Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan a dining,


saboda farin cikin ganin tuwon malmala biyu Umma ta cinye,

cike da jin dadi Haleesa ta kalleta tace
"yau Umma taci abinda take so, san samu kullum da safe da dare a dunga miki tuwo,
to hakan bazai yiwu ba,
hidimar Maman Raees tafi karfinta,
harara Indo kanwar Umma ta jefawa Haleesa tace
"yau da tayi kasheta aikin yayi,


Dariya Haleesa tayi tace
"waya fada miki ita tayi,
ita bata gidan ma,
mai aikin gidan ce tayi,

a daidai lokacin fatima ta shigo kwashe kayan abincin,
albarka suka shiga sa mata har ta gama ta fita,

umma dai da ido ta bita,
a kullum tana ma danta adduar samun mace ta gari ba mai kyale kyale irin Radiya ba,

yanzu din ma bazata fasa ba,

ganin da tayi wa Fatima na farko taji ta shiga ranta,
saidai bazata tilasta shi ya nemeta ba,
za dai ta cigaba da addua,
dan tabbas danta bashi da mace a gidanshi......





*Wai ina Hajiya Goggo Ma'u ne*




Bangaren Goggo kuwa tunda Anni ta tare kullum cikin kunan zuci take,
tayi asirin,
tayi tsafin duk a banza saboda yin auren Baffa ma kadai karyewar alkadari ne,

ga yawan abinci sadaka da Anni keyi kusan kullum domin nema musu tsira ranar Gobe kiyama,


Tunda Goggo taga asirin nata yaki aiki saidai suyi ta cin kudinta sai ta hakura ta fara kunno wutar tashin hankali da masifa a gidan,

idan Allah yasa ranar a dakin Anni Baffa zai kwana tofa babu bacci,
dan ta dinga dukan kofar da muciya kenan,
abun ba karamin damun Baffa yakeyi ba,
Anni ke hanashi magana ta nusar dashi yanzu tsufa yazo,
ba lokacin sa'insa bane,
lokacin da zamu koma ga Allah ne,
haka zasu mike suyi ta Sallah har ta gaji ta koma daki tana zage zage kamar wata yarinya,




Yau ma kamar Kullum Anni na tsakar gida ita da mai aikinta suna girkin sadaka ,

Shinkafa ce da wake sai lettuce da su tumatur,
suna gamawa aka fara zubashi a farantai ana fita dasu waje almajirai na rige rigen karba,

makota masu karamin karfi suma suka shigo da robobinsu aka zuba musu,
sunyi nisa sosai gurin rabo Goggo ta fito da bokitin fenti karami, fitsari ne a ciki ya kai rabi,
nan ta doshi katuwar tukunyar ta antaya fitsarin a ciki,


Da kyar Anni ta iya danne bacin ranta dan ta harzuka matuka,
rufe tukunyar tayi tace

"Harira, ki kira almajirai su kwashe abincin nan su kai ma dabbobi yau ranar tasu ce,

tana kaiwa nan tayi hanyar dakinta,

gabanta Goggo tasha ta dinga dura mata zagi,
ita dai Anni dariya kawai takeyi tana fadin nagode,

"ni yanzu ai bana fada,
fada na yara ne da kuma wanda bai samu abinda yake so ba,
ni kuwa me zance ma Allah,
ai sai godiya, in nayi fada ai na butulce mishi,

inaaa ni ba butulu bace,

Allah ya gamai min komai,


Hannu Goggo ta daga yana rawa zata kwadama Anni,
da sauri Baffa ya rike hannun ya maida nashi kan fuskarta,



Rike hannunshi Anni tayi tace "Haba dan Allah,
ba girmanka bane,
yanzu kaga ni bata mareni ba,
ka mareta,
da ka kyaleta wallahi bazai min tabo ba,

Dan Allah mijina kar ka sake daga hannu a kan mace koda kuwa yarinya ce,
kasan daraja garemu,

sake matse hannun tayi tace muje kaci abinci ka fita nemo mana halal,



Duk abin nan da akeyi akan idon Mummy da su Radiya ake yinshi,
nan ran Mummy ya kara baci,
a harzuke ta iso kusa da Baffa tace
"Baffa duka?

