Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


"zo ka fitar min a gida,
wallahi zanyi mugun sabawa uwarka in har bata ja maka kunne a kaina ba, yaro sam baya ganin girmana,

Hilal cikin zafin zuciya zaiyi magana Musaddiq yayi saurin janshi sukayi daki,

Kitchen Husnah ta kai abincin da ta kasa ci,
ta rasa dalilin da yasa mummy da Hilal sam basa jituwa,

ita a ganinta Hilal bashi da mutunci, kuma sam bashi da kunya,
baya ganin kowa da gashi,
zata iya kirga maganar da suka taba yi da Hilal tun tasowarta har kawo yanzu,
kullum kallon mai bakar zuciya take mishi....


Sai da Daddy ya gama saisaita zuciyarshi,
ya kalli mummy dake zaune tana zuba ruwan masifa a waya,

gyaran murya yayi yace
"kashe wayar nan in kin gama kai karar jikanki gurin diyarki,

a hassale mummy tace "kana ganin abin da yaron nan yake min,
ba tun yau ba,
walhy bazan dauka ba, dole uwarshi ta ganar dashi muhimmaci na,

"Uhmm Daddy yace, ya cigaba da fadin
"yanzu kin kirata ne ta zaba ko ke, ko shi,
ko kuwa kin kirata ne tayi fushi dashi,

kin san meye matsalarki!?
baki da hakuri in dai akan Badariyya ne,
da ke, da Hilal halinku daya,

kinsan ance magaji mafiyi,

saidai shi akan gaskiyarshi yake yi, sabanin ke da keyin naki bisa son zuciya,
babu ranar da Allah zai hadaku da Hilal baku raba hali ba,
ke ba hakuri shima hakan yake,

shin sa'anki ne?
Duka nawa Hilal yake da zaki tsaya maida magana dashi,

kara kaurara murya yayi yace
"wannan ya zama na karshe a gidannan,
na daina daukar irin wannan abun,

yaron nan saboda ke sam baya son zuwa nan gidan in suna kasar nan,
ke ba abun alfaharinki bane zuciyarshi ta fara muradin gidan,
tunda ya shigo yake janki da wasa, saboda yasan halinku ya sabarwa juna, amma kikayi biris dashi,

Connection dinshi da Musaddiq kin sani tun suna yara, babu wanda ya isa ya taba Musaddiq a gaban Hilal,
ko da kuwa ke da kika haifeshi,

bakya ganin kina kara karyar da zuciyar da bata karfi,
kin sani sarai rashin son fada shi ya sanya musaddiq yake kaffa kaffa da duk wani abun da zai bata ma kowa rai,
zuciyarshi raguwar zuciya ce kin sani,
meyasa kike son kara raunana ta,

Sau tari akan Badariyya  kina sa yaron nan zubar da hawaye,

ke a ganinki baya sonta,

wani irin so kikeso yayi mata,
kowa nada labarin irin shakuwarsu kafin ta fara girma bakin Halinta ya raba su,
ki dinga yaki da zuciyarki,
sannan ki tauna abu kafin ki fadeshi,

ni kaina yau badan na kai zuciyata nesa ba da walhy sai munyi abun kunya a gaban yara,

sai Allah ya taimakeni akwai tsageran da ya fini son d'ana,,
ya karashe cike da zolaya,

sosai Daddy yayi mata nasiha akan yadda take tafiyar da yaranta, da kuma nuna banbancin da takeyi a tsakaninsu.......!



•••••••••••
Kiran sallar farko a kunnen Nadeeyah akayi shi,
mikewa tayi hade da mik'a
idanuwa da kanta sun mata nauyi sosai,
da kyar ta iya jan kafarta ta shiga bayi da niyyar dauro alwala,
bako ta riska a tattare da ita,
tashin hankali sosai ta shiga na rashin audugar da zatayi amfani dashi, tsumma sam baya tare ta,
bata ma san yadda zatayi amfani dashi ba, saboda duk zata koma makaranta sai an sai mata guda uku, ragowar ta dawo dasu gida tayi amfani dasu,
kayan jikinta ta cire tayi wanka da ruwan zafin dake zuba a pampo,
gasa gefen kanta dake mata nauyi tayi da dukkan jikinta,
sai da taji dadi sannan ta fito,
pant dinta ta dauko da wani karamin dankwalin Zainab, tayi dabara ta sanya a jikinta,

shiryawa tayi tsab cikin doguwar riga kimono jaa,
dinkin yayi mata cib a jikinta,
duka kayan basu wuce dubu biyu ba, amma yadda suka karbeta kamar kayan dubunnai,
blue baby hijab tasa a wuyanta ta fara gyara kayansu,
tana gamawa ta hau gyaran dakin, tsintsiya ta fara dubawa bata gani ba ta tabbatar tana parlor, ko kitchen,

fitowa tayi ta fara dube dube,
can ta hango tsintsiyar a bakin kofa,
daukowa tayi ta sharo dakin sannan ta dawo parlor ta fara gyara shi,
sai da ta gyareshi tsaff, tayi mopping kamar ba'a taba taka kasan tiles din ba,
kitchen ta wuce shima ta gyareshi tass, ta hada kayan wanke wanke ta fara yi...


Da hira suka shigo parlon kowa da farar jallabiya a jikinshi,
sama Daddy ya wuce dan baccin bai isheshi ba,
badan sallar asuba ba babu abinda zai fitar dashi,,

Kallo sukeyi suna hira hade da dariya,
hamma Musaddiq ya fara yi hade da tsaki,
"wai kai yau baka jin baccin safe ne, zo muje mu kwanta mana,

gyara zama Hilal yayi yace "Baccin safe asara ne my guy,
kullum sai mum ta fada mana,
hararashi Musaddiq yayi yace "really!!! yau ne kasan da wannan, dalla tashi muje mu kwanta,

kafin Hilal ya bashi amsa suka jiyo ihu a kitchen,

Hanyar sama Musaddiq yayi a tsorace dan shi a tunanin shi wani mugun abun ne,
dan yasan a gidan babu mai shiga kitchen a wannan lokacin,

Hilal kuwa mikewa yayi ya tsaya kyam cike da jarumta yace "Hasbunallahu wa ni'imal wakil,

"wayyo Allah hannuna, wayyo Allah na,
abin da suka jiyo cikin ihun kukan kenan,
da sauri Hilal yayi kitchen din saboda ya gane mamallakiyar muryar,
dawowa musaddiq yayi ya bi bayan Hilal shima da sauri,

A durkushe Hilal ya sameta rike da hannun sosai tana kuka kamar ranta zai fita,
mugun radadi takeji har tsakiyar kanta,
karasowa yayi a gaggauce ya dagota, hannun ya fara kokarin kamawa ta kara tamkeshi saboda azaba,

"me ya sameki?, and me kikeyi a kitchen at dis hour,
saitin windon ta nuna mishi hade da runtse idon ta,

katuwar KUNAMA ya hango tana tafiya a hankali,
hannun ya saka da sauri ya dauko takalmi,
mugun duka ya kai mata har saida net din windon ya tsage,
duk wani bacin ranshi ya tattaro ya sauke a kan kunaman,

saida yayi mata pieces sannan yayi wurgi da takalmin,

waigowa yayi da niyyar fita da Nadeeyah yaga wayam babu kowa,

da sauri ya fito parlon yaganta zaune a kan dining,
kusa da ita Musaddiq ne yayi kneeldown rike da hannun yana hurawa, yana fadin sorry, zafin yana raguwa ko?,
girgiza kai tayi saboda zafin kamar dado shi akeyi,

tsaki Hilal yayi yace "who told u zafin harbin kunama na ragewa haka nan,
bari in dauko key mu kaita hospital,
gyada kai Musaddiq yayi yace "kayi sauri plss,


Hawayen fuskarta ya fara share mata yana fadin
"stop crying, it won't help sai dai ya kara miki ciwon kai,
kiyita addu'a, kinji!,
uhm ta fadi tana gyada kai,


Badariyya da tun ihun farko ta farka,
tana zaune a inda take tana tsaki,
a ranta tana fadin "Allah yasa ciwon mutuwa Nadeeyah keyi ta mutu kowa ya huta,

mikewa tayi ba tare da tunanin yin sallah ba ta bude kofar dakinsu dan surutai da shashshekar kukan da takeji sun fara damun kunnenta,

Mummunan gamo tayi wa idanunwanta,
wani abu taji a kirjinta kamar saukar aradu,
tashin hankali marar misaltuwa ya ziyarci zuciya da ilahirin jininta,

bata karasa gama shiga cikin kogin bacin rai ba taji muryar Hilal na fadin "ke miko mata babban hijab cikin kayanta,

a firgice kamar me farfadowa daga suma tace
"Hijab din wa?

Wa kika gani anan?

Ko ina sa Hijab ne?
Hilal ya fadi yana harararta

Cike da ficewar hayyaci da rashin kunya tace
"sai kuma kaga nayi kama da yar aikenta ko,
sai kaje can dakin da ta sauka ka dakko da kanka dan kasan bata isa muyi sharing daki da ita ba,

a hasale ya nufeta, Musaddiq yayi saurin cewa rabu da ita Kangiwa, muje mu kaita a haka,
ciwon k'aruwa yake yi,,

dagota musaddiq yayi ya riketa sosai suka nufi hanyar waje,

"zamu hadu in na dawo Hilal ya cewa Badar hade da nunata da hannu,


wani irin kuka ta saki hade da fadin ka kasheni in ka dawo,
karka sake ka barni da rai,

bai tsaya biye mata ba yayi waje
dan ba ta tata yake yi ba,
burinshi yaga Nadeeyah ta daina kukan nan da takeyi,
sannan yasan wani daki aka sauketa a gidan, kuma yasan musababbin shigarta kitchen a wannan safiyar kamar baiwa..

A iya saninshi a sama, dakin mummy da Daddy ne kadai,
a kasa kuwa na musaddiq ne sai nasu Badariyya da na masu aiki,

ko BQ mummy ta kaita ita kadai?

kauda tunanin yayi ya shiga motar ya tada ta suka wuce.....!!!!


Mrs Tijjani Shattima.. ... ***

[01/03 12:08 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 2⃣3⃣
By *Aysha Ya'u Kurah*



Sallamanku!!
A razane Ma'u ta juyo dan jiyo sallamar tayi bagatatan hade da shigowar me sallamar,
"wa sallama" ta fadi tana kokarin kare fuskar bakuwar,
"Ayya Haire am kece tafe da maraicen nan,
"Aaa nice, mon be sare! Haire tace tana kallon kafar wacce Ma'u ke karewa,
dad'a kareta tayi tace "Yauwa sannu Haire, tayi saurin cigaba da cewa "babu fura!
yau tun safe ta kare saboda masu shigowa siyan nono,

Haire ta kara matsowa tana leken idon bakuwar tace "Ni ba fura nazo siya ba,
labari nazo in baki, yau ko nonon bamu samu ba, bare ayi zancen siyan fura!

Cike da kaguwar san jin labari Ma'u tace "Baku samu nono ba?
Ba'a tatsi madarar nonon bane?

Haire tace "Hmmm, yau ai anyi rigima a kofar gidan jauro,
har Shaho ya kashe rai,
kisa,,,
ma'u tace gabanta na dukan uku uku kamar bata san komai ba,
wa aka kashe?
Ke ko Ma'u baki bani gurin zama, duk irin gajiyar nan da na kwaso ki barni a tsaye,
Tsaff ma'u ta gano manufarta, taja hannunta tayi hanyar sakarkari da ita,
saboda tsaho irin na ma'u tsaff ta hana haire damar waigowa,

Labarin abin da ya faru ta fada mata hade da cewa "yanzu Hardejo yasa a dauke gawar yaron ayi mata sallah, dan ance saurayin musulmi ne,
kuma ya wakilta wani yaje can tsaunin ya nemo inda yan uwanshi suke a fada musu,
cike da damuwa Haire tace "ni yanzu yar buduwar nake tausayi, dan shaho na can ya tashi hankalin gari,
kuma yace duk wanda ya dauketa ya boyeta in dai ya samu labari sai ya hallaka shi,
kinsan shaho,
a wala hore na,,
duk dakiya irin ta ma'u saida cikinta ya dauki kugi saboda yadda take jin labarin shi tun zuwanta garin da aure ya kawota,,
magana ta fara yi jiki a sanyaye tace
"Haire am kinsan babu abinda zan boye miki,
gyada kai Haire tayi tace "nasani ma'u,
yauwa tace tana mai gyara tsayuwa,
ta kwashe yadda akayi Baffa ya kawo yar makka gidan da kuma amfanin da take ganin yar makkan zata yi mata,
ta karashe da fadin duk irin kokarin da zanyi in ga na samu wani abu a gurin iyayenta da ita zanyi,
sannan kema bazan barki a baya ba, rabawa zamuyi daidai in kin yarda zaki rufa mana asiri,

Ajiye kwarya Haire tayi ta zauna tana washe baki tace "wannan ai karuwar mu ce duka,
ke ni har na fara hango ni a kasa mai tsarki,
yadda su Hardejo suke fadin kasar ace muma gamu a cikinta, shewa sukayi dukkansu Ma'u tace "ai kaff kauyen nan sai sun dawo yi mana bauta,
ke dai ki bani hadin kai mu samu abinda muke so,
yanzu bari kiga sarkar da na dauke mata na hadata da tarkacen tawa,
"aiko dakko ta mu gani,
kin gani, ashe dai dama gaskiyar Hardejo da yace musulunci dadi gareshi,
gashi nan cikin kwanaki kadan da karbarshi mun sami damin arziki, dariyar murna ma'u tayi ta wuce daki inda take jiyo kukan boddo, rashin ganin Baffa a dakin baisa ta kawo komai a ranta ba, ta dauki Boddo Halima ta duba gurin da ta ajiye sarkar taga wayam ba komai,
dube dube ta farayi a gefen da tayi ajiyar, nan ma bata ga komai ba,
a kidime ta fito da sauri tana kiran sunan Baffa,
Rashin ganin bakuwar a inda ta barta ne ya kara daga hankalinta matuka,
bayin gidan ta duba ko tana ciki, nan ma taga wayam babu kowa,
gurin Haire ta koma jiki a sanyaye tace "Baffa ya dauketa a gidannan,
dama yace zai koreta na hanashi, shine ya faki idona ya aiwatar,
shi tsoro gareshi,
daya barni da shaho ni nasan yadda zanyi inyi maganinshi, yanzu gashi ya janyo min asarar sarkar gwal da kyautar da iyayenta zasu mana in sunzo daukarta,
Cike da kunan rai Haire da ta gama hango kanta a wata duniyar tace "amma Baffan Bingel bai kyauta mana ba,
badan sunan annabin Hardejo gareshi ba da sai inyi kokwanton amsar musuluncin shi, tunda ai addinin Hardejo yace mu sowa dan uwanmu abin da muke sowa kanmu,
jugum dai ma'u tayi tana bawa Boddo nono, tunanin ko ina mijinta zai kai yar Makkah ne ya cikata ya hanata magana.....



Shi kuwa Baffa jin hirar da sukeyi da Haire ne ya sashi dauko sarkar da rigarta ya rufe mata fuska hade da kamo hanunta suka fita a gidan,

Hanyar gidan yayanshi Hardejo yayi,
duk wanda ya gansu a hanya sai yayi tunanin Ma'u ce,
wasu a ganinsu wani abu ne ya faru ta rufe fuskarta take kuka,
babu wanda ya ganeta kasancewar ma'u ma fara ce sosai,
saidai farin nasu ba iri daya bane..


A kofar gida ya samu Hardejo yana koyar da samari karatun Allo,
can ciki ya shige gurin matan shi, aiki ya samesu sunayi dukkan su a tsakar gidan,
dakin uwar gidan ya shige kai tsaye tare da ita,
ganin su a haka ya sa uwar gidan cire hannu a aikin ta wankesu tabi bayansu dan jin ko lafiya taga Ma'u haka,

A tsaye ta sameshi yana safa da marwah a cikin dakin,
yana ganinta yace "yauwa me babban suna, dama ke nake jira, taimakona nazo kiyi,
zama tayi kusa da budurwar da take tunanin ma'u ce, tace "me ya sameki ma'u?
Zama yayi daidai kafarta ya bude fuskar budurwar yace ba ma'u bace,
bakuwa ce wacce rayuwarta ke cikin hatsari,
labarin abinda ya faru kaff ya kwashe ya fada mata har dalilin da yasa ya kawota gurinsu,
ya cigaba da fadin "nasan Shaho bashi da karfin da zaizo gidan nan yace zai dauke ta ko ya mata illah,
gata nan zan bar miki ita,
domin Allahn Hardejo ki kula da ita har iyayenta suzo daukarta,,,

A tsorace Aisha (mai babban suna) ta kalli budurwar tace "a wani gari take?
Inafa zan san daga inda take, Baffa ya fadi cike da zullumi, gyara zama tayi tace "to babu matsala, na samu labarin abinda ya faru sama sama dazu,
Kuma naji ance malam ya tura aje a dauko gawarshi mutanen shaho sun hana sun zauna jiran dawowar budurwar ko wanda zai dauki gawar,

cike da tausayawa ta kalli budurwar tace "ya sunanki,
Baffa yayi dariya yace "ai bata jin komai, larabcin kadai na lura take ji,
da yake Aisha ta dade cikin musulunci,
babanta babban malami ne a jalingo, kuma sanadiyyarsu Hardejo ya musulunta har aka bashi aure, tace "maa ismuki ya ukhtee...

cike da jin dadi budurwar tace "ATIKA " *ATIKA SHEIK SAHEEB SAIFUDDEEN*

Juya sunan Baffa yayi tayi yace "kai ilimi akwai dadi, yanzu kinga sai musan labarinta ta dalilinki mai babban suna....

Mikewa Aisha tayi tace "bari in kawo mata abinci taci sai tayi sallah, kaga magariba ta kusa....




Bayan sallar isha'i kowa ya nutsu a gida,
kuka da karai kainin shanaye kadai ke tashi a cikin gidan,
matasa da yaran gidan duk suna zaure suna daukar karatun dare, yayin da wasu daga cikin malaman hardejo suka wanke gawar Habeeb da suka samu daukowa da kyar, hade da suturceta kamar yadda hardejo ya koya musu...


Zaune yake cike da damuwa ya zurawa abincin gabanshi ido, "mutanen kauyen nan har yanzu imani bai gama ratsasu ba,
duk irin fatawar nan da ake badawa bazai sa su hankalta su saduda ba,
Hannu yasa a sama yace " *YA ALLAH DUK WANDA ZUCIYARSHI TAKE A KESASHE BATA DA NIYYAR RUSSUNAWA KUMA BA MAI SHIRYUWA BACE YA ALLAH KAYI MANA MAGANINSU DA GAGGAWA* AMEEN
suka amsa dashi dukkansu,
Adduoi yayi sosai akan duk abinda zai zamto barazana akan alummar musulmi Allah ya kauda shi....


******
Cikin Harshen larabci take bawa Aisha da Hardejo labarinta...


Sheik Saheeb Saifuddeen shine sunan mahaifina,
dan asalin kasar cairo ne, babban malami ne kuma dan kasuwa wanda ake ji dashi a egypt..

Ummuna ta rasu shekara shida da suka wuce gurin haihuwar kanina,
ummuna mahaifinta dan cameroon ne,
mahaifiyarta ce yar cairo,
kasancewata babba gurin mahaifina yasa yake ji dani fiye da kowa,,
Tun bayan rasuwar mahaifiyata aka aura mishi kanwarta Ummul khair saboda ta kula da kanina,
tun daga lokacin rayuwa ta fara sauya mana zuwa yanayi na ban mamaki da tsoro,
abin ya faro ne saboda ganin da ummulkhair tayi Abbuna ya dauki dukkan kulawarshi ya bamu ni da kanina *ATEEK*
kiyayya iri iri babu wacce Ummul bata nuna ma Ateek,
kiyayyarta a garemu batayi karfi sosai ba har saida ta haihu,
a lokacin ne ta nuna wa Ateek karara ba ita ta haifeshi ba,
in na tafi makaranta na barshi kafin in dawo gida ya jigata da yunwa,
gaba daya Ummul ta shafe idonta ta manta da zumunci saboda kasa ta rufe idon ummuna wacce ta zamto yar uwarta ta jini,
burinta a kullum Abbuna ya kula da ita da yaranta guda uku " Haidar, Affan, da Farouk,"

saboda rashin zaman Abbunmu shiyasa bai taba sanin halin da muke ciki ba,
bai kuma kula ya duba ba, saboda a ganin shi kamar da ummunmu muke tare,
bai taba kawo ummul zata taba koda yi mana kallon banza ba, bare har ta kai ga cuzguna mana,

Kakarmu ita kadai ce gatanmu, gurinta hankalinmu ke kwanciya, wannan zuwan da mukayi ma ta'aziyar rasuwarta muka zo, daga can muka taho nan mambila inda kanwar kakanmu (wanda ya haifi ummunmu) take domin gaisheta..
gidan sam baya min dadi saboda duk yan uwa basa kulawa da lamarin mu saboda rashin idon uwa,
kuma suna ganin Ummul ce mai rike damu sannan ga kudi tana musu facaka dashi shiyasa duk suka dauke idonsu akan mu,

rashin jin dadin zaman gidan yasa da na ga Habeeb ya fito zai taho siyan madara na biyoshi dan in zaga inga gari hankalina ya kwanta,
ashe kaddararmu ce anan ni da shi,
tunanina daya *Ateek* da na tafi na barshi yana bacci,
yaya rayuwarshi zata kasance in har babu wanda ya biyo sahun duba ni,
yaya rayuwar Ateek zata kasance, ta karashe cikin kuka mai ratsa zuciya,,,,,


Share hawayen tausayi Hardejo yayi yace "zasu zo su sameki, nasan zasu zo dan na tura a nemo inda iyayen yaron suke,
ko basu zo ba ni zan je har mambilan in kaiki gobe,

cikin kuka tace jirgin su a daren yau zai tashi ya koma cairo,
kuma kasani ba'a samun jirgi akai akai,

Kwantar mata da hankali Hardejo yayi yace "Gobe tun da asuba zan tafi in kaiki, ki kwantar da hankalinki, "
"Abin da Hardejo bai sani ba shine labarin mutuwar Habeeb ya karade ko ina a tsaunin mambila, kuma an hade harda ita Atikar ance an kasheta,
saboda firgicin labarin kuma ance musu limamin garin yasa an dauke gawar an suturce yasa gaba daya yan uwanta suka shirya komawa Cameroon a daren,
harda ita kanwar kakar tasu wacce dama Habeeb din ne karfinta a garin....



Suna idar da sallar asuba sukayi janaizar gawar Habeebu,
bayan an binneshi kamar yadda Hardejo ya karanta sukayi mishi adduoi sosai sannan kowa ya wuce gidanshi,
ko abincin safe bai ci ba ya shirya ya tarar da Atika tana shan fura,
tana gamawa ta mike suka dauki hanyar tafiya tun kafin garin ya gama yin haske,
sai da sukayi tafiyar awa daya sannan suka samu motar awaki ta karasa dasu,


A garkame suka samu gidan da ya kasance daki biyu tall, cike da tashin hankali malam Hardejo yabi makotan gurin yana tambayarsu, sukace ai kuwa tun daren jiya suka tafi saboda firgicin mutuwar su Habeebu,

zamani na babu waya bare ace za'ayi kiransu su dawo,


Takalmin Ateek ta gani a kofar gidan kafa daya,
dauko takalmin tayi ta zauna dabas taci kuka ma ishi hade da rungumar takalmin tana sumbata,
"Allah yasa ina da rabon sake ganinka Ateek,
ya Allah ya hadamu da kai da alkhairi,,

Hardejo saboda tausayi baiyi yunkurin hanata ba,
saida tayi kukanta sosai sannan ta tashi suka koma can kauyen su Hardejo,,

kauyen da rayuwa tayi dadi hade da wuya ga Atika,
kauyen da ya maida yar gata baiwa,
kauyen da Atika tayi rayuwa mai cike da ban tausayi....



Ya Allah kai ka zama gatan mara gata,
Allah ka sanyani na zama uba kuma gatan Atika dan alfarmar annabi da hasken alkurani...
addu'ar da Hardejo yayi tayi kenan har suka isa gida......


Mrs Tijjani shattima....
[01/03 12:08 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU*•• 2⃣4⃣
By *Aysha Ya'u Kurah*



Satin Atika hudu ta fara sakin jiki da yaran gidan duk da bata gane yarensu,
karatun qurani da littattafai take yawan koyar da yan matan da yan yaran gidan, sai addu'oi na azkar wadanda ta koya daga gurin mahaifinta...

Shaho kuwa tunda ya fahimci tana gidan Malam Hardejo hankalinshi ya tashi,
duk iskancin shaho yana tsoron Malamin saboda kwarjinin da yawaitar ambaton Allah ya haifar masa,
kullum in yayi niyyar zuwa gidan sai yaga gidan ya zame mishi bakikkirin,,
gashi kullum bashi da nutsuwa saboda yawan mafarkin Habeeb da yakeyi,
bacci sam ya daina daukarshi dan daga ya rufe ido zaiga fatalwar Habeeb..


kwance yake yayi firgai firgai zuciyarshi cike da kunci da radadi wanda baisan daga inda suke ba,
hatta da abinci ya daina samun lokacin ci saboda yanayin rayuwar da ya tsinci kanshi,, rashin ilimin addini ya sa ya kasa gane jinin mu'muni da kuma adduar malami irin na zamanin da wanda baya iya yin komai na sabon Allah ne ke dawainiya dashi ba,

iyayenshi sun kasance masu kudin kauyen sosai, shiyasa yake yin abin da yaga dama,
ganin halin da ya shiga ba karamin daga hankalin mahaifiyarshi yayi ba,
duk irin sangartar da yakeyi ita sam bata ganin laifinshi,
ko da aka kawo mata labarin abinda yayi murna tayi tace "sai ku jerasu cikin sauran mutanen da ya kashe,
ai ba yau ya fara ba, ita a kullum alfahari takeyi da halayyarshi saboda jahilci....


Halin da taga danta a ciki ne ya sanya ta dangata halin da son bakuwar gidan Hardejo,
alkawari ta mishi na a cikin satin nan zata aura mishi ita koda kuwa duk abin da take dashi zasu kare.....



******-------********

Jin inuwar mutum a kansu ne ya sanya su dagowa daga duba littafin dake hannunsu,
Maryam yar Hardejo ta mike tsaye jiki na rawa tace "ina yini, bata amsata ba tace "kira min Mai babban suna,
da sauri ta shiga daki ta kira mahaifiyarta,

kafin su fito maman shaho ta karewa Atika kallo sosai,
a zuciyarta taji dadi da danta zai samu wannan zukekiyar yarinyar a matsayin mata..,

"Gambo kece tafe, Aisha ta fadi tana shimfida tabarmar kara,
ba zama nazo yi ba mai babban suna,
nazo ne in fada miki Shaho yana son bakuwar gidanku,
in Hardejo ya dawo kice mishi yazo ya sami Barde (mahaifin shaho) sai su shirya ayi musu aure yadda addinin Hardejo ya tsara,
"galala Aisha tayi a zuciyarta tace "yau isar har ta kawo kansu,
kafin tayi magana Baffa ya shigo gidan tare da ma'u,
duk abin da ta fadi akan kunnensu,

"ko bakiji abin da nace bane mai babban suna? Gambo ta tambaya tana huro hanci,

karap Ma'u tayi tace "yo ko taji amsar me zata baki,
yanzu ke d'anki har wani d'a ne da zakizo kina hurawa mutane hanci kina nuna iko akan yar mutane,
to walle duk wani iskancinku yazo kurewa,
dan ko sama da kasa zasu hade yarinyar nan bazata auri azzalumi irin shaho ba,
ba Aisha da matan gidan dake tsaye a tsorace ba, har Baffa da yake namiji saida ya kusa sakin fitsari,
dan yasan ahalin shaho gaba dayansu babu imani a tare dasu,
bai bari maman shaho tayi magana ba yace "kiyi Hakuri dan Allahn Hardejo,
kinsan Ma'u bata da hankali,
Da hankali na!! Nace da Hankali na, in sun isa su kas--- toshe mata baki Baffa yayi ya jata dakin Aisha,
hakuri Aisha ta bata hade da tabbatar mata da Hardejo zaizo

Please Login or Register in order to submit comment