ta wurga mata tace "dauki kayan war---- bata karasa fadi ba saboda hada ido da tayi dasu Hilal da Mummy a palon,
sakin kofar tayi ta koma ciki ta fada bayi da sauri,
a yanayin da taga Hilal tasan zai iya yi ma jikinta lahani,
tsaki tayi tace "shigowar yarinyar nan rayuwata babbar matsala ce wallahi,
hankalina bazai taba kwanciya ba har sai ta bar gidan nan,
tunowa da tayi an kusa komawa school yasa ta sakin murmushi tasan in ta tafi school zasu dan sarara....



A tare Musaddiq da Hilal suka mike suka isa gurin Nadeeya, jakar Musaddiq ya karba Hilal ya bude dakin yana kwala ma Badariyya kira,
farkawa Husnah tayi a tsorace tace "ya Hilal lafiya,
"ina Badariyya?, ya tambaya yana huci,
bargonta Husna taja tace "anan take kwance sai dai ko in tana toilet,
hanyar toilet din yayi mummy tayi saurin tare shi, tace "kwantar da hankalinka,
barni da ita,
Nadeeyah dauki kayan ki sa a drawer,
jin muryar mummy yasa Badariyya fitowa a bayin tana kukan da ba hawaye,
"Mummy fa ba wani abu na mata ba,
cewa nayi kayan sunyi datti kuma sun kode ta fitar mana dasu kar ta kawo mana kudin cizo, kuma mummy ki kalli gadon yayi mana kadan mu uku, dan Allah ki barta ta koma dakin da ta sauka,

Dunkule hannu Hilal yayi zuciyarshi na tafasa,
baya son kai mata duka saboda kunyar idon mummy da suka fara dasawa yau,
jiran hukuncin da zata yanke yakeyi,
in baiyi mishi yaje ya roki Papa kawai a hada Nadeeyah da zainab su tafi tare,
Murya a kausashe Mummy tace " Nadeeyah a dakin nan zata zauna cikin yan uwanta, dukkanku 'ya'ya na ne,
babu wanda yake bare a cikinku,
ya zama dole ku koyi zama tare saboda zumuncinku yayi karfi,

kallon Husna tayi tace "maza matso ki tayata ku jera kayan,
ke kuma Badar, bana son tashin hankali,
Nadeeyah yar uwarki ce, kaddara ce ta sanya kukayi nesa da juna, yanzu kuma Allah ya hada ku, kuma kinsan baki da yadda zakiyi da hadin Allah...

Ajiyar zuciya Hilal yayi a ranshi yace "Allah yasa Mummy ta daure a haka,
yanzu ne zai tafi hankalinshi a kwance,
yafi son yayi nesa da ita ta samu damar yin karatunta ta zama cikakkiyar mace,
yasan in har yana ganinta kullum bazai iya controlling kanshi ba, dole yayi abin da zata gane halin da yake ciki,
shi kuma ba yanzu yake son furta mata ba,
yana matukar tattalin kalmar har sai ta cimma lokacin ta.....




Karfe 5pm suka dawo gida hannunsu rike da ledoji,
kalolin jallabiya guda shida Hilal ya siyo ma Nadeeyah, sai flat shoes guda biyu milk nd brown, dayar ledar kuma jallabiya ce guda biyu,
kwala kiran Husna yayi,
da sauri ta fito daga kitchen tana tsane hannunta tace "ya Hilal gani,
"ledar ya mika mata yace "wannan naki ne,
kinsan yanzu mun fara dasawa, tsalle tayi tana ihu tace "Thank u *bro Son* , bai damu da sunan da ta kirashi ba yace "wannan ki kaima Nadeeyah,
kinga kayanta duk sun kode,
zan ma Anty Rally magana sai kuje kasuwa a samo mata yan atamfofi,
karbar ledar tayi tace "ummm ya Hilal ashe dai kana da kirki, gaskiya thank u,
kamar kasan in tasa kaya abin na dan taba ni,
wasu ma sun mata kadan,
Murmushi jin dadi yayi yace "yauwa gaskiya i love u, u will be my personal person daga yanzu,
dariya tayi tace "godiya nake, gashi gobe zaka tafi, gaskiya zanyi missing dinka, bari naje na kai mata, nasan zata ji dadi....




