Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ya kasa dauke idonshi a kan Papy,
yanayin maganarshi,
da komai irin nashi ne,
gayu, gogewa da yarinta ne kadai ya banbanta su,

taba shi Goggo tayi tace
"lokacin Sallah ya kusa tashi ka shiga kayi alwala,

da sauri Papy ya kalli agogon hannunshi yace "uku da kwata ne yanzu Inna lokaci baiyi ba,

tun Goggo na daurewa kar ta fara nuna mishi halinta,
har saida ya kaita bango ta dakawa Baffa tsawa tace "ya tashi su wuce daki,

wannan mutumin in ba aljani bane to maye ne,

jiki a sanyaye Baffa ya tashi yace ma Papy "yaya Sunanka,
da sauri papy yace "Abdallah" nan Baffa yayi ajiyar zuciya yace "ba SAIFU bane,
Ma'u ba saifu bane,
duk tunanina shine shiyasa na cika da tsoron ya za'ayi wanda ya mutu ya dawo,
nasan ni na binneshi da hannuna,

kallon Papy Goggo tayi tace "kaji ko,
dan Allah tashi ka fitar mana a gida,
kuma karka sake zuwa kaje can ka nemi ubanka..

Nan tsakar gida suka barshi zaune yana ta nazarin abubuwa,

kodai da gaske bashi bane mahaifinshi,
sai da yayi wasu yan mintuna sannan ya tashi hade da gamsar da zuciyarshi koma meye in Anni tazo zata warware mishi komai....




Ita kuwa Goggo safa da Marwah ta dinga yi a daki tana tunanin ta inda wannan mutumin ya fito,

tasan a hannunta saifu ya cika,
kuma a gabanta aka binne shi, anya ba aure Baffa yayi ba lokacin da yake tafiye tafiyenshi,

katse mata tunani yayi yace "Ma'u wannan yaron ko dai dan Hardejo ne,
kodai..... saurin katse shi tayi murya a kausashe tace "ko kuma naka ba,

ni zaka ciwa Amana Muhammadu,?

ashe dama kayi aure a boye ban sani ba,

"Nan jikin Baffa ya fara rawa yace "wallahi banda Atika ban taba auren wata mace ba, daga ke sai ita,

kwafa Goggo tayi cike da masifa tace "gaskiya zatayi halinta ai gobe,
da bana son yaron nan ya dawo gidannan amma gobe da kaina zansa Hafeez ya kawo shi dan a warware min wannan kullin,

ina ganin watan jin kunyarka ne ya tsaya,

saboda sanin yana da gaskiya shiyasa yace "Allah ya kaimu,

komawa yayi ya zaune a zuciyarshi yace "shi yaushe ma ya kalli wata mace a matsayin mace har ya aureta,
har yanzu gani yakeyi duk duniya babu macen da ta kamo kafar ma'u a komai,
sauran mata duk kallonsu yakeyi kamar gumaka,
tsaki yayi yace "Ma'u batayi mishi adalci ba,
tasan bazai taba cin amanarta ba,

amma babu komai gobe gaskiya zatayi halinta...



Haka suka kwana dukkansu zuciyoyinsu ba dadi,
kowa da abun da yake sakawa a ranshi,
har gari ya waye Baffa bai bar hango fuskar Abdallah ba.....



**********●●●*******

Karfe biyu da rabi suka iso kaduna,
Hotel din da su Papy suka sauka can Badamasi ya wuce dasu,

bayan sun huta a masauki suka ci abinci sannan ne Mami ta tambayi Papy dalilin zuwan nasu,

bai amsa ta ba saboda yaga Anni ta dan kashingide tana son tayi bacci,


Ruwaidah ya daura akan cinyarshi yace "me Mamana tayi miki jiya kika duketa,

irin kukan nan da tayi nasan ba karamin duka kikayi mata ba,


Harararta Mami tayi tace "ai badan Anni ba walhi da sai na balla hannunta sai ayi dauri,
kaga daga nan ma huta da barna,
turo baki Ruwaidah tayi hade da tura kanta cikin kirjin Papy,

