Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta karbi jakar hannunshi ta turo baki,

"yanzu zaka tafi?
haba my PP,
shikenan da bamu dawo ba bazaka jiramu ba,


Bakin yaja yace "oya kara turoshi shi gaba,
dariya tayi sosai tace
"Allah da gaske da ka tafi baka jirani ba ko waya ka kirani bazan dauka ba,


Gurin motar suka karasa yace "dama nayi niyyar baki wata kyauta,
na fasa..
leda ya mikawa Nadeeyah dake tsaye tana murmushi,
"amshi wannan ke,
Husnah ta lashe,

Tura daya ledar cikin motar yayi yana dariya,

bude motar tayi da sauri tana fadin
"sorry my pp,
dauko ledar tayi cike da kosawa ta fito da abun dake ciki,


waya ce sabuwa dal mai tsadar gaske,

wani irin ihu ta saki tana fadin "thank u yaya Hilal,
u are the best,


Da kafada Musaddiq ya zunguri Nadeeyah dake tsaye kamar statue, murna ta hanata magana,

kallonshi tayi zatayi magana, yace "ke bazakiyi godiyar bane,
oya say it out kema,
*Yaya Hilal u are the best*,
yadda yayi da murya kamar mace yasata sakin dariya sosai harda rike ciki,
shima dariyar yakeyi,


Duk wannan abun da sukeyi a kan idon Badar da ta shige ciki tun shigowarsu gidan,
dakyar ta iya danne tukukin da ya yaso mata, ta saki labulen windon da karfi,


Shi kuwa Hilal tsintar kanshi yayi cikin nishadin ganin dariyarta mai kayatar dashi,

wani masifar sonta ke ratsashi kamar dama a cikin jininshi akayi halittar son,

ya shagala sosai cikin farin ciki shiyasa baiji muryarta tana mishi godiya ba,

tabo shi Husnah tayi tace
"Ana maka magana,

kallonta yayi ya saki dan murmushin da ba kowa ke ganinshi ba yace

"never mind, ki godewa Allah, nd ki kula da karatunki,

murmushi tayi tace "inshaa Allah, Allah ya kiyaye hanya ka gaida min da kowa da kowa,

gyada kai yayi suka shiga mota yaja suka wuce,
saida suka fita a gate din sannan ya iya maida hankali kan tukin da yakeyi,

gaba daya jikinshi yayi sanyi,

gani yakeyi kamar wannan rabuwar da zaiyi da Nadeeyah itace rabuwarsu ta karshe,

"ko dai mutuwa zanyi,
saurin taka burki yayi saboda yadda tunanin yazo mishi,


kashe motar yayi yace "malam Ali dawo ka tuka,
ya bude baya ya shiga malam Ali yaja suka wuce,


Har suka isa Abuja ya rasa asalin abin da ke taba zuciyarshi akan Nadeeyah,


Addu'a kawai yayi na Allah kar ya kawo sanadin da wani zai zo ya kwace mishi ita,

badan yanada abubuwan yi ba da ya dawo nigeria har ta gama secondary school ya sama mata university a cyprus,

cikin damuwar da ya rasa dalilinta yace
" in shaa Allah tana gama school nan da 5month zai dawo da ita cyprus,
gara tana gabanshi,
hakan kadai zai hutar da zuciyarshi,
zai cigaba da tunasar da ita muhimmacin karatu har ta gama secondary...


Text ya tura cikin layin da ya sai mata..



*Kyawun alkawari cikawa, Dan Allah ki kula, ki maida hankali kan karatun waec, nd ur line ya zama personal, kar ki bawa ko wani namiji ko macce numberki sai wanda ya zamto shakikinki, take care*....





