Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

musaddiq yasan baida cikakken hankalin zaman duniya,,

Sam baisan inda yake mishi ciwo ba,
bai San darajar kudi ba saboda baya nemosu, kashesu kadai ya iya yi,
da yasan darajar kudi bazai daukesu ya kaisu muhallin suwaiba ba saboda bata da bukatarsu,
bata ma San me zatayi da su ba,

bai San su kudi ana kaisu inda in suka shiga zasu fito da mafiyinsu ba,
a'a kawai shi ga mai tausayin banza ya dauki zunzurutun kudi ya kaiwa suwaiba,
K'ara kaurara murya tayi tace "wallhy tun muna Shaida juna ka fita kaje ka karbo kudin nan, kafin wani azal ya afka musu,
ka bar mata dubu biyar din da na saba bata kuma ka tabbatar ka kaima kanwar Hajiya Nafeesa kana Jina ko,?
kasa dago kanshi  yayi saboda kwallar da ta taru a idonshi,

wani karamin tsaki Hilal yaja yayi waje cikin kunan rai,

Kiyi hakuri mummy, Anty Reemah ta fadi cikin taushin murya,

hakuri daya zanyi inji kudi na a hannuna,

Radiya da Raudha suka kalli musaddiq suka ja tsaki,
Radiya tace
''haba little dubu dari biyu fa,
kaima kasan kayi rashin hankali,
mutanen da duk iya rayuwarsu basu taba rike dubu goma ta kansu ba,

"Raudha miko min wayata maza in kira mama suwaiba dan Kar ma ganin kudin ya sa su kirkiri amfani da shi, dan su kudi kana ganin su amfaninsu ke zuwa ko ba budget,
gara ko man Mota mu Sha dasu Kinga sunyi mana amfani,

dauko wayar Raudha tayi ta fara latsawa,

''ba sai kin kira ba Raudha ga kudin nan nazo dasu ta fada cikin sanyinta had'e da karasa shigowa cikin parlon,

ajiye zainab tayi ta tsuguna har kasa ta gaida mummy,
ta ciro kudin cikin jaka ta mik'a mata tana murmurshi,

tun bayan tafiyar musaddiq ban yarda aiko shi kikayi ba,
nasa a raina ko mantuwa yayi shiyasa na biyo baya,
da na kiraki kika tabbatar min kin aikoshi sai na ajiye har Malam ya dawo shine yace in dai kawo in tambaya da kaina,
tunda na doso naji maganganu sai na tabbatar mantuwa yayi ya kawo,

nagode sosai Allah ya saka da alkhairi,
ameeeen!!!
mummy tace hade da karbar kudin,

Matsananciyar kunya ce ta lullube Reemah da Raliya,

Musaddiq kuwa daki ya wuce ba tare da ya dago kanshi ba hawaye sai ambaliya suke a idonshi ,,

dambun kifi mama suwaiba ta dauko a Jakarta ta ajiye a Kasa kusa da mummy tace ''gashi ba yawa da fatan kunyi sallah lafiya,
''kalau suwaiba,!

to alhamdulillah Allah ya Maimaita mana,

"ameen ya Allah" mummy ta fadi ta wuce daki rike da kudinta a hannu,

waigowa mama suwaiba tayi fuskar nan dauke da murmushi tace duk Ina kwananku,
da sauri anty reemah ta karasa gabanta tace Ina kwana mamma,
lafiya lau Ant--Dan Allah ki daina cemin anty mamma, Reemah ta katseta da sauri,
murmurshi tayi tace to na daina, yaushe kuka zo,?
hannun zainab ta kama tace "dazu muka zo ina su Nadiya da Hafiz,
Hafizu ya tafi gurin aiki Nadiya kuma tana gida,

yau bata zo mana yawon sallah ba, Raliya ta fadi tana karasowa gurinsu,

har mun shirya tace Wai kanta na ciwo shine nace tayi zamanta a gida,
nan suka shiga taba hirar yaushe gamo da anty Reemah da bakin ciki da kunya sukayi mata katutu a zuciya,
kallon fuskar mamma takeyi wacce kyawu da fara'a suke boye ainihin bacin ranta,

Mama suwaiba jarumar mace ce mai tsananin kawaici da boye bacin rai, kullum fuskar nan cikin murmurshi take......

