Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fice,


"aiko zaku mutu,
wallahi tallahi kaji rantsuwar da bata da kaff------

ido cikin idon da sukayi da Daddy ne ya hanata karasa mummunan furucinta,

ciki ta juya hawayen ido suka kafe sai na zuci da suka dinga kara kaini,
kasa zaune tayi tanata safa da marwa tana tunanin ta inda ta kuskuro har wadannan abubuwan suka cakude mata haka,
ga kayan dakinta duk an fitar dasu bare ta samo wasu cikin surkullenta tayi amfani dashi,
dakyar ta zauna tana maida numfashi kamar zata mutu......





Foiling naman walima Nadeeyah da Husnah sukeyi a cikin tray suna hira,

Mummy na bayansu tana hada coleslaw na dole dan ba yadda zatayi Daddy ya dauki nauyin walimar a gidanshi,

suna gamawa suka jere komai a inda ya dace,
rissinawa Nadeeyah tayi tace "Mummy akwai wani abun ne?
gyada tayi kawai alamar a'a kamar me ciwon baki,


Daki suka wuce dan yin wanka,
kaya kala daya Papy ya dinka musu harda su Anty Raly,
lace ne dark purple mai ratsin manyan pattern pink flower,
dinkin riga da skirt mai matukar kyau,
ko ina an sanya farin stones wanda ya kara kayata lace din,

*Bismid cream* Husna ta dauko tana shafawa tana dariya,

wayaga Baffa ango,
wallahi ni abun kunya ma yake bani,
su Daddy kuma harda wani daurewa karya ...... wai harda walima,
dariya Nadeeyah tayi hade da jan zip din rigarta tace
"ni kaina abun jinshi nake wani iri,
saidai ba yadda za'ayi da hukuncin Allah,


Badar sarkin nukufurci tana kwance cikin bargo tana latsa waya bata ma san suna shiri ba,

light make up sukayi wanda ya dace da fatarsu,
sunyi kyau sosai saboda lace din kalar farare ne,
dauri sukayi mai matukar kyau iri daya suka feshe jikinsu da turaruka masu kamshi da saukin karfi,


kara wayar Nadeeyah tayi alamar shigowar sako,
da sauri ta dauka dan tasan wanda yayi text din,
"baya kiranta a waya, amma text duk minti biyar yinsa yakeyi,
ko ya rasa abin cewa sai ya nemo write up na yaudarar maza, ko yadda zata kula da kanta, ko adduoi ya tura mata,
reply dinta koda kalma daya ce means the world to him,


*Yunwaaaaaaaa, plss ku kawo min abinci kar in mutu*.....


Dariya sosai tayi dan ganin mai sakon, ta mikawa Husna wayar,
itama dariyar tayi tace acici,

kinsan yau ya tashi da wuri to fa kowa ya bani a gidannan,

flat shoe suka saka suka wuce kitchen,
flask Nadeeyah ta dauka da hot chocolate da ta san yafi san karyawa dashi,
ita kuma Husnah ta dibi naman kaza cikin pepper din da sukayi foiling,
wani sakon ne ya sake shigowa..



*Nadeeyah so kikeyi in mutu ko, ba komai... ya sanyo alamar kuka* 


Reply tayi mishi tana murmushi tace

*Sorry, kana ina ne*


Yana ganin reply din yayi saurin kiranta
"ina BQ, yanzu muka dawo,
plss kiyi sauri cikina na ta kiran sunanki,
yasan ke kadai zaki taimaka,
kashe wayar tayi tana dariya suka wuce BQ din,



Murda kofar Husna tayi saboda ita ke da rangwamen kaya a hannu,

karo tayi da mutum shima ya sako kai zai fito,

subhanallah ta fadi hade ja baya tana kallon tray din da ya fadi kasa,
kallon shi tayi taga shaddarshi ta baci da source

"Ya salam.. Ya Hafeez dan Allah kayi hakuri,
wallhy bansan zaka fito ba,


Murmushi yayi yace "haba karki damu,
da kinsani bazaki shigo ba nasani,
ke da gaisuwa ma sai na roka, yaushe zakiso kiyi karo dani,

dariya tayi sosai tace
"kiji sharri Nadeeyah,
bari in duba maka kayan Ya Musaddiq ka canza,

"inyi yawo dai a ciki ya fadi yana goge jikinshi hade da kallon Musaddiq da yayi fuskar tausayi,

dariya yayi ya kalli Nadeeyah yace
"saura kiris a zare ran fa,
maza kije ki bashi break fast..