Husnah na miko mata wayar bayan ta gama setting dinta,
text din ya shigo da sunan

*Arc Kangiwa*

karanta text din tayi hade da murmushi,
saboda sabo da rike wayar Husnah yasa ta iya wasu abubuwan,
reply tayi mishi



*In shaa Allah will keep my words,
Allah ya saka da alkhairi thanks for caring*



Yana gama karanta reply dinta ya ajiye wayar,

inama zai iya ce mata
*I love you*


Yana matukar son ganin reply din da zai hana mishi sukuni ya sanya shi yawo cikin sararin samaniya kamar yadda jirginsu zai lula,


saidai kashh..
bazai iya ba,
domin tanadin da yayi wa soyayyarsu ba na yanzu bane,

sai ta mallaki dukkan hankalin kanta,
sai ta koyi duk wasu nau'ika na soyayya,

yana son yin soyayyar da a tarihi ba'a taba samun kamarta ba,

cije lebe yayi domin hango yadda zai maida ita sarauniyar shi,
kuma sarauniyar matan duniya....



*(A bari ya huce)*.....
🤪😜😝




*MAFARI* ......
*(kauna)*



*Shin so samu ne*

Nidai rubutuwa nakeyi,
mijin Nadeeyah na cikin ukun nan,
Allah ya riga ya zaba...
muje zuwa a Mafari....



*Team Hilal*
*Team Diku nah*
*Team Taheer*






Mrs Tijjani Shattima......
[01/04 3:08 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣9⃣
By *Aysha Ya'u kurah*






*MOROCCO*


Kuka sosai Shareefa keyi tana kwala kiran Doctor,
Doctor....


kokarin cire oxygen din Ummu Ayyu takeyi hawaye na tsiyaya ta gefen idonta,
hannunta Sarki Tidjani ya rike yayi saurin maida mata oxygen din,
girgiza kai ta shiga yi hawaye na tsare da dan uwanshi,

Allah kadai azabar da mai rai yakesha yayi da yazo gangara,
dago idanuwanta da suke lumshewa tayi tana musu alama da akwai abin da takeson fada musu,

zuwan doctor ne ya sa suka matsa gurin suna kuka dukkansu babu mai ba wani hakuri,
ganin Doctorn na girgiza yana cire oxygen din ya sanya Shareefah matsowa a gigice tana tambayarshi,
bai ce mata komai ba ya zagaya ya cire drip din da ke taimaka mata ta samu karfi a jikinta,
bin bayanshi Shareefah zatayi taji hannun Ummu Ayyu ya riketa,
damke hannun tayi cikin kuka tace
"Kiyi hakuri ummu na,
nasan zai canza miki magani ne,
bari in tambayeshi,
tari ummu ta fara yi da karfi tana fadin
"a'a, ki tsaya a nan in cika a gabanki,
shima likitan yasan rayuwata yanzu bata da wani sauran amfani,
amfaninta a gareni da Allah bai dauki raina ba ya barni in sanar miki da sirrin da ya dade a rufe,

gyara zama Shareefah tayi tana sauraron mahaifiyarta,

Shareefah.....

ta fadi a wahalce saboda fitar maganar ma wahala ce a gareta,

"na aikata abubuwan da ban taba tunani akansu ba,
na aikata abubuwan da rana irin ta yau bata taba zuwa min a kwalkwata ba,

*YAREEMA*....

*YAREEMA A....DA....*

nan ta shiga tari sosai har tana jirkitowa daga kan gadon,

kuka mai karfi Shareefah ta fashe dashi tana kallon Doctor dake tsaye yana monitoring heart beat din Ummu,
doctor help me,
kayi wani abu dan Allah,
girgiza kai yayi yace
"babu abinda zaiyi amfani a wannan ranar Shareefah,
not even power,
just listen to her before its late,
"may be what she is going to tell u will be a relief to her,

hannun Tidjani ummu ta kamo tace
" *HAJJA*,

*RUGAR HALDON SASSOUNBOROUN*

ku nemi Hajja yar Riga,
zata fada muku komai game da

*YAREEMA... AD...*

kasa karasawa tayi saboda yadda tayi wani tarin da ya hado da gudan jini,
nan ta shiga fisge fisge suna danneta suna kuka sosai,
murya can kasa take cewa

*da na sani, da na sani, na cuci ka....ina*

kalmar da dunga fada kenan har ta cika da ihun da ya ratsa ko ina a cikin katafaren asibitin.....


