Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta yiwu tana can tana kulle kullenta,
shiyasa ma ta kwantar ma Baffa da hankali...



A ranar da Mummy tazo gidan, ginin da akeyi har yakai linta,

aiki maginan sukeyi ba dare ba rana dan Papy baya son ginin ya wuce wata daya,


Tasha mamaki da takaici,
har ta dan yadawa Baffa habaici tace
"bari a gamawa amarya nima insa ayi ma Goggo irinshi,

karaff

kalamanta cikin kunnen Papy da ya doso kai zai shigo,

nunawa yayi baiji ba,
suka gaisa ya gama duba ginin, yaga komai yayi mishi yadda yakeso,

yana matukar son ganin Anni cikin jindadi shiyasa zai wadata ta da komai na bukata a cikin gidan,
ko gishiri baya fatan ta neme shi koda na second daya ne......



Bayan tafiyar Mummy Papy yace ma Baffa
"ko za'a fitar da kayan dakin Goggo sai ayi mata renovating in yaso itama sai a sake mata sababbi,

nan take Baffa ya saki murmushi,
guilt din da Mummy ta tafi ta barshi a ciki ya sakeshi,


Albarka ya shiga sawa Papy kamar zai ari baki,
farin cikin da yake ciki a wannan lokacin ba mai misaltuwa bane,
ashe akwai ranar da zaiga danshi namiji har ya dauke mishi nauyin abu mai girma haka,

alhamdulillah ya dinga jerowa babu adadi...



Washe gari ko Mummy Baffa bai fadawa za'ayi aikin dakin Goggo ba,
da kanshi ya cire kayan da yasan masu muhimmaci ne sauran yasa aka fitar dasu zuwa bola,
duk wani takarcenta da take yawan ce mishi maganin basir,
hawayan jini da na neman budi,
duk ya zubar dasu,


Gadonta mai runfa ya kira yan gwangwan suka tafi dashi,

abubuwan da suka fado daga saman gadon Allah yayi yawa dasu,
ba tare da ya kula dasu ba yasa Garzali da sauran samarin suka tattaresu suka konesu tass,
harda dan akushin Goggo da ya fado kayan ciki suka far fashe.....


*(shin ina Goggo take ake yi mata wannan ta'asar,)* abeg ummu iman nd Siyama help me luk fr her... ku hada kudi kubawa Meelah ta nemo ta...






Yagar naman farfesun kazar dake gabanshi yayi da sauri hade da kara wayarshi a kunnenshi,

"yes Mum,

daga daya bangaren Anty Reemah tace
"Hilal har yanzu baka wuce Abuja ba?

"on my way mum,
meyasa kika damu, 6pm ne fa jirgin zai tashi,

"dis is madness Hilal,
hanyar taka ce,
pass 3 yanzu kana da assurance din kaiwa Abuja 5:30 or 40,
ka maida hankalinka dani wallahi,
wannan ai iskanci ne,


"ohhhh calm down sweet heart,
tare da little kaninki zamu tafi,
ni zanyi driving, sai su dawo gobe da Malam Ali,


"cikin sarkewar murya tace "ban yarda ba,
karka soma yin wannan mahaukacin tukin naka,
maza ka bani Malam Ali!

"ummmm am nt a kid anymore haba mana,
ki bari pls kar kisa a raina ni,
in shaa Allah your Mukhtar will come home safe nd sound,
kiyi min addu'a,
yana kaiwa nan ya kashe wayar gaba daya dan yasan bazata fasa kiranshi ba, sai ta jishi a jirgi zata hakura...



A gaggauce yayi sallama da Mummy suka fito daga parlon lokacin da sukaji horn din Malam Ali,


Husnah na hangoshi ta rugo da gudu ta karbi jakar hannunshi ta turo baki,

"yanzu zaka tafi?
haba my PP,
shikenan da bamu dawo ba bazaka jiramu ba,


Bakin yaja yace "oya kara turoshi shi gaba,
dariya tayi sosai tace
"Allah da gaske da ka tafi baka jirani ba ko waya ka kirani bazan dauka ba,


Gurin motar suka karasa yace "dama nayi niyyar baki wata kyauta,
na fasa..
leda ya mikawa Nadeeyah dake tsaye tana murmushi,
"amshi wannan ke,
Husnah ta lashe,