"ni kike turowa baki,?
mami ta tambaya tana nuna kirjinta da yatsa,

a ina ta turo miki baki,
ki kyalemin uwata ta huta,

shikenan dan bana nan bazatayi abin da takeso ba,


Mikewa Mami tayi tace "ko kai da kana nan sai ka tayani,

man gyada na zaune cikin jarkarshi ta dauko tukunyarta ta wasan yara wai zata soya dankali,

tasan jarkar tafi karfinta haka tasa karfi ta yar da ita kasa,
gaba daya kitchen da store babu inda bai samu albarkar mai ba,

"tabbb...
ai Mami kin ma mata da sauki, da kin cire hannun ne sai a sa mata na roba..

harara Papy ya jefa gefen da Jamal ke zaune yana latsa waya kamar bashi yayi maganan ba,


"shikenan dan ta zubar da mai sai a duke ta,

ba koyon girki takeyi ba,

in bata koya ba waye zai dinga tayaki aiki,

"Na yafe Mami tayi saurin fadi tayi hanyar bayi tace "ka cigaba da shagwaba yarinyar nan,

ta riga ta maida mu kamar kakanninta,

bayan Ruwaidah Papy ya shafa yace "rabu da Mami kinji,

zan siyo miki kayan abincinki ki koya da kanki ki dinga dafa min inci kinji ko?
Gyada kai tayi tace "kuma bazamu samma Yaya Jamal ba,

dariya papy yayi yace
"eh mana wama zai bashi,
yaje can yaci jagwalgwalon Mamin shi,


dariya sosai Jamal yayi yace "opposite,
Kuma in na kara ganin kin taba ma Mami ko da gishiri ne sai na yanka hannun da wuka,
murguda mishi baki tayi tace "ni da Papy zai siyomin nawa me zanyi da naku,
ko kitchen din mami ma bazan kara shiga ba,

"yauwa Good Girl,
muna komawa zan yi miki cefanenki,
karki kalli kayan Mami sun tsufa,


mikewa Jamal yayi yana dariya yace "har abincin Mami ma kar ta kara ci papy,
ta dafa nata da kanta,

dakuwa Papy yayi mishi ya fita daga dakin yana dariya....



Suna idar da Sallar la'asar Papy yace su shirya zasu je wani guri,

manufar shi nakin fadawa Anni shine kar ya fada mata suje bashi bane hankalinta ya kara tashi,

gara in suka je yaga bata sanshi ba sai su tafi ba tare da ya daga mata hankali ba,

tun yana shekara bakwai ya yankewa kanshi daina matsa mata akan maganar mahaifinshi,
domin ya kan ganta cikin tsananin damuwa duk ranar da yayi mata maganar,
a irin yadda ya taso yaga ta wahala akanshi shi yasa baya san ganinta cikin damuwa ko kadan...



Biyar saura suka isa kofar gidan,
motar Mummy Hafeez ya gani a cikin gidan,
Addu'a ya fara yi zuciyarshi na Allah yasa kar su hadu su wulakanta bayin Allahn nan,

gabanshi bai tsananta faduwa ba saida ya jiyo muryar Radiya,

farin sani yayi mata akan rashin mutunci,

dake wa yayi ya karasa ciki dasu,

Sallama sukayi dukkansu suka shiga cikin gidan,

daga cikin daki sukaji an amsa Sallamar,

mikewa Goggo tayi ta fito dama zaman jiransu take,

tana fitowa idanuwanta suka sauka kan Anni,
baya taja kamar zata fadi bakinta na rawa tace,

H-an-ne.......



Mrs Tijjani Shattima.....
[18/03 8:06 AM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣9⃣
By *Aysha Ya'u kurah*




Kallon rashin sani Anni tayi mata dan bata gane fuskarta ba,

nan dai ta fadada murmushinta tace "Na'am barkanku da gida, dafatan mun sameku lafiya,

Goggo dake tsaye jikinta na rawa kamar mazari tace "lafiya lau,

matsawa tayi gefe tace ku shigo ciki,

tabarmi Mummy ta fito dasu tace "a'a Goggo bari su zauna a waje yafi iska..


