Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana faďin

*ohh Abbu?*

wurgi tayi da jakarta kan doguwar kujera ta zauna kusa dashi,
hawayen ta fara share mishi tana magana da larabci,
tasan Irfan ne kadai kesa mahaifinta hawaye haka,
hoton da ya rike a kirjinshi ta karba ta zuba mishi ido,
ajiyeshi tayi a mazauninshi ta dafa kafaďunshi,

"Bazan hanaka zubar da hawaye ba dan nasan a wannan lokacin babu abinda zaisa su tsaya sai dai domin kansu,
tunda nazo duniya nake ganin hawayen nan,
plss Abbu kayi hakuri,
kayi tawakkali,
in kanada rabon ganinta zaku haďu cikin sauki in shaa Allah,


Fuskarta ya tallabo haďe da sakin murmushi a bayan kukan yace

"Allah ya kawo min lokacin my love,
yanzu na samu labarinta daga gurin Hilal,

kallon inda ya nuna mata tayi,
shigowarta tabbas ta ganshi, amma ganin halin da Abbunta yake ciki ya mantar da ita akwai mutum a gurin,


cikin ido ta kalleshi dan shima ita yake kallo tun shigowarta,
mamaki ya hanashi furta komai dan ya tsorata da hukuncin ubangiji,
irin wannan kamanni har haka, ya salam,
tabbas badan gogewa da wayewarsu ba daya bace da babu abinda zai hanashi kiranta da Nadeeyah,

Takalmin kafarta mai tsini ta cire ta mike rai a haďe ta isa gurin Hilal,
ta riga ta gama hararo abun da ya kawo shi,
tasan sarai yazo da niyyar cutar mahaifinta ne,
shekara sama da hamsin da batar ta sai yau zaizo yayi taking advantage din son da mahaifinta kema yayarshi yace ya san inda take,
in shi yasan inda take meyasa baizo da ita ba,

"Heyyy,
ta faďi haďe da buga hannunta a saitin idonshi,
firgigit Hilal yayi ya dan matsa dan baisan ta karaso inda yake ba,
kusa dashi ta zauna sosai tana fuskantar mahaifinta tana dariya dan kar ya gane manufarta,

"Wa ya aiko ka?
Ta tambaya ba tare da ta kalli inda yake ba,

cikin rashin fahimta ya share hawayen dake makale a idonshi yace

"Ban gane ba?

"Zaka gane,

hannu tasa cikin nashi tace

"Muje ciki akwai tambayoyin da zan maka,
mikewa yayi dan ta fara jan hannun tana tafiya,
da larabci tace mahaifinta tana zuwa...



Sosai ran Hilal ya baci da ta gama jero accusations dinta cike da faďa kamar zata mareshi,
maganarta ta karshe ce ta sashi daka mata wata tsawar da ta daidaita ta,

"Yesss nasan Irfan,
sani sosai,

"Ehen i knew it,
nasan Irfan ne yasaka wannan aikin dan ku samu kudin banza ku je kuyi iskancinku,
ku ko kunya bakwa ji,
at ur age baku san yadda zaku dinga samun daily income ba sai kunyi cuta,
to this deal is cancelled sai ku nemu wani,
nuna shi tayi da ďan yatsa tace

"Wallahi in na sake ganinka gurin Abbu na sai nasa anyi maka daurin rai da rai,
babu inda ba'a sanni ba world wide duk inda na nemi alfarmar a kam-----

Gerraut Hilal ya faďi haďe da buge hannun kasa,
duk sanyin da ya shigeshi na rashin Nadeeyah ya fice gaba daya,

"Count me out,
ban sanki ba, ban taba ganinki ba,
sannan Irfan a companyn nan na sanshi,
u most be stupid in har kikayi tunanin nazo nan ne dan kudin mahaifinki,
he called me himself,
go and ask him,
i'm his company architect,
ban taba ganinshi ba sai yau,
nd wat i saw ya sani faďi saboda ur aunt is my relative,
hannu na rawa ya dauko wayarshi ya nuna mata hoton Nadeeyah,
ganin jikinta ya fara sanyi ta kuma tsumu da mamaki ya sanya shi kwace wayar yace

