Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yaga shagwabar da baya yi Mamma nayi,
abin kunya ya faďi cike da zolaya yana girgiza kai,


Dariya tayi sosai tace
"Kai ka koya min, leka cikin motar tayi ta hangoshi kwance ya mike yana bacci,
"ya kamata ku tafi gida,
plss uncle kuyi bacci gobe kasan zakasha wahala sosai,

"Ai bakinki ne wahala,
ke zanma wannan faďan,
kuma ki tabbatar kinci abinci yanzu kafin ki kwanta,
inason gobe in ganki kinyi kiba kamar Husnah kina jina ko,


Buďe baki tayi tana dariya tace "sai dai in kamoka,
ko kuma------

Ihun da suka jiyo a cikin gidan ne yasata katse maganar da tayi niyya,
tabbas wannan muryar Hilal ce sai kuma ta Husna da ta biyo baya,
da sauri ya rufe kofar suka ruga ciki da gudu..





Ganin daukacin yan gidan sun nufi dakin da Musaddiq yake yasasu nufar ďakin suma,
a tare suka iso ciki da Daddy,
abin da suka tarar ne tada hankalinsu,

Hilal ne ke kokawar kwace kwalbar hannun Musaddiq ya kasa saboda wani irin karfi da ya karu wa Musaddiq,
sannan kuma girman ba ďaya ba, duk sauran yan uwanshi dake gurin sunyi yunkurin karba ya hanasu,

Tsaye Daddy yayi ya kasa tabuka komai saboda bashi da karfin yin wani abu domin yayi iya kokarinshi ya fahimtar da ďàn nashi ba komai kake so kake samu ba,
bazai iya tunkararsa ba a yanzu ya riga ya sare da rayuwar danshi,
yasan zaiyi matukar wahala ya rayu..
ganin Daddy ya kasa cewa komai yasa su Anty Reemah sake sakin wani kukan,
ita kuwa Husnah kiran wayar Hafeez da Papy takeyi tana ihu tana kiran sunan Musaddiq,


Da sauri Taheer yayi gurin suka haďu da Hilal suna kokawar tare,

wani hauri ya kaiwa Hilal a ciki wanda sam baisan yayi ba ma,
ya riga yaci alwashin aikatawa shiyasa yasa ďaya daga cikin abokansu siyo mishi ba tare da yasan abun da zaiyi dashi ba,

sannan abun da idonshi ya gane mishi daga sama shi ya sake tunzura zuciyarshi ya tabbatarwa kanshi babu fashi sai ya aikata abun da yayi niyya...


Rike ciki Hilal yayi ya kasa tashi aka bar shi da Taheer da ya matse hannunshi koda kuwa kwalbar zata tsaga dukkan hannunsu,
ba tare da ankara ba Taheer yaji nashi ta bayan hannun,
a gigice ya saki hannun wanda hakan ya bawa Musaddiq damar ďaga kwalbar da sauri,
ihuu dakin ya dauka suna rokarshi da Allah da annabi,


Juyawa Daddy yayi ya bar ďakin yana mai kuka cikin zuciyarsa na irin tarbiyar da kowanne cikin 'ya'yansa suka samu,
ya sadakar ďan da yafi kowa kauna cikin yayanshi yau zai kauracewa ganinshi,
ya barshi ya aikata abun da yake so domin kuwa ko ya hanashi sai ya aikata tunda tun tasowarshi bai nemi abu ya rasa ba sai wannan..



A hanzarce Nadeeyah ta haye gadon da zai sadata da daidai hannunshi ta sanya iya karfinta ta kabe hannun haďe da daukeshi da lafiyayyun mari har biyu sannan tayi mishi wata iriyar runguma wacce bin umurni ne daga zuciyarta,


Tsittt dakin yayi kamar babu wani mahaluki da yake rayuwa a cikinsa,
daddadar muryar Nadeeyah kaďai ake ji wacce take fitar da ita cikin raunannen kuka.......





Mrs Tijjani Shattimah........


[02/07 9:55 am]: *FINAL*
-
*ALHAMDULILLAH ALA KULLI HALIN*


"Why are u doing dis to urself?

Meyasa kake son sanya iyaye da yan uwanka cikin wani hali saboda san zuciya?