Bayan sun zazzauna an gaggaisa, Goggo ta kalli Hanne kirjinta na duka uku uku tace "baki ganeni ba ko Hanne?,

gyada kai Anni tayi tace "ban ganeki ba,


gyara zama Ma'u tayi kishi ya motso mata ta fara charge ta kalli Papy tace
"wannan ce mahaifiyarka??

Eh!!
Papy ya fada yana mai jin dadin an gane mahaifiyarshi a gidan,


"TABDIJAM Goggo tace "tana kallon Anni,


Wato Hanne ke kika haifeshi,?

wannan karan mamaki yasanya Anni cewa kwarai ni na haifeshi, dana ne,
lafiya??

Idon Goggo ya rufe ta manta da yara a gurin tace
"wato dama cikin shegen da kika dinga yawo dashi a tsakanin jalingo da Gembu dama Mijina ne yayi miki shi,

kenan lokacin da nake tausayin ki in su Harira suna tsangwamarki ashe kallon sakarya kike min mijina ne ya kunsa miki,


kallon Radiya tayi tace "maza tafi shagon Gidado ki kira min Baffan ku,

kafin Radiya ta mike Baffa ya shigo gidan da sallama,

yana ganin wucewarsu ya mike a shagon Gidado hade da amso musu lemu,

Goggo sam bata basu damar amsa sallamar ba tace "yauwa gara da Allah ya kawo ka,
nuna Hanne tayi tace ka gane wannan,?


kallonta yayi yaga samm shi bai taba ganinta ba,

ita kuwa Anni kallo ta bishi dashi idonta ya ciko da kwalla tana fadin
Alhamdulillah,
Alhamdulillah,

zama Baffa yayi yace "ban santa ba,
wacece ita?

Tafa hannu Goggo tayi tace "yau ni naga Bariki,

Hannen ce baka sani ba?

Hannen gidansu Inna wuro kanwar Harira,

wacce ta kunso cikin shege aka korota daga garinsu ta dawo nan,

ashe kai ka kunsa mata,
gashi dai kamanni sun bayyana min komai,
wallahi kaji kunya, ta karasa fadi tana haki..


"innalillahi wa inna ilaihir rajiun kawai Baffa da Papy ke fada,

ganin shurun da Baffa yayi ya kara hassala Ma'u ta fara surfafa masifa da bala'i,
babu inda baya rawa a jikinta,

da dai Anni taga shuru bazai taimakesu ba tace.

"Wallahi tallahi ban taba koda magana dashi ba...


shuru Ma'u tayi tana hararar Hanne tana fadin rainin hankali, uban wa zaki rainawa hankali?


"gyara zama Anni tayi ta kalli Baffa tace "in ka yarda dani ka bani dama inyi maka bayanin komai,

idonta ta mayar kan Goggo tace "in kikaji labarin abinda ya faru, da kuma yadda ya faru ni nasan gode min zakiyi ba zargi da zagi ba,

ni ko a yau Allah ya dauki raina walhy naji dadi saboda zan cika buri na,


kullum bani da tunanin da ya wuce ta yaya zan wankewa Abdallah zuciyarshi,

ta yaya zan hada shi da mahaifinshi,

nasan duniya tana da fadi wata rana ina da yakinin Allah zai amsa min addu'ata,

sai gashi ta dalilin Hafeezu adduar da na dade ina yi Allah ya amsa...
Alheri danko ne...



Kallon su Radiya dasu Hafeez tayi tace "dan Allah ko yaran nan zasu dan bamu guri,

"babu inda zasu, Ma'u ta fadi tana tafa hannu,


kallon Jamal Mami tayi tace "dauki Ruwaidah ku tafi mota,
noke wuya tayi tace "um um,
zare mata ido Mami tayi zatayi magana Anni ta dakatar da ita,
"zo takwara,
zo kuje ku siyo min Goro kinsan kin fishi wayau naki yafi kyau,

Jiki na rawa ta mike zata wuce ta taka kafar Radiya,

da karfi ta hankada ta cikin ihun azaba saboda tsinin takalmin tace "ke makauniya ce?

baki ta bare ta fara kuka idonta kyar akan Radiya,

da sauri Hafeez ya ja hannunta suka fita yana rarrashinta,


Harara Mummy ta sakarma Radiya tace "sai kace kina yi da sa'arki,

turo baki tayi tace "mummy zafi wallahi,

"tashi ki bamu guri dalla,mummyn ta fadi a hassale,

da sauri Goggo tace "babu fa inda zata,
gyara zaman ki,
abun kunya ce suka kwaso suji kunyar su kadai,


Girgiza kai Anni tayi tace "babu komai ma,
zauna! labarin an yishi ne, ba kirkirarre bane,
kaddara ce..