Kad'an daga cikin abubuwan dake faruwa cikin zuri'ar mu kenan anty,
laifin duk na su Baffa ne, su suke nuna fifiko saboda abin duniya,
soyayyar abin duniya ta rufe musu ido sun mance taimakon Yan uwansu na jini sai dai bare na neman suna,,
har ga Allah nayi niyyar kaiwa Baffa kudin dan na je har gidanshi,
abin da naga sun ma Nadiya shi ya karya min zuciya har zuciyar ta rinjaye ni da aikata hakan,
bansan abin zai kwabe haka ba, da ban kai ba,
da na jira dawowar Daddy sai in karba in kai musu, yanzu nasan "ransu bazai musu dadi ba" ya karashe cikin shashshekar kuka,

share mishi hawaye tayi tace
"Ya Allah ka karfafa min raguwar zuciyar Diku nah,
har yanzu kana nan da halinka na kuka,
lokaci ya canza Little, yanzu ka fara girma u are not a child anymore,,
tashi kaje kayi wanka muje gida,
akwai wani surprise din da na shirya maka,
cikin sanyin jiki ya tashi ya shiga bayi,, 

Tagumi Reemah tayi tana tunanin hanyar da zata bi ta wanke zukatan bayin Allahn nan,
Allah ya sani bata da masaniyar halin kuncin da suke ciki, ita dai tasan suna da wadatar zucin da zaisa kullum ka gansu cikin farin ciki...

Mrs Tijjani Shattima....
[04/12 09:44] Meela Adeel: 6⃣
Ayi min Afuwa pls wasu hidimdimu ne suka rike ni, Ina Mai baku hakurin jiran da kukayi nagode matuka da kauna, Ina kaunarku har cikin raina Yan uwana... In shaa Allah zaku jini kullum yanzu

°ZUMUNCINMU A YAU °
By Aysha Ya'u Kurah

Ashe gaskiyar babanku ne da yace kila mantawa Musaddiq yayi,
hakan ce kuwa ta faru, dan kudin na Baffa ne,
tayi tayi ma in amsa nace mata a'a kudin sunyi yawa, mamma ce ke maganar cikin sakayawa tana kallon ya'yanta,

Nadiya dake kulla kankarar kuka, tace "nima dai mamma jiki na ya bani ba namu bane,
dan dai naga kin kirata ne shiyasa na dauka da gaske ne,
  Alwala Hafiz ya karashe hade da addu'a yace "mun gode Allah ma da yasa ba muyi amfani dasu ba, wannan din ma da ta bamu Allah yasa musu albarka,
"Ameen mamma tace hade da mikewa ta nufi cikin daki, babu wanda a cikin su ya karanci ainihin bacin ranta saboda fuskarta dake dauke da murmushi...

******
Hey handsome duk wannan cika da batsewar na menene?
Come on chill my guy,
yau fa is my day banason kowa yayi fushi a cikin ta,

Kara tamke fuska yayi hade da jan dan karamin tsaki ya mike yace
  "bansan me ke damun zuciyarka ba, bana cika mu'amula da masu irinta saboda wata rana haushin su zai sa inyi musu tsana marar misaltuwa,

u'r my uncle nd friend as well bana son abun da zaisa inji haushin ka,
nowadays masu irin zuciyarka basa samun nasara a komai saboda sanyinsu,

"sanyinka yasa kana namiji kai kadai a gidanku amma kowa ya rainaka harda BADAR for dat matter,
yaushe aka haife su?, dey are just 9! if am nt mistaken,
kuma ka tsaya a gabansu kana wani kuka,

gaskiya ka bata min rai, just go nd have fun Kar in bata maka naka ran, Hilal ya karashe fadi yana nuna mishi kofar fita da hannu,

