Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Momma bari in fara wankan sai inci abincin....






********


_Agadaz_....

*DIYA MURADUN AHMEDOO TIDJANI YALLO PALACE*


Karar busar algaitar dake fitowa daga katafaren gidan shi ya bawa mutanen gurin damar mimmikewa saboda alamu ne na fitowar sarki,


kirari dogarai suka fara yi cikin farasanci ana kodashi kamar yadda akewa sarakuna,


Cikin daya daga jerin motocin da aka jera mishi ya shiga,

nan ma fadawa suka dinga masa kirari har saida sukaga kurewar motar..




Wani katafaren gida motocin suka shiga,

da sauri aka bude mishi kofa ya fito suka taka mishi har kofar parlon,
suka murda ya shiga sannan suka juya dan shiga cikin gidan na iyalan gidan ne kadai...




Cikin kasaita ya taka ya isa can sama ya fada wani kayataccen parlor,


Zaune ya sameta kan dadduma jakadiyarta na danna mata kafa,

tana ganin shigowarshi ta tsuguna ta gaisheshi ta fita daga dakin,



Rawanin kanshi ya zare ya zagayo ta bayanta ya shiga daddanna mata kafudunta hade da cewa

"My Sheri,

wannan damuwar har yanzu bazaki daina ta ba,

shekara da shekaru kina tunanin abu daya,

haihuwa Allah ke bada ita,

kuma bai rubuto mu cikin wadanda suke da rabon samu ba,


kuka ne mai karfi ya kufce mata tace

"ina tsoron ranar da zamu wulakanta bayan ranka,

Mulkin nan ficewa zaiyi daga gidan nan,

kuma in ya fita babu irin wulakancin da bazamu gani ba,


zama yayi sosai ya janyota jikinshi yace


"SHARIFAH,
mulki na Allah ne,
shi ke bawa wanda yaso,


A lokacin da mahaifinki ya rasu,
kin taba tunanin Allah zaisa a bani mulki duk da ni ba danshi bane sai dan na kasance miji a gareki,
gudan jininshi wacce kika zama tilo,


Da Allah ya ga dama,
da fitar da mulkin zaiyi tunda sarki bashi da magajin kujerarshi, to da yake Allah ya rubuto ni din nan ni zan zama sarki shi ya sanya ya hadamu aure,

rashin bamu haihuwa kuma wannan shi kadai ya barwa kansa sanin dalilin hakan,

ta yiwu yayi wa wani can wanda bamu sani ba tanadin gujerar,

shiyasa ya hanamu samun magaji...



Share hawayen fuskarta tayi cikin gamsuwa tace "Allah ya kawo mana taimako,


A zuciyarta tana tunano rayuwar kuruciyarta wacce tasan tayi shi tare da wani wanda ya zamto jinin ta,

cikin kankanin lokaci kuma ya bacewa ganinta da tunaninta,

a yan kwanakin nan ne take tunano shi da suffofinshi da dalilinshi na barin gida...


Bata iya fadawa mijinta ba saboda ta kasa sanin hakikanin kusancinsu,
,

ko da yaushe ta runtse ido sai ta ganshi cikin mafarkinta,
tare da farin saurayi mai tsananin kama dashi,

saidai idanuwan saurayin sun fi nashi kyawu da girma,

karar Waya ce ta katse mata tunani,


Tana kallon shi ya dauki wayar cike da farin ciki,

"Kuna lahiya Saude,?

"lafiya lau kawu, an wuni lafiya?

"Kalau kalau ina Tahiru Yallo?



Yana nan lafiya kawu,

dama akan maganarshi na kiraka,

ya samu macen da yake so,
shine nace ka shirya kazo sai muje gidan iyayenta,


fadada murmushinshi yayi yace "to masha Allah,
tuzuru zai angwance,


Dariya sosai Anty saude tayi tace "haba kawu,

ai ko danye ne sharr,


nan suka cigaba da hira kamar ba surukai ba,

saida suka gama ya mikawa matarshi wacce ta zamto kawa kuma shakikiyar Anty saude,

nan suka shiga hirar yaushe gamo,
Anty saude tace "kizo fa tare da kawu,

dan tare zamu fara shirye shirye,

bazamu sa bikin da nisa ba,


Dariyar kasaita "Sharifa" tayi tace

"to wacece uwar in ba ni ba,
komai dani za'ayi,

gobe in shaa Allah zamu biyo jirgi mu iso.......




