Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma tabbas lokacin barinta gidanta yayi.....





Suna isa asibitin babu bata lokaci suka karbeta sukayi aune aunensu,
bayan sun gama suka yankata suka ciro santalellen yaro wanda ya shiga cikin zuciyar Anty saude a ganin farko,
farin ciki a gurin Taheer da Amal ba'a cewa komai,
tun daga nan yaro ya fara ganin gata ta musamman domin yini yakeyi a hannu...





Ranar Suna yaro yaci suna Mukhtar.. Hilal,
shima dakyar Nadeeyah ta faďi dan da cewa tayi su sa da kansu,

duk yadda Anty Saude taso ta nuna ma Nadeeyah bata kaunarta Taheer ya hana domin ya nusar da ita cewar ba laifinta bane...



Akwai wani dare da tace mishi

"Kar dai so kakeyi ka koma gurin bazawarar yarinyar nan,
to wallahy Taheer in har tunaninka kenan gara ka janye dan bazan taba yarda su kashe min kai ba,
karka yarda kace zaka dawo da ita cikin rayuwarka in ba haka ba sai nayi mugun saba maka,

Shidai kwantar mata da hankali yayi bai bata amsa ba....




Watanta biyu da haihuwa Taheer ya fara lallabata su tafi gida,
cikin kankanin lokaci ta yarda cike farin cikin sake ganin Musaddiq,
tasan in yaga gudan jininshi zai dawo da ita su cigaba da rayuwarsu cikin kaunar juna,


Saboda tsabar sonshi da takeyi ta manta da irin wulakancin da yayi mata shi da su Anty Raudha,
tayi musu uzuri na ajizancin dan adam...



Ganin yadda take farin ciki ya sanya Taheer soma shirin tafiyarta,
ranar da suka tafi tare dasu Amal saida Anty saude tayi kewa,
tayi matukar sabawa da Junior, komai ita ke mishi,
tsanar da tayi wa Nadeeyah sam bata shafi danta ba,
domin sau daya takk a rayuwarta ta taba samun opportunity din raino,
sai gashi Allah ya kawo mata wani wanda kaddarashi tazo da ta tsani mahaifiyarshi,

Soyayyar Taheer ce kadai tasa ta yarda Nadeeyah ta zauna har wadannan kwanaki,
sai kuma soyayyar dan mala'ikan Allah.....





Lagos Nigeria..


Da murnarta ta sauko a cikin motar haďe da lumshe idonta,
memories din baya ya shiga yi mata yawo,
kofar gate din ta kama ta tura,

Mummunan gamon da tayi shi ya sanyata sakin kofar Garammmmmm.... ta koma motar su Taheer da sauri tana sheshshekar kuka...


"Lafiya Nadeeyah? Menene,

"Muje kawai uncle,
zanyi maka bayani,
tada motar yayi yajata ya fita daga layin ya wuce hotel din da ya sauka kwanakin baya,
daki biyu ya kama da parlor,
saida suka gama kimtsawa sannan ne ya tambayi Nadeeyah da har lokacin bata bar kuka ba...




"Babu amfanin komawa garesu Uncle,
sun manta dani,
Musaddiq ya riga yayi aure,
ya auri Faida wacce tayi sanadiyyar rabuwarmu,

Dan Allah uncle karka matsamin in koma gurinsu,
domin rayuwata bazata taba inganta ba,
bazasu taba barina na zama independent ba,
kowa a cikinsu ya manta dani,
bani da sauran gatan da ya wuce in nemi ilimi,
ku tafi kawai,
zan shiga duniya neman ilimi har Allah yasa in dace da tsayuwa da kafafuwata...




