Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake,
nasan tunda naga gudan jininshi dole shima ya kasance a kusa....

Garammm....
gaban mutanen parlon ya faďi,

Sai a lokacin yawancin su suka tuna cewa sunan buzu mai gadi marar asali da galihu
*Adamu*,

Daddy ne yayi saurin cewa "Kwarai Adamu shine mahaifin Hafeezu da Nadeeyah ne,

Allah dai yasa lafiya,
ya karashe cikin zullumi ko Adamun ya taba yi musu wani mummunan abu ne,


"Lafiya kalau sai alheri,
Shareefah ta faďi idonta cike da kwallar farin ciki,

"Ina Yayana Adamou??

Dan Allah ku nuna min shi,
ku nuna min shi ko zan samu salama a cikin zuciyata....

Kallon kallo aka fara yi a cikin parlon,

Papy ne yayi karfin halin cewa Sarki ya zauna sai ayi maganar a nutse,

Kamo hannun Hafeez yayi suka koma inda yake zaune,

share kwallar da ta ziraro mishi yayi yace

"Dan Allah ku kira min Adamou, ashe munada rabon sake ganin juna...


Anya ba kuskure kukayi ba?
Wannan buzu Adamu, mai gadi ne, bashi da wata alaka da sarauta,
inajin kamanni ne kawai,
kunsan babu yadda Allah bai iya yi cikin halittarshi...
Baffa ne ke maganar cikin taka tsan tsan dan kar ya bata ran Sarkin...



Murmushin takaici Shareefah tayi  ta nuna Hafeez da hannu tace

"In dai wannan jinin Mai gadin ne, to tabbas jinina ne,
idan yayana yayi nisa dan Allah ko zan iya samun hotonshi saboda in tabbatar da zancenku in karyata kaina...

Cikin azama Daddy ya tashi zai nufi sama,
kafin ya karasa Hafeez ya dakatar dashi ya ciro wallet a aljihunshi,
kananan hotunan iyayenshi ne suka bayyana,
da sauri ya mika mata...


*Pappa.....*

Ta faďi cikin kuka dan fuskar mahaifinta ta gani a cikin ta dattijo Adamu,
shi kuwa Hafeez fuskar Yareemah Adamou Sarki Tidjani ke gani a idonshi,

Dan Allah ina yake,
Ku faďa mana inda yake??

Sarki ya tambaya cikin ďaga murya...

Da sauri fadawa suka shiga faďin Allah ya huci zuciyarka...

Baya tare damu,
dan uwanku ya rigamu gidan gaskiya,
ya tafi inda duk zamu tafi komi daren dadewa,
shin dama shi ďin dan gata ne kuka barshi cikin gararin rayuwa?
Ya ilahi me muka maida *ZUMUNCINMU A YAU*
ace yanzu sai in baka raye za'ayi Zumunci da kai,
To Adamu yayi tafiyar da ganinshi yake da matukar wuya,
Adamu yayi muku nisa,
saidai 'ya'yanshi....
yadda Daddy yake maganar ya sanya Parlon yin shuru, sai tashin sheshshekar kuka....



Cikin matsanancin kuka Shareefah ta zaune a kan carpet tace

"Yareemah shine Gata,
kalmar Gata in aka zo kanshi an disa aya,
Shine ďan Sarkin Agadez
*Diya Muradun Abdallah Yallo* na farko,
shine Yareeman Agadez....


Kaddararshi a nan take,
kaddarar samun magaji a nan Nigeria take,
hannayen Hafeez ta rike tana kuka sosai tace

"Rubutun Allah baya goguwa, Allah bai nufeshi da zama Sarki ba wanda hakan shine muradin mahaifinmu da duk daukacin mutanen Agadez,
lallai sarauta rigar ubangiji ce,
ya baiwa mijina wanda yake ďan uwa ga mahaifinka,
sannan ya hanamu haihuwa dan dama ya tanade ta ne domin ka..

