Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sun gaggaisa Anty Reemah ta kalli Sheik cike da al'ajabi zatayi magana Hilal ya rigata dan baya son yasan mutuwar yar uwarshi samm sai yaje ga mijinta,



"Mum wannan kanin maman su mama suwaiba ne,
labarin yadda haďuwarsu ta kaya ya basu wanda ya cikata da mamaki,

"lallai komai da sanadinsa, sanadin aiki ya sa ka samo wannan muhimmin abun,
kaii masha Allah wallahi naji dadi sosai,

introducing dinsu Hilal yayi, yana zuwa kan Zainab da Sheik ya kasa daina kallonta yace

"Ur grand daughter sir,
she is urs!

hawayen farin ciki ne ya fito mishi dan yajita sosai a jininshi,

mikewa yayi ya dauketa sosai a jikinshi,
ya kosa a wayi garin gobe yaje yaga zuri'arshi, shakikanshi, wadanda yake da rashinsu tun kuruciya,
a gidan Papa ya samesu shima yayi farin ciki sosai sukayi hirar kasuwanci da na iyalai,


Sheik jin kanshi yakeyi kamar a yaune aka haifeshi dan ya fara jin kamshin yan uwanshi danginshi na uwa...





Assalamu alaikum.....


maida hankalinsu kan mai sallamar sukayi dukkansu,

Sauka jikin Abbu Zainab tayi ta ruga gurin Meerah,

"Anty Mee zo kiga Maleekah da nake baki labari dazu,

hankalinta sam bai kan zainab tana can kallon yadda Maleeka tasa kafa tana shafo ta Hilal yana matsarwa,
tray din hannunta ta damke dan kiriss ya rage ya faďi kasa,

"Muje zee,


Har kasa ta tsuguna ta gaida su Abbu sannan ta mike ta nufi kujerar da su Hilal suke,
kan hannun kujerar ta zauna,
ganin duk manyan suna can suna hirarsu yasata yi mishi raďa a kunne,


Dariya sosai yayi dan ya gama gane inda ta dosa,
mikewa yayi ya nufi dakinshi..

bin bayanshi tayi rai a bace dan ta gama kulewa,
dangwarar da tray din snacks din da tayo mishi tayi a kan madubi,


"Meerah plss,

kar muyi creating scene a gidan nan kinga munada baki,



"Eh naga baki,
su bakin da suka san inda sukazo ai na samesu suna hira,
kai fa,
ko kunyar idon iyaye bakaji ba ka zauna kusa da mace tana shafa maka kafa kana jin dadi,



Wannan karan dariya yayi mai sauti wanda ya kular da Meerah
ya sata sakin kuka mai karfi,

"La'ila,
ke rufa min asiri plss,
haba meerah,
yarinyar nan kema kinsan tafi karfina daga yanayinta in kika kalla,


"Me zanyi da yanayinta ni,
abun da idona ya gane min shi na lura dashi,
na gama fargabar wata yanzu kuma ga wata zata shi----


Meera..
ya katseta haďe da tsugunowa gabanta,
Na faďa miki soyayya yanzu na rufeta a shafin rayuwata,
bana tunanin zan sake faďawa cikinta so quick,
na faďa miki kiyi hakuri,
wallahi in nace miki zan yarda ki jirani nasan cutarki kawai zanyi,
bazan iya sake yin wata soyayya ba,
u are my best friend tun muna yara,
dan Allah mu tafi a haka,
Allah zai baki wanda yafini alkhairi,



Share hawayenta tayi ta mike tace
"Nagode Hilal,
zanyi hakuri dakai dan dama nasan ba sona kakeyi ba,


"Nooo Meerah...
ya faďi haďe da matsowa kusa da ita,
hawayen da ya makale a idonta ya share mata yace

"kinsan Allah ina sonki,
amma bazan iya zaman aure dake ba,
who will be the husband?


Yadda yayi tambayar cike da zolaya yasata yin dariya,

tasan irin matan da yakeso,
yara kanana wadanda zai yi musu yadda yake so,

bayason a juyashi sam,

ita kuwa Meerah kusan mates ne in ma bata girme mishi ba,

"All the best besty ta faďi tana murmushi,
Allah ya sake baka wata soyayyar wacce tafi ta da,


"U will always be my best Meera, Allah ya baki farin ciki kema....