Tura daya ledar cikin motar yayi yana dariya,

bude motar tayi da sauri tana fadin
"sorry my pp,
dauko ledar tayi cike da kosawa ta fito da abun dake ciki,


waya ce sabuwa dal mai tsadar gaske,

wani irin ihu ta saki tana fadin "thank u yaya Hilal,
u are the best,


Da kafada Musaddiq ya zunguri Nadeeyah dake tsaye kamar statue, murna ta hanata magana,

kallonshi tayi zatayi magana, yace "ke bazakiyi godiyar bane,
oya say it out kema,
*Yaya Hilal u are the best*,
yadda yayi da murya kamar mace yasata sakin dariya sosai harda rike ciki,
shima dariyar yakeyi,


Duk wannan abun da sukeyi a kan idon Badar da ta shige ciki tun shigowarsu gidan,
dakyar ta iya danne tukukin da ya yaso mata, ta saki labulen windon da karfi,


Shi kuwa Hilal tsintar kanshi yayi cikin nishadin ganin dariyarta mai kayatar dashi,

wani masifar sonta ke ratsashi kamar dama a cikin jininshi akayi halittar son,

ya shagala sosai cikin farin ciki shiyasa baiji muryarta tana mishi godiya ba,

tabo shi Husnah tayi tace
"Ana maka magana,

kallonta yayi ya saki dan murmushin da ba kowa ke ganinshi ba yace

"never mind, ki godewa Allah, nd ki kula da karatunki,

murmushi tayi tace "inshaa Allah, Allah ya kiyaye hanya ka gaida min da kowa da kowa,

gyada kai yayi suka shiga mota yaja suka wuce,
saida suka fita a gate din sannan ya iya maida hankali kan tukin da yakeyi,

gaba daya jikinshi yayi sanyi,

gani yakeyi kamar wannan rabuwar da zaiyi da Nadeeyah itace rabuwarsu ta karshe,

"ko dai mutuwa zanyi,
saurin taka burki yayi saboda yadda tunanin yazo mishi,


kashe motar yayi yace "malam Ali dawo ka tuka,
ya bude baya ya shiga malam Ali yaja suka wuce,


Har suka isa Abuja ya rasa asalin abin da ke taba zuciyarshi akan Nadeeyah,


Addu'a kawai yayi na Allah kar ya kawo sanadin da wani zai zo ya kwace mishi ita,

badan yanada abubuwan yi ba da ya dawo nigeria har ta gama secondary school ya sama mata university a cyprus,

cikin damuwar da ya rasa dalilinta yace
" in shaa Allah tana gama school nan da 5month zai dawo da ita cyprus,
gara tana gabanshi,
hakan kadai zai hutar da zuciyarshi,
zai cigaba da tunasar da ita muhimmacin karatu har ta gama secondary...


Text ya tura cikin layin da ya sai mata..



*Kyawun alkawari cikawa, Dan Allah ki kula, ki maida hankali kan karatun waec, nd ur line ya zama personal, kar ki bawa ko wani namiji ko macce numberki sai wanda ya zamto shakikinki, take care*....





Husnah na miko mata wayar bayan ta gama setting dinta,
text din ya shigo da sunan

*Arc Kangiwa*

karanta text din tayi hade da murmushi,
saboda sabo da rike wayar Husnah yasa ta iya wasu abubuwan,
reply tayi mishi



*In shaa Allah will keep my words,
Allah ya saka da alkhairi thanks for caring*



Yana gama karanta reply dinta ya ajiye wayar,

inama zai iya ce mata
*I love you*


Yana matukar son ganin reply din da zai hana mishi sukuni ya sanya shi yawo cikin sararin samaniya kamar yadda jirginsu zai lula,


saidai kashh..
bazai iya ba,
domin tanadin da yayi wa soyayyarsu ba na yanzu bane,

sai ta mallaki dukkan hankalin kanta,
sai ta koyi duk wasu nau'ika na soyayya,

yana son yin soyayyar da a tarihi ba'a taba samun kamarta ba,

cije lebe yayi domin hango yadda zai maida ita sarauniyar shi,
kuma sarauniyar matan duniya....



