Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har gida ya sami Barde,
Har kofar gida matan gidan suka rakata suna tausarta...




Cike da fargabar rashin son tashin hankali Hardejo yace
  "Ya zama dole in yi wani abu akan yarinyar nan,
buri na in samu kudin da zan kaita gaban iyayenta har can  egypt,
to a halin da muke ciki ko daya cikin kwatan kudin babu,
ga sarkar ta da nake tunanin saidawa an nemeta ko sama ko kasa an rasa,
dafe kanshi yayi yace "ya Allah ka nuna min hanyar da zanbi in ceci yarinyar nan daga sharrinsu Shaho...


Sallama dai...
dago kai Hardejo yayi cike da bacin rai yace "sau nawa zan maka magana akan cika sallama Muhammadu,
cike da girmamawa yace "Ayi hakuri, sai a hankali komai zai zauna min,
neman guri yayi ya raba ya zauna,
zuwa gidan yanzu duk dare ya zamewa Baffa jiki saboda zuwan Atika,
kallon Hardejo yayi yace "yanzu me ka yanke akan maganar Atika, shin zaka aurar da ita ga shaho ne tunda bamu da kudin kaita gida,
girgiza kai Hardejo yayi zaiyi magana ya kalli fuskar Muhammadu,
wani irin Hasken annuri yaga ya gifta a fuskarshi,
murmushi yayi yace "tabbas zan aurar da ita,
amma ga kai muhammadu,
kai zaka aureta saboda mu tseratar da rayuwarta daga azzaluman nan,
saida ya tsugune saboda tsoro,
ni kuma? A'a inaa,
sam bazan iya hada kaina da tashin hankali ba,
yo ta ina zan fara ma ma'u bayani,
sannan ni kake so ka bari da bala'in Shaho da iyayensa,
dariya Aisha tayi tace "matsoraci bashi zama gwani Baffan yara,
to dama ni nace miki ina son zama gwani ne? Ya fadi a harzuke,
dariya sosai sukayi,
Hardejo yace "yanzu dai fada min cikin biyu, wanne kake tsoro?

Ma'u,
wallahi bazan iya yi ma ma'u kishiya ba,
ka tuna fa rabo ta nayi daga can garin su na kawota nan ba uwa ba uba,
sannan yanzu inci amanarta, haba malam,
kaifa kace addinin ka ya hana cin Amana,

kwarai ya hana cin amana muhammadu, amma kuma shi addinin ya halasta auren mace hudu,
ko baka lura da matan dake gidana ba?
Kirne fusķa Baffa yayi yace "kai ai ka girma, ni fa?
duka yarana nawa,
biyu kadai sai ince zanyi aure,
ganin da hardejo yayi samm Baffa bazai fahimta ba yasa shi cewa "gobe zanje gurin Barde kawai a daura mata aure da shaho,
a kasalance Baffa yace "Haba malam!!
yanzu babu wata mafita sai wannan,
mafitar kenan, kuma kaki bamu hadin kai,

cike da Hikima irin ta mai ilimi Aisha tace "to me zai hana ya aureta har lokacin da zaka samu kudin da za'a kaita gida sai ya saketa, ta tafi,
yauwa mai babban suna kin kawo shawara Baffa ya fadi yana gyara zama,
yanzu kinga sai kije kima ma'u bayani gobe,
cike da mamakin irin tsoron da yakewa ma'u tace "babu matsala, in ka amince wannan duk mai sauki ne,
da wannan suka tsaida shawarar yadda zasuyi su taimaki marainiyar Allah daga sharrin ahalin shaho,
sam basu da masaniyar halin da zata shiga yafi wanda shaho zai sanyata,
wannan shine mafarin shigar baiwar Allah Atika cikin cakwakiyar rayuwar da zatayi sanadiyyar rayuwarta.....