Kamar yadda kika sani ni kanwar Harira ce,
mahaifina asalinshi dan Gombe ne,
mahaifiyata ce yar jalingo..


Allah ya jarabceni da soyayya da dan kanin babanmu,
mun dade tare dashi,

kullum in na fita tallan nono a gurin yake zama har ya kare, mu tafi gida..


wata rana nono na yayi kwantai, yakai ni dare,

a hanyar mu ta dawowa gida kaddara ta afka mana,

kaddarar da dan adam bai isa ya tsallake ta ba,

kaddarar dake sanya rayuwar budurwa da iyayenta cikin mawuyacin hali...

kaddarar da ta sanya Mahaifina rasa rayuwarshi...



Bayan an fahimci ina dauke da ciki,
saboda tsabar kunya irin ta fulanin "da" mahaifina ya kashe kanshi ta hanyar fadawa cikin teku, a cewarshi bazai iya fuskantar jama'a ba..

mahaifiyata da kishiyoyinta suka sani a gaba,

bani da katabus cikin kauyenmu,
ko kofi na taba babu wanda yake dauka,

haka in na fita gari an dinga darewa kenan,


shi kuma wanda yayi min cikin an nemeshi ko sama ko kasa an rasa,

daga baya ne muka samu labarin mutuwarshi,

nan fa na cire duk wani tsammani na samun mijin aure,


saboda tsabar tsana da iyaye da yanuwana suka min na fita hayyacina na kare na lalace,

mahaifiyata ma kunya ta sanyata ta rame,

saida abin ya isheta tace "in shirya in tafi jalingo gurin mahaifiyarta,

To acan ma hakan take domin kuwa saida na gwammaci zama a Gombe da zaman jalingo,

duk ranar jumma'a sai Yakumbo kakata ta turani Gembu gidan Harira saboda gudun kunyar jumma'a,

tana tsoron kar mutane su shigo su ganni,

gaba daya yan uwa sun tsane ni ta ko ina,
bani da gurin shan iska...



wata ranar jumma'a mai cike da ban alajabi da tsoratarwa,
Jumma'ar da manta ta ga yan uwan mutanen kauyen Gembu abu ne mai matukar wahala..


Tun cikin dare nake jin kaina kamar bani ba saboda yadda cikina ya dinga murda min,

a hakan Yakumbo tace in fito in wuce Gembu,

tun a hanya cikin ke murda min har al'amarin yaso fin karfina,

cikin ikon Allah cikin ya lafa min har muka shiga cikin kauyen,

a daddafe na karasa cikin kauyen nayi gamo da tashin hankalin da yasanya cikina kadawa har kafata ta gaza daukata,

ina kallonka sanda ka dauko matarka da wata mace kuna gudu,

da rarrafe na bi bayanku har nazo lungun shiga gidanku,

nan gaba daya karfina ya kare, haihuwar ta taho min gadan gadan,

Cikin ikon Allah na haifi 'yata mace,
dankwalina na cire na nadeta dashi hade da mahaifar,

koda na duba ta na dinga jijjigata na tabbatar bata raye,

anan ne nayi kuka sosai har muryata ta dashe,

ban kara sanin inda hankalina yake ba saboda zubar jinin da nakeyi..