Tissue ya mika mata yace ta share hawayenta,
wayarshi ya dauka ya kira number mai gadin gidansu ya sashi ya duba ko Raliya na nan..

saida yayi kusan minti goma sannan ya kirashi yace bata nan amma ya samu number da take aiki dashi yanzu,
cike da murna ya umurceshi da ya turo mishi,
bayan ya turo mishi ya wuce daki dan kiranta,
yana kira ta daga kamar dama tana jiran wayar,


"Hello salamu alaikum,
ameen wa alaiki salam mummyn Fadeel, ya gida?

Cikin rashin sanin muryar tace "lafiya kalau ya harkoki,

fine alhamdulillah ya faďi yana gyara zama,

Taheer ne,
in bazaki damu ba dan Allah ina son ganinki,

Ayya Taheer ya su Anty saude,
shikenan sai kuyi zamanku haka akeyi..

dariya yayi yace
"Ba haka bane karatu ne ya rikeni,
ina Fadeel?
Gashi can yana wasa,
yaushe zaka zo?

Gobe da safe in shaa Allah,
to Allah ya kaimu Taheer, sai kazo.....



Washe gari suka hau jirgi zuwa kaduna,
saida ya fara sauke su Amal a gida suka ci abinci suka huta sannan suka wuce gidan Anty Raliya...



Basu sameta a gida ba saida suka jirata har na tsawon minti goma..



Ayi min afuwa Taheer, na kusa fara exams ne walhy,
ban cika samun zam----
muryarta ta kakare saboda yin tozali da Nadeeyah da tayi,


Mutsitstsika ido tayi haďe da sakin hannun Fadeel,

Na---dee--yahh....
ta faďi cikin rawar murya,
rau rau idon Nadeeyah yayi tace
"Na'am Anty,
kirji Raliya ta rike itama idanuwan nata suka kawo ruwa,

"Nadeeyah,
dama kina nan a raye?

Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ina kika shiga?


Kasa bata amsa tayi sai kuka mai karfi da ta fashe mata da shi,
zama Anty Raliya tayi ta rungumo Nadeeya tana share hawayen farin cikin,


Taheer ina ka nemo mana Nadeeyah,
shekara ďaya da watanni kenan muna nemanta,
an shiga matsaloli sosai na rashin ta,
ashe tana nan da rai..

Alhamdulillah,
Allah nagode maka da ka dawo mana da Nadeeyah cikin koshin lafiya,
kankame Nadeeyah tayi tana shafa bayanta haďe da kukan farin ciki....


kushun kushun din yaro taji yana shirin fara kuka,
hannun Taheer ta kalla taga ya daurashi a kafadarshi yana jijjigashi,

kallon mamaki ta bishi dashi tace "Taheer kayi aure ne?
Babynka ne?
ina Mamanshi?
Duk wadannan tambayoyin tayi su ne cike da zullumin kar yace mata Nadeeyah ya aura,
tasan in hakan ne tabbas rayuwar kaninta na cikin hatsari..


Jin Babyn tayi a kusa da ita tayi saurin kallon Nadeeyah da ta fara kokarin bashi nono,
dago kai tayi da sauri taga Taheer har ya fita daga dakin saboda ya bar Nadeeyah ta shayar da Babynta...


Nadeeyah yaushe kukayi aure?

Ya salam ta faďi haďe da dafe kai hawaye ya sauko a idonta...


Daura mata babyn tayi a hannunta tace
"Danki ne,
jininki ne Anty, dan yaya Musaddiq---neeee..
ta karashe cikin kukan tunanin Musaddiq yayi mata nisa...


Wata irin runguma Raliya tayi ma Junior ta dinga sumbatarshi tana zubar hawayen farin ciki,
tabbas wannan jininta ne,
komai nashi na mahaifinshi ne,

wayyo Allah,
wannan ita ake kira

*Zazzafar Kaddara*,
ina ma Musaddiq zai iya zuwa yanzu yaga gudan jininshi...
kuka sosai ta dinga yi tana sambatu a fuskar Junior....