A dimauce tayi wurgi da Boddo akan gado tace "samm bazai yiwu ba,
in har so yakeyi ya taimaketa ya saki wata a cikin matanshi ya aura,
in yaso sai ya maida ita bayan ya samu kudin kaita,
kuka ta saki da karfi tace "yanzu duk halaccin da nayi maka da wannan zaku saka min?
ashe ni dazu fadan da nayi da Gambo kaina na jawa,
ashe abin a kaina zai kare..

dakyar ya nutsar da ita hade da yi mata alkawarin bazai taba kusantar Atika ba, sannan yayi mata nuni da irin alherin da zasu samu da Atika,
"nasan kece kika dauki sarkarta! to in kinason sarkar ta zama taki har abada, kuma kinason ki samu mafiyansu in muka kaita gida ki bani hadin kai mu ceto rayuwarta,
alkawarin da nayi miki bazan taba canza shi ba...

ki yarda dani.....
(wannan kalmar nada matukar tasirin ruguza rayuwar macen da ke da saurin yadda).. Allah ka tsaftace mana zukatanmu, dan in mutum nada gurbatacciyar zuciyar da bata yadda da kaddara, to tabbas wannan kalmar ta sama zata sanya mutum cikin hadari in har aka samu akasin dagawar kalmar zuwa ga wani muhallin na daban...
Allah ka taushi zuciyar dukkan matan musulmi su yarda da kaddara in tazo garesu.....





Washe gari tun karfe goma na safe Hardejo ya daura Auren Atika da Muhammadu a sadaki nairah bakwai da sule biyar,
cikin kudin da ya fara tarin tafiyar ya cire ya biya dan yasan Baffa bazai biya ba,
bayan shaidu sun shaida daurin auren,
Hardejo yayi adduo'i sosai na neman tsari a garesu da samun zuri'a a tsakaninsu..
dan shi kam yana hango ma kaninshi alherin kasancewarshi da Atika,
zuwanta garin ma kaddara ce rubutacciya,,
(Abinka da adduar mutanen da, masu tsantseni da tsananin tsoron Allah,
malamai masu tsaftatacciyar zuciya wadanda basu san meye sabon Allah ba,
malaman da Allah ke amsa adduarsu cikin gaggawa saboda tsantseninsu.)......





Juyi yakeyi sosai yana rike da kirjinshi da yake jinshi kamar ya fitar dashi ya yar ya huta,
ba ciwo yakeji ba,
amma abin da yakeji yafi ciwo zafi,

Muryar mahaifiyarshi yaji tana shararo Ashar tana fadin yau lahira zatayi baki,

Da karfi shaho ya kwala kiran sunanta,
gurinshi ta nufa da sauri tana fadin kaji Hardejo ya aurar da matar da naci burin aura maka,

dan tsaki yayi yace "Gambo ke kike ta aure,
bakya ganin halin da nake ciki,
ko bacci bana iya yi,
daga na runtsa fuskar saurayin da na kashe nake gani yana matsowa kusa dani zai illata ni,
mafitar halin da nake ciki zaki nema, ba wai maganar aure ba,

cike da alajabi tace "yau ka fara kashe mutum?
a kiyasin da nayi ka kashe ya kai talatin banda dabbobi,
meyasa zaka sa wannan a ranka,

Katseta yayi yace "wannan na daban ne Gambo,
duk sauran kisan da nayi musu akwai kwakwkwarar hujjar yin hakan ya karashe ido yayi mishi jajur,
kasa daure damuwarta tayi tace "tashi muje gurin Hardejo,
tashi maza,
bazan juri rashinka ba Shaho,
mikewa yayi jiki babu kwari suka kama hanyar gidan Hardejo....




Allah gafurur rahim,
lallai "Bala Shaho" Allah yana sanka da rahama,
wannan abin da kakeji Allah ne ya fara nuna maka illolin abinda da kake aikatawa,
lallai jinin Habibu jini ne na mu'imini,
Adduoin da iyaye da yan uwanshi sukeyi akanka bazai taba barinka kayi sukuni ba,