"Uhmmm wonderful..,

Maleekah ta faďi tana karasowa haďe da tafa hannu,
a tsakiyansu ta tsaya cike da tsiwa,

hannun Meerah Hilal yaja yace da hausa dan yasan bata ji.

"Muje in rakaki,
ba kunya gare yarinyar nan ba,


kallo ta bisu dashi ta rasa menene ainihin abin da yasa ta biyosu,

kwafa tayi ta kama hannun Zainab suka koma parlor,


lokacin har su Abbu sun mike da niyyar tafiya,

wayarta ta dauka sukayi hotuna kala kala da Zainab da Hinad,


Har kasa su Anty Reemah suka rakosu,
tana ganin Hilal ya nufo inda suke tayi saurin sanya Abbu cikin mota,
gefen driver ta shiga ta sashi ya koma mazauninta,

Saida taga yazo dab da motar ta tadata haďe da bata wuta da karfi,
tana kallon yadda ya tsaya cike da mamaki ta fito da hannunta waje haďe da yi mishi wani irin sign wanda bai gane ba,
tana gama juyar da motar ta leko tayi mishi gwalooo sosai haďe da kaďa kai da ido,


Tsintar kanshi yayi da dariya sosai yana faďin
"naughty girl,
matsalar yan drama kenan,
komai sai sun maida shi wasan kwaikwayo,
Har ya karasa cikin dakinshi bai bar hango yadda tayi mishi da fuska ba,
duk abin da yakeyi in ya tuna sai ya keche da dariya shi kadai........





Mrs Tijjani Shattima.....
[10/06 9:33 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣7⃣
By *Aysha Ya'u kurah*




New story from
*Atika Saheeb*

"Yaushe rabo,, Jamal ya faďi haďe da budewa,

Tallanta na film din
*Saheebul qalbee*
ya gani wanda ya gani a wall din Samir dazu yayi saving,
a da yana son films dinta saboda haďuwarta da barkwancinta da tsantsar iya soyayyarta,
amma yanzu abun ya haďe mishi,
yana matukar sonta saboda kamanni da takeyi da yar uwarshi Nadeeyah,
bai gama wannan tunanin ba ya hango fuskar da ya yi ma sani sosai,
fuskar Masoyiyarshi Hinad da yar uwarshi Zainab,
sai ita kanta Maleekar,
rawa hannunshi ya fara yi ya kara ma wayarshi full light,
sune tabbas,

Cike da mamaki yake karanta post din,
*My hidden fam, love yah muahhh....* ta sanya alamun kiss,

kwancewa kan Jamal yayi ya rasa ta inda zai kamo tunaninshi,
da kyar ya tattaro nutsuwarshi yayi screenshot din hoton ya turawa Hinad haďe da tambayar wacece wannan?

Hinad na bude hoton taga Maleekah,
alamar dariya kawai ta tura mishi ta kashe wayarta gaba daya dan ance karta faďa ma kowa suna son ya zama surprise......




Su shidda ne cikin jirgin,
Abbu, Ummi, papa, da Anty Reemah,
sai Hilal da Maleekah,
inda Hilal yake zaune nan Maleekah taje ta zauna da sharaďin kar ya soma yi mata magana,

dauke kanshi yayi dan gidan ta tarar,

Chocolates ta fito dashi da su ice cream tana sha tana bin wakar Nancy Agram,
toshe kunne Hilal yayi ya jingina jikin kujerar haďe da rufe ido,
duk ledar chocolate din da tasha sai ta wurga kan jikinshi,
da taga yaki kulata har ya rufe ido tayi saurin bude wani ice cream mai hade da chocolate ta kai saitin bakinshi,

Tura mishi tayi iya karfinta har sai da ya shige bakinshi,

wata dariya ta saki ganin yadda bakinshi yayi dama dama,

A harzuke ya ja gashin kanta da karfi wanda ya sanyata sakin kara,

"Hilal wani irin iskanci ne wannan,
Anty Reemah da karan yasa ta buďe ido ta fadi cike da masifa,