Mrs Tijjani Shattima....
[25/03 10:07 PM] Safiyya Umm Ab: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣4⃣
By *Aysha Ya'u kurah*




Juyi Musaddiq yayi a karo na biyu yace

"ka duba cikin aljihun wandona, plss ka barni inyi bacci,

tsaki Hilal yaja ya dauki wandon zai duba ya hango keyn a saman windon dakin,

jefa wandon yayi kan fuskar Musaddiq dan a cike yake dashi,


yafi 20mints yana tashinshi yaki tashi,

daukar keyn motar yayi yace "in kaga dama ka kai 4 kana bacci, idiotic being kawai,

murda kofar dakin yayi yana mitar yawan baccin safen Musaddiq,
wannan in ya fara aiki ya kenan,

sam Mummy bata kula da tashin shi,

shi kuwa saboda sabon da Papa yayi mishi tun asuba in ya tashi baya iya komawa bacci...


Zama yayi a parlor yana jiran ganin ta inda zasu bullo dan yayi alkawarin da kanshi yau zai kaisu makaranta,

yana son nunawa Taheer shi din mai babban matsayi ne a gurin ta...




Farin tight din da suke sawa a ciki saboda gajartan skirt dinsu ta dinga dubawa bata gani ba,

tayata dubawa Husna tayi har tsawon minti uku basu gani ba,

black kuma in suka sa korarsu gida akeyi,
da suka gaji da dubawa Husna tace "dan Allah zo mu tafi,
kar muyi latti,


kallon kanta tayi tace "nice zan fita a haka,

"to sai me,

nima bakiga bana sawa ba,
dama iyayinki ne, Husnah ta fadi tana nuna kafarta,

dauko school bag Nadeeyah tayi ta rataya, ta tura gashinta cikin hular makarantar da taki zama akanta saboda cikowar gashinta.....



Gud morning my PP,
Husnah ta fadi hade da zama kusa dashi,

"morning small aunt,
har kun shirya,

"eh yanzu zamu wuce ta karashe tana mikewa,

"ina kwana,

Nadeeyah ta fadi tana boye kanta a bayan kujera,

"Lfy kadai yace ya mike yana kallon Husna,

muje in kaiku makaranta,
zanje gida dauko ma Mum abu,

"yeyy... Husnah tace ta fara tafiya ya bi bayanta,


Yana gab da shiga motar ya dago kai ya kalli Nadeeyah da har lokacin tana gyara hular kanta,

Rufe motar yayi yana mata wani irin kallo har ta karaso gurin motar,

sam bai kula da skirt din Husnah da har yafi nata gajarta ba,


wani irin kishi ne ya turnukeshi, nan da nan zuciyarshi ta tafi tunanin irin kallon da Taheer yake mata da wannan gajerun uniform din,


kama hannun motar tayi zata bude yayi saurin cewa

"wait,
da wannan skirt din kuke zuwa makaranta?,

daga cikin motar Husnah tace "ya Hilal ka manta ne,

haka uniform din legacy yake,

"yes amma ai ana sanya wando ko,

ku ko kunya bakwaji makaranta ba ta mata zalla ba ku dinga tsilla tsilla da wannan skirt din,

maza fito kuje ku sa wando ya fadi yana bude kofar motar,


Agogo Husnah ta duba tace "ya Hilal munyi latti,

kuma bamu da legens fari sai baki ba'a barin mu muje school dashi,


"okay to sai ku fasa zuwa school din,


A firgice suka kalleshi dukkansu dan zasuyi submitting project dinsu,

marairaicewa Husnah tayi tace "plsss muje ka kaimu,
kasan dai muna shekarar karshe ne,
kullum cikin assignment ga project zamuyi submitting,

key yasa ya rufe motar yace

"ko kusa bakin ko kuma ku hakura da school yau,

da sauri Husnah ta fito tace "muje Nadeeyah,



Bayansu yabi da kallo yaja tsakin takaici,

tunanin yadda zaiyi ya rabata da skirt yakeyi,

a da uniform din school din na burgeshi,
ba kamar lokacin suna yara in su Anty Raly sun saka,
amma yanzu gaba daya ji yayi ya tsani makarantar ma ba uniform din ba,


Bai ga fitowarsu ba sai jin taba motar da Husnah tayi,

saida ya kalli kafafuwansu sannan ya shiga motar ba tare da ya samu gamsuwa sosai ba dan ba mage ba miyau.....



