Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haneshi cike da zolaya yace

"To ko zaka fara bauta min ne, dukkan ku kannena,
sorry nd thank u is not allowed, kar in sake ji plss,
babu abinda nayi Allah ne ya kaddaro hakan, shi ya taba zuciyata har na fahimci komai, sannan ya bani ikon sadaukarwa, ka gode mishi, domin shi ya gama maka komai...



******************



Ai ni Abubakar bazan taba amsa maka,
kaje can kayi rayuwarka,
u left me all alone,
kaji daďin zaman india ka mance damu,
Daddy ya karashe yana mai tada motarshi,
brown jallabiya ce a jikinshi wacce ta amsheshi sosai,
jin shurun da gidan yayi ne ya sanyashi fitowa dan nemo lipton din da zaisha,
yasan mutanen gidan sunyi baccin gajiya dan basu dawo gida ba sai kusan tara da rabi na dare...



"Haba Kyari,
kasan u are always in my heart, nasan ban kyauta ba,
amma ya zanyi aiki ya hana ni sukuni,
ga makarantar yara,
kayi hakuri in shaa Allahu karshen watan nan zanzo...



Kace zaka zo a sa'a, zaka zo ka tarar da Amarya,
Daddy ya karbe maganar daga bakin Uncle Abu..

Gyara zama uncle Abu yayi yana murmushi yace
"Kyari aure ka kara?
Lallai kana jin daďi,
ko wannan ma zaisa ni in dauki hutu in taho..


Ai sai ma kaji wacce na aura,
Abubakar duniya nada faďi,
duk inda kaje ka dawo juyo maka takeyi,

Kasan wacece amaryar tawa?


"Ya za'ayi in sani,
ko an faďa maka karatun sanin boyayyen alamari nayi..


Dariya sosai suka kece dashi bayan furucin uncle Abu,

"To sarkin bakar magana,
rike abunka,
ka kuma buďe kunnuwanka,
Amaryata ba wata bace face *SAUDEN ALHAJI HALLIRU*....



Saude dai?
Uncle Abu ya tambaya ciki da mamakin wannan kudira ta ubangiji,


"Ita fa, Saude ďalibarka,

Daddy ya faďi cike da jaddadawa...


Hukumullah Uncle Abu ya faďi haďe da rufe laptop din gabanshi.

"Allah ya cika burin ran da ya shekara yana bara,, ya furta a hankali,
ya daďe da sanin irin soyayyar da Sauden keyi wa Daddy,
a lokacin duk littafanta sunanshi ne a jiki,
sannan yaga wasikar da ta boye cikin littafinta da ta mishi ranar da zasuyi haďuwar karshe da ita,

Ashe kaddara na nan sarkafe da su,
cike da farin ciki yake labartawa Daddy abubuwan da ya sani a baya,
ya karashe da cewa

"Ashe tana nan a raye,
kai naji daďi matuka Kyari,
in shaa Allahu ina nan tafe next upper week...


Da murnar zuwanshi sukayi sallama kowanne ya kashe wayarshi cike da kewar ďan uwanshi......






Nishaďi zallah...
shi Daddy ya tsinci kanshi bayan gama waya da Amininshi sannan kuma ya jiyo sirrin da ya sanyashi ya sake bawa Anty Saude matsayi a cikin zuciyarshi,

Big treat yaje ya siyo snacks sannan ya tsaya ya sai lipton ya wuce gida..


Yana yin parking yaji karar shigowar sako a wayarshi,
bai duba ba dan yasan sakon bai wuce daga gurin Anty Saude,
rufe motar yayi ya wuce ciki,
duk wanda ya ganshi a wannan lokacin yasan yana cikin farin ciki matuka,
wani sabon farin cikin da ya tarar a parlon gidan na ganin su Musaddiq zaune suna hira da Hilal shi ya sanyashi karasowa ciki da sauri haďe da mikawa Maleekah dake zaune a cikinsu ledar yace ta bashi ruwan Zafi,

A ladabce ta karba ta ďaura little Nadeeyah a kan cinyar Hilal ta wuce kitchen...