Gyalen wuyanta yaja ya goge bakinshi dashi ya mike  zaiyi magana Ummi tace

"Ba laifinshi bane,
ina kallonta tun dazu,
dawo nan kusa da Abbu kaji,

Matse gurin Maleekah tayi tace saidai ita ta koma gurin Abbu,

"To dawo ki zauna,
ni sai in zauna a inda yake,

"Noo bazai zauna kusa dake ba, saidai ya zauna shi kadai,

"Maleekah...,
Ummi ta faďi cikin tsawa dan iskancinta ya isheta,
ga yadda take ganin fuskar Hilal zai iya maketa saboda bacin rai,

Tabe baki tayi tana shirin yin kuka Abbu ya taso da kanshi ya kamo hannunta ya maida ita kusa dashi,
badan taso ba haka ta zauna tana turo baki gaba,


kwantar da kanta sheik yayi cikin sigar lallashi dan koda wasa baya son abin da zai bata ran diyar da yake matukar kauna,
soyayyar yayarshi ya sanya shi sanya ma 'yayanshi biyar mata sunan suna wabi,
bai fasa sawa ba dan yace ko zai haifi goma su mutu sai ya sanya sunan wacce ya sani a matsayin mahaifiyarshi,
cikin ikon Allah Maleekah ta zauna duk da har yanzu da girmanta basu bar dar dar ba,
tun daga kanta haihuwa ta tsaya musu, ba haka sheik yaso ba dan shi mutum ne mai son tara 'ya'ya domin ya huce haushin tashin da yayi a maraya babu uwa babu wani dan uwa da zai kira nashi,
wannan yasa ya dauki son duniya ya daurawa Irfan da Maleekah,
sam babu no a agendar shi ta 'yayanshi,
hakan yasa Irfan ya zama sangartacce,
ita kuma Maleekah sai Allah ya sanya ta zamo mai hankali da sanin ya kamata,
shagwaba kaďai ta iya zubawa kamar baza'a mutu ba, amma in abu na serious yazo tafi kowa zama serious,
son da sukewa juna da mahaifinta yasa basa yarda ran wani ya baci koda kuwa anyi mishi abun bacin ran....  



Lumshe ido Maleekah tayi tana son yin bacci,
gagararta baccin yayi saboda wani irin yanayi da takeji game da Hilal wanda mutum bai isa ya sanyashi ba saidai Allah,
mikewa zaune tayi kamar an tsikareta ta dauko madubi cikin jakarta ta saitashi daidai inda zata ga Hilal,

karaff idanuwansu suka sarke cikin na juna domin shima ita yake kallo tun zamanta,

saurin daga kanshi sama yayi yana mai jin haushin kanshi,

murmushi tayi wanda yake bayyana duk wata kyawun surar fuskarta,
komawa jikin Abbu tayi ta lumshe ido tana mai mamakin yadda akayi zuciyarta mai mugun tsantseni tayi na'am da Hilal,
tafi minti goma tana tunani har bacci mai cike da mafarkai yayi awon gaba da ita......





Sauri sauri yayi rounding aikin dake gabanshi dan yaje airport taro mutanen da a koda yaushe burinsu ya kasance cikin farin ciki,


Zubair ne ya shigo cikin office din da wasu files haďe da zube mishi,

harara Musaddiq ya bishi dashi yace

"Wallahi bazanyi ba,
kaga dan na daga maka kafa ka angwance shine zaka wani lalace ka haďani da aikinka,
to saidai in kwana zakayi a office amma sai ka gama su,

keyn mota ya dauka ya cigaba da faďin
"Dama gida kaje Faidah ta tayaka,
dan naga yar karanbani ce,
bye ni na tafi...



Dariya Zubair yayi yace
"Gobe nan zaka dawo ka tarar dasu,
in ka bude zakaga ko menene..

Musaddiq bai saurare shi ba ya wuce ya danna lift,
yana buďuwa ya shige ciki da sauri ya danna basement..

Lafiyyar motarshi ya shiga ya tadata yayi hanyar airport....