Wallahi Allah dole ya zama abin tsoro da girmamawa cikin mu bayinsa,
domin ya wuce duk yadda muke tsammani,
ku duba kuga yadda ya maida dan sarki wanda ya kamata ya zama sarki bawa, mai gadi kaskantacce a gidan bayin da ya kamata su zasu bauta mishi,
cikin kankanin lokaci ubangiji ke sauya alkalaminsa,
ku dubi nisan Agadez da Nigeria, haka kudurar ubangiji ta ingizo shi nan da taimakon marasa imani da tsoron Allah,
duk dan saboda me?
saboda yasan akwai wanda ya tanadarwa aron rigar sarautarshi,

Lallai zaren kaddara baki ne,
ganinshi sai wanda ya halicci kaddarar kanta,
haďuwar Taheer da Nadeeyah,,
zuwan mu nan domin su biyun duk zaren ne ke janmu ba tare da mun ganshi ba,

Allahu Ahad,
Allahu Samad,
buwayi gagara misali,
mai dauke da rayukan da babu wanda yasan adadinsu sai shi kaďai...

Naji dadi matuka da Allah bai dauki raina ba sai da naga gudan jinina,
rungume Hafeez tayi ta yafito Nadeeyah ta haďesu tana kuka tace

"Ina sauran 'yayana?

Share hawayen farin ciki Papy yayi yace
"ďaya ce ta rage,
Zainab,
tana can Cyprus tana karatu,
ga wacce take rikonta can ya nuna Anty Reemah da hannu,

Kiranta gabanta tayi itama ta rungumeta tana mata godiya haďe yin hamdala gurin ubangiji....


Na faďa muku,
yanzu kun gasgata zancena? Yareemah Suhail ya faďi cike da kasaita,
maida dubansu inda yake zaune shi da 'ya'yanshi sukayi,
a harzuke Daddy ya mike yace

"Kai ku tashi ku fice min a gida,
mikewa Papy yayi ya dakatar dashi yace
"Yau ranar farin ciki ce,
ka bar shi alkhairin ne zai fitar dashi in shaa Allah.....




Labarin irin gatan da Yareemah Adamou ya samu da kuruciyarshi suka shiga basu har kawo sanadiyyar barinshi gida...
sannan Sarki ya faďa musu yadda suke da Adamoun ya kuma nuna Taheer yace
"Wannan shine dan kanina, shima dan uwan Adamoun ne....

Kallon juna sukayi shi da Nadeeyah yayi murmushi haďe da kashe mata ido,
da sauri ta kauda kanta cike da kunya,
dadin da takeji a yau kamar an mata albishir da gidan aljanna...



Ashe Taheer dan uwan Nadeeyah ne na jini, haba kaunar tayi yawa, Taheer baya taba likewa mace haka,
ashe connection din mai karfi ne, Anty Saude ta faďi tana dariyar farin ciki....


Dariya akayi a parlon duk da zuciyar Daddy ta ďan sosu da jin maganar kauna daga bakin Anty Saude.....


Baffa ne ya fara basu labarin irin wahalar da Adamun yasha da kuma haďuwarsu da Mamma Suwaiba har mutuwarsu...

Cike da jin daďi hira ta barke a tsakaninsu...



Har wannan lokacin su Daddy basu san da zaman junior ba dan basu ganshi ba.....


Su Mummy bayin Allah suna can dai a rabe har lokacin,
sunga karshen asali,
kowacce a cikinsu tana cike da dana sanin rayuwa..


Raliya da Reemah ne kadai ke kai kawo a kitchen suna hada hadar haďa lunch,
sai Husna, Maleekah da Nadeeyah dake tayasu,

Maleekah da Nadeeyah hira sosai sukeyi kamar sun dade da sanin juna,
gasu dukkansu wayayyu babu wacce ke jin kunyar yin magana...


