Join Our WhatsApp Group

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

Login Register

yayi murnar ganin Zubair yaci,
sam matarshi bata da masaniyar ya amshi takardun yaron,
kannenta wadanda suke ciki daya ta bada takardunsu ta zame na Zubair,
da yake Allah shine ke taimakon bawa, gashi Allah ya bashi sauran kannenta basu samu ba,

Allah kenan mai kyauta a gurin wanda yaso a lokacin da yaso,

Hotel ya kamawa Musaddiq bayan ya gama ture turen takardun su ta computer zuwa lagos,

kwanciya yayi yana mika saboda gajiya,
ga yunwar da ta addabeshi,

wanka ya shiga dakyar saboda tsabar gajiya,
bai taba irin yawon da yayi yau ba,
duk block din cikin Towers saida suka kewaye shi,

da ruwan zafi sosai yayi wanka hade da alwala,

yana idar da sallah ya janyo jakarshi,
ledar da Nadeeyah ta bashi ya fara karo dashi,
da sauri ya bude,
naman da suka soya na walima wanda aka basu suka ajiye cikin microwave shi ta dumama mishi tayi foiling tasa a leda,
zafi har yasa naman ya fara nakewa,

zai fara ci kenan yaji an buga kofar dakin shi,
abinci ne aka kawo mishi wanda ya tabbatar zaiyi wuya ya iya cin shi,
karba yayi hade da mishi godiya,

ajiyewa yayi ya fara juya salad din,
da sauri ya ajiye cokalin ya dauki juice din dake kai,

Naman kadai yaci ya hada tea,

yana idar da Sallar isha'i ya janyo wayarshi da ya soka ta a charge,
23missed calls ya gani ya fara dubawa,
na Daddy da Mummy ne a sama sai Hilal, Badar, Nadeeyah da Husnah,

Daddy ya fara kira sukayi murnarsu sosai sannan ya mikawa Mummy wayar itama tayi murna sosai hade da yi mishi adduo,i,
cike da murna sukayi Sallama ya kira Hilal,

Sunfi minti goma suna hira yana mishi fada akan ya dauki aikinshi serious,
"banda baccin asara dan nasanka, baka cika daukar abu serious ba,
dariya Musaddiq yayi yace "yau ma dakyar na tashi,
saida Nadeeyah toshe min kunne ta kusa kasheni,
yarinyar nan bata jin magana, but ta kyauta fa,
gashi Allah yasa nazo akan lokaci kuma na samu nasara,

saida Hilal ya danji abun a ranshi,
kauda mugun tunanin da shaidan ya kawata mishi yayi saurin yi hade da cigaba da hirarsu....

Game yakeyi yana juyi akan gado bacci na dan fisgarshi kadan kadan,
karar wayarshi ce ta sa ya watstsake ya dauka,

"congrat yayana, Husnah ta fadi da karfi har saida ya cire wayar a kunne,

"Thanks sis, baku kwanta ba?,

"10 fa yaya,
har ka fara bacci ne?

Juyi yayi yace "ummm na fara,
to ga Nadeeyah ku gaisa ta mika mata wayar da sauri,

"Congratulations, Allah yasa ka fara sa'a, ya kaika matakai masu daraja a cikin aikinka,

Sosai yaji dadin da ya rasa ko na meye,
dadin jin muryarta da yayi ko kuma na adduoin da ta jero mishi,

Ameenn My PS, ya fadi ya lumshe ido,

Dariya tayi tace shi PS din meye shi?

"Problem solver,
nayi missing dinki sosai,
furta kalmar yayi cikin gushewar hankalin mai bacci, bude idonshi yayi yace "naman da kika san min ya taimakeni, wani abinci suka bani kamar tsutsa, na kasa ci,

Murmushi tayi mai sauti tace "haka nan zaka koya, aiki fa zaka fara,
dole ka koyi cin abincin waje tunda ba'a gida bane, da haka zaka saba, Shuru yayi yana jin muryarta na ratsa ko ina na jikinshi, saboda tsabar dadin murayarta da yakeji har bacci mai cike da mafarkai ya daukeshi ba tare da ya sani ba......