Dukan mahaifiyata Baffa,
dama irin ukubar da take ciki kenan,

habawa kamar an bude famfo Goggo ta fara kuka mai sauti,

riketa Radiya tayi tana harara Baffa da Anni,

Murmushi Anni tayi tace


"cikin jin dadi take wannan ma tsauts-----

rufe min baki,
Mummy ta katseta cikin tsawa,

"wacece ke da zaki samin baki a cikin magana ta,
da wanda ya haifeni nake ba da ke ba,


ki tsaya a matsayinki kin gane ko?


Murmushin dake kan fuskarta bai gushe ba ta sake damke hannun Baffa dan taga yana yunkurin kwacewa yayi wata aika aikar tace

"muje mijina,
kar yunwa tayi maka lahani,

Bayanta yabi suka bar su da sakkaken baki,

Goggo kuwa kuka takeyi bilhakki da gaskiya wanda ya zame mata dan kullum,
wannan kukan da Baffa ke sata tasan bashi ne,
duk ranar da ya dawo hannunta sai ya kwashi kashinshi a hannu, dan walhi bazata barshi ba,
bari dai asirin da Anni tayi mishi ya sakeshi, ita kuma ta daura nata,

"a tunaninta asiri Anni tayi mishi dan yadda ya zama sauna akanta tasan ba lafiya ba,
bata san kyautatawa da kissa yafi asiri tasiri a gurin namiji ba...





Wata ashar Raudha da Radiya suka saki da Mummy ta labarta musu shirin da Daddy yayi na auren Musaddiq,


Raudha ta daga murya tace

"Wallahi bazai yiwu ba,

wannan uwar daular da Musaddiq ya shiga ni kadai na santa,
sannan yadda muka ci burin aura mishi Faida mahaifinta yasa a kara mishi girma nan take shine Daddy yake mana bakin ciki,

wallahi bazata taba sabuwa ba,

wallahi da ya auri Nadeeyah gara ya mutu ba Aure,
haka nan ga inda ake harkar arziki mu kare a dangin tsiya, dangin marasa asali,

wallahi da kaina zanyi maganin abun,

karma kisa kanki Mummy,

ki bani kwana Hudu zakiji labarin ya wargaje,

badai ni ke zaune dashi a lagos din ba,
zanyi brain washing dinshi,

ki barni dashi kawai,
ki nunawa Daddy kin amince sai mu cigaba da shirya musu kulli ta bayan kasa...





Assalamu Alaikum,

Anni ta fadi hade da shigowa dakin ta ajiye musu cooler,

"ga abin kari da fatan ban shiga cikin maganarku ba,

tsaki Mummy taja ta juya baya dan bata kaunar ganin fuskar Anni,
dariya tayi tace "na barku lafiya,


A kofar fita ne tayi karo da Raliya,
da sauri Anty Raly taja baya ta tsuguna ta gaida ta,

mika hannu Anni tayi ta karbi Fadeel tace


"Maigidan da babu cefane,
muje daki na baka abincin tunda dai ni baka bani ba,

dariya kawai Anty Raly tayi tace "Baffa na ciki,

"yana wanka Anni ta bata amsa cike da kulawa,


Daki ta wuce da Fadeel tana tunanin kalaman Rauda,
ta rasa irin wannan kiyayyar da ake ma Suwaiba da 'yayanta, amma in shaa Allahu zata nuna musu itama tanada rawar takawa cikin rayuwar su Nadeeyah...


waya ta dauka ta kira Papy tace "duk abin da yakeyi ya barshi yazo yau,
da yake bashi da wani aiki ran monday sosai sai ya fara shirin tahowa.....




Ita kuwa Raliya hankalinta ba karamin tashi yayi ba dan bata san ko kadan Nadeeyah ta kasance cikin danginsu,
tasan zata sha wahala matuka,
ta riga ta gama auno mata zamanta gurin Taheer wanda take da tabbacin zata ji dadi a gurinshi,
a take ta kalli Mummy tace "gaskiya Mummy zanje in samu Daddy,
dan Nadeeyah na bukatar wasu familyn bamu ba,
nasan in ta auri little, ba karamin wahala zata sha ba,

nan take Mummy ta gimtse farin cikinta dan duk tunaninta Raliya ta dawo hanya ne,
ashe ita wani tunanin takeyi daban,
nan suka shiga zaginta sosai har ta hassala ta tashi ta fita ta wuce gidan su.....





