Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake ciki ga kuma tausayin Taheer  wanda ya sallamar da dukkan hope dinshi a kanta,
tsaki tayi a hankali ta ture indomien gefe dan dama cinta takeyi badan daďi ba sai dan yunwar dake neman yi mata illah...

"Nadeeyah in kin gama Daddy yace kizo..

kafin ta juyo ta ba Husnah amsa har ta bacewa ganinta,
ruwa kaďan ta kurba ta gyara gyalen dake daure a kanta ta nufi parlon kamar wacce kwai ya fashewa a ciki...




Cikin dariyar karfin hali Daddy yace

"Amarya taho nan ki zauna mana,

Cike da karyewar zuciya ta tsuguna can nesa dashi tace

"Ina kwana Daddy,

" Lafiya kalau Nadeeyah,
ke kuma haka akeyi,
kullum ina son muyi magana sai kiyi bacci baki jirana in dawo,
baki kyauta min ba,
gashi yau saura kwana huďu kadai ki tafi,
yanzu dai kije ki shirya kizo muje ki zabi abinda kike so..



Hawayen dake kwance cikin fararen idonta ne suka sauko kan kumatunta,

"Daddy bana bukatar komai ta faďi cikin rawar murya..

Cike da zolaya yace
"Nasani Nadeeyah,
amma ai a matsayina na uba duk da ban kai matsayin kuďin su Taheer ba ai bana kai ki haka ba, sai a goranta mana,
tashi maza ki shirya..

"Sautin kukanta ne ya fara karaďe cikin falon wanda ya dauki hankalin Hilal dake saukowa kasa..

"A'a Kuka kuma Nadeeyah,
ki daina kuka dan Allah kar ki karya min zuciya,
wasa nake miki,
tashi kije ciki zamuje da Reemah..

"Dan Allah Daddy kuyi hakuri, wallahi na rasa yadda zanyi,
ina cikin tsaka mai wuya.....
ta karashe cikin tsananin kuka..

Tasowa Daddy yayi ya isa gareta, a hankali ya dagota ya shiga share mata hawaye,

"Allah shi zai fidda ki,
nasani baki da laifi dan baki isa ki ketare kaddararki ba,
duk abinda Allah ya rubuta akanki babu wanda ya isa ya gogeshi,

Musaddiq ko baki aureshi ba yana nan dai a matsayin jininki babu wanda ya isa ya raba,
rabuwa da Taheer kuma samm babu adalci domin bazan fifita son ďana akan na wani ba,
shima ďa ne,
kuma yana da zuciya a kirjinshi,
ki kwantar da hankalinki ki barwa Allah lamuranki shi ne mai saukakawa...

Ajiyar zuciya tayi mai karfi zatayi magana muryar Junior ya katseta..

A tare suka waigo suka kalleshi Daddy ya saki murmushi haďe da cewa
"Aboki, kaine a gidan da safe?
Ina Daddynka?

Jin ya ambaci sunan Daddy yasa shi waigawa dan tare suka tako har kofar parlon,

"Daddy,
Daddy..
ya fara kwala kiran sunan Taheer wanda ya riga yayi nisa,
"Dama kawoshi yayi ya zauna a gidan dan ya saba dasu,
sai kuma abinda kunnuwanshi suka jiye mishi abin da ya sanyashi cikin tsananin tausayi da kuma sake ganin girma da kimar Daddy..




Kuka sosai Junior ya farayi dan ya fito baiga motar Taheer ba,

Hilal da ya gama sauraron su Daddy shi ya fito wajen yana lallabashi haďe da yi mishi alkawarin maidashi in yayi wanka,
da kyar ya yarda amma har lokacin bai bar kuka ba...



Cike da kuluwa Nadeeyah ta kama hannunshi ta nufi ďaki dashi tayi mishi tsawar da ya sake sanyashi cikin wani gigitaccen kuka,

"Tsanar da kikayi wa ubanshi ce ke neman shafarshi,
Husna ta faďi tana janyoshi jikinta,
ga mamakinta sai ya turata baya ya koma jikin Nadeeyah ya kankameta yana cigaba da kukan,

Kukanshi da kalaman Husnah su suka sake dugunzuma zuciyarta, nan take ta turashi gefe ta faďa bayi tana kuka mai sosa zuciya, tana jiyo ihun kukanshi yana faďin "bazai sake yin kuka ba Dan Allah ta buďe mishi kofa,
duk yadda Husna taso kamashi kasawa tayi haka Anty Reemah da Maleekah,
duk wanda ya tabashi sai ya turasu ya cigaba da ihun sunanta,

Hilal ne kaďai ya iya calming dinshi ya daukeshi suka fita daga dakin,


Sama suka nufa yana rarrashinshi haďe da yi mishi alkawura kala kala...