Mintina kadan suka kaishi airport din,
parking yayi a inda yasan bai tare kowa ba,
koda ya isa gurin ya tarar jirgin  bai sauka ba,
guda biyu ne kadai ya sauka,
na USA,
tambaya yayi aka tabbatar mishi da nan da minti talatin na Turkey zasu sauka,
guri mai kyau ya nema ya zauna kusa da wani saurayi rike da jinjiri wanda bai wuce wata uku ba yana baccinshi cikin showel hankali kwance,

Shima saurayin bacci ne ya fara daukarshi dan saukarsu kenan daga jirgi,

Musaddiq na lura da yadda saurayin ke gyangyaďi ya kura mishi ido dan kar yayi sanadiyyar faduwar yaron,
gyangyaďi mai karfi ne ya kama saurayin har yayi sanadiyyar subucewar wayarshi da yaron,

Cike da azama Musaddiq ya taro yaron da har lokacin bai farka daga baccin da yakeyi ba,

rawa jikin saurayin ya fara yi cike da tsoro dan da yaron ya faďi ba karamin buguwa zaiyi ba,
waya ma kenan da take bata da karfi ta tarwatse inaga rai,

Kallon Musaddiq yayi wanda ya zubawa yaron ido suna kallon juna dan yana zuwa hannun Musaddiq ya buďe idonshi tangaran,
dariya jinjirin yayi wa Musaddiq wanda ya sanya duka kumatunshi lotsawa,
cike da kasala Musaddiq ya maida mishi dariyar haďe da taba kumatunshi,
haka nan yaji son yaron na yawo cikin jininshi,
matsowa saurayin yayi yana ma Musaddiq godiya haďe da sa hannu ya karbi jinjirin,
kuka sosai jinjirin ya fashe dashi wanda a iya saninsu bai taba yin irinshi ba tun haihuwarshi,
a ruďe saurayin ya fara jijjigashi yana hangen wani guri alamar neman mahaifiyar yaron,
kuka sosai jinjirin yakeyi har yana shakewa,
hawaye shabe shabe a rufaffen idonshi,
har cikin rai Musaddiq ke jin kukan jinjirin,
ganin yadda saurayin ke jijjigashi cikin rashin iyawa yasashi matsowa kusa ya mika hannu ya karbeshi,
sanyashi yayi a kafaďa nan take gurin yayi tsitt sai alamar shakuwa da ajiyar zuciyar jinjirin,
cike da mamaki dan saurayin yace


"Lallai junior,
wato nayi maka yaro da raino ko?


Dariya Musaddiq yayi yace

"Abun mamaki,
ban sanshi ba amma ganin farko ya shiga raina,
ya sunanshi?

*Mukhtar amma Hi*------- 


"Amaaan..

da sauri ya katse maganar ya amshi junior yace
"Sorry.. uncle dina na kirana, inaga zamu wuce ne,
thanks alot,
bin bayansu Musaddiq yayi dan keyn motarshi ya makale jikin showel din,
tsayawa Aman yayi cike da mamaki yace

"Any problem?

Nuna mishi keyn yayi lokacin ya cireshi haďe da jan kumatun junior,
"Bye Daddy,
ka daina rigima kaji ko?

yadda ya kaďa mishi keyn yasanya yaron sake yin dariyar da ta tsaya a ran Musaddiq,
saida suka kurewa ganinshi sannan ne yayi ajiyar zuciya haďe da kokarin cire tunanin yaron a cikin zuciyarshi...






Faďuwar da gabanshi yayi ne ya sanyashi faďin

"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun...
kamar an sake hura faďuwar gaban domin kuwa da sauri da sauri take harbawa kamar ana lugude,
runtse idonshi yayi haďe da dafe kirjinshi,
tunanin da yake kwana yi shi ya dawo mishi sabo fil kamar yau aka halitta shi a cikin zuciyarshi,



Karar wucewar takalma ta bayanshi ya sanyashi buďe idon a hankali,
kafin ya juyar da fuskarshi duk sun bi ta kofar sun shige sai Aman da shima ya bi bayansu,
kamshin turarukansu da ya biye gurin shi ya sanya Musaddiq sake jingina da kujerar yana mai tsintar kanshi cikin shaukin da ya daďe bai shiga irinshi ba....