Da sauri ta zare takalmin kafarta ta shiga da sallama tana fadin "sorry pls,

rike cikin yayi ya kara bata fuska yace
"naki sorryn na koshi,

bude flask din tayi ta zuba ruwan zafi ta hada mishi tace
"gashi kayi hakuri dan Allah kar a zare ran,
in aka zare bamu san inda zamu sa kanmu ba,

"Dadi zakuji mana ku huta da acici,
sosai sukayi dariya Nadeeyah ta gimtse tata dariyar tace

"ai ci dole ne yayana,
kowa ma acici ne,
gashi kaji, plssssss, ta fadi tana karkace kai gefe,

"badan ni zansha ba sai dan tausayin hanjin cikina,

Saboda dariya saida Nadeeyah ta durkushe a gurin,
"dan Allah karka kashe ni,
bari in kawo maka wani abinci me nauyi,



kallon Husnah yayi dake kara jaddaddawa Hafeez suje ta bashi kayan shi ya saka,

"in kinje ki bashi riga kadai ta isheshi,
kinga sai kuji dadin zagin halitta ta,
ya karashe yana kai kofin bakinshi,
dariyar ma kin fitowa Husnah tayi suka fita tare da Nadeeyah,

Dariya Hafeez yayi yace
"manta da ita kaji,
gida zan koma in canza kaya,
bari in kira Jamal ya kawo min mota,

ciro key Musaddiq yayi yace "ga tawa kaje ka dawo kafin a fara walimar,

karbar keyn yayi yace "ka dai ajiye min nawa abincin kar ka cinye kai kadai,


"Haaahaha...
zan daina cin abinci kwata kwata a idon mutane,
gara in rage wannan kibar,
da zan iya ma harda tsawo zan rage,

"dariyar Shirmen Musaddiq Hafeez yayi ya fita yana jin dadin yadda al'amura suke kasancewa kamar yadda Mamma take so,

Allah sarki Mamma,
ina ma ana mutuwa a dawo kiga yadda wuya take neman rikide mana ta zamto dadi,
kiga yadda dan uwan da baki sani ba yake gatata mu kamar shi ya tsuguna ya haifemu,

Allah yayi miki Rahama ya fadi ya shiga motar zuciyarshi a dagule saboda tuno iyayenshi da yayi.......




Ana idar da sallar isha'i su Nadeeyah suka fara shirin barin gurin su Anni,

hankalin Nadeeyah a kwance ta gama shiri dan tasan yanzu su Anty Radiya sun bar gidan,

"kallon banza da habaicin talauci hade da rashin asali da suke mata yana sosa ranta matuka,

kalmar da Anty Raudah ta fadi na "anyi clean fata ta murje da abinci akan kari sai kace wata yar shugaban kasa,
a dai dinga tuno asali dan kar garin iyawa a wuce gona da iri!!


Wadannan kalamai sun matukar tsaya mata,
dan ma Musaddiq dake bayanta wanda dan shi Anty Raudah tayi mata habaicin yace
"Haba Anty, sai kace sa'arki,
dani take magana bada ke ba,
ku ke jawa kanku raini wallahi, yayi tsaki a hankali hade da cewa Nadeeyah ta kira Husnah su tafi...



Hannu ya kyasta mata a kusa da idonta,
a firgice ta dawo daga tunanin abubuwan da suka gifta dazu a gidan,
rage Murya yayi yace

"Tunanin su Anty ko?