Mrs Tijjani Shattima.....
[12/06 7:55 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣8⃣
By *Aysha Ya'u kurah*







A tare suka waigo dan ganin wanda yayi wa kofar gidan haka kamar dama yanada haushin gidan,
horn din da zubair yayi ne ya sanyasu manta batun kofar Hilal yaje ya bude mishi gate din....




Daya bayan daya sheik ya kalli su Papy da su Baffa,
ganin har ya gama kallonshi bai dire idonshi kan yayarshi ba ya sanya shi tambayar inda take,


Baffa da tun shigowarshi gurin ya ke kallon Sheik yana hasashen da ya tabbatar gaskiya ne,


Daddy ne yayi karaff ya fara ma sheik nasiha da sigar tunatarwa sannan ya nuna Baffa yace wannan shine mijinta,
wannan kuma danta ne,
Allah yayi ma twin sis dinshi rasuwa,
introducing kowa na gurin Daddy yayi mishi sannan ya karashe da cewa Nadeeyah is no were to be found,
bamu samu gawarta ba shiyasa muka yarda da cewa she is alive,



Baffa ne ya cigaba da magana bayan Daddy ya dire ya ba sheik labarin yadda rayuwar Atika ta kasance da yadda kullum bata da magana sai tashi,
har ranar da zata koma ga mahallincinta saida ta ambaci sunanshi....



Kukan da sheik yakeyi mai sauti shi ya katse Baffa daga bashi labarin Atika,
babu wanda ya hanashi zubda hawaye saima wadanda ke tayashi irin su Papy, Baffa da Maleekah,
saida sukayi mai isarsu sannan suka fara tsagaitashi saboda nasihar da Daddy ya cigaba dayi,



Labarin gararin rayuwar da Papy ya gani suka bashi wanda ya sake jefashi cikin mamaki da tsananin tsoron Allah,
sosai Sheik yayi bakin cikin rashin sake ganin yayarshi,
amma yayi murna matuka da ganin yadda zuri'ata ta yaďu gwanin ban sha'awa duk da baiga mutum biyu ciki ba,
daya bayan daya ya shiga rungumarsu kamar zai maidasu ciki,
farin cikin kasantuwa da yan uwa baya misaltuwa,
a wannan rana sheik ya kira Hilal da alherin rayuwarshi,
dan a sanadiyyarshi ne ya haďu da yan uwanshi na kusa,
zuri'ar yar uwarshi da tasoshi matuka......




Masauki na musamman Daddy ya kamama Sheik da iyalanshi,
a can ma saida suka raba dare suna hira kamar babu gobe....





Jamal da Ruwaida ne zaune kusa da Maleekah suna faďa mata yadda suka daďe suna kallon films dinta,
cike da jindadi tayi musu alkawarin tafiya tare dasu domin kallon sabon film ďinta Saheebul qalbee,
sun dade suna hira haďe da daukar hotuna,
sai kusan 12 na dare suka fara shirin zuwa masaukinsu suma..



Har waje ta rakasu tana karewa kasar da bata taba zuwa ba kallo,

Har motar su Papy ta bacewa ganinta bata koma ciki ba saima waje da ta fito tana zagayawa dan karewa arear kallo sannan ta jira ganin fitowar Hilal da ke can kasa yana ma Abbunta order irin coffeen da yakeso duk dare....





"Omoo see fine girl..
wani dan bayerabe ya faďi bakinshi kunshe da wiwi,
dayan da gaba ďaya a buge yake yana kallonta dishi dishi yace

"O boy i no see anything,

kamo hannunshi yayi suka nufi inda take takunta day day hannunta rungume da kirjinta,

rigar dake jikinta girmanta duka bai wuce gwiwa ba,
sai dan karamin mayafi da ta ďaura shi akanta,



Suna karasowa kusa da ita taji wani mugun warin da bata taba jin irinshi ba duk rayuwarta,
da sauri ta matsa baya tana faďin

