Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a hanunshi yana jin haushin dalilin da yasa ya mallaketa tun farko,
screen guard din daya fashe ya zare.. nan hoton da ke daure kan screen din nata da Musaddiq ya fito baroro,
maida wayar yayi da sauri saboda wani abu da yaji ya taso mishi,


Dakyar ya iya mikewa ya shiga dakin,
rub da ciki yayi yana hango wa kanshi halin da zai shiga,

yaso Nadeeyah kamar rayuwarshi,
daidai da second daya bata taba fita a ranshi ba,
sai gashi yau Musaddiq da bayan iyayenshi bashi da kamarshi shi yake son abun da yakeso,

juyi ya dingayi a gado ya rasa abun da zaiyi yaji sanyi cikin ranshi,
komai ya daina aiki a jikinshi,



Zainab ce ta fado dakin da gudu,
drawershi ta bude ta shiga tana fadin "boyeni yaya, Anty zata dukeni,

yadda ta rufe kofar da karfi ya sa takardun saman drawer zubowa kasa,
jiki ba kwari ya mike ya tattarosu ya zubasu a kan gado,
nan take zuciyarshi ta raunana da yayi tozali da zanen da ya gama satin da ya wuce,
tsugunawa yayi ya janyoshi ya zuba mishi ido,
dariyar dake matukar burgeshi yayi nisa cikin kallo ba tare da sanin halin da idanuwanshi ke ciki ba...

hannu yaji kan kuncinshi ana share mishi hawayen da baida masaniyar zubarsu,
dago kai yayi ya kalleta itama nata idon ya ciko da kwalla,
da sauri ya hada jikinshi da nata ya saki wani irin kuka mai tsayawa a zuciya,
ita kuwa da karfi ta saki nata wanda ya janyo hankalin su Anty Reemah da Papa da shigowarshi gidan kenan,


Da sauri ya turata waje ya sama dakinshi key,

Hinad dake lekenshi tayi saurin komawa itama kukan ta saki dan abin da bata taba gani bane tun tasowarta kuka a idon Hilal,
takardun ya tattaro yayi musu runguma kamar zai maidasu ciki, a lokacin kukan da yakeyi ya ci karfinshi dan har sheshshekarshi su Anty Reemah sunaji,
babu irin bugun da basuyi ma kofar ba yaki budewa,
da yaga sun matsa sai ya tattara duka takardun, ya zaga baya ya sanya musu wuta,
ganin hayakin dake fita ta kasan dakinshi ya sanya Anty Reemah sakin Kuka sosai tana fadin "dan san annabi Muhammadu Hilal ka bude kofar nan,

Papa kuwa ranshi ya gama baci ya dinga dukan kofar,
ko gezau batayi ba dan mugun karfi gareta,
murya a kausashe yace

"Muktar bude kofar nan,
wallahi kaji na rantse in baka bude ba zanyi maka mummunan furu---

bude kofar yayi ya tsaya a gurin,
har lokacin idonshi bai bar zubar ruwa ba,

da sauri Anty Reemah ta karasa tana share mishi hawayen, itama masu zafi na fita a idanuwanta,


Rungumeshi tayi tana tambayar dalilin zubar hawayenshi,
kamar ta sake kunno wutar cikin zuciyarshi haka ya kwantar da kanshi a jikinta yana kuka kamar karamin yaro,


Papa bai bi ta kanshi ba duk da shima ya shiga tashin hankalin ganin hawayen dan nashi,
bayan dakin yaje yaga komai ya kone sai toka,
dawowa yayi da sauri rai a bace yaja hannun Hilal,

"meye wannan?

Yanzu in abun nan da kayi yazo da tsautsayi fa?
dan iskanci ka rasa inda zaka sa wuta ka kona takardu sai a nan,


karkatar da kai kawai Hilal yayi baya ma gane fadan da Papa ke mishi,
abubuwa da dama ke mishi yawo a kai,

"Papa please,

Anty Reemah ta fadi cikin sigar tausayawa,
bai kalleta ba yaja tsaki ya fita shima zuciyar ta shi a karye take,
baisan me ya sanya Hilal kuka ba,
amma yasan koma meye ba karamin abu bane...