Abin da ya kamata ki saba dashi ne tunda saidai in basu zo gidan ba,

in kika kula mutum a kullum burin shi ya bata miki rai to sai kiyi fatali da duk abin da yace, domin shi kadai zaiyi dakon bacin ransa,

"Zuciya is very special my sister,
fill it with love,
karki bari bacin rai ya samu kofar shiga cikinta, dan bacin rai na destroying duk abin da aka tanadarwa zuciya, dan haka bana san ganin tunani ko bacin rai nan a tare dake,
kinji ko?

gyada kai tayi hade da murmushinta mai kyau,


"Thats my lovely sis,

oya kira mana Husnah mu tafi,

kafin ta kai ga amsawa suka hango Husnah sun fito tare da Hafeez da Ruwaidah a tsakiya,

gefe kuma Jamal ne sanye da kayan bacci shima yana dosar inda suke, 


"Badai bacci zakayi ba,
Musaddiq ya tambayeshi yana mishi kallon mamaki,
jingina jikin motar yayi yace
"in banyi bacci ba ai sai in kasa moruwa,

yau ko tamola bata kaini garuwa ba,
wahalar da Baffa ya bani yau ba kadan bace,
"duk wani abokinshi da yazo gurin daurin aure wanda baida mota saida na maidashi gida,

just imagine kaine,

hmmm thank Goodness akwai ruwan zafi,
da yau sai na tashi aiki, ya karashe yana danna bayanshi,


"Lazy youth!!

Ruwaidah ta fadi tana boyewa a bayan Hafeez,

dariya ta basu dukkansu Nadeeyah tace
"duk kokarin nan da yayi ki kirashi lazy,

murya cakwai tace
"Allah Adda he is very lazy and he can exaggerate,

yanzu haka gida uku yaje,
haka Mami ke fama dashi baya san a moreshi,


Rai a bace Jamal yayi inda take yana fadin

"ni sa'anki,

wani irin ihu ta saki hade da rugawa ciki,
bayanta yabi da gudu dan yaci alwashin ko a gaban Papy ne sai ya gurji bakinta,


Dariya Hafeez yayi yace ku shiga mota ku tafi dare nayi,
indai su Jamal ne kullum sai sunyi sau ba adadi,

ya kasa gane dadin tsokanarshi takeyi,
saboda bata da abokin wasa shiyasa ta maidashi abokin wasanta, shi kuma san girma yasa baya wasa da ita,

" haushin hakan yasa ta rainashi sosai,
motar suka bude suka shiga suna dariyar Ruwaidah da Jamal,


Sallama sukayi ma Hafeez da kunya ta hanashi katabus saboda irin kallon da Husnah take mishi, 
dalilin da yasa ya sanya Ruwaida a tsakaninsu kenan da ya fito yi musu rakiya,
ko a da lokacin da yayi wauta da rudin kudi mata ke kawo kansu,


ita kuwa Husnah ganin irin gidan da ta fito ya sanyashi jin kunyarta da taka tsantsan,
dan yasan tafi karfinshi, shi da bashi da cikakken asali kamar yadda Goggo ke yawan fada,

wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa,
gara ya nemi saffa saffa dai dai shi....



Mrs Tijjani Shattimah......
[01/04 3:08 PM] fareedah: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣0⃣
By *Aysha Ya'u kurah*






Kasa tabuka komai Nadeeyah tayi ta dauki wayarta ta latsa number Hilal,
sai tayi kamar zata shiga sai tayi saurin kashewà,
tun daren jiya take abu daya,
tasan yadda ya saba da yi mata text haka nan bazai ki turowa ba sai da dalili,


Abin da bata sani ba shine, duk latsin da zatayi ma numbershi tana shiga kadan sai ta katse,
da haka ya fahimci ta damu da rashin tura mata sakon wanda yayi shi domin fahimtar wani abu daga gareta,


Yana gama shiryawa ya dauki wayar ya latso ta,

ajiye kwan da take kadawa tayi da sauri ta dauka ringing na farko,
"ajiyar Zuciya yayi a hankali,

ita din ma hakan tayi amma nata ya dan fito kadan,

shuru ne ya ratsa wayar na yan sakwanni,

shi ya fara katse shurun ta hanyar cewa

"ina kwana Anty,

saura kiris wayar ta fado a hannunta tayi saurin riketa tace "kayi Hakuri,
ina kwana,

"a'a ai ni ya kamata in fara gaisuwar,
kina nan lafiya?

bata amsa ba ta sake cewa

"ina kwana, yasu Anty?

