Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace "to ya zakayi, saidai ko dan mu fita kunya a hada auren da Zainabu,
kaga shikenan asirinka a rufe,
ita kuma tunda rayuwar da ta zabarwa kanta kenan shikenan sai taje can tayi,
dan taga tana da farin jinin ne,
in kayi tafiya itace wannan saurayi itace wancan,
cike da bacin rai Baffa ya hau kan zancen Ma'u ya zauna,
ya fita yanata sababi cikin zuciyarshi..
bai nemi shawarar mukhtar ba dan baisan samm ya rasa shi a matsayin siriki saboda tarin hidimar da yakeyi mishi,
gurin daurin auren yaje ya zauna aka fara gudanar da auren kamar yadda addini ya tanada,

saida aka daura aure akayi komai sannan maroki ya fara fadin, "Tuwon girma miyarsa nama,
yau naga auren da ban taba ganin irinsa ba,
jama'a ku shaida an daura auren *ZAINAB* DA *MUNTARI* akan sadaki naira na gugan naira har naira Dubu Uku....

Ba Mukhtar bane kadai ya girgiza, hatta Mahaifinshi saida ya tafi tunanin Zainab ko Suwaiba......



Mrs Tijjani Shattima.....
[07/03 2:02 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣0⃣
By *Aysha Ya'u kurah*




Alhaji ku yafe ni!,
na yanke hukunci ba tare da neman yardarku ba,
dan Allah ku gafarce ni,
nayi hakan ne dan in fitar damu daga kunyar jama'ar da muka gayyata,
Baffa ne ke jero musu bayanan ban baki lokacin da suka kebe da Alhaji Garba yayi mishi tambayar dalilin sauya akalar daurin auren,
share hawaye yayi ya cigaba da cewa, "yarinyar nan taso ta wulakanta ni, sai Allah yasa ina da 'ya'ya matan da basuyi aure ba,
kuma bana son mutum kamili kamar Muntari ya subuce min,
da zainab da Suwaiba duk daya ne, uwa daya uba daya suke, dan haka kaga wanda yazo daukar suwaiba kuma ya samu zainab ai duk daya ne tunda tsatso daya suka fito,

kasa Magana Mukhtar da zuciyarshi ta kai kololuwa gurin bacin rai yayi,
har lokacin baiji ko daya daga kwatan son da yake ma Suwaiba ya fita a ranshi ba,
da yaji Babanshi na kokarin amincewa da batun yayi saurin cewa "Abba, dan Allah kuyi hakuri,
ni suwaiba kadai nakeso,
in aka daura mana aure da ita nasan zata hakura ta zauna dani!

"Naso yin hakan,amma abin yaci tura saboda guduwa tayi tabar gidan, Baffa ya karashe cike da damuwa,
wani abu Muntarin yaji ya soki kahon zuciyarshi,
har kiyayyar ta kai haka,
ta ina ya gaza da ya samu macen da ta nuna mishi irin wannan kiyayyar,
me ya rasa,
babu abinda bai mallaka ba na daga dangin kyau, ilimi, gayu, uwa uba arziki na jama'a da kuma na dukiya,
me yasa Suwaiba zata rusa tanadin da yayi wa rayuwarsu, yanzu kenan dukkan mafarkinshi zai zamto cikakken mafarki, kenan babu ko daya a cikin mafarkinshi da zai zamto gaskiya,
baisan Hawaye ya fito a cikin idanuwanshi ba saida yaji duminsu a kuncinshi,
mikewa yayi ya fita zauren hade da share hawayen fuskarshi,
motar da suka zo shi da abokanshi ya shiga hade rufe fuskarsa dan hawayen sunki daina zuba,
Allah ya sani ba karamin so yake yi ma Suwaiba ba....


Godiya sosai Baffa yayi wa Baban muntari saboda fahimtarshi da yayi,da Kuma alkawarin da yayi mishi na yarshi bazata wulakanta a cikin zuri'arshi ba,
ko yana so ko baya so dole ya karbeta hannu bibbiyu a matsayin matarshi,
dan zuri'armu kaff babu me wulakanta mace...