Bayan sun dan taba abinci duk suka nufi waje dan yin Sallah..

su kuma matan suka nufi daki dan yin tasu a can...




Gyara parlon Husna da Nadeeyah sukeyi suna hirar yaushe gamo, labarin abubuwan da suka faru bayan bata nan take bata, ga mamakinta bata ji inda tace "Musaddiq yayi aure ba, sharewa tayi ta kauda tunaninshi a ranta domin yanzu tana son tayi moving forward...
rashin ganinshi a cikinsu ya tabbatar mata yana can yana rayuwarshi cikin jin dadi....




Duk wannan budurin da akeyi Musaddiq na cikin daki ya kure volume suna game shi a dole bayason jin wani abu da ya shafi su Badariyya....

Ganin little Nadeeyah tayi bacci ne ya sashi gyara mata kwanciya ya shiga ya watsa ruwa,
kananan kaya yasa wadanda suka fitar da kyawunshi sosai,
yanzu girma ya sanya Musaddiq ya zama moderate,
wannan kibar duk babu ita,
sai tsawo sosai da dan murjajjen jiki,

kwantacciyar kasumbarshi ya taje ta kwanta lup a fuskarshi, turaruka masu kamshi ya feshe jikinshi dasu sannan ya kashe wutar dakin,
Sallah kawai zanyi in nemi abinci,
abinda ya faďi kenan haďe da murďa kofar dakin ya fito....



Ta sama ya leko yaga ko an ragu a parlon,
ganin bakowa ya sashi fara tafiya cikin kasaita dan isa gurin steps din, 
kamar ance ya sake kallon gefen console,

Tsaye ya hangota ta maida gashinta gefe tana kokarin cire dankunnenta a jikin rigarta,

Hannayenshi biyu ya daura akan karafen da ke kewaye da saman yana kokarin ganin fuskarta ta mudubin...


Haaaa...

ta faďi bayan ta cire dan kunnen, maida gashin baya tayi ta naďe shi ta goge fuskarta da hannunta sannan ta fara kokarin nade gyalen,
jin kamar wani abu yabi ta kunnenta yasata noke wuyan dayan dan kunnen ya sake makalewa, wannan karan ya shiga da karfi,
ajiye gyalen tayi ta fara dambe dashi tana tsaki....


Tunda fuskarta bayyana a gareshi ya shiga rudani,
da sauri ya mutstsika idonshi yaga ko gizon da ta saba yi mishi ne,
ganin dai mutum ce a tsaye ya sashi sake dubawa da kyau ko Maleekah ce,
yadda yaga tayi da baki kamar zatayi kuka yasa shi lumshe ido kirjinshi sai lugude yakeyi...

"Husnaa...
yaji ta faďi da muryar neman taimako,

A hankali kafarshi ta fara janshi,
shidai yaki gasgata idanuwanshi wadanda suka tara ruwa a lokacin..


Saura kaďan ya isa gareta yaji wani kamshi mai dadi acn gurin na bugo mishi,
zuciyarshi ce ta ingiza hannunshi ya dagoshi da niyyar taimaka mata...


Mamma...
we am back..


Juyowa tayi da sauri ďan kunnen ya fita a kunnenta gaba ďaya,

kyammm..
idanuwansu suka makale cikin na juna,
nan fa zuciyoyin da suka daďe suna kewar juna suka fara zubar da hawaye a junansu, 
daga Nadeeyah har Musaddiq babu wanda jikinshi baya rawa, babu kamar Musaddiq da a lokacin yake jinshi kamar mutum mutumi,

Cikin karfin hali da dauriya Nadeeyah ke kokarin raba idonta da nashi amma sam zuciyar da ta daďe tana ďoki da marararin ganin mahaďinta taki bata haďin kai.....




A tare Hilal da Musaddiq suka shigo parlon suna ďan taba hira,
hirarsu makalewa tayi da sukayi arba da abinda ya sosa ran Taheer..