Wata sabuwar hira ce ta barke a tsakaninsu dukkaninsu sunajin daďin da suka dade basu ji ba yana ratsa dukkan sassa na jikinsu,
cikin hirar ne Daddy ya sako musu nasiha mai ratsa jiki da kuma nuna musu muhimmacin addu'a a rayuwa,
sai kusan Sha biyu da mintina Daddy ya wuce sama dan yaga hirar tasu ba mai karewa bace...



Ganin wucewar Daddy ne yasa Musaddiq daukar wayarshi dan kiran Maleekah yaji ko har yanzu idonta biyu,
tun da suka dawo gidan yake tsananin son ganin mallakinshi,
so yakeyi yaga yadda ta ďaukeshi, har yanzu tana fushi dashi ko kuwa ta sakko,
ko da ya shiga dakin ya samesu duk sunyi bacci,
ita gaba ďaya ma ta dunkule kanta cikin bargo baka iya ganin fuskarta,
bayajin zai iya runtsawa ba tare da yasan makomarshi a gurinta ba...
ganin har wayar ta katse bata ďauka ba yasa Hilal kwace wayar yace
"Karka damar min mata,
ohh wato dan haka ka hanata kwana gurin nata iyayen ko,
to bazan ďauka ba,
tashi muje mu kwanta,
tunda yanzu ka samu sauki ai bazamu huta ba..


Dariya Musaddiq yayi ya mike suka nufi sama suna tsokanar junansu....





Da asubar fari karar wani sakon ya kuma shigowa wayar Daddy,
dafe kanshi yayi dan samm ya manta da sakonta na jiya,
da sauri ya karasa azkar ďin da yakeyi yayi adduo'i ya shafa ya naďe daddumar ya maida ita mazauninta, sannan ya wuce gefen gado inda wayar take..


Sakon daren jiya ya fara karantawa wanda take faďa mishi sirrin zuciyarta,
a karshe kuma ta bukaci sanin ranar da zai maida ita tashi, ma'ana ya dawo da ita cikin gidanshi...



Sako na biyun wanda saida ya sashi darawa,
cike da kauna da tsananin tausayawa ya furta,


"Babu namijin da zai ki ki *Saudatul Khair*...
in shaa Allah zan saki farin ciki har karshen rayuwarki....




Reply mai daďi yayi mata wanda ya sanyata peacefull sleep wanda bata samu yi ba da safiyar ranar...





Waigowa yayi dan ganin wanda yake mishi sallama,
mikewa yayi zaune yana murmushi yace

"Nadeeyah shigo mana, kece kike ta sallama, da kin shigo tun ďazu ai..

Tsugunawa tayi daga can nesa tace
"Ina kwana Daddy?

"Lafiya kalau Nadeeyah, kin tashi lafiya?, ya amsata cike da fara'a...


Kasa ta sunkuyar da kanta tace "Lafiya lau..


Shuru ne ya ďan ratsa a cikin ďakin..

Murmushi Daddy yayi ya katse shurun ta hanyar tambayarta abun da ta ke so,


Wani shurun ta sakeyi wanda hakan yasashi cewa

"Ko kinada wata matsala ne?
Ko auren da aka miki ne bakya so, in shine kiyi saurin faďa min dan bazan so a shiga hakkinki ba,
ke 'yata kamar yadda Husna take, saboda haka feel free ki faďa min kinji...



A hankali ta ďago kanta tace
"Daddy dan Allah kayi hakuri da abin da zan faďa maka,
kayi min wannan alfarmar guda ďaya takk,
dan Allah ka dawo da Mummy,
wallahi hankalina ba'a kwance yake ba in na tuna sanadiyyata kuka rabu,
dan Allah kayi mata afuwa, nasan bazata sake ba..



Ajiyar zuciya Daddy yayi dan duk tunaninshi zata kawo mishi korafin aurenta ne,

"To Nadeeyah, naji, zanyi shawara, in shaa Allah duk abin da ake ciki zaki gani...


"Daddy da wa zakayi shawara in ba damu 'yayanka ba?
Husna ta faďi bayan ta shigo ta ďakin,
Dariya yayi yace
"Me kuke bani da zanyi shawara da ku,
shawara ta manya ce, da su zanyi...

Daddy dan Allah kayi hakuri ta faďi a shagwabe kamar zatayi kuka...