*(Shin masu zalunci basa tuna wannan ranar, ranar da babu wani wanda zai iya taimakonsu, ranar da babu wani sauki sai saukin Allah da na abun alkhairin da ka shuka, shin in ka shuka tsiya baka tunanin wannan tsiyar ta zame maka kaya mai nauyi ranar da rayuwarka zata zamo ba taka ba, shin menene kazantar duniya da zata sanyamu mu dinga kauce hanya har mu dauki nauyin hakkin wasu muyi dakonshi, rayuwa kalilan ce, wallahi tsakanin mutuwa da rayuwa kamar kiftawar ido ne, yanzun nan komai na iya canzawa, dan Allah yan uwa ko me zamuyi mu tuno da wannan ranar, ranar da take tafe ga dukkan wanda yake numfashi a doron kasa, ba'a dauketa ga kowa ba dukkanmu zamu tafi, Allah kasa mu cika da kyau da imani)*........






********

Orange rigar da ta saba bacci da ita ta dauko ta saka ta sanya bakar hula,

minti minti ta duba wayar da ta barta a gida ta dawo ta tarar babu missed call da text ko daya daga gurinshi,

abin da bai taba faruwa ba tun da ya bata wayar,
dauko wayar tayi ta hau kan katifar da aka siyo dominta ta fara dannata,
tunanin tura mishi text takeyi taji ko lafiya,
lallai sabo turken wawa,
tayi matukar sabawa da ganin sunan *Arc kangiwa*
a cikin inbox dinta,
har ta rubuta text din, ta kasa turawa tanata juye juye da wayar a hannunta,


karar wayar yasata bude ido da sauri dan ta dauka shi ne,
ajiye wayar tayi kirjinta na duka saboda dadin da taji na daukar shi ya kirata,
saida wayar ta kusa tsinkewa lokacin ta saisaita kanta tayi saurin ďauka

"Kin kwanta ne?

"Ummm ta fadi kamar da gaske baccin takeyi,

"shikenan ya fadi kamar abin tausayi,
dariya tayi tace
"idona biyu kana san wani abu ne?

"Nidai na gaji..
zan bar gidannan,
shikenan ku dan kunci abinci baku damu da nawa cikin ba,
ki kwanta kawai ya karashe hade da kashe wayar,
yaye abun rufarta tayi ta kalli Husna dake dariya da waya a hannu tace
"muje kitchen pls,
bata kalleta ba tace "muyi me?
irin kallon da Badariyya ke mata yasa ta kasa bawa Husna amsa dan kar ta ambaci sunan Musaddiq ta fada mata bakar da zata hanata bacci,

ficewa tayi a dakin ta wuce kitchen,
tuwo ta gani guda biyu a cooler Daddy,
har ta fara zuba mishi ta tuno baya san tuwo,
gas ta kunna ta dafa mishi indomie da fish source din dake fridge,
tana gawa ta soya mishi kwai ta kai mishi kan dining,
dakinshi ta wuce ta fada mishi abinci na kan dining,
da sauri ya tsayar da ita ya dauko coke mai sanyi a fridge dinshi,


Zama yace tayi ta tayashi hira,
bata mishi musu ba ta zauna,


kallonshi takeyi yana cin abin kamar wanda yunwa ta gama cinyeshi,
dago ido yayi suka hada ido tayi dariya hade da sunkuyar da kanta kasa,

shima dariyar yayi yace
"kallona kikeyi ki gama kwashe rahoton yadda nake cin abinci ko, zaki sani,

dariya sosai tayi tace "wa zan fadawa in na kwashe,
saidai in barshi a cikina duk ranar da na hadu da matar da zaka aura, labarin cikinka zan fara bata, dan in bata kula dashi ba akwai matsala,

dariyar shima yayi yace
"ai basai kin fada mata ba,
day 1 zan fada mata,
tayi wasa da komai banda cikina, har saima na jira wani ya fada mata,

dariya ta sakeyi, kafin tayi magana taji ya dauki waya shima yana dariyar,


"Main man, how far,
hope ka kwashe, nasanka da kwashewa,

tsaki Hilal yayi yace
"Duniya ba gaskiya Musaddiq,

kasan na baka labarin Irfan da yake san cutar mahaifinshi,
to yau throughout muna tare,
saboda naki amincewa da bukatarshi,
kuma na rubuta letter zuwa company akan wannan business din fake ne, yau saida guy dinnan ya kusa kasheni,