Hannun da Musaddiq ya ďaga yasa a gefen rigarta ya cire mata dan kunnen har lokacin bai dauke idonshi cikin nata ba...



Badariyyah data fito daga kitchen ta tsaya kallonsu zuciyarta sai rawa takeyi hawaye ya shiga yi mata ambaliya..
a yanzu tasan mai gadi ma rayuwarshi tayi mata nisa bare Musaddiq..



Mamma..

Junior ya faďi yana girgiza mata riga,
a firgice ta kalleshi cikin sanyin murya tace

"Ummm,
ina kaje?,

"Munje yawo ni da namesake,
yace shima sunan mu ďaya haka ne Mamma?

Gyaďa mishi kai tayi ta karbi ledar hannunshi ta ajiye ta wuce kitchen da ďan gudu gudu tana maida numfashi.....



Bayanta Junior ya fara kokarin bi Musaddiq ya rikoshi da sauri,
dafashi yayi ya tsuguna kirjinshi na dukan uku uku yace

"My Twinny,

Zaro ido Junior yayi yace

"Yayyy
*MMK*  right?

Yess...
Musaddiq ya faďi jikinshi samm babu kuzari..

Kallon inda Taheer yake tsaye yayi ya taho da sauri yace
"Daddy, zo kaga strangern da na gani a Hallmark,
i told u he is just like me,
har gaban Musaddiq ya janyo Taheer yace
"Kaga idonshi irin nawa,
i will not lv here sai nayi grabbing face dinshi,
sketch din da nayi baiyi kyau ba....




*Daddy.....*

Musaddiq ya dinga maimatawa a cikin ranshi,
dakyar ya iya dago kanshi suka haďa ido da Taheer,
nan take halittar nan marar dadin faďi a baki ta shiga motsi a zukatansu...



Ganin haka Hilal ya karaso gurinsu da sauri yana murmushi,

"Hey Kyari,
ka ganeshi, Uncle din su Nadeeyah,
ashe all this while Nadeeyah is with him..
sun kula da ita sosai da gudan jininka,

Janyo Junior yayi kusa da Musaddiq ya haďe hannayensu guri ďaya yace
"He is ur blood Kyari,
ur flesh and blood..


"Tell him ur name,
Hilal ya sake cewa ma Junior cike da doki,

*MUKTHAR HILAL MUSADDIQ KYARI* a.k.a *MHK TAHEER* ya karashe haďe da damke hannun Taheer....



Runtse ido Musaddiq yayi yanajin dukkan nauo'in biyu a cikin zuciyarshi,
farin ciki da akasin haka,
a hankali ya buďe idonshi ya sake tsugunawa a gaban Junior, janyoshi yayi ya rungumeshi tsamm a jikinshi..

Wasu zafafan hawaye ne suka shige tsere tsakanin idanuwanshi zuwa kuncinshi,
da sauri junior ya raba jikinshi da nashi saboda jin ruwan hawaye da yayi a kafaďunshi,

"Hey twinny, ya faďi a dan tsorace yana ja da baya zai koma gurin Taheer,
rike hannunshi Musaddiq yayi yana girgiza kanshi wasu hawayen na fitowa kamar ana ingizo su,


"Daddy...
Junior ya fara faďi yana kokawar kwace hannunshi cikin na Musaddiq,
a tsorace yake matuka dan bai taba ganin zubar hawayen babba ba,


Cikin sanyin jiki Hilal ya tsuguna a gaban junior,
dayan hannunshi ya kamo yace "My dear he is ur Dad too,
ur biological father,
go to him,
he is *MUSADDIQ KYARI*
His name is connected with urs...


Juyawa Taheer yayi wani makoko ya tokare kahon zuciyarshi,
hawayen da yaketa matsesu suka zubo daga idonshi..