dariya yayi mara sauti yace "kowa lafiya,

"harda k---

shuru tayi ta kasa karasawa,


"Harda ni Nadeeyah,
lafiyata kalau,

alhamdulillah ta fadi a zuciyarta,

a fili kuma tace
"to Masha Allah,

gyara tsayuwarshi yayi yace "jiya kuma bakiga sakona ba,
ke kuma baki damu ki turo ba,
shikenan da mutuwa nayi haka zaki manta dani bare har in sa ran addu'a,


cikin rawar Muryar da take nuni da alamun tayi matukar missing sakonnin shi tace
"Dan Allah kayi hakuri,
na rubuta sai na kasa turowa,

"ehen me kika rubuta?
fada min da baki,


toshe bakin tayi da hannu taki sakinshi dan bata san abun da zata ce mishi ba,
tana jiyo Muryar Hinad na cewa "Papa na kiranka,

muryarshi taji bayan fitar Hinad yace "ina jiran ganin sakon irin na jiya sakk,
zan gane rubutun na jiya da na yau,
sai na jiki ya karashe hade da kashe wayar ya sauka kasa gurin Papa....



*******

Karfe goma na dare Mummy ta shigo dakin su Nadeeyah bayan ta gama kashe kayan kallon parlon,
kallon Nadeeyah tayi wacce ke zaune da blue riga da wando na bacci,
tasan Nadeeyah ce kadai a gidan zata iya yi mata aikin tashin asuba,

"Nadeeyah,
dan Allah da asuba ki tashi Musaddiq,
ki hada mishi break fast dan jirgin 6 zai bi zuwa abuja,


Yaye bargo Badariyyah tayi da sauri tace
"zan tasheshi Mummy,

"a'a Badar kar kisa ya makara,
9 ake son ganinsu,

"Allah Mummy zan sa alarm ta fadi tana hararar Nadeeyah,

to shikenan Allah ya kaimu,
dan Allah kar ki bari ya makara,

"karki damu Mummy ta fadi hade da dauko wayarta ta sanya alarm karfe biyar da rabi dan tsabar kwancewar noti,
yaushe har ya tashi yayi wanka ya ci abinci,
al'amuran Musaddiq lokaci suke bukata,
mutumin da sai afi awa ana tashinshi a bacci,

Badar kuwa cike da murnar zata kasance da abin kaunarta ta ja bargo ta rufe kanta....






Karfe hudu saura Nadeeyah ta tashi,
kallon yadda Badariyya ke bacci ba tare da motsi ba tayi,
a zuciyarta tana tsoron tashinta kar ta jama kanta zagi,
"dakyar ta fara tashinta tana fada mata lokaci yayi,

inaaaa Badar bacci yaci karfinta ta juya ta cigaba da baccinta,


Hudu da yan mintuna Nadeeyah ta fita dan tasan in dai aka biyewa Badar tofa babu abin da zai hana Musaddiq kaiwa tara a gidannan,


Murda kofar dakinshi tayi taji karar alarm a gefenshi amma ko gezau baiyi ba,

karasawa tayi tana murmushi ta dauki wayar ta kara mishi karan a kunne,


"ummmmmm kawai ya fàdi hade da toshe kunnenshi da pillow,

ajiye wayar tayi a kan gadon ta yaye bargon jikinshi ta fara zare pillon,


kara kankame pillon yayi yana sambatun dadin bacci,
dan a wannan lokacin wani irin rarrashi shaidan yakeyi ma mutum mai sanya bacci dadi,

babu lokacin da yakai karshen dare dadin bacci,
dakyar ta iya fisge pillon wanda hakan yayi sanadiyar fadawanta jikinshi da karfi,


cikin bacci ya kankameta ba tare da yasan yayi ba,

kici kicin kwace kanta ta shiga yi wanda hakan yaki yuwuwa saboda girma da tsawon Musaddiq,
gaba daya jinta tayi kamar wata babyn roba a jikinshi saboda tsabar kankantar da ta mishi,

ganin ta kasa kwatar kanta ya sata sanya hannu a hancinshi ta toshe,
tasan dole ya bude ido saboda babu hanyar numfashi,


wani irin numfashi ya saki ta baki hade da bude idonshi ya sanya su cikin nata,


kara runtsesu yayi dan ya dauka duk cikin mafarkin da yakeyi ne,
yana kara rufesu ta kara rufe hancin,

bude idon yayi gaba daya kamar zaiyi kuka yace

"menene?