*****

Ke Badariyya,

Wai bazaki tashi bane,

tashi kije kiyi wanka ko bazaki makarantar bane?


Mikewa Badar tayi da mika hade da goge zufar wuyanta,

tun da ta taso bata taba azababen bacci irin na yau ba,
fanka ma kashewa Goggo tayi wai sanyi take ji,
shi kuwa a.c tun goma na dare ta kasheshi wai bazata sankarar da ita ba,

duk soyayyar da takewa Badar ashe ta nesa ce,

saboda ba ita ke hidimarta ba,

sannan kuma ita ma tana cikin nata kuncin dan Baffa bai dawo gidan ba sai 1 na dare suka dawo tare dasu Papy,
anan ma hirar suka zauna yi har 1:30,
ya nunawa Papy gurin da yake sa ran zai mishi gini in yazo ya dinga sauka,

Tana jiyo su dan ta kasa rintsawa,
tana jin Papy na cewa nan da shekara daya shima zai baro Gomben ya dawo nan kaduna cikin yan uwanshi,
ganin irin farin cikin da Baffa yakeyi shi ya sake tunzura zuciyar Goggo ta dau alwashin aiwatar da abin da tayi niyya shekarun baya....




"Gaskiya bazan sha wannan kunun ba Goggo,
walhi bazan karya da wadannan kazantar ba,

haba common tea ma sai kice bazaki bani in sha ba,
Badar ce ke maganar kamar zatayi kuka saboda takaicin karo da kunun da tayi,

tabe baki Goggo tayi tace

"Sai dai kar kisha,
tun da na tashi nake jiran Rilwanu bai zo ba,
ni kikeso in fita in siyo miki kayan shayin,

Da tsufana me zanyi da shayi ni, in kinga dama kar k---- 


Assalamu Alaikum,

sallamar da akayi ta katse Goggo daga karasa maganarta,


kaya niki niki taga Jamal da Hafeez suna shigowa dashi,

a bayansu kuma ta hango Anni da Mami,

papy ne ya shigo a karshe sai Rilwanu da Garzali suma dauke da wasu kayan,

fitowa Baffa yayi da sauri saboda jin muryar Papy,


kallonshi Anni tayi cikin zolaya tace
"Alhaji karka fadi,
irin wannan sauri haka,
shima saurin yazo ya ganka ne ya hanashi ya barmu sai anjima muzo,


Dariya Baffa yayi yace "marabanku,
ai sai ki bani kunya,

yanzu dai bari in boye murnata,

Dariya dukkansu sukayi Papy ya tsuguna ya gaida Baffa,

bai amsa ba ya dauko tabarma ya shimfida musu,

saida ya zauna sannan suka gaisa dukkansu cikin farin ciki,


Hira sosai Baffa sukeyi da Anni tana bashi labarin yarintar Papy har zuwa girmanshi, da irin nasarorin da ya samu,

gaba daya Baffa ya manta da Goggo dake tsaye kasake tana kallonsu, ko tafiyar Badariyya makaranta bata sani ba,




Kallon Anni yayi yace "tun jiya nake ta tunanin abun da zan miki in saka miki abin da kikayi min,


Na tattaro duk abinda na mallaka naga sun yi min kadan in baki a matsayin tukwicin abin alherin da kikayi mini na taimakon dana da kikayi har ya zama abun da ya zama,
na kwana ina miki addu'ar Allah ya sanyaki cikin farin ciki duniya da lahira,

Allah shi kadai zai biyaki da aljanna firdausi,
nagode nagode sosai Hanne,



Kafin Anni ta amsa Ruwaida tayi saurin cewa

"Ameen mijin Anni,
baban Papy,
kaka na ni kadai banda yaya Jamal,


garammmm


Goggo taji maganar kamar saukar aradu,

tsayuwace ta gagareta ta dawo cikinsu ta zauna saboda shurun da taji sunyi,


kallon kallo suka shiga yi a gurin Mami tayi saurin cewa Jamal ya kai Ruwaidah gurin su Nadeeyah,


"suna makaranta Hafeez ya fadi yana rike hannun sarkin katobara,
yace muje ki rakani..