Bude kayan Husna tayi ta dinga yaba kyawunsu tana gwadawa a jikinta,
tana cikin gwada wata ja a cikin na Nadeeyah Badar ta shigo dakin,
zama tayi a gefen gado ta dauki daya a ciki tace "waye ya kawo mana jallabiya, shine har kika fara zaba baki jirani ba ko ta fadi a gadarance,
kwacewa Husna tayi tace "to Mummy kiyi hakuri,
ya Hilal ne siyan ma Nadeeyah,
ta dauko nata tace 'kinga nawa nima,
wayyo, ai kamar Husna ta watsa mata ruwan zafi haka taji,
dama duk yau cikin kunci ta wuni saboda yadda Mummy tayi wata wuzu wuzu akan Nadeeyah,

mikewa tayi idonta ya ciko da kwalla zata bar dakin,
tausayi taba Husnah tace "sis zo wasa nake miki,
guda biyu ya kawo mana ni da ke fa,
sauran ne na Nadeeyah saboda bata a kaya,
bata saurareta ba ta fita daga dakin dan tasan Hilal bazai taba yi mata kyauta ba,
ninke kayan Husna tayi ta maidasu cikin ledar ta wuce kitchen ta kira Nadeeya,

A tsorace Nadeeya ke daga kayan tace "duka nawa ne?
gyada mata kai Husna tayi tace "u are very lucky, yaya Hilal bai taba kyautar ko da naira dari biyar ba, yaushe ma kaga fuska a gurinshi bare ya baka,
sai gashi yau har ni ya hada,
dark blue din ta dauko a ciki tace "gwada wannan nasan zata miki kyau,
bayi taje ta sa a jikinta,
fadin rigar yayi mata cibb saboda tana da dan jiki,
sai dai tsawon ya so yayi mata yawa,
madubin bayin ta kalla hade da gyara gashin da ya kwanto a goshinta,
ita kanta ta yarda a zuciyarta rigar ta mata kyau,
dakyar ta iya fitowa daga bayin saboda kunyar Husna,

wooooww..
Husnah ta fadi a fili,
a cikin ranta kuma tace "see beauty, oh Gosh, Allah baya bawa mai wuka nama,
"kinga yadda yayi miki kyau kuwa,
kunya ce ta ishi Nadeeyah tace " nagode,
bari inje in cire,
tareta Husna tayi tace "godiya dai zamu je kiyi ma "ya Hilal, daburcewa Nadeeyah tayi tace "a'a dan Allah bari in canza kaya sai muje, dagewa Husna tayi tace lallai sai dai suje a haka,
dakyar ta yarda ta yafa gyalen a kanta,

murda kofar dakin suka ji anyi,
a tare suka waigo,
daburcewa Nadeeyah tayi ganin Musaddiq da Hilal tsaye a bakin kofar,
karasowa ciki Musaddiq yayi cikin zolaya yace "a'a iyye, kaga kanwata,
ashe dai kina da kyau haka,
to juyo ki nuna mana kwalliyar mana,
janyo hijab tayi ta cukwikwiye kanta tace "ba kwalliya nayi ba, Husna ce tace in gwada ko zai min daidai,
dariya yayi yace "kuma ya miki kyau, ashe dai mun iya zabe,
to babu ko yar godiya,
kara rufe fuskarta tayi tace "yanzu dama zamu je muyi, kuyi hakuri, Nagode Allah ya saka da mafificin alkhairi, Ameen Ameen, muma mun gode da addu'ar da muka roka,

gurin Hilal Husna ta matsa tace "ya Hilal kaga yadda kayan suka karbemu,
thank u once again,
murmushi yayi yace "never mind, kinga mukullin motata cikin kayan nan,
zazzage kayan ta koma tayi,
babu komai a cikin su, dago kai tayi tace "baya ciki, ko ka barshi a jikin motar?
Tunani ya fara yi yace "eh to bari inje in duba,
ta gefen ido yake satar kallonta tun shigowarshi dakin,
sai da zai fita ne ya kalli yadda ta matse kanta,
murmushin shauki yayi ya fita zuciyarshi wasai saboda yadda yaga ta fara samun sakewa a gidan.....