Tana shiga gidan ta wuce dakin Musaddiq,
a tsaye ta sameshi yana taje gashin kanshi yana yar waka,


Ajiye Fadeel tayi a kasa tace
"Zo ka zauna Diku ina son magana dakai,
ajiye brush din hannunshi yayi ya dawo kusa da ita ya dauki fadeel suka zauna tare,


kallonshi tayi sosai tace

"baka isa aure ba kanina,
in kana so ma zan iya tsuguna maka,

Dan Allah ka hakura da Nadeeyah,
she deserve better life,

kasan halin da zaka sata in ka aureta mahaifiyarka bata so,

ka hakura da ita,
in har kana santa zaka so ganin ta cikin farin ciki,

Dan Allah Diku kayi hakuri,
ka barta tayi aure cikin wani familyn ba namu ba,

kaga akwai wani makocinmu Taheer,
inaga ma zaka ganeshi,
wanda yazo nan suka samu matsala da Hilal,
wallahi yana mutuwar kaunarta,
kuma inada assurance akanshi, dan na dade da sanin shi da mahaifiyarshi,
mu hadu ni da kai mu samar mata farin ciki mai daurewa kaji kanina...


"Ajiye Fadeel yayi ya kamo hannunta yace

"Anty Raly bakya sona ko?
Kin fi son bare a kaina,

yanzu har in furta ina son Nadeeyah kuce in hakura,
ke da nayi tunanin zaki mara min baya ki taimakeni in samu abin da nake so,
sai gashi kece kike iya cewa ni bazan bata farin ciki ba,

kin fi son wani ya sameta bani ba ko?

wallahi ban taba tunanin matar da zan aura zata shiga cikin bakin ciki ta sanadiya ta ba ko ta yan uwana,
bare Nadeeyah da ta kasance jinina,


wallahi alkawari ne bazan taba bari Nadeeyah ta wulakanta ba,

Dan Allah ki goyamin baya plsss,


"share kwallar idonta tayi dan ita tana hango mishi abinda bai hango ba,
tasan in ya auri Nadeeyah ya gayyatar wa kanshi da Nadeeyah rashin kwanciyar hankali kenan har su koma ga mahaliccinsu,
ita kuma Sam bata san duk su biyun su kasance cikin kunci,



A hankali tace "To Little,
in Nadeeyah mafi alkhairi ce a gareka Allah ya baka ita,
Allah ya baka juriya da jajircewa,


Hannun Fadeel ta kama hade mikewa tace
"Bari in tafi gida, Babanshi na hanya,

mikewa shima yayi ya bi bayanta har suka isa parlon,


Dakin su Husnah ta shiga dan yin magana da Nadeeyah,

bai bita ciki ba ya nemi guri ya zauna a parlon yana nazarin maganganunta.......




Mrs Tijjani Shattimah.......
[06/04 9:42 AM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣5⃣
By *Aysha Ya'u kurah*




*Matar Mutum kabarinsa*




Kwance ta samesu a kasa su biyun Husnah na rarrashin Nadeeyah da har lokacin idonta bai bar zubar hawaye ba,


kan Nadeeyah Fadeel ya fada yana tsallen murnan ganinta,


cikin kukan ta fara mishi wasa tana dariya mai kama da yake,


Tausayi sosai ta bawa Anty Raly,
gefen gado ta zauna inda Badar ke bacci ba ta san wainar da ake toyawa ba,

kallon Nadeeyah tayi tace "Ashe haka kuma abu ya faru,
to Allah ya sanya alkhairi,

kanina ya kasa Taheer,

ko da yake so so ne,
amma son kai yafi,
ga Musaddiq dole Taheer ya hakura,

Tashi muje ku rakani gida ku tayani aiki sai mu fara tsara yadda zamu shirya bikin,


Mikewa Nadeeyah tayi da sauri dan sam bata san abun da zai zaunar da ita a gidan yau har su hadu da Mummy,
muje Anty,

kinyi wanka ne? Anty Raly ta tambaya tana kallonta..