dariya tayi maganarshi ta mantar da ita a inda take tace
"ka tashi karfe shida har da rabi, ga Daddy can ya je dauko bulala,
*Haka Mummy ke ce mishi in yaki tashi ya tafi makaranta*,
Husnah ta bata labarin jiya kafin su kwanta,


"uhmmm ni zan kara minti biyar ya fadi yana sake runtse idonshi,

"Hello Daddy yaki tashi wai bazai je inter-----

da sauri ya mike har yana bige mata hannu,
dariya ta saki tace
" kayi sauri kayi wanka,
lokaci ya kusa,
bari inyi saurin hada maka break fast,
bayi ya fada yana lumshe ido kamar zaiyi kuka,
daurewa yayi ya shiga shower ya wanke jikinshi tass,


A bayin ya shafa mai bayan yayi alwala,
saida ya idar da Sallah ya shirya cikin kananan kaya masu kyau cool colour,
dakin ta kawo mishi kayan kari lokacin biyar da minti goma,


"Bana karyawa da wuri,
dan Allah ki maida, in naje can zanci abinci,


"noo gara kaci tun yanzu in kaje can babu time,
hada mishi tea tayi ta bashi bread guda biyu ta mika mishi plate din kwai,

ka canza wadannan kayan,
kai da zaka shiga cikin manyan mutane sai a ganka kamar area boy,


"dauko min wasu kawai ya fadi yana mai jin kuncin tashi daga daddadan baccin da yakeyi,


Drawershi ta bude tana dariya ta fito da golden brown shadda mai kyau da yauki,

yana gama karyawa ta fita tabarshi,
kayan jikinshi ya canza hade da feshe su da turare,

milk takalmi yasaka sannan ya ratayo jakar takardunshi da laptop dinshi ya fito parlon,


"ina hular fa?

ta tambaya tana karasowa inda yake da leda a hannunta,
shi yama manta da wata hula yace
"ta dauko mishi,
"gefen jakar hannunshi ta bude ta saka ledar hannunta,
taba gurin yayi yace
"meye wannan?

"zaka gode min in kaje can,
karka bude,
zama yayi akan kujera yana jiran ta kawo mishi hular,


Hular data dace da kayan ta dauko ta mika mishi,
kanshi ya miko mata a cewarshi bashi da karfin daga hannu,
gyara karin hular tayi ta sanya mishi ita akai,
yayi kyau matuka kamar wani babban mutum mai cike da haiba da kwarjini,
sakkowa Daddy yayi yana dariya yace

"Saaaadiq ne yau da tashin asuba,
baki ya turo gaba yace bakai kasa ta dameni ba,
dariya Nadeeyah tayi ta tsuguna tace
"ina kwana Daddy,

"lafiya kalau yar albarka,
kin samu ladan yayanki,
Allah ya biyaki,
murmushi tayi taja da baya ta barsu suna zantawa,
kudi masu yawa Daddy ya bashi sannan yayi mishi fatan alkhairi,

"har bakin mota Nadeeyah ta rakashi da addu'a sannan ta fada mishi in zai shiga ya karanta suratun Nasr kafa uku,


Har Malam Ali ya tada motar tayi saurin cewa ka kira Mummy da Daddy lokacin da zaka shiga gurin,
adduarsu mai karfi ce a gareka,

gyada kai yayi yana murmushi ya daga mata hannu,
itama hannun ta daga mishi tana fadin Allah ya bada sa'a,
saida motar ta fita a gate din sannan ta koma ciki ta gyaro mishi dakinshi da kyau,
lokacin biyar harda minti arbain,


Dakinsu ta shiga ta ji karar alarm din Badar,
tana hangenta tayi tsaki ta kashe wayar gaba daya,
samm baccin asara yasata ta mance abin da kudiri niyyar yi,

" bayi Nadeeyah ta shiga tayi wanka ta canza pad saboda tana hutun sallah,

komawa tayi ta kwanta tana sauraron karatun qu'rani har bacci yayi gaba da ita,



Badar bata tashi ba sai karfe tara da minti ashirin,
da sauri ta duro a gado tana fadin "na shiga uku,

kallon agogo tayi taga lokaci,
jiki na rawa ta fito parlor taga ba kowa,
dakin Musaddiq ta fada ta ganshi a gyare kamshi mai dadi hade da sanyi na tashi a ciki,
tsaki taja mai nuni da tsanar irin lalurar baccin dake dawainiya da ita.......