In baka damu da rayuwarka ba baka tunanin yin sadaukarwa ka zauna ko dan saboda mahaifinka wanda ke faďi tashi akanka,

Meyasa ka zabi yin abinda zai dawwamar da ahalinka cikin kunci sannan kaima ka dawwama cikinsa har abada,

baka da masaniyar wanda ya kashe kansa da gangan bazai taba ďandanar kamshin aljanna ba,




"Ba komai ake so ake samu ba, sau tari abin da muke so bai taba samuwa a garemu saboda Allah ma yasan ba alkhairi bane,



Rage murya tayi ta ďago da kanta a kan kafaďunshi cikin ficewar hayyaci tace,

"Bakayi tunanin halin da zamu shiga ni da ďanka a rashinka ba....

har yanzu your heart is not strong,

you are the worst father smone cud ever imagine having,
saboda biyewa son zuciya zaka kashe kanka ba tare da tunanin zama domin ganin ka kula da ďan da baka taba sanin kana dashi ba,


Dis is nt love,
it's selfishness,
u are selfish,
kai dai duk abin da kake so sai ka samu,
baka tunanin halin da wasu zasu shiga,
kanka Kawai ka sani,
in ka samu abinda kake so kowa ma ya rasa,
ba'a yin rayuwa haka,
kowa daurewa yakeyi,
kowa koyan yin tawakkali yake badan yaso ba,

*"Sometimes it's better to move forward someone away, not becs u hv stopped loving that someone, but becs u have to shield urself from pain..*




Dan Allah kayi hakuri,
karkayi sanadiyyar rayuwarka saboda soyayyata,
bazan rayu ba,
bazan rayu da guilt din ba,

Allah ya kaddara rabuwarmu,
ka bar mishi komai shi kaďai yasan yadda zaiyi da rayuwarka tunda shi ya halicceka,

Na rokeka--- k...aa koyi hakuri... badan kowa ba,
saboda iyaye da ďan-----ka,
ta karashe tana mai haďe hannayenta guri ďaya cikin tsananin kuka.....




Hannayen ya kama jikinshi na rawa yana girgiza kanshi,

"Ur love is my weakness Nadeeyah,
how am i going to be strong without u?
I can't lv without u,
i just can't---
ya karashe faďi cikin kuka yana kokarin sake haďa jikinsu guri ďaya dan bayajin zai iya barinta ta bar jikinshi,



Da karfi ta ture hannunshi zatayi magana yayi saurin rungumeta,

"Plss don't lv me Nadeeyah,
Der is an emptiness inside my world,
I don't want to live life without you,
God knows how hard I've tried,

You are the one I need,
You're all that I want, you're my everything..


***

*Sadaukarwa....*

Ya zame mishi dole yayi abinda yayi niyya tun kwana uku da suka wuce koda kuwa wani sashi na zuciyarshi yaki aminta da hakan,


Nadeeyah yar uwarshi ce,
jininshi ce,
she deserve to be happy,
in Musaddiq ne happiness dinta ya zame mishi dole ya hakura,
soyayyarta tayi mishi karfin da dole ya samar mata abin da takeso,


"Furucinta na

*Bakayi tunanin halin da zamu shiga ni da ďanka a rashinka ba*

shi zuciyarshi keta bitarshi,

Yasan *SO* bai mishi adalci ba da ya sanya mishi dakon yin shi na tsawon shekaru,
haka Allah ya kaddara,

Nadeeyah ba tashi bace,
mallakin waninshi ce..

A hankali yake maimaita "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun,
dakyar ya iya ďaga kafarshi ya fara tafiya har ya bar ďakin,

Hilal ne kaďai ya ankara dashi,
da sauri ya mike yabi bayanshi,

A parlor ya sameshi tsaye yana kallon Daddy na zubar da hawayen da ya sake karya zuciyarshi,
da sauri sauri ya bar parlon hawayen da yaketa adduar kin fitarsu suka shiga tsere a idanuwanshi..



Yana shiga motar Hilal ya karaso ya rike murfin motar,

Dakyar ya iya juyawa ya share hawayen yajuyo da murmushi a fuskarshi yace

"Na fito ba sallama ko,
dare yayi ne kuma na bar junior a mota nasan zai iya tashi at any time.


"Dan Allah yallabai kayi hakuri, Hilal ya katseshi cikin rauni, yasan abinda ya gani dole ya taba zuciyarshi,


"A haba Hilal, me akayi? Babu komai walhy,
kowa yasan irin wannan yanayin, kuma duk kannena,
Allah zai kawo mana sauki dukkanin mu,
ka kwantar da hankalinka Taheer ya karashe cike da dauriya yana dafa hannun Hilal...




