Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a bola.. mistakely ya sauka cikin waken da Radiya ke gyarawa,

Wata ashar ta sakar mata haďe da mikewa tace
"wallahi bazan dafa abincin ba,

ni na gaji wallahi,

duk ku kuka jamin,
yanzu ga Shamsu ko waiwayata baya yi,
yana can ya koma Italy da zama shi da yarinyar da tayi min aikatau,
wannan wace irin masifa ce..




Mummy dai jinsu kawai takeyi tana kokarin daga Goggo ta daurata akan pour,

Kafin ta daurata har ta saki kashin a gurin,
a sittin su Raudha sukayi waje dan dama su ba aikin sukeyi ba,

Shekara uku kenan Goggo na fama da ciwon da babu wanda yasan irinshi,
asibiti sun gaji sun maido ta gida,

wani katon rami mazaunanta yayi saboda zama,
ga wasu ramuka da jikinta yayi yana fitar da ruwa mai matukar wari,

Mummy ce kullum ke hidima da ita saboda a yanzu komai ya fice mata a rai,
gara tayi wannan, ta yiwu Allah ya yafe mata sanadiyyar hakan,

Dakyar ta iya wanke mata kashin ta canza mata gurin kwanciya,

saida ta gyara dakin tsaff sannan ta fita dan shan iska..




Tana zama taji sallamar su Papy da ahalinshi da su Anni,
nan fa ta mike ta dinga musu maraba,
yadda ta fita hayyacinta sai wanda dama ya santa shi zai ganeta,
duk da yanzu suna samun gata domin Raliya na taimakonsu sosai..


Bayan sun duba jikin Goggo suka koma dayan dakin suna ta hirar yaushe gamo,

Awan su ďaya sai ga su Hafeez da 'yayanshi uku..
Suwaiba, Adam, da Autan wanda yake hannu mai sunan Papy,
sai Husna da ta zama big madam,


Dakin suka shiga suka gaida su Mummy sannan suma suka zauna akayi hirar dasu....





Daddy ka dawo ne?
akwai abin da nake so mu tattauna..
Raliya ta faďi cikin girmamawa kamar yana gabanta,

"Eh Raliya,
muna kaduna, jibi zan koma lagos kina iya zuwa gida yanzu,

Cike da jin daďi ta mike ta fara shirin zuwa gidan su Goggo dan ta taho dasu Mummy,
dama tun last week ta gindaya ma Anty Reemah karyar Goggo ta shiga coma tazo su dubata..

Anty Reemah ta tabbatar mata yau suna nan tafe,
saida ta kaiwa su Fadeel abinci makaranta sannan ta wuce gidan Goggo...




Taji dadin ganin su Papy,
nan take ta shirya plan din da yasa duk suka shirya tafiya gida..


Goggo kaďai aka bari a gida sai Rilwanu dake zaman jiran zuwan iyayenshi....




Suna isa gidan Mummy ta fara hawayen bakin ciki da dana sani,

lallai in baka godewa Allah ba to tabbas zaka godewa azabarshi,

A darare ta karasa cikin gidan saboda gudun wulakanci a gurin mamallakin gidan...



A lokacin da yaji sallamar su yana parlor yana kallon news,
da sauri ya mike ya taro Papy yana faďin maraba da proff,
bismillah shigo,
bai lura da mutanen bayanshi ba saboda yadda yayi kewar ganinshi shekara da shekaru,


Saida suka nutsu cikin gaisuwa sannan ya kalli sauran mutanen parlon,
yana sauke idonshi kan su Mummy mood dinshi ya canza gaba ďaya,

Cike da masifa ya mike zaiyi magana yaji Sallamar su Anty Reemah,
nan take fuskarshi ta sauya yace "A'a yau gida yayi albarka,

Allah ya sanya alkhairi a wannan taron..

kafin a amsa da Ameen
Muryar little Nadeeyah ta karaďe parlorn,


*HABIBI*,

*YAA OMRI*..


Ta sama Musaddiq ya leko dan jin muryarta kamar amsa kuwwar speaker..
ganin parlon a cike yasashi sakkowa da sauri..