Anty Reemah kuwa zaunar dashi tayi tana rarrashinshi tana tambayarshi abun dake damunshi har ya sanyashi zubar hawaye,
kwanciya yayi a jikinta wanda har ya manta rabon da ya kwanta a jikinta haka,

Mugun tausayin kanshi yakeyi dan ya rasa makomar zuciyarshi,

"Tell me Babana,
menene?



Cikin muryar kuka yace
"Mum pls don't ask again,
ki zauna anan karki tafi ki barni,
hannu tasa ta share hawayenta ta fara shafa mishi kai,


Hinad ce ta shigo dakin ido jajur hannunta da plate din farfesun kifi ta tsuguna a gabanshi tace

"yaya ka tashi kaga nayi maka abun da kakeso,

"harda zobo mai dadi, Zainab ta fadi itama har lokacin bata bar kukan ba,

runtse idonshi yayi hawayen dake kwance ciki suka jika gashin idon,


Cikin muryar Kuka Hinad tace

"Yaaayaaa plss ka daina kuka dan Allah,
ka fada mana abun dake damunka,

Muryar Papa sukaji da karfi yana kiran Anty Reemah,
amsawa tayi tace tana zuwa,

"ki ce mishi ya fito mu tafi Masallaci,

tadashi Anty Reemah tayi tace

"Tashi kuje kuyi Sallah kaji,
in ka dawo sai ka fadamin damuwarka koma meye in shaa Allahu zanyi maka maganinta....



A tare suke jerowa kai kace wa da kani ne,
har Hilal ya dan dara Papa tsaho, bai tambayeshi abun dake damunshi ba dan baisan ji saboda kar nashi hankakin ya tashi,
nasihohi ya dinga mishi akan yadda rayuwa take

"dama dole a duniya mutum bazai samu abinda yake so daidai ba,
dole yau zuma gobe madaci,

Ganin hawaye a idonka ya fara tabbatar min da yanzu ka fara sanin me duniya take ciki Hilal,

wacece ita??

Wani irin kallo yayi ma Papa ya dauke kanshi dan baisan sake zubda wani hawayen,

lallai mahaifi daban yake,
yasan abun da zai raunata Hilal har haka bai taba wuce soyayya,

"Papa mu bar maganar,
she is dead,

"subhanallah Papa ya fadi cikin tausayawa,
hannun Hilal ya rike cike da rarrashi ya shiga bashi hakuri dan tsaff ya yarda ta mutun ne...





Dakyar Hilal ya ci wani abu sannan ya tashi ya wuce daki,
da ido iyayenshi suka bishi suna tausaya mishi dan sunsan mecece soyayya,
basu san tashi har gara ace mutuwar tayi da abun dake shirin rabasu ba,



Five missed calls ya samu a wayarshi na Musaddiq,
yana kokarin kira Musaddiq din ya sake kiranshi,
bai bari yayi magana yace

"ka fada mata?

Gyaran murya Hilal yayi yace "karka damu,
Nadeeyah is all urs in shaa Allah,

godiya ya shiga yi mishi wanda ya sanya Hilal ajiye wayar a kan gado,

wani irin tagumi ya zuba zuciyarshi na kukan rashin abin da ta dade tana dakon so,
yafi awa biyu zaune a haka...




Da wuri ta gama komai ta ciro wayarta a charge ta kwanta tana game,
bini bini ta duba lokaci,
ta kosa taji wani irin sakone wannan da har yake da lokacin badashi,
ganin da tayi goma ta gifta harda minti goma yasata fara rubuta mishi sako,

kafin tagama taji karar shigowar sako,
da sauri ta goge ta bude sakon...