"I have my own self respect,
nasan i'm nothing like ur father but i'm contented with the little i have,
am not needed here, kuje ku nemi  real yan uwanku tunda ni fake na kawo,
yana kaiwa nan yayi hanyar waje haďe da buga tsaki,

Da gudu tasha gabanshi haďe da rike mishi hannu,

"Sorry sorry sorry,

plssss... ta kara faďi haďe da tsugunawa a kasa,

kwace hannunshi yayi zaiyi magana yaji muryar Sheik a bayanshi,

"Kayi hakuri Hilal,
she is always like that,
akwaita da tambayar da zata kai mutum bango,
zo ka zauna na yarda da kai 100%,

juyawa Hilal yayi ya koma kan kujera ya zauna fuskar nan a murtuke,
wannan babu abun da ta haďa na hali da Nadeeyah,
kalamanta na cin mutunci sun mishi zafi matuka,
dannewa kawai yayi ya zauna dan sauke wannan nauyin badan ita ba sai dan Nadeeyah da su Hafeez,
tambayoyi sheik ya fara mishi,

babu abinda ya iya faďa mishi sai dai kawai ta Haifi twins...

Yadda yaga ya ruďe da murna ya kasa sanar dashi ta mutu,
a ranar maida Hilal ciki ne kadai sheik baiyi ba,
tafiya ya shirya musu da private jet din abokinshi dan baya son wani delay a zuwa ganin yar uwarshi da zuri'ata,


Murna tasashi ya yafe mata rashin nemanshi da batayi ba,
tasan irin ukubar da ta tafi ta barshi a hannun Ummul da 'yayanta,

share hawayenshi yayi bayan ya tuno gararanbar da yayi a baya wanda ya zame mishi tarihi...




Har Hilal ya bar office din bai kalli inda Maleeka take ba,
ita kuwa sai kai kawo takeyi da kayan kwadayi tana dire mishi, tasan bata kyauta mishi ba, idonta ya rufe ya hanata hango kamalar fuskar Hilal,

Sukuku ta yini ranar har ta koma gida,
duk abinda takeyi Hilal kawai take gani,
masifarshi da komai nashi burgeta yakeyi,
samm bai bata fuskar da zata amshi number shi ba,
tayi yawon duniya sosai, ta haďu da maza haďaddu wadanda suke macewa akanta,
bata karo da wanda zuciyarta tayi na'am dashi ba tun bayan Mutuwar Na'em sai Hilal,

*Saheebul qalbee*

ta furta a hankali tana mai hango soyayyarsu ta cikin film din..

"Kwatanta soyayyar da mai zafin zuciya irin Hilal zai fi armashi.. 

murmushin dake kan fuskarta samm yaki daukewa,
tana hango Abbunta da Ummi na sakkowa daga sama cikin jallabiya tayi saurin nutsuwa ta isa gurinsu dan tambayar inda zasu a daren nan...


Amsar da ya bata ya sanyata yin murmushi mai kyau haďe da cewa su jirata dan Allah zata rakasu,

"Jira fa Malee? Ummi ta faďi da harcensu na larabci tana rike haba..


Kwantar da kanta tayi a kafaďun Abbu tace

"Abbu kaga ummi ko?

"Zan jiraki,
komai dake zanyi,
ke zata fara gani tunda sunanta gareki,


rungumeshi tayi ta haye sama da gudu dan shiryawa....



40mins Ya Habeebi,
kasan jiran Maleekah...

bata gama rufe baki suka hangota cikin purple jallabiya mai walkiya,
kan nan ta yaneshi ta fito a balarabiyar asali,
light makeup tayi wanda ya fito da kyawunta na musamman,
kamshinta kuwa dadinshi kansa mai saurare yayi baccin da bai shirya ba,


*ATIKA ATEEK SAHEEB SAIFUDDEN* kenan

ta haďu matuka,
tun tana karama take sha'awar drama,
Shiyasa samm taki maida hankali a karatu,
gata da kokari sosai,
ganin hakan yasa Abbunta yi mata jumping,
tanada 14yrs aka kaita university inda ta karanci theartre art,
da yake field dinta ne sai ta dage sosai dan kullum cikin drama suke,
hakan yasa ta kware sosai,
a yanzu duk kasashen larabawa babu inda ba'a santa ba,
haka tsirarrun yan wasu kasar irin nigeria masu kallon arabic dramas suma duk sun santa,

shekarunta basu wuce 21 ba amma wayewarta ta zarce dan 30...