Gaban mudubin da babu glass suka samu Musaddiq zaune da towel a jikinshi alamun yanzu ya fito wanka..

a kunne Hilal ya raďawa Junior cewa
"Go nd say sorry to ur Twinny, kasan bashi da lafiya,
he will feel better in dai yaji sorry daga bakinka..

Da sauri ya sauka ya isa kusa dashi yace
"Sorry Twinny,
hw is body? Hope u are feeln better?

A hankali ya maida dubanshi gareshi ya tallabo fuskarshi yace "Yes twinny,
hw are u?

"Nt fine, Mamma shoutd at me nd she is crying..
ya faďi kamar zai sake yin wani kukan,, 

Raunanniyar zuciyarshi wacce ake lallabawa ta fara mishi zugi, nan take idanuwanshi saka kawo ruwa,
burinshi bai wuce ace in ya rufe idonshi ya farka ya ganshi a kabari ba,
ya tsani rayuwar gaba ďayanta,

Tunda ya taso a duniyar nan baisan mecece rayuwar duniya ba,
shiyasa ya ke kiran Nadeeyah da rayuwarshi baki ďaya,
itace duniyarshi,
Daddy ya kasa fahimtarshi,
kowa ya zuba ido yana ganin za'a rabashi da rayuwarshi..
hannun Hilal yaji a kafadarshi wanda ya sanya hawayen karasa saukowa kamar an ingizo su,

"Hilal babu wanda zai iya taimaka min a cikinku,
haka zaku zuba ido---
toshe mishi baki Hilal yayi yace

"Bamu isa mu shiga hurumin ubangiji ba Kyari,
ka fahimci hakan,
dan Allah kayi tawakkali,
kaddara babu yadda bata zuwarma bawa,

Rungume junior yayi saboda jin hannunshi yana share mishi hawaye,

"Please Hilal take care of my son bayan raina,
wallahi bazan rayu ba,

Dogon tsaki Hilal yaja haďe da raba junior da jikinshi yace
"Sai ka kashe kanka tunda rayuwarka a hannunka take..

Muje kasa kaji takwara,
ur twinny is crazy ya karashe haďe da jan hannun junior sukayi waje...



Maida kai Musaddiq yayi ya kwanta yana rusa kukan da tunda aka haifeshi bai tunanin ya taba yinshi,
duk yadda yaso yin karfi da zuciyarshi kamar yadda Daddy ya bukata ya kasa saboda zuciyar ta raunana matuka da kaunar Nadeeyah,

Ya Allah Ka sàssauta min,
haka ya dinga faďi yana juyi akan gadonshi....



*******
Alkawari dai Kyari,
gashi har karfe biyar baka ba labarinka,

Yadda take maganar ya sanya Shareefah kureta da ido domin ta dade bata ga yar uwarta cikin wannan yanayin ba,

"Kiyi hakuri Saudatu,
in shaa Allahu zanzo zuwa anjima,
ina nan sane ban manta ba,
Daddy ya bata amsa yana mai duban agogon hannunshi domin ganin lokaci...

"To ina nan dai ina zuba ido, nasan dai baka saba alkawari bansani ba ko ka koya kasan shekarun da yawa,

Dariya suka saki a tare saboda yasan tabbas tsokanarshi takeyi,

"In ma na koya bazan so in gwada miki shi ba,
domin an daďe ba'a hadu ba, ya kamata a barwa juna memories masu daďi bayan rabuwa,
ina nan zuwa,
just a second plss inada baki zan kiraki,
bai jira jin amsarta ba ya kashe wayar ya cigaba da duba abubuwan da aka kawo mishi...




*BAYAN RABUWA*

Shi ta dinga maimaitawa a cikin ranta,
yana tunanin rabuwa da ita kenan bayan shekarun da suka dauka basuga juna ba,
har yanzu Mukhtar baya tunaninta kamar yadda tayi a baya da kuma yanzu da ganinshi ya tado mata matacciyar soyayyarshi....