Washe gari Dr Barau yace su shirya tafiya lagos,
badan yana so ba haka ya daure suka tafi,

A can ya sai kayyaki dan sun ma fada mishi tafiyar kwana bakwai ce,
wahala iya wahala babu irin wace Musaddiq bai sha ba, nuna musu abubuwa akeyi ana koya musu yadda zasuyi ayyukansu,

kwanansu takwas cirr suka dawo gida dauke da takardunsu na offer da komai nasu na accomodatio, wardrobe money da sauransu,
tun a jirgi Musaddiq ke kiran wayar kowa a gidan bata shiga, dakyar ya samu number Malam Ali yace ya fada musu yana hanyar dawowa sannan yazo airport ya daukeshi.......

Wurgar da komai nashi yayi a parlor ya nufi kitchen saboda muguwar yunwar da yake ji,
a tsaye ya tadda ita tana goge gas tana bitar haddar da zata bayar,

a hankali ya karaso inda take ya sanya yatsunshi daya cikin kunnenta,

wani irin ihu ta saki wanda ya sanyashi toshe mata baki yana kyakyata dariya,

rankwafowa yayi daidai kunnenta saboda gajertan da tayi a gabanshi yace "matsoraciya,
irin wannan ihun ai sai ki firgita mutane,

me kika dafa min?

"Ayya bansan zaka dawo ba ai,
kayi hakuri bari in tuka maka tuwo,
kaje ka huta awa biyu ya isa,

"In na kara minti talatin a duniya ki godewa Allah,
kawai kice kaje ka kashe kanka, dan Allah ki daina wasa,

Dariya sosai tayi ta fitar mishi da cooler shinkafa da miya da salad,

kamar mayuwancin zaki ya fara cin abincin da ya dade baici irinshi ba,

saida yaci yayi katt sannan ya fara dawowa cikin hayyacinshi,

Dakinshi da ya shiga ne ya sake sanya nutsuwa a tattare dashi saboda irin gyaran da Nadeeyah tayi mishi,

da takalmin kafarshi ya mike a gadon ya fara kwasar bacci hankali Kwance.....

*TUN RAN GINI*

Mrs Tijjani Shattimah......
[01/04 9:50 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣1⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

*EMIR PALACE SASSOUN BOROUM*

Sarkin sassoun boroum ne tsugune a gaban sarki "TIDJANI YALLO" yana mika gaisuwa kamar yadda sarakuna keyi wa na gaba dasu,
bayan sun gama gaisawa aka cika kayayyakin abinci da sha a gabansu saboda girmamawa,
babu abinda Sarki Tidjani da Shareefah suka kalla, bare har su kai ga cin shi,

cikin nutsuwa da kasaita suka gabatar da dalilin zuwansu,
nan da nan aka wakilta dogarai dan suje can rugar Haldo su nemo Hajja yar Ruga su taho da ita,
da yake rugar bata da nisa da gidan sarki sai gasu sun dawo,

cikin girmamawa suka ce bata da lafiyar da zata iya zuwa,

daka musu tsawa sarkin sassoun burum yayi yace "maza su koma su dauko ta,
dakatar dasu Shareefah tayi hade da mikewa tace "su barta kawai, su zasu isa zuwa gidanta,

Duk yadda sarkin sassoun burum yaso nuna musu kaskancin zuwa rugar Haldo hakan bai hanasu zuwa ba,
a cewarsu su suke nema a gurin ta,
ya zame musu dole su ganta yau kota halin kaka.....

Wani irin wari dakin Hajja ke fitarwa,
warin ma marar misaltuwa,
tana kwance a kan tabarmar da takai rabi saboda cinyewa,
dakyar aka iya dagota ta jingina da wani sudadden pillow,

"wani dan kara tayi saboda wani ciwo da yayi mata rami a mazaunanta,
yaron dake kula da ita ne ya sa mata wani pillow a gurin ciwon,

saboda tausayin halin da Hajja ke ciki ya sanya Shareefah sharar kwalla,

Dakyar muryar Hajja ta iya fita tace "sannunku da zuwa,
da kai suka amsa hade da gyara zama akan daddumar da dogarai suka shimfida musu,

saboda son jin abun da ya kawosu ko kyankyamin dakin basu ji ba,

"Daga ina ranka ya dade?
Hajja ta fadi baki na rawa,

Shareefah ce ta fada mata sunanta da dalilin da yasa suka zo gurinta,
bude ido Hajja tayi sosai ta kure shareefa da ido,