Da ita ya fara tozali rike da kugu tana mishi wani irin kallo,

karasowa yayi ya dagata sama ya dinga juyata tana kyalkyala dariya,


Wani wawan duka Hilal ya kai mishi a baya sai a sannan ya dakata ya rungumeshi,
haka nan ya tsinci kanshi cikin farin cikin da ya rasa na meye,

Cikin parlon suka karasa suka gaiggaisa da mutane,
Mummy ce kadai ya gimtse fuska kafin ya gaisheta,
shi dinma dan yaga su papy ne a zaune da Anty Reemah dake yawan matsa mishi,
hirar yaushe gamo palon ya karaďe dashi,

Sudai su Mummy suna ra'be kamar Mamma Suwaiba lokacin da take da rai bata da galihu,

*Allah kenan*,
babu yadda bai iya ba.....




Murďa kofar dakin sukaji anyi an shigo ba tare da sallama ba,


Yara biyu farare cikin kayan fulani kafarsu tayi butu butu suka shigo suna ta ďari ďari da kafarsu dan kar su faďi,
can bayansu kuma mace ce ta shigo naďe da zani akanta hannunta rike da kullin dankwali,
sai wani namiji fari da riga budaddiya da layu a duk jikinshi har kunne,


Babu wanda a cikinsu ya gane Badariyya, sai Mummy wacce ko a cikin dubu ne zata tsamo ta,



"BADARIYYA!


"Na'am Mummy ta amsa haďe da fashewa da kuka,
karasowa inda take tayi ta rikota haďe da yin wurgi da kayan hannunta,
kowa a cikin parlon da ido ya bita cike da mamaki,

Zama yaran sukayi a gefe suka matse juna su a dole suna tsoron tiles,


Shi kuwa Yareemah Suhail gani yakeyi duk ya fisu muhimmanci a parlon,

Hafeez ne kaďai yayi mishi kwarjinin da zai iya tsuguna mishi,
direct gaban Hafeez yaje ya tsuguna har kasa irin gaisuwar da akema sarki yace

"Ina wuni ranka ya dade,

Shi Hafeez abin ma tsoro ya bashi,
da sauri ya maida kafarshi baya yace

"Ga iyayenmu can su ya kamata ka fara gaisarwa,


"Duk cikin runkar nan babu mutum mai muhimmanci,
daga kai saini, ranka ya daďe, sauran duk mu ya kamata su gaisar...


Kallon mahaukaci duk sukayi mishi suka maida dubansu kan Badariyya wacce take kuka tana neman gafara,


Labarin abinda ya faru da ita ta fara basu,
har yadda ta taimakawa su Mummy suka raba Nadeeyah da Musaddiq saida ta faďa musu sannan ta roki gafararsu domin ita yanzu rayuwarsu ba irin tata bace...


Cike da takaici Daddy yayi daya sanin haďa zuri'a da jinin Ma'u,

Wani irin huci ya furzar na bakin cikin irin halayyarsu,
mugunta ma har ga kanka sai kayi ta domin biyan bukata,
tirrr da dabiyar karnuka irin tasu Goggo ya faďi da kausassar murya...




Ke Badariyya...
,tashi maza ki fitar min a gi----


Jiniyar da sukaji ne ya sanya shi yin shuru domin sauraron daga inda jiniyar ke fitowa....


A take Yareemah Suhail ya durkusawa Hafeez kamar zai bauta mishi,

Allah yaja ran sarki mai jiran gado,

Abubuwa masu Muhimmanci Allah ke yinsu,

Mu aron mulki mukayi ta karfin tsiya,

kai kuwa Allah ne ya baka shi daga fadar shi,
wannan mulkin rubutacce ne a cikin allon Allah,
Allah ya baka nasara...

Buďe baki Hafeez yayi ya koma can baya,

da sauri Husnah ta riko hannunshi suka koma daki dan a ganinsu wata cutar yarima suhail zaiyi mishi.....