Saida jirgin yakai 45mins sannan ya sauka a wani kebabben guri saboda dama private ne,


A gajiye likiss suka sauko kowa yana mika saboda zaman guri daya,


Anty Reemah Musaddiq ya fara gani yayi saurin karasawa kusa da ita yana mata sannu da zuwa,


Sakkowar Sheik ba karamin gigita Musaddiq tayi ba,
bai dawo daga wannan shock din ba ya shiga wacce ta fishi,


Maleekah ya hango kanta dauke da hular Hilal wacce ta cire suna gab da fitowa,


"Kaga Nadeeyarka ko?
Kunci ya kare,
Papa ya faďi yana murmushi...



Hmmm ya faďi cike da mamaki,

"Mai kama da ita dai,
Nadeeyah ba haka take ba,
amma a ina kuka samo mai kama da ita,
in ma kunyi haka ne dan hankalina ya kwanta in sake wani auren to ku sani ni da aure sai dai a lahira,
yadda Nadeeyah ta gama aure ta tafi ta barni nima hakan zan je in sameta yadda ta barni..


Hannun Papa Anty Reemah ta kama haďe da girgiza mishi kai suka tsaya a gefe,

cike da murna Hilal ya sauko ya rungume Musaddiq haďe da tambayarshi bayan rabuwa,

Murmushin da dole uwar naki ta koya mishi shi ya sakar mishi haďe da tambayarshi su waye wadannan masu kama da su Mamma?



"Hello broo,
Ayyam Atika Ateek, a.k.a Maleekah,
tsaki Hilal yayi haďe da cire hular kanta yayi gaba,


"Salamu alaikum,
nyc meeting u Atika,
i am Musaddiq Kyari,


Maida hannunta baya tayi dan yadda ya amsa mata sallamar ya burgeta,

har kasa ya tsuguna ya gaida su Sheik,
dagoshi Sheik yayi ya rungumeshi haďe da amsa gaisuwar,
saida suka gaisa sosai sannan suka fita suka isa motar Musaddiq da wata da aka basu a airport din dan zurga zurga,
har suka isa gida Musaddiq bai bar tambayarsu daga ina suka nemo dangin Mama suwaiba ba....






Cike da al'ajabi Daddy ya ke duban Sheik,

"Ikon Allah kenan,
to meyasa babu wanda ya nemeta?


Murmushi sheik yayi yace

"Kaddarar Zuri'a,
a lokacin da labarin yazo mana ina da shekara shida a duniya, amma nakan tuna wasu abubuwan,


Lokacin da labarin mutuwarta ya riski ummul bata tsaya tayi binciken komai ba,
kamar jira takeyi ta tattara 'yayanta suka fita daga gidan da niyyar in ta koma tace harda ni aka kashe,
wani yaron da muke wasa dashi *Husaimin*
shi ya shigo ya tasheni yace
"inyi sauri gashi can za'a gudu a barni,
a lokacin ne yake faďa min cewa an kashe Habeebullah da yayata,
da gudu nabi bayansu lokacin har sun hau amalanke sun fara tafiya,
takalmina da ya cire na waiga zan dauko Husaimin yajani da tayar hannunshi mukayi gudu muka kamo su,
dakyar na iya hawa saboda tsayin abun,
ina hawa ummul ta fara yi min masifar borin kunya tana tambayata inda naje,
ban bata amsa ba na tsugunar da kaina inata kukan rashin gatan da zan tarar,
har muka isa inda zamu tsallaka ruwa ban daina kuka ba,

muna zuwa muka samu wadanda zasu tsallaka zuwa Egypt,
nan aka loda mu ciki muka fara tafiyar da ta kaimu washe gari cikin ruwa...




Karya da gaskiya Ummul ta fadawa mahaifina har ta ce mishi an sallaceta a gabanta domin tasan bazai yarda da ita ba sai yasa an je an dubo ta,
saboda tsabar bakin cikin rashin Atika mahaifina ya kamu da mummunan ciwon stroke wanda ya daukeshi shekara biyu yana yi kafin Allah ya dauki ranshi,
gaba daya dukiyarshi ummul ta tattareta ita da yayanta ta maidani dan aikinsu,
son zuciya yasa ta manta matsayina a gurinta,
ta mance cewa inda mahaifiyarmu ta tafi itama zata je komi daren dadewa,
gidan Sheik Al' Mannar abokin babana nan nake zuwa daukar karatu,
ganin hazakata yasashi ya sanya ni a makarantar boko,
daga can sai in wuce gurin da suke aikin gini in dinga koya ina samun na abinci,
gaba daya kwanan gidanmu ya gagareni domin kwana nakeyi aiki bani da wani hutu,
abinci ma ummul sai taga dama take bani a cewarta itama ba kudi gareta ba,
duk wasu kadarori na mahaifinmu ta haďe ta siyar sun cinye kudin da 'yayanta...