Sai dare suwaiba ta dawo gida lokacin Ma'u na buduri da makota ana shirin kai Zainab dakin miji,

kallo ne ya dawo kanta,
daga mai yi mata habaici,
sai mai yi mata kallon marar hankali,
dakin Baffa ta shige a darare, zaune ta sameshi yayi tagumi yana tunanin ta inda zai fara neman suwaiba,
jin muryarta ne ya sanyashi waigowa da sauri,
sanyi yaji a zuciyarshi da ya ganta lafiya kalau,

a fili kuwa fada ya rufeta dashi, saida yayi mata cin mutunci sannan a karshe yace "Wallahi, wallahi, kinga rantsuwar nan, bata da kaffara, bazaki kara daga kafarki kije makaranta ba,
kina cikin gidannan har sai na samu wanda zan bawa ke sadaka, ke ba takamarki kinada farin jinin samari ba,
kin daukesu kamar rigar canji,
to ki sani kin jawa kanki a gurina,
fita ko nan da kofar gida ne ban yarda kiyi ta ba,
sai ki zauna a gidan tunda kin zabi butulcewa Allah da ni'imar da yayi miki,
tashi ki fita ki bani guri mutuniyar banza mutuniyar hofi,
tashi tayi ta fita da gudu tana rusa kuka,
a kofar dakin tayi karo da masu kai Amarya ana wakar "Ayye mama",
ta gefensu tabi ta shige dakinsu ta kara bude wani sabon babin kukan.... (oyoyo talauci inji Meela)





Rayuwar auren Zainab da Muntari kadaran kadaham,
sam baya wulakanta ta saboda ya karanci hakkin mace akan miji, kuma mahaifinshi ya sake tunasar dashi,


Da fari ta dan samu matsala da mahaifiyarshi domin sam bata san zainab,
gani takeyi an lika mishi ita ne dan a cuceshi,
saida "Abba" yayi mata nasihar cewa matar mutum kabarinsa, kuma wata bata auren mijin wata,
sannan ne ta dan sakko,
amma duk da haka bata cika bata muhimmanci ba,

biyayyar da zainab ke mishi ne ya sanya shi sake sakewa da ita,

wani lokaci yakan tuna suwaiba wani shashin zuciyarshi yaji yayi mugun tsanarta,
wani shashin kuma yaji ta ciki a killece,
ya sha in zai ambaci sunan zainab yace suwaiba,
in ko yayi tafiya to fa sai ya cirewa suwaiba tsaraba,
kome zaiyi da ita yake hadawa yayi,

wannan abu shi ya kara dungunzuma zuciyar Zainab taji gaba daya Suwaiba ta fice a ranta,

kullum cikin kulli Goggo take dan dai kawai kar auren yarta ya mutu,
a irin zaman da sukeyi Zainab ta samu ciki har ta haihu, haihuwarta ita ta kara daraja ta a idon iyayenshi da shi kanshi,

sannu sannu ya fara fitar da Suwaiba a cikin ranshi, saboda samun zuri'a da ya farayi.

Saida Zainab ta jera mishi 'ya'ya Mata uku a karancin tsakani (gwarne ) cikin shekara hudun aurensu,

Reemah ce Babba,
sai Radiya
Sai Raudha,

a lokacin da take da cikin na hudu ne Muntari ya saduda ya mika mata ragamar rayuwarshi,
domin yasan yanzu indai za'a kirashi to itace ta biyun da za'a kira a rayuwarshi....




Ita kuwa suwaiba baiwar Allah ta zama baiwa ta gidi,
komai na gidan ita takeyi,
babu makarantar islamiyya, babu fita cikin gari,
iyakarta shagon buzu Adamu mai gadin jikin gidansu,
duk irin kyawun da ta ke dashi ya disashe,
rayuwar dai yinta kawai takeyi saboda Allah a hakan yaso ya ganta,
kullum saidai tayita yi mishi Godiya da bai daura mata ciwo ba....



Leemah kuwa ta zama yar gayu sosai,
university take zuwa Abu zaria,
babu abinda zatace tana dauka a makaranta,
ita dai kawai ta shiga gayu,
yau ta tsaya da wannan gobe wancen,
Baffa daga yayi niyyar yi mata magana Ma'u zata hanashi,
takan ce in ba'a barta taje makaranta ba ina zata samu mijin aure,
dole badan yaso ba ya barta tayi abin da taga dama..