"Ya subhanallah,

sake matsota sukayi gadan gadan har suka samu sa'ar cafke hannunta,
gaba daya yanayinsu kyama ya bata hakan yasa ta fara masifa cikin harcen larabci tana kokarin kwatar kanta,
da taga sunfi karfinta kuma suna janta iya karfinsu ta saki wani ihu tana neman ceto,


Shurun unguwar ya sa babu wani mataimaki a gurin sai Allah,
kara karfin ihunta tayi lokacin da taga sun nufi wani lungu da ita,

"Ya hayyu ya qayyum bi rahmatika astagithu....
hakan ta dinga faďi hawaye na fita sharrr daga cikin idonta...



Full light aka saki wacce ta haska gurin da suke,
basu saketa ba sai sa hannu da sukayi suna kare fuskarsu suna masifar dalilin haskasu,


A haka Hilal ya bar motar ya fito da sauri ya nufi inda suke,
ganin haka yasa dayan me makami sakinta ya zaro wuka a cikin aljihunshi ya tsaya a gaban Hilal,

a ruďe Maleekah ke rokon Hilal da ya koma kar su kashe shi,
bai ma san abun da ta ke cewa ba dan hankalinshi yafi tafiya gurin dayan dake luguiguitata,


Tsugunawa kasa yayi da niyyar cire takalminshi yayi saurin jan kafar mai rike da wukar,
sara ya kai mishi a hannu kafin ya ankara yajishi a kasa,

sosai saran ya shiga hannun Hilal wanda baisan dashi ba saida ya danneshi ya kwace wukar haďe da tattakashi,
shiko dayan na ganin haka dama ba cikin hayyacinshi yake ba yayi saurin ja da baya,
kamoshi Hilal yayi ya nakaďa mishi mugun dukan da duk suka kasa motsi,
wurgi yayi da wukar haďe da yin gaba yana mai dafe inda jinin ke zuba,


A guje ta biyo bayanshi ta kwance dankwalin kanta tana kokarin kama hannunshi dashi,

ture hannunta yayi da karfi har ta kusa faďuwa ya buďe motar ya shige,

"Ta inda kika bi kikazo nan ki bi hanyar ki koma masauki..
yana kaiwa nan ya tada motar da karfi yana shirin janta,

buďe kofar tayi da sauri tace

"Heartless being,
so zaka iya tafiya ka barni a nan a matsayina na bakuwarku?


"Kokarin banbare rikon da tayi mishi yayi ya kasa saboda tayi mishi mugun riko,

kallon cikin idonta da yayi jawur yayi yace
"let go off me!

Sake dukunkuneshi tayi haďe da noke wuya,
yadda tayi da baki tana shirin fara kuka ya sanyashi kashe motar haďe juyar da kanshi gefe,
ganin haka yasa ta sa hannu ta buďe bayan motar sai a sannan ta sakeshi tayi saurin shigewa ciki..


kuka sosai ta shiga rerowa kamar karamar yarinya,
gaba daya ta tsorata da Nigeria gani takeyi kamar in ta sake kwana ďaya za'a iya kasheta bayan an lalata mata rayuwa,


Jan motar Hilal yayi ya maida ita masaukinsu,
sosai kukan da takeyi yake taba mishi zuciya,
sakkowa yayi ya buďe bayan motar,
"Its late, i want to go home,
dago kanta tayi ba tare da ta kalleshi ba tayi saurin bin dayan gefen ta ruga ciki da gudu tana sake yin wani sabon kukan...





Rufe motar yayi da niyyar bin bayanta sai wata zuciya ta haneshi da yin hakan,
motar ya shiga ya tada ya canza wata hanyar da ya tabbatar zata kaishi gida domin gudun sharrin dare da na mutanen da suka samu matsala.. ..




Washe gari tun asuba Maleekah ta shirya ta wuce dakinsu ummi...