"sannu ubanshi, Anty Reemah ta fadi tana karasa shigowa dakin,
Hilal ka fita idona walhy, bana son iskanci,
kasan inda zaka dinga nuna wannan bakar zuciyar taka,
kai a kullum duk inda kaje sai Kasa mutane sun tafi da kai a baki,
meye amfanin rashin hakuri, abin da hakuri bai baka ba wallahi rashin shi bazai taba baka ba,
duka nawa kake kaima da kake barin zuciya tafi karfinka,
wallahi kayi gaggawar sauke bakar zuciyarka har mu bar kasar nan in ba kanaso inyi mummunan saba maka ba, sakarai kawai,
"haba anty sorry mana,  ba fa wani abu yace min ba, musaddiq ya fadi cikin tausasawa hade da kama hannunta,

kallonshi tayi cike da son halinshi tace ko baice maka komai ba meye amfanin abun da yayi a gida,

"mum nifa babu abin da nayi, kawai dai gaskiya ce bakwa so, shiyasa Sam bana son shiga gidanku saboda ni ba na gani in kyale kuma in nayi kuce nayi rashin kunya, Allah ma yasan akan gaskiya na-- rufe min baki anty reemah ta fadi hade da bige bakin a hankali,

Janta musaddiq yayi suka bar dakin tanata masifar da Sam bata karbeta dan ba sabawa tayi ba,

kullum cikin bakin cikin halin danta takeyi wanda Sam bai biyo halinta dana ubanshi ba,
da ya tashi sai ya dauko halin mamanta har ya damata ya shanye saidai shi Sam bashi da neman suna kuma komai zaiyi sai yanada hujja...

Ruwa musaddiq ya bata tasha yace "kiyi hakuri anty kin so ki bata ranki ne,
kinsan halin Hilal, babu mai iya canza shi sai Allah,
kuma kin San duk abin da zaiyi akan gaskiya yakeyi he is open,
baya barin abu a ranshi,

dole ya koyi barin abu a ranshi musaddiq, Reema ta fadi tana mai ajiye kofin da ta sha ruwa,!

meye amfanin duk abun da akayi ma mutum yace sai ya rama,
wani lokacin ma ba dashi akeyi ba sai ya sako kanshi saboda shi baya gudun bakin duni--
kwanciyar da taji anyi a bayanta ne ya hanata karasawa,
kamshin turaren da taji ne ya sanar da ita ko waye,
Kara tamke fuskarta tayi hade da Jan tsaki,

cikin muryarshi ta yan gayun yaran hutu yace
"ki daina gudun bakin duniya Momma na,
in dai duniya muke son mu burge to lallai munada aiki babba a gaban mu,
"chapter closed",
am so sorry for hurting you mum,

wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta hade da kara kaunar dan nata,
duk iya inda yakai da zuciyarshi ya tsani bacin ranta,
baya daukar mintina sai yasan hanyar da yabi ya wanke zuciyarta,

dariyar farin ciki musaddiq yayi "yace komai ya wuce ''aunty momma!! ,
murmushi tayi hade jan kunnuwansu,
zama sukayi suka sata a tsakiya suna mata hira kamar babu wani abu na bacin rai daya gifta a tsakanin su,,

karar da wayarta tayi ne ya katse musu hirar,
zaro ido tayi ta mike tana fadin ya ilahi hade da daukar wayar, sorry Rally shaff na mance da ku,
daga dayan bangaren Rally tace ai na Lura da hakan, gashi har mun gama komai,
cikin farin ciki Anty reema tace kinyi komai simple dai ko, kinsan komai namu very simple muke yinshi,
saima kin gani anty, abin sai ya burge ki ta fadi tana gyara balloons din da sukayi kasa kasa, ok thank u babe,
gamu nan Zuwa,
juyowa tayi tace kuje ku shirya ku raka ni wani guri,
Hilal da ya riga ya harbo su yace ni a shirye nake mum,
bata kalleshi ba ta kamo hannun Musaddiq sukayi daki,
a cikin sababbin kayan da ta siyo mishi ta zaba mishi tace ya saka ta fita ta bashi guri,
saida ya dau minti goma yana shiryawa,
jar riga ya saka mai matukar kyau da deep blue wando, ya taje kwantaccen gashin shi, kyawun  bakar fatarshi mai sanyi ya kara bayyana, hatta madubin da ya kalla yasan babu karya shi din mai kyau ne matuka,,