*A rayuwa kowa yana tafe da kaddararsa, duk wanda Allah ya rubuta kaddararka ta zama tare dashi ne, to baka da dabara sai ka zauna dashi, naso kiyi zurfin karatu ta yadda zaki kere wasu matan kema a sanyaki cikin jerin masu ilimi sannan kiyi aure... amma hakan bazai yiwu ba saboda kaddararki batazo a haka ba, _I love Nadeeyah_ .... wannan itace kalmar da dan uwana yace in isar miki, Musaddiq na matukar kaunarki Nadeeyah, da fatan zaki amshi soyayyarshi, domin kun dace matuka, kuma nasan bazai barki ki zubda da hawaye ba, Allah ya barku tare kanwata take care.....*




Tana kaiwa karshe taji wani irin jirin da Allah ya taimaketa a zaune take, dan ta fadi,

Ya Musaddiq ke sonta,
"innalillahi wa inna ilaihir rajiun,

ya zama dole gobe tayi shirin tafiya Gombe kuma ta zauna a can,
ina zata iya da bala'in Badar,
su Anty Raudha,
uwa uba Mummy da ta dau burin duniya tasa a kan shi,

inaaa samm bazama ta taba nuna taga text dinnan ba,
da sauri ta kashe wayarta ta dukunkune cikin bargo....



*MAFARKI*


_Hannu tasa ta cire akan farar fuskarshi da ta koma jaaa saboda kukan da yaci, "rau rau idonta yayi murya ta fara rawa tace "Yaa Hilal, me ya sameka, wanene? Hannunta kawai ya rike dan kukan yaci karfinshi ya kasa magana, hawayen dake makale cikin idonta ya fara zuba kamar fanfo, a shagwabe tace "Dan Allah ka fada min, menene? Zaiyi magana kenan ya hango wani farin haske dan karami ya doso inda suke, hannun Nadeeyah ya rike yana janta yana fadin ta kyaleshi tazo su tafi, mikewa tayi duk da kankantar haske haka ya rinjayeta ta dinga binshi tana waigen Hilal da ya sunkuyar da kanshi kasa sautin kukanshi ne kadai ke tashi a gurin....




A firgice ta tashi zufaa duk ta jikata,
janyo wayarta tayi da sauri ta kunnata,
bata bari ta gama settling ba ta latsa number Hilal,
lokacin karfe 1 a nigeria,
tasan dakyar yanzu in bai yi bacci ba,
saida ta kira sau uku bai daga ba,


kwanciya tayi taji duk babu dadi dan so takeyi taji ko lafiyarshi kalau,

yana idar da Sallah ya bi bayan kiran da tayi mishi,

hannu na rawa ta dauka tace
"ina wuni?

"Kwana dai Nadeeyah ya fadi murya a dashe,

"umm haka ne,
ba kayi bacci ba?
dama bacci ne ya daukeni kuma bani da charge shiyasa na kiraka saboda tunin sakon..

"yasani sarai ta gani,
danne zuciyarshi yayi yace "mantawa nayi kanwata kuma surukata,
bari in fada miki da baki amaryar Small uncle,
yadda ya fadi murya na rawa ya sanyata kashe wayar da sauri,
dana sani ta dinga yi dan yanzu ya tabbatar mata a kunnenta,
Allah ya sani bata kin Musaddiq amma koda wasa bazata taba iya aurenshi ba,
komawa tayi ta kwanta tunane tunane marasa dadi suka dinga zuwan mata har wani baccin ya dauketa....




A parlor ta zauna da asuba tana jiran ganin Daddy ya dawo daga Salla,
ga mamakinta tare suka shigo da Musaddiq,
dama ita ke tashinshi Sallar asuba to yau taki zuwa,
tasan Daddy ne ya tasheshi,


Har kasa ta tsuguna ta gaida Daddy,
amsawa yayi hade da cewa baki koma bacci ba,
"gyada kai tayi tace
"eh Daddy dama ina son in tambayeka ne,
cikin palon ya shiga ya zauna yace

"zo zauna inji,

kusa dashi taje ta durkusa tace
"Daddy mun gama jarabawa,
dan Allah ina son inje Gombe,
tare zamu tafi da Husna,


fadada Murmushinshi yayi yace "jiya muka gama magana da mamanku,
ku shirya jibi Malam Ali zai kaiku,

godiya sosai tayi mishi ta mike ta shiga kitchen,
shima sama ya wuce dan bacci zai koma saboda lahadi ce babu aiki..



Saida yaji Daddy ya rufe kofar dakinshi sannan yayi saurin zuwa kitchen din,
tsaye ya sameta a kofar shiga kitchen din tana jiran su shiga daki itama ta fito ta shige daki,



Tana ganinshi tayi saurin juyawa zata koma ciki,
shan gabanta yayi da sauri tsayinshi yayi mata rumfa babu abin da take gani a gabanta sai shi,
jan hijab dinta tayi ta rufe bakinta tace
"zanyi aiki ne,

"nima shi zanyi ya fadi yana kwaikwayonta..


