Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace mamma muje in kaiku,,
ayi haka.... mamma ta fadi tana rike baki,

bakomai ku shiga muje,
baya suka shiga ya ja motar suka wuce....

********
Tun daren suka gama shirye shiryen komai na tafiya,
ba kananan kudade daddyn shi ya turo na siyayyar tafiyarshi ba, mummy da kanta ta shirya mishi kaya suna ta hira cikin farin ciki,
Yaya wata nawa zakayi? Husna ta tambayeshi tana bude ledar dambun naman da mamma tayi mishi,
mummy tayi dariya tace shekara nawa dai, ai sai kin ganshi kawai, Husna tace "tabdi har shekara anya mummy zai iya zama kuwa, shi da baya ko iya kwana a wani gari,
shafa kanshi mummy tayi tace "can ma ai gida ne ko little? ,
gyada kai yayi ya kwanta kan cinyarta yace but I will miss you so much mummy,
i will miss u more my baby,
ka kwantar da hankalinka zan dinga zuwa ganin ka a kai kai kaji,
um kawai yace yana kallon Badariyya dake mishi kallon shi din baida wayau,
tsaki yaja ya mike ya nufi dakinshi,
rainin Badariyya a gareshi yayi yawa,
lallai taga gadon barcinshi amma babu komai with time Shima zai zama jajirtacce marar daukar raini in shaa Allah ya fadi yana mai karfafa zuciyarshi.....

Mrs Tijjani Shattima....
[04/12 09:46] Meela Adeel: 9⃣
°ZUMUNCINMU A YAU °
By Aysha Ya'u Kurah

HAPPY NEW YEAR, Allah yasa mun shigeta a sa'a AMEEN....

2017 is unforgettable... Allah yayi Maka Rahama Babana...

"Kilode sis"...
Husna ta fadi tana zungurar Badariyya da tayi tagumi tana kallon Kasa,

tsaki Badar ta ja tace "nothing bacci kawai nake ji,

Husna ta tabe baki hade da kwanciya tace
"to ai sai ki kwanta,

Badar ta dan kashingida ta runtse ido kamar mai bacci,

har cikin ranta bata son tafiyar Musaddiq,

duk da yawan samun sabanin da sukeyi tafi son kasancewarshi kullum a gida tana mishi koda kallon raini da wulakancin da ta saba ne,

to in ya tafi wa zata dinga gani,
Husna tayi mata kadan a cewarta,
duk da sa'oin juna ne amma a koda yaushe Badar gani takeyi ta girme ma Husna nesa ba kusa ba saboda tsantsar sangarta da d'agawa,

tunanin hanyar da zata bi ta hanashi tafiya ta shiga yi,
ta dade tana tufka da warwara kafin daga karshe ta samo mafita,..

a hankali ta Mike ta murda kofa ta fita ,

dakin mummy ta nufa dan tasan bata ciki tana can gurin musaddiq,

drawers ta fara janyowa ta shiga binciken visan musaddiq da aka kawo mishi jiya,

da kyar ta gano inda take cikin wata karamar jaka,

dariyar farin ciki ta shiga yi a ranta tace zanga yadda za'ayi ya tafi ba wannan,

hannu tasa zata fara yagawa taji an Fisge visan  a hannunta,

saurin waigawa tayi dan ganin ko waye,
Husna ta gani tsaye tana kallonta cikin ido,

"haba Badar yanzu muguntar taki har ta kai haka,
meye amfanin yaga mishi visa,?
tun fitar ki na biyo ki dan nasan ba fitar alkhairi kikayi ba,
akwai abin da kike shirin kulawa da shurun da naga kinyi,,

mtswwwwwwwww Badar taja dogon tsaki tace "dalla malama bani,
ni nace miki yagawa zanyi,

to me zakiyi dashi? husna ta tambaya fuskarta dauke da mamaki,

ban sani ba Badar ta fadi tana mik'a hannu zata kwace,
kaucewa husna tayi tace wallahi bazan baki ba,
sai dai ki kwata ta karfin tsiya,

nan suka fara kokawar da ya janyo hankalin su mummy,

Kaiiii, kaiiii,
lafiya menene haka, mummy ta fadi da karfi tana shiga tsakaninsu,

Husna tasaki wahalalliyar ajiyar zuciya hade da haki tace mummy visar Yaya zata yaga,

Visa kuma, to me yasa??
mummy ta tambaya cike da mamaki tana kallon Badar,

Cike da shagwaba Badar tace
"mummy karya fa takeyi wai dan taga na dauko na rike a hannuna ina karantawa shine tace wai zan yaga,
akan me zan yaga mishi visa,
me yaga war zai amfane ni dashi,
kawai dai sharri zata min dan taga ba k----- mummy tayi saurin rufe mata baki ta rungumeta tana rarrashinta,
yi hakuri Badar din mummy,
nasan karyar husna ai, in mafadin magana wawa ne majiyinta bazai zama wawa ba,