Iska mai karfi ce ta taso a kauyen wacce kafin ruwa ya sauka saida ta dauke gidaje,


wannan iskar ita ta farkar dani nayi saurin mikewa da gawar yata na fada cikin gidan ka,

koda na shiga babu kowa a gidan sai kasar da ke tashi tana rufe ko ina na gidan,

Daki na shige da sauri,
har cikin dakin kasar ke shiga saboda iskar ba ta wasa akeyi ba,

Iskar na lafawa ruwa ya tsuge kamar da bakin kwarya,

A nan ne naji ihun jariri daga waje,

da sauri na fito na iso gurin na hango dan Mala'ikan Allah cikin zani kwance a kirjin mahaifiyarshi,


Share hawayen idonta tayi tace
"Allah shi ke raya Matacce a lokacin da yaso,
in ba Allah ba waye zai raya wanda kasa ta rufe idonshi,

ko da na dagoshi jini ne ke fita daga cikin cibiyar da ba'ayi mata yanka da kyau ba,

nan take nayi daki dashi na gyara yankan cibiyar na daureta da tsumma,

ruwan bai tsagaita ba sai can gurin magriba,

yana tsayawa na kunshe yata na mayar da ita cikin gawar da Allah ya nuna ikonsa akanta,


A tare na rufesu da kyau saboda ko yadda aka zuba kasar wata rana ruwa ka iya dago gawar saboda sam kabarin baiyi zurfi ba..




A lokacin ne na fahimci wani abu guda daya game da cikin da nayi,
wannan abu kuwa shine bak'in zare mai shara shara wanda babu mai ganinsa sai ubangiji,

wannan zaren kuwa shine zaren kaddara!

kaddarar rainon Abdallah ta nuna Baffa tace "danka, ita ta sani na dauki ciki har sanadiyar shi nazo har wannan kauyen..

Da fari a kullum ina tunanin ni kadai ce Allah baya so a duniyar nan da ya jarabceni da yin cikin shege a cewar bahaushe,

haduwata da Abdallah na fahimci dama nazo duniya ne domin shi,


koda na koma gida Yakumbo tayi tayi ta rabani dashi,
a lokacin ne na nuna musu nima ina da hakki akan dana, tunda ni na haifeshi,

babu wanda ya taba samun labarin bani na haifeshi ba,

A lokacin da na bijirewa yakumbo sai ta koreni tace in tafi gurin uwata ita bazata iya da wannan abun kunyar ba,

bani da kudi haka na goyashi saboda bashi da kayan sawa,
ga rashin karfi nawa da nashi,


Cikin ikon Allah muka samu motar zuwa Gombe,
saida muka kwana uku a hanya muna tafiya,

duk kauyen da muka tsaya anan zan roki ruwan zafi in mishi wanka,


wata baiwar Allah ce ta hada min da wani maganin da nasha har na samu karfin jikina,
sannan ta bani wanda na barbada ma cibiyarshi hade da gishiri,


koda muka isa gida nan ma akayi min caaa ana Allah wadai dani,

ban saurari kowa ba na shiga gurin mahaifiyata na roki gafararta,
nace mata zan tafi neman abun da zan rike ďa na,

Bata kalleni ba amma shashshekar kukanta shi ya tabbatar min da tana cikin tsananin damuwa,

har na kai kofa ta kirani,

dawowa nayi naga ta kwanto gefen zaninta ta fito da kudi masu yawa na furar da takeyi ta bani ba tare da ta kalleni ba,

Murmushin farin ciki nayi na dauki wannan kudin a matsayin sa min albarka tayi,
nan nayi mata sallama na fita,

A tsakar gida sai zunde na sukeyi, babu wanda ya kula da halin da zamu shiga ni da dana,
su dai burinsu in rabasu da abin kunyar da na dauko musu,



cikin gari na wuce dan neman aikin da zanyi in ciyar da kaina,

Da farko a wani kango muke kwana wanda ake gininshi kullum,

kayan sawa na dasu nake dukunkuneshi saboda bashi da na sawa,
da safe in masu ginin sun zo sai in goyashi in tayasu dan in samu wani abun rikewa a hannu,

a haka har mukayi sati daya a cikin gurin,

Ranar da muka cika kwana takwas Abdallah ya tashi da ciwo mai zafi kamar bazai yi ba,

saboda rashin sanin abin yi na zauna na tasa shi a gaba nayi ta kuka,

daya daga cikin masu kula da gidan ne ya tausaya min ya dauke mu a gurin ya kaimu wani shagon kwano yace mu dinga kwana a ciki,