Karfe takwas na safiyar ranar Papy da iyalanshi sukayi shirin komawa Gombe,
gidan Baffa suka wuce dan suyi Sallama dashi,


A kofar gida suka tadda shi yana gaisawa da makota,
fara'arshi ce ta karu da ya hangosu,
Suna karasowa ya gabatar musu da danshi, jikokinshi, da amaryarshi,

Gaisawa sukayi da su,
Alh Jogana ya kalli Hafeez yace
"wannan ba sai an fada min ba,
dan marigayi Adamu buzu ne,
kamanin sun nuna kansu,
dariya Baffa yayi yace
"kwarai kuwa babban danshi ne,
Allah sarki...
Alh Jogana ya fadi cike da tausayi,
har yanzu dai ba'a samu labarin danginsa ba,
mutumin kirki,
ko yaushe na tambayeshi sai yace min daga Agadez yake,
amma sunan garin da yake a agadez ya bace mishi,
ba mamaki maraya ne,
Allah yayi musu rahama,


Ameen... dukka mutanen gurin suka ce sannan Baffa ya sallamesu ya shige gida,



Wata sabuwar gaisuwa suka sake yi Baffa yace "Har kun shirya tafiya,
"eh Papy yace hade da fito makudan kudi a aljihunshi ya bashi yace koda za'a bukaci wasu abubuwan,
ya cigaba da cewa
"na biya kudin furnitures a *landninterior* Raliya zata kawo matar tazo taga taga yanayin girman kayan da zasuyi,
receipt din na gurinta,


"dan Allah duk abin da ake bukata a kirani,
in shaa Allah ana gama komai zansa ranar da zamu kawo Anni itama tazo tayi zamanta a gidan babana, ya karashe yana dariyar ganin fuskar Anni,

Godiya sosai Baffa yayi mishi hade da sa albarka,


"Ina Goggon take?
Anni ta fadi tana mikewa dan taje su gaisa,
rakata Baffa yayi yace "tana ciki babu lafiya,
jiya saida wata nurse a makota tazo ta kara mata ruwa,
mikewa sukayi gaba dayansu suka shiga dakin da Goggon take kwance tana kallon sama,


koda suka shigo bata waigo ta kallesu ba saboda kar ta karawa kanta bakin ciki,
har suka karaci yi mata sannu bata ce musu ta tafasa ba,
dan tasan yadda takejin tashin kamshinsu in ta kallesu zuciyarta na iya fashewa,


"Tana jiyo Baffa a tsakar gida yana fadin
"zafin ciwo ne, haka takeyi in bata da lafiya,

har bakin mota ya rakasu yana godiya hade da sa musu Albarka......



Cikin yaran shida uku yayan kusoshin gwamnati ne, uku kuma kannen matar GMD ne,
interview din da za'a yi musu ma duk sun dauka camouflage ne,
dan a ganinsu matsayin iyayensu ya wuce su tsaya yin wani interview,
shiyasa basu damu ba sam,

lift suka hau aka nuna musu hanyar office din GMD,


Hira sukeyi sosai saboda sanayyarsu da juna,

shidai Musaddiq Addu'a yayi tayi kamar yadda Nadeeyah ta fada mishi,
suna gab da shiga office din wata mace ta dakatar dasu,
basu samu ganin GMD din ba saboda yana cikin meeting,
yadai bari ayi musu interview din,