Husna ta fito da ido waje cike da mamaki tace Badar kiji tsoron Allah,
tabdi!!!! ta kara fadi cike da kullewar Kai tana tsananin mamakin halin Badariyya a Yan Kananun shekarunsu,

ajiye visar tayi a kan madubi ta raba ta gefen musaddiq da ya nade hannayenshi yana kallon ikon Allah ta wuce rai a bace,

rufa ma Husna baya yayi hade da hararar Badar yana fadin Allah dai ya kyauta,

"Ameen"
mummy ta fadi a fusace tana sharewa Badar fuska tana kara bata hakurin abinda husna tayi mata,

Sam bata son bacin ran Badariyya,
wata iriyar kazamtaciyyar soyayya takeyi mata wanda bata da masaniyar wannan zurfaffan son zai mata illah marar misaltuwa anan gaba.......

********

"Babu sallama......"
Ta ji an fadi a bayanta,

da sauri ta waigo a firgice ta kalli motar,
kwantar da sit yayi a gaggauce hade da karasa bude tint glass din,,

nan da nan ta saki murmushi mai sanyin kyau,
tace "ina kwananku,

Hinad ta turo kanta daga baya tace "leko kiga mai magana Nadiya,
Yaya Hilal ne yake bukatar yin sallama dake,

Hilal ya chire hular da ya rufe kanshi dashi ya dago sosai ya hade girar Sama da kasa yace wallahi zan karya yarinyar nan,

Hinad ta zaro ido ta kalli drivern mummy tace dan Allah mal---- bige bakinta yayi yace dan Allah Malam ja muje inda mum ta aike ka,

Hinad ta turo baki tace "Nadiya bani milk candy pls Kinga yau zan tafi,

Nadiya tayi saurin juyawa shagon tasi ta dauki robar da ko minti biyar batayi da bashi ba ta miko ma Hinad tace gashi ki tafi dashi duka,
Allah ya kaiku lfy,
ki gaida anty da Yaya Musaddiq,,

ta cikin bakin glass Hilal yake satar kallonta,

duk tunanin shi ba wanda ke ganinshi bai San drivern mummy idanshi kyar akanshi ta mudubin motar ba,
sai yanzu ya fahimci dalilin da yasa ya biyoshi kuma ya tursasa mishi biyowa ta layin dan ko kusa ba hanyar inda zasu bane,

murmushin zuci yayi yace
"yarinta hooo,"
in ba yarinta me wannan dan yaron ya sani akan mace,
macen ma jaririya,
ko da yake akwai Soyayyar  yarinta da kuma ta jini,

muryar Hilal ce ta maido shi daga duniyar zancen zucin da ya tafi,

da sauri ya tada motar suka fara tafiya,
daga musu hannu Nadiya  ta shiga yi alamar bye bye,

suna gab da kure layin ya sake kallon madubin gefenshi karo na barkatai ya hangota tana juyawa gurin mai shagon,

kwantar da kanshi yayi kan sit hade da lumshe ido yana Nazarin abubuwa da dama....

LARNACA INTERNATIONAL AIRPORT CYPRUS

2:27am daidai,, agogon kasar Cyprus ya buga,
daidai da karfe 1:27am na agogon kasarmu Nigeria,,

Hayaniyar mutanen cikin jirgin ne ya farkar da musaddiq da bacci yayi can wata kasar dashi,

mik'a yayi ya sake gyara seat belt dinshi, ya kalli Hilal  yace
"har mun iso? ,
da kai Hilal ya bashi amsa, alamar eh,,

Alhamdulillah Ala kulli halin musaddiq ya fadi yana mai gyara zamanshi kafin jirgin ya karasa tsayawa,,,

"Welcome to the third largest nd third populous island in the Mediterranean uncle"

Hinad ke maganar cikin kwarewa tana bude hannayenta hade da lumshe idanunwanta a Saman matattakalar benen jirgi,

thank u my darling daughter, musaddiq ya fadi yana mai sunkuyawa dai dai kumatunta yayi mata peck,
saukowa sukayi  kowa rike da Jaka suna ja, suna baza idanuwa,,

daga can nesa suka hangoshi tsaye cikin ash jallabiya yana hamma hade da duba agogo,

a guje Hinad ta ruga tana kwala kiranshi da karfi, "PAPA",

bude hannayenshi yayi yana murmushi ta shige jikinshi ya dagata Sama yana juyata,