Mrs Tijjani Shattimah......
[12/06 7:23 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 7⃣1⃣
By *Aysha Ya'u kurah*







Cikin azama ta fara tattara langunan gabanta tana turasu cikin lokar katakon dake kofar dakin da aka bata,


"Badariyya ina naman da kande tace mu raba?
Kinga bana son tashin hankali,
ki fito dashi kawai mu raba,
wannan ma ai keta ce,


Sharce zufar da ke goshinta tayi ta kalli Marakisiyya tace
"Na cinye,
na bawa Tanimu da jazuli suma sunci,
kinga sunci kason uwarsu,
ni nawa 'yayan ko kamshi basu ji ba,



"Marakisiyya ina namanmu?
gashi can su Hannafi suna ci suna mana gwalo,
"Tanimu ďan Marakisiyya na farko ya faďi cike da dacin rai..

Maida kallonta gurin Badariyya tayi zuciyarta na k'una ta kasa yi mata magana sai nuni da tayi mata da hannu na
"kina jin abin da Tanimu yake faďi?

Tsaki mai karfi Badariyya taja ta wuce daki tana goge fuska da zaninta da yasha jiki,

Tana sanya kafarta cikin dakin taji an shako wuyanta harda haďawa da labulen tsummar dake kofar dakin,

Marakisiyya bata jirayi komai ba ta fara naushin bakin Badariyya tana faďin ina naman mu yake?wallahi in baki fito da naman nan ba sai na yagi na jikinki ya zame mana naman shekarar da bamu ci ba,

"Ke ni fa a yanzu saidai a mutu a gidannan,
dan wallahi kiriss ya rage in fara maita,
in banda mugunta naman da kika san sai shekara muke cinshi shine kika haďa da nawa da naki kika cinye saboda haďama,
Wallahi ko ki fito min da naman nan ko inyi fata fata da naman cinyarki,
yin karar suya bazai min wahala ba ko Tanimu yayo...


Yadda take maganar tana haki idanuwanta yayi jawur ya sanya Badariyya tsurewa,

"Tabbas Marakisiyya ta fara maita,
cikin muryar azaba jini faca faca da bakinta tace
"Sakeni zan baki!

Sake shake ta Marakisiyya tayi tace
"Ai saidai muje tare,
wallahi babu inda zaki ke daya, matsiyaciyya mai bakin hali,


Kuka Badariyya ta fashe dashi ta fara tafiya har ta isa gurin da ta boye naman,
tana sa hannunta taji an wafce langar harda hannunta sannan ta hankadata jikin katakon,

kusar dake jiki ta caki tsakiyar goshin Badar,
Wani irin ihu ta tsala wanda ya tattaro hankalin mutanen cikin yalwataciyyar bukkar sarkin,

Kande ce ta isa gareta ta toshe mata gurin jinin sannan ta shige da ita daki,
ita kuwa Marakisiyya ko a jikinta, namanta ta tusa a gaba suna yaga ita da 'yayanta.....


******


Nayi Nadama,
Na tuba,
wallahi na yarda zan zauna da kai,
yanzu 'yayana biyu da kai, Hannafi, da Suwidi,
ina zan tafi in barsu?
dan Allah ka yenta ni kamar yadda ka yanta gimbiya Sailuba,
na saduda zan zauna dakai, wahalar da nake sha a gidannan ta isheni,
ka taimakeni ka kaini inga iyayena ko sau ďaya ne takk,
nayi alkawarin bazan bujire maka ba duk abin da kake so shi zanyi----

ta karashe cikin matsanancin kuka.. garin maganin da aka sa mata a goshi ya murmuso mata a ido...





Dariya yayi sosai yace
"Wuya makarantar kare,
To ai dama laifinki ne da kika biye wa mai son zuciya irin Marakisiyya,
da a yadda aka kawoki gidannan kinyi min ladabi da babu abinda zai hanaki fin Sailuba fada a guri na,
to sai kika nuna kinfi Marakisiyya rashin imani,
shiyasa na nuna muku karfina a kanku,
na sanya ku kuka zamto tamkar karnuka,
tunda kin gane kanki yanzu to baki da matsala,
zan kaiki kiga yan uwanki nan bada jimawa ba,
amma sai naga kamun ludayin nadamarki,
in har kika canza hali gaba daya to babu wanda zai kaiki jin dadi duk cikin matana domin na fi kaunar kasancewa dake....