Jirgin karfe shida na yamma zasu bi,
tun safe Hinad da Zainab suka tafi saloon suka wanke kansu akayi musu kitso,
daga can gidan Mummy aka wuce dasu,
nan suka yini har bayan la'asar sannan suka soma shirin tafiya,
har bakin mota ta rakasu tana dada yi ma zainab nasiha,
saida taga sun shiga motar sun zauna ta kalli Zainab da idonta ya ciko da kwalla tace "kuka kuma zakiyi, to bari in tafi in barki tunda kuka zakiyi,
hannunta Zainab ta rike tace "Adda zan tafi in barki a gidan mummy su dinga saki kuka, meyasa bazaki zo mu tafi ba,
share mata hawaye Nadeeyah tayi cikin dakiya tace "inji wa yace miki zasu sani kuka,
bana nuna miki kayana da mummy ta kawo min ba,
yau ma tace zata kuma kawo min wani,
kar kiyi kuka kinji dukkan mu zamuji dadi,
gyada kai Zainab tayi tace "Haka mumyn Hinad tace min, sake matse hannunta tayi tace "banda rashin ji kinji,
in kikayi rashin ji zasu fada min, ni kuma sai inyi ta kuka anan,
kinaso inyi kuka,
girgiza kai tayi da sauri tace "a'a bana so, bazan kuma yi rashin ji ba,
kumatunta Nadeeyah taja tace "good girl,
hira suka cigaba dayi suna jiran drivern yazo suka hango motar Hafeez ta shigo gidan,
da murna Nadeeyah taje gurin shi tana mishi barka da zuwa,
rungumeta yayi suka wuce gurin su Zainab,
ta window zainab ta fito ta dane wuyanshi tana murna,
komawa mota yayi ya dauko katuwar leda yace "wannan sweets dinku ne ke da Hinad, kuma saura inji labarin kin mayar da shi abincinki,
kara kankameshi tayi tace mun gode yaya, amma zaka dinga zuwa gurina ko?
"Kullum zaki ganni, kedai kiyi karatu, banda rashin ji, banda takurawa mutane akan abin da babu kina ji na ko,
gyada kai tayi tace "duk na sani Adda Nadeeya ta fada min,
motar ya mayar da ita yace "to Allah ya kiyaye hanya, Hinad ki gaida Anty Reemah kinji, "in shaa Allah zan fada mata, ta fadi tana murmushi,
hannu suka dinga dagawa juna har motar ta fita,

kallon Nadeeya yayi yace "kina nan dai lafiya ko?
Amsa mishi tayi da "lafiya lau yaya,
labarin canjin da mummy tayi ta bashi sannan ta kara da hidimar dasu Hilal suka mata,
hira sosai sukayi kafin ya shiga ya gaida mummy,
bayan sun gama gaisawa yace ma mummy zai koma Gombe,
akwai makarantar da yayi applying, sun mishi email ya samu shine zaije ya fara registration, addu'oi ta jero mishi na fatan alkhairi sannan ta tambayeshi in da ya ajiye sarkar da Goggo ta basu,.
damun da Goggo tayi mata akan sarkar ba kadan bace,
nuna mishi tayi bata san sarkar ta salwanta,
Murmushi Hafeez yayi yace "tun ranar da aka bani Daddy ya karba,
bata kwana a gurina ba,

murmushin yake mummy tayi tace "yauwa ai kaga tana gurin Babba ya fi,
Allah yayi muku albarka, amsawa dukkansu sukayi sannan Hafeez ya tashi ya tafi cike da kewar yan uwanshi......


Mrs Tijjani Shattima....
[09/03 9:57 PM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣3⃣
By *Aysha Ya'u kurah*





A makare suka isa airport din,
sauri sauri suka shiga inda ake layin shigewa gurin da jirgin yake,
kallon Musaddiq Hilal yayi yana son mishi magana amma bakin shi yayi nauyi ya gaza furta komai,
to me zai ce mishi,
in yace ya kula da Nadeeyah,
ya zai dauki kalmar a cikin zuciyarshi,
saida layi yazo kansu sannan yayi musu sallama cike da kewa ya juya ya koma gurin motarshi,,

Yana shiga kafin ya tada yaga wayarshi na fitar da haske alamar kira,
"har ka fara missing dina? Musaddiq ya fadi yana dariya, daga daya bangaren Hilal yace "come on wani missing,
hutawa ma zanyi da matsalolinka Mr soft,
dariyar Musaddiq ya sakeyi yace "to why did u call, admit kawai *Head of elephant* ,
dariya sukayi dukkansu sannan Hilal yace "Zee ce tace in kiraka,
and tace in fada maka kasa mata ido akan yayarta,
gata nan kwance duk ta damu,
canzawa wayar kunne yayi ya rage sauti yace "Plss Kyari ka kula da yarinyar nan, kasan bata da kowa, nd Daddy bai cika zama ba, kai ne mazaunin gidan for nw kafin ka samu aiki,
dan Allah ba sai ta tambayi wani abu ba, u shud knw abinda mace ke bukata every nw nd then, kawai tausayi suke bani, at der early age sun rasa iyaye duka,
plss try kyari kaima ka zama jajirtaccen namiji ya karashe cikin shakiyanci,
gerraut Musaddiq ya fadi yana dariya,
dama ni ai jajirtacce ne, kawai dai.... bari ma dai meyasa nake fada maka,
and karka damu tana bani tausayi as well, in shaa Allahu bazan bari tayi lacking komai ba, kuma zansa ido akanta,