"Bani omo malam Ado, !
dauko mata kullin bulan omo biyar yayi yace "jeki kiyi amfani dashi, na bar miki kudin ki siya silifas naga naki ya tsinke,
murmushi tayi tace "nagode Adamu,
"ba komai suwaiba kedai ki daina yawo ba takalmi,
gyada mishi kai tayi ta wuce cikin gida,
kallo ya bita dashi hade da girgiza kai cike da tausayawa,
duk wannan abun da sukayi a idon Baffa wanda yazo shiga da mota gida,
wani abu ya darsu a ranshi ya shiga gida yayi parking...



"Kanason 'yata Suwaiba?
Daburcewa Adamu yayi da yaji tambayar yace "a'a Alhaji,
ai tafi karfina,
in ba cutarwa ba ta yaya zan auri mace cikin gata alhali ni din ba kowa bane,
dariya Baffa yayi yace "in dai kanajin zaka iya zama da ita to zan aura maka ita,
washe baki Adamu yayi yace "suwaiba mace ce mai kawaici da hakuri Alhaji,
waye zai kita a matsayin mata, bana tunanin akwaishi,

murmushin farin ciki Baffa yayi yace "kaje ka shirya,
rana ita yau zan daura muku aure,
godiya sosai Adamu ya tsuguna yayi ma Baffa sannan ya wuce cikin gidan da yake gadi dan sanar dasu....




Koda ya fada ma Suwaiba nan take ta amince saboda a ganinta gara taje tayi bauta mai dalili, domin ta gaji da aikin jakin da takeyi....






Ranar da aka daura auren duk wani masoyin Suwaiba saida yayi mata bakin cikin karewa da kaskantaccen mutum irin Adamu mai gadi,

shi kuwa Muntari gani yakeyi Hakkinshi ne ke bibiyarta shiyasa ta dade batayi auren ba a karshe ta auri mai gadi...





Rayuwa mai cike da jin dadi da rufin asiri daidai gwargwado sukeyi,
gidan da ya dade yana tari ya siya mai dauke da daki biyu da kitchen nan aka kaita,
sosai take jin dadin zama dashi dan dama sun saba,

shekararsu biyar da aure ta samu cikin Hafeez bayan ta fidda rai,

lokacin Zainab Mummy ta haifi yarta Raudha,
dakatar da haihuwar tayi ta hanyar allura saboda ita a ganinta in dai zata cigaba da haihuwa tofa tabbas mata zata haifa,
wannan jinin zuri'ar mahaifinta ne kamar yadda suka canfa,

a lokacin da aka haifi Hafeez ba karamin girgiza mummy tayi ba, ta dinga tambayar suwaiba yadda akayi ta samu namiji a haihuwar farko wanda saidai tajishi a gari ba'a zuri'arsu ba,

ko da ta tambayeta saidai tayi murmushi tace "daga Allah ne,
tun daga haihuwar Hafeez abubuwa suka fara dan ja baya saboda mai gidan da Adamu ke gadi ya bar garin,
jikin gidanshi ya manna shagonshi da babu isassun kaya a ciki,
dama da albashin shi yake cika shagon yayi hidimar gida,
babu wanda a cikin yan uwanta yake taimaka musu, a ganinta basai ta fito ta fada ba sun san bata dashi...


Shekarar Reemah 15 ta tafi karatun gaba da secondary sokoto,
hazakar ta tasa aka dinga promoting dinta har Allah ya kaita jami'a, anan ne ta hadu da Gaddafi dan 400l,

sanadiyar haduwarsu saboda ya kasance hazikin da ake ji dashi a engineering department,
ko wani irin science course ya iya, kuma yana koya musu dan su biyashi ya samu na siyan hand out,

zuwan Reemah ne yasa suka shaku,
itace siyan hand out da komai nashi,
shiyasa baya kasa a gwiwa gurin kowa mata karatu,
ko da ya gama makaranta ya fito da first class babu wanda ya lura dashi bare yayi yunkurin bashi aiki,
ajiye takardunshi yayi ya dawo cikin school yana hada tutorial dan a dinga biyanshi,
tausayinshi yasa Reemah tayi ma Daddy magana har ya amshi takardunshi ya samar mishi babban aiki a lagos,
tun daga lokacin kauna mai karfi ta kullu a tsakaninsu har ta kaisu ga aure...