*(A bari ya huce)*.....
🤪😜😝




*MAFARI* ......
*(kauna)*



*Shin so samu ne*

Nidai rubutuwa nakeyi,
mijin Nadeeyah na cikin ukun nan,
Allah ya riga ya zaba...
muje zuwa a Mafari....



*Team Hilal*
*Team Diku nah*
*Team Taheer*






Mrs Tijjani Shattima......

[01/04 3:08 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣6⃣
By *Aysha Ya'u kurah*




Ajiye motarshi yayi a gurin da aka tanada dan ajiyar motoci,
saida ya kusan minti biyar yana tattara duk wasu abubuwa masu muhimmanci a cikin motar, sannan ya fito ya rufe hade da mikawa wani yaron gidan mai musu hidima kayan ya wuce ciki, jikinshi sam babu kuzari da walwala,


Kauracewa abinda kake so dan farin cikinsa,
ba karamin jarumta bane wanda samun masu yinsa sai an tona....




Koda ya shiga bayi domin watsa ruwa kasa tabuka komai yayi,
yana tsaye a tsakiyar shower ruwa na ratsa dukkan sassan jikinshi,
a maimakon yaji sanyin ruwan a zuciyarshi sai yaji wani irin zafin da ke kona duk wata kwayar halitta da aka halicceta domin soyayya a cikin ma'adanar ta,
alwala ya dauro ya fito jikinshi sam ba karfi,


karfe goma da rabi lokacin,
brown jallabiya yasaka ya shimfida sallaya dan yin sallahr walaha (Duha)..


Yafi minti talatin yana kai kukansa gurin rabbil izzati akan ya mallaka mishi Nadeeyah kuma ya sanyata farin ciki har karshen rayuwarta,



"Tee lafiya ka dawo gida?, Momma da ta shigo dakin bayan ta fita taga motarshi a parke ta fadi hade da zama a kujerar dake fuskantarshi,

Shafa addu'a yayi yace "Lafiya lau momma,
dama yanzu nake shirin zuwa gurinki,

Mikewa yayi ya nade daddumar ya dawo kusa da ita ya zauna,


"Ina son komawa school Momma, munyi magana da Uncle Mus'ab nace su shirya min visa,
ina son yin phd dina tun yanzu Momma,
rike makaranta irin legacy sai da Phd, daga nan ma sai in kara gaba in shaa Allahu,
ina son mu samu rassar makarantar a ko ina a cikin Nigeria,

kinga dole in gogu cikin il---

"Ba gaskiya bane Taheer ta katseshi cikin sauri dan kar yayi zurfi cikin karyarsa,

"Kalleni Tee,
ni na haifeka,
na raineka har kawo wannan lokacin,
a kan murmushin fuskarka ina iya hangen damuwarka,

"jiya ka gama cemin ka samu yarinyar da kake so da aure,
yau kuma sai kazo min da zancen tafiya har Canada kuma ba wai kwana daya ba har shekaru,
sannan kake tunanin in yarda baka da damuwa,

"Fada min matsalarka maza maza,
ka sani babu abin da yake cikin duniyar nan wanda bazan iya magance maka shi ba,
koma me kake so ka fada min yanzun nan kaga aiki da cikawa,


Hannunta ya rike a hankali yace "nasan zaki iya magance min komai Momma,
amma ban da soyayyar Nadeeyah,
bana son in a matsa mata ta zauna dani,
nafi son ta zauna dani domin kanta,
nafi son ta soni da kanta ba tare da an tursasata ba,
nasan Allah swt zai kawo mana wannan ranar,

Addu'a kawai zamu cigaba dayi,
in shaa Allah zamu dace,

Zan tafi ne dan in bata damar yin karatunta cikin kwanciyar hankali,
in shaa Allahu lokacin da ta kammala karatunta nasan zata karbi bukatata,


"Jiranta zakayi Taheer?