*Flash back a gurguje*

_Shekaru da dama da suka wuce Allah ya jarabci Anty Saude da Soyayyar abokin makocinsu kuma malaminta wanda yake mata lesson Uncle Abubakar, a duk lokacin da uncle Abu yazo yi mata lesson Kyari kan je gidansu yayi ta tsokanarta musamman in akazo kan mathematics, tun abun na bata haushi har ya rikiďe ya koma birgeta, in yana tsokanarta sai ta biye mishi suyi tayi har lokacin tashi lesson yayi ba'a tabuka mata wani abun arziki ba, in Kyari yayi tafiya babu zancen karatu ta dinga damun uncle Abu kenan tana tambayarshi ranar da zai dawo, kasancewarsu dukkansu 'yayan masu kudin lokacin sai ya zamana tasu tazo daya musamman ta bangaren Anty Saude, ita duk a tunaninta soyayya ce ke kawo Kyari (kamar yadda taji uncle Abu na cewa) gurinta, bata san shakuwar da sukayi da Abubakar tun suna makaranta ita ce ta sanya ďaya baya barin daya ba, a ranar da ta yanke shawarar faďa mishi abinda ke ranta a ranar taji mummunan labari daga gareshi na haďuwa da wata yar makaranta wacce ya kwallafawa ran aurenta, cikin sanyin jiki ta tattara takardunta tace ma Uncle Abu bata da lafiya, bata tsaya duba kulawar da Kyari ke kokarin nunawa a gareta ba ta wuce cikin gida idanuwanta na zubar da hawaye, tasan tabbas kyari ya faďa cikin tarkon so domin a yadda ta kula baya son kula mata gashi da yawan kushesu tasan wannan din da ya gani ta dabance, a daren ranar taci kuka har ta gode Allah sannan ta roki Allah da ya kawo mata wanda zai aureta cikin gaggawa ko ta samu ta mance *Mukhtar Garba Kyari*..._

Washe gari da safe da taje gaida Mahaifinta  Alhaji Halliru Ďan Magarya, bayan sun gaisa yake tambayarta yaushe zasu fara jarabawa,
cike da damuwa ta amsa mishi da cewa
"Jibi in shaa Allah,
"Mashaa Allah Mamana,
Allah yasa ku rubuta alkhairi, yasa ku fito da sakamako mai kyau, tunda an kusa zana jarabawar karshe sai maganar aure,
shin kina da wanda kike so?
nasan dai bazaki rasa ba kar inyi miki katsalandan,

Kauda kanta gefe tayi dan bata so sam mahaifinta ya gane halin da take ciki tace
"A'a Pappa, duk wanda ka zabar min ina maraba dashi,

Cike da murna yace
"Mashaa Allah, shiyasa nake daďa sonki a cikin raina,
sai yanzu na fahimci dalilin da yasa Allah ya mallaka min ke kadai,
saboda yasan ke ďin daya ce tamkar da dubu,
Allah yayi miki albarka,
ki shirya gobe,
Haroun Yallo dan wazirin Agadez zaizo neman aurenki,
satin da ya wuce da naje Agadez na bawa mahaifinshi ke,
shi mazaunin nan ne, a nan yake kasuwancinshi,
Allah ya sanyawa haďin albarka,

Amsa mishi tayi da Ameen sannan ta tashi ta wuce ďaki tana kuka ririss....



Bayan tayi candy da sati biyu aka daura aurenta da Haroun,
da fari ta dan samu matsalar zama dashi saboda tunanin kyari da takewa son da bai san tanayi ba,
sai daga baya kyautatawar Haroun ta kashe boyayyar soyayyar cikin zuciyarta...


Ashe dai soyayyar ba mutuwa tayi ba,
ashe doguwar suma tayi,
wanda a yanzu ruwan soyayyar Daddy ya farfaďo da ita...


Ajiyar Zuciya tayi tace
"Wannan karan bazan rasaka ba Kyari,
koda zuciyarka bata sona zan koyar da ita yadda zatayi shi,
a yanzu na haďu da kai bayan na cire rai da sake yin wata soyayya bare har inyi aure,
haduwarmu dakai ta nuna min tabbas kai ďin nawa ne koda kuwa ba nawa bane ni kadai, rabuwa a tsakanin mu babu ita saidai mutuwa ka raba,
tana kaiwa nan ta tashi ta nufi daki dan sakeyin wani wankan....