Allah ya taimakeni da Meerah muka tafi,
ita ta kira police suka tafi dashi, but alhamdullilah..
anyi bailing shi dan kar Babanshi ya sani amma i promise not to work der again,
bana son abun da zai kara hadani da Irfan,
nd sai na nemi mahaifinshi na fada mishi irin cutar da suke mishi a companynshi,


Ajiye cokali Musaddiq yayi yace
"gaskiya gara kabar aiki a gurin,
kar yazo da tsautsayi wata rana,

dan ma kai ya samu,
da su mune ai sai dai mu kusa kashe shi,

"gerraut Hilal ya fadi yana dariyar da tunda ya dawo baiyi ta ba,
dariya Musaddiq yayi yace
"ka fa raina ni,
irin girman uban nan ma baka bani,
bakomai yaran zamani,
sai da safe,

sosai Hilal yayi dariya harda kyakyatawa ya kashe wayar dan kar Musaddiq yasa cikinshi ya murda,
shiyasa in ya shiga damuwa mutum na farko da yake fara kira Musaddiq ne,
dan yakan mantar dashi damuwa,
haka shima Musaddiq Hilal yana solving ko wani irin problem dinshi,
saidai in bai fada mishi ba,
yana gama cin abinci ya kalli Nadeeyah dake kokarin tashi yace
"ina zuwa?


"Bacci nakeji ta fadi kamar zatayi kuka,
"ni kadai zaki bari a parlor, ya fadi yana kwaikwayonta,

Murmushi tayi tace "dan Allah kaje ka kwanta kaima,

"To miss problem solving,
thank u,

dariya kawai tayi ta wuce daki,


Daddy dake tsaye yana kallonsu daga sama ya wuce daki zuciyarshi cike fal da farin ciki da tunanin Allah yasanya abinda zuciyarshi ta kitsa mishi ya tabbata,

hango futurn danshi yayi a tattare da Nadeeyah,
ita kadai ce macen da ta dace da yanayin rayuwar dan da ya tashi cikin taron mata cike da rauni kuma a sangarce,

badan Hilal dake sanyashi a hanya ba, yasan da Musaddiq ko sanin menene kalmar Namiji bazaiyi ba,

Addu'a sosai Daddy yayi na Allah ya tabbatar da tunaninshi kuma ya sanya ta zamo alkhairi a gurin danshi.....






Kasar Nigeria,
kasar who u knw ba what u knw ba,

washe gari tun safe Daddy ya kira abokinshi GMD din NNPC towers dake Abuja,
bayan sun gaisa suka dan taba hira,

kafin Daddy ya gabatar da bukatarshi Dr Barau ya rigashi da cewa
"Musaddiq har yanzu bai gama servn ba?

"saura watanni in shaa Allah Daddy ya bashi amsa yana dariya,

"okk to ba matsala gobe akwai yara 6 da za'ayi ma interview a

*EXXONMOBIL*

ka turomin shi sai su hadu su 7,
in ya karbi nysc cert dinshi sai a hada a cikin takardunshi,

cike da farin ciki Daddy yace "ina ne Exxonmobil kuma?


Dariya sosai Dr Barau yayi yace "Nigerian EXXONMOBIL, Oil nd gas company ne,
American multinational oil nd gas cooperation,

yanzu ake daukar yara,
so gara yaran mu su samu tun yanzu, kaga nan gaba sun dade a ciki, lokacin da karfin mu zai tafi sukuma lokacin zasu mike,


Fadin irin farin cikin da Daddy ke ciki ba kadan bane,
dama kiran da yayi mishi kenan,
matakin farko da zai fara sanya Musaddiq zama cikakken mutum shine aiki,
in yaga ya fara samun kudinshi na kanshi zai nutsu sosai ya nemo girma ya daura ma kanshi,

godiya sosai yayi Dr Barau sannan ya kashe wayar,
Mummy dake tsaye da flask a hannu ya fada ma,
ita ma cike da farin ciki ta sauka kasa ta kira dukkan yan uwanshi ta fada musu,


Raudha dake lagos tasan in ne Exxonmobil,
dan haka ta fara koda gurin tana sanyawa Mummy shirin fara nemo mishi mata yar masu kudi ko sarauta,

dariyar farin ciki Mummy tayi tace
"ba sai kin fada ba,


Matar Little dina zata zamo yar gata gaba da baya,

yar da iyayenta basa kyashin kashe mata dukkan dukiyarsu,
yar da zata ayi aman kudi daga ko wani bangare,

biki ne wanda nake shiryashi tun kafin yau,

biki ne na garari.......