Janyota jikinshi yayi cikin wani irin siga ta sha'awa,
karfin turaren dake tashi a jikinshi ya kusa zautata saboda tsabar rashin dadi,
wasu zafafan hawayen dana sani ne ya dinga kwaranya a cikin idanuwanta,
dana sanin rashin kasantuwarta mutuniyar kirki har halayyarta da kaddararta ta sanya wannan masifar afkuwa da ita,
tunano irin rashin mutuncin da ta dinga yi ma yan uwanta musamman Nadeeyah da Musaddiq tayi,
da ace lokaci zai sake bata dama, da ta kaunaci har mai gadin gidansu,
da ta nuna ma yan uwanta kauna domin tana tsananin kewar su...


Ta sha wahalar da ko makiyinta bata fatan yasha,
mace kamar ita ace bata da zanin kirki da take daurawa,
dakin baccinta babu ko katifar da zata sanya hakarkarinta,
ba'a ma maganar hasken lantarki domin bata taba ganinshi a gidan ba,
duk yadda mai karatu ke auno kuncin rayuwar da Badariyya take ciki ya wuce haka domin kunci ne na mutane marasa galihu da 'yancin kai,
'ya'yanta da ta samesu ta hanyar tursasawa, tamkar almajirai saboda tsabar wahala da suke sha,
tasan tabbas in akayi bincikenta abin da za'a fara cin karo dashi a tare da ita shine infection,
sannan wasu ciwukan su biyo baya,

Runtse idonta tayi saboda azabar da takesha na cakalkalata da yakeyi,
saida yayi fin awa yana abu daya,
bayan ya gama yayi mata albishir da indai tana san ganin yan uwanta to ta cigaba da kasancewa mai biyayya da dauriya a gareshi kamar yadda ta kasance mishi a yau......





*Canada*


Ohhh..
ya Allah Mukhtar ai sai ka karyani,
ajiye remote din hannunta tayi ta karbi cupin da ya bata,

"Mashaa Allah,
nasan jika na is the best,
Allah ya albarkaci rayuwarka..
ta karashe haďe da sumbatarshi...


"Barka da gida Aunty!!

Nadeeyah ta faďi a ďan russune,

"Barka dai ta amsa babu yabo babu fallasa,
ta cigaba da yi ma junior wasa..



Ciki Nadeeyah ta wuce ba tare da ta damu da yadda Anty Saude ta amsa mata gaisuwarta ba,
ko wacce uwa hakan zatayi in dai danta ya fuskanci abunda Taheer ya fuskanta,
soyayyar da take nunawa Junior shi yake sanya zuciyarta sanyi a duk lokacin da ta ga irin halin ko in kulan da Anty sauden ke nuna mata,
kula babu wacce bata yi mashi,
ita ko me zata ce mata banda godiya,
sannan tana rokon Allah ya kawo lokacin da zata saka musu da mafificin alkhairin da sukayi mata.....





"Me zaka ci?, noodles ko peppersoup?

Kallon Taheer Junior yayi yace Daddy me zamu ci?

A'a my dear ba cin abinci yanzu sai anyi wanka,
jeka Mamma tayi maka wanka kazo muci duk abinda kake so,


"Kallon Anty Saude yayi cikin fuskar mamaki yace
"Momma ba kince ni zan dinga yin shower da kaina ba,
ni dai ba wanda zai min wanka,


"Yess big boy jeka toilet dina kayi wankanka,
amma fa kar kayi min barna,

kuma ka wanke kanka da kyau kaji?
Gyaďa kai yayi ya nufi bayin da gudu bayan ya watsar da dukka kayanshi a parlon.....




"Momma...
wai meyasa har yan----

look Tee,

Dan Allah kar mu fara wannan zancen,
go and get urself ready kazo kaci abinci,
kayi abinda kake so na kyaleka,,
ka barni inyi abinda nakeso...


Mun fara magana dakai akan Amal,
zan kira Mus'ab anjima in sha----

Bai karasa jin abinda zata ce ba ya mike yayi hanyar dakinshi...


Taheer lokaci yayi da bazan zauna in zuba maka ido ba,

wallahi tallahi cikin kwanakin nan zakayi aure....