Bugu sosai tayi ma kofar wanda ya sanyasu mikewa a tare dan ganin mai dukan kofar haka,

"Lafiya?
Ummi ta tambaya haďe da janyota cikin dakin,


Jakar dake hannunta ta ajiye ta karasa kusa da Abbu tace


"Abbu ka shirya mu tafi yau plss,
i hate Nigeria,
yadda takeyi kamar zatayi kuka ya sanya shi zaunar da ita haďe da tambayarta abun da ya faru,
labarin abun da samarin nan sukayi mata ta bashi sannan ta kare da cewa

"Ta rantse bazata sake kwana a kasar nan ba!

Jin haka Sheik ya bata hakuri akan ta bari ya gama yan uwanshi dan yayi niyyar tafiya dasu,


"Noo Abbu,
ka tsaya ka tafi tare dasu,
we will go with Jamal nd Ruwaidah,
gamsuwa yayi da maganarta bayan ya tabbatar da hakan ya gamsar da ita...




Karfe goma na safe dukkan ahalin suka iso masaukin Sheik,
bayan an gaggaisa duk suka haďu sukayi breakfast cike da kaunar juna sannan suka shiga hira sosai,


Matan na bangarensu haka mazan ma,
anan ne Sheik ke sanar dasu komawar Maleekah ya kuma ce tare zasu tafi dasu Jamal,
cike da murna Papy ya amince dan dama cikin hutu suke,
shi kuwa Jamal aiki ake nema mishi,

"Na dauka sai tayi sati daya itama?
Daddy ya tambaya yana dariya,


Murmushi Abbu yayi yace
"Akwai abinda zai maida ita, sannan she is not comfortable here,
kaga ita kadai ce mace,


"Sai in kaita gurin Husna,
itama dan bazata iya zuwa bane shi yasa na barta a gida,
Hafeez yayi karaff ya amshe saboda yana matukar jin dadin ganinta,
ko ba komai tana ďebe mishi kewar mutane biyu a idonshi,


Dariya sheik yayi yace
"Bazata yarda ba ai, next time zatazo ta dade muku in shaa Allah,

nan suka kauda zance suka shiga wani zancen daban na tsara inda zasu je ziyara ya ga yan uwa wadanda suka jibanci yayarshi ko sukayi zama tare,
Kaduna... nan ne gurin da suka tsara tafiya washe in Allah ya yarda.....






Karfe sha biyu na rana jirgin nasu zai tashi hakan yasa Jamal yin wasu yan siyayya near by dan bada shiri yazo ba,

Hilal ke tuka motar yana sauraron duk murnar da su Jamal sukeyi na yin kallo cikin cinemas din turawa....




Ya rasa asalin abun da yake ji a cikin ranshi,
duk tunanin da ya dauko sai yayi saurin kaudashi dan ba'a cikin muhallinshi yake ba,
soyayyar da yayi a baya bayason sake yin makamanciyarta dan zata iya buga zuciyarshi,
ya samu dakyar ya maida soyayyar Nadeeyah wani muhallin daban,
baya kaunar sake tsintar kanshi cikin mawuyacin halin da ya shiga a baya,
suna isa airport din yayi parking haďe da runtse idanuwanshi yana tuno abubuwa da dama,



"Ur problem is lving!

Buďe idonshi yayi yaganta tsaye jikin windon gefenshi,
bai dago kanshi daga kwanciyar da yayi ba ya zuba mata manyan lumshashun idanuwanshi,
ita din ma cikin idonshi take kallo babu ko kiftawa,
maida idonshi yayi ya rufe dan a rayuwarshi ya tsani mace a tsaytsaye,
abubuwa da dama kan sashi ya ragawa Maleekah,
kofar ta buďe tasa hannu ta buďe idonshi duka biyun,
nata idon ta gwalo ta turo fuskarta kusa da tashi,


Ya Allah... ya fadi haďe da kauda fuskarta,

"Maleekah kin tabbatar kina da lafiyar....... kanta ya nuna da hannunshi,


haďe rai tayi kamar zatayi kuka tace


"Dan ina kulaka shine zaka ce bani da hankali,
laifi na ne,


"Heyy tambaya ce,
ya faďi da ďan sakin fuska..


bata tsaya sauraronshi ba taja hannun Ruwaidah suka wuce ciki,


Murmushi yayi bayan yaga kurewarsu yaja motar yayi gaba.....