Suna fita Anni tace "yarinta hoo,

ita a dole farin ciki takeyi taga babanta cikin yanayin da yafi na da,


"Yarintarta Ruwaidah akwai hikima a cikinta Anni, Papy ya fadi yana gyara zama..


Kallon Baffa yayi yace
"Baffa kana son sakawa Anni,

baka da abun saka mata dashi,
dan Allah ne kadai mai saka mata,

"abu daya zakayi ka kwatanta kyautata mata shine ka aureta,

Ta zamto matarka,

makwafin mahaifiyata,

wannan shine kadai zai sani farin ciki,

Anni ta ki yin aure saboda ni,

bata jure ganin kowa ya wulakanta ni, shiyasa ta hakura da aure domin taga auren wani mabudi ne na wulakanci a gareni,


Dan Allah Baffa ka auri ANNI,

kallon Goggo da ta kureshi da ido yayi yace

"INNA dan Allah kisa baki,

auren shi kadai ne abun da zamuyi mu saka mata......





Kafin Goggo ta gama tattaro amsar bayarwa Baffa yayi murmushi yace

"yo har sai ka roka,
ni da nake neman abun da zan bada tukwici,

ai na karbi wannan karramawar,

kuma in shaa Allahu zata ga karamci domin wannan din ma wani sabon karamcin ne da yake bukatar tukwici,


Dariya Mami tayi ta kalli Anni dake share kwallar da ta gangaro mata,

hannunta ta kama tace

"Alhamdulillah Anni,
dan Allah ki amince,


kuka ne ya kufce mata tace

"na Amince Maimuna,

wannan ya wuce tukwici,

domin kuwa zan shiga cikin jerin matan da nake fatan in mutu cikin sutura,

zan shiga jerin matan da zasu mutu ana maraba dasu,

hannu ta daga sama tace

"Alhamdullillah ala kulli halin,



Karkiyi saurin Hamdallah Goggo da ta gama charge ta fadi tana mikewa da kyar,

kiyi gaggawar maida murnarki domin a haka zaki mutu babu aure1,



Mijina bai min kishiya tun da jajayen sawunmu ba,
sai yanzu da muke rai a bakin rami,

in banda kwadayi ma me zakiyi da wannan tsohon,

me ya rage mishi da zaki suďa,


"Murmushin ilimi Anni tayi dan a ganinta kishi ne,


tace "ko ban samu abin sudewa ba zan samu martabar zama matar aure,


kwantar da Hankalinki bazan zo dan yin kishi dake ba,

zanyi aure dan in samu cikar kamalar da na dade ina nema,



"Aiko zaki mutu baki samu wannan kamalar ba in dai mijina zaki aura,

bakin da ya furta miki cewa zai aureki shi zai dawo yace miki ya fasa,


Shekeke Baffa ya kalli Goggo,

dauke kanshi yayi da sauri da yaga suna kokarin hada ido dan idanuwanta kan sanyashi manta komai, yace

"Aure babu fashi,

sati ma in shaa Allahu,

Kallon Papy yayi yace "ka daukesu ka maidasu gida sai ka dawo mu nemo magina su fara aikin ginin nan..



Sallama Papy yayiwa Ma'u dake tsaye galala masifarta ta makale saboda furucin Baffa,


Bin su tayi da ido har suka bacewa ganinta sannan ta fada dakin da sauri,


kofar bayin ta shiga bugawa tana masifa tana fadin "baka isa ba,

walhy Muhammadu baka isa ba,

alkawarin da kayi min kenan,

ni zaka butulcewa duk irin halaccin da nayi maka, 

to wallhi ka fito nan ina jiranka, saidai ka zaba koni ko ita, dan wallhi bazan zauna da kishiya ba..