"To duk naji ku tashi ku tafi, Allah ya yafe mana baki ďaya,
in shaa Allah zan duba maganarku,
kuma in wani ya sake magana zan canza shawara ya karashe cike da zolaya....




Karfe ďaya na rana a gidan Baffa tayi ma Daddy,
bayan sun gama gaisawa da Anni ta kawo mishi abin sha ta zauna can nesa dashi suna ďan taba hira kafin Baffan ya fito..


Cikin hirar ne ta sako mishi maganar da yazo dan suyi da Baffa,
Nasiha sosai tayi mishi akan irin ladan da masu hakuri suke dashi a gurin Allah,
bayan ta gama ta rokeshi Allah da Annabi ya mayar da Mummy ďakinta,
tana tsaka da maganar Baffa ya fito yana mai jin dadin sauyin da ubangiji yayi mishi na mace ta kwarai..

Fitowar Baffa yasa ta takaita maganar ta basu guri dan su tattauna...




Farin ciki da murnar da Baffa yayi na amincewar Daddy ba ta misaltuwa,
cike da gaggawa ya kira Papy wanda suke tare da Abbu ya sanar mishi sannan ya umurceshi da suzo domin ayi ďaurin auren a masallacin kusa dasu bayan an idar da sallah...





Labarin ďaurin auren bai isa kunnen kowa a cikin matan gidan ba saboda duk yaran gidan basu da labari,

Saidai fa Anni ta kasa boyewa ta shirya ta wuce gidan da Mummy take,


Zaune ta sameta tana lazumi da carbi a hannu,
tun mutuwar Ma'u ta cika da tsoron ubangiji hakan yasa ta komawa Allah saboda kar tayi mutuwa makamanciya ko fin haka...




Bayan ta sallame ta gaisar da Anni cike da mutuntawa..


Anni bata amsa mata ba sai washe baki kaďai takeyi,
naďe dardumar Mummy tayi tace "Anni me muka samu ne,
irin wannan annashuwa haka?


Dole inyi farin ciki Mummyn yara,
addu'ar da muka daďe muna yi Allah ya amsa ta.


Cikin rashin fahimta Mummy tace "Wani abun alkhairin ne ya same mu?


"Alkhairi kai,
taho ki zauna,
nan fa ta dinga yi mata nasiha cikin hikima da ďaure kai,
a karshe ta sanar da ita taje saloon ta wanke kai,
Abdallah (Papy) zai kawo miki sutura ki zabi mai kyau sai ki shirya bayan isha'i angonki *ALHAJI MUKHTAR KYARI* zai zo ďaukar uwar 'yayanshi..


Ya ilahi, zo kuga kukan farin ciki gurin Mummy,
da azama ta maida dardumar tayi sujjudl shukr,
tana idarwa ta kankame hannun yar tsohuwa Anni wacce itama idonta ke fidda ruwan farin ciki..



"Nagode Anni,
Allah ya saka miki da gidan aljanna firdausi,
nagode kwarai..

Mu godewa Allah, shi ya yanke miki wannan wahalar,
Allah ya kauda fitina,
Dan Allah ki zauna da abokiyar zamanki lafiya...


"Yar uwa ce Anni,
tayi min karamcin da bazan manta ba,
sun taimaki rayuwar ďana,
niko in ba butulu ba yaushe zan ďauketa kishiya...


Sunfi awa suna hira har su Anty Reemah da labarin ya iskesu ta gurin Hafeez suka iskesu a gidan suma cikin farin ciki.


Daukarta sukayi suka wuce Hadidi dan a wanke mata kai, kafin a gama sun tafi Senegalese inda ake saida ready made na manyan mata, nan suka siyo mata lace kala biyu da shadda kala biyu, atamfa ce kaďai basu samu ba, daga nan suka wuce shagon takalmi,
flat kala biyu suka sai mata sai gyale da turaruka masu sanyin kamshi....






A masallacin kofar gidan su Anty Saude Daddy da Papy sukayi Sallah,
bayan sun idar suka nufi cikin gidan da taimakon Taheer wanda ya maida komai ba komai ba, ya sanya mahaifiyarshi haďashi da duk wacce taga tayi mata a lokacin da take so...