A farkon zuwan musulunci kauyen nan, naso mu rugumeshi cikin tsaftatacciyar hanya,
amma sam kuka ki,
kuka amsheshi sama sama,
ku ka dinga aikata sabo saboda ance muku ko an aikata Allah na yafewa,

cike da kunan zuci shaho yace "maleee, (sunan da suke ce mishi kenan cikin isgili) yanzu ka fada min abinda zanyi in daina jin wadannan abubuwan da nake ji,
gyara zama malam yayi ya mishi bayanin addinin Allah da duk abinda Allah bayaso,
sannan ya daura mishi da cewa "ta yiwu Allah ya yafe maka saboda kayi abubuwan da kayi a baya cikin rashin sani,

kasan Allah baya kama mutum da laifin da baida masaniya akai,
sannan sharadin tuba,
sai ka tabbatar in ka daina ji da ganin abin da kake gani bazaka sake komawa cikin aikata sabo ba,
'""Bazan sake ba malee"" ya fadi da sauri,
ni kadai nasan irin wahalar da nasha,

to Alhamdulillah Hardejo ya fadi yana murmushi,
sannan ya fara koyar dashi kalmar shahada da kuma istigfari,
ya horeshi da yin istigfari kafa dubu a kullum saboda yana kankare zunubai,
sun dade tare yana koya mishi abubuwa zuciyarshi na samun nutsuwa,

ita dai Gambo zama tayi kamar gunki tana kallon sabon mutum a gurin danta,
da yake ita din mace ce mai son danta, da duk abin da yake so nan take itama tayi mubaya'a,
malam Hardejo ya cigaba da fadakar dasu akan abubuwan da Allah keso da wanda baya so.....





Rayuwar Atika a gidan Baffa, Rayuwace da ta fara yinta kadaran kadaham,
sam ma'u bata kishi da ita saboda sanin yanayin da sukayi auren,

da fari ta fara bijirowa da cewa tunda yanzu Shaho yayi nadama ya shiryu mai zai hana Baffa ya saketa ta koma ta auri shahon,

a lokacin taga ainihin Fillo Hardejo,
dan saida yayi mata wuzu wuzu sannan ta maida hankalinta,
da yaga ta nutsu ne yasa shi ya koma lallashi,
ya cemata ta sani ko tuban muzuru Shaho yayi,
irinsu ba'a gane tubansu har sai an musu gwaji mai karfin gaske,

cikin hikima ya kwantar mata da hankali,
samm baya ko kaunar hango rabuwar Atika da Muhammadu saboda yasan ko babu rayuwarshi Atika zata zame ma dan uwanshi alkhairi.....



****

Ashe dai ma'u baki da hankali ban sani ba kuma ban gama tabbatarwa ba sai yau,
yanzu har wannan tsaleliyar budurwar Baffa zaice baze kusanceta ba kuma ki yarda,

naman zomon da ta gasa takai bakinta tace " Haire am niko nake da hankali,
an fada miki hakanan na sakankance,
ai ba sakarai nake ba,
nasan yadda Baffa yake da sakarcin nan akan mace wata rana zai iya kusantarta a bayan ido na,
shiyasa na aika can garinmu gurin "Iyan gida" ta amso min gadalin mu na ukari,
sannan ta hada da duk wata mallakar maida mace namiji a idon Baffa,
yaushe zanyi wannan wawancin a barni in zama yar kallo,
ai dole na mike tsaye ko dan yadda Hardejo ke nuna min ita din kamar yarshi take ta jini,

shewaaa sosai sukayi hade da tafawa,
dariya Bingel tasanya itama ganin mahaifiyarta na dariyar babu kakkautawa,
dariyar tata ta sake sasu wata dariyar hade da kai naman zomon na karshe cikin bakinsu....



Kallonsu Atika tayi itama tayi murmushin saboda bata san abun da suke fadi ba,
kara gyara goyon boddo tayi tana jijjigata tana mata wakensu na larabawa,
tunanin Ateek ta tafi wanda ya zame mata tamkar shan ruwa dan kullum,

Ya Allah ka dubamin Ateek.. kalmar kadai take ta maimatawa cikin harshenta na larabci......


Mrs Tijjani Shattima......
[02/03 9:59 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 2⃣5⃣
By *Aysha Ya'u Kurah*





*RUBUTACCEN AL'AMARI*



Sauri sauri yake yi dan samun sahun gaba a cikin masallacin kofar gidan Hardejo wanda Barde da Gambo iyayen shaho suka gama gininshi,
dabe ne na kasa suka bada kudi aka hada karfi da karfe aka ginashi cikin gaggawa,


Shaho ne tsaye a kofar shiga yana sallama ga duk wanda yazo shiga, sanin muhimmacin Sallama da yayi, da kuma irin ladan da ake samu ya sanyashi a koda yaushe fara yin ta ga duk wanda yayi tozali dashi..