Dariya sosai yayi saboda yadda ta daga murya,
bai waigo ya kalleta ba ya shige dakinshi yana cigaba da dariyar da yasan zuwar mishi kawai tayi babu shiri,


Gefen katafaran gadonshi ya zauna haďe da dafe kanshi,

"Ta ina zai fara sanarwa da Momma abinda ke ranshi,
yasani sarai ko za'a haďi sama da kasa bazata yarda ya auri Nadeeyah ba,
da yaya ma ta yarda da zamanta a gidan,
saida ta gindaya mishi tsauraran sharudda akan Nadeeyah kafin har ta yarda da zamanta,


Haihuwar junior da tayi ita ta sake samarwa da mahaifiyarshi kwanciyar hankali domin Allah ya daura mata son yaron...



kishingida yayi yana tunano baya lokacin da ya fidda rai da samun muradin ranshi,

Sai gashi kaddara ta haďasu a lokacin da bai taba zato ba........






*Tuna baya....*





Suna isa asibitin ya fito daga motar dakyar,
Mutumin da ya sasu a mota ya taimaka mishi suka shiga da ita saboda yanayinshi na buguwa da kuma jini da daketa zuba a kanshi,
da sauri nurses suka iso garesu suka sanyata akan gado,


Dishidishi Taheer yake gani saboda karfinshi ya kusa karewa,
bayan nurses din yabi har zuwa kofar dakin emergency,
suna gab da shiga ganinshi ya sauka a kan Nadeeyah da gefen fuskarta ya baci da jini,
a firgice ya karasa kusa da gadon ya fara kiran sunanta yana kuka sosai,

Dakyar mutumin da ya rakosu ya rabashi da gadon ya zaunar dashi a kan kujera,
karfafa jikinshi yayi ya dauko wayarshi ya shiga neman number Anty Raliya,
dakyar ya iya ganin number dan hankalinshi ya fara gushewa,


Ya kira wayar yafi sau goma bata daga ba,
cikin neman mafita yayi kiran uncle Kamal,
ringing biyu tayi ya dauka,


Cikin wahalalliyar murya yace mishi yaje gidan Alh Mukhtar kyari ya sanar dashi hatsarin da sukayi,

Rashin sa'a akayi Kamal yace mishi yana hanyar dawowa daga Abuja, amma gobe da sassafe zai safe zaije gidan ya sanar musu,
sunan asibitin da suke ya faďa mishi sannan ya kashe wayar dan gaba ďaya jijiyoyin kanshi sun daina aiki,


Ba karamin tashin hankali kamal ya shiga ba na jin muryar Taheer,

yana kashe wayar ya nemi *Comr-David* ya sanar mishi da halin da Taheer yake ciki sannan yasashi zuwa asibitin dan ganin halin da yake ciki...


Kafin zuwan David har Taheer ya faďi unconscious,
cikin kankanin lokaci shima aka bashi gado...


Washe gari Yadda David ya ga jikin na Taheer ya tabbatarwa da Kamal suna cikin mayuwacin hali, ya kamata ya sanarwa Anty Saude saboda gudun bacin rana,



Hankali a tashe Kamal ya a jiye wayar ya sake kallon masu gadin kofar gidan da sukayi bake bake suka hanashi shiga,

Rokonsu ya shiga yi akan suje su fadama me gidan hatsari yarshi tayi,
cikin halin ko in kula suka daka mishi tsawa suka tabbatar mishi babu kowa a cikin gidan...

Rasa abin yi yayi gashi Taheer bai san inda yake ba,
motarshi ya shiga ya koma gida ya soma shirin tafiya Lagos......





Yana isa bai bata lokaci ba ya kira Anty Saude ya sanar da ita,
rikitashi tayi da kukanta tace maza ya shirya su taho nan zaifi samun kula,
bai mata musu ba ya koma dakin da Taheer yake...



Doctorn da take kula dasu doctor Marliyya batayi jayayya da Kamal ba tayi yan rubuce rubucenta ta bashi sannan ta shawarceshi da ya bari su farfado saboda komai ya tafi mishi cikin sauki,
ta dade tana faďa mishi irin Halin da Nadeeyah take ciki,
sannan ta faďa mishi tana dauke da karamin ciki,
barinta ta farfaďo yana da matukar muhimmaci,


Na'am yayi da zancenta ya gaza furta mata ba tare da Nadeeyah zasu tafi ba saboda kar taga rashin hankali da kyautawarsu.....





Nadeeyah...
Nadeeyah...