Kauda da kai Hilal yayi cike da tausayawa halin da dukkaninsu suka kasance,

"Allah ya warware mana matsololin nan,
mun gode da fahimta sai Allah ya kaimu gobe.. Hilal ya faďi dakyar can kasan zuciyarshi na mishi raďaďi..



Saida yaga fitar motar a gidan sannan ya koma ciki.


A inda suka bar Daddy anan yake har lokacin,
shi bai ma san abinda ya karasa wakana a cikin dakin ba,
duk zatonshi by nw kayan cikin Musaddiq sun zagwanye,
jira kawai yake yaji kukan yan uwanshi ya tabbatarwa zuciyarshi ya rasa ďanshi na har abada.


Jiki babu kwari Hilal ya karasa kusa dashi,
a kasa ya tsuguna zaiyi magana Daddy ya dakatar dashi,

"Ya mutu ko?
Allah ya yafe mishi,
ba sai kace min komai ba Mukhtar,
kaje ka kira liman sai a mishi sutura,
kowa lokacinshi yake ci,
shi nashi ajalin a hannuns----

Katseshi Hilal yayi ta hanyar share mishi hawayen da baida masaniyar suna zuba a idonshi,


cikin kuka yace "Daddy Musaddiq bai mutu ba,
har yanzu yana da sauran lokaci, in shaa Allah bazai aikata abun da zai sanya ka cikin kunci ba,
yana nan da ranshi,


Kallon Hilal Daddy yayi yana ganin kamar yana son boye mishi abun da idonshi ya gaza karasa gani ne,

"Mukh---

ganin Musaddiq a gabanshi ne ya hanashi karashe kiran sunan.

Runtse idonshi yayi saboda baya kaunar ganin yadda ďanshi ya koma.

Durkushewa Musaddiq yayi a gabanshi yana kuka wiwi yana faďin
"Ka yafemin Daddy,
dan Allah ka daina zubar da hawaye saboda ni, na rokeka...

Muryoyin su Anty Reemah su suka sa Daddy buďe idonshi, suma hakurin suke badawa suna tabbatarwa Daddy Musaddiq bazai sake aikata abu makamancin haka ba...


"Nadeeyah ya kalla wacce har lokacin bata rufe bakinta daga nemawa Musaddiq yafiyarshi ba,

"Nagode Nadeeyah,
Allah ya datar dake alheri a cikin sabuwar rayuwar da zaki shiga,
nasan ke kaďai ce zaki iya fahimtar dashi muhimmacin rayuwa da illar da yaso yi wa kanshi da mu ahalinshi,

Allah yayi miki albarka,
dama ban kullace shi ba,
a kullum burina ya fahimci cewa Allah ke bada abu a lokacin da yaso,
matsawar bawa bata isa Allah ya sauya al'amarinsa ba,
in babu rabuwa ai akwai mutuwa wacce tafi rabuwar zafi,
tunda in aka tafi ba'a sake ganin burbushin mutum,

Allah ya albarkaci rayuwarki,
shi kuma Allah ya bashi wani sabon farin cikin..


Da sauri Musaddiq ya kwantar da kanshi akan cinyar Daddy yana sake sabon kukan domin har lokacin zuciyarshi bata hakura ba,
daurewa kawai yayi da irin lallabawar da ban bakin da Nadeeyah da yan uwanshi sukayi mishi,
sannan yayi alkawarin zama cikin kuncin rashinta har karshen rayuwarsa..


Shafa kanshi Daddy yayi yana yi mishi addu'ar samun salama a cikin zuciyarshi....




Daddy ya dauki minti talatin yana mishi nasiha shi da sauran yan uwanshi akan cirewa kansu san zuciya domin shi ke kai bawa ga halaka,
saida suka tabbatar ya samu nutsuwa sannan kowa yayi ďakinshi domin kwanciya....



****
Karo na biyar kenan tana kiran Taheer wayarshi a kashe.
tunda hankalinta ya dawo jikinta ta tabbatar Musaddiq ya samu nutsuwa ta tuno dashi dan bata san da tafiyarshi ba,

"Allah yasa ba fushi yayi ba ta faďi a fili cikin sanyin jiki,
dakyar ta iya kiran Anty Saude,
ringing biyu ta ďauka,
saida suka gaisa sannan ta tambayeta inda Taheer yake cike da kunya,

Mikewa Anty Saude tayi tana mutstsika ido tace

"Allah yasa lafiya,
bari in duba dan kashe waya is unlike him,
zan kiraki Nadeeyah ki kwantar da hankalinki lafiya kalau yake dan naji dawowarshi..