Bayan idar da Sallah Malam Hardejo ya zauna a tsakiyarsu ya fara janyo musu wa'azi mai kashe jiki,
kowa a cikin massalacin saida ya nutsu,
zuciyoyinsu suka narke matuka da tsoron Allah,
a cikin wa'azin ya sako musu muhimmacin aure da kuma hakkin da mace take dashi akan mijinta,

"Hakkin duk wani namiji ne ya ciyar da matar shi,
Hakkinshi ne ya tufatar da ita, sannan Hakkinshi ne ya sauke duk wata bukata tata,
lissafo bukatun yayi cikin hikima, sannan ya tunatar dasu azabar da mutum zaisha a gurin ubangiji in bai sauke wannan hakkin ba, wa'azi sosai yayi mai cike da tausayi da al'ajabi...
jikin kowa a sanyaye suka tashi suka fita daga masallacin,
matsowa Bala (shaho) yayi kusa da malam yace "Assalamu Alaikum, a sanyaye Malam ya miko mishi hannu suka gaisa hade da yiwa juna murmushi, kayi hakuri Bala,
yau jikina baya min dadi, bazamu samu damar yin karatu ba, murmushi Bala yayi yace "Babu matsala Malam, Allahn Hardejo ya kare ka da lafiya,
dariya malam yayi yace "Allahn mu gaba daya, gatan mu, kuma gatan zuri'armu....



●●●●●●●●●●

A hankali ya tura kofar gidan ya shiga,
wa'azin Hardejo keta kai komo cikin kwakwalwarshi, zama yayi a tsakar gidan kan wani dakali, tunani ya dingayi na yadda zai sauke hakkin marainiyar Allah akanshi,
ga kuma alkawarin da yayi wa ma'u shima kuma Allah baya son mai saba shi,
yana cikin wannan tunanin ne ruwa ya kece a kanshi,
mikewa yayi da niyyar wucewa daki sukayi karo da Atika ta fito ta kwashe kayan da ta wanke a kan duwatsun shanyar gidan,
matsawa baya yayi da sauri yana mayar da numfashi,
rab'awa tayi ta wuce ta kwaso kayan,
kafin ta gama kwashe kayan gaba daya ta jike sharkaff,
kallonta Baffa ya tsaya yi shima ruwan ya jikashi sosai,
saida ta gama kwashewa tazo wucewa yaji ta dan gogeshi da kaya sannan yayi firgigit ya gane ta wuce,
yasan ma'u bata gidan,
tana can gidan inna wuro tare da yara,
da jan kafa ya bita dakin,
cikin kudurar ubangiji ya fara jin wani abu na fusgarshi game da ita,
shaukin da bai taba jin irinshi ba ya shiga,
a hankali ya kusanceta ya taimaka mata ta rabu da jikakun kayan jikinta,
tuni labarin ya canza zuwa wani sabon babi na shafin labarin....


Mikewa yayi jiki a sanyaye zuciyarshi kamar an sauke nauyin da yakai girman dutsen mambila,
ita kuwa azaba ta hanata yin kuka, dakyar ta iya tashi,
abinka da mutumin "da" shi ficewa yayi yaje bayi ya wanke jikinshi ya barta a cikin dakin,

A daddafe ta fito tsakar gidan, tunanin yadda zatayi ta rabu da wannan azabar da take ji take yi, dakyar ta iya ďiban ruwa ta wuce bayi,
tsugunon ma zame mata aiki yayi amma haka ta daure dan dai kawai ta daina jin zafin gurin, tana watsa ruwan sanyin tayi wani irin ihun azaba,
tsakar gidan ta fito tanata safa da marwa tana zubar da hawaye tana kiran sunan Allah,

Azaba kam iya azaba Atika tasha ta a wannan ranar domin ko abincin kirki babu a gidan gashi babu abin da zata iza wuta ta sa ruwan zafi,