Na-dee-yaaàaa....

ya furta da ďan karfi,
da hanzari Kamal da David suka shigo dakin,

Kwanta Uncle T,
baka da karfi a jikinka,

Alhamdulillah tunda ka farfaďo, dama na riga na yanki ticket 8pm jirgin mu zai tashi,

"Where is Nadeeyah Kamal?
Ya tambaya dakyar yana dafe kanshi..

She will be alright Tee,
lafiyarka itace abin bukatarmu,

i went to der house ance babu kowa,
in na kaika gurin Anty safely zan dawo in sake komawa gurin yan uwanta,
i promise u i will neva lv her alone Taheer,
trust mee,


Runtse ido Taheer yayi hawayen dake boye a idonshi ya sauka a kumatunshi..






"Ba babanmu daya ba,
iyayenta sun rasu shine Daddynmu ya daukota ya dawo da ita gidanmu...


"Gara kai Uncle,
kana ganin Mahaifiyarka,
ni fa bani da dukka,
maraici ya kangeni gaba da baya, bamu da kowaaaaa....



Mikewa yayi dakyar bayan ya gama tunano kadan da ya sani daga labarin Nadeeyah...

Cannular dake hannunshi ya cire ya fara tafiya dakyar zuwa Dakin da Nadeeyah take Kamal da David na binshi a baya...


Ganinta da oxygen ya sanyashi zaman dirshan a gaban gadonta,
kuka ya shiga rerowa mai sosa zuciya wanda komin rashin imaninka sai ka tausaya mishi,


Dan Allah karki mutu Nadeeyah,

Karki mutu ki barni da guilt din kashe abinda zuciyata tafi kauna,

Dan Allah ki tashi...


"Zata tashi ranka ya daďe,
wata nurse ta faďa mishi cike da tausayawa,

"Yaushe?
Yaushe zata tashi?,
Dan Allah ku tasheta----


"Calm down Taheer,
tunda suka ce zata tashi she will be fine,
ka tashi mu tafi,
cikin raďa Kamal ke maganar,


Wata gigitacciyar tsawa Taheer ya dakawa Kamal wacce ta sanya kanshi juyawa ya tafi tagaga,


Tsugunawa Kamal yayi ya rukoshi yace
"Meyasa kakeson wasa da rayuwarka, why Tee?


Plss Kamal kasan yadda zakayi mu tafi tare da Nadeeyah,
i will call her Aunt,
in taji sauki zan dawo da ita, nasan ba karamin abu bane ya fito da ita da daddare da akwatinta,

plsss Kamal,


Yadda yayi maganar yana ambaliyar hawaye ya karya zuciyar Kamal,

"Karka damu in shaa Allah zamuje da David muyi mata duk abin da ya dace...


Nurse din dake tsaye a kansu tace "ku samu Dr Marli,
she will help alot da report dinta, ba shine mijinta ba?

N---

Yess nine yayi saurin katse Kamal,
fine biyoni muje,
in shaa Allahu ko gobe zaku gama mata komai,


Taimaka ma Taheer sukayi ya koma daki tayi mishi allurai sannan suka wuce office din Doctor.......





A daren da zasu tafi a daren Nadeeyah ta farfado,
ba karamin farin ciki Kamal yayi ba dan yanzu kam zasu san inda wani nata yake dan wayar Taheer tun daren ranar basu sake ganinta ba...




Da matsanancin kuka ta farka amma ta gaza furta komai dan daga ta buďe idonta zata maida ta rufe,
hawaye ne kaďai bai yanke mata,
ga azabar ciwo da take ji a hakarkarinta da hannunta,
babu irin tambayar da Kamal baiyi mata ba taki kulashi sai ma kallo kawai da take binshi dashi,


Dr Marliyya ce ta hanashi matsa mata domin gudun kar wani abu ya sameta,
badan yaso ba ya kyaleta har suka fara shirin tafiya airport a motar asibitin.....




****

Satin Taheer ďaya ya warke sosai kamar bai taba ciwo ba,
saidai ita Nadeeyah kamar lokacin ciwon ya sameta domin ta jikkata sosai a jikinta,
Sau huďu Kamal na zuwa gidan Alh Mukhtar sai ya samu a rufe,
karshe karya yayi ma Taheer yace mishi sun bar kasar kwata kwata,
sannan Number Raliya sam basa samu,
haka gidanta sau uku mai gadin gidansu na zuwa bai samunta..