Gefenshi tabi zata wuce taga yasa hannu ya tare gurin,
marairaicewa tayi tace "dan Allah ka matsa,
ko baka san Daddy ya karya da wuri?
nade hannuwanshi yayi yana murmushi yace
"sai kin yarda muyi tare,
gyada mishi kai tayi alamar amincewa,

yauwa ya fadi hade da jan hannun jallabiyar shi,
dankali ta debo ta dauko abin ferewa guda 2 ta mika mishi daya,

karba yayi yana dariya yace
"Allah sa dai kar in yanke,

"in ka yanke zaka hakura ai ta fadi itama tana dariyar,

"har so kikeyi in yanke ko?


"Kai ka fada nidai bance ba!


"Kin ce mana,
ya fadi a shagwabe kamar karamin yaro,

dariya tayi hade da tattara dankalin ta juya mishi baya ta cigaba da aikinta,

"An fada miki sakona??

Wani irin faduwar Gaba taji da ya jefo mata tambayar,
bata samu bakin amsashi ba ta cigaba da aikinta hannunta na rawa,

Gabanta ya dawo yasa hannu ya dago fuskarta,
da sauri ta runtse idonta tace

"wani sako?
In abinci ne kasan yanzu zan gama,


"uhm ga acici ko?
To wannan sakon yafi cikina muhimmaci,

Hilal bai fada miki komai ba?
Ya karashe tambayar cike da kasalar da soyayyarta ta sakar mishi,

turo baki tayi hade da ture hannunshi tace
"ni bai fada min komai ba,
hannu yasa a aljihu ya dauko waya ya fara latsata,
da sauri ta daura hannunta kan wayar tace

"Dan Allah yaya Musaddiq ka bar wannan maganar,

yin soyayya ni da kai ba abu bane mai yiwuwa,

"dalili??

Ya tambaya fuskarshi ta nuna alamun damuwa,
rasa abun ce mishi tayi kawai tace

"saboda inada wanda nake so, zoben dake makale a hannunta ta nuna mishi tace wannan zoben alkawari ne,
kuma kasan babu kyau karya alkawari,


Hannunta ya rike a hankali yana shafa zoben zuciyarshi kamar zata soye saboda azabar radadin da take yi,

iya karfinshi yasa ya fincike zoben a hannunta,
tana kallonshi ya sa hakori ya karyashi yayi wurgi dashi ta window,


kallonta yayi da wani irin yanayin da bata taba gani a tare dashi ba yace
"koma waye saidai yayi hakuri dan ba samunki zaiyi ba,
ke tawa ce ni kadai,
kin gane ko?


Kasa tayi da kanta hawaye ya fara zubo mata tace
"kayi hakuri, ina sonshi sos----

*Nadeeeyah....*
ya fadi da karfi rai a bace kamar namijin gaske,
sautin kukanta da yaji ne ya sa jikinshi mutuwa,
hannu na rawa ya dago fuskarta ya fara share mata hawayen,

"kiyi hakuri ki daina kuka,
bazan iya jin bakinki ya furta san wani bayan ni ba,
bazan jure ba,
rage murya yayi yace
"dan Allah ki soni ni kadai,

kamar dada ingizo kukanta yayi saboda bata son ya matsa su shiga cikin matsala tare,
ganin yayi mata tsawo sosai ya sanyashi rage tsawonshi daidai fuskarta,

"Nadeeyah----
"dan Allah kayi hakuri ta katseshi cikin kuka,

"wai dame zan hakura ne?
ya za'ayi in hakura da abun da nake so,
kin san bazai yiwuwu ba,
ya karashe yana daura hannunshi a saman idonta,

"ki daina min kuka, bana so,
in ba so kikeyi inyi ba nima,
kiyi hakuri kinji?
ki manta dashi ga dan uwanki,
kinsan nafi sonki,
kuma kema kina sona,
zaki fi kula dani,
abinci na, komai na,


"Ni bana sanka ta fadi tana goge fuska da hannunta,


saboda shaukin so dake dibarshi baisan sanda ya hada jikinshi da nata ba ya kankameta hade cewa

"zaki soni sosai,

Fiye ma da kanki Ma...