Ajiyar zuciya Nadeeyah tayi tace "To Anty ina jiranki,
kiyi hakuri na tasheki a bacci,


"A'a haba babu komai Anty Saude ta faďi tana mai kashe wayar ta nufi ďakin Taheer....




Subhanallahi,
Tee Lafiya?

Anty Saude ta faďi tana nufar inda yake zaune ya dafe kanshi da dukkan hannayenshi,
a gefenshi ta zauna haďe da janye hannayen,
hawayen da ta gani kwance a fuskarshi ya sake ďaga hankalinta,
"Me ya far----

Kukan da ya kwanto a jikinta ya fashe dashi ne ya hanata karasa maganar,
ji tayi ta kasa hanashi saboda yadda dukkan lakar jikinta suka katse..
Saida ta barshi yayi ma ishi sannan ta ďagoshi hankali a tashe,
tasan inda matsalar take,
tun farko tasan hakan zai faru shiyasa ta haneshi da sake sanya kanshi cikin wannan halin,

"Ba sai ka faďa min komai ba Taheer,
nasan matsalarka,
na kuma san hakan zai faru,
duk mace bazata so rabuwa da wanda ta fara haďa zuri'a dashi ba,
hakan na gujar maka tun farko, nasan illar da zaka sake yi wa kanka amma kaki ji..

Share hawayen fuskarshi tayi tace
"Yanzu faďa min me kakeso?
Ta ina zan iya taimaka maka?


Cikin raunanniyar murya yace "Karki ga laifin Nadeeyah,
sannan ki goya min baya akan duk abin da nake son yi,
dan Allah karki kullaci kowa, Allah shi zai bani karfin gwiwar warware komai,
Ki goya min baya dan Allah Momma, shi kaďai nake so a gareki...



Cike da kulawa tace
"In ka tabbatar abun da zakayi bazai taba min zuciyarka da walwalarka ba, me zai hana in goya maka baya,
Allah ya sanya albarka cikin abun da kake da niyyar yi sannan Allah ya sassauta zuciyarka ya sanyaka cikin dawwamamman farin ciki...


Karar wayarta ce ta hanashi amsawa,

"Nadeeyah ce,
ka amsa mata, tun dazu take nemanka..

Mikewa yayi yana share hawaye yace
"Kice mata nayi bacci,
dan Allah karki matsamin amsawa,


Da sauri ta ďauka dan kar ta katse tace
"Ya--ya--yi bacci,

Yadda tayi maganar ya sanya Nadeeyah zaman dirshan,
tasan tabbas idonshi biyu,
Taheer baya bacci ba tare da yaji muryarta ba,
lallai fushin da yakeyi da ita mai karfi ne,
jin diff yasa ta duba wayar taga har Anty Saude ta kashe,
kuka ta fara yi tana rubuta mishi text ,
saida tayi text kusan goma Sha na ban hakuri sannan ta dauro alwala ta fara sallar da ita kanta bata san adadin rakao'in da tayi ba.....





Tun karfe tara na safiyyar washe gari kowa ya gama shirin zuwa gurin daurin aure,

Abbu da suka iso da daddare ya iso gidan da taimakon Hafeez,
yayi farin cikin ganin Nadeeyah matuka,
kauna sosai suka nuna mata shi da matarshi,
kyaututtuka kuwa tashasu a gurinsu.


Irfan da Allah ya fara shiryashi shima ya nuna farin cikinsa na ganin yar uwarshi.

A gidan suka karya tare da dukkan zuri'ar yayarshi,
sun daďe suna hira har Anty Reemah tazo ta dauki Nadeeyah dan suje ta shiryata..



A yanzu dukkaninsu sun daina jin zafin ta saboda sun san basu isa suyi jayayya da ikon ubangiji ba..