  "Kinyi kyau my love,

kiss ta mishi a kumatu tace

"Thank u Abbu,

nasan anyi complain?

Dariya yayi yace
"as usual, kin santa,

gaba ummi tayi tana dariya tace "kwaji dashi.....





Basu sha wahala gurin zuwa gidan ba dan estate dinsu sananne ne sosai,


Da fara'a Hilal ya taresu tun daga kasa,
dama ya gama shirya ma zuwansu,
ya faďa ma Anty Reemah zaiyi baki amma bai faďa mata ko su waye ba...




Zainab na zaune tana home work tana zana sunan da yake bace mata a kai,

Maleekah sahy,
Maleekah Sa'eed,
Maleekah sahab

haka ta dinga rubutawa a bayan littafinta,
ko da taji an murda kofar duk su Anty Reemah sunje suna musu maraba bata dago ta kallesu ba,


Na--deeyah...
Hinad ta faďi a hankali tana nuna Maleekah,
dago kai Zainab tayi ta mike da sauri ta isa gurinsu,
kallonsu ta shiga yi daya bayan daya,
tasan ba Nadeeyah bace,
dan in itace abun da zatayi mata ya wuce ta tsaya tana kallonta,


"Maleekah sahab ko?

Dariya Maleekah tayi ta tsuguna kusa da Zainab tace

"Saheeb dai my young fan,

ko dai brothernki ne ya faďa miki sunana, ta karashe tana kallon Hilal,

shuru Zainab tayi dan turancin na Maleeka yafi karfinta,


Anty Reemah ce ta katse shurun ta hanyar nuna musu gurin zama,

bayan sun gaggaisa Anty Reemah ta kalli Sheik cike da al'ajabi zatayi magana Hilal ya rigata dan baya son yasan mutuwar yar uwarshi samm sai yaje ga mijinta,



"Mum wannan kanin maman su mama suwaiba ne,
labarin yadda haďuwarsu ta kaya ya basu wanda ya cikata da mamaki,

"lallai komai da sanadinsa, sanadin aiki ya sa ka samo wannan muhimmin abun,
kaii masha Allah wallahi naji dadi sosai,

introducing dinsu Hilal yayi, yana zuwa kan Zainab da Sheik ya kasa daina kallonta yace

"Ur grand daughter sir,
she is urs!

hawayen farin ciki ne ya fito mishi dan yajita sosai a jininshi,

mikewa yayi ya dauketa sosai a jikinshi,
ya kosa a wayi garin gobe yaje yaga zuri'arshi, shakikanshi, wadanda yake da rashinsu tun kuruciya,
a gidan Papa ya samesu shima yayi farin ciki sosai sukayi hirar kasuwanci da na iyalai,


Sheik jin kanshi yakeyi kamar a yaune aka haifeshi dan ya fara jin kamshin yan uwanshi danginshi na uwa...





Assalamu alaikum.....


maida hankalinsu kan mai sallamar sukayi dukkansu,

Sauka jikin Abbu Zainab tayi ta ruga gurin Meerah,

"Anty Mee zo kiga Maleekah da nake baki labari dazu,

hankalinta sam bai kan zainab tana can kallon yadda Maleeka tasa kafa tana shafo ta Hilal yana matsarwa,
tray din hannunta ta damke dan kiriss ya rage ya faďi kasa,

"Muje zee,


Har kasa ta tsuguna ta gaida su Abbu sannan ta mike ta nufi kujerar da su Hilal suke,
kan hannun kujerar ta zauna,
ganin duk manyan suna can suna hirarsu yasata yi mishi raďa a kunne,


Dariya sosai yayi dan ya gama gane inda ta dosa,
mikewa yayi ya nufi dakinshi..

bin bayanshi tayi rai a bace dan ta gama kulewa,
dangwarar da tray din snacks din da tayo mishi tayi a kan madubi,


"Meerah plss,

kar muyi creating scene a gidan nan kinga munada baki,



"Eh naga baki,
su bakin da suka san inda sukazo ai na samesu suna hira,
kai fa,
ko kunyar idon iyaye bakaji ba ka zauna kusa da mace tana shafa maka kafa kana jin dadi,