Fiye da komai a duniya...

lumshe idanuwanshi yayi ya cigaba da fadin

*I love yhu Nadeeyah, more than life it self......*



Innalillahi wa inna ilaihir rajiun.....
maimata Kalmar Mummy tayi sau uku tana tafa hannun cike da mamaki da takaici.......



Mrs Tijjani Shattimah......
[05/04 10:42 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣4⃣
By *Aysha Ya'u kurah*





Na shiga uku ni Zainab!
yau me zan gani a cikin gidana,

Da sauri Musaddiq ya mike har takalminshi daya na fita a kafarshi yace
"me kika gani Mummy?

"Ubanka na gani ta fadi a harzuke,
abin da kukeyi kenan Musaddiq?

yau ni na shiga uku na lalace,


Oooh wato shiyasa kullum kike hanyar dakinshi da nufin tashinshi a bacci,
ashe zuwa kikeyi ki koya mishi yadda mace da namiji suke jiyewa kansu dadi,
yanzu Nadeeyah har kinyi girman da zaki koyawa namiji yadda zai dinga yi miki kiji dadi,

*DANKARI!*

lallai wannan abun babba ne,


"Wai Mummy me ya faru ne? babu abin da mukayi fa,
kawai ina taya----

zan ci maka mutunci in ka sake yi min magana,
wallahi kana cewa takk zan kwada maka mari,
sakarai wanda bai san inda yake mishi ciwo ba,
maza ka biyoni....

kallon Nadeeyah dake tsaye tana share hawaye tayi tace

"To munafuka maza ki wuce daki ki jirayi hukuncin da zan miki, yar iska mara mutunci,


Rai a bace Musaddiq yace
"ki daina zaginta Mummy,
me tayi miki da zafi har haka kike kiranta da munanan kalamai,
haba....



"Bance karka sake samin baki ba, zo ka fita ka wuce sama gani nan zuwa,


Saida ya bari Nadeeyah ta fita sannan shima ya fita ya haye sama yana kunkuni dan shi samm baiga abin da sukayi ba.....






"Ashe yarannan Iskancinsu sukeyi,
wallahi da wani ne yazo ya bani labarin cewa yaga Musaddiq da mace a yadda na gansu wallahi bazan yarda ba,
dan rashin kunya a cikin gida,

ita kuma dan ta gama zama yar iska harda kankame wuyanshi....


*Zainab....*


Daddy ya daka mata tsawa da karfi dan yaga tana neman wuce gona da iri,

shuru tayi tana hucin bacin ran kalaman da ta jiyo danta da ta gama shirin kece raini dashi yana fadawa Nadeeyah,
Nadeeyar Adamu mai gadi!
da sauri ta runtse idonta dan wallahi tuno abun ma mugun taba zuciyarta yakeyi,


kallon Musaddiq Daddy yayi fuska babu alamun wasa yace

"ka fada min gaskiya,
menene tsakaninka da Nadeeyah?

Nasan ko kai zaka iya rungumar mace Nadeeyah bazata taba kusantar namiji ba saboda i have full faith in Suwaiba's upbringing,


Shin me mahaifiyarka ta gani wanda ya sanyata yin wannan tunanin,


kamar jira yakeyi mahaifinshi ya kai aya yace

"Daddy dan Allah ka aura min Nadeeyah,
wallahi ina santa sosai,



"Bakin cikin kiran Sunan Suwaiba da Daddy yayi da kuma na kalaman Musaddiq su suka hadu suka dugunzuma zuciyar Mummy ta sakar mishi wata irin kazamtaciyar ashariya,

kallo daya Daddy yayi mata tayi saurin dauke kai idanuwanta sunyi jaa saboda bacin rai,



Maida hankalinshi gurin danshi yayi Zuciyarshi fess saboda dama abin da yake ma danshi addu'a kenan,