Mrs Tijjani Shattimah........
[13/06 10:15 PM] +234 807 161 1811: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 7⃣4⃣
By *Aysha Ya'u kurah*




Mamaki sam ya hana mutanen parlon yin magana sai Badariyya data dawo kusa da mijinta ta rokeshi da yayi shuru,
in gaskiya ne zasu fahimci hakan da kansu...


Jin da sukayi jiniyar taki tsayawa yasa Hilal da Daddy yin waje,

Shi kuwa Musaddiq sama yayi da little Nadeeyah dan ya bata chocolates,
samm bai tausayawa Badariyya ba domin ta sanyashi cikin ukubar da bata da magani...


Suna fita sukayi karo da motoci takwas,
huďu daga gidan sarkin Zaria, biyu daga gidan gwamnati sai biyu tasu Taheer,

Dukkan motocin numfashi kawai sukeyi,
saboda tsabar haďuwa babu wanda a unguwar bai bisu da kallo ba,


Dogarai ne suka fito da sauri suka tattare kofafin fitowar kowacce mota,

Sarki Tidjani ne ya fara fitowa shi da Shareefah,

Sai ďayar motar Sarkin Sassounburom da mutanenshi,


Cikin kasaita Anty Saude ta fito cikin wani kasaitaccen lace irin na jikin Shareefa,
wuyoyinsu da hayyensu sai kyallin zinari yakeyi..


Samm idon Anty saude bai kai mata kan Daddy dake tsaye a kofar shiga parlon ba..


Motar karshe wacce Kamal ya tuko ita wani dogari ya buďe,

Junior ne ya fara fitowa yana rawar wakar *Issa goal* da Kamal yasa mishi,

Dariya Anty saude tayi tana kara jin kaunar yaron a cikin ranta...



A hankali yake mata magana cike da kauna yana lallabata ta fito,

karfin gwiwa ya bata akan babu abinda zai faru,
ta fito su tafi,
he will not lv her here,


Dakyar ya samu ta ziro kyakykyawar kafarta wacce take cikin wani lafiyayyen jan flat shoe mai beza..


Numfashin Hilal neman daukewa yayi saboda ganin yatsun da ko cikin magagi ya tashi zai gane maishi...

*NADEEYAH....*

ya furta a hankali gabanshi na dukan uku uku..

Bayyana kanta tayi fatar nan sai kyalli takeyi,

Ash jallabiya ce a jikinta wacce akayi ma ado da jajayen duwatsu,

gyalen kanta bata samu nutsuwar yane shi ba sai nadashi da tayi akan jelar suka sakko a dukka kafadunta..

Rufe kofar Taheer yayi yace

"Calm down Baby,
babu abinda zai faru,

ďaga idon da zatayi dan bashi amsa ta saukesu cikin na Hilal wanda ke tsaye kamar wanda aka dasa...

Wani irin sanyi taji ya ratsata ta fara gudu a hankali dan isa gurinshi,

"Ya Hilal..
ta faďi cikin muryar kuka,

Kauda kanshi yayi dan baya so sam taga hawayen da ya taru a cikin idonshi..

Ganin hakan yasa ta shigewa cikin jikinshi ta fashe da matsanancin kuka,

kukan da yake boyewa dole ya sakeshi ya rungumeta shima yana fadin

"Kina nan da ranki all this while Nadeeyah,
ina kika shiga?

Alhamdulillah ya Allah...


"Barrister Nadeeyah!
ur Nadeeyah is now a Barrister Ya Hilal,
i missed u alot...