Wannan karan dariya yayi mai sauti wanda ya kular da Meerah
ya sata sakin kuka mai karfi,

"La'ila,
ke rufa min asiri plss,
haba meerah,
yarinyar nan kema kinsan tafi karfina daga yanayinta in kika kalla,


"Me zanyi da yanayinta ni,
abun da idona ya gane min shi na lura dashi,
na gama fargabar wata yanzu kuma ga wata zata shi----


Meera..
ya katseta haďe da tsugunowa gabanta,
Na faďa miki soyayya yanzu na rufeta a shafin rayuwata,
bana tunanin zan sake faďawa cikinta so quick,
na faďa miki kiyi hakuri,
wallahi in nace miki zan yarda ki jirani nasan cutarki kawai zanyi,
bazan iya sake yin wata soyayya ba,
u are my best friend tun muna yara,
dan Allah mu tafi a haka,
Allah zai baki wanda yafini alkhairi,



Share hawayenta tayi ta mike tace
"Nagode Hilal,
zanyi hakuri dakai dan dama nasan ba sona kakeyi ba,


"Nooo Meerah...
ya faďi haďe da matsowa kusa da ita,
hawayen da ya makale a idonta ya share mata yace

"kinsan Allah ina sonki,
amma bazan iya zaman aure dake ba,
who will be the husband?


Yadda yayi tambayar cike da zolaya yasata yin dariya,

tasan irin matan da yakeso,
yara kanana wadanda zai yi musu yadda yake so,

bayason a juyashi sam,

ita kuwa Meerah kusan mates ne in ma bata girme mishi ba,

"All the best besty ta faďi tana murmushi,
Allah ya sake baka wata soyayyar wacce tafi ta da,


"U will always be my best Meera, Allah ya baki farin ciki kema....




"Uhmmm wonderful..,

Maleekah ta faďi tana karasowa haďe da tafa hannu,
a tsakiyansu ta tsaya cike da tsiwa,

hannun Meerah Hilal yaja yace da hausa dan yasan bata ji.

"Muje in rakaki,
ba kunya gare yarinyar nan ba,


kallo ta bisu dashi ta rasa menene ainihin abin da yasa ta biyosu,

kwafa tayi ta kama hannun Zainab suka koma parlor,


lokacin har su Abbu sun mike da niyyar tafiya,

wayarta ta dauka sukayi hotuna kala kala da Zainab da Hinad,


Har kasa su Anty Reemah suka rakosu,
tana ganin Hilal ya nufo inda suke tayi saurin sanya Abbu cikin mota,
gefen driver ta shiga ta sashi ya koma mazauninta,

Saida taga yazo dab da motar ta tadata haďe da bata wuta da karfi,
tana kallon yadda ya tsaya cike da mamaki ta fito da hannunta waje haďe da yi mishi wani irin sign wanda bai gane ba,
tana gama juyar da motar ta leko tayi mishi gwalooo sosai haďe da kaďa kai da ido,


Tsintar kanshi yayi da dariya sosai yana faďin
"naughty girl,
matsalar yan drama kenan,
komai sai sun maida shi wasan kwaikwayo,
Har ya karasa cikin dakinshi bai bar hango yadda tayi mishi da fuska ba,
duk abin da yakeyi in ya tuna sai ya keche da dariya shi kadai........





Mrs Tijjani Shattima.....

[09/06 11:14 AM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 6⃣9⃣
By *Aysha Ya'u kurah*






*Kaduna garin gwamna...*




Share gumin dake tsatstsafo mata akai tayi ta sake gyara zaman jakarta da ke kunshe da dubu uku kachal,
samm bata san hawa adaidaita dan kar ta taba kudin da suka rage mata gaba da baya,
auna tafiyar tayi taga cikin mintina talatin zai kaita gida...


karya wata kwana ke da wuya taji an hankaďeta haďe da fisge jakar da tayi ma kyakykyawan riko,
wani irin ihu ta saki haďe da bin yaron da gudu,
inaaa gudun ba ďaya ba dan kafin kiftawar ido ta nemi yaron ta rasa,
tsayawa tayi a bakin titi tana haki tana kokarin maida hawayen dake neman fitowa daga idonta,
hijab din jikinta tasa ta share hawayenta haďe da juyawa zata cigaba da tafiya cike da tunanin halin da zata shiga na rashin kudin da take cancanawa..