Mrs Tijjani Shattimah......
[01/04 3:08 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣8⃣
By *Aysha Ya'u kurah*



*Kaduna, Niger, Abuja, Nasarawa, direct,*

wani dan saurayi ke tsaye jikin zungureriyar mota yana busa taba yana fadin sunan garuruwan da zasu,
nan aka fara tururuwar shiga motar kowa na fadin inda zashi,


cike da hanzari ta karaso gurin motar tana fadin kaduna,
kallon motar saurayin yayi yace

"Baba motar ta cika saidai Ko zaki hau baya kan kaya, 

"karfe nawa wata motar zata zo to,  ta fadi cikin gatsali

"keeee yane... kike min magana kamar wani danki,
in zaki jira motar karfe shida na yamma ki jira in baki iya jira wareee,


Cike da mamakin rashin ganin tsufanta tace
"kai da uwarka baku da tsofaffi a gidanku ne,
yaran yanzu sun fitsare kafarsu, basa ganin girman na gaba dasu, gaskiya anyi asarar haihuwa wallahi,
ta karashe tana kokarin jan jakar gana most go dinta,

"tare ta yayi da sauri ya busa ma fuskarta hayaki hade da cewa,
wallahi bazan duba tsufanki ba zan yaga miki chuna,
zigidir zan miki anan gurin kika sake sako sunan gyatuma ta,


A fusace tace "nace kaci uwar ubanka,
kaji min dan iskan yaro,
ni nan da ka ganni bani da mutunci, zan iya yi maka mummuna illa in baka maida hankalinka ba,


"ehhhhh yeeeeeeee,

ya saki ihu hade da chukumar jakar Goggo yayi wurgi da ita,

nan jakar ta yage  kayan ciki suka firfito,
wata katuwar kwalba wacce take nade a zani ta tarwatse ruwan cikin ya bata sauran kullin dake cikin wasu takardu,

ďaga hannu yayi zai kai mata mari drivern motar yayi saurin rikeshi,

"kyaleta GARO,
barta ta shiga bayan boot din ta zauna,

kallon Goggo yayi wacce ta tsurawa kayan da ta kwana tara a hanya tana nemansu,

wani irin tukuki taji a zuciyarta tayi kukan kura ta kama wuyan Garo,

Dagewa yayi iya karfinshi yayi wurgi da ita gefe hade da zaro zarbebiyar wuka mai kyalli,

nan take Goggo ta maida hankalinta ta mike tana kukan wayancewa hade da cewa mutanen dake rike Garo
"yanzu dan Allah in ba sauyin zamani ba wannan yaron banyi jika na uku dashi ba,


"Na sha tara kikayi dani dan mai cin-----

toshe mishi baki drivern yayi yace
"yi hakuri Garo,
nasan laifinta ne,
ka barta ta shiga mota mu tafi,

maida wukar yayi yana ta muzurai hade da hararar Goggo,

sum sum ta wuce tana kallon jakar da ta sha wahala ta kashe makudan kudi dan samo su,

"tuno kashedin da bokan yayi mata na ta kula da kayan domin a shekara sau daya ake samun sa'ar samunsu,

wasu zafafan hawaye ta share zuciyarta a dagule ta nufi bayan motar inda kayan mutane suke,

"tana zama taji kukan talotalo a cikin wani kwali a bayanta,

Tagumi ta zuba saboda shiga wani yanayi da tayi,
yanzu ya zatayi ta sake samun wannan sa'ar,
bazata ta taba bari tayi wata daya da Anni da papy ba tare da ta illata su ba,
so takeyi taga bayansu dukkansu,
so takeyi ta mallaki zuciyar Baffa da gidanshi baki daya ita kadai kamar yadda tayi a baya,
daga ita sai yarta da jikokinta,