Parlon yasha gyara sai kamshi mai taushin sanyi ke fita daga cikinshi,

Cikin biyu daga kujerun da suka kewaye parlon suka zauna suna karewa hoton mahaifin Taheer kallo,
babu inda ya bar sarki saidai hasken fata da shi sarkin ya ďara shi.


Sake gaishesu Taheer yayi a mutunce sannan ya wuce ďaki dan barinsu su wala a cikin parlon..


Gidan yayi musu kyau matuka, ga tsafta da ta wadaci ko ina na cikinshi, suna ďan taba hira suka jiyo alamar shigowar masu gidan, Shareefah ce sanye da hijab sai Raahila itama cikin nata hijabin sun sanya Anty Saude a tsakiya,


Wata doguwar rigar leshi ta sanya wacce ta fito da kyaunta da masu gyaran fuska suka kuma matso shi,
murmushin da takeyi shi kanshi na musamman ne, tunda ta shigo parlon take kokarin haďa ido da mutumin da ya mamaye ruhinta, da kyar kunya tabar shi ya iya kallonta saboda yadda su Raahila suka kureshi da ido,
kan doguwar kujera suka zauna aka gaggaisa sannan Shareefah cikin tsokana tace

"To nawa za'a siya baki? kasan al'ada bata tsufa, kuma soyayya a wannan lokacin tafi ta yarinta daďi.....


Cike da fara'a Papy yace kwarai kuwa,
Matured Minds,
to mudai kunsan bamu da kuďin siyan baki,
dan amaryar nan tsada gareta, saidai muyi addu'ar Allah ya sanya wa auren albarka ya kauda fitina.

Ameen Rahila ta faďi cike da yaba kalamanshi,
ta cigaba da cewa "ai mutunci yafi kudi,
kaunar dake tsakaninsu muke fatan ta ďaure har lokacin da kasa zata rufe idanuwansu...
nan fa suka ďan taba hira kafin daga karshe suka bar Anty Saude da Daddy su kaďai....





Shurun kusan minti uku ne ya ratsa gurin.


"Ikon Allah,
ashe dai zanga wannan ranar, Daddy ya katse shurun da faďin kalaman cike da mamaki.


A kunyace tace
"Aifa Allah ya nuna mana..


"Ai abun ne ya bani mamaki dan dai kamar bake ba,
ko sauya ki akayi,
nasan dai bakinki baya shuru...


Dago kanta tayi ta gimtse farin cikin ta hade da hararshi tace
"Au, wai dama tsokana ta kakeyi..


Dariya Daddy yayi yace
"Kin ďauka yabawa nayi, to ayi Hakuri, na yaba, kinyi kyau abinki *Amaryar Kyari*..


Harara ta watsa mishi zatayi magana Junior ya fito daga ďaki rike da plate ďin da yasha fruit...


Ganin shi yasa Daddy saurin kiran sunanshi,

"Aboki, yau dai gani a gidanku, da fatan za'a daina disga ni,
ajiye plate din yayi ya karaso gurinshi yace
"Aboki yau kazo, kaima anan zaka kwana?

Riko hannunshi Daddy yayi yace "Noo kune zaku koma gidana ku dinga kwana,
kai da Anty Saudatun Kyari...
ya karashe yana kallon cikin idonta..

Wani irin daďi ne ya ziyarci ruhi da jinin jikinta..
binsu tayi da kallo Junior na mishi shirme yana biye mishi,

Lekowa Taheer yayi ya kwala mishi kira dan ganin ya daďe bai dawo ba..


Gud nyt Aboki... ya faďi ya nufi gurin Taheer da gudu...




Hira sosai su Anty Saude sukayi wanda dukkaninsu suka ji dadinshi,
a cikin hirar yake sanar mata ya dawo da Mummy,
ganin bata nuna damuwarta bane yasa shi jin daďi matuka har yayi mata alkawarin tarewarta cikin sati ďaya,

Akwai gida da yake son siya mai sassa uku manya da BQ,
nan yake son su koma dukkansu dan baisan raba iyalinshi samm, da farko ta kawo mishi maganar ya barta ta zauna a gidanta,
ya ki samm dan a ganinshi gazawa ce matuka,
batayi jayayya dashi ba dan tasan zaiyi wuya ya yarda,
sai gurin tara na dare ta kyaleshi ya tafi bayan ya ďan taba wasu dan abin ci sha.....