A haka tayi tsaye tanata kuka a gurin har dare ya farayi,

surutun Ma'u ta fara ji sama sama a kofar gidan,
nan hankalinta ya fara kwanciya, tasan zata samu ko dan abinci ne taci,

sallamaa dai Amarya,
hannu tasa ta karbi Boddo dake kuka jikinta jike da fitsari,
saboda duhun dake tsakar gidan Ma'u bata lura da yanayin tafiyar Atika ba,
daki ta shiga ta yayo yayi ta fito ta dauko dutsen kyasta wuta, kyasta shi tayi cikin yayi nan take haske ya bayyana,
bata kara bi takan Atika ba ta wuce daki ta dauko ragowar Tuwon da sukaci da rana,
saka iya wanda zai ishesu tayi a tukunyar kasa dan ta dumama,
ta zubawa Atika mai sanyin a cikin roba ta tura mata,
dakyar ta iya dukawa ta mika mata Boddo, sannan ta dauki tuwon,
can baya taje ta zauna dakyar tanajin radadin a can kasanta, tsabar yunwar da takeji yasa bataji sanyin abincin ba ta dinga turashi tana zubar da hawaye,
muryar Bingel taji akanta tana share mata hawaye tana bata hakuri,
wani sabon kukan ne ya kufce mata hade da rungume Bingel wacce itama kukan takeyi....




11:34pm●●●●

Tsugune take tana wanke geron safe tana gyangyadawa hade da shashshekar kuka,
sanyin dake shigarta ta sama da kasa shi ya haifar mata da rawar sanyi sosai,
jingina tayi jikin kwaryar ta fara kiran sunan Allah a cikin ranta, nutsuwace ta fara ratsata kaďan kaďan har bacci ya soma ďaukarta,
ko mintina biyar batayi ba taji muryar Baffa da ya lallabo ya fito yazo inda take,
murya kasa kasa yace "Atika, Atika,
tashi muje ki kwanta,
Kuka sosai ta fashe mishi dashi cikin yarenta na larabci wanda bayaji tace "Dan Allah ka kaini gurin "ummi Aisha",
sunan Aishan da yaji ta kira ne yasa shi cewa "Mai babban suna? Gyada kanta tayi jikinta na rawar sanyi,
Yace "to me mai babban suna tayi?
Ganin da tayi bai gane abun da tace bane yasa ta mike ta fara tafiya dakyar,
wani tausayinta ne ya ratsashi ya tuna abin da ya mata dazu kuma bai samu damar tsayawa ya taimaka mata ba saboda kar ma'u ta dawo,
takawa yayi da dan sauri ya isa gareta ya kamo hannunta ya zaunar da akan dakali,
dan ihu ta saki ta mike tsaye saboda zafi,
"yi hakuri ya fadi jiki a sanyaye tsoro duk ya cikashi,
yaayi ya debo da yawa ya iza wuta ya daura ruwa,
saida ya tabbatar ruwan yayi zafi sannan ya juye mata cikin kwarya yayi mata nuni da ruwan,
da sauri ta matso kusa da ruwan bata damu da tsayuwar da yayi a gurin ba, ta cire kaya ta tsugunna ta fara tsarki tana kuka sosai saboda azaba,
saida ta tabbatar daga zafi ta fara jin dadi sannan ta watsa sauran ruwan a jikinta,
kayanta ta dauka tasa ta wuce dakin da take kwana ta runtse idonta ko baccin da ta fara zaizo ya dauketa,
saidai fa bacci yace ki nemani inda kika ajiye ni,
mikewa tayi tana adduo'i tana rokon Allah abin da yafi zama mata alkairi koda kuwa ace mutuwa ce,
ta tabbatar da yanzu bata da ragowar gata daga Allah sai Hardejo,
shi kuma Hardejo sam bashi da masaniyar halin da take ciki,
da wannan tunanin ta fara gyangyadi har bacci mai cike da mafarkai yayi gaba da ita.....