Da ido Shareefah ta bita tana mata adduar samun abinda take so,
domin Allah ma yasan tayi hakurin rashin miji a gefenta, yadda ta damu da maganar Kyari ta tabbatar tana matukar sonshi, zata tayata da addu'a in alkhairi ne Allah ya tabbatar.....




Bayan isha'i Daddy yazo gidan, tarba mai kyau ya samu daga dukkansu harda Taheer wanda a yanzu yake matukar jin kunyar haďa ido dashi, kimarshi ta karu sosai a idonshi..


Bayan sun gama gaisawa Anty Saude ta cika gabanshi da abinci da sha,
zama tayi a gefenshi tana mishi hira yana cin abinci suna tuntsira dariyar tuna baya,
sosai sukayi hirarsu har Daddy yakai karfe goma bai san ya kai ba,
yayi matukar jin daďin hira da ita, zuciyarshi da tayi mishi nauyi ta rage saboda ta tuno mishi da memories ďin baya,
lokacin yana kan ganiyarshi, bashi da wani bacin rai sai tarin farin ciki musamman lokacin haďuwarshi da Suwaiba....



Rike murfin motar tayi bayan ta gama jin tambayarshi na
"Bayan biki zaki koma can canada ne?

Kallonshi takeyi cikin ido dan jinta takeyi kamar yar budurwar da ta fara tsayawa da saurayi tace

"In ka shirya komawa can me zai hana!

Dariya Daddy yayi yace
"Wato dai kin maidani joker, karfin ramawa ne bani dashi da kema kinsan bazaki sha ba,
dare na daďa yi bari in wuce,

Ina miki fatan alkhairi haďe da murnar samun suruka irin Nadeeyah,
Allah ya basu zaman lafiya...

"Ameen Anty Saude tace haďe da rufe mishi kofar cike da tausayawa halin da ďanshi yake ciki,
ya zatayi ta iya yin wannan taimakon?
Ya zatayi da zuciyar tata ďan in ya rasa Nadeeyah,
Addu'a ita kadai ce mafita a garesu domin Allah shine kadai mai sassautawa....



Bayan tafiyarshi da awa ďaya ta tura mishi text din godiya da ban gajiya sannan tace
"Akwai muhimmin abun da zan faďa maka,
in shaa Allahu bayan biki komai zai ziyarci ji da ganinka,
have a nice dream *Joker* ...


Dariyar rashin shiri Daddy yayi ya kashe wutar dakin da Musaddiq yake ya fita daga dakin, saida yayi shirin kwanciya sannan ya tura mata cewa...

*Same Sauden Himma, Amaryar gandiroba...*

Dariya sosai tayi na tuno sunan Himma,, gandiroban da ya like mata lokacin yarintarta,
ashe bai manta ba ta furta a hankali cike da nishaďi,

*Soyayya ruwan zuma, ita soyayya babu ruwanta da tsufan mutum, in ta kama ka dole ta zautaka*.....





Good morning bride,
Maleekah ta faďi tana haďawa Little Nadeeyah tea,

Rau Rau Nadeeyah tayi da idonta haďe da kwabe baki zatayi kuka,

"Hey, ba ruwana fa,
kiyi saving kukan nan zuwa anjima ki sakarwa Abbu shi,
kinsan yau zasu zo bikin unknown jika... ta karashe cike da zolaya,
kafaďunta Nadeeyah ta daka haďe da haďiye da kukan dake shirin zubo mata,

Dariya Maleekah tayi tace
"Let it flow beb,
kinsan in daďi yayi maka yawa hawaye kansu dadin fita sukeji,

My Inlaw da ciwo ke da kuka,
nd for once baki taba tunanin zuwa dubashi ba,
haba Nadeeyah,
if nt for him sai kiyi for his child, kinsan duk inda kikaje that child will always connect u saboda ya riga ya haďaku...


Share hawaye Nadeeyah tayi ta juya ma Maleekah baya,
zancen zuci takeyi wasu hawayen na sake bulbulowa,
rabon da tasa shi a idonta tun ranar mutuwar Goggo da ta shiga ďakin dan duba jikinshi lokacin yana bacci,
bata san abun da zai sake sawa ya ganta domin bata san yi mishi fami akan abun da take da yakinin yana yunkurin mantawa dashi,
kwana uku ya rage ta zama mallakin wani,
runtse idonta tayi saboda hangota cikin wata sabuwar rayuwa,
rayuwa ba tare da Mussadiq ba,
wanda ya fara koyar da ita soyayya,
wanda ya shayar da ita gubar soyayyar da ya illata ruhinta...