Direct gidan su Mummy suka wuce,
a shirye ya sameta su Reemah na kewaye da ita kowacce da abun da takeyi mata,
isowarsu ce ta sa suka fito sukayi sallama da matar Rilwanu dashi kanshi sannan suka dunguma zuwa gida kowa na cikin farin ciki marar adadi musamman Mummy da take jinta kamar yau ne ranar farko da ta fara haďuwa da Daddy.....





Karfe goma da wani abu, Hilal da Musaddiq suka koma masaukin su Abbu domin dauko matansu wadanda suke gurin tun da safe kafin tashinsu daga bacci,

Duk iya kokarin da Musaddiq yayi nason ganinta abin yaci tura, dan ko ya kira Maleekah bata dauka ko kuma ta ďauka tace Nadeeyah na bacci,
manufarta dan ta ďan kara wana shi ya sake sanin darajar yar uwarta ko nan gaba kar yayi gangancin rabuwa da ita..



A harabar hotel din suka haďu da Irfan wanda ke makale da waya a kunne,
daga gani yana jin daďin wayar..


Tun daga nesa ya hangosu yace "Ur best friend Hilal is here, cike da doki tace
"let me speak to him pls,

Suna karasowa gurin ya kara mishi waya a kunne yaja hannun Musaddiq suka shiga cikin ďakin yana mishi hira..




Hilal yasha mamaki da yaji muryar Meerah,
cike da al'ajabi ya tambayeta a inda suka haďu,
nan fa ta labarta mishi


"Ai tunda wannan matsalar ta faru yake bibiyarta,
daga karshe bayan kunyi aure har kun haihu ya nuna min zai shiryu indai har zan yarda in aureshi..


"And Alhamdulillah ya Shiryu,
Kai Meerah Turaki you are a darlyn,
i heart u beb Hilal ya karashe cike da farin ciki...



Hirar yaushe gamo sukayi kafin su kashe wayar kowa ya cigaba da abun da ke gabanshi...




"We are sleeping here inlaw, kaga gobe su Abbu zasu tafi nd i miss dem alot, plss kuje gida mu anan zamu kwana..
Maleekah ce ke maganar on a serious note ba tare da ta kalli idonshi ba,


Dariya Mahaifiyarta tayi cikin turancinta da bai fita sosai tace "Rabu da ita, yanzu zasu shirya su biku,
ku jira Abbu ya dawo sai ku tafi, yana can kasa ..


Turo baki Maleekah tayi tace "Babu inda zasu, su da gida sai gobe,

Hilal ya lura da ita ya biye mata suka dinga jan ran Musaddiq wanda shi kacokan hankalinshi na kan Nadeeyah wacce ta dukunkune da hijab ďin mahaifiyar Maleekah..

Shigowar Abbu ne ya kashe musun ta hanyar cewa sai abun da Nadeeyah take so za'ayi mata,

cike da kulawa ya tambayeta zata kwana ko zata tafi,
murya can ciki tace anan zata kwana..

Ihuu Maleekah ta sanya tana ma Musaddiq da Irfan dake goyon bayan shi gwalo,

Duk da yaji ba daďi amma hakan yayi making day dinshi dan sun sashi nishaďi matuka,
sallama sukayi ma su Abbu Musaddiq ya dauki little Nadeeyah yace

"Tunda kin hanani babbar bari in tafi da karamar..


Thank u inlaw,
shiyasa nake sonka,
plss Husna tasa mata pampers before going to bed, i will enjoy my night..


Ajiyeta yayi da sauri yana dariya yace
"Walhy baki isa ba, a kunne ya raďawa little Nadeeyah yace "Trouble ur Mum, don't let her sleep in peace,
Dariya sukayi a tare sannan suka tafa tana ďaga mishi hannu har suka kure.....



A cikin yan kwanakin shakuwa mai karfi ta sake kulluwa tsakanin Daddy da Anty Saude, dama da sabon mai karfi...

Bangaren Mummy kuwa kadaran kadaham saboda ya fahimci canji matuka daga gareta,
shima ya canza saboda a yanzu gidanshi ya zama happy home wanda yake cike da kaunar juna.....