Watanni uku sun shude,
watanni masu cike da tsananin wuya ga Atika,
duk wani aikin gidan na karfi ita take yinsu, kama da wanki, surfe, da sauransu,
a cikin watannin an samu sauyi na cigaba sosai a kauye,
cigaba daga bangarori da dama,
sannan ci baya ga Baffa,
kullum kwanan duniya sai shanayen da aka bar musu da wadanda ya siyo da kudinshi sun kasa,
saidai ya yanka ya kaisu kauyuka domin a saya,
a haka ne ya zamto mahaucin karfi da yaji,
bai kara marmarin bi takan Atika ba saboda kar tsautsayi yasa har ma'u ta gane,
a cikin wannan halin Ma'u ta dage da sana'oi kala domin ta yi hidimar gidanta da ya'yanta,
Atika itace karfin sana'oin domin ita ke yinsu amma ko dankwali Ma'u bata taba tunanin siyan mata ba...



Yammacin ranar asabar Ma'u na tsugune tana gasa naman gafiya, nan take kamshi mai hade da kauri ya gaurayen gidan,
sannu a hankalin kamshin ke ziyartar hancin Atika dake tsugune tana goga gero a jikin dutse,
tun tana daure jin kamshin har ya gagareta tayi saurin mikewa baki cike da amai ta dinga kwaro shi,
saida ta amayar da komai na cikinta,
ta zaune a gurin tana maida numfashi bayan ta dauraye bakinta,
Bingel wacce ta zamo kawar hirarta ita ta matso da sauri tana shafa mata kai,
ita kuwa ma'u sam bata kawo komai a ranta ba sai ma cigaba da gashi da tayi,
duk tunaninta shawara ce ke damunta, tana gama gashin ta kalli Atika shekeke tayi mata nuni da geron,
a hankali ta mike ta koma bakin aikinta,
tana kallon ma'u ta kasafta naman ita da ya'yanta,
dama naman bai bata sha'awa ba samm,
aikinta ta cigaba dayi,
in kaga yadda take aikin sai ka dauka baiwa ce...,

Jin nama tayi a saitin bakinta,
da sauri ta dago taga Bingel a tsaye tana mata murmushi,
a kasonta ta cire mata da yawa dan taga ba'a bata ba,
wani aman taji ya kara tahowa gadan gadan,

wannan karan a gurin ta sakeshi, wata irin Ashar Ma'u ta saki tace "A kan gari na kikayi min amai,
bata karasa maganar ba taji ta kara kwararo Aman har akan dutsen,

"A'a wannan ba lafiya ba, Ma'u ta fadi tana matsowa kusa da ita,
hannunta ta finciko ta duba,
jiki na kyarma ta daga mata riga, ganin da tayi nonuwanta sun ciko kansu yayi bakikkirin ya sata sakin wata yar kara hade kiran sunan Allah,
ciki gareki?
Ciki gareki Atika?

Babu mayafi haka ta fita ta nufi gidan Haire dan taga Atikar zata bata mata lokaci,
a tsakar gida ta samu Haire da maryam yar Hardejo tana koya musu karatu,

"Haireeeeee ta fadi da karfin gaske,
a kidime Haire tace "lafiya Ma'u? Kuka ne ya kufce mata tace "Haire Atika ciki gareta,
mikewa Haire tayi tace "ci me? Ciki Ma'u ta fadi cikin rawar murya,
Gaba daya idonsu ya rufe sun manta akwai Maryam da yar Hairen kawar maryam a gurin,

"anya ma'u ciki ne, ba kince Baffa bai taba kusantarta ba,
to waye ya mata cikin?
Ma'u tace "nima tunanin da nakeyi kenan,
mayafi Haire ta dauko tace "muje gidan,

Suna fita maryam tace ma Laraba "bari inje gida bayan la'asar zan dawo,
Laraba tace "to sai kin dawo, kinga zanyi aiki da na raka ki,
"babu komai maryam tace sannan ta kwashe yan littafanta tayi gida...




Da gaske kike Maryama? Wallahi ummi (sunan da Atika ta radawa mai babban suna kenan) dagaske nake,
Aisha batayi kasa a gwiwa ba tasa yaro yayi mata magana da Hardejo,
kwashe komai tayi ta fada mishi sannan tace
"Dama Laminjo tasha fada min halin da Atika take ciki a gidan, bana kamawa ne saboda kowa yasan Laminjo yawancin maganganunta karya ne,
rai a bace Hardejo yace "ki shirya zansa Bala ya rakaki sai kuje ku taho min da ita,
tunda Muhammadu ya fara tafiye tafiyen nan nasan lallai rayuwar Atika na cikin garari..

cikin gida Aisha ta shiga ta shirya tsaff da mawafi,
Bala shaho wanda a yanzu ya zamto shakikin gidan Malam Harďejo shi yayi mata rakiya har gidan..