Waya sukeyi da Zainab tana ta zuba kukan an hanata zuwa taganta,
itama Nadeeyar kukan takeyi na farin cikin irin sauyin da rayuwarsu ta samu,

A baya basu taba tunanin zuwa koda Abuja ba,
sai gashi karatu ma ba'a kasar nan sukayi shi ba,

Allah sarki Mamma da Baba, Allah yayi muku rahama,
kun tafi da tunanin halin da zaku barmu,
sai gashi Allah ya kawo mana taimako ta ko wani bangare,
taimakon dangi na jini,

*Allahu Ahad......*





Shiryata Anty Reemah tayi cikin mint green lace mai touch ďin red, faďin irin kyawun da tayi bata lokaci ne domin ta matukar yinshi,
fuskar nan sai kyalli takeyi..

Bayan an gama shiryata ta dauki wayarta dan ganin ko Taheer ya ga sakonta ya aiko mata reply,
ganin babu reply yasata saurin kiranshi,
shigar wayar ya sata sakin murmushi mai kyau na jin dadin zasuyi magana,
har wayar ta gama kararta bai ďauka ba,
tana sake kira taji ta a kashe..


Dakyar ta iya daure kukan da ya taho mata,
tasan bata kyauta ba,
to ai itama ba laifinta bane,
tayi shi ne cikin ficewar hayyaci da kuma taimakon rai...





Cike da kasala yake shiryawa bayan ya kashe wayar da ya kunnata yaga sakonta rututu wanda ya kusa sauya ra'ayinshi,
samm baya san jin muryarta domin jinta kan iya sauya komai da ya kuduri aniya,
babbar rigarshi ya ďauko ya sanya sannan ya maķala hula wacce ta dace da kayan jikinshi..

"Daddy...
Junior ya kwala kiranshi lokacin da Shareefah ta gama shiryashi cikin shiga irin ta Taheer ďin..
ganin yanayin Anty saude yasata shiryashi saboda komai cikin sanyi takeyinshi tun safe..



"Hey my love,
all set?

Gyaďa kai junior yayi yace
"yes,
muje mu dauko Mamma..
hannunshi Taheer ya kama yace "Ai sai anjima,
yanzu bakason muje ayi biki kayi rawa?


"Inaso,
uncle Kamal ma zaizo ko?

"Why not,
muje su Kawu na jiranmu a waje, kasan in bama nan babu daurin aure....




A babban parlon gidan suka tarar da taron yan Agadez,
ganin babu sarki Tidjani yasashi gaishesu ya nufi ďakin da ya sauka..


A zaune ya sameshi wani dogari nasa mishi takalmi,
ganin Taheer ya shigo yasa dogarin gaishe shi ya bar ďakin.


A kasa Taheer ya tsuguna ya gaisheshi,
bayan sun gama gaisawa Taheer ya bijiro mishi da bukatar da ta sanyashi cikin ruďani,

Allah ya sani yana son kasancewa da ahalin Adamou a kusa dashi,
baya son abin da zai nesanta su,
to ya zaiyi Taheer yayi mishi magiya,
tunda shine mai auren dole yabi abin da yake so...

Sunfi minti goma suna tattaunawa sannan suka tashi suka ďunguma zuwa gurin daurin auren....



********

Masallacin da za'a ďaura auren ya cika tatil da mutane masu tsananin daraja da kima,

Kowa ka ganshi cikin shiga ta alfarma fuskar nan ďauke da annuri,
in ma akwai wanda zuciyarshi babu dadi to tabbas ya gayyato dangin farin ciki ya azawa fuskarshi,


Can gefe Musaddiq ne tsaye cikin blue shadda yana gaisawa da mutane duk dan ya sanya mahaifinshi farin ciki,
kusa dashi Hilal da Hafeez ne suma suna gaisawarsu da mutane cike da farin cikin yadda Musaddiq ya sake,
ganin shigowar Jamal ne ya sasu faďada fara'arsu,
Bayan ya gama gaida manya ya isa gurinsu yana dariya yana zolayarsu cike da barkwanci..




Sai kusan 12 dangin Taheer suka iso gurin daurin auren,
busar algaita ce kaďai ke tashi har suka iso gab da masallacin,

Sarki na shiga suka daina busar kowa yabi bayanshi,


Guri na musamman aka yi mishi iso ya zauna shi da mutanen shi,

Ganin shigowar Taheer da Junior ba karamin sosa ran Musaddiq yayi ba,
daurewa kawai yayi suka gaisa ya kamo hannun junior yana kokarin zaunar dashi a kan cinyarshi,
kinn yarda yayi yace

"Ni gurin Daddy zanje, Sakin hannunshi Musaddiq yayi ba tare da yace uffan ba,

"To ďan Daddy yau anan zaka zauna cewar Hafeez yana dariyar yake..