"ka nemi soyayyarta? Daddy ya tambayeshi cikin sakin fuska,


"Eh Daddy, ita ma tana sona,



"Karya kakeyi wallahi,
inaji tana cewa bata sanka,


Yadda Mummy tayi maganar ya sanya Daddy dauke kai dan dariya ta kusa kufce mishi,
jiya bata barshi ya runtsa ba saboda labarin Faida yar gidan *Hon Danjuma Diriss*,
ta matukar cin burin bikin,

shi kuwa a gurinshi sam bayasan danshi yayi auren
*MATAUL HAYAT*,

irin su Nadeeya ya dade yana fata,
sai gashi Allah ya kawo mishi cikin sauki,
waya ya daga ya kira number Husnah yace suzo tare da Nadeeyah,



Mummy najin haka ta dauko wayarta ta tura text din gargadi zuwa ga Nadeeyah,


A lokacin da ta tura text din a lokacin Nadeeyah da Husnah sun kusa taka step din karshe.....




Cikin hikima Daddy yayi musu Nasiha ya nuna musu muhimmancin aure at early age,
sannan ya kalli Nadeeyah yace

"Nadeeyah kina da wanda kike so? Aure zan muku ke da Husnah...



A kunyace taja hijab dinta ta kasa hada ido dashi,

ya za'ayi ta iya furta bata san danshi na cikinshi,

Daddy,
Hilal,
Anty Reemah,
Musaddiq,
Anty Raly,
uwa uba Husnah da bata banbanta kanta da ita,
duk a cikin zuriar mutumin dake gabanta yana tambayarta ko tana san danshi,

ta ina zata iya butulce mishi,
a cikin jerin da ta lissafo babu wanda bai taka rawar gani cikin rayuwarta ba,

kuma Daddy ne ya samar dasu,
dago kai tayi suka hada ido da Mummy ta harareta hade girgiza mata kai,
dauke kanta tayi da sauri ta kalli Daddy dake sake jefo mata tambayar,
gyada kanta tayi a hankali alamar eh,

wanene shi?

Dan Musaddiq yazo min da zancenki,
in wani kike so shikenan sai sawun giwa ya taka na rakumi,


wani irin girma ya kara a idonta ta kasa bashi amsa,

"Ko Musaddiq din kike so?


Hannun Husnah ta rike sosai ta kasa dago ido ta kalleshi bare ta bashi amsa,

sau uku yana tambayarta tana yin shuru,

dariya yayi yace su tashi tafi,

Nadeeyah har tana tuntube da kofa tayi saurin fita,

Maida kallonshi gurin Musaddiq yayi yace

"To Malam ka shirya ma aure?

nawa ka tara daga albashinka,

nidai kasan ba ruwana nima da kaina na auri matata ya karashe cikin zolayar dukkansu biyun,


Ganin ya saki fuska yasa Mummy zama a kasan kafarshi,

"Dan Allah Daddy ka rufa min asiri,
bai kalleta ba yace

"Allah ne mai rufawa Zainabu,
me ya faru?

Hawayen bakin ciki ta fara yi tace "Yanzu kai farin cikinka ne danka guda daya tiloo ya kare anan,
tsakani da Allah duk yadda manyan abokanka ke miko ya'yansu mata gurinka domin shi, sai kuma suga ya kare a gurin yar Mai gadi,


yadda ta fadi abun ya soki Daddy Matuka,
nan da nan fuskarshi ta sauya yace

"akan Nadeeyah zan iya bata miki rai wallahi,
idan kika sake kiranta da yar mai gadi a matsayinta na jininki wallahi hukuncin da zan miki ba mai dadi bane,


cikin bacin rai ta mike tace

"ba jinina bace,

uwarta ce kadai jinina,

kai kasan asalinsu ne,

wa yasani ma ko ubanta barawo ne ya shigo cikinmu aka bashi aure,

wallahi bazan yarda in hada jini da marasa asali in samu bara gurbi cikin zuri'ata da zanyi tunkaho da ita ba,

"wallahi bazata sabu ba,
ai nima ina da hakki akan shi,
saboda haka wallahi indai ni na haifeshi bai isa ya auri Nadeeyah ba,


Sam Daddy bashi da saurin hannu amma tabbas a lokacin yayi niyyar dauke fuskar Mummy da mari,

a hankali yace
"ke kika haifeshi,
ke kuma nike iko dake,

wallahi tallahi in har kikayi abun da auren nan yaki yiwuwa sai kin bar min gidana,
kinga sai kowa ya nuna ikonshi,