Tana cikin wannan tunanin mai cike da takaici drivern yace ta bashi kudi,
"nawa ne?
, jaka goma sha biyu,

"jaka har goma sha biyu, abin na sat-----
ganin Garo a bayanshi yasata saurin sauya maganar zuwa
"abin har yayi sauki haka,
fito da lalitarta tayi ta bashi kudin ciff,
irin kallon da Garo ke mata yasata saurin sunkuyar da kanta, shaff ta manta da yar posan kudinta a gefe,
tana jin motar ta fara tafiya, ta dago kanta,
tunane tunane ta shiga yi marasa dadi har bacci yayi gaba da da ita....




Mikakkiyar tafiya sukayi ta tsawon awa 8 saboda ana yi ana tsayawa Sallah  da cin abinci,


Suna daidai *kawo* suka fara shelar kowa ya hada kan kayanshi domin yanzu yan kaduna zasu sauka,

Goggo da bacci yayi gaba da ita sam bata san sunayi ba,
haka drivern baisan kaduna tace ba,
da yake yan kadunan basu da yawa ko minti biyar basuyi ba suka daga zuwa garin gaba da zasu,

saboda tsabar baccin gajiya ko kuma ince hakki, saida suka kai bus stop din tafiyarsu da Goggo,


Nan drivern ya tasheta a gajiye dan bacci yakeji matuka,

a firgice ta tashi tana laluben poss dinta tana fadin har munzo Kawo?

Wani kawon? drivern ya tambayeta cike da kosawa,

"Kawo ta kaduna ďan nan,
tsaki yaja yace "dan Allah Baba fito kar in miki rashin kunya,

fitowa tayi cikin rashin fahimta tace "ban gane ba, ina ne nan,

rufe boot din yayi yace "je ki tambayi wadancan, ya nuna wasu gungun mashaya a gurin ya wuce yana mika hade da wakar dan kwairo ta "mai dakin gabas,


Zaman dirshan Goggo tayi a garin da bata san ko ina ne ba,

saboda baccin da ta tika idonta ya soye sam bata jin shi,
ga muguwar yunwa tana ji,
ga bakin cikin satan da akayi mata,


Tashar cike take da mashayan da basu da aiki sai na shaye shaye duk minti,
mayafinta ta cire tayi matashi dashi, ta rasa yadda zata fassara irin hau din da hauta a wannan rana,

saboda tsabar takaici har sambatun bacin rai takeyi,
ga tsabar ciwon kai da ya sata a gaba, 


Wani mai butar shayi ne ya gifta tayi saurin kwala mishi kira,

dawowa yayi da sauri dan a tunaninshi siya zatayi,


"sannu ďan albarka,
nan wani gari ne dan Allah?


"Tashar Akwanga!
bakisan a Nasarawa kike ba,

wani kululu Goggo taji ya taso mata,
nan take hawaye ya wanke fuskarta,
da yaron yaga ba siya zatayi ba yayi saurin mikewa ya nufi gurin wadanda suka kirashi,


kuka mai hade da majina Goggo tayi shi a daren ranar,
maimakon ta saduda tasan hakki ne ya fara dawainiya da ita sai ta kara kullatar bayin Allahn da zata sake ninka zunubbansu akanta....




Motar dake tashi da asuba zuwa kaduna tabi tanata roko su sata ko a sama ne,
tana cikin wannan magiyar taji muryar da ko a mafarki taji ta zata ganeta,

"Rilwanu ta fadi bakinta kamar gonar auduga,
daga ina kake?

Nuna mahaifinshi yayi yace daga Benue muke zamu wuce kaduna,

wannan Mahaifina ne,
kamar yadda na fada miki zan dawo dashi kaduna in nema mishi magani,
da yake a cikin duhun subahi ne sai basu samu damar ganin fuskar juna ba,
nan dai Goggo ta shiga aljihun kaskastaccen bawan gidanta Rilwanu......