A shekarar Farko Allah ya azurta ta da ciki,,
lokacin Mummy ta fidda rai da haihuwa saboda dadewar da tayi, bata san akwai dan makale a tare da ita ba,

Tsirar Haihuwar su kwana tara ne,
domin Reemah ta haihu da kwana tara Mummy ma ta haihu, wannan abun ga mutanen "Da", bawani abun kunya bane,

murnar Samun Musaddiq ba a gurin mummy bane kadai,
har da kakanninshi da babanshi da ya dauki dukkan so ya daura mishi, gata babu irin wacce (Mukhtar) Hilal da Musaddiq basu gani ba, babu tafiyar da Daddy zaiyi ba tare dasu ba..



Kamar yan biyu haka suka taso, kansu daya, kayansu iri daya, kamanni ne kadai suka banbanta shi Hilal fari ne musaddiq kuma Baki ne irin bakin barebari,
gasu da jikin girma Masha Allah, komawar su Reema Cypros ne ya raba su, amma kafin nan koda yaushe suna yare.....




Bangaren Halima kuwa tunda tayi karyar makaranta sun tura ta china karatu shikenan su Goggo suka hau suka zauna ba tare da bincike ba,

yawon barikinta ta tafi yi da kuma neman kudi,
saida ta zama hamshakiyar kanta sannan ta waiwayi gida bayan shudaddun shekaru,

ko da ta dawo saida ta gyara gidansu dan acewarta bazata iya zama a irin gidan ba,


Sana'arta ta business ta cigaba dayi tunda dai yanzu ta gama rikewa tasan babu wanda zaizo yace zai aureta,
abu daya gareta wanda za'a yabeta dashi
shine duk irin duniyancin ta bata yarda da karunwanci ba saboda shegen kyankyami gareta,

shekaru da dama bayan dawowarta ta hadu da wani mayaudarin yaro mai tsantsar *SIHRUL KALAM*
a take ya baibayeta ta fada tarkon kaunarshi,
bata tsaya dogon bincike ba ta yarda ya aureta, hatta sadaki ita ta biya mishi saboda shaukin samun wanda ya furta mata kalmar so...


Sai bayan auren ne ta gane yaudararta yayi,
yazo ne kawai dan ya kwashi dukiyarta yayi gaba,
ko da ta fahimci haka bata dauki zafi ba dan ita mai bashi dukiyarta ne,
abin da ya tsiro dashi na shigowa da mata gidane yafi tunzurata har ta kai ga aikata kisa a gareshi cikin rashin sani,


A kotu ne aka fahimci cewar tana dauke da cikinshi na wata hudu, koda ta fahimci hakan saida taci kukan dana sanin zuciyarta marar kyau,
Kotu bata yanke mata hukunci ba har sai ta haifi dan dake cikin ta ta yaye,

haka kuwa akayi har cikinta ya isa watan haihuwa,
kamar hadin baki dukka ukun ya'yan Baffa cikin garesu,

Husna aka fara haifa, washe gari Nadiya ta biyo baya,
haihuwar Badariyya tayi gardama saida aka yanka Leemah,
ba karamar wuya Badariyya ta ba mahaifiyarta ba,
bayan awanni da yi mata aikin aka fahimci jikin nata babu dadi,

cike da kwarewa doctors ke aikinsu amma ina abin yaci tura, aikin mala'ika da na mutun ba daya bane,
Ashe leemah ajalinta ta auro har ta haifo mishi 'ya,
ba karamin tashin hankali duk suka shiga ba na rashin yar uwarsu, musamman Goggo da tayi karamar hauka...
mummy ce ta dauki Badariyya ta hada da Husna ta shayar dasu cike da kulawa...



Tun a karancin shekarun 'yayan suwaiba suka fahimci zumuncin zuri'arsu sai in kana da kumbar susa, marasa wulakantasu aciki kadan ne....


Rayuwa Badariyya tun tana karama ta tashi a sangarce, bata ganin mutunci ko jin kunyar kowa,
Hilal shine wanda tun fil'azal basa shiri, a gurinshi tasan ba mummy bace ta haifeta,
ranar yaci dukan tsiya a gurin mummy,
Tana gama dukanshi ya fita dan ko a jikinshi dama so yakeyi ya nuna mata ita fa ba yar gidansu bace ta daina kusu fi'ili......