Dago fuskarta yayi yana dariya mai dauke da kuka,

"Missed u more,
dis is tears of joy,
Alhamdulillah...


"Nadeeyah...

da sauri ta waigo ta kalli Daddy dake tsaye idonshi jajur,

'Kasa ta tsuguna yayi saurin dagota ya haďata da jikinshi...

"Kin nuna min ban haifeki ba Nadeeyah,
meyasa kikayi min haka?
Daddy ya faďi yana mai jin zafi a cikin ranshi na rashin ta cikin wadannan shekarun..

"Kayi hakuri Daddy,
kaddara ce,
dan Allah kayi hakuri..

"Bana fushi dake Nadeeyah samm banyi fushi ba,
Nadai gode ma Allah da yasa zan sake ganinki kafin na mutu.....

  " *MG Kyari*
cike da mamaki Daddy ya dago ya kalli me maganar...

" *SAUDATU HALLIRU*...
ya faďi yana zaro ido....

"Ikon Allah....
Anty Saude tace tana rike haba,
ashe rai kan ga rai?,

"Saudatu kina nan abinki,
lallai duniya tanada faďi,
shekara kusan nawa rabon da mu haďu,

Kaii mashaa Allah Nourun ala nourun ya faďi cike da farin ciki..

Ga kawu na can ka barshi a tsaye...

Cikin daburcewa Daddy ya karasa kusa dasu ya tsuguna har kasa ya kwashi gaisuwa sannan yace su shigo ciki...

Cikin takun kasaita suka fara takawa har cikin parlon...


Kashe wakar Kamal yayi Taheer ya kama hannun junior suka bi bayansu..

Hannu Hilal ya mika ma Taheer da fara'a dauke a fuskarshi,

"Wow,
matured mind, Taheer ya faďi cikin tsokana,
yanzu ba faďa ko?

Dariya Hilal yayi  yace we are Family,

hannu Taheer ya mika mishi da sauri haďe da rungumeshi....


Durkusawa Hilal yayi ya kalli junior,
a hankali ya zare glass din idonshi yace

"Mashaa Allah Junior Kyari,

Mr soft or Hard?
ya tambayeshi yana nuna mishi hannu,
da karfi junior ya dunkule hannu ya buga hannun Hilal yace
"Mr Hard ofcourse!!

Dariya sosai Hilal yayi yace
"Name?

*MHK TAHEER*
amma
*MUKTHAR HILAL MUSADDIQ KYARI* ake cemin a school....


Runtse ido Hilal yayi ya kankame Junior kamar zai maidashi ciki,

my nmsake,
ya Allah..,
I love you boy...
ya karashe haďe da sumbatar shi.....

I love yhu too Junior ya faďi yana mai mayar mishi da sumba..

Hannunshi ya kama suka nufi mota dan su fita ya dan jiyar dashi dadi kafin ya zauna....





A cikin parlon kuwa kowa mamakin ganin Nadeeyah yayi banda Raliya daketa dariya da farin cikin ganin yadda Nadeeyah ta koma...

Anty Reemah da Anni kuwa faďa suka rufeta dashi wanda ita kanta tasan na daďi ne....

Sun dade rungume da Anty Reema tana tambayar ina Zainab?

Cikin kuka Anty Reemah tace "Tayi Fushi,
kika manta da ita ma bare ita, tuni ta mance dake,
tana can gida suna jarabawa ne shiyasa ban taho da ita ba...



Dakyar Nadeeyah ta iya gane Mummy dasu Raudha,
har kasa ta tsuguna ta gaida Mummy wacce fuskarta tayi faca faca da hawayen farin ciki,
rungumae Nadeeyah tayi wani irin kamshin sanyi ya daki hancin dukkaninsu wanda tun zuwansu duniya har kawo yau basu taba jin irinshi ba...