" I  MISS U SO MUCH PAPA"

misd u more more more angel,
Hw waz ur trip? , boring ta fadi tana tabe baki,,

ohhh why my dear?  Ya tambaya yana Jan kumatunta,-----

for crying out loud PAPA abinda kazo yi nan kenan, anty reema ta fadi cikin katse musu hanzari,

sauketa yayi yace come on my dear Reems u knw am here for u,

kallon musaddiq yayi cike da murna yace welcome broo, ya hanyar? ,
"lafiya lau alhamdulillah, mun sameka LFY? musaddiq ya tambaya yana murmushi,,
fine fine ka dai ganni sai dai dan wuya na rashin girkin yayarka ya fadi cikin zolaya,
dariya musaddiq yayi yace I cee,

Gud morning father,
PAPA ya fadi yana mai tsugunawa HILAL dake ta faman latse latsen waya,

ohh dad  neman magana ne kawai kasan zan gaisheka ai,
just don't want to interrupt you,
you knw i miss u,,
gaisuwar mu dabanne,

harara Papa ya bishi dashi ya karbi jakar hannun matarshi yace
"oya lets go bacci nake ji sosai sosai, kama hannunshi Hinad tayi suka nufi hanyar waje....

Mrs Tijjani Shattima......
[04/12 09:46] Meela Adeel: °ZUMUNCINMU A YAU°

By Aysha Ya'u Kurah
1⃣0⃣

Agios tychonas, limassol..

Estate ne gari guda na ma'aikata,
da yawansu turawa ne yan kasashe daban daban,

yan kasar turkiya sunfi kowa yawa a cikin estate din,
sai tsirarrun bakaken fata yan Africa,,

A katafaran parking space din harabar gidan sukayi parking motar,

fitowa sukayi kowa na mik'a suka nufi cikin gidan,
lift suka danna suka shiga, ya kaisu hawa na takwas,

"AMB G KANGIWA 380"

shine rubuce a Saman kofar part din,
wani kati mai kauri yasa ya bude kofar,
tsayawa fadin tsaruwar parlon ma bata lokaci ne,
parlor ne na garari na kuma gani a fada a ko'ina,

Daki kowannensu ya wuce sukayi wanka suka sauke da farali,


kafin su fito parlon, kawar anty Reema matar abokin
"amb GADDAFI KANGIWA" ta aiko da abinci kala kala,

Babbar diyarsu "MEERAH "  wacce sa'ar Hilal ce ita ta kawo abincin ta shiryashi kan table,

da murmushi anty reema ta karaso gurin tana fadin
"oh Allah ita ko Ammi bata gajiya,
irin wannan hidima haka,

Meerah tayi murmushi tace "ina kwana mum,

lafiya lau diyar albarka, har ke bakiyi bacci ba, ina su Adeel? ,

sunyi bacci,
ina tsaye a balcony naga shigowarku ai,, Meerah ta fadi tana mai Jin kunya,

ikon Allah anty Reema ta fadi tana shafa kanta,
to kice mata mun gode sosai kinji,

gyada kanta tayi tace "mum Hilal fa,

Anty Reema ta kalli kofar dakin shi tace yana ciki tare da kanina,

wata cooler ta dauka mai kyau ta yi hanyar dakin,

Tarar gabanta hinad tayi tace "Hey smarty,
ajiye cooler tayi ta rungumeta tace "my little smarty, tot kinyi bacci,?

Hinad tace "banyi ba ni ina nawa?

Ohh smart gal bansan zan ganki ba, ki bari gobe da safe zan miki duk abin da kike so,

"naki Wayan,
hinad ta fadi tana Noke wuya"
wannan na coolr zanci ko nima in miki rowar abin da na kawo,

dariya Meerah tayi tace "issoryt" muje sai kuci tare,

No.. no.. no.. Hinad ta fadi tana girgiza kai, tsaya a nan in dauko plate, wannan acicin ne zai bari muci tare,

Dariya ce ta gauraye parlon ciki harda musaddiq da suka fito tare da Hilal,

wani miyau Hinad ta hadiye ta kwalolo ido saboda irin kallon da Hilal ke mata,

baya ta fara ja a hankali tana kallonshi,
a guje ya bita ta saki wata razananiyar kara ta nufi Sama tana fadin "wayyo Allah Papa zai kasheni,,

cike da tsokana papa ya daka mishi tsawa yace,
"karka taba min 'ya tunda ba karya tayi ba,
duk rabin abincin gidan nan wake cinye wa,?
Sanin ci irin naka ne yasa Meerah tayi Maka naka abincin daban,
ko ba haka ba Merah?,

  aaaahhh... Papa pls karka hada ni da Hilal meerah ta fadi fuskarta  dauke da murmushi,
favourite dinshi na dafa mishi daban,

Papa ya murtuke fuska yace nayi karya kenan? Meerah ta daura hannu a kai tace nooo baka yi ba,,