Muna da shekara sha takwass 'yaranta biyu sukayi wa wata yarinya fyaďe wanda hakan yayi sanadiyyar yi musu hukuncin da yayi ajalinsu,
a lokacin ummul hauka ne kawai batayi ba domin saida tayi wata biyu a asibiti,
ni nayi jinyarta saboda dayan yaronta an nemeshi an rasa ya gudu da ragowar kudin da ta ajiye,
ashe shima smuggling din kwaya yakeyi,
ranar da dubunshi ta cika aka kamashi ita ma a ranar rayuwarta tazo karshe saboda shock din fille mishi kai da akayi...


Gaba daya ummul ta manta cewa akwai mutuwa a bayan rayuwa,
damar da Allah ya bata ta butulce mishi tayi wasa da ita,
lokacin aji na biyu a jami'a,
da taimakon Allah da taimakon Sheik na samu na kammala makaranta,

Dan kudin da gwamnati ke bamu na scholarship da kudin aikin ginin da nakeyi yasa ni na fara dan karamin business dina,
cikin ikon Allah kafin shekara abun ya bunkasa dan har na sai fili nawa na kaina,
a lokacin ne kuma Allah ya azurtani da samun mace ta gari Zeenat yar gidan Sheik,


Shekararmu biyu da aure muka samu Irfan,
daga nan ne kuma duk shekara sai ta haihu wasu suzo babu rai, wasu kuma suyi watanni su mutu,
daga kan Maleekah ne kuma haihuwar ta tsaya mana duk da ba haka naso ba,
amma zabin Allah shine zabin komai.....
ya karashe yana share hawaye haďe da yin murmushin takaicin fitar da irin kunar ukubar da yasha yana yaro.....





Babu wanda bai zubda kwalla ba a dakin,
lallai mutanen zamanin yanzu banda rikon sakainar kashi da sukayi wa zumunci,
harda illata rayuwar juna ma sun kware akanta....




Babu wanda yake da kwarin gwiwar faďin mutuwar Atika domin basu san katse mishi shaukin da yake ciki...




Wayar Papy Daddy ya kira domin jin ko sun kusa isowa,
kashe wayar yayi yace wa Musaddiq "har sun iso bakaje ka daukosu ba,

"Zubair zai dauko su, Musaddiq ya faďi cikin girmamawa..


"Okk to, Allah ya kawosu lafiya, Daddy ya faďi haďe da sake jan sheik da hira....




Motar da Zubair ya sai mata farar matrix sabuwa dall ita ta tuko tazo gidan tare da kayan abincin da ta hadawa bakin,
koda ta isa gidan kiran Musaddiq tayi a waya dan ya fito ya tayata shiga da kayan,



Fitowa sukayi shi da Hilal suka kwaso kayan abincin,
tsokanar Musaddiq Faidah takeyi wanda ya sanyashi yin murmushi haďe da matsowa amsan tray din hannunta,



Garammmmm....
sukaji an saki kofar gidan da karfin gaske......





Mrs Tijjani Shatimah.....
[11/06 8:34 PM] +234 807 161 1811: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 7⃣2⃣
By *Aysha Ya'u kurah*







Anty....


Nadeeyah ta faďi cikin dashewar murya,
juyowa Raliya tayi ta sake kankame junior a kirjinta,

"Na'am Nadeeyah,

wayar dake hannunta da take kokarin kira Nadeeyah ta karba ta ajiye a gefe,


"Dan Allah kiyi min alfarma ďaya!

Dan Allah karki sanar da kowa dawowata,
inada dalilai masu karfi da in na faďa miki zaki fahimceni,
dan Allah Anty ki dubi maraicina kiyi min wannan taimakon!


Cikin sanyin jiki Raliya tace
"Nadeeyah nayi miki alkawarin in har dalilanki masu karfi ne zan taimakeki har sai kin cika burinki, faďa min kanwata....