"In naje can zanyi, bari in dauki kaya,
to kuyi sauri ina jiranku,

ko minti biyu basuyi ba suka fito da maka makan hijabansu har kasa kamar wadanda akayi ma mutuwa,


kallo Musaddiq ya bi ta dashi yana ta kokarin hada ido da kumburarrun idanuwanta taki yarda dan kanta a sunkuye yake,


Mikewa yayi ya sa hannu zai karbi fadeel,
noke wuya yayi ya kwanta a kafadun Nadeeyah,


"iyye to sauka zakayi yaro kar sa min ita ciwo,
maza sauko,



"kaga kyale min yaro ya rungumi abar kaunarshi kafin ka dauke mishi ita ka kai can wata uwa duniya,
gara yaji duminta da kyau,
dariya sosai Musaddiq yayi yaje saitin kunnen Husnah yace

"Amaryar tawa tayi miki,

murmushi tayi ta janyo kunnenshi tace
"sosai ma,
amma ina jin tsoro,

girgiza kai yayi yace

"karki ji tsoro,
babu abin zai faru,


"i pray soo ta fadi tana rugawa da gudu dan ta isko su,

shima saurin yayi ya fito,
lokacin har sun shiga mota,


Gefen da take zaune ya zagaya ya kira sunanta cikin wani irin siga,

kife kanta tayi a bayan Fadeel saboda kunyar Anty Raly da taji,

murmushi yayi ya sunkuyo daidai kunnenta a shagwabe yace

"Zaki fita bance I love yhu ba,

u knw dat i love yhu ko?
"take care of urself for mee alone,

tada motar Anty Raly tayi tace "mijina zai dawo karka sa in makara,

hannu ya daga musu yace "zanzo in dauke su anjima,

Husna ki kular min da ita,

*I LOVE YOU*

ya fadi da karfi yana dariya dan yasan ya hana mata sukuni......






Ta window Badar ta leko dan ganin wacce Musaddiq dinta ke cewa i love u,
babu kowa a gurin sai Musaddiq dake tsaye cikin Nishadi,
sai kuma gate da taga an rufe...

nan ta shiga tunanin su waye suka fita daga gidan kuma wacece yake cewa I love you cike da annashuwa,


Bayi ta shiga tayi brush ta fito parlon ko zata ganshi,
tana fitowa taji tashin motarshi,


wani irin zazzafan kishi taji ya taso ya tokareta,
da kyar ta samu nutsuwa ta dan tsakuri abin kari kadan......







Karfe biyar da yan mintina Papy da Hafeez suka iso gidan Baffa,



Saida suka ci abinci suka huta sosai sannan Anni ta koro mishi dalilin da yasa tayi kiranshi,


"Nasan zakayi mamakin dalilin da yasa nace kazo,
to dalilin mai karfi ne,
nan ta labarta mishi abun da taji daga bakin su Mummy da Rauda sannan ta daura da cewa,
a yau ba gobe ba ina son kaje gidan Alhj Muntari domin maganar auren Musaddiq da Nadeeyah,

Alh Muntari ya cancanci ayi mishi fiye da haka domin ďan halas ne,
mutumin kirki ne,
zuciyarshi kamar auduga haka take,

tunda har ya nuna ya son abun nan,
dan Allah mu nuna mishi mun fishi so saboda mu saka alkhairi da mafificin alkhairi,


Cike da jin dadi papy ya gamsu da maganar Anni kuma yayi alkawarin a yau zaije ya sameshi su tsaida maganar auren,
bazai jinkirta ba dan kar shaidan yasa shi jin kunya.....







Tare sukayi Sallar Isha'i a masallacin kofar gidan Daddy,

Cike da murnar sake ganin shi Daddy yaja shi zuwa cikin gidan dan suyi dinner tare...



Suna gama cin abinci suka hau hira Daddy yace

"Yata tana shirin zuwa sai gaka kazo,

dariya Papy yayi yace

"Nima zuwan ďana nayi,
neman auren yarka nazo yi,

Allah yasa ba'a riga mu ba?


Dariyar rashin fahimta Daddy yayi yace wacce yar a ciki??