"Noo...
Junior ya faďi haďe da fisge hannunshi daga dukkansu,
da gudu ya koma gurin Taheer ya rungume kafafuwanshi ta baya,

"Dis is my Dad,
his name is also connected with mine,
"Daddy plss tell them u are my biological father ya karashe bayan ya dawo gaban Taheer ya tsaya..


Daga kai Taheer yayi sama ya share hawayen da ya sake taruwa yana neman zubo mishi, dan kar Junior ya gani,
ďagoshi yayi ya daurashi a kirjinshi yace
"He is ur father Sweetheart,
i'm ur father and ur name sake is ur father too,
we are all ur Dad..



"Only one is my biological,
who among the three?
ya tambaya idonshi kyamm akan Taheer,


Runtse ido Taheer yayi maganar da yake kokarin yi ya kakare mishi a makoshi...



Share hawaye Anty Saude tayi ta karaso ciki da sauri ta karbi Junior,
"Ina ka shiga My dear,
ko abinci baka ci ba, and all ur so called fathers basu damu da su baka ba,
duk kace bakayi dasu muje kaci abinci..

Kwantar dashi tayi akan kafadarta ta wuce cikin kitchen dashi,
tayi hakan ne dan ya samu nutsuwar sanin ainihin mahaifinshi,
duk nauyin Junior a wannan lokacin Anty Saude ji tayi yayi mata shafal,
zaunar dashi tayi akan kujera ta kwalawa Nadeeyah da ta hangota acan baya kira....




A gaggauce Mummy tabi bayan Anty Saude itama idonta cike da kwalla,
samm bata damu da ganin su Daddy tsaye curko curko bayan gama kallon abinda ya faru ba..



Tana shiga ta kankameshi tana kuka mai sauti haďe da sumbatar ko ina na jikinshi...


Cike da kyankyami kamar zaiyi kuka yace

"Momma,
plss lts lv dis house...


Mummy bata damu da kyankyaminta da yaji ba ta sabashi a jikinta ta durkushe gaban Nadeeyah tana kuka tana rokon gafararta,
cikin kuka Nadeeyah ta tsuguna tace
"Dan Allah Mummy ki bari,
we are all humans, we are bound to mk mistakes, walhy ban rikeki a raina ba..



"Kuskurena yakai girman da za'ayi min koma meye,
sakarcina ya hanani hango alkhairan dake tare dake Nadeeyah,
yanzu wannan jikan nawa da kuskurena ya sanya fitarshi bazan taba yafewa kaina ba,
dan Allah kuyi hakuri ta karashe cikin matsanancin kuka....


Su Anty Reemah da suka shigo gurin duk idonsu ya ciko da hawayen tausayi,

Raudha da Radiya ma cike da Kuka suka tsuguna a gabansu suka shiga ba Nadeeyah hakuri...



Hamdala Raliya tayi a cikin ranta sannan ta sake godewa Allah da yasa dukka yan uwanta da mahaifiyarta suka gane kuskurensu...




To kukan ya isa a miko min jikana in bashi abinci,
dariya Mummy tayi ta Saki Junior da yake a matse dama,
da sauri ya koma gurin Anty Saude ya ďane jikinta haďe da kwanciya ya runtse idonshi....



Sai a hankali zai saba,
kunsan yanzu ne ganinku dashi na farko,
sai kunyi hakuri da koma meye...
yadda Anty Saude ke maganar cikin fitar da tsammanin zamanta tare dashi ya sanya Nadeeyah barin kitchen din da sauri,
ta riga ta gama yanke hukuncin zama da Taheer,
babu wani dalili na tausayi ko wani abu da zai canza mata ra'ayinta,
Halaccin da zatayi wa bayin Allahn nan kenan, ta kare rayuwarta tare dasu.....





Gyaran murya Sarki Tidjani yayi yace
"Hukumullahu laa Ajabun, hukuncin Allah ba'a mamaki akanshi,
abin da ya kawo mu daban sai gashi Allah cikin ikonsa mun haďu da abinda muka shekara da shekaru muna nema.....