Dafa kafaďunta taji anyi ta raba jikinta da Mummy ta waigo tana murmushi tana kallon matar cikin rashin fahimta,

"Nadeeyah,
dan Allah ki yafe min,
yadda ta haďe hannayenta biyu tana kuka sosai yasa Nadeeyah rike hannun tace
"Me kikayi min, baiwar Allah? Wallahi na yafe miki duk da ban sank----

Badariyyah zanyi fitsari,
Hannafi ya katse Nadeeyah yana matse cinya dan fitsarin ya fara zubar mishi,

Zaro ido Nadeeyah tayi,,

"Badar!!

Ke---ce... ta faďi cikin rawar murya,
nan take wani tsagoron tsoron Allah ya tsarga a zuciyar Nadeeyah,
tana kallon Badariyya ta ďaga yaron da yayi faca faca da fitsari tayi famfon waje dashi...


Jikin Papy Nadeeyah ta kwanta bayan ya gama mata faďa tana tambayarshi Ruwaidah...

"Tana can gurin su Jamal, a can take makaranta...
ya bata amsa yana mai jin dadin ganinta...

Husnah da ta tura mijinta daki saboda mijin Badar, ta fito kamo hannun Nour da Abi taga parlon a nutse sai manyan mutane masu rawuna dake zaune kowa na kasa a nutse,

Gefen da Papy yake ta kalla ta hango fuska kamar ta Nadeeyah,

tasan dai ta baro Maleekah a cikin daki tana sallah, to wacece wannan?

Karasawa tayi ta tsuguna ta gaida bak'in sannan ta kai dubanta kan Nadeeyah,

"Nadeeyah...

ta faďi da karfi har saida Hafeez ya jiyota..

Da sauri ya buďe kofar ya fito yana dube dube yana faďin

"Me ya sameta?,
duk tunaninshi Nadeeyar Hilal ce,

Ganinsu kankame da juna yasa shi saurin matsawa kusa dasu dan ya gasgasta idonshi...

"Yaya Hafeez..
ta faďi tana nufo inda yake,

Share hawayen dake idonshi yayi ya juya zai koma inda ya fito,

Da gudu ta bi bayanshi ta rungumeshi,

"Am sorry,
dan Allah kayi hakuri,

rufe idonshi yayi hawaye na mishi ambaliya..
gabanshi ta dawo tace
"Dan Allah yaya..

Share hawayen yayi yace

"In kowa yayi deserving haka ni banyi ba Nadeeyah,
in akwai wanda ya kamata yasan inda kike to nine,
meyasa zaki bar min tabo a raina?,

kullum ina ganin kamar gazawata ce tasa kika bace,
samm na kasa rike zumuncinmu..

Meyasa zaki min haka?

Sake kankameshi tayi tace

"Nasan ban kyauta,
haka kaddararmu take,

Dan Allah kayi hakuri Yaya....

sunfi minti biyar suna tattaunawa kafin ya sauko ya fara share mata hawaye....



Tun fitowar Hafeez Sarki Tidjani ya mike fadawan shi suka fara yan yameshi,
haka itama Shareefah da hirar Daddy da Anty Saude ta hanata jin komai ta mike cike da firgicin ganin Hafeez...


"ADAMOU YALLO...
sarki ya faďi cikin rawar murya,

Adamou,
innalillahi wa inna ilaihir rajiun, ashe kana nan da ranka Adamou?

Ajiye sandar hannunshi yayi ya isa gurin Hafeez,
sai a lokacin ya dawo hayyacinshi ya fahimci cewa shekarun da yawa Adamou bazai kasance haka ba,
fuskar Hafeez ya shafa yace
"Ina Adamou?

Mikewa Papy da Daddy sukayi suka isa gurin cikin girmamawa,

"Ranka ya dade,
ba Adamu bane,
wannan Hafeezu sunansa,
"Eh na gane yanzu,
ina Adamoun

Please Login or Register in order to submit comment