Da wannan labarin zumunci ya faro,
sila itace mace,
uwa,
wacce take da daraja,
wacce Allah swt ya bata ragamar tafiyar da zuri'a,
lallai Macce ta gari itace ginshikin alumma,
domin gyara rayuwae ya mace kamar gyara alumma ne,
mu dage tun yanzu gurin yi ma 'yayanmu maza adduar mace ta gari domin wayau ko dabara bazai basu ba,
sukuma yayanmu matan ka sanya su zamto Mar'atus saliha ga mazansu.....


Mrs Tijjani Shattimah....



[08/03 12:28 AM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣1⃣
By *Aysha Ya'u kurah*



_HAKKI, HAKKI BABBAN ABU NE YAN UWA, KOMIN KANKANTARSHI MU GUJI DAUKARSHI DAN KANANAN ZUNUBBAI SUNFI MANYA ILLAH, DAN ALLAH MU KIYAYE HAKKIN JUNA_


*Cigaban Labari*



Jiki a sanyaye ta dauko sarkar dake cikin akushin tayita juya ta a hannunta,
tasan Baffa ya dade da mantawa da zaman sarkar shiyasa tayi mata muguwar ajiya,
ko da wasa bata taba yunkurin sata ba,
tun da taje ta tambayi kudin sarkar taji kudi ne masu tarin yawa ya sanyata kara yi mata kyakykyawan ajiye,
ajiye sarkar tayi hade da tagumi. ya zame mata dole ta nuna musu gaskiyarta, shiyasa ta fito da sarkar dan bawa su Nadeeyah gadonsu,
tasan wannan ita ce kadai mafita a gareta da diyarta,
tasan in tayi hakan Muntari bazai yi mata zargin muguwar uwa ba,
zaiyi mata kallon mai amanar da ta iya rike abu mai daraja saboda soyayyar uwarsu,
wannan hanyar ita kadai ce abin da zai samar mata mafita...


Rufe akushin tayi bayan ta dauko wasu magunguna a ciki,
inda ta daukoshi nan ta maidashi ta fito parlor ta dauko leda mai kyau ta zuba sarkar a ciki, sannan ta shiga yin amfanin da magungunan domin rufewa su Daddy da sauran baki....




*1:51pm*

Motaci uku ne suka shigo cikin harabar gidan Baffa,
Motar Anty Reemah ce ta fara shigowa, sannan sauran kannenta suka rufa mata baya,

Raliya ce zaune a gaban motar Anty Reemah, sai Zainab (kanwar Nadeeyah) da Hinad,

a motar Radiya aka tara taron marasa mutunci,
Raudha da Badar,
Cikin kunci Badar take saboda Nadeeyah da Husnah sun shiga motar Hilal,
duk yadda taso taja Husna suzo a mota daya taki saboda farin cikin tayin da Hilal yayi mata na shiga motarshi,
ko kallon motarsu batayi ba ta wuce cikin gidan tana huci,
a zaune ta samu Goggo hannu rike da carbi tana ja,
Allah kadai yasan abin da take furtawa domin janshi kawai takeyi,
babban tashin hankalinta bai wuce kar Baffa ya fada musu komai na labarin Atika ba,
burinta su sameta ita kadai ta hada musu kirkirarren labari ta fada musu saboda tseratar da auren yarta,
jikin ta Badar ta fada ta fara zuba mata shagwaba,
gyaran murya Goggo tayi ta mata nuni da carbi alamar ja takeyi,
sauka tayi ta daura kanta a kan cinyarta,
damuwar da Goggo take ciki ta hana ta fahimtar damuwar dake kan fuskar yar lelenta...