Kamar dai yadda na faďa maka Alh Mukhtar,
Taheer ďana ne,
kanina ne ya haifeshi, mahaifinshi Allah yayi masa rasuwa shekarun baya da suka wuce,
to yana zaune tare da mahaifiyarshi acan Canada,
wannan zuwan da mukayi, alkhairi ne ya kawo mu,
a yanzu da na fahimci wacece Nadeeyah sai nakejin kamar yau dinnan a kaddamar da komai a hutar da kowa,
domin ita din 'ya ce ga kowanne a cikin mu,
duk da na fi kowa karfi akanta a al'adarmu da kuma musuluncinmu,
yanzu a gurina nine mutum marar karfi akanta dukkanku nan kun fini karfi,
ku kuka san komai nata tun tasowarta,
Saboda haka Alhaji Mukhtar nazo gareka ina nemawa ďana *Taheer auren ďiyarka Nadeeyah.... *
yana disa aya fadawa suka yi mishi kirari haďe da miko mishi ruwa yasha domin yin magana mai tsayi...




Ya ilahi... haskowa masu karatu halin da daukacin yan uwa da masoyan Musaddiq halin da suke ciki..


A kiďime Musaddiq ya mike da zaman da Papy ya tursasa masa yinsa,
domin yaso bin bayan su Anty Saude da kuma Nadeeyar da ya tabbatar tana kitchen din...


Cikin kaurarrar murya yace

"whatt a jo----
da sauri Hilal ya toshe mishi baki haďe da kokarin maidashi ya zauna,
iya karfinshi yasa ya hankaďa Hilal ya tafi tagaga zai faďi..


Daddy da a ganinshi yafi Musaddiq din shiga tashin hankali yayi saurin mikewa ya rike Musaddiq dake shirin sake magana,


"Da aka fara magana kaji an kira sunanka?
Ko irin tarbiyyar da ka samu kenan?,
a gaban bakin mu wanda yake kamar Mahaifi ga Nadeeyah kake kokarin nuna musu irin rashin mutuncin da ka koya cikin kankanin lokaci ko?,
to bismillah,
in ka gama dasu sai ka dawo kaina.....


'Dago idonshi da ya zama kamar gauta yayi ya kalli gefen da Taheer yake,
da sauri ya kauda kanshi haďe da fara takawa baya a hankali,
cikin rashin sani yayi muguwar buguwa da bangon bayanshi..

Da gudu Hilal ya doso inda yake, kafin Hilal ya karaso ya juya ya haye sama da gudun da taku uku kaďai yayi ya isa ďakin da yake...



Dafe kai Papy yayi cike da tausayi ya kalli Daddy da ya koma ya zauna yana magana cikin karfin hali..


"Mashaa Allah ranka ya daďe,
na baku Nadeeyah,
Allah ya sanya albarka a cikin auren,
karku damu da sakarcin Musaddiq,
yarinta ke damunshi..




Cike da jindadi Sarki yace
"To madallah,
sai a yanke mana sadaki domin muna da nisa,
munfi son ayi komai cikin lokaci...




Wannan karan duk wani kuzari na Daddy ya kare da kyar ya iya cewa

"Da kai da kaya duk mallakan wuya ne,
ranka ya daďe duk hukuncin da ka zartar daidai ne...



Kuka sosai Anty Raliya ta fashe dashi na tausayin dan uwanta da kuma halin da taga mahaifinta,
daki ta wuce da gudu Husna ta rufa mata baya itama kukan takeyi...





Innalillahi wa inna ilaihir rajiun... shi kaďai take maimaitawa tana faďin duk laifi na ne,
a tunanina in Nadeeyah ta dawo zata komawa Little,
ashe wata kaddarar Allah ya shirya mana daban,


Cikin kuka take bawa Husnah labarin komai da tayi wanda yake neman jefa dan uwanta cikin barazanar rayuwa....