fitowa yayi cikin takunshi na nima na fara girma,
kallon kauna anty reema ta bishi dashi tana fadin wowwww kanina,
babu kamarka a wannan zamanin,
gaskiya kayan nan sun karbe ka,
sajenshi ta shafa tace "Allah ya nuna min aurenka dole in zauna da matar saboda kar ta cutar min da kai,
Hilal ya ajiye cup din coffee yana dariya yace saboda kinsan uncle din nawa is nt brave ko,
zanci ub-- toshe mata baki yayi da sauri hade da rungumeta yana dariya harda kyakyatawa,
tureshi tayi tace "wallahi yaron nan ya rainani sosai,
zanyi maganin ka,
dariya suka saki Hilal ya dauko keyn mota Kan centre table yace oya mu wuce,
Anty reema ta kalleshi Sama da kasa tace da wannan wandon zaka fita,,,
pls mum karki fara muje kawai ya fadi yana wani narkewa,
hmmm kawai tace ta kama hannun musaddiq suka fita Zuwa gurin Mota.....

Mrs Tijjani Shattima.....!
[04/12 09:44] Meela Adeel: 7⃣
°ZUMUNCINMU A YAU °
By Aysha Ya'u Kurah

Mamma duba min kiga kwabin yayi haka,
mamma dake kashingide ta dan mike ta kalli kwanon madarar da Nadiya ta kwaba,
hannu tasa ta dan taba ta gutsuri kadan tasa a bakinta,
"mmmm gaskiya yayi dadi kuma yayi danko ta fadi tana lumshe ido alamar santi duk dan ta kara ma diyarta kwarin gwiwa,
murmushin Jindadi Nadiya tayi ta ajiye a kan tabarma ta shiga kitchen ta dauko leda da kwalbar da zata murza madarar,

Cikin nutsuwa take murzawa tana yanka su kanana tana sawa cikin wata tsaftatacciyar robar sweet da ta amso a shagon Tasi makocinsu,
hira sukeyi cikin jindadi mamma na taya ta kirga wadanda ta yanka, saida suka gama tsaf, Nadiya ta kalli mamma tace
"Mamma in rokeki wani abu,
mamma ta karashe rufe robar tuwon madara tace fadi kanki tsaye yar albarka,

Dan Allah Mamma kiyi hakuri ki daina yin "wankau" ban taba Jin zafin masu yi min gorin kina wankau ba sai yau da Nafi'un Baba Atika yayi min a shagon Tasi,
wai masu wanke daudar wasu bazasu taba yin arziki ba,
Dan Allah mamma ki daina, in shaa Allahu wannan karamar sana'ar da muka fara zata dinga rufa mana asiri da dan abun da baba da yaya hafiz zasu samo,
tunda ta fara maganar idon mamma ya ciko da kwalla,
kauda kanta tayi ta dan share da gefen zani tace
"Nadiya wanki baya kawo talauci duk canfin hausawa ne,

saidai zan daina saboda in karfafa gwiwar ki tunda hakan kika bukata,
sannan zamu hada da ruwan kankara saboda yayi karanci a unguwar nan,
wani farin ciki ne ya lullube Nadiya tace "alhamdulillah" nagode mamma,
bari inje in kaiwa Tasi dan yace ina gamawa in kawo mishi,
gyada kai mamma tayi tace "a kai da bismilla Allah yasa mishi albarka, Ameen Nadiya tace tana kiciniyar sa hijab dinta,
karo tayi da samari biyu suna kutso kansu gidan hade da sallama,

da sauri taja da baya ta kame jikin bango saboda irin kallon da Hilal yake yi mata,
tsaki yaja hade da kakkabe kayan jikinshi ya wuce,
kanta a kasa ta gaida musaddiq ta raba ta gefenshi ta wuce,
binta yayi da kallo zuciyarshi a karye,
Allah kadai yasan irin tausaya musun da yakeyi, yarinya karama tasan wahalhalun rayuwa,
muryar Anty Reemah ya jiyo tana tambayarta inda zata,
sunne kai tayi tace "zanje shago ne in kai tuwon Madara,
Hinad ta kalli hannunta tace "wow dan sammin, budewa ta fara kokarin yi Anty Reemah tace "kyaleta kinji na nawa ne duka,
cike da Jin kunya tace
"na dari takwas da hamsin ne, sai na dari ribar Mai shago,
Anty Reemah tayi murmushi tace duka dari tara da hamsin kenan ko,
girgiza kai Nadiya tayi tace ki bani dari takwas kawai, dubu daya ta zaro a Jakarta tace to gashi ki dauki dari takwas na tuwon Madara canjin ki siyo takalmi ki cire wannan hadi da Bautan kinji yar kasuwa,

rufe fuskarta tayi tana dariya tace nagode sosai Allah ya saka da alkhairi,
Ameen anty Reemah tace ta mikewa Hinad tuwon madarar suka karasa cikin gidan tare da Musaddiq,,

Hilal suka tarar a tsaye mamma na mishi hira yana fadin umm in na a'a ne yace um um,

mamma na ganin su ta karaso tana musu oyoyo,
a dadduma suka zauna ta kawo musu ruwa,
duk ta rasa inda zata sa ranta saboda dadin yau nata yazo inda take,
me za'a dafa muku tayi ta fada kamar zata fado kansu saboda murna,

Anty Reemah tace wallhy a koshe muke mamma daga gurin partyn Musaddiq muke nace bari mu biyo mu gaisheki mu kuma yi miki sallama dan inaga jibi zan koma,

Ayya mamma ta fadi tana Mai zaunawa kusa da ita, har zaki koma Antyn Yara,

Reemah tace eh zamu koma tare da musaddiq na sama mishi makaranta a can,,
Allah sarki musaddiq zaka bamu kewa ashe, to Allah yasa ka je ka fara a sa'a,
Ameen musaddiq yace yana Sosa keya,

da sauri ta dawo gidan da sabon silifas a kafarta da ledar madara da suga,
ajiyewa tayi a kofar kitchen tace sannunku,

mamma ta kalleta kallon tuhuma tace a Ina kika samo sabon takalmi? ,
canji ta ciro a cikin aljihunta ta mika ma mamma tace Anty ce ta siye duka ta kuma bani kudin takalmi,

shine dan sakarci baki shigo kin fada min ba mamma ta fadi rai a bace,

Anty Reemah tace "kiyi hakuri mamma ni nace tayi sauri ta siyo takalmi,

mamma tayi murmushi tace to mun gode fa Allah ya saka da alkhairi, Ameen anty Reemah tace tana kallon Nadiya da ke rabe tana wasa da hijabinta,

ni ko mamma wace makaranta Nadiya ke Zuwa?

  Mamma ta yi murmushi tace ta zana jarabawar aji shida zata cigaba da makarantar gaba in shaa Allah,

to ai mamma naga har an kusa gama third term wace makaranta kuke neman mata? ,

mamma ta kalli gefen da Nadiya take tace makarantar kwana ta Queen Amina dake kakuri,
to har yanzu bata samu bane? Reemah ta tambaya cike da damuwa,

muna ta kokarin har hada abin da zata tafi dashi ne mamma ta fadi cike da Jin kunya,

Anty Reemah tayi ajiyar zuciya tace mamma karatun diya mace nada matukar amfani,
Dan Allah Kar ayi wasa da ita first term din nan da za mu shiga,
ki bar batun queen Amina,
zan ma abban Hilal magana zai sa a bata admission a fgc malali in shaa Allah,
sannan ki turo min hafiz inason ganinshi gobe kafin muje gidan Baffa,

Kasa rufe baki mamma tayi saboda murna,
share hawayen farin ciki ta shiga yi tana kallon Nadiya dake ta dariya,
kai gaskiya nagode Antyn yara, Allah ya biyaki da aljanna, nagode sosai,

anty Reemah ta mike  tana fadin haba mamma me akayi ai duk daya ne,
Dan Allah ki daina min godiya,
Godiya ta zama dole Reemah mamma ta fadi tana rike baki, kedai kawai Allah shine zai saka miki,

Ameen anty Reemah tace ta fito da dubu biyar a jaka ta bawa Nadiya tace wannan na auta ne in ta tashi kice mata gashi inji ni kinji,
Nadiya ta karba ta shiga godiya hade da bayyana kyawawan hakoranta,

har gurin Mota suka raka su suna ta godiya kamar bakin su zai tsinke, musaddiq mamma ta kalla tace "me kake so in kawo maka ka tafi dashi? , murmushi yayi yace koma meye mamma nagode,
mamma tace to an gama dan albarka.. 

Hon Hilal yayi yace muje ko mum, bata bashi amsa ba sai ma harara da ta bishi dashi,

mamma tayi dariya tace Hilal Allah ya kiyaye hanya ka gaida abbanka kaji,
zaiji kawai Hilal yace ya tada motar sukayi gaba.....

Mrs Tijjani Shattima......
[04/12 09:45] Meela Adeel: 8⃣
°ZUMUNCINMU A YAU °
By Aysha Ya'u Kurah

Washe gari karfe 8 a gidan Anty Reemah tayi wa Hafiz,
a kitchen ya sameta tare da Yan aikinta suna ta aikin abun karyawa,
da fara'arta ta tarbeshi tasa ya wuce parlor,
sai da ta kammala komai tasa shi ya karya sannan ta dawo gurinshi,

Wace sana'a kakeyi? Tambayar da ta fara yi mishi kenan,
kanshi a kasa yace "dako nakeyi da wheelbarrow,
wheelbarrown naka ne? Ta sake jefo mishi tambaya,
a'a ya fadi yana mai girgiza kanshi, haya nake daukowa duk yini dari uku nake bashi,
Good anty Reemah tace tana gyara zamanta,
Hafiz ka saurare ni da kyau kanaji ko,
gyada kanshi yayi yace inajinki anty,

da farko dai zanso insan sana'ar da kake sha'awar yi, ka ture batun dako, dan banga amfanin sa ba,

sunne kai yayi yace walhy anty bani da wani idean sana'a yanzu sai dai in kika bani shawara bazanki dauka ba,
ajiyar zuciya tayi tace
"to akwai mijin kawata a railway station yana sana'ar fruits,
zan mishi magana in hadashi da kai sannan zan baka jarin da zaka tsaya da kafafunka ka rike mahaifanka da yan uwanka,
basu da kowa a duniya sai kai Hafiz,
hakkinka ne ka kula dasu da ilimin su,
nasan kana nema, rashin Jari ne ya taushe ka amma inada yakinin in na baka zaka kula da hakkinsu,
Dan Allah Hafiz karka bari suyi kuka da kai ko ba dade ko ba jima na rokeka da Wanda bama gani amma shi yana ganin mu,

mikewa daga zaunen da yake yayi ya durkusa yace wallhy zan rike amanar su in ban rike amanarsu ba tawa zan rike,
nagode sosai anty Allah ya saka da mafificin alkhairi, Ameen anty Reemah ta fadi ta dauki wayarta ta kira Hajiya Maryam,
sun dade suna magana sannan sukayi sallama, tace "gobe in shaa Allah zaka fara Zuwa ka koyi yanda sana'ar take,
zan turo maka kudin a account dinka, in baka dashi ka bude dan gara in baka su a hannunka,
Allah yasa ka fara a sa'a,

Ameen ya Allah nagode kwarai Allah ya kara daukaka,
Ameen ameen Hafiz ban kuma ce ka fadawa kowa ba,
ka rike shi sirri a tsakanin mu,

angama anty babu wanda zaiji in shaa Allah,

nan suka dan taba hira har kusan goma yayi mata sallama ya tafi cike da farin ciki....

Duk nuku nukunki sai kinje Nadiya,
Baffa mahaifina ne duk abin da yake min badan baya sona bane tunda shi ya kawoni duniya,
Nadiya da bata da mafita tace "zanje mamma rigar ce taki shigana,
zama ta shige ki ne matso in zage miki zip,
matsawa tayi badan ranta yaso ba mamma taja mata rigar ta shige tsaf kamar a jikinta aka dinka,

gashi ya shige maza daura dankwali muje,
dankwalin ta daura ta yafa gyale duk ranta a jagule,
ta tsani wulakancin su Badariyya, tasan Sam haduwarsu ba Mai dadi bace kullum suka hadu sai sun tozarta ta kuma babu Mai hanasu,
daukar zainab tayi ta bi bayan mamma suka fita hade da rufe gidan...

Gidan cike yake da 'yayan kawayen mummy da iyayensu da ita kanta,
suna can ciki anata wasa da ciye ciye,
iyayen kuma suna hira hade da Shewa,
can gefe kuwa su Reemah ne ita kannenta sunata hira babu Wanda ya lura da zuwansu,

hakan ya ba Nadiya daman zama can nesa dasu tana kallon yaran dake dakin 'ya'yan hutu kawayen su badariyya,

zainab da hankalinta ya gama tashi da tulin kayan wasan yara sa'aninta ta mike a jikin Nadiya tace anty zanyi wasa,

Nadiya ta zaunar da ita tace ki bari su gama kema sai kiyi kinji,

gyada kanta tayi tanata binsu da ido suna wasa babu kakkautawa,

Mamma kuwa tana can gurin su goggo da mummy da kawayenta sunata hira, tunda ta gaishesu ta nemi guri ta zauna a kasa itama, babu Wanda yace musu ga abinci haka in za'a ba yara barka da sallah babu wanda ke kallonsu,
sallah kadai ke tada iyayen Sannan su dawo su cigaba da hira,

"Suwaiba tashi ki tattara gidan nan tunda baki San abinda ya kamata ba sai an fada,
muryar goggo ta dakin kunnen daukacin mutanen dake cikin parlorn,

da sauri mamma ta mike tana murmushi ta fara tattare kwanukan da suka ci abinci,
kwala Kiran Nadiya tayi tace taho ki fitar min da kwanukan nan,

zaunar da zainab tayi ta mike sum sum ta karbi kwanukan hannun mamma tayi waje dasu,

Badariyya dake kwance tana game a iPad dinta ta bita da ido cike da rainin wayau,
tsaki taja ta cigaba da danna iPad dinta,
ta rasa dalilin dayasa ta tsani Nadiya,
bata jin ko digon kwayar Santa a cikin zuciyarta,
tasan tafi Nadiya dukkan gatan rayuwa, haka kyau karyarta ta nuna mata, can kasan zuciyarta ta jiyo yayi amsar kuwwar "KYAWUN JIKIN FA" tsaki taja tace saidai jikin Shima dan bamu gama girma bane amma Nadiya babu abin da ta fini dashi,

Husna da Laila yar kawar mummy suka bita da kallon mamaki sukace to waye ya ce Nadiya tafi ki wani abu,
gimtse fuska tayi hade da runtsa ido dan bata San maganar zuci ta fito fili ba,

A ranar babu wani abu da ya shiga tsakaninta da badariyya saboda Hilal da yayi kaka gida a parlorn, Kasa katabus tayi saboda tsoron Kar ya sake marin kyakykyawar fuskarta,
ta tsani abin da zai taba fatarta koda kuwa kuda ne,,

Yaji mamma tayi ma Reemah da yawa na tafiya sannan tayi ma musaddiq dambun kifi da nama,

murna sosai sukayi sunata godiya,

sai bayan Isha mamma ta fara shirin tafiya,
dakin Baffa ta shiga Wanda yake cike da 'ya'yan mummy da ita kanta suna meeting ana ciye ciye,
durkusawa tayi tace Baffa mu zamu tafi sai da safe, to madalla sai da safe suwaiba,
yaki taho zainabu ki karbi kudin mota,
nokewa zainab tayi saboda rashin Sabo,
mamma tayi murmushi tace "quiwa gareta, ,
toooo... to ta rike kanta ta cinye, sai Allah ya tashe mu ki gaida Adamun,
to zaiji Baffa,
ta waiga tace masu sai da safenku,
to sai da safe duk sukace suna masu kai nama bakinsu..

Reemah dai kai kawai take girgizawa cike da takaici,

yafito Hilal tayi da hannu tace maza yaje ya sauke su a gida,

kunkuni ya fara yi yana buga kafa,
musaddiq ya mike yace bani mukullin,
da sauri ya wurga masa ya koma ya zauna ya cigaba da latsa wayarshi, a can bakin gate ya tarar dasu suna kokarin fita,
Mota ya bude yayi musu hon yaja ya isa gaban su,
bude musu yayi

Please Login or Register in order to submit comment