Cike da gajiya ya ajiye hularshi akan kujera haďe da kora ruwa mai sanyin dadi,
saida ta tabbatar ya samu nutsuwa sannan tayi serving dinshi lafiyayyen abincin da ta shirya mishi.
Tsakurar abincin yayi saboda ba karamin gajiya yayi ba...


"A gaskiya gida in ba kai ka gina ba zaiyi wuya ka samu choice ďinka,

Murmushi Anty Saude tayi tana mai ďiban abinci tana kaiwa bakinshi,

"Haka ne dama,
ba lallai tsarin wani yayi maka ba,
ya kamata ka daina wahalar min da kanka,
ka bar aikin nan a gurin ďanka Taheer,
zansa su dubo min bangaren Marafa naga wasu gidaje masu kyau..


Cike da jin dadi yace aiko da sun kyauta min,
Amma fa kar su nemo wanda yafi karfina ya karashe cike da zolaya...

"Kaji shi,
dan ban ce a Abuja zamu zauna ba,
da a can ne zaka nemi daidai da kai..


"Wane ni, ai ni barni a kaduna, baruwana da ďara koda Gonin Gora ne,

Dariya tayi suka cigaba da hira har Taheer da Junior suka dawo akayi hirar tare dasu cikin Nishaďi...





A yanzu Daddy ji yakeyi tamkar ya samu cikon wani gurbi da ya rasa a cikin zuciyarshi,
ko wane bangare daga iyalinshi yana samun nutsuwar kasancewa dasu,
Alhamdulillah Ala kulli halin... shi kaďai yake yawan fadi in yaji daďin na neman yi mishi yawa....





"Buwayi gagara misali Kyari, wallahi da gaske kakeyi bazaka dawo aiki ba,
to wallahi ka sani in baka dawo gobe ba akwai gagarumar matsala, umurni ne daga oga, wato dan kaga ana ce maka kai ďanshi ne shiyasa kake iskancinka san ranka ko?


Dariya Musaddiq yayi haďe da gyarawa Little zaman takalminta yace

"Zubair ban san iskanci, na faďa maka bazan dawo bane?



90% cikin ďari sun nuna hakan Dikuun Daddy..


Yadda Zubair ya faďi sunan yasa Musaddiq kyakyatawa dan yasan zallar tsokana ce,
"In na biye maka su Hilal zasu iya rasa jirginsu, bari in kaisu train station in dawo, zanyi lokacinka..
Bai jira jin amsarshi ba ya kashe wayar yayi waje yana dariya...



Tun kafin ya sakko yayi tozali da Nadeeyah tsaye kusa da Maleekah suna magana kus kus,
ganin ba kowa a parlon ne ya sashi sakkowa a hankali,
Bai ankara ba yaji muryar little tana kwalawa mamanta kira..
Suna ďago kai suka ga sakkowarsu Nadeeyah tayi saurin fita daga parlon baki ďaya..

Cike da takaici ya sakko kasan yana hararar Maleekah wacce tayi mishi kaka gida cikin al'amura,


"Yau dai zaki tafi, sai inga kuma ta inda zaki bullo,


"Don't worry Inlaw,
inada hanyoyi da dama,
kai da matarka sai an kwana biyu..
Tana kaiwa nan tayi waje inda su Anty Reemah suke jiranta tana dariya.....




*****

Washe gari bayan tafiyar su Hilal Daddy ya matsawa Musaddiq komawa aiki saboda kiran da ya samu daga ogansu,
duk yadda yaso a barshi su tafi da Nadeeyah Daddy da Mummy suka ki suka ce sai yaje ya gyara gidan ya zuba komai sababbi..

Haka nan badan ya so ba ya fara shiri cikin kunci da gajiyawa... Allah ya sani ya fara kuluwa, saidai ba yadda zaiyi tunda akan abin da yake so ne...



Saida ya fara zuwa gurin Junior wanda hakan ya zame mishi sabo kullum sai yaje gidan ya ganshi, bayan sun gama hira da Taheer da Anty Saude yayi musu sallama ya ciro tsarabar da ya tahowa da junior ya bashi sannan ya wuce cike da kewar gudan jininshi wanda rashin sabo yasa yaki sakin jiki sosai dashi....