"Go nd see him for the last tym Nadeeyah,
atleast zai samu sukunin cewa kin damu dashi, kaddara ce zata rabaku, plsss Nadeeyah..
ta karashe haďe da hada hannayenta guri ďaya tana rokonta... duk wadannan maganganun cikin harcen turanci take yinsu...



Share hawaye Nadeeyah tayi da Hijab dinta ta fara tafiya dan bin umarnin yar uwarta,
tana zuwa kofar dakin taji kafarta ta fara rawa,
dakyar ta iya murďa kofar tana addu'ar Allah yasa yana bacci,

Ajiyar zuciya tayi bayan ta gansu kwance suna bacci shi da junior da fushi ya hanashi kwana a gurinta,
shagala tayi cikin kallonsu tanajin wata irin nutsuwa na saukar mata a curarrar zuciyarta,
ko ba komai hankalinta ya kwanta tunda Junior ya saki jiki da mahaifinshi,
ko a yanzu tasan Musaddiq zai samu saukin kaso 50 cikin ďari...

Cikin sanďa ta isa gurin gadon dan gyarawa Junior hannu dan gab yake da famawa Musaddiq ciwon dake hannunshi wanda hakan zaiyi sanadiyyar katsewar baccin da ta tabbatar yana jin dadinsa,
da dabara ta gyara mishi taji ya rikota yana sambatun
"Daddy am very angry with u, i will nt talk to u ever again,

Dariya tayi haďe da sumbatar kumatunshi ta zame hannunta cikin nashi,
bargon dake jikinsu ta gyara musu ta shafa kan Junior ta dago da niyyar yin hanyar waje,
kamar gizo haka taga idon Musaddiq a buďe,
sake juyowa tayi ta kalleshi tagansu a rufe,
ajiyar zuciya tayi ta fara tafiya dan zuwa kofar da zata sadata da waje,

"Nadeeyah...

Taji ya furta a hankali wanda ya sanya hantar cikinta kadawa,
tsayawa tayi cakk a gurin ba tare da ta amsa ko ta waigo ta kalleshi ba..

jin har minti uku baiyi magana ba yasata juyawa dan ganin halin da yake ciki,
wannan karan a juye yake idanuwan nan a rufe wani sabon bacci ne ma yayi gaba dashi wanda daga gani kasan yana cikin mayen magani ne,
da sauri ta murďa kofar ta fita saboda kwalla da taji ta taru a idonta,
wannan wacce iriyar zazzafar jarabawa ce,
ya Allah ka kawo mana mafita baki dayanmu dan alfarmar annabi Muhammad s.a.w.....



Gidan Alhaji Mukhtar ya zama tamkar gidan zaman makoki, kamar babu wata hidima da za'ayi a cikinsa nan da kwana biyu,
Anty Reemah dasu Raudha sune kadai ke hidimarsu bisa ga umurnin Daddy,
sai kuma Mummy da a yanzu takan samu shigowa duba jikin Musaddiq,
duk da bata samun koda gaisawa da Daddy hakan yayi mata daďi tunda ya yafe mata kuma ya yafewa 'yayanshi yana sakar musu yanzu,
a yanzu bata da burin da ya wuce taga rayuwar Musaddiq ta inganta,
ta rasa kalmar da zata roki Nadeeyah dashi ta yarda da auren ďanta wanda ta zama sila a rabuwarsu,
gashi abun da tayi yayi sanadiyyar sanya shi cikin tsakiyar rayuwa da mutuwa...