"Mummy....,

juyowa tayi da sauri dan kamar cikin mafarki ta jiyo muryar,

*Ra'eess...*
ta furta a hankali wanda ya sanya idonta bijire mata har saida hawaye suka zubo,
balle motar yayi suka fito shi da kannenshi suka rungumeta,

Uwa uwa ce,
koda kuwa magajiya ce ta karuwai,,
nan fa Radiya ta fashe da kuka haďe da daga autarta ta kankameta kamar zata maida ita ciki,


Kafar Fatima ta hango cikin wani tsadajjen takalmi flat mai matukar kyau wanda ya dace da kafar da tasha jan lalle,
dagowa tayi ta kalleta tana takowa cikin doguwar rigar atamfar bubu taji stone work tana nufo inda suke,
fuskar nan tayi dau tayi kyau sosai,
hannunta rike da ďaya daga cikin yan biyun da ta haifa cikin showel,


"Ina wuni Anty,

firgigit Radiya tayi dan bata san ta karaso inda take ba,

"Lafiya lau.. kawai tace haďe da cigaba da hira da 'yayanta zuciyarta fal kishin Fatima..



"Teemah na zo mu tafi Hussain ya fara kuka,
sai a lokacin ta kalli Shamsu dake tsaye jikin motar yayi fresh sosai shima rike da dayan jinjirin,

Saurin kauda kanta tayi dan kar ya gano halin da take ciki,

"Ammi in nuna ma Mummy, Ra'ees ya tambayi Fatima cike da girmamawa,

"Yess my boy,
bari in koma mota akwai rana,
Anty sai anjima...
bin bayanta kananan sukayi suna ďagawa uwarsu hannun...





Mummy kingani abokin Abba ne ya bamu kudi da yawa,
kina so?

kallon motar tayi taga duk sun shige sun ďage tint glass tace
"Kawo in boye maka,
ina na kannenka?,
"yana cikin mota,
ya bawa Ammi da yawa itama,
in ce ta baki?

"A'a barshi,
wannan ma boye maka zanyi karka faďa musu,
hope kuna karatu ko?


Kafin ya bata amsa Shamsu ya danna mishi horn,
da gudu ya koma motar yana ďaga mata hannu,
ta window suka turo kai suna mata bye bye,


Duk yadda taso rike hawayenta yaki rikuwa neman dakali tayi ta zauna taci kuka ma'ishi ta kuma yi dana sani marar iyaka.....





Yau ma teba Mummy?
Ko kallon inda take bata yi ba karasa kwashe tebar cikin cooler,
miyar ganyen da sukayi wacce bata samu arzikin nama ko kifi lando ba ta mayar kan gawayin da ta sauke tebar,
na Goggo ta ďauka ta wuce mata dashi ďaki,


Tari ta fara yi sosai cike da faďa tace

"Wai har yanzu bazaki dawo hanya ba Goggo,
kullum Allah na nuna miki abubuwan da kikeyi ba masu kyau bane ya cire hannunshi akanki sai cigaba kikeyi,
da tsufanki kullum sai mugun abu kikeyi yana dada dawo mana,
kai gaskiya da ana canza uwa da tuni na dade da canzaki wallahi,

Ko ni da na faďa cikin wannan jarabawar nasani sarai hakki ne,
hakkin Suwaiba da zuri'arta,
na dade da mikawa Allah lamarina,
nasan wata rana zaizo rescue dina,


Maganin Goggo ta kuma zubawa cikin wutar tace

"Tun kina karama nake shan bakar wahala dake,
badan a gida na haifeki ba da zance daga tsatson Harďejo kika fito su suka canza min ke,
in ke sakara ce to ni bazai yiwu in zama sakarai ba,
ku uku ne a gidan nan dukkanku sakakku,
mazajenku basu ko waiwayarku sannan kice in nemi guri in zauna,
bana tunanin zan mutu nan kusa, nasani sai naga mutuwar zuri'ar Atika da tun shigowarta rayuwata ta tagayyara komai nawa...