Yana gama wanka ya bude kofar ya fito ba tare da ya kalleta ba,

kaya ya dauko yasa yace

"Ma'u halacci babu wanda ban miki ba,

shekararmu sama da hamsin dake ban taba yunkurin yi miki kishiya ba da kaina ba,


sai yanzu da nake son saka alkhairi da alkhairi,



yanzu ke ba abun kunya bane ki ts----


ka kalli idona ka fadamin haka Muhammadu, ta katseshi da karfi tana juyo kafadunshi,

juyar da kanshi yayi ya dauki turare ya fesa yace

"kallon idonki na daina shi har in koma ga mahallincina,


kallon cikin idanuwanki sun sanyani fita cikin hayyacina har na aikata ma diyar cikina abubuwan da har na mutu bazan yafewa kaina ba,

ki rike idanuwanki in rike rayuwata da mu'amalata,


yana kaiwa nan yasa kai ya fita ya bar Goggo da masifa kamar zata ari baki,


kayan dake tsakar gidan yasa Rilwanu kwashewa yasa mishi a dakin waje..


crates din kwan Goggo ta farfasa su da tabarya,
ta dinga bin kayan tana tsine musu,


Dakyar Rilwanu ya kwashesu,

yana gamawa yayi mata sallama yace "gobe zai koma garin su,

mahaifinshi baida lafiya,

bata bashi ansa ba ya cigaba da cewa
"ina tunanin dawo dashi garin nan Goggo zan kaishi asibitin dutse a duba shi, dan jikin nashi yaki dadi,


tabarya ta dago ta kundumo mishi ashar tace "Allah yasa ya mutu dan ubanka,

shege matsiyaci,


Fita yayi yana kunshe dariyarshi dan shi fushin nata ma dariya ya bashi.....




Mrs Tijjani Shattimah.......
[25/03 11:25 PM] Aysha Ya'u Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 4⃣5⃣
By *Aysha Ya'u kurah*





A tare suka iso makarantar da uncle Taheer,

kallon gaban motarshi Hilal yayi ya hango Sabrinah a gaba tana ta zuba iyayi,

Gyara parking dinshi yayi ya kalli Husnah yace "ina sakon da kike ce zaki maida yau,
taba jakarta tayi tace "yana cikin nan,

"okay take care my personal p,
In shaa Allah ta fadi ta murda kofar fita,

Tun da suka tsaya take ta kokarin bude kofar ta kasa,
saida Husnah ta fita sannan ta matso dayan gefen dan ta bude,
A zatonta lalacewa abun yayi..


"Ki kula da abun da ya kawoki makaranta,
in kuma soyayya kika zaba to bismillah babu mai hanaki, its ur life afterall..


Cikin sanyinta tace "ba soyayya nakeyi dashi ba,
yace yana sona kuma har yanzu ban bashi amsa ba *ALLAH*,

sai a lokacin Hilal ya dan samu nutsuwa ya waigo ya kalleta,
narkewa zuciyarshi tayi saboda yanayin da yaga fuskarta,

Cikin muryar da bai san yana da ita ba yace "kin tanadi amsar bashi?

"Um um,

ta fadi tana girgiza kai,
hannu tasa ta kara gyara hular kanta da ta kakarce dalilin girgiza kanta da tayi,

Bakar hular sanyin dake ajiye a gefen motar ya mika yace "wannan nada dan girma ki sata,
ki daina saka ta kanki tunda tayi miki kadan,
sannan in kika dawo gida zan baki amsar da zaki fada mishi,

Dafatan ba saina sake tuna miki dalilin zuwanki makaranta ba,

Yadda yayi maganar cikin dakiya yasata kallonshi,
ido ya daga mata alamar kin gane,

Sanya hular tayi da sauri tace "Eh in shaa Allah,

"Good ya fadi hade da cire lock din ya fito ya bude gefen da take,

yana hango Taheer tsaye a gate da Husnah da wasu yara a gefe,
tana fitowa a motar ya dakatar da ita ta hanyar gyara mata gashin da ya leko,

"wai bakya kitsone?,

ya fadi a saitin kunnenta,

gyada kai tayi tace
"ko yau nayi zai warware,

"okay to sai a yankeshi kawai ya fadi yana kallon yadda zatayi,

Dariya ce ta kubce mata tace
"to in na dawo zan yanke,

"akwai barber karki damu kina dawowa sai muje,

Maza ki shiga school nd becareful,

"In shaa Allah ta fadi tana mamakin yadda ya damu da ita a yan kwanakin nan,
mutumin da ba kowa yake kulawa bare har kaga dariyarshi,
ta ta'allaka abun da tausayinta yake ji da kuma shakuwarsu da zainab,