Anty bani da gatan da wuce Allah,
bamu da asali ni da yan uwana kamar yadda ake faďi..
na taba ji a bakin wani malamin mu cewar Allah da ilimi sune gatan maraya,
babu wanda zai zama maraya sai rago,
sannan wannan ilimin shi zai sa ka samu yancinka a cikin al'umma,
a yanzu in na zauna tare daku, Mummy da su Anty Raudha bazasu taba barina in yi rayuwar yanci ba,
sannan bazan iya jurar ganin yaya Musaddiq da wa------

Shhhhhh...
Anty Raliya ta katseta saboda ganin junior na kokarin yin bacci,
sabashi tayi a kafaďa tace
"ina jinki?


Na dade da burin yin ilimi mai zurfi,
dan Allah ki goyamin baya in samu abinda zan tsaya da kafafuwa na,
banason mu kare a haka ni da zuri'ata,
kinfi kowa sanin rayuwar rashin gatan da mukayi mu da iyayenmu,
bana fatan mu kasance a cikinta ni da ďan da na haifa,
nayi miki alkawarin zan kare mutuncin kaina,
zan nemi kuďin halal inyi sponsoring kaina,
su uncle Taheer sunyi min duk abinda ya kamata dan uwa yayi maka,
yanzu zan fita in nema da kafata har Allah yasa na dace....



"Duniya nada faďi Nadeeyah,
ta ina zaki fara?
Gabas, yamma, kudu ko arewa?
Inada dukkan karfin da zan dauki nauyin karatunki a duk inda kike so,
bazanyi hakan bane sai da yardar wani naki,
shiyasa na kawo ki nan saboda ita kadai na sani a cikin yan uwanki, in yarintarki na faďa miki cewa duniya kankanuwa ce to kinyi kuskure,
domin ko a kaduna north kaďai aka barki an haďa ki da aiki dan bazaki taba sanin ta inda zaki fara ba,
ki dogara da Allah sannan ki nemi zabinsa akan duk abinda zai zame miki alkhairi a rayuwarki,
in karatun alkhairi ne ni zan dauki nayinshi har ki gama..
In kuma babu alkhairi to tabbas Allah zai nuna miki ta hanyar zama cikin yan uwanki...



Gyara zama Anty Raliya tayi bayan Taheer ya disa aya, kallonshi tayi tace
"Taheer zauna,
zauna muyi magana,
ka riga ka zama dan uwa,
babu abin da zamu boyeshi a gareka...


Bayan ya zauna ta kwantar da Junior ta dubi Nadeeyah,

"Tabbas maganganun ki gaskiya ne Nadeeyah,
nasani sarai a yanzu in har kika dawo cikin mu wasunmu bazasu bar rayuwarki da ta ďanki su inganta ba,
zan jure duk wasu matsalolin da nake gani a cikin yan uwana,
zan kauda tausayin nawa domin rayuwarki ta inganta,
nayi miki alkawarin babu wanda zaiji inda kike daga gareni,
yanzu inada wasu kuďaďe zasu kai 1.2m.. zan baka Taheer sai kayi amfani dashi ku koma can Canada da zama tunda Anty saude nacan,
in yaso duk abinda ciko ya biyo baya ka sanar dani,
sannan zan dinga turo da wasu yan kuďaden da zata dinga amfani dasu,
nayi alkawarin inganta rayuwarki da ta Daddyna in shaa Allah...


Hawayen dake zuba a kuncinta Nadeeyah ta share mata ta tsuguna tana mata godiya kamar zata bauta mata..

Kallonsu Taheer yayi cikin tausayawa da farin cikin cewar akwai mai kaunarta a cikin yan uwanta...

"Anty Raliya,
ba sai kin bani ko sisi ba,
nima ki barni in samu ladan marainiya,
babu mamaki sanadin hakan ya sanya na samu biyan bukata a gurin Allah sannan zanyi hakan sadakatul jariya Allah ya kai ladan kabarin mahaifina....



Murna sosai Anty Raliya tayi ta dinga mishi godiya da addu'ar samun abin da yake so cikin sauki ba tare da yasha wahala ba..



Bayan yaci abinci ya koma gidansu ya bar Nadeeyah da junior Anty Raliya nata

Please Login or Register in order to submit comment