Wani irin wawan mari Anty Reemah da ta biyo bayansu taji komai ta wanka mata..

cikin masifa ta fara zaginta tana kiranta da marar imani,
tasan inda Nadeeyah take tabar kowa cikin zullumi musamman Mahaifiyarta dake fuskantar rayuwar ukuba saboda hakan,
ta inda take shiga bata nan take fita ba..



Durkusawa Anty Raliya tayi cikin kuka ta bata hakuri da kuma amsar laifinta,
ita tayi shi ne in a good faith dan Nadeeyah ta samu ingantacciyar rayuwa,
ashee inganta rayuwarta zaiyi sanadiyyar shigar rayuwar Musaddiq cikin wani rudanin..... ta karashe cikin matsanancin kuka.....





Zama sukayi su ukun suna cikin jimami suna zubarwa da dan uwansu hawaye...






Minti goma kaďai su Sarki suka kara sukayi shirin tafiya,


Kallon Hafeez Shareefah tayi tace anjima suzo shi da iyalanshi su sameta..
cikin ladabi ya amsa mata da "To,

Adress ta karba gurin Taheer ta bashi cike da farin ciki.....




Katse wayar dake shigowa cikin wayar Baffa yayi karo na biyar ya tashi ya tafi yin rakiyar su Sarki shima jikinshi ba kwari,
kawai dai basu da bakin bijire musu ne dan suna da dukkan iko akan Nadeeyah,
ga kuma taimaka mata da sukayi, ya zama dole suma su rama musu halaccin da sukayi mata...





Kallonshi tayi cike da tausayi bayan ya gama nacin Junior yazo gurinshi yaki,

A hankali tace "Bari mu tafi *KYARI*
in shaa Allah gobe da safe zan kawo maka shi,
baka bani phn numbernka ba,
kai dai har yanzu kana nan da miskilancinka akan mace,
to ni na tambaya a bani,


Dariya yayi wacce da gani yake ce, ya fara faďa mata number,

Shafa kan junior yayi yace "Takwarana sai gobe ko,
ka zo da kaya da yawa dan rikeka zanyi....



Saida suka ga fitar motocin sannan suka koma ciki dukkansu babu mai karfin yiwa dan uwanshi magana...






*DADDY*

sunan da ya bayyana a jikin wayar haďe da special ringing tone,

Dauka Husnah tayi ta nufi kitchen da wayar,
can baya ta hangota zaune tana wasa da yatsun kafarta,
dafata tayi haďe da zama a gefenta,


Idonta da sukayi luhu luhu ta dago ta kalli Husnah haďe da kakaro dariya, zatayi magana kenan wayar ta sake kara,

Ajiye mata wayar Husnah tayi akan cinyarta ta kauda kanta can gefe,
ganin sunan ya tabbatar mata da junior ne da aikin nan dan tare suka siyo sim din Nigeria dashi,,


Saida ta kusa katsewa ta dauka,,

"Mamma..
ya faďi kamar karamin yaro..

"Uhmmm Uncle,,
tafiya babu sallama ko?

Kwantar da kanshi yayi a jikin kujerar yace
"Na daga miki kafa ne,
nasan yau baki da lokacin mu ni da junior,
kinga yan uwa bayan dogon lokaci,
just call to tell yhu
"I love yhu alot..

Runtse idonta tayi tace
"Uhum,

"Uhummm, say it plss,
ya faďi cikin kaguwa,

"Same to yhu..


Dariya yayi yace
"Muna nan zuwa anjima bayan isha'i, take care plss...


"Ohk uncle, in shaa Allah bye.. tana kaiwa nan ta katse wayar...




"Husnah kun dawo kaduna ne ko kunzo hutu ne?