A tsakiya suka sata suna ta jero mata tambayoyi irin na kurame,
da haushi ya ishi ma'u ta tashi ta dauko sandar shaďi ta fara narkarta dashi,
bata taba raba dayan biyu Baffa ne yayi cikin nan,
dukanta takeyi sosai Haire na tarewa tana faďin karki kashe musu 'ya Ma'u,
ki bi komai a hankali,
wani irin hankali zan bishi shi amm,
ni Baffa zai ciwa amana?
Ni zai ha'inta?
kuka sosai takeyi tana dada narkar baiwar Allah da sanda,

kwace sandar Haire tayi tace "shiyasa nace baki da wayau Ma'u,
in ba rashin dabara ba kya fara jibgarta, maimakon ki bari mu yi komai cikin hikima,
ga magunguna nan da zaisa cikin ya fita cikin makwarara....
Saidai kiga bin makwarara a gidanki da yardar Allah Aisha ta fadi tana karasa shigowa cikin gidan rai a baceee.....



Mrs Tijjani Shattima.....
[03/03 9:47 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 2⃣6⃣
By *Aysha Ya'u Kurah*





*Rabon Ajali*


Da gudu Bingel ta rungume Aisha tana kuka tana fada mata irin dukan da mamanta tayi ma Atika, share mata hawaye tayi tace "Allah ya turo mai cetonta Zainabu,
in da take tsugune suka karaso Aisha ta dagata tace "muje can gida,
in shaa Allahu daga yau kin bar zaman wahala,
cikin nan kuma sai kin haifeshi koda kuwa dukkan kauyen nan zasu taru akanki,
kuma dole ya amsa sunan Muhammadu a matsayin uba,
wani irin kululun bakin ciki ne ya ziyarci Ma'u,
bata dubi girma da darajar da Aisha kedashi a kauyen ba ta fara zaginta,
ta inda take shiga bata nan take fita ba,
Aisha dai bata waigo ta kalleta ba tace "sai dai ki mutu da bakin ciki dan cikin nan babu abin da zai hanashi zuwa duniya,
wani sabon faifan zagin ta bude idanuwanta sukayi jajur,
asalinta na arniyar ukari marar imani ya bayyana a jikinta,
da sauri Haire ta toshe mata baki tace "mai babban suna kike zagi Ma'u?,
kinason Allahn Hardejo yayi fushi da dukka yan kauyen nan ne?, idan hankali ya gushe nemo shi akeyi,
cike da masifa ta ture Haire tace "wallee sai kunga abinda zai sameku, dukkanku, badai ni *NANKWAT MANASIR* kukayi wa haka ba,(sunanta kenan kafin haduwarsu da Baffa) walle duk sai kun gani,
ta finciko hannun Bingel hade da daukar Boddo ta fice a gidan, hakuri Haire ta bita tana bata, sam bata saurareta ba ta wuce da yaran, Bingel na kuka taki ko kallonta bare ta kula da abinda take so,


Alkhairi!!!
in shaa Allah Aisha ta fadi tana kallon ma'u da tayi nisa da gidan,

gida suka wuce suma Haire na biye dasu tana fadin "Dan Allahn Hardejo kiyi hakuri mai babban suna,
walle ko taba jikinta banyi baa,
katseta Aisha tayi tace "Babu komai Haire, kowa yayi nagari dan kansa...



Suna isa yaran gidan suka rugo suna ihu hade rungumeta,
dama sunyi kewarta matuka dan ma'u bata yarda suzo gidansu,
Matan Hardejo ma suka fito suna musu barka da zuwa hade da jajantawa Atika,
Ďaki Aisha ta wuce da ita, tasa maryam ta iza wuta tasa ruwan wanka,
kafin ruwan yayi zafi ta dama mata fura da nono,

Please Login or Register in order to submit comment