"yayyy dats my Good Boy, shiyasa nake sonka kanina, kuma kasan sosai fa nake sonka,Hilal ya fadi yana dariyar tsokana.
"And i hate u ni kuma Musaddiq ya fadi murya a kausashe,
dariya sosai Hilal yayi yace "chill kanina zamu shiga jirgi, take care plss,
bai jira amsarshi ba ya kashe wayar ya isa gurin jirgin cike da annashuwa.....




Satittika sun zo sun wuce,
zaman gidan mummy a gurin Nadeeyah ya zama babu yabo babu fallasa,
kula sosai Musaddiq yake bata duk da bata cika sakin jiki dashi ba,
ita ma Husnah duk da tana shakkar Badar takan zauna suyi hira jefi jefi da Nadeeyah,
kyawun Nadeeyar da yanayin jikinta ke matukar burge Husna, ita haka Allah yayita tanason ganin farar mace,
uwa uba farin ya hada duk ingredients na dangin kyau,

Matsalarta Nadeeyah 'Badar ce kadai, shima sai sunzo bacci,
ta dinga zaginta kenan tana fadin saidai ta kwana a kasa,
wani lokaci in Husna tasa baki fadan ya dawo kanta,
haka dai Nadeeya ta maida gurin kwananta kasa kan bargo dan dai hankalin kowa ya kwanta,
saboda mugunta irinta Badar sai ta kure a.c. ta kuma dukunkune a cikin bargo,
in sanyin yayi yawa cikin dare sai Husna ta tashi ta rage ko ta kashe gaba daya ba tare da Badar ta sani ba, saidai in safiya tayi kaji hayagagar ta tana masifar dalilin da zaisa a dinga kashe mata a.c.,

kullum haka sukeyi har Husna ta gaji da kashewa,
in taga sanyin yayi yawa sai ta tashi Nadeeyah ta matsa mata su kwanta,
da yake tana rigasu tashi shiyasa Badar bata ganewa....




Zaune suke a tsakarsu gidan ta can baya,
Badar na gyara kumbar ta,
ita kuma Husna na tsifa, dayake kalaba ne shiyasa take tsefewa da hannu,
kallon Nadeeyah tayi wacce take zaune tana taya mai aikunsu gyaran cabbage,
"Nadeeyah yaushe zaki koma school? Barin yankan Nadeeyah tayi tace "15th,
bude baki Husna tayi tace "jiya kenan, gyada kai Nadeeyah tayi tace eh amma zan iya komawa next week,
"tabe baki Husna tayi tace "kuma kinajin dadin boarding?
Kai ni ai bazan iya rayuwar wani guri, in ba gida ba,
dariya Nadeeyah tayi tace "kuma akwai dadi, mutum na koyan abubuwa da dama na daga halin mutane,
mabanbantan mutane kake haduwa dasu masu halaye kala kala,
comb Husna ta dauka tace "ni fa koma meye bazan iya ba,
kema da zaki yi ma Mummy magana a canza miki makaranta ki dawo day da yafi miki,,
sai a sannan Badar tasa musu baki,
"miss I too knw,
madam over sabi, ai sai ki canza mata,
tsaki taja da karfi ta mike hade da cewa "wallahi shegen iyayinki ya fiki karfinki,
ita tasan public school ne daidai ita,
in kuma kina da kudin canza mata sai ki bada himma tasa kai ta shige kitchen tana hararar Nadeeyah,
tsaki Husnah tayi tace "gama muje ki rakani saloon ayi min kitso, kema sai ayi miki kiji dadin kanki, gurin famfon tsakar gidan Nadeeyah ta kai cabbage din ta kunna ta wanke shi tass ta tsane,
tace ma Husna "na gama! muyi sallah sai mu

Please Login or Register in order to submit comment