Da haka Taheer ya hakura ya maida hankalinshi kan nemawa Nadeeyah lafiya,
duk wadannan abubuwan da yakeyi yana yinsu ne kawai dan Allah da kuma wani abu da yake ji a cikin jininshi game da Nadeeyah,
amma bawai dan ta dawo mishi ba,
tunda yaji labarin tana da ciki yasan lallai Nadeeyah tayi mishi nisan da bazai taba kamo ta ba,
yasan duk inda mijinta yake yana nan yana nemanta,
ya dauki alwashin sai ta warke sarai sannan zai maida ta gidan mijinta domin shine silar ciwonta...






Watanta uku ta fara tafiya kaďan kaďan da taimakon su Amal da Aman domin Taheer ko rabar kusa da ita bayayi,
shidai burinshi ta warke sosai,
a kullum in ya tambayeta number wanda zata kira sai dai ta fashe mishi da kuka,
samm bata da number Hafeez da shi zata bayar domin tasan yana can cikin tashin hankali,
number Hilal ma in tayi yunkurin kawota kanta sai ta manta domin gargadin da su Raudha sukayi mata na su ba danginta bane..



wahalar da take sha kashi biyu ce,
ga ta rabuwa da Musaddiq wacce tayi mata kiki kaka a cikin zuciya, ga kuma ta azabar ciwo wanda take tunanin babu ranar warkewa....





Cikinta na wata takwas da kwanaki ta warke sarai har tana iya hawa da sauka,
babu wanda baiyi farin ciki ba a cikinsu,


Anty Saude kula sosai take bata domin bata san wacece ita ba a lokacin,
duk tunaninta wata ce daban wacce danta ya bige da mota yake taimaka mata...




*Nadeeyah....*

Ajiye ice cream din da take sha tayi tace
"Na'am uncle,

kujerar da ke fuskantar gadon da take ita ya zauna yace
"Ina son yau mu kai karshen komai,
kinga lafiya ta gama samuwa a gareki,
ki faďa min inda yan uwanki da mijinki suke dan in maida ki,
nasan yanzu hankalinsu na nan a tashe,
a yanzu na daukeki tamkar kanwata ta jini, babu zancen soyayya a tsakaninmu..
bazan so inga wani naki ya cutu saboda ni ba,

Dan Allah ki faďa min inda suke domin mu samu mu maida ke hankalinsu ya kwanta muma namu ya kwanta...




Tunda ya fara maganar take kuka,


"Kuka bazaiyi mana magani ba,
ki faďamin matsalarki,
in zan iya inyi miki maganinta,
nasan bani da hurumin sanin damuwarki,
dan Allah ki faďa min ko zan samu sukuni....



"Ya sakeni,
Mijina ya sakeni,
sun ce kar in sake zuwa inda suke,
sunce bani da asali uncle..
bani da number wayar yayana,
yana zaune a gombe,
nasan shi kaďai ne yake cikin damuwa,
sai Papy, sai kanwata Zainab....


Rashin asali na bazai barni in zauna cikin masu asali ba,
nasan mahaifina mutumin kirki ne,
ba barawo bane kamar yadda su---ka fadaaa....
runtse idonta tayi saboda yadda taji wani irin ciwo a bayanta...



Share hawaye Taheer yayi bayan ya dawo daga shock din labarin sakin da ta bashi..

Mikewa yayi saboda yadda yaga tana cije baki,
Subhanallah, lafy?

Ya faďi da karfi bayan ya isa gurinta,

mararta ta rike tana kokarin mikewa ta kasa,


"Momm----
gani nan Tee,
gani nan, ina jinku,
duk abinda kuke faďi inaji,
ashe dama itace Nadeeyar da ta yaudareka?

"Momma plss help her,
in muka dawo gida zamuyi maganar nan,

kinsan sunce kar mu bari tayi labour,
c.s zasuyi mata,

hararashi tayi ta kamo Nadeeyah domin tasan ciwon nakuda bazata taba barinta cikinshi ba,


Please Login or Register in order to submit comment