Sannan ya nemo min bedi da yawa da icce da tukunya yace in dafa mishi ya dan sha ruwan in mishi wanka,


kafin inyi mishi godiya naga ya fita ya karbo wata kwarya,

tuwon dawa ne a ciki da miyar kuka,

nan na hau ci kamar karamar zakanyar da taga nama,


A haka dai muka cigaba da rayuwa har na samu aikin shara a wani gurin gwamnati,


saida na shekara biyu ina aiki a gurin,
a lokacin Abdallah ya fara girma amma yau da lafiya gobe babu,


kullum matsalar cibiya yake fama da ita,

saida ya shekara bakwai sannan na kaishi asibiti,
anan ne ake fada min tarin datti ne ya shiga cibiyar,

jinjina tsawon rai irin nashi likitan yayi da na bashi labarin yadda na sameshi yace "lallai yaron nan Allah yana san saukar da rubutacciyar aya ta dalilinshi,

anan dai likitan yayi mishi aiki,

cikin lokaci kalilan ya samu lafiya muka dawo aikinmu,


kullum tare muke zuwa yana tayani,

A gefen gurin da nake shara akwai wata makaranta,
da naga yana yawan zuwa gurin ya tsaya, kuma yana sha'awar karatun, sai na kaishi makarantar, islamiyya ma yana zuwa ta allo sannan ina koyar dashi a gida..


gwagwarmaya babu irin wacce bamu sha ba ni dashi,


Lokacin da ya gama makaranta, ya fito da sakamako mai kyau,

gwamnati ce ta dauki nauyin cigaban karatunshi saboda hazakar shi,

A lokacin da yake karatun ne muka dan fara samun sauki saboda in aka bashi kudi a nan gida yake barin su,
ya gwammaci in ya dawo gida muyi amfanin da kudin,



*Nasara*
ta Allah ce amma ni zan iya cewa ita ainihin kalmar ma'anarta shine Abdallah,


shekarar da ya gama jami'a aka bashi aikin koyar da yan aji daya a makarantar,

duk inda yaje a unguwarsu zakiji Ana fadin *Abdallah Hanne*,
da sunan da yake amfani kenan ko a makaranta,
ko kuma ace uncle Abdallah.. yaran unguwa yake tarawa yayi ta koya musu karatu..


jan majina tayi dan kuka na neman cin karfinta ta cigaba da cewa "tunda muke da Abdallah sau daya ya taba cemin

"Ina Babana *ANNE* sunan da yake kirana kenan tun yana yaro,

a ranar nayi kuka sosai wanda ya tayar da hankalinshi,

tun daga ranar duk gorin da ake mishi bai damunshi,
saboda yasan wani mai uban ma bazai nuna mishi jin dadi ba,

A kullum saidai in dinga fada mishi kana da uba,
kai ba dan shege bane,
kai dan sunna,
aure ne ya samar dakai,



Kullum addu'ata Allah ya hadani da mahaifin Abdallah koda sau daya ne ya ji wannan farin cikin da yayi dakon su shekara da shekaru,

bayan ta kai aya ta kalli Papy da ya fita hayyacinshi saboda tsabar kuka tace
"shine mahaifinka Abdallah,
wannan shine ya haifeka!


Rungume Anni Papy yayi ya tsananta kukanshi yace "duk duniya babu na biyunki Anni,

saboda ni kika bar gida, kika bata rayuwarki da lokacinki!

saboda ni kika ki yin aure,

saboda ki inganta rayuwata kika hana taki ta zama ingantacciya, why Anni,
Why??
Ya karashe yana kuka sosai,


Itama kukan takeyi tace "bani nayi ba Abdallah,
Allah ne,
yin Allah ne,
in ba Allah ba waye zai rabaka da iyayenka,

babu mamaki yayi haka ne domin ka zama nagartacce,

ya rabaka da danginka ne dan ka zama gawurtaccen mutum,

babu mamaki da kana gida duk wadannan abubuwan bazasu samu a gareka ba,

dalilin da yasa Allah ya barka da rai bayan ka shiga karkashin kasa ba karamin dalili bane..