*SHAREEFAH YALLO*

kece?

murmushi Shareefah tayi tace "nice,
ashe ma kin sanni,

kuka Hajja ta fashe dashi tace "farin sani,
ni na raineki tun kina tsumma,

nafi shekara ashirin a gidanku tun kafin a haifeki,

ashe zan sake ganinki,

rabona da ke inaga in banyi karya ba yakai shekara arbain, dan tun kina shekara goma sha biyu na bar agadez,
ashe ina da rabon sake ganinki ta karashe da kuka hade da tari,

Cike da kosawa sarki Tidjani yace "sai hakuri Baba,
dama haka rayuwa take,
kuma duniya fadi gareta, wata rana in da rai dole a hadu,
yanzu gashi sanadiyar mutuwar UMMU AYYU Allah ya kawo mu gurinki,
yanzu bamu da isashen lokaci zuwa mukayi ki fada mana labarin da Ummu tace ke kadai ce kika san dashi,
labarin YARIMA,

wani kukan ne ya kufcewa Hajja a zuciyarta tace

"yau labarin da yayi shekara da shekaru a kunshe, hali yasa zata bayyana shi,
labarin da ya zame mata tamkar kwai a cikin zuciyarta saboda riritarshi,
ajiyar zuciya tayi tace
"babu mamaki fitar labarin nan ya zama silar samun warakarta,

Nuni tayi ma yaron dake kula da ita wani gurin dake cike da kaya,

mikewa yayi ya dauko wata jakar saka ya mika mata,

hannu na rawa ta karbi jakar ta dauko wani ginin mutum mutumi wanda yake kewaye da kawunan mutane babu adadi,

Saboda tsananin tsorata saida shareefah ta rungumi kafardar mijinta,
abun ba karamin tsoro ya bata ba kuma ya daga tsigar jikinta matuka,

yadda aka yanyame shi da wasu abubuwa kamar kwari yasanya har sarki jin tsoro amma kadan,

wani guri ta daga a gefenta, inda take ajiyar abubuwa,
nan ta mike dayar ruwa nabin bayanta ta fita tsakar gidan ta daki wani dakali dake kofar dakinta,

nan take gurin yayi rami, hannu tasa ta ciro layu masu tarin yawa,

daga can kasa ta hango kurciyar da suka binne shekara da shekaru kwance babu rai ga layu kewaye da ita,

a gigice ta ciro kurciyar da duk wata sai ta bata ruwa ta mayar ta rufe,
tun da ta kwanta ciwo kusan watanni takwas bata kara bi takanta ba domin itama ba lafiyar gareta ba,

girgiza kurciyar tayi tana kuka tana fadin
*YARIMA ADAMU*

wayyo Allah Kunzo a kurarren lokaci,
nasan duk inda Yareema yake a yanzu to kasa ta rufe idonshi,

wannan kurciyar rayuwar Yareema ce,
Allah na tuba,
wayyo ni Allah,
haka ta dinga fadi hankali tashe,

Da karfi ta saki mutum mutumin hanunta ya tarwatse a tsakar gidan,
nan tabi kowane kai ta cire dabaibaiyin da aka mishi,
runtse ido Sarki Tidjani yayi saboda juyawa da yaji kanshi nayi,
dakyar Shareefah ta tallabe shi ya zauna a kasa ba tare da duban dattin gurin ba,
itama hakan ce ta kasance da ita, saidai ita ta kasa fahimtar komai,
sabanin Sarki Tidjani da komai ya shiga yawo a kanshi,
yadda abubuwa suka faru ya dinga tunowa kamar yanzu ake yinsu,

kusa dasu Hajja taje dan itama wani karfi taji a jikinta,
burinta ta sanar dasu komai da suka sani da wanda basu da masaniya...