Nadeeyarka nazo nemawa ďana Musaddiq,


Ajiyar Zuciya Daddy yayi dan gaba daya tunaninshi ya tafi can gurin ďan Papy Jamal,


fadada Murmushinshi yayi yace wannan dan naka sai a hankali,
gaskiya kace ya nemi wata,
ni 'yata sai Governor,


Wata irin dariyar manya Papy yayi yace
"kasan in da rabo shima zai taka wannan matsayin,
mun kawo kokon baranmu,
Allah yasa a cika mana shi,


Duk wanda yaga fuskar Daddy a lokacin yasan yana cikin farin ciki matuka,

"Na baka ita Alhj Abdallah, au Proff Saifullah,

Nadeeyah ta Musaddiq ce,
in shaa Allah,
yanzu sadaki kawai zan yanke muku ku kawo,
sai a sa ranar daurin aure,
kunsan yar tawa mai tsada ce,
ku kawo miliyan goma,


Mikewa Papy yayi yana dariya yace
"zamu kawo fiye da haka,
mun gode kwarai Allah yasa ayi auren nan a sa'a,


Ameeen ya Allah... Daddy ya fadi hade da mikewa,

rakiya yayi mishi suna hira har suka karaso gurin motar,



Motar Musaddiq ce ta kunno kai cikin gidan,
yana yin parking suka fito suka karaso gurin su Daddy,
cike da girmamawa Musaddiq ya gaida Papy,
dagoshi yayi ya amsa hade da cewa
"kana lafiya Ango,
sunkui da kai Musaddiq yayi yana sosa keya,
dariya Papy yayi yace

"Allah ya tabbatar mana da alkhairi,


Ameen Papy...
Musaddiq yace ya ja baya ya tsaya,


kallon Nadeeyah da Husna Papy yayi yace
"baku tambayi mutuniyar taku ba,
da sauri Husnah tace

"Ay gobe zamu je Gombe in shaa Allah,

"aaa to masha Allah sai ku shirya goben sai mu tafi tare karfe sha biyu,
da Murnarsu suka amsa da

"To zamu shirya da wuri,


Gurin Hafeez suka zaga suka cikashi da Hira,
saida suka fi 30mints a gurin sannan duk suka shiga cikin motar,



Hafeez na kokarin tada motar Husnah tayi saurin dakatar dashi,
number wayarshi ta bukata nan take ya karanto mata sannan yayi musu sallama suka wuce.......




Tashin Husna Nadeeya ta dinga yi akan taje ta tada Musaddiq kar ya makara dan jirgin 6 zaibi zuwa lagos,


mikewa tayi tana turo baki tace "kije ki tasheshi mana,
ni bazan iya ba,
hakuri ta shiga bata har ta samu ta yarda ta wuce dakinshi,


kamshin turarenshi da taji ne ya bata tabbacin ya tashi,
a tsaye ta sameshi yana gyara links din hannun rigarshi,


"ashe ka tashi?,
alhamdulillah na huta,


dariya yayi yace aikin Mummy ne,
tun dazu ta tasheni,
ina matata?

Hamma Husnah tayi tace "tana daki ita ta matsa min inzo in tasheka karka makara,
sosai yaji dadi har cikin ranshi yace
"muje in ganta kafin in wuce,


A kofar shigowa suka kusa karo da Mummy rike da plate din indomie da kwai,

Cup din hot choco kadai ya karba ya yi hanyar dakin su Nadeeyah,

"Ina zaka je?
Mummy ta fadi tana bin bayanshi,

"amm zan je.... zan ----
dawo nan ka zauna kaci abinci,

ko jirgin na ubanka ne in lokaci yayi bazasu jiraka ba,


"Mummy,
Nadeeyah bata da lafiya ne zai duba ta....

wani mugun kallo tabi Husnah dashi wanda yasa ta saurin murda kofa,

"zo nan sakarya wacce bata san ciwon kanta ba,

sum sum Husnah ta dawo inda Mummy take,
kunnenta ta kama tace

"wallahi kinji na rantse,
wannan rawar kafar da kikeyi akan Nadeeyah in baki daina ba sai na ci miki mutunci,
kuma in sake jin maganar tafiya Gombe a bakinki sai na tattaka ki, marar mutunci kawai..
ta karashe hade da dungure mata kai,


kafa Husnah ta fara bugawa a kasa tana fadin

"ni wallahi sai naje,
hanyar dakin Daddy tayi Mummy tayi saurin tareta dan karansu na daren jiya baiyi mata dadi ba,
yanzu in ta bari Husnah ta kai kararta tofah tasan bazai mata da kyau ba,


"Ina matsayin mahaifiyarki kike kokarin bijire min har kike yunkurin kaini kara,

ni zakuyi ma tawaye?