Sallamar su Anty Reema ne ya sanya Goggo sakin Murmushi hade da tattara hannu guri daya tana musu gaisuwa dan su gane carbin take ja bata son a katseta,

neman guri sukayi suka zauna suka bude flow din hirarsu ta kasuwanci,

shigowar su Nadeeya ne ya katse musu hirar saboda yadda Goggo ta yafito su da hannu ita da Zainab,
a darare Nadeeyah ta sauke zainab suka matsa kusa da ita suka durkusa zasu gaisar da ita tayi saurin durowa daga kan kujerar ta hadesu ta rungumesu hade da kuka mai karfi,
"Allah sarki Suwaiba,
ganin jininki ya tuno min ke,
inama ni mutuwa ta dauke ta barki cikin 'yayanki,
inama zan juyo da hannun agogo baya da na nuna miki irin muhimmacin da kike dashi a cikin rayuwata,

cike da mamaki daukacin mutanen parlon ke kallon Goggo,

Ciki kuwa harda Baffa da ya sanyo kanshi cikin parlon ya tarar da abun da idanuwanshi basu taba tozali dashi ba,
yaran da ko cikin parlon basa samun albarkacin shiga bare har su samu darajar runguma,

wani dadi ne ya ziyarci zuciyarshi yayi tunanin mutuwar Suwaibar ce ta kadata haka,
da sallama ya katse shurun mamakin yace "yau gidan nawa cike yake da matana kenan,
sai wacce na zaba,
Murmushi dukkansu sukayi suka gaida shi hade da cewa ai dukkan mu zaka hada,

Badariyya ya kalla da ta rike kanta saboda bugeta da Goggo tayi gurin sakkowa daga kujera,
"a'a Amaryata me akayi miki naga kin rike kai?
sakin kan tayi ta turo baki tace "ba Goggo bace ta bigeni, kallonta Goggo tayi tace "yi hakuri Badariyya ban kula bane, hankalina nakan marayun Allah, babu uwa babu uba, kai wannan rayuwa abar tsoro ce,

Anty Reemah da abun ya bar bata mamaki tace "dama haka ne Goggo,
Allah baya barin wani dan wani yaji dadi,
ta yiwu mutuwar ita kadai Allah ya ga zata zamto hutu a garesu, shiyasa yayi gaggawar daukesu, Allah sarki Mama Suwaiba,,

wani kukan Goggo ta kuma kecewa dashi tana dada kankame zainab,
kallon tsoro zainab din take mata shiyasa ta saki kuka ta fisge kanta ta koma jikin Nadeeya,

share ma juna hawaye sukeyi gunin tausayi,
shigowar su Mummy dakin ne yasa duk suka mike domin bawa Daddy gurin zama,
bayan yan gaishe gaishe Baffa yace " yau gida yayi albarka, dariya Daddy yayi ya tsuguna ya gaishesu,
bayan yan hirarraki Daddy ya gabatarwa da Baffa dalilin zuwansu, ya kuma kara da cewa "kayi hakuri Baffa nayi maka shishigi a cikin alamarin gidanka,
inason sanin dalilin kiyayyar ne saboda yana neman zama min matsala a cikin Zuri'ata...



Kuka Goggo ta saki tace "Babu kiyayya cikin zuri'ata da na gina ta shekara da shekaru,
kasan zumunci yanzu ya zama na yan zamani,
amma ni a gurina kowa daya yake,
bana banbanta su,,
gyara zama Daddy yayi yace "nasan bakya banbanta su, domin dukkansu 'yayanki ne babu bare a ciki, amma ya kamata ku tsawatar akan yadda akayi ma zumunci rikon sakainar kashi,
bana san yadda abubuwa suka kasance a nan gidan su kasance a cikin 'ya'yana,
bazan dauka ba,
inason 'yayana su fahimci muhimmancin mai shi da marar shi,
banason dattin duniya ya zamana sillar yankewar zumuncin 'ya'yana,
shiyasa nazo a warware min komai kuma ayi ma tufkar hanci,

Gyaran Murya Baffa yayi zai fara Magana Anty Reemah tayi saurin cewa "yi hakuri Baffa zan katseka, dan Allah so nakeyi ka fada mana wacece *ATIKA*
a duburce Goggo ta waigo ta harareta ba tare da sun hada ido ba,
a zuciyarta tace "kaji shegiyar yarinya, ana neman kai magana karshe ba tare da an bullo da maganar Atika ba ta sako zancen ciki,
kara gyara zaman carbinta tayi tana kallon Baffa dake shirin basu labarin Atika....