"Um um, ya faďi yana noke wuya haďe da rugawa gurin Taheer da ya fara tafiya dan isa mazauninsu....



Bayan Sallar jumm'a aka zauna ďaurin aure,
bayan an gama tsara komai yadda ya dace waliyyai suka matso gaba,

Daddy da Sarki,
waliyan asali, daga bangarori..
*(Team Taheer Sorry kun min halacci)*....



Cike da kasaitar masu martaba Sarki ya kalli Daddy,

Sadakin daga gareka nake bukata Alhaji,
domin Taheer ďanka,
yace basai na biya ba kai yake so ka biya...


Dariya sosai Daddy yayi ya fara lalubar aljihu,
yaji daďin karamcinsu matuka,

Kafin ya fiddo kuďin cikin aljihunshi waďanda yake da yakinin kankantarsu Kamal yayi saurin ajiye bandir ďin dubu ďaya a cikin tafukan hannunshi,

Murmushi Daddy yayi yace "Nagode Uncle ďin yara,
kamar kasan babu isassu a gurina,
Cike da girmamawa ya mikawa sarki yace
"Gasu,
a dawo min da sadakin ďiyata, wanda na biyawa ďana..


Dariyar kasaita mai martaba yayi ya kalli liman yace
"Ka Shaida,
Na karbi Sadakin ďiyata Nadeeyah,
sannan kuma na bada aurenta ga ďanshi *Musaddiq*...



Runtse ido Taheer yayi yana maimaito adduoin neman salama a cikin zuciyarshi...



Ba Daddy kaďai bane ya girgiza, ďaukacin mutanen cikin masallacin wadanda suka zo ďaurin auren Taheer saida suka girgiza,
shiko Liman sai faďi yake


"Sarki ya bada auren Nadeeyah ga Musaddiq,
waliyyin Musaddiq ka karba?

Saida ya maimaita sau uku Papy yayi saurin faďin
"Eh mun karba,
ubangiji Allah ya albarkaci wannan auren...



Rutsa hannayen Musaddiq Hafeez da Hilal sukayi wanda yake jin hakan tamkar mafarki,

Saida Jamal yadan mintsili kumatunshi sannan ne ya buďe idanuwanshi waďanda suka cika da hawayen farin ciki da tausayin irin sadaukarwar Taheer a gareshi,


"Alhamdulillah, hakan ya cigaba da furtawa kamar yadda yake ji daga bakin yan uwa makewayenshi...




"Ranka ya ďade ya zakuyi haka? Daddy ya furta bayan ya dawo daga mamakin ikon ubangiji,
a lokacin har an gama adduo'i,



Murmushi sarki yayi yace
"Kun cancanci fin haka,
Taheer shi ya umurceni da yin hakan,
ya nunar min irin halaccin ku garesu da ďan uwana,
wannan ba komai bane,
mu dai fatanmu zumuncin ya dore,


Hawayen farin ciki Daddy ya zubar ya rike hannunshi yana godiya matuka,
yasan wannan wata kudira ce ta ubangiji,
lallai bawa kar ya cire tsammani daga rahamar ubangiji..


Karar sako ne ya shigo wayar Daddy yayi saurin dubawa yana yashe hakora,


*Congratulations Kyari,
ashe sa'ar taku ce, Allah ya sanya Alkhairi*...


Cike da farin ciki ya maimaita sakon,
wani irin abu yaji ya zarga mishi game da ita,
Allah yayi mata kyakykyawan hali wanda ba tun yau ya sani ba,
saidai a yau ya sake tabbatar da cewa Saude mutum ce,
mace mai zuciyar zinari kamar yarda ya gani a gurin ďanta...




Amsa ya tura mata wacce ta sanyata manta duk wata damuwa da tuhumar Shareefah a gareta..

Bata san sa'ar da ta tura mishi
"I always love nd care for u Mukhtar,
Dan Allah karka fassarashi da wata manufa...
sai bayan ta tura taji duniyar ta mata ďumi,
tayi dana sani yafi a kirga ganin babu reply dinshi har tsawon mintina biyar...


Wayar Taheer ta gani tayi saurin ďagawa jikinta na rawa duk zatonta Daddy ne,


"Are u ready to be Happy again Momma...?
Tambayar da yayi mata kenan bayan ya Sarki Tidjani ya gama yi mishi Nasiha sannan ya sanar dashi alkhairin da abun da yayi zai jawo wa mahaifiyarshi,
hakan yasanya shi cikin tsananin jin dadi domin mahaifiyarshi zata shiga jerin ma'aurata wanda yake mata fatan ta mutu a ciki..