A yau ma kamar kullum bayan ta gama gyara ďakin Goggo inda take kwana ta shirya tsaff dan tafiya dubo Musaddiq sannan ta zauna ayi kamun Nadeeyah da ita,
tana rufe kofa ta jiyo muryar Badariyya wacce a yanzu Yareemah Suhail ke fitowa da ita ya kawo ta har gida tun dawowar Nadeeyah,,
kwancen kayan da su Husna suka bata shi ta sanya tayi kyau abunta, sannan su suwidi suma sunyi kyansu dan a yanzu suna samun sake da kuma abinci wanda duk tazo sai yan uwa sun sai mata,


"A'a Badariyyah kece a gidan, to juya muje ki duba jikin Musaddiq daga nan ki jira ayi kamun Nadeeyah dake,
cike da damuwa ta juya suka fita suna tattauna damuwar da Musaddiq din ke ciki a sanadinsu, Badariyya a cikin ranta ta dau alwashin kebewa da Nadeeyah ta faďa mata abubuwan da tayi wanda ya rabasu, babu mamaki taji tausayinshi in tasan baya cikin hayyacinsa sanda yayi sakin....



Bayan ta gama sauraron kalaman Badariyya wanda takeyinsu cike da nadama tace

"Badariyya abun da kukayi bai isa ya raba mu ba,
tunda kika ga mun rabu to tabbas Allah ya rubuta rabuwar tamu ne a lokacin,
sannan a yanzu in na ki uncle Taheer shi munsan halin da zai shiga,
dan Allah ku fahimceni,
ni kadai nasan halin da nake ciki, ku tayani addu'a nasan komai zai daidaita da yardar Allah...

Share hawaye Badariyya tayi tace "Zamu tayaki, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi....




Karfe huďu da yan mintuna Nadeeyah ta shirya cikin wani lace mai kyau da tsada cikin kayan da Taheer ya dinka mata, Anty Raly ke tsaye a kanta tana gyara mata kwalliyarta haďe da yi mata ďauri,
wata farar alkyabba mai adon yellow ta dauko ta daura mata a kanta wanda hakan ya sake fitar da kayatuwar da amaryar tayi, jan lallen da akayi mata ya rinu sosai ya koma dark maroon hakan ba karamin sake fitar da suffar yatsunta yayi ba,
zaunar da ita Anty Raly tayi tana jiyo sautin maganganu yan biki daga waje,,



Cike da masifa take shirya su Nour tana daka musu tsawar su tsaya ko ta zanesu,
a hankali Nadeeyah ta janyo hannun Abee tace
"Kawo in shiryashi Husna,


"Barshi.. kadai ta faďi haďe da janyo hannunshi ta sa mishi irin kayan dake jikin Hafeez,
oya a je ayi wasa, banda barna da bata jiki,
mikewa tayi da niyyar shiga bayi Nadeeyah ta riko hannunta,


"Husnah nasan ni mai laif---

Lokaci na kurewa Nadeeyah,
baki da laifin komai kaddararmu ce tazo a haka,
na kasa dai jin saukin zuciyata ne shiyasa har yanzun kika ganni haka,
with time in shaa Allah komai zai daidaita,
Husnah ta katseta fuskar nan murtuke tamkar wacce akayi ma mutuwa..
ganin Nadeeyah na kokarin sake magana yasata zame hannunta daga cikin nata ta faďa bayi,

wani irin kuka ne yazo musu a tare mai cin rai,
saida sukaci suka koshi sannan Husnah tayi wanka ta fito ta shirya da sauri sauri tayi waje....




Sai biyar da kusan rabi dangin Taheer suka zo sa lallen amarya, sai da suka biya kawayen amarya wacce Amal ce kaďai sai Raliya da ta shiga cikin zancen,
turaruka masu kamshin gaske suka karar a jikinta sauran yan uwansu na Agadez wadanda suka ji dadin ganin Nadeeyah da Hafeez suna rangaďa guďa,

kwaryar nono wacce suka kawo gidan kanta ta kai hamsin,
banda sauran gararrakin arziki da suka kawo,
sunci sun sha a gidan sosai dan komai nasu daban aka ware musu,
sai bayan Isha'i motocin da suka kawosu suka maida su....