Harde hannu yayi yana kallonta har ta karasa gate din,

"Good morning sir,
ta fadi hade da rankwafawa,
duk yadda yaso danne abun da ya tokare wuyanshi ya kasa,
bai amsata ba ya juya dan komawa office dinshi,

Husnah da hankalinta ya gama tashi tace "pls sir plss kasa baki ya barmu,
bai waigo ba dan a harzuke yake matuka,

Ko Musaddiq da Hilal yace shine wanda zai aureta bai tsaneshi ba kamar yadda yake jin tsanar Hilal,


Yana shiga office ya jingina jikinshi jikin kofar office din zuciyarshi sai tafasa takeyi,

Allah kadai yasan adadin abubuwan da suka dahu a cikin zuciyarshi,

  Yana tsaye a gurin yaji bugun kofar office din,

dakyar ya iya matsawa hade da bude office din,

Husnah ya gani tsaye tana mishi murmushi,

"ehen what again?

Shigowa tayi ta sauke jakar makarantarta tace

"Sir dakyar uncle Kamal ya barmu muka shigo school kuma yace mu cire black legens din jikin mu,

Ledar da ya kai gidansu ta ciro ta mika mishi tace
"ance in dawo maka dashi,
bai kalli ledar ba yace

"Okay ajiye ki tafi,
ajiyewa tayi tace "sorry sir,
gidan mu ba'a tsayawa da saurayi sai an gama sec school,

Kaga Daddy baisan ka kawo ba Yaya Hilal yace a maido maka,

"nt bad jeki kawai...
ya fadi yana gyara gujerar da zai zauna,


Tana fita ya kifa kanshi a tebur,
tunani kala kala babu wanda baiyi ba,

Da sauri ya fatattaki tunaninshi na karshe na

" *ka rabu da ita*,
dan bama zai iya imagining ba, bare ya aiwatar,

Mikewa yayi dan zuwa ajinsu duk da yau bazai musu darasi ba,

sa'a yaci da ya shiga babu malami dukkansu suna zaune suna hira,

Gaisheshi dukka ajin sukayi ya amsa hade da cewa su zauna,

Rasa abin ce musu yayi dan ba darasi yazo basu ba,
saida ya kusa 5mints sannan yayi tunanin neman wadanda zasu gyara mishi office,

Dadi tunanin yaji a zuciyarshi ya kalli duka yan class din yaga kowa idonshi na kanshi ita kadai ce kai a sunkuye,


"Hey u with black cap,

" *kyari*

sunan dake rubuce a jikin hular, tabo ta *Amal Mus'ab* tayi  tace "Nadeeyah ke yake kira,

Mikewa tayi da sauri tace

"yes sir, keyn office din ya bawa khalifa yace
"mika mata taje ta gyara min,

da sauri Sabrina ta mike tace "zanyi sir,

"noo zauna ki huta,
ya karashe yana fadin hv a nice day class,

thank you sirrrr...



A hanyar shigowa harabar clases din ta ci karo da Badariyya,

Ja baya Nadeeyah tayi dan ta bata hanya,

wani irin kallo Badar ta bita dashi from head to toe,

tana zuwa daidai kanta taga hular wanda take kira da *Rayuwarta*

*iyyye.....*

Badar ta fadi tana kallonta shekeke,

uban waya baki hular nan, 

Taba hular Nadeeyah tayi taga babu amfanin bata amsa tayi saurin bi ta gefenta zata wuce,

Janyota tayi ta zare mata hular tace

"ke har kin isa ki hada jiki da shi, tattara gashinta da zubo har gadon bayanta tayi ba tare da ta amsa ta ba ta juya dan komawa dauko hularta,

Hada ido sukayi yana tsaye duk abin da Badar tayi a idonshi,

"zan dauko hula ta a class sir,

karasowa gurin Badar yayi yace "Hular ki ce,
girgirza kai tayi tace
"ta mijin da zan aura ne,