*(KUSKURE BABBA DA 'YAYA KE TAFKAWA NA HANA IYAYENSU MATA AURE BAYAN MUTUWAR MAHAIFINSU, MU SANI AURE DARAJAR MACE NE, MUTUWA A CIKINSA KUMA RAHAMA NE, KAR SON ZUCIYA YA HANA MU BIN UMARNIN UBANGIJI, ALLAHN DA YA KASHE MAHAIFANMU YA FIMU SANIN DALILI, MU DINGA BARIN IYAYENMU SUNA RAYA SUNNAR MANZO S.A.W, MUYI KOYI DA TAHEER DON ALLAH...)*




Cikin rashin fahimta Anty Saude tace
"Are u alright my dear?

Perfectly fine Momma,
I asked a question?

Yes ofcourse ur happiness is mine, me ya faru?


Kashe wayar yayi ya kalli sarki yace
"Kayi abinda ya dace Kawu,
Allah ya sanya Alkhairi...




Murna da Mamaki ta hana mutanen cikin masallacin sukuni
bayan an ďaura auren Anty Saude da Daddy,
babu wani kishi da ya darsu a zuciyar zuri'ar Mummy sai ma farin ciki da sukayi na samun alkhairai biyu lokaci ďaya,


Lokacin da labari ya iske gidajen..
Anty Saude Sallah tayi na farin ciki,
duk yadda Shareefah ta kai ga fushin rashin auren Taheer da Nadeeyah saida ta taya yar uwarta farin ciki...



Gidan Daddy kuwa tsitt akayi bayan gama farin cikin Auren Musaddiq,
labarin auren Daddy ya tsuma su ya sanya duk jikinsu mutuwa,

Ita kuwa Mummy dakewa tayi ta dinga faďin Allah ya sanya alkhairi,
matar mutum kabarinsa,
ni farin cikin samun abin da Little yake kokarin rasawa kaďai ya isheni farin ciki..


Duk sunsan sambatu takeyi domin ta kasa haďa ido da kowa,
saida ta shiga bayi ne tayi kukanta a hankali dan kar wani yaji ta..


Bayan ta gama ta wanke fuskarta sosai dan kar a gane tayi kukan, tana fitowa tayi kacibus da 'yayanta suna tsaye cike da jimami,
wucesu tayi ta ďauki hijab ďinta tana faďin

"Babu wanda yayi Sallah a cikinku,
ko duk kuna hutu ne,
bata jira amsarsu ba ta fita daga ďakin ta nufi bayan gidan dan zama ko zata samu sukuni a cikin ranta....





Bangaren Nadeeyah kuwa tana jin labarin aurenta da Musaddiq ta shiga tsananin tashin hankali,
kuka sosai ta fara yi na tunanin Taheer yayi fushi da ita,
tasan yanzu yana can ya zargeta da rashin adalci..

Ganin sakonshi na taya murna da kwantar da hankali shi ya sanyata nutsuwa amma duk da hakan tana bukatar ganinshi domin taji karin bayani daga bakinshi,
sam bata son hakkinshi ya bibiyeta...


Tayi matukar tausayawa Mummy bayan sunji maganar auren Anty Saude,
alwashi ta ďauka a cikin ranta na yi wa Daddy magana ya taimaka ya maidota cikin gidanshi kodan darajar 'yayanshi...




Walima ta musamman Daddy ya shirya musu a Shagalinku,


Shaukin da yake jin kanshi a lokacin bazai taba iya misaltuwa ba,
ganin fara'ar kan fuskar gudan jininshi wanda ya kasa zaune ya kasa tsaye tunda kunnuwanshi suka saurari ďaurin aurenshi shi yafi komai yi mishi daďi..



Godiyar da Musaddiq yayi wa Taheer bata faďuwa domin ji yayi da ana wa bawa sujjada zai iya mishi,
yayi mishi abubuwa da dama wanda son zuciyarshi ta gaza barinshi ya gani,
hakuri kuwa zame mishi yayi tamkar common saying domin daga sun haďa guri sai ya bashi hakurin abubuwan da ya yi mishi,

Saida Taheer ya

Please Login or Register in order to submit comment