"Nasan yanzu wasu abubuwan sun fara dawowa a kanku da kuma daukacin mutanen da suka san Yareema a Agadez,
to saidai abin da baku sani ba shine dalilin da yasa ya kaurace muku ya tafi can wani guri inda babu wanda zai ganshi bare har yasa shi waiwayen gida,

"Adamu Yallo... sarki ya dinga maimaitawa a bakinshi,
fuskarshi yake kallo kamar yanzu suka rabu cikin lambun *Shehrah Agadez*,

ina dan uwanshi ya tafi har tsawon wannan lokacin,
yana kallon fitarshi daga lambun lokacin bakinshi yayi mishi nauyi ya kasa kiranshi bare har ya tambayeshi inda zashi,
sai yau yaji tunanin ya dawo sabo dal game dashi,

Da sauri ya maida idonshi kan Hajja yace
"ina Adamu?
Me ya sami Adamu?
Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, me ya shiga kaina har na manta da dan uwa kuma aminina,
Ya salam ya fadi hade da dafe kai..

"Ba laifinka bane Yallabai,
Laifin namu ne,
bakai ba ma kowa a garin Agadez a yau sai ya tambayin dalilin da yasa ya manta da Yareeman da suke matukar so fiye da sarkin Kanshi...
har ke ma Shareefah,
a karancin shekarunki zaki iya tunawa da
*Yeeman ki* ,

*Yeeman Pappalinto*

nan take mafarkinta ya dawo mata sabo,
sunan Yeema take yawan fadi cikin mafarkinta,

wani irin kuka ne ya kufce ma Shareefah ta dinga nanata sunan a ranta,
tabbas ta tuno kuruciyarsu saboda mafarkinta bai rage mata komai ba,

cikin kuka tace "Bani labarin Yeema nah!
Bani labarin dalilin da yasa yayi nesa dani.....

*TUNA BAYA.......*

**********

Ranki ya dade kici abinci dan Allah,
rashin cin abinci zai iya zame miki illa,
kuma kin sani sarki bazai fasa abun da yayi niyya ba,

cikin Kuka Fulani Ayyu tace "Hajjara yanzu anyi min adalci,
ace sarki ya rasa da wacce zai hadani sai da

*Kuyanga Rosalin* ,

kuyangar da na bawa yarda tasan sirrina fiye da kowa,
tayaya zan iya kallon mutanen gari,

wannan ai cin mutunci ne a gareni da masarauta baki daya,

Gabanta Jakadiyya Hajjara ta dawo tace "ki kwantar da hankalinki,
ki barshi yayi auren,
zamu san yadda zamuyi da ita,

da kalamai masu dadi Hajjara ta kwantar mata hankali har taci abinci....

Wata hudu bayan auren *sarki Abdallah Yallo* da Kuyangarshi mai kula da komai na alamuranshi *Rosalin Mujdaha*

mahaifinta shine mai bawa sarki kariya,
bayan rasuwar mahaifiyarta mahaifinta ya bawa sarki ita domin ta zama mai aikinsu ta jikinsu wacce zata kula dasu,
garin binciken shi na rashin haihuwa Rosalin ta fado ciki har malaminshi ya fada mishi alherin da ke tattare da aurenta,
bai damu da kalubalen da ya fuskanta daga yan uwa da matarshi ba aka sanya rana, har Allah yasa ta zamo matarshi,

kyakykyawar gaske ce doguwa sambal,
ga biyayya da hakuri,
hakan yasa yake matukar kaunarta,
babu irin asirin da Fulani Ayyu batayi ba dan taga bayanta amma Allah cikin ikonsa duk ta tsallake,

saboda tsoron Fulani da Rosalin keyi hakan yasa bata fita ko nan da can,
duk abin da zai hadasu tana neman hanyar kaucewa saboda bata san tashin hankali,
mugun hakuri gareta ga kawaici da sanin ya kamata,

Babu wanda keda masaniyar tana dauke da ciki domin tsakaninta da bayinta yar kallon fuska ce,
ko mikewa a gabansu batayi,

A ranar da cikinta ya cika wata tara ranar akayi haihuwa a gidan,
wazirin sarki wanda ya zamo kani ga sarki,
a gurin barka ne kowa ya fahimci ciki gareta,
ranar Fulani mutuwa ne kadai batayi ba,
gaba daya kansu ya kulle ita da Hajjara suka rasa ta inda zata bullowa al'amarin..