"ikon Allah ya fadi cike da mamaki,

"ehen ita kuma wacece kenan a gurinshi,

"ba komai bace sir,
kawai dai tana zaune a gidan mu ne,
mamanta da babanta sun mutu,
talauci yasa yayansu bazai iya rikesu ba shine aka dawo dasu gidanmu,

"Nan da nan alamun shi suka sauya yace "abin da na tambayeki kenan?,


"Na baka amsar abin da ka tambayeni a farko na cike da karin bayan ta fadi tana turo baki,

Hannu ya mika mata yace "bani hular nan,
rai a bace kamar zata mutu tace "sir ya za'a yi tasa min hul---

give it here ya katseta cikin tsawa,

Daura mishi a hannu tayi tana kunkuni,


Mikama Nadeeyah Hular yayi ya wuce,

ďan labarin ta da yaji ya sanya mishi kwadayin sanin cikakken labarinta.....





"Alo Hajja Saude,
kiyi  hakuri bazamu samu daman zuwa yau ba,
zamu tafi morocco kai *ummu Ayyu* asibiti,
jikin yaki,


Gyara zaman wayar Anti saude tayi a kunnenta tace

"Allah sarki, jikin har yanzu dai,
to Allah ya bata lafiya,
babu komai, karku damu ni zanje in fara gabatar dashi kafin ku dawo,



Cikin jindadi aminan suka hau hira duk akan sarautarsu da kuma familynsu.....





Hoton da ta gani a kan table din ta dauka tana kallo sosai,
saida tayi mishi guga na musamman sannan ta ajiye,
tana gama gyaran office din ta sake daukar hoton tana kallo,


Hakanan taji mutumin cikin hoton ya shiga ranta,


Sanye yake cikin babbar riga da hula,
yayi kyau sosai,


Tana kokarin ajiye hoton taji yace "my late Father
" *Alhaji Haroun Yallo*,


Ajiye hoton tayi da sauri tace sorry Sir,

na gama yanzu zan wuce class,


Bashi da niyyar matsa mata a makaranta sam,
dan a yadda ya tsara a makaranta nuna mata rashin sani zaiyi kururu.
amma ya zaiyi,
soyayyarta ta hanashi katabus,


Takowa yayi ya karaso inda take tsaye ya dauko hoton,


"Wannan shine Mahaifina,
rayuwar da mukayi dashi ba mai goguwa bace,

kullum in ban tunashi a duk numfashin da nakeyi ba to tabbas zan tunashi a duk takun da zanyi a rayuwata,

He is my best friend,


Mutuwarshi ita ta kashe wasu sassa na farin cikin dake cikin zuciyata,

mutuwa ce wacce yayi ta ba zato babu tsammani,


Ajiye hoton yayi yace

"Mutuwa wata abace wacce zafinta yafi dukkan zafin wutar dake cikin duniyar nan,

zafin wuta na warkewa ya barka da tabo,

amma mikin rashin makusanci kullum sabo yake zama,


Mahaifina ya nuna min kauna har ranar da zaiyi tafiyar din din din,


"A ranar da zai mutu ranar na dawo daga Canada,


saboda kar ya daga hankalinmu shiyasa ya boye mana ciwonshi, ya dinga biye ma duk wata rigima tawa,

Tare muka je aski,
cikin rashin sanin yana ciwo nasa akayi mishi askin dukka kanshi dan ya zame min abin tsokana,
haka nan badan yana so ba ya yarda akayi mishi,

Daga gurin askim muka wuce yawo muna ta zaga gari muna ziyarar gidajen Abokanshi,



Masallacin cikin gidan mu nan ne guri na karshe da muka tsaya,



A daddafe ya idar da sallar magriba,
jin irin numfashin da yake fitarwa ya sani tambayarshi ko baida lafiya ne,
dariya ya kakaro hade da naushin cikina kamar yadda muka saba yace
"in yana da ni ta ina ciwo zai samu muhalli a jikinshi,


Nan take Muryar Taheer ta raunana, hawayen da suka cika idanuwanshi suka dinga tsere a tsakaninsu,

ya cigaba da cewa

"A sujjar karshe ta sallar isha'i karfin Abbana ya soma karewa,

Gaba daya masallacin yayi shuru saboda jam'i da ake bi,

numfarfashin Abbana kadai ake ji

Please Login or Register in order to submit comment