*MUSADDIQ...*

jin Raudha tayi ihun sunan gudan jininta da ta shekara har da doriya bata sashi a ido ba yasata fasa bawa Goggo amsar da tayi niyya,
da gudu ta fito waje har tana bugewa da kauren ďakin,
tana shirin karasowa ta rungumeshi yayi saurin ja baya wanda hakan yayi daidai da shigowar su Baffa da Sheik,


Share hawayen da zubo mata tayi ta wuce daki ta dauko hijab,
ďakin Anni da ta bari Baffa ya shiga dasu,
sam baiyi niyyar shigowa da Sheik gidan ba, dan dai Papy ya matsa ne,


Shigowa Mummy tayi da sallama hannunta dauke da tray din pure water,
Papy, Papa da Sheik ne kaďai suka amsa sallamarta,
da ido Papy yabi Musaddiq yana ta kokarin su haďa ido,
kamar ance ya ďago suka haďa ya sakar mishi lafiyayyar harara,

Kauda kanshi yayi ya sake tamke fuska ciki ciki yace

"Ina wuni,

kallon shi kadai tayi ta maida dubanta gurin Sheik wanda tsufa bai hanata ganin Atika cikin fuskarshi ba,


"Ateek right?

Cike da murna Papy yace
"shine,
ashe kin sanshi,
hawayen daya zubo mata ta share tace

"Na fi kowa mu'amala da yayarshi,
lokacin inada karancin shekaru dan zan girme mishi da shekara biyu ko uku,
kullum sai ta ambaci sunanshi fin sau goma a rana,
duk wanda ya santa a cikin yaran gidan Harďejo yasan Ateek,
dan labari nashi take bayarwa Maryam din Harďejo ko mai babban suna su dinga yi mana fassara,


Kuka sosai ta fashe dashi na tuno ukubar da mahaifiyarta ta bawa Atika wanda bata da bakin faďawa wani..
Share hawaye Papy yayi yana matukar jin kewar rashin ganinta bawai dan ya rasa uwa a gurin Anni ba,
shima Sheik kukan ya keyi bayan an fassara mishi abun da tace....



Dakyar Goggo ta iya shigowa dakin,
a tsay tsaye ta gaisa dasu ta fita saboda rashin son ganin fuskar Sheik,
duk ta kalleshi sai gabanta ya faďi...




Hira sosai sukayi da Mummy, Papy da Sheik,
Papy yaso Daddy ya shigo yaga sauyin da matarshi tayi,

haka nan yaji ya kasa tsanarta duk ko irin abun da akace tayi,
bayan fitarta ne ya kewa Musaddiq faďa sosai akan Muhimmancinta duk ko irin laifin da tayi mishi,
ko gezau Musaddiq baiyi ba dan zuciyarshi ta kangare sosai bayajin akwai abinda zai sauya shi daga dawo ma mahaifiyarshi yanda yake da...




Zubo teban Raudha tayi ta zauna a bakin kofa tana ci saboda tsabar yunwar da takeji,


Hilal da ya shigo gidan bayan ya gama order abincin da zasu ci da kuma masaukin da Sheik zai sauka ya kureta da ido,


Karyewa Zuciyarshi tayi yaji abun na yawo a cikin jininshi,
blood is thicker than water,
lallai bature yayi gaskiya,


Bai bari ta ganshi ba ya fita ya je wani store dake kusa dasu ya lodo kayan abinci masu yawa har saida kuďin dake hannunshi suka kare,
yana zuwa kofar gidan yaga
Rilwanu,
kiranshi yayi yasashi ya shiga da kayan yace ya faďa musu inji Daddy,



Basu bama har Papy saida yayi murna sosai ya kuma sake zage damtsen yin addu'a har sai Allah ya daidaita su,


Ita kuwa Goggo cewa tayi hayakin da tayi ne,
ta dinga fankama nan da sati zaizo ya maida Mummy dakinta....





Gidan Anni suka yada zango nan suka ci suka sha sannan suka bararraje anata hira har bayan la'asar,


Anni hana matan tafiya tayi tace saida mazan su tafi,
haka kuwa akayi su Mami suka zauna a gidan suka raba dare suna hira ana fassarawa Anni da ummi....