Maimuna ma ta taka rawar gani a cikin rayuwarka,

tasoka a lokacin da kowa ke kiranka da dan gaba da fatiha,
Duk kushe ka da akeyi a lokacin kamar ana zugata ne,
ta tubure sai ta aureka,

Maimuna ta nuna mana kauna lokacin da kowa ya kyamace mu,


Cikin Kuka Mami tace "kinyi jarumtar da ko kwatanshi banyi ba Anni,

hadasu yayi ya rungumesu yace "banyi regretting rashin tashi a cikin yan uwana ba,

domin babu abin da ban samu ba a gareku,
uwa,
uba,
mata,
kawa,
Aboki,

ni ko me zancewa Allah,

babu abin da zance sai tarin godiya a gareshi da ya hada ni daku....




Shuru ne ya dan ratsa gurin,
sai ajiyar zuciyar kuka kawai ke tashi,

kallon farin ciki Baffa yakewa Papy,
fuskan nan tasu jike sharkaff da hawaye,


Hannun shi ya kamo ya sake fashewa da kuka yana fadin *SAIFULLAH*,
Ma'u dana ne,
*SAIFULLAH*,

jinina ne Ma'u......





Mrs Tijjani Shattima.....
[19/03 8:17 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣0⃣
By *Aysha Ya'u kurah*




*Rayuwa takaitacciya ce. Kada ka cika ta da damuwa. Kada dogon Buri ya dauke hankalinka daga mutuwa. Aikata alheri a kowane lokaci watakila shi zai zamo mabudin Aljanna a gare ka*.





Alkalamina bashi da karfin rubuta irin gigitar da Ma'u tayi,
a zaune take amma jinta take tamkar a tsaka tsaki take,
ita bata kai kasa ba haka bata kai sama ba,
jinta take kamar wacce take lilo a tsakiyar iska,
gaba daya hanyoyin sadarwa na jinin jikinta da kwakwalwarta sunyi balaguron wucin gadi..


Jin hannu da tayi cikin nata ya sanyata dawowa cikin hayyacinta a firgice,

kallon hannun tayi hade da mamallakin hannun,
ido cikin ido sukayi Anni tace
"Da fatan kin gamsu da bayani na,
da fatan kin tuno abubuwan da suka faru kamar yadda kika ji na fadesu,
yanzu kin yarda da maganata na cewa ban taba magana da mijinki ba,
na yafe miki zargin da kikayi min,
domin a yau bana fatan abun da zai bata min rai,
a cikin farin ciki nake matuka na ganin Abdallah na ya samu abinda yayi shekara da shekaru yana kawaicin tambayarsa duk da nasan babu ranar da zata fito ta fadi ba tare da yayi tunanin rashin mahaifi ba,

kullum in na kalli murmushinsa nakan hango damuwa a bayan murmushin,
wannan suna da ake kiranshi dashi na *ABDALLAH HANNE*, yana matukar yi min ciwo,
ansha zuwa gabanshi a kirashi da dan mace,
duk damuwar da Abdallah zaiyi bai taba yarda yayi ta a gabana ba,
sakin Goggo tayi hade daga hannun sama tace "Alhamdulillah,
Allah zan cika maka alkawarin da na dauka na yin azumi duk ranar da ka cika min buri na...

Murmushin farin ciki Baffa yayi yace

"Alhamdulillah,

Allah mun gode maka da ka dawo mana da saifullahi,
ina ma Allah zai dawo da Suwaiba ta dawo taga dan biyun ta,
sai dai kashh Allah baya barin wani dan wani yaji dadi,

kallon Mamaki Anni tayi ma Baffa tace
"kana nufin Abdallah yan biyu ne?

Kwarai kuwa Baffa ya fadi yana gyara zama,
Gaba daya ya manta da Ma'u da bai samun katabus in tana guri, ya cigaba da cewa
"su biyu mahaifiyarsu ta haifa, kamar yadda kika sani shi

Please Login or Register in order to submit comment