Yadda tayi maganar cikin damuwa yasashi jin wani iri a jikinshi,
yayi karfin halin cewa

"kamar yau ne Momma,
kuma kinga karatu zan tafi nima,

lokaci gudu yakeyi,
sai kiga kamar yau ne ta kammala,



Shafa fuskarshi tayi tace
"lokaci sakarai ne Taheer, wucewa yakeyi da abin da muke so,
amma tunda ka bukaci haka kuma kana ganin itace wacce zuciyarka ta gamsu da ita shikenan,

zan tayaka addu'ar samunta indai alkhairi ce a garemu,

Sannan visar biyu za'ayi,
me zan zauna inyi babu jigon gidana,

murmushi yayi yace "nine gidan ma gaba daya,

"ofcourse,
yaushe zan zauna ni kadai a gida,
ai sai zuciyata ta buga,
School kuma zan barshi gurin Kamal da  Mr Kabeer,
nasan zasu cigaba da rike mana Amana,


cike da gamsuwa yace kwarai kuwa,
ai ko yanzu ma su suke wasu abubuwan,
zan koma school din anjima daga can sai in wuce office din *Captain Mus'ab*.......






Dariya Hilal yayi ya kalli Baffa yace
"me zan zana anan?,
saidai in a rushe filin gidan kaf in zana full house a fara aiki malam,
nan me za'a gina? Akurki!



"Daidai ruwa daidai tsaki,
Baffa ya fadi yana dariya hade da cewa nan din nakeso ka zana musu,
kaga masu ginin suna son fara aiki,



kallon Hafeez yayi yace "zo kayi mishi bayani dan Allah,
  naga kamar akwai rikicin tsufa akanshi,


Dariya Hafeez da Jamal sukayi Hafeez yace
"wannan kawai fa za'a danyi yabe ne Baffa,
abun da bai wuce koni in nuna musu ba,
har sai an zana a takarda,


kaga Zaharadden je ku gama kwaso sauran kayan,
kuma kunsan yadda zakuyi,
ciki da parlo zaku fitar ku dan yayyaba, tsofaffi ne,
suyi maneji,



"Gidanku Hafeez,
su tsofaffi basu san abu me kyau ba,
muma munsan mai kyau dan haka sai an zana min,


"Muntari tun muna mu biyu kaje ka fara zanen nan,


"wai Baffa wa ma yace maka ina zane,
to ni abu biyu kawai na iya zanawa a rayuwata,

*full house*

nd

*complete face that only me can relate* ..


kusa da maginin yaje yana dariya yace "zaku iya fitar da 2 bedroom ko,
gyada kai Zaraddeen alamar eh,

"Yauwa to sai kayi 2 toilets,
karka matse su komai kayi shi enough saboda tsofaffine kamar yadda kaji yayana ya fada,


Juyawa gurin Baffa yayi yace "shikenan kiran ko?


"Shikenan tunda bazaka zana ba, ina son ginin zamani amma hali bazai sa in samu ba,
bakomai, ya fadi da fuskar tausayi,


Gaba daya gurin suka dauki dariya harda maginan,

Duk wannan hidimar da akeyi Goggo bata nan,
babu wanda yasan inda ta tafi,

Wayar Hilal ce ta soma kara alamar kira na shigowa yayi saurin cewa Baffa sai anjima ginin sai yafi na zamani kyau,
hannu ya dagawa su Jamal yana Murmushi sannan ya fita,


A lokacin wayar ta katse,
saida ya shiga cikin mota ya kira...



Assalamu alaikum,

Hilal ya fadi cikin girmamawa,

daga daya bangaren aka amsa mishi sallama hade da fara magana cikin harcen turanci,



"Hilal...
Sheik yana yabawa kokarin ka,
sannan yana kara yi maka godiya,
domin kuwa a halin yanzu babu construction building companyn da yakai namu a cikin gari da wajen Turkey,
muna godiya sosai,


Sannan akwai wani business da zamuyi dakai, 
akwai wasu estates guda hudu da zamu gina,

each ana son 400 building, 
different houses guda hudu a each estate,


"Dat means in each estate ana son 100 houses iri daya har 400 ko?