A ranar da ya koma Washe gari tafiyar gaggawa ta kamasu zuwa London shi da colleagues ďinshi, Hakan yasa ya bar komai na gyaran gidan a hannun Faidah.....



***

Gida mai kyau suka samu a Marafa wanda dama Anty Saude tasan da zamanshi,
ita da kanta tasa akayi renovating tun farkon fara neman gidanshi..

Cikin sa'a aka gamashi kan lokaci kuma su Kamal suka kai mishi tallarshi cikin farashi mafi saukin da Anty Saude ta tabbatar bazai musa ba zai biya,
ďaya daga cikin guest house din marigayi ne wanda masu aiki da Kamal ke maintaining dinshi,

Tayi hakan ne dan ta hutar dashi nema sannan tayi saving kudinshi tunda gidan dama babu abinda zatayi dashi,
cikin tumuninta ya faďo....



Yayi farin ciki matuka dan gidan yayi mishi kyau,
saidai saukin da yayi yasa shi tuhumar mai gidan...


Wani aminin Taheer mai suna Okasha wanda dawowarshi daga Canada kenan shi suka gabatar da sunan nashi ne,
wannan shi ya gamsar da Daddy har ya fara shirya gidan......



A hankali ya gama cike ko wani sashe da kaya har saida hakan ya daukeshi tsawon kwana uku..

Tsarin ginin irin na mutanen da ne wadanda gayu da ilimi ya ratsatsu,
ko ina a kasan gidan grass carpet ne mai taushin takawa wanda yake shan kula gurin masu kula da flowers,
kana shigowa gidan zaka taradda sashen mai gidan,
sannan daga baya zakabi ta wata kofa da akayi ta musamman da koren ganyen mai tsananin kyau ita ce zata sada ka da boys quarters,
daga can ciki kuma bangare biyu ne iri ďaya waďanda suka sha gyara irin na zamani..
gidan yayi matukar kyau kuma ya dace da tsarin ahalin gidan...







Satinsu ďaya da tarewa suka soma shirye shiryen tafiya Agadez bisa ga umurnin Sarki,
babu wanda bai hallara ba harda Badariyya da a yanzu Daddy ya sanya mijinta lallai sai ya rabota daga cikin jejin da babu mai zuwa sai aljanu,
badan yaso ba haka ya hakura dan sunfi karfin shi ya nuna zai barta a cikinsu amma fa bazai saketa,
duk sun yarda da hakan da sharadin zai sauya rayuwarshi.....


Gidan da Mummy ta bari nan aka gyara mata take zaune da yaranta da mijinta da sai yayi sati bai zo ba...



Agadez

Sun ga Arziki da karamci a gidan sarki musammamn Hafeez da aka dinga kewaye dashi...

Tsofaffin gari waďanda suka San Yareemah Adamou suka dinga kukan murna suna kiran sunanshi,
dangi makusanta babu inda ba a kai Hafeez da Nadeeyah ba.
ranar farko da biyu sunsha yawo sosai a cikin gari da wajen Agadez.

Sai a kwana na ukun ne suka samu hutu aka fara shirye shiryen gagarumin bikin da ba'a taba yin irinsa ba...



Shareefah gata take nunawa Nadeeyah kamar zata maida ta ciki,
a gurinta take kwana,
abincin cinta ma sai ta zaba mata saboda lafiyar jikinta a matsayinta na amarya, magunguna kuwa na tsari da na ni'imar jiki babu wanda jikin Nadeeyah bai gani ba,

Tun tana shansu babu daďi har yabi jikinta saboda yadda suke matsa mata shan su,
cukwi ne kaďai in an damoshi har yanzu bata iya shanye shi saboda samm bai mata ba.
Gatan da uwa takeyi wa yarta a lokacin aure babu wanda Nadeeyah bata gani ba a agadez,

Kafin zagawowar ranar biki tayi wani fresh ta cicciko daga ramar da damuwa ta sanyata....




Filin dake kofar fadar mai martaba wanda yasha adon sarauta ya cika tatul babu masaka tsinke,
ga busar algaita da kidin sarauta masu matukar daďi dake tashi,


Cikin gaggawa ba tare da

Please Login or Register in order to submit comment