Abin da yaran basu sani ba shine ba yan Nigeria bane zasuyi musu interview din,

samun aiki a irin gurin ba sanayya bane, dace ne da kuma kwazo,


Da ďan kanwar matar GMD
*Zubair Ribeh*
aka fara,

yana shiga gabanshi ya fadi saboda irin mutanen da ya gani a gurin,
takardunshi suka bukaci ya miko musu,
nan ya mika musu a mutunce,
dubawa sukayi sam basu damu da ganin takarddun Nysc dinshi ba,
second class lower gareshi a
*Bsc Chemistry* ,
tunda daga nan suka rufe takardunshi suka tambayeshi abubuwan da ya kamata,
yayi iya kokarinshi ya basu amsa har jikinshi ya jike sharkaff,

sallamarshi sukayi hade da tafa mishi dan yayi iya kokarin yake da dashi,
haka ce ta kasance da sauran yaran,
mai first class din cikinsu da suke da hope akanshi shima ya kasa amsa wasu abubuwan,
sarewa sukayi har suka fara tunanin daukar *Zubair* dan shi kam result dinshi ya nuna kwakwalwarshi ce ta bashi,
sauran kuwa duk siyan musu akayi,


shigowar Musaddiq ne ya katse musu tattaunawarsu,
da fari sun ki yi mishi dan ganin mutane shida kadai suka nema,
babban cikinsu ne yace abashi chance may be su sameshi da abubuwan da sukeso,
takardunshi suka bukaci gani, yayi saurin fitowa dashi,

ledar da Nadeeyah ta bashi ce ta fado kasa,
da sauri ya dauketa hade da mika musu takardun cike da girmamawa,


Juya ledar yayi yana murmushi shi kadai,
nan take kalamanta suka shiga yi mishi yawo a kai,
baiyi wata wata ba ya fito da wayarshi, kasa kasa ya sa wayar ya tura ma Mummy da Daddy text din su tayashi addu'a yana cikin gurin,
har zai mayar da wayar aljihu yaji karar shigowar text,
dubawa yayi hade da murmushin ganin sakon Nadeeyah,

kamar tasan yana bukatar irin wannan adduar a wannan lokacin,
maida wayar aljihu yayi ya dago kai ya kallesu,

Saida ya kusa kaiwa kasa saboda yadda suka zuba mishi ido,

"am very sorry pls, ya fadi dan yasan laifinshi,


cike da bacin ran rainuwar yan nigeria wata mata tace

"nan gurin wasan yara ne,
in ba aiki kazo nema ba, chatting kazo yi ka fita dan babu wanda ya zai matsa maka,,

kartawa cikinshi yayi ya fara basu hakuri cikin harshen turanci yace


"ina bukatar addu'ar iyayena, domin addu'a ita kadai ce zata samar min wannan aikin,
shiyasa na tura musu sakwanni saboda su tayani addu'ar samun aikin,


jikinsu ne ya mutu duk sukayi sanyi suka maida fushin da suke da niyyar sauke mishi,

tambayoyi suka shiga yi mishi akan yadda ya kamata a sarrafa gas da karafan gas,

da yake I.T din da yayi a cyprus a companyn gas yayi shi, nan ya basu gamsashiyar amsa mai cike da ilimi,


Saboda tsabar burgesu da yayi basu san suna jefo mishi wasu tambayayoyin ba,

kaca kaca suka fada da lamarin Musaddiq,
ko amsa zai basu saiya russuna,
duk inda bature yake yana matukar san girmamawa,
nan take suka mike suna tafa mishi hade da jinjina mishi,

wata takarda mace tayi signing tace
"congratulations my dear, ta mika mishi takardar,
har kasa ya tsuguna ya karba hade da sujjadar godiya ga ubangiji,


sunan *Zubair* suka kira shima ya shigo da saurin shi,
takardar shima suka mika mishi ya hau musu godiya hade da kukan murna, rasa inda zai kai murnar da yake ciki yayi dan yasan yau mahaifiyarshi bazatayi bacci ba saboda murna,
Allah ya taimakeshi,
yanzu zai tallafi yan uwanshi da mahaifinshi.....


Sauran yaran basu damu ba saboda dama aikin ba damunsu yayi ba,
iyayen keson gina su saboda gaba,


Sosai Dr Barau

Please Login or Register in order to submit comment