Exactly my boy...
mutumin ya fadi yana murmushin hakanshi ya kusa cimma ruwa,

ya cigaba da cewa dat will make it 16 different houses, kuma duplex sukeso,
yanzu maganar kudi nakeso muyi dakai,
yadda oga yake yaba ayyukanka nake son muyi deal da kai,
bari in baka ďan oga kuyi magana,
shi ya kawo business din,

gyara zama Hilal yayi yana sauraronsu,



"Hey xup, sunana
*Irfan Ateek Deen*

kamar yadda manager yayi maka bayani ni na samo business din,
to yanzu so mukeyi ka rubuto adadin kudin da za'a biya ka,
ni zan fada maka yadda zaka rubuta da adadin kudin,
bayan payment sai ka cire actual price din da ake biyanka,
ka bani sauran,
karka damu da yawan amount din da zan fada maka,

i'm very sure Dad will never refuse u,
saboda ur hand work mks him loose control,
baya iya rike farin ciki lokacin da yaji ana yaba irin aikinshi,
so pls wannan aikim taimakon juna ne,

*DAD*

Hilal ya maimaita a zuciyarshi, katse mishi guntun tunanin da ya fara Irfan yayi yace

"ka fahimceni,

"yes na fahimta, karku damu,


Yanzu bana nan but zan dawo on wed or Thursday daga na dawo zanzo sai mu kara tattaunawa,


"Yessssssss Irfan yace  zuciyarshi wasai dan ya hango irin kudin da zai samu,

sam mahaifinshi bai bashi kudi saboda halayyarshi na yaran masu kudi na shaye shaye,
zinace zinace, da mugun yawo,


Baiki dan almubazzaranci kullum yabi jirgi ya fita wasu kasashen ba,
babu kamar ma in ana champions league,
a lokacin ko baida kudi haukacewa yakeyi ya sato su gurin umminshi,
ko kuma cikin sarkokin kanwarshi dake nema ba dare ba rana,


Yanzu ma fake business ya kirkira saboda ya samu kudi, yana son zuwa kallon *Zee cine award* a london shi da budurwarshi masoyiyar india,
yasan Hilal ne kadai wanda zai rubuta kudi a bashi nan take,


Daga nan sai ya bar Hilal cikin matsala,
shidai bukatarshi ta biya baiji kunyar *Ailah* ba,

Sallama Irfan yayi wa Hilal,
saboda tsabar farin ciki ya manta bai kashe wayar ba,
nan suka shiga hira da managern suna fadin yadda zasu kasafta kudin da yadda zasuyi denying basu suka sa Hilal ba,
dama managern na matukar jin haushin Hilal,
saboda a da kaninshi ke musu zane kafin zuwan Hilal ya doke su,

Saida ya gama jinsu tsaf har Irfan ya tafi sannan ya katse wayar yana tunanin rashin imani irin na mutane,
wai ciki harda dan da ka haifa,

kai duniya ina zaki damu ne,

shikenan san kudi yasa mun manta komai na duniya,

mun manta duties dinmu, zumuncinmu,
matsayinmu,
da kuma addininmu,


Ya Allah ka sanyawa zukatanmu kyankyamin daudar duniya,


*(Irfan Ateek bai san da wanda yake son ya fara harka ba)......*



Mrs Tijjani Shattimah.......
[01/04 3:08 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣7⃣
By *Aysha Ya'u kurah*





Zaune take cikin duhu da waya a hannunta,
zuciyarta kamar zata fashe saboda bakin ciki,

Tuno sanda suka taso daga makaranta tayi,
tabi bayan motar malam Ali dan ya maida ita gida yace "Daddy yayi mishi kashedin kar ya daukata,


kwafa tayi ta sake duba agogo karfe takwas da rabi,

har lokacin Goggo bata dawo ba,

plate din da taci chips da dankalin da ta siyo tayi wurgi dashi waje,
tana jiyo masu ginin gidan na mata sallama tayi banza dasu dan bataga abun da zata musu ba,



Muryoyi ta jiyo suna shewa suna fadin
"lallai masu ginin nan sun iya fitar da foundation,

sosai ginin ya burge Baffa domin irin ginin da yake so ne,



Fitowa tayi da sauri dan tana ganin rokon Baffa ne kadai mafita,
shi zai je ya samu Daddy ya bashi hakuri,
inda suke taje ta fashe da kuka,


Papy da ya tsani kuka musamman na mace yayi saurin cewa
"lafiya?, meya sameki?,


"kyaleta shagwaba ce,
yanzu haka wani abun takeso, Baffa ya fadi yana kauda wani katon dutse,


"Baffa dan Allah ka maidani gida,
ka bawa Daddy hakuri,
wallahi bazan kara ba,
kusa da ita Baffa ya dawo dan baida masaniyar dalilin dawowarta gidan,
"lafiya, me kikayi mishi?