A daddafe Musaddiq ya amsa gaisuwar Taheer wanda ke tsaye rike da danshi cikin tsadajjiyar shadda iri ďaya,
lallaba Junior ya shiga yi bayan ya fuskanci irin fushin da yakeyi dashi,
sannan kuma dan ya daukewa kanshi damuwar da ke cinshi tun kwana uku baya,
wani mugun tari yaji Musaddiq nayi wanda ya sanyashi sakin hannun Junior ya isa gareshi haďe da dauko ruwa yana faďin sannu, ga ruwa kasha,
runtse ido Musaddiq yayi haďe da kauda fuskarshi gefe,
ya riga ya gama yanke duk wani hukuncin da ya dace,
yasani a yanzu ganin gobe a gareshi nada matukar wahala, a yanzu ya sadaukar da komai yasan Nadeeyah da ďanshi bazasu taba yin kunci ba tunda suna tare da nagartaccen mutum irin Taheer wanda a haďuwarka dashi ta farko zata tabbatar da hakan komin kinka dashi,
dafe kanshi yayi da hannayenshi biyu saboda hawayen dake zubo mishi babu kakkautawa,

Mikewa Taheer yayi dukkan lakar jikinshi a sake ya kama hannun Junior suka sauka kasa,
a hanyar da zai sadasu da kofar fita ya haďu da Hilal da ya dawo daga rakiyar abokansu,
shima duk ya fukace ya fita hayyacinshi kamar shine mai ciwon,
"A'a yallabai har kun fito,
ya faďi yana mika mishi hannu,

"Eh dare nayi,
Allah ya bashi lafiya,
"Ameen Hilal ya amsa haďe cewa sai da safe mun gode,

"Allah ya tashemu lafiya Taheer yace yana mai saka kafarshi a waje,


A gurin motarshi suka tsaya ya kira number Nadeeyah wacce ke kan dadduma tana zubda kwallar da ta zame mata jiki,
a hankali ta ďauka cikin nuna bata cikin damuwa tace
"Uncle kun wuce ne?

"No muna waje,
muna san ganinki ne ya faďi wani ďaci na tokare makogaronshi,

Kara sassauta murya tayi tace "Gobe ne fa, daga gobe bazan sake barin gefenka ba, har sai ka gaji da ganina,
kayi hakuri plss,


Lumshe idanuwanshi yayi haďe da kallon sama a zuciyarshi yana rokon ubangiji sassauci akan wannan jarabawar,
*Tayi min tsauri da yawa* ya faďi ba tare da yasan ta fito ba, yana mai kwantar da kanshi kan murfin motar,


"Gani nan zuwa Uncle, in dai rashin ganina yayi maka tsauri, bakayi deserving shan wahala akaina ba,
bata jira amsarshi ba ta kashe wayar ta mike haďe da ninke dardumar tayi waje....
Duk abin nan da sukeyi a kunnen Raudha wacce ta fashe da kukan Nadama,
gashi dukkaninsu na suffering daga mugun halinsu,
babu wanda ya tsira,
shiyasa akace Sharri dan aike ne, in ka aikashi dawowa yakeyi ya shafi wanda bai nan sanda kayi aiken,
tayi nadama matuka a yanzu da itama bata ga tsuntsu,
domin ko ďuriyar 'yayanta bata ji, har gara Radiya ta roki Shamsu ta waya yayi mata alkawarin yana dawowa italy zaizo su sasanta,
ita fa, babu waya daga Abbati bare har tasan ko har yanzu yana nan da ragowar soyayyarta a cikin ranshi,

Addu'a ta shiga yi ba kakkautawa tana faďawa Allah damuwarta haďe da neman afuwarshi.....




Cike da kulawa ya kalleta yace "Kuka ko?
Wa ya sa kanwata kuka har ya koďar min da idanuwanta?

Rufe fuskarta tayi da hijab kukan da ke tokare a wuyanta ya fito da karfinshi,
barinta yayi tayi ma'ishi sannan yace

"Me kike so?
Tell me ko me kike so zanyi miki in dai zai saki daina zubar hawaye kullum,
Junior ya faďa min bakya cin abinci,
bakya kula dashi,
har ihu kike mishi,
tell me ur problem,
i promise to solve it for u komin wahalarshi...



Hannunshi ta riko a hankali tace "With u my problems are always solved,
bani da wata matsala Uncle, thanks for always being dere for me....



Sanya hannun yayi ya share mata hawayenta shima duk gabban jikinshi a karye suke a zuciyarshi yace

"I will also solve this for u, sadaukarwa a soyayya wani abu ne,
i will make sure u get wat u want,
a fili kuma cewa yayi ta kwantar da hankalinta zai cigaba da solving ko wace irin matsala tata har ranar da kasa zata rufe idonshi..



kwantar da fuskarta tayi kan tafukan hannunshi wasu sabbin hawayen na zuba a kansu..


"Bari in tashi Junior yazo

Please Login or Register in order to submit comment