Asali kuma Nadeeyah bata da wanda ya fini,
a yanzu na zama asalin Nadeeyah,

ni ne ubanta,
ni ne danginta da komai nata,

sai ki je maiduguri ki binciki Asalin Alh Garba kyari mai fata,


kallon Musaddiq yayi yace ka tashi kaje ka fara shiri daga bangarenka,
ni a bangarena bani da matsala...


jiki a sanyaye Musaddiq ya mike ya fita daga dakin,
bai taba tunanin zai samu wannan matsalar ba,
gashi kuma har ga Allah yana son Nadeeyah bazai iya rabuwa da ita ba,
ga kuma Mummy zata yi mishi karan tsaye cikin rayuwarshi,
tunane tunane ya dinga yi ya rasa mafita ya dauki wayarshi dan kiran Hilal,

a kashe wayar take dan haka ya kwanta yanata sakar da bata da karshe....





Mummy kuwa tana fita dakinta ta wuce cike da bakin ciki ta daga waya ta kira Radiya da Raudha da ta dawo gida weekend tace su kira Raliya suzo su sameta a gidan Goggo,

jin yadda muryarta ke rawa suka san ba lafiya ba,

ko wacce hankali tashe ta shirya tafiya gidan Goggo...




"Radiya ina zaki da sassafe?,

ko abun karyawa bakiyi ma su Umma ba kuma kinsan ba ita kadai bace,


shekeke ta kalleshi tace

"ni ma uwata ke nema na,
ko bani da ikon amsa kiran,

su tashi su daura da kansu tunda dai suna da hannu,

shikenan ni bani da sukuni saboda umma tazo,
a'a wallahi bazai yiwu ba,


Raees babban danta ne ya shigo yace
"Mama wai inji Umma tace ki kawo mata ruwan zafi zata sha magani,

wani dogon tsaki taja tace
"maza jeka gurin Gyatum kace ta kai mata,
hijab ta dauko tasa tana kunkunin da tun zuwansu gidan takeyinshi,


Mikewa mijinta yayi ya kira kanwarshi Haleesah yace "tazo tayi ma Su umma abinci,

sam baya jin dadin abin da Radiya kema yan uwanshi dashi kanshi,
hakuri kawai yakeyi saboda darajar mahaifinta,
yana shiga kitchen ya tarar da wata yar budurwa wacce shekarunta bai wuce sha tara ba. tana tsaye tana taya gyatum aiki,


Da sauri gyatum ta gaisheshi ya amsa yana kallon yarinyar,
itama tsugunawa tayi har kasa ta gaisheshi,

kamanninta da gyatum shi ya tabbatar mishi yarta ce,

saidai wannan din bak'inta mai kyau ne,
da dara daran ido farare tass ga kyawun diri,
har zai fita yace

"Gyatum wannan yarki ce?

Murmushi tayi tace "eh Alhj,
auta ta ce,
a gurin kanwata take a jos,
a can take karatu,
yanzu ma tazo hutu ne tazo tayani aiki,

gyada kanshi yayi yace

"Dan Allah ku taimakeni ku hada ma su Umma abun karyawa,
in san samu ne ma su samu tuwon laushi,
da sauri gyatum ta mike tace

"har sai ka roka,

Bar wanke wanken nan Fatima ki fara hada kayan karyawa,



Cike da jin dadi ya fita dan ko abincin baiyi dadi ba yasan zai fita kunyar mahaifiyarshi da kannenta...



Cikin kwarewa Fatima tayi miyar kukar da taji daddawa da dagargajajjen naman kaza, sannan ta tafasa kifi kadan ta sa citta da karumfani da tafarnuwa ta dakesu tsaf ta juye a cikin miyar,
nan gida ya kaure da kamshi, tana gamawa suka shirya komai cikin cooler gyatum ta dama musu kunun gyada ta fito da garin kosai ta kwaba tasa kwai da albasa ta soyashi gunin dadi,

manyan Coolers gyatum ta zuba abincin aka kai musu sannan ta zuba a kananan coolers ta ajiye wa mai

Please Login or Register in order to submit comment