Share hawaye tayi tace
"fada mukayi da Nadeeyah,
kuma itace ta fara tsokanata,
shine yace in zo nan gidan inyi wata daya,
kuma Goggo bata bani abinci,
tun safe banci komai ba,
da na dawo makaranta ma haka,
kuma har yanzu bata dawo ba,
ga duhu gashi sauro sai cizona sukeyi,


Papy duk yaji babu dadi,
duk tunaninshi Daddy ne ya haifi Badariyya,
girman Daddy ya kara gani idonshi,
saboda yar da ba taka ba kace yarka ta bar gidanka,
bazai yiwu ba,
shima dole ya taka rawar gani a matsayinshi na uba ya mayar da ita,

"share hawayenki, ki shirya mu tafi in maida ki,
ai ba'a shiga fadan yara,

maza shirya mu tafi,
nasan yana gida yanzu,


Murmushin jin dadi Baffa yayi yace "aiko ka kyauta,
nasan zai hakura dan bai taba yin irin wannan fushin ba,
kace ina gaisheshi,
zaiji in shaa Allah,
bari insa Jamal ya fitar da mota kafin nan ta fito,



Fada sosai Baffa yayi mata na ta iya maraicinta,
"Kina gani yanzu Muntari har ya fara cewa ki bar mishi gida,

ina ga nan gaba in kika kaishi bango,

wallahi ki maida hankalinki,


Gyada kai tayi kamar taji abinda yace,
bai san so takeyi ta koma tun kusancin Nadeeyah da Musaddiq baiyi nisa ba,
tun yanzu ma kenan ta fara sa hularshi,
gaba sai hada jiki da sunan soyayya.... ta karashe hade da runtse ido tana fadin Allah ya kauda idon Musaddiq akan Nadeeyah......




Saboda kunyar idon Papy, Daddy baiyi wata jayayya ba ya ce ta shiga gida,
godiya Papy yayi mishi, nan suka shiga hira,
ya fada mishi shirin da yayi na auren Baffa da Anni,


Ba karamin farin ciki Daddy yayi ba,
dan ya hango tsantsar tsoron Allah da ilimi a tattare da Anni,

Yana da yakinin yanzu zumuncin zuri'ar matarshi da ta 'yayanshi zai gyaru ta sanadiyar Papy da Anni,



Zama Mummy tayi bayan ta gama jin zancen auren,

A zuciyarta bata ji dadi ba dan abun kunya ne a gurinta tace babanta zaiyi aure,
me kawayenta zasu dauke shi,


A fili kuwa saboda yadda taga Daddy na farin ciki kamar shi zaiyi auren,
ta nuna itama ta amince, ta cigaba da cewa
"gara a sakawa Anni ta wannan hanyar,
dan tayi mana abun da bazamu taba mantawa ba,
samun mutane irinta sai an tona....




Sai kusan goma Papy ya fara shirin tafiya,


Dakatar dashi Daddy yayi,
ya dauko Sarkar Atika yace

"wannan Sarkar mahaifiyarku ce wacce mukayi tunanin su Hafeez ne magadan ta,
to yanzu kai ne ke da gadonta domin Baffa yace ya bar musu,



Dariya Papy yayi ya karbi sarkar dan jin dumin mahaifiyarshi yace

"nima na bar musu,
domin duk 'yayanmu ne,
ka ajiyeta a gurinka, kaine uba a garesu,

mun gode sosai da yadda kake kula dasu,


karbar Sarkar Daddy yayi yace "to Madallah,
zan cigaba da ajiye musu har lokacin da zasu bukace ta,

Allah yayi wa zuri'armu albarka,

Ameen....
Papy ya fada hade da mikewa yayi sallama da Mummy,


Har gurin mota Daddy ya rakashi, nan ma suka dan taba hira sannan suka wuce cike da shaukin shakuwa kamar sun shekara tare......