Hannayen Nadeeyah Husnah ta kama ta fashe mata da kuka,

"Dan Allah Nadeeyah karki auri Uncle,
dan Allah karkiyi sanadiyyar mutuwar Yaya Musaddiq,
Sake dawo mata da ainihin labarin halin da ya shiga bayan tafiyarta tayi,
sannan ta kara mata da irin halin rashin walwalar da ya ke ciki har yau dinnan da ya ganta..


Da sauri Nadeeyah ta share hawayenta tace

"Walwala?
wacce yakeyi da FAIDA matarshi fa?

"Faida?
Husna ta faďi cike da mamaki,

Faidar da keda 'ya'ya uku?
Faida ai tayi aure bayan rabuwarku da sati biyu,
ta auri abokin yaya Musaddiq Zubair..



Cikin sanyin jiki Nadeeyah tace "Na gansu tare a gidanshi suna tsaye cikin annashuwa da jin dadi..


"Kwarai kuwa zaki gansu,
basu da nisa,
kinsan bayan rabuwarku Daddy ya saki Mummy,
sai ya koma lagos da zama,
duk wanda yaje gidan ita ke kawo mishi abinci,
may be kin samesu ranar da baki a gidan ne.. 



Shuru Nadeeyah zuciyarta ta raunana matuka,
tausayin dan uwanta Musaddiq ya ratsa dukkan sassa na jinin jikinta,
saidai is too late... wata zuciyar ta faďi mata yayin da ta tuno da irin halaccin Taheer a gareta,


Shanye kwallar da ta taso mata tayi tace

"Husnah, Allah ya kaddara zamana da yaya Musaddiq na ďan lokaci ne,
rabon da ya haďa mu gashi nan ya fito duniya,
kinsan an ce Matar mutum kabarinsa,
a yanzu bana tunanin zan iya zama da kowani namiji in ba Uncle ba,
dan All---
da sauri Husnah ta bar gurin tana fitar da kuka mai sauti...


Rufe fuska Nadeeyah tayi itama ta fashe da kukan da ya daďe da tokare makoshinta.....







Tun Hilal na bugun kofar dakin Musaddiq har ya hakura da bugun ya koma ban baki..


"Look Kyari,
don't harm urself,
ka bude min kofar nan, everything will be alright,
trust me....




Kamar da dutse yake magana, dan Musaddiq bai ma san abinda yake fada ba,
tsaye yake gaban madubi hannayenshi dukka biyu ya daurasu kan table din yana fitar da numfarfashi kamar zakin da ya hangi nama,


Kalmar
"Daddy da yaji daga bakin gudan jininshi, da kuma kalamanshi,
har kawo furucin sarki, sai amsa kuwwa sukeyi a kunnenshi,

runtse idanunwanshi yayi saboda wani irin yanayi da yake ji a cikin jikinshi,
kaunar Nadeeyah dake adane a majiya mai tsafta ta taso mishi gadan gadan kamar guguwa mai karfin gaske,
da sauri ya buďe idanuwanshi wanda hakan yasa ya daki glass din mudubin dake dakin saboda yadda yaga idon kamar jini dan tsabar jaaa....  



A firgice Little Nadeeyah ta farka da tsananin ihu tana waigen ta inda karan ya daki kunnenta,
hango Musaddiq tayi yana sake bin glass din yana farfasa su da hannunshi da jini ke zuba..
a tsorace ta nufi kofar fita tana ihu tana kiran sunan Mahaifinta..


Muryar Hilal taji yana magana cikin ihu yana umurtata da buďe kofar,
dakyar ta iya dabarar da ta murďa lock ta buďe da sauri ta faďa jikinshi tana ihun kuka,,,


Mika ma Maleekah da karar glass ya tarkato su zuwa sama yayi ya nufi Musaddiq da gudun gaske,


Hilal na ta'bashi yayi wurgi dashi ya cigaba yin wurgi da kayan gaban madubin yana faďin
"i'm useless,
Daddy is right i'm a fool nd a looser,
bani da amfani a gurin kowa,
gara in mutu

Please Login or Register in order to submit comment