Firgai firgai ta shigo gidan yunwa kamar zata kasheta,
a lokacin har masu ginin sunzo,

da masu gyara mata daki da masu karasa ginin da ake buga kwano,

goge idanuwanta tayi dakyau ta fara dubawa ko ba gidanta ta shigo ba,
dakin waje shi ya tabbatar mata da gidan ta shigo,

zagaye dakunan tayi hade da fadawa dakinta,

wani irin ja baya tayi cikin firgicin rashin ganin ko tsinke a dakinta sai ma hake haken kasa da akeyi ana sa tiles masu kyalli,
nan take yunwar da takeji tayi murabus a cikinta ta fara fadin,


"uban waya saku fasa min daki, ina kuka kai min kayan daki?
Tabdijam,

wallahi hukuma ce kadai zata rabani daku,
ashariyya ta fara kundumo musu babu kakkautawa,



Muryar Papy tajiyo daga tsakar gidan yana sallama,
fitowa tayi da sauri har tana tuntunbe,
tana fitowa Baffa ya murda kofa ya fito yana amsa sallama,

baki ta saki tana kallon yadda muhammadunta ya canza a cikin yan satittikan da ta tafi ta barshi,

gaba daya an aske farin gashin dake gemunshi da kanshi,
tsufanshi ya boye sai wani annurin kyau da yake fitarwa,


Bugaggiyar shadda blue ce a jikinshi sai hula da takalmi masu matukar kyau, ga wani uban kamshin turare da yake fitarwa,
duk su biyun ta kalla taga kayan nasu iri daya har dinkin ma,
bata kara shan mamaki ba sai da jiyo sallamar Daddy,

kallon hanyar shigowar tayi taga ya shigo da danyar gezna ash,
bayanshi Musaddiq, Hafeez da Jamal ne suma sunyi kyau sosai,

*Zuri'ar Atika*

ta fadi a hankali,
wata juya ta fara ji wacce ta sanyata yin zaman dirshan,
Papy ne ya fara isa gareta yana fadin

"subhannallah, Inna lafiya?
ina kika tafi har wannan lokacin kika barmu da jimami,
bata iya yin magana ba sai kukan takaicin da ya kufce mata,
taruwa sukayi akanta harda Baffa suna mata sannu, dan yanayinta na marasa lafiya ne,
dakin waje suka shiga da ita Baffa ya tsaya a kanta yana mata tambayoyin inda ta shiga,

kureshi da ido tayi alamar tuhuma,
ga mamakinta murmushi yayi kamar yaro karami,
haibarshi ta lokacin samartaka ta tariyo kanta,
shi ma ita din yake kallo amma fa a tsorace yake dan yana tsoron abun da zai canza ra'ayinshi akan auren nan,
dan kwanakin da ya jera yana haduwa da Anni yaji tayi matukar kwanta mishi a rai,
yana fatan suyi zaman tare har mai rabawa ta raba,
"Biki akeyi na ganka da sababbin kaya?
yadda ta jefo tambayar sai ta bawa mai kallonta tausayi,

"Gyada kai yayi yace "eh bikin Muhammadu da Hanne,
agogon bango ya kalla yace
"goma daidai za'a daura,
yanzu tara da rabi,
bari muyi saurin zuwa gurin, akwai kayan abinci a cikin drawer can kiyi kokari kici kafin mu dawo, sai ki fada min inda kika je kuma da izinin wa,

*IZINI*

Goggo ta maimaita kamar me koyon magana,
yana gab da fita tayi karfi da jikinta ta damki babbar rigarshi hade da fadin
"wallahi babu inda zaka,
kai baka isa ka wulakanta ni ba Muhammadu,
ko kunya bakaji,
banda jika har tattaba kunni gareka amma dan budurwar zuciya irin taka harda yin anko kai a dole zaka angance,
to wallhi saidai in ka kasheni ka ka fita,

saboda rashin kuzarin da take ciki yasa shi kwace rigar yace
"Raya sunnar ne abin kunya, bazan kasheki ba,
kuma aure babu fashi mutuwa ka raba,
yana kaiwa nan yasa kai ya

Please Login or Register in order to submit comment