Har kwana hudu babu Goggo babu dalilinta,


Hankalin Baffa ba karamin tashi yayi ba dan ba inda bai nemeta ba,
wayarta a kashe take,
duk inda yasan tana zuwa yaje ya duba shuru,

Allah kadai yasan inda ta shiga,


Itama Mummy ba karamin tashin hankali ta shiga ba,

saidai tasan bazata bata ba,
ta yiwu tana can tana kulle kullenta,
shiyasa ma ta kwantar ma Baffa da hankali...



A ranar da Mummy tazo gidan, ginin da akeyi har yakai linta,

aiki maginan sukeyi ba dare ba rana dan Papy baya son ginin ya wuce wata daya,


Tasha mamaki da takaici,
har ta dan yadawa Baffa habaici tace
"bari a gamawa amarya nima insa ayi ma Goggo irinshi,

karaff

kalamanta cikin kunnen Papy da ya doso kai zai shigo,

nunawa yayi baiji ba,
suka gaisa ya gama duba ginin, yaga komai yayi mishi yadda yakeso,

yana matukar son ganin Anni cikin jindadi shiyasa zai wadata ta da komai na bukata a cikin gidan,
ko gishiri baya fatan ta neme shi koda na second daya ne......



Bayan tafiyar Mummy Papy yace ma Baffa
"ko za'a fitar da kayan dakin Goggo sai ayi mata renovating in yaso itama sai a sake mata sababbi,

nan take Baffa ya saki murmushi,
guilt din da Mummy ta tafi ta barshi a ciki ya sakeshi,


Albarka ya shiga sawa Papy kamar zai ari baki,
farin cikin da yake ciki a wannan lokacin ba mai misaltuwa bane,
ashe akwai ranar da zaiga danshi namiji har ya dauke mishi nauyin abu mai girma haka,

alhamdulillah ya dinga jerowa babu adadi...



Washe gari ko Mummy Baffa bai fadawa za'ayi aikin dakin Goggo ba,
da kanshi ya cire kayan da yasan masu muhimmaci ne sauran yasa aka fitar dasu zuwa bola,
duk wani takarcenta da take yawan ce mishi maganin basir,
hawayan jini da na neman budi,
duk ya zubar dasu,


Gadonta mai runfa ya kira yan gwangwan suka tafi dashi,

abubuwan da suka fado daga saman gadon Allah yayi yawa dasu,
ba tare da ya kula dasu ba yasa Garzali da sauran samarin suka tattaresu suka konesu tass,
harda dan akushin Goggo da ya fado kayan ciki suka far fashe.....


*(shin ina Goggo take ake yi mata wannan ta'asar,)* abeg ummu iman nd Siyama help me luk fr her... ku hada kudi kubawa Meelah ta nemo ta...






Yagar naman farfesun kazar dake gabanshi yayi da sauri hade da kara wayarshi a kunnenshi,

"yes Mum,

daga daya bangaren Anty Reemah tace
"Hilal har yanzu baka wuce Abuja ba?

"on my way mum,
meyasa kika damu, 6pm ne fa jirgin zai tashi,

"dis is madness Hilal,
hanyar taka ce,
pass 3 yanzu kana da assurance din kaiwa Abuja 5:30 or 40,
ka maida hankalinka dani wallahi,
wannan ai iskanci ne,


"ohhhh calm down sweet heart,
tare da little kaninki zamu tafi,
ni zanyi driving, sai su dawo gobe da Malam Ali,


"cikin sarkewar murya tace "ban yarda ba,
karka soma yin wannan mahaukacin tukin naka,
maza ka bani Malam Ali!

"ummmm am nt a kid anymore haba mana,
ki bari pls kar kisa a raina ni,
in shaa Allah your Mukhtar will come home safe nd sound,
kiyi min addu'a,
yana kaiwa nan ya kashe wayar gaba daya dan yasan bazata fasa kiranshi ba, sai ta jishi a jirgi zata hakura...



A gaggauce yayi sallama da Mummy suka fito daga parlon lokacin da sukaji horn din Malam Ali,


Husnah na hangoshi ta rugo da gudu

Please Login or Register in order to submit comment