Papa ya kalli Hilal yace "to kaji, zo kawai ka zauna Kaci abinci nasan kana jin yunwa,

hade rai Hilal yayi yace "nakoshi"  yasa kai yayi hanyar daki,

kiranshi anty reema ta shiga yi ko waigowa baiyi ba ya shige dakin ya bugo kofar da karfi,,

kallo anty reema tabi Papa dashi ya dauke kanshi ya cigaba da cin abincinshi yana yan wake wake,

Musaddiq ya mike zai bi Hilal Papa ya tsayar dashi yace dawo Kaci abincinka indai hilal ne yana zuciya da komai banda abinci,
ka rubuta ka ajiye ko karfe nawa ne sai ya fito yaci abincin shi,

  nan take Hinad ta saki dariyar da ta dade tana gimtsewa,

Anty reemah ranta ya kara baci tace "walhy zanci mutuncinki yanzun nan,

sa'anki ne?

Gyada kai tayi tace "sorry mum,

dalla yi kiyi ki tashi kije kiyi sallah ki kwanta, da wani katon bakinta Mai shegen surutun tsiya,

Papa dai baice komai ba ya mike ya nufi gurin meerah dake tsaye yace "je ki kwanta Dota Allah yayi miki albarka,
Ameen Papa,, ta kalli anty reemah tace "gud nyt mum, nyt sweet heart ki gaida Ammi....

*******
Kaduna.. Nigeria

Rayuwa ta dan fara sauyawa su mamma suwaiba saboda yar sana'ar da sukeyi,

ga hafiz dake harkar fruits, yanzu kullum sai ya samu dari biyar wata rana fiye da haka, ga kuma rarar fruits da yake samu ya taho dasu gida su Sha su kyautar da sauran,

Yana matukar Jin dadin sana'ar saboda sana'a ce mai albarka,

Saida yayi sati uku yana koyan harkar sannan anty reemah ta turo mishi da dubu dari biyar,

a ranar saida yayi kukan murna dan ko a mafarki bai taba tunanin rike dubu hamsin tashi ta kanshi ba, bare dubu dari har guda biyar,
Allah kenan in yace "ku fa ya kun" shikenan, (Allah ka datar damu)..

Zama yayi da Mai gidanshi sukayi shawarar abunda zaiyi da kudin,

d'aura shi yayi akan harkar sosai saboda yanada jarin shi na kanshi, babu inda basa Zuwa saro Kaya basu onitcha, enugu Lagos da sauran guraren sarin kayan fruits,,

Cikin ikon Allah da taimakon Papa aka bawa Nadiya admission a fgc malali,
Hafiz yayi kokari wajen yi mata komai na tafiya makaranta,
haka babanta da Mamma suwaiba duk sunyi mata kokari,

Sam bata San tafiya saboda tausayin mahaifanta,
wani bangare na zuciyarta kuma ya bata shawarar, Ilimi shine gishirin zaman duniya,
kuma ko ba komai zata kauracewa ganin Badariyya,
da wannan tunanin ta samu karfin gwiwar tafiya makarantar kwana....

*****
Frederick University..

Gudu yake shararawa cikin motarshi kirar KIA karama ruwan goro,

wakar "Rockabye" ta "Anne-marie ya Kure volume yake saurare yana bi a hankali,

hon ya latsa da karfi yana sauke glass din motar hade da kallo inda take..
mikewa tayi ta isa gurinshi ta bude kofar gaba zata shiga yayi saurin dakatar da ita,
"baya zaki zauna ko kin manta bani kadai bane,

rufewa tayi bata ce kala ba ta bude baya ta shiga,

ko kallonta baiyi ba ya tada motar ya wuce "faculty of engineering"

a kofar dept din ya hango shi zaune yana duba wasu littafai,
kashe motar yayi ya fito ya karaso gurinshi yace
"heyyy guru" shall we,
musaddiq ya mike yana kakkabe jikinshi yace eh mu tafi,

waya Hilal ya mik'a mishi yace "call ur mama ta kirani Wai wayarka a kashe,

  Musaddiq ya dan ja tsaki yace "barta zan kira in naje gida na gaji Sosai,

mayar da wayar aljihu yayi ya bude kofar motar ya shiga,,

gaisawa musaddiq sukayi da meerah dake baya tana shafa hoda a fuska,.

kallonta Hilal yayi ta mudubi yace "madam makeup"  an fara, banza tayi mishi ta cigaba da kwalliyarta,

jan motar yayi yana murmushin ko a jikina yarinya...

Mrs Tijjani Shattima...
[04/12 09:46] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU
By Aysha Ya'u Kurah
1⃣1⃣



Shekaru sun dan jaaa,
cikin farin ciki da akasin shi saboda halin rayuwa na yau zuma gobe madaci,