Babu komai kuyi abin da kuka ga dama ta karashe tana matso kwalla,


kewayeta sukayi suka shiga rarrashinta,
dakyar ta hakura ta tasa keyar Musaddiq har mota sannan ne ta samu kwanciyar hankali.....




Dubu dari biyu Papy ya bada kudin sadakin Nadeeyah,
sai dubu dari na gaisuwa...

cike da farin ciki Daddy da abokinshi Alh Abubakar suka karbi kudin,
nan Daddy yasa biki wata biyu dan yana so ya samar musu gida a can lagos dan suyi nesa da duk wani tashin hankalin gida.....


*(Shaff ya manta Raudha na lagos kuma duk tafi kowa matsala cikin 'yayan nashi,)...*




*******

Woww mashaa Allah my little brother ya girma,
yaushe aka sa bikin Daddy?

"June amma bamu cire date ba,

Maganar shirye shirye na kira inyi miki,
inaga zan turo miki kudi ku shiga Dubai kuyi mishi siyayya,
sannan zan bawa su Raliya su siyo wasu anan dan mahaifiyarku tace babu hannunta,

dariya Anty Reemah tayi tace
"ko sisinka karka kashe Daddy,
zamu hadu mu hada mishi lefe na gani na fada,


"wallhy naji dadin wannan hadin dan dama bana son Nadeeyah ta kufce mana,
kullum cikin tunaninta nake..




"Ajiye kofin zobon dake hannunshi yayi ya dafe kanshi da ke sara mishi,

"shikenan ya rasa Nadeeyah, tunda har akasa ranar auren ya fidda ranshi da tunanin ko Allah zai taimakeshi ta zamo tashi,

maida kwallar da ke kokarin fito mishi yayi da sauri yace

"wish u all the best Nadeeyah,
Allah ya dawwamar dake cikin farin ciki...


yasan Musaddiq na can yana nemanshi,
haka itama Nadeeyar,
bashi da karfin kunna waya yayi magana da ko daya daga cikinsu,
dan raunin da yake ciki bazai barshi ya danne zuciyarshi ba,
dole ya koka musu har su gane yana cikin damuwa,



Yana cikin wannan tunanin yaji Anty Reemah ta dafashi tace
"shine baka fadamin wannan abun dadin ba,
yanzu sai mu fara shiri daga bangarenmu,
dan bazan bar kowa yayi mishi kayan lefe ba,
kai kuma sai ka shir----

Mum kinsan ina Msc,
kuma mun kusa fara exams, dakyar zan samu zuwa,

"cike da Mamaki tace

"Hilal...

Musaddiq ne fa,

kada kanshi yayi cike da damuwa yace
"Mum bance bazani ba,
amma for nw banda karfin shirye shirye,
plsss ku barni inyi karatu...


Mikewa tayi cike da tausayin danta tace
"take ur time dear,
Allah ya bada sa'a...
tana kaiwa nan ta wuce kitchen ranta duk a dagule.....





Gaba daya Nadeeyah ta mance damuwarta tunda tazo garin gombe, gidan karamci,

wani irin ji dasu Mami takeyi kamar ita ta tsuguna ta haifesu,


Yawo kuwa babu gurin da basu je ba a cikin Gombe,
ga wani shiri na musamman da Mami tasa akewa Nadeeyah wanda ya kara fitar da kyawunta ta ciko tayi bulbul,

fatar jikinta sai sheki takeyi ga santsi kamar tarwada...