Ranar suna Yaro yaci sunan *TIDJANI*,

A daren ranar sunan Rosalin ta tashi da nakuda,
sarki da kanshi ya sa aka kira unguwar zoman gidan ta karbi haihuwar,

yana daga bakin kofa yaji kukan jinjiri,

wani irin kuka ya fashe dashi na murna wanda yaki dauke mishi har saida yaji dumin danshi a jikinshi,
nan gaba daya gari ya dauka Sarki Abdallah Yallo ya samu magaji.....,

kwana goma akayi ana buduri a garin,
gidan kuwa zama yayi kamar gidan gala, domin cike yake tun safe har washe gari,
babu abin da akeyi sai ciye ciye da raye raye,
ko ina ka zaga cikin garin farin ciki ke dauke a fuskar kowa saboda sarki ya zamo mai kyautatawa a garesu....

Shekarar Yareemah Adamu bakwai rikonshi ya koma gurin Fulani Ayyu da tayi sanadiyyar mutuwar Rosalin da karamin ciki bayan barin da ta dinga yi,

sarki yayi kuka yayi bakin cikin mutuwar Rosalin mace mai matukar nuna kula a gareshi....

Duk yadda Ayyu takai ga son kuntatawa Yareemah Adamu hakan yaki yiwuwa saboda sarki yana sanya ido sosai akanshi,

sai kuma matar waziri mahaifiyar Tidjani wacce yake yini a gurinta bacci kadai ke maidashi gida gurin mahaifinshi,

Albarkacin Adamu Allah ya azurta Fulani da samun ciki a lokacin da ta fidda rai,

saidai kashh tayi matukar bakin cikin ganin ya mace ta haifa,

haka nan tayi ta dakon kiyayyar Adamu a ranta,

shi kuma Allah ya daura mishi kaunar yarta Shareefah haka itama Shareefan,
ko ina zasu tare suke zuwa...

Yana shekara goma sha shida sarki ya fara barin mishi kujera yana ganin yadda yake gudanar da al'amuran sarauta,

Adalin sarki Abdallah, ashe a lokacinshi bai kwatanta adalci kamar yadda Adamu ke kwatantawa yanzu ba,

Izza ta mulki da kasaita gaba daya sun tabbata a jikin Adamu,

wani irin farin jini Allah yayi mishi wanda ya sanya ko ina a garin ake maganarshi da yabonshi,

A rana in baiyi abun alkhairi sau goma ba to zaiyi fin goman,

gaba daya kowa a garin ya tabbata cikin walwala saboda zuwan Yareemah Adamu....

*Mummunan Kaddara*

Ranar da ya cika shekara Ashirin ciff, ranar kaddara mummuna ta afka mishi,
a ranar al'amura marasa dadi suka faru a cikin garin agadez....

*Yadda Abun ya faru*

Cikin farin ciki Sarki ke sanarwa da fulani Ayyu ya game shirin komai na hutawa ya barwa Yareemah kujerarshi,
sannan ya fada mata an kawo mishi yaran sarakunan da zai aura mishi saboda cikar kamalar sarki,

nan ta nuna mishi farin cikinta sosai harda cewa zata tayashi zabe a cikin matan..

Tana barin gurinshi zuciyarta kamar zata buga ta kira Hajjara,
nan suka kulla duk shirinsu na kawar da Abdallah domin a cewarta in ta kuskura ta yarda aka nadashi sarki kuma yayi aure wasu familyn zasu zama iyalan sarki su kuma su zama yan kallo..

Makudan Silalla ta bawa Hajjara ta shirya tafiya can kauyensu Sassoun burum,

cikin sa'a, da kuma lokacin akwai wani boyayyen al'amari wanda Allah ya boye a rayuwar Adamu Hajja ta samu bokan da yayi nasarar yin aikin,
ya kuma bukaci auren Hajja,
a take ta yarje mishi domin dama tana bukatar yin auren,
bayan sun kammala aikin ta koma agadez ta karbo sha tara ta arziki daga gurin fulani Ayyu....

Cikin Kuka Hajja tace "kudi ne wadanda basu rufe shekara ba suka kare suka barmu da wahala,

saboda muhimmacin Amana naki yarda in watsa asirin, amma fa duk wata tana bibiyar asirin kamar yadda mijinta ya koya mata....

Shuru gurin yayi bayan Hajja tayi shuru,
sai kuka dake tashi a gurin,

Murya a dashe Sarki yace
"Bazan manta ranar karshe da na ganshi ba,
ranar muna tsaye a lambu muna hirar sarautar da za'a bashi,
yana tsinko ma shareefah yalon lambu,
a kasa ya zubar da yalon ya nufi kofar fita,
yana kurewa ganina na bishi na hango Haroun da abokanshi, suna Kallon Adamu ya gifta gefensu babu wanda ya gaisheshi bare ya tambayi inda zashi shi daya...

Ashe abubuwan da akayi mishi ba kanshi kadai ya tsaya ba har dukkan mutanen agadez,

koda na koma gida babu wanda ya tambayeni shi kowa harkarshi yakeyi har sarki bai damu da tambayar inda yake ba domin babin yareemah shafewa yayi a cikin garin agadez,

Ya Allahu ina zanga Adamu,
ina zan ganshi....

Ganin kukan bazaiyi musu ba suka fita a gidan Hajja domin babu wani hukunci da zasuyi ma musaka irin ta,
hukuncin Allah ma ya isheta,

Motocin sarkin sassounburum suka shiga suka je gidanshi suka sallemashi sannan suka wuce airport din katsina domin hawa jirgi zuwa agadez, saboda sassounburum tafi kusa da garin daura....

Shawara suka yanke na baza malamai ayi adduar da Allah zai kawo sanadin haduwarsu in har yana da rai,
domin basu yarda da maganar Hajja na ya mutu ba....

*Bawan Allah Adamu tun a cikin garin Agadez ya fara watangaliliya, duk inda ya wuce babu wanda ke ganeshi bare har ya bashi girman dan sarkin da suke matukar so, har ya samu motar da zataje zinder, a can ma saida yayi shekara biyu yana wahala, irin masu shigowa daga kawo kaya daga kano zuwa zinder su yabi zuwa nigeria, A kano ma saida ya shekara daya da watanni har Allah ya hadashi da Alh jogana, nan ya kaishi gidanshi dake kaduna dan yi mishi gadi, anan ne ya bude shago har kaddara ta hadashi da Suwaiba, barin agadez, zuwanshi kaduna, haduwarshi da Suwaiba, rabo ne na ya'ya, wanda Allah swt ya boye wasu al'amura a garesu, Tabbas haihuwar da namijin da suwaiba tayi a farko rubutaccen al'amari ne, mulki na Allah ne, shine yake bada aronshi ga wanda yaso koda kuwa almajiri ne.......*

*A gurguje na takaita muku labarin Adamu saboda mu kai inda muke san zuwa a kan lokaci*

_Akwai shagalin biki a page fifty...... ku cinka_

Mrs Tijjani Shattima....

[01/04 9:50 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣1⃣
By *Aysha Ya'u kurah*

*EMIR PALACE SASSOUN BOROUM*

Sarkin sassoun boroum ne tsugune a gaban sarki "TIDJANI YALLO" yana mika gaisuwa kamar yadda sarakuna keyi wa na gaba dasu,
bayan sun gama gaisawa aka cika kayayyakin abinci da sha a gabansu saboda girmamawa,
babu abinda Sarki Tidjani da Shareefah suka kalla, bare har su kai ga cin shi,

cikin nutsuwa da kasaita suka gabatar da dalilin zuwansu,
nan da nan aka wakilta dogarai dan suje can rugar Haldo su nemo Hajja yar Ruga su taho da ita,
da yake rugar bata da nisa da gidan sarki sai gasu sun dawo,

cikin girmamawa suka ce bata da lafiyar da zata iya zuwa,

daka musu tsawa sarkin sassoun burum yayi yace "maza su koma su dauko ta,
dakatar dasu Shareefah tayi hade da mikewa tace "su barta kawai, su zasu isa zuwa gidanta,

Duk yadda sarkin sassoun burum yaso nuna musu kaskancin zuwa rugar Haldo hakan bai hanasu zuwa ba,
a cewarsu su suke nema a gurin ta,
ya zame musu dole su ganta yau kota halin kaka.....

Wani irin wari dakin Hajja ke fitarwa,
warin ma marar misaltuwa,
tana kwance a kan tabarmar da takai rabi saboda cinyewa,
dakyar aka iya dagota ta jingina da wani sudadden pillow,

"wani dan kara tayi saboda wani ciwo da yayi mata rami a mazaunanta,
yaron dake kula da ita ne ya sa mata wani pillow a gurin ciwon,

saboda tausayin halin da Hajja ke ciki ya sanya Shareefah sharar kwalla,

Dakyar muryar Hajja ta iya fita tace "sannunku da zuwa,
da kai suka amsa hade da gyara zama akan daddumar da dogarai suka shimfida musu,

saboda son jin abun da ya kawosu ko kyankyamin dakin basu ji ba,

"Daga ina ranka ya dade?
Hajja ta fadi baki na rawa,

Shareefah ce ta fada mata sunanta da dalilin da yasa suka zo gurinta,
bude ido Hajja tayi sosai ta kure shareefa da ido,

*SHAREEFAH YALLO*

kece?

murmushi Shareefah tayi tace "nice,
ashe ma kin sanni,

kuka Hajja ta fashe dashi tace "farin sani,
ni na raineki tun kina tsumma,

nafi shekara ashirin a gidanku tun kafin a haifeki,

ashe zan sake ganinki,

rabona da ke inaga in banyi karya ba yakai shekara arbain, dan tun kina shekara goma sha biyu na bar agadez,
ashe ina da rabon sake ganinki ta karashe da kuka hade da tari,

Cike da kosawa sarki Tidjani yace "sai hakuri Baba,
dama haka rayuwa take,
kuma duniya fadi gareta, wata rana in da rai dole a hadu,
yanzu gashi sanadiyar mutuwar UMMU AYYU Allah ya kawo mu gurinki,
yanzu bamu da isashen lokaci zuwa mukayi ki fada mana labarin da Ummu tace ke kadai ce kika san dashi,
labarin YARIMA,

wani kukan ne ya kufcewa Hajja a zuciyarta tace

"yau labarin da yayi shekara da shekaru a kunshe, hali yasa zata bayyana shi,
labarin da ya zame mata tamkar kwai a cikin zuciyarta saboda riritarshi,
ajiyar zuciya tayi tace
"babu mamaki fitar labarin nan ya zama silar samun warakarta,

Nuni tayi ma yaron dake kula da ita wani gurin dake cike da kaya,

mikewa yayi ya dauko wata jakar saka ya mika mata,

hannu na rawa ta karbi jakar ta dauko wani ginin mutum mutumi wanda yake kewaye da kawunan mutane babu adadi,

Saboda tsananin tsorata saida shareefah ta rungumi kafardar mijinta,
abun ba karamin tsoro ya bata ba kuma ya daga tsigar jikinta matuka,

yadda aka yanyame shi da wasu abubuwa kamar kwari yasanya har sarki jin tsoro amma kadan,

wani guri ta daga a gefenta, inda take ajiyar abubuwa,
nan ta mike dayar ruwa nabin bayanta ta fita tsakar gidan ta daki wani dakali dake kofar dakinta,

nan take gurin yayi rami, hannu tasa ta ciro layu masu tarin yawa,

daga can kasa ta hango kurciyar da suka binne shekara da shekaru kwance babu rai ga layu kewaye da ita,

a gigice ta ciro kurciyar da duk wata sai ta bata ruwa ta mayar ta rufe,
tun da ta kwanta ciwo kusan watanni takwas bata kara bi takanta ba domin itama ba lafiyar gareta ba,

girgiza kurciyar tayi tana kuka tana fadin
*YARIMA ADAMU*

wayyo Allah Kunzo a kurarren lokaci,
nasan duk inda Yareema yake a yanzu to kasa ta rufe idonshi,

wannan kurciyar rayuwar Yareema ce,
Allah na tuba,
wayyo ni Allah,
haka ta dinga fadi hankali tashe,

Da karfi ta saki mutum mutumin hanunta ya tarwatse a tsakar gidan,
nan tabi kowane kai ta cire dabaibaiyin da aka mishi,
runtse ido Sarki Tidjani yayi saboda juyawa da yaji kanshi nayi,
dakyar Shareefah ta tallabe shi ya zauna a

Please Login or Register in order to submit comment