Kuka sosai Nadeeyah da Hafeez sukayi najin ba Goggo bace ta haifi mahaifiyarsu,
ashe dalilin kiyayyar kenan,
sun sani tabbas in har uwa daya suke dasu Mummy bazasu taba wulakanta mahaifiyarsu ba ko da kuwa mijinta yafi *KAMAYE* talauci


Shi kuwa Daddy banda daurewar kai zuciyarshi ce ta tafi tunanin lokutan da ta dinga mishi magiya akan ya janye maganar aurenta,

kalaman Abbakar ya shiga dawo mishi " *Kyari, yarinyar nan tana cikin matsala, anya kuwa mutanen gidannan su suka haifeta? "Ko a makaranta bata hutawa saboda hidimar yar uwarta, yadda kasan baiwa haka suka maida ta, ina tunanin yar riko ce, ka bita a hankali ka lallabata zaka fahimci daga inda matsalar take, walhi ta bani tausayi matuka saboda yadda naji tana kuka kamar ana yankan naman jikinta*
dana sani marar amfani ne yayi mishi dirar mikiya cikin zuciyarshi,

muryar Goggo ce ta katse tunaninshi,
cikin kuka ta fito da sarkar da ta zame mata mafitar karshe da zaisa ta fita a zargi ta damkawa Hafeez a hannu, tace "wannan sarkar Kakarku ce da mahaifiyarku ta gada,
nayi nayi suwaiba ta karba taki, yanzu gashi bata raye dole in sauke nauyin magada a kaina,

kallon sarkar Baffa yayi ya share hawayenshi yace "Samun mace mai rikon Amana irinki sai an tona Ma'u,
nagode da rike min Amana da kikayi,

Anty Reemah dai kallonsu kawai takeyi hawaye yaki tsaya mata,
tuno irin ukubar da mama Suwaiba tasha takeyi,
babu abinda bata sani ba na daga halayyar da kakarsu kewa mama suwaiba da ahalinta,
wannan shine dalilin da sanyata take matukar kauna da tausayinsu...

Labarin halin kirkin Suwaiba Goggo ta dinga fadi saboda dai ta wanke kanta a idon Daddy,
shi kuwa ya gama fahimtar komai tun da yaji cewar ba ita ta haifeta ba,
sai Gab da la'asar suka fara shirin tafiya,

kallon Aljihun Hafeez Goggo ke tayi tana tsine mishi a ranta,
wato ma bazai ce mata ta ajiye musu sarkar ba,
taso hada baki da Mummy su karbe sarkar taga mummy ta kanta takeyi,
burinta kar Daddy ya canza mata...
ko da ta fito waje ya riga ya shiga mota har ya tada ta yana kokarin tafiya, da sauri ta karasa ta shiga ciki tana mishi kallon tsoro da mamaki....







*GOMBE*

Uncle Abdallah..
Kawu Abdallah...
Sweet Papy Abdallah


Ajiye takardun hannunshi yayi yace "Ruwaidah problem,
ta dawo makaranta yanzu fa babu wanda zai huta,

kafin ya ankara yaji ta fado jikinshi,
nishi yayi da karfi yace "Ruwaida ai sai ki karya ni,
baki san yanzu kinfi *OBENIZA* girma ba,
dagashi tayi hade da bude baki tace "Papy Obe what?
Hancinta ya ja da karfi yace "OBENIZA,
bata rai tayi ta fara daga hannun rigarta tace "yanzu Papy har girmana ya kai na Obeniza ben?
Wallahi sai na hadaka da *Anni* !
nan ta bar jakar islamiyyarta ta ruga cikin gida da gudunta tana kiran Mamy nd Anni da iya karfinta,

Jamal ne ya fito daga daki hannunshi rike da Game yace "problem child is back again,
tana zuwa zata gifta dakinshi tace "Yaya Jay,
wai dagaske nakai girman obeniza ben?
Kallonta yayi sama da kasa yace "to ai an cuci obeniza ma da ake hadaku,
kinfi shi girma sau goma, hannunta ya kamo hade da rike kunnenta yace" warning na fito in miki,
yau sunday,
wallahi in kika kuskura kika dameni a gidan nan sai na kusa maida ke jaka dan duka,
salin alin kije kiyi baccin rana kafin a kira la'asar,
da fatan kinjini

Please Login or Register in order to submit comment