Kuďi masu yawa Anty Reemah taba Mummy sannan ta je gidan Raliya tayi mata faďa sosai akan rashin taimakama su Mummy,
a sannan ne Raliya take faďa mata Daddy ne ya hanata yace in tayi sai ya saba mata,
dafe kai Reemah tayi tace


"Daddy yayi fushi da yawa, wallahi ko maganar Mummy baya son ayi mishi,


"Addu'a kawai zamu cigaba dayi danni ita kadai ke bani tausayi ba su Anty ba,
dey deserve it... Raliya ta faďi rai a bace...

sun dade suna hira suna nemawa mahaifiyarsu mafita....







Kwanansu Sheik Uku suka shirya komawa gida da yan uwa dan suje suga inda yake,

kyautar ban girma yayi ma su Mummy wacce zata mantar dasu talauci na wucin gadi,
tayi murna sosai da wannan kyauta dan saida tayi kamar zata mishi sujjada,
har suka tafi baisan cewa Mummy matar Daddy bace,
ya dauka kawai a gidan take zaune, ya dai san yayar su Papy ce....



*Cyprus...*

Da yake mansion din Sheik yana da matukar girma hakan yasa ya kwashe dukkansu,
harda Husna da suka taho da ita dan ta haihu,
dadin duniya babu wanda bai jiyar dasu ba,
duk companies dinshi saida ya nuna musu harda na wasu kasashen,

Saboda murna ya cire wani babban companynshi dake Holland ya mallakawa Papy a matsayin gadon mahaifiyarshi,
sannan ya bawa Hafeez wani abun shima,
gaba ďaya ya kasa controlling kanshi akan zuri'ar yayarshi....




Kwanansu biyar a garin akayi ma Husna tiyata aka ciro mata baby girl saboda haihuwar tazo da Matsala,

lokacin su Daddy sun koma Nigeria,
murna a gurinsu ba'a magana saboda dama cikin na yawan bata wahala,


Papy da kanshi ya shiryawa Mummy tafiya dan taje gurin yarta taga jikarta,


Ita dai a kullum haushin kanta takeji na biyewa zuciya tayi wa Suwaiba abubuwa marasa dadi kafin mutuwarta,
gashi yanzu danshin su take raba taji dadi,
lallai da ta hana auren Hafeez da Husna da sai takaici ya kusa ajalinta,
kullum bata da addu'ar da ta wuce Allah ya dawo da Nadeeya cikin koshin lafiya dan danta ya samu farin cikin rayuwa,
a yanzu ko ita bata samu farin ciki ba 'yayanta su samu,
ta fahimci farin cikinsu shine nata,
ďan zaman da tayi da su Radiya ta fahimci cewa ba kowani ďa bane ke sadaukar da farin cikin sa akan iyayenshi,
a nan ta koyi basu farin ciki,
in ta gansu cikinsa tasan itama zata kasance a ciki...






Ranar Suna Daddy ya sanya wa yar suna Suwaiba,
sosai dangi suka nunawa yar gata dan ta samu kaya na gani na faďa,


Mummy ta sake tsorata da ikon Allah da tazo taga daular duniyar da dangin Atika ke ciki,
inama Suwaiba na raye tazo ta dandani arziki,
wayyo,
ita nata dadin a lahira ta ďeboshi.....





Na fa lura da wani abu Anty,
Raliya ta faďi tana sanyawa Nour ďiyar Husna pampers,

"Me fa?
Anty Reemah ta tambaya haďe da gyara zama,


"Na kusa yin siriki, Raliya ta faďi tana murmushi..


"Wa kenan??


"Dadina dake ganewa Anty Raly,
Husna ta faďi tana ajiye kofin shayi,
ni ai tun tuni na sani,

Jamal ya hanani faďi,


"Kaii nifa ban gane ba,
wai me kuke nufi?
Anty Reemah ta tambaya cike da mamaki,


"Y'ata ta wajenki tayi kasuwa, soyayya sukeyi da Jamal,

Mikewa Anty Reemah tayi tace
"to ai ba sai kun faďa min ba, kuma iyaye ne,
in akwai alheri Allah ya tabbatar...



Dariya sukayi haďe da tafawa suka ce Ameen

Please Login or Register in order to submit comment