Husnah da Hafeez kuwa wata shakuwa mai kama da soyayya ce ta musamman ta shiga tsakaninsu,
tun Hafeez na dari dari har ya saki jikinshi sosai da ita,
raba dare sukeyi suna tsaftattaciyar hirarsu mai ban sha'awa,
da Papy ya lura da hakan ya kirasu duk su biyun ya tambayesu,


Husna ce ta fara amsawa da tana sonshi,
sannan ne Hafeez ya samu karfin gwiwar bada tashi amsar,

farin ciki marar misaltuwa Papy ya shiga..

sallamarsu yayi hade da kiran Daddy ya labarta mishi,

Daddy cike da jindadi yace to ai bazamu jira ba,
gara a hade bikin ayi shi rana daya,
nan suka gama tsara yadda zasuyi sannan sukayi sallama cike da jindadi....




Kwanciya Daddy yayi yana kabbara da girmama hukuncin ubangiji,
wato ubangiji ya hanashi auren Suwaiba saboda wannan ranar da auratayya zata bullo a tsakanin jinin da suka yi tsaftattaciyar soyayya ta tsakani da Allah,


lallai
*kaddara*
itace jigon rayuwar dan Adam,
domin da ita yake yawo duk inda zashi....
ina ma Suwaiba zata dawo taga hukuncin ubangiji,
taga yadda rayukan 'yayanta suka canza,

wata yar kwallar murna ya share yayi adduoinshi hade da runtse idanuwanshi......




Hauka ne kadai Mummy bata yi ba da taji labarin hade auren harda na Husnah da suka gama maganarta da kawarta Hajiya Safara'u,
babu irin masifar da batayi ba,
shiko Daddy ko a jikinshi kudin kayan kitchen ma yayi mata transfer zuwa account dinta dan sauran da kanshi zaiyi su,


Sa kai yayi ya fita ya bar gidan dan lagos ma zai tafi da daddare akan maganar gidan da aka samu...




Kuka ta zauna a parlor tana yi sosai kamar an mata mutuwa,
bakin cikin da take ciki yau har gwammaci dama bata taba sanin Daddy a rayuwarta ba,


Badar ce ta fito tana hamma,
duk wainar da ake toyawa a gidan bata da masaniyarsu dan ba zaman gidan takeyi ba,
da sauri ta isa gurin Mummy tana tambayar abun da yasa ta kuka,


Ganin da tayi wa Badariyya ya sa hankalinta dan kwanciya,
dan wani abu da ya darsu a ranta,
tasan Badariyya ce kadai zata iya yi mata maganin damuwarta...



Hannunta ta rike ta sake rushewa da kuka tace

"Badar na shiga uku,
Musaddiq zai auri Nadeeyah, Hafeez kuma Husnah,

kinji a inda zan kare a ya'yan da basu da asali,

yayan mai gadi ni zainab.....



Wani irin ihu Badar ta saki tace

"Whattt?

Nadeeyah zata auri Musaddiq dina....
ta fadi hannu na rawa tana dafe kirji.......




Mrs Tijjani Shattimah........
[11/04 12:07 AM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 5⃣6⃣
By *Aysha Ya'u kurah*





Mikewa Mummy tayi zuciyarta ta fara sanyi na yadda taga Badar ta harzuko, tasan tabbas Badar bazata taba bari auren nan ya tabbata ba koda kuwa zai zama ajalin Nadeeyah...



Hannunta ta kamo tace "Musaddiq dinki Badar,
mun gama magana da wani malamina akan halascin aurenku, da murnata nazo na fadawa Daddy,
shine yake cemin wai ai Papy Saif yazo mishi da maganar yanason hadin auren Nadeeyah da Musaddiq,
shi kuma nan take ya amsa mishi saboda kinsan yadda Daddynku yake da s-any-in haaa--li,
ni yanzu bansan yadda zanyi da raina ba,
ta karashe da kuka sosai wanda yake nuni da tabbas tana bukatar taimakon Badar...




Furzar da huci Badar tayi murya a kausashe tace
"Wallahi bazai yiwu ba,
na dauki alwashin saidai Musaddiq ya zauna babu aure in har ban halasta a gareshi ba a baya lokacin da kika ce ba aure a tsakanin mu,,
bare kuma yanzu da na tabbatar na halasta a gareshi zan yarda ya auri wata,
watar ma Nadeeyah,

wallahi Mummy saidai ayi auren nan babu raina,
bazan ma mutu ba,
sai dai ita ta mutu,
hannu ta daura kan kafadun Mummy tace
"ki kwantar

Please Login or Register in order to submit comment