Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

musu hidima kamar kar su tafi....




Wannan shine mafarin zaman Nadeeyah da junior a gurin su Taheer..



Da farko da suka koma Anty Saude kin yarda tayi da zaman Nadeeyah a gidan,

Duk da tana kaunar zaman junior haka ta rufe ido dan gudun kar ďanta ya koma gidan jiya,

Saida ya tubure yace shima zai bar gidan sannan ne ta amince da sharaďin bazai taba zuwar mata da zancen soyayyar Nadeeyah ba...


Ba tare da doguwar jayayya ba ya yarda dan a lokacin so yakeyi yaga ya taimaketa ya mayar da ita cikakkiyar mace.....





Cikin sauki yasa Kamal ya turo da result dinta na waec sannan ya fara cuku cukun samar mata makaranta mafi kyau ta mata zalla a canada....



Ba tare da bata lokaci ba ya samar mata ta fara zuwa,
da fari rainon junior yana dan bata wahala saboda yadda karatun yazo mata,
saidai kuma cikin ikon Allah Anty saude ta hanata fita dashi ko nan da can a cewarta rana na matsa mishi...


Soyayya da kauna babu irin wacce junior bai gani ba a gurinsu,
shekararshi daya ta yayeshi a nono saboda wahalar da karatu ke bata,
nan Taheer ya maida ita Hostel saboda ta samu nutsuwar yin karatu,
hutu kadai ke dawo da ita gida...



Hakan ya sanya hankalin Anty saude kwanciya dan taga sam hankalin danta baya gurin Nadeeyah...
a yanzu bata da burin da ya wuce ta hadashi da Amal domin tana matukar kaunar yarinyar,
koda ta sameshi da maganar nuna mata yayi ta jira Amal din ta gama karatu...
a haka dai rayuwarsu ta cigaba da tafiya yau da dadi gobe babu saboda dama haka rayuwar duk dan Adam take...




Ranar da ta kammala karatunta ta fito da sakamako mai kyau Taheer yayi farin ciki matuka domin dama hakan yake so, yana son daga ta gama ta fara practicing aikinta...


A yanzu kuwa Nadeeyah ta zama wayayyar mace wacce tasan yancin kanta,
in ka ganta shuru to a gaban Taheer ko Anty saude take,
amma a school bakinta buďe yake, ko wani irin presentation da defense da ita,
bakinta ya goge sosai da kwararren turanci wanda in tana yi zaka rantse baturiya ce...

Bata kara girma ba saidai ta murje sosai kamar renon turawa.....




Ajiyar zuciya yayi bayan ya gama tunano duk abubuwan da suka faru a baya,

Sai a yanzu sharaďin mahaifiyarshi ya dameshi da ta fara tuna mishi maganar Amal,
yaya zaiyi ya nusar da ita bazai iya zama da kowacce mace bayan Nadeeyah ba,
ya zaiyi da soyayyar da ya dade yana danneta a cikin ranshi..


Juyi yayi ya rungumi pillow kamar karamin yaro,

"Ya Allah karka kawo abinda zai rabani da Nadeeyah..

Abin da ya fadi kenan cikin nukurkusar soyayya,
soyayyarta na cin can cikin ruhi da bargon jikinshi,
daurewa kawai yakeyi saboda baya son ya furta mata taga ko domin haka ne ya taimaketa,


karar agogo yaji alamar hudu tayi,
mikewa yayi ya nufi bayi dan watsa ruwa...


Zuciyarshi cike take da tunanin yadda zai fuskanci duk mutane biyun nan masu muhimmanci a rayuwarshi da sirrin zuciyarshi,


Runtse idonshi yayi lokacin da ruwa ya fara ratsa tsakiyar kanshi,
ajiyar zuciya ya dinga jerowa yana jin wani abu na tsargawa a jininshi..


Wannan abu babu mai fahimtarshi sai wanda ya taba tsintar kanshi cikin matsananciyar soyayya......




Cikin coffee jallabiya ya shirya yayi sallahr la'asar ya fito ya nufi dakin junior dan ganin ko yayi sallar...



Shi kanshi yasan yazama tuzuru domin yanzu kiriss ya rage ya shiga arba'in,
in har zaiyi ma Momma adalci yasan dole taso taga zuri'arshi,
da wannan zancen zucin ya isa dakin Junior wanda yake kusa da na su Nadeeyah..


Daki ne na musamman Anty saude tayi mishi domin faranta ranshi,


Da katuwar kwallo yayi karo a bakin kofa,
can ciki kuma tulin kayanshi ne da ya zubosu daga cikin drawer,
dayan gefen kuma takardu ne na sketch dinshi da katon Allon da ake koya mishi...



Can cikin luntsumammiyar kujerar dake gaban tv ya hangoshi sanye da sky blue riga da jan gajeren wando hannunshi dauke da control din game yana bugawa...

Ta jikin switch din ya kashe tvn ya karaso ya mika mishi hannu,
"Tashi muje sallah,
ajiye game din yayi ya kwantar da kanshi jikin kujera haďe da noke wuya,


Zaro ido Taheer yayi yace
"Sallah fa Junior,
wasa kakeyi sweetheart tashi kaji,
in ka idar da sallah sai muci abinci muje yawo,
cire glass din idonshi yayi ya fara sosa idonshi yana shirin yin kuka,


Hankali tashe Taheer ya zauna ya daukeshi a jikinshi,
"waye ya taba min kai?
Faďa min,

"Mamma..
ya faďi a hankali kamar me raďa,
"Me tayi maka? Faďa min,

kayan dake kasa ya nuna mishi yace
"wai sai na kwashe da kaina ko ta min bulala,
Daddy zan iya kwashewa?


Dariya Taheer yayi yace
"Ina fa zaka iya,
nasan dai ka iya zubarwa amma kwashewa sam bazaka iya ba,
rabu da ita,
zansa Amal ta kwashe,
kuma in zaka sa kaya ka kirani inzo in dauko maka kaji?
Gyaďa kai Junior yayi haďe da rungume Taheer yace I love u Dad...
"love more dear,
tashi muje.....



*********

Sauri sauri ta wanke hannunta da liquid soap dan gudun kar wayarta tayi karni,
kafin ta isa ta dauki wayar har ta kuma katsewa a karo na uku,
bin bayan kiran tayi da sauri,


Saida wayar ta kusa tsinkewa taji an ďaga,


"Hello Aunt Rally!!,


A kiďime ya cire wayar a kunnenshi ya sake duba number me kiran, *M J Canada* sake maida wayar kunnenshi yayi,


Cikin harcen turanci wanda ko me take faďi saita haďa dashi tace "yhu der?
Jingina yayi da ginin gurin dan yadda yaji kanshi ya fara juyawa, samm bazai iya tuna inda yasan muryar nan ba, amma ruhinshi ya tabbatar mishi yanada alaka da mai muryar,
"will call back may be ba network...
kittt.. yaji ta kashe,
bai cire wayar a kunnenshi ba sai muryarta daketa mishi amsa kuwwa...



Gabanta ne ya faďi da ta doso gurin da ta bar wayarta taga Musaddiq da ita a kunne,
cikin dakiya ta zare wayar tace

"Little kai ne yau a gari,
kallo ya bita dashi da kyawawan fararen idanuwanshi,


Karaso ka zauna mana,
ko ka shiga force ne ban sani ba, ta karashe cikin zolaya,


Babu laka a jikinshi ya karaso ya zauna,
zamanshi yayi daidai da sake shigowar wayar,

Dakewa tayi dan kar ya gane ta dauki wayar,
kafin ta kaita kunnenta tace "Maraba da Dikuu,
yau an tuno damu,

Hello Maman junior ya kike?
Ina Daddy na,
da sauri Nadeeyah ta kashe wayar numfashinta ya shiga safa da Marwa..


Ita kuwa Raliya cigaba da wayarta tayi tana dariya kamar dayan bangaren ma ana magana,
saida tayi minti daya sannan tace "Kiyi hakuri inada bako, kanina yazo gida after a long period of time,
to sai na jiki ta ajiye wayar a gefenta..




Diku kaga yadda ka zama kuwa?
kuďi sun zauna ka manta damu,
yaushe ka dawo daga Malay?


Ajiyar zuciya yayi ya fara kauda tunanin mamallakiyar muryar nan,
Shekaran jiya,
Ance Mummy bata da lafiya shiyasa nazo dubata,
me akeyi a gidan ne naga ya cika?


"Bikin Rilwanu almajirin Goggo, Baffa,
ya bashi dakin waje yasa amaryarshi,
walhy stress ne yake damun Mummy,

Yaushe Daddy zai dawo daga Holland? ta tambaya cike da kosawa,
dan taci alwashin in shaa Allahu wahalar mahaifiyarta tazo karshe tunda yanzu kam ta gane kuskurenta fiye da tunani...


Kasumbar daya tara a fuskarshi ya shafa yace
"Zan je in sameshi jibi,
zamu wuce Canada gurin wani taro,
In shaa Allahu next week ko upper zamu dawo tare,
to Allah ya kaimu ta faďi tana mikewa dan kawo mishi abin ci da shi...




Wai ya maganar aure ne Little,
haba, ka zama tuzuru,
komai ya zauna,
ya kamata ace ka ajiye iyali sune cikar mutuncinka..


Zai bata amsa kenan wayarshi tayi kara,
da sauri ya dauka annurin fuskarshi ya karu sosai,


"Habibi! ta faďi cikin shagwaba..

Yess My Baby,
hw r u? ya amsata cikin kulawa..


"Fine sweetheart..


"Yhu sure My life? Ya tambaya cike da kulawa..


"Yeah buh i wanna see yhu,
yadda ta make murya kamar zatayi kuka yasa yayi saurin kashewa dan suyi video call,
tab dinshi ya dauko ya kirata...

Nan take kyakykyawar yarinya yar shekara hudu ta bayyana, gashin nan yasha gyara da jan ribon,
rigar jikinta ma jace mai tsananin taushi,
tana da yar kiba wanda ya kara ma fuskarta kyau...


"Yeyyy Habibi,
i love uu,

"Like wise my angel.. muahhh..

Sai a lokacin hankalin Anty Raliya ya kwanta,

"Nadeeyah ce?,
juyota in ganta,
yar banza in ba iyayenta da kai ba, bata yarda da kowa,
juyo mata ita yayi yana dariya yace

"Matsa mata kukeyi, ku kyalemin matata tayi abin da ranta yake so...



Tana ganin Anty Raliya ta hada rai haďe da turo baki,
dakuwa Anty Raliya tayi mata tace

"Ubanki Hilal kikayi ma,
daga nesa ta hango Hilal yana dariya a gefen gadon yace

"Nagode Anty,
na karba,,


Wai Hilal bazaka zo gurin yan uwa yarinyar nan ta sanmu ta ganemu ba,
wallahi zanzo in dauketa in dawo da ita nan saidai ta mutu da kuka...


Karbar wayar yayi yana dariya yace
"kinsan Allah da kin kyauta, fitinar yarinyar nan sai irinku, gara a ďan gyara mata zama,
Musaddiq ya batata da yawa,
nan fa suka cigaba da hira da Hilal har Maleeka ta shigo ta zauna akayi da ita.......





Uncle...
ta faďi murya can kasa,
Rufe mujallar hannunshi yayi ya fuskanceta sosai,

"Nadeeyah ya akayi?
Kina san wani abu ne?

Girgiza kai tayi tana murmushinta mai sanyi,
takarda ta mika mishi tace

"An gayyacemu wani taro ne a Hallmark..
shine na kawo maka,
buďe takardar yayi ya duba sosai,
ganin karuwarta ce yasa shi cewa Allah ya kaimu ya kuma bada nasara,
godiya sosai tayi mishi ta mike ta koma cikin daki...


Ajiye jaridar yayi ya luntsuma cikin tunani,

lokaci yayi da ya kamata ya sanar ma Nadeeyah abinda ke ranshi,
burinshi ya shawo kan mahaifiyarshi kafin ya gabatar mata da bukatar zuciyarshi...






Momma.. ya faďi haďe da kwantar da kanshi a kan cinyarta,
hannu tasa tana shafa kanshi haďe da cewa yau shagwabar ce ta tashi,
hannunshi ya daura akan nata ya rike sosai,


Momma Junior is lvin us soon,

"Saboda me?
Ina zashi?
Ta faďi da alamun tashin hankali,
ya za'ayi ta iya zama a gidannan ba tare da Mukhtar ba,
inaa sam saidai in Nadeeyah ta siyar mata dashi amma ko sama da kasa zasu haďu bazata taba bata shi ba...
maganar da takeyin ta a zuci ta fito fili,

Wani irin sanyi Taheer yaji a cikin ranshi dan a yanzu shawo kanta bazai mishi wahala ba...

"Momma dole ya barmu,
yana da uba,
kuma itama mahaifiyarshi dole zata barmu tayi aure,
a wani dalili zata bar mana danta?

"A wani dalilin zata daukeshi ta kaishi agolanci wani gidan,
wallahi bata isa tace zatayi aure ta tafi dashi ba,
yadda take haki ya sanyashi mikewa zaune...


"Calm down Momma,
babu abinda muka haďa da Nadeeyah,
ina faďa miki ne dan na kusa maida ita gida,
kuma kinga tunda babu abinda muka haďa bazata bar mana danta ba...


Rau rau idon Anty Saude yayi tana shirin fara kuka,
gaskiya ne Tee babu abin da muka haďa da ita,
amma ai tasan rabani da Mukhtar abu ne mai wahala,
zata wahala dani matuka,
Allah ya daura min kaunarshi a cikin raina..


"Ki kaunaci mahaifiyarshi Momma,
Nadeeyah ba muguwa bace,
bari in baki labarinta,
ta yiwu ki tausaya mata ki barni in aureta kodan mu taimaki maraicinta..
cikin nutsuwa ya bata labarin Nadeeyah wanda saida ya sanyata zubar hawaye,
tausayin Nadeeyah da soyayyar junior ta sanya Anty saude ajiye dukk makamanta, ta yarda da batunshi sannan ta umurceshi da ya sanar da Nadeeyah domin ta kira can Nijar suje nema mishi aurenta..


Cikin jikinta ya shige ya fashe mata da kukan murna,
jikinshi har rawa ya farayi saboda tsabar farin ciki,
Addu'ar da ya kwana yi Allah ya amsa mishi...

Alhamdulillah...
ya dinga jerowa babu adadi.....




Shigar bakar doguwar riga tayi wacce ta ďan kamata ta ko ina,
can kasan shima a tsuke yake saidai a tsage yake dan jin dadin tafiya,
ta yane yellow dankwali a kanta,
dan karamin yellow dankunne ta maķala a kunnenta sai sandals mai tsini yellow wanda a yanzu sashi ya zama sabon ta..


Kamshin da take fitarwa abin dadi ne domin kamshi ne mai ratsa zuciya..

"Haba Anty Amal ba rakiya?
Juyi Amal tayi a kan gado tace "Wallahi Anty Mamma project zan kai karfe tara,
naso zuwa inga yadda zaki ruďa min su,
dariya Nadeeyah tayi ta dauki jakarta tayi waje,



Dakin Amaan ta nufa dan ta dauka shi zai kaita,
a parlor ta hangosu su biyu a tsaye suna jiranta,

Gezna shadda suka sa blue iri ďaya haďe da hula,
sunyi matukar kyau a sanyin safiyar nan...


Da murmushi ta karasa gurinsu, saidai duk ta tsargu da kallon da Taheer yake mata,
samm yaki dauke idonshi a kanta,


Wani irin sonta yakeji kamar ana ingizashi,

"Ina kwana,
Lafiya kalau Mamma!
Ya amsa har lokacin bai daina binta da kallo ba,

Sunkuyar da kanta kasa tayi ta kama hannun junior tace
"Harda kai,
zaka bar Momma cikin kewa ko?
Koma gida,


Noke wuya yayi ya kankame Taheer yace
"Daddy ne yamin wanka dan mu fita,
ni sai naje,

agogon hannunta ta kalla tace "7:40 uncle,
8 zasu fara,

wucewa gaba yayi yana faďin muje na manta ne,
bin bayansu tayi suka shiga motar suka wuce......





Mrs Tijjani Shattimah.....
[11/06 8:35 PM] +234 807 161 1811: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 7⃣3⃣
By *Aysha Ya'u kurah*






Hall din ya cika makil da turawa da bakar fata domin taro ne na karawa juna sani a kasa da professor's suka shirya,
duk wasu dalibai da suka gama makaranta a kowani course an gayyaci mutum daya a cikinsu domin ya wakilcesu,
kaf universities din dake Ontario a law su biyu kadai aka turawa gayyatar,
daga ita sai dan wani makaranta Godwin...




Cikin kwararren turanci professors din suka fara gabatar da abunsu,
bayan sun gama bayanansu aka shiga jefo tambayoyi ga masu professional courses domin asan yadda karatun nasu zai amfanesu,
da doctors aka fara,
sai engineers,
tafi tafi har aka iso kan Barristers....



Tambayace akayi musu na yadda zasu gane mai laifi, kuma cikin kankanin lokaci su wanke marar laifi...



Cikin zazzakar muryarta tace
"Assalamu Alaikum,
Nan fa guri ya dauki shiru har wadanda suke ba musulmai ba,

Cikin kwarewa ta dinga jero yadda za'ayi a fidda mai laifi cikin kagen da aka mishi,
in ta hau kan common law sai ta sakko zuwa islamic law kamar yadda aka koyar musu...




Musaddiq dake cikin masauki yana jiyo komai da akeyi daga Hall din domin cikin Hotel din ne kuma kusa da dakinsu..
bai fara jiyo su daga farko ba dan yana waya da little Nadeeyah,
tun yana daure jin muryar har ta kaishi ga mikewa ya sanya riga ya fita...




Jiki a sanyaye ya bar cikin lodge din ya nufi kofar Hall din,
yana isa gurin tana gamawa,
kai tsaye yasa kanshi zai shiga gurin, security suka dakatar dashi da tambayar ticket dinshi,


Runtse ido yayi saboda takaicin zasu hanashi gasgata zuciyarshi wacce tayi mishi ingiza mai kantu zuwa nan,
yana hango inuwarta tana barin,

"Plss let me in,
its very important, plsss..


Ko kallonshi basuyi ba suka cigaba da karbar pass din wasu,


Ganin bazasu bashi dama ba ya sashi komawa baya ya tsaya,

gaba da toilet din dake kofar shiga hall din ya tsaya,


"Heyy mista,
u can have my ticket!!
Ya fadi haďe da mika mishi ticket din,


Musaddiq bai waigo ya kalleshi yace
"Thanks.. kawai yasa kai zai wuce dan bijirewa umurnin zuciyarshi...



Shan gabanshi Junior yayi cikin fushi dan tun kafin ya shiga fitsari yaga ana wulakanta shi, kuma alamu sun nuna shi musulmi ne tunda Shadda ce a jikinshi duk da baiga fuskarshi ba,
cikin tsiwa yace
"Hey stranger i offered u my ticket nicely,
who are u to refuse m---

Makalewa maganar tayi a makoshin juniir saboda tsabar firgici,

komai dake kan fuskarshi ya gani a ta mutumin,
glass din idonshi ya cire ya zura mishi ido sosai,


Durkusawa Musaddiq yayi cikin ruďani ya tallabo fuskar yaron,
saman idonshi ya shafa wanda ya lumshesu ya sake budesu dan ganin ko gamo yayi,

raba hannunshi yayi akan kuncin yaron ya shiga shafa ko ina nashi,

zuwanshi yatsun hannun yaron yasanya duk ilahirin jikinshi saki,


Duk kyankyamin mutane da junior keyi saboda rashin sabo ya kasa nuna shi ga Musaddiq, saima shafa kasumbar da tayi kwance a fuskarshi da yakeyi,


"Who are yhu....

Suka faďi lokaci ďaya suna nuna juna,
wata irin dariya Musaddiq ya saki wacce bai san sanda ta fito ba,
ďaga kanshi sama yayi ya shaki iskar dake kadawa ya maido da dubanshi gurin yaron da ya gama naďe zuciyarshi,
yatsunshi ya ďaura kan bakin yaron yace

"What is ur name,


Murmushi junior yayi wanda ya sake bayyana kamannin su,
lotsawar da kumatunshi daya yayi shi kaďai ya banbanta su,

"Ur Twinny,
My name is Mukhtar,
*MHK Taheer..*

nd uu.. ya nuna kirjin Musaddiq,

Rike hannunshi Musaddiq yayi cikin wani irin yanayi yace "

*MMK*, Mus-----


Juniorrr...,

cikin gaggawa yace
"Yess Tell me, My Dad is calling me,

Kafin Musaddiq yayi magana wani security ya janye hannun Junior suka wuce,


Yana gab da shiga cikin Hall din ya waigo suka haďa ido,
ďaga mishi hannu yayi haďe da sumbatar hannun ya hura mishi iskaa,

Lumshe ido Musaddiq yayi yana jin kaunar yaron da kamaninsu yazo ďaya har cikin qalbinshi......




*MMK*
*MMK*
sunan yayi ta maimatawa a cikin mota,
tun yana faďi a hankali har ya furzoshi da ďan karfi dan mutumin ya makale a cikin ranshi..


"MMK, who is he Juju?

Kallon Taheer yayi yace
"A stranger Dad,
he looks just like me,
he is my twinny,


"Really...
Taheer ya faďi dan shi gani yakeyi shirmenshi ne,

"Yeaahh baka ganshi bane,
will try nd sketch him tonight..

Dariya Taheer yayi yace
"Allah ya kaimu,
Pizza Hut or restaurant?
Pizza nd ice cream Dad,

kwanar da zata sadasu da Pizza hut ya shiga suka karasa suna dan taba hira da junior,
ita kuwa Nadeeyah dake zaune a baya gabanta sai faďuwa yakeyi tana Maimaita sunan,

*MMK*

*Musaddiq Mukhtar Kyari*...

No no no,
tayi saurin kauda hakan a ranta haďe da runtse idonta....




Duk da bai kware a zane ba yayi kokarin zana fuskar Musaddiq haďe da kasumbar da ta kawata kayunshi,

saidai zanen samm bai fita ba dan yayi yarinta da yinshi...
daga gefe ya rubuta katon

*MMK Mus*

Bayan ya gama ya zura mishi ido har bacci ya daukeshi a gurin....





Madarar da ta shigo mishi da ita ta ajiye akan madubi ta fara tsince kayan dake kasan dakinshi tana mitar yadda kullum yake bata daki,

"Bai yar a kasa ba,
zuciyarta ta yi mata tuni da hakan,
murmushi tayi bayan ta tuno da Musaddiq a baya kafin soyayya ta shiga tsakaninsu har kaddarar rabuwa ta gifta..



Zanen da yayi ta daga ta ajiye a gefe,
ta maidashi kan gadonshi ta tofeshi da addu'a haďe da rufe mishi jiki da bargo,


warm ta maida a.cn dakin mai hade da room heater saboda sanyin garin,
tana gamawa ta tattara takardun dan maidasu mazaunin su,
tana dauko wanda ya zana tayi saurin wurgi dashi haďe da dafe kirji,
Yaya..Musa...ddiq,
ta faďi a hankali idonta ya ciko da kwalla,
dago takardar tayi ta kare mata kallo,
bata san lokacin da zuciyarta ta ingizata ta haďe hoton da kirjinta ta durkushe a kasa ta fara jero kuka mai taba zuciya,

"Yhu forgt all the love,
all the promises,
Why did u lv me,
dis is nt fair, why will yhu remind me of ur existnce,
Whyyy.....???

Ta karashe cikin silent cry mai cin rai...
saida tayi kukan ta ma'ishi sannan tayi ma takardar buya ta musamman inda junior bazai taba ganinta ba.....





A sanyaye ta fito daga ďakin bayan ta kashe mishi wuta,
hanyar dakinsu ta nufa dan babu abinda take son kasancewa dashi sai gado da pillow,
tana gab da shiga dakin taji iska sosai tana kaďawa,
dama tun yamma hadari ya haďu,
ragowar kayan junior dake veranda tayi saurin fita dan ta kwaso,


Tsaye ta samu Taheer ya na kwasosu,

karasawa tayi kusa dashi ta fara tayashi kwashewa haďe da cewa "Ashe ka rigani,
bani in kai su daki,

"Bakiyi bacci ba?

Eh yanzu zanyi in shaa Allah, ta bashi amsa tana cigaba kwashe kayan saboda yadda ruwan ya fara sakkowa da feshi,

Jallabiyar da ta rage ta karshe ta daura hannunta zata cire shima ya daura kan nata cikin rashin sani saboda sauri,

A firgice ta kalleshi ta fara kokarin cire hannunta,
yanayin da ya shiga ya haneshi cire hannun saima sake damkeshi da yayi..

Cikin rawar murya tace
"Uncle ruwa,

duk irin karfin da ruwan yayi shi bai gani ba saboda yanayin da yake ciki,
ya zame mishi dole yau ya sauke duk wani nauyin dake cikin ranshi ko zai samu sukuni,
a hankali ya ďaga hannun haďe da rikoshi cikin nashi,
cike da kasala ya matso dab da ita har yana iya jiyo numfashinta haďe da bugun zuciyarta,

Runtse idonta tayi ruwan dake fesowa ya dinga gangara akan fuskarta zuwa jikinta,
sajen ta da ruwa ya kwantar ya kalla wanda hakan yayi sanadiyyar tashin tsigar jikinshi yayi saurin kai bakinshi saitin kunnenta,

"U promise to be with me years back,
will u fulfill ur promise?
everything is back Nadeeyah,
ur love is back,
i love yhu alot,
Will u marry me?
Plsss Nadeeyah....


Yadda yake maganar a wahale ya sanya jikinta mutuwa tubuss,
ya zama dole tayi ma Taheer adalci,
ya sota tun kafin ta gama sanin kanta,
saboda ita ya kai matakin tuzuru babu aure,
ya kula da ita da danta ba tare da bijiro mata da soyayya ba,
ita kuwa me ya rage mata a yanzu banda ta yarda da nagartaccen miji irin Taheer wanda zata samu nutsuwa a tare dashi,


"Uhmm answer me plss ya sake faďi kamar zaiyi kuka,

kayan dake hannunta ta saki kasa cikin raunanniyar murya tace
"Yess i will,
am all yours Uncle...


Ko babu shaidan a wannan lokacin dole zuciyar da ta daďe da tsumuwa da soyayya ta aikata ba daidai,
kamar yadda bature yace (Everything is fair in love and war)

Taheer baisan sanda ya haďa jikinshi da na Nadeeyah ba,

"Thank yhu Nadeeyah,
Thank u so much,
itama lupp tayi cikin faffadan kirjinshi tana sakin ajiyar zuciya mai karfi...
duk irin ruwan dake zuba yana jika su basu dubashi ba saboda dukkaninsu sun shiga wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa....


Saida zuciyar Taheer ta samu nutsuwa sannan ne ya nemi tsari daga sharrin zuciya ya raba jikinshi da nata,
da sauri ta wuce ciki tana maida numfashi da sauri sauri.....





Cikin kwanaki uku soyayya mai karfi ta wanzu a cikin gidan wanda har saida duk mutanen gidan suka gane,

Amal da ta sawa ranta auren Taheer tayi gaggawar cirewa dan tasan dama tuni Nadeeyah yake so,
a take tayi wa kanta addu'ar samun duk abin da zai zamo mata alkhairi....



Ga mamakin Nadeeyah sosai Anty Saude ta sake mata ta dinga lallabata tana nuna mata kauna ta musamman..
Hakan ba karamin daďi yayi ma Taheer ba..




A daren ranar alhamis suna zaune dukkansu a parlor Taheer na yanke ma junior farce yana tsoma baki cikin hirar tasu....



Kallon shi Anty Saude tayi tace "Munyi magana dazu da kawu Tidjani,
na faďa mishi maganar zuwa neman aurenka,
na sanar dashi ina son ayi komai cikin sati ďaya dan banasan wata matsala ta biyo baya,

Mikewa Nadeeyah tayi ta wuce ďaki da sauri,


Dariya yayi yace
"Sai su taho ranar sati dan mu haďu tunda gobe zamu tafi,
ni zanso ma a ďaura auren a ranar Mommah tunda babu wani shirin da ya rage..



Buďe baki tayi cikin mamaki haďe da sakar mishi dakuwa,

Dariya yayi sosai ya dauki Junior suka wuce dakin Nadeeyah......






*******
*Kaduna*


Toshe hanci Raudha tayi kamar zatayi amai,
hawayen idonta ta share tace

"Ya Allah ka sassauta mana,
mun wahala iya wahala,
mun gina ramin mugunta mun auka ciki,
wuyar da muka so wata tasha ita muka haďiya har na tsawon shekaru takwas...

Audugar da ta share ruwan ciwon dake fita a jikin Goggo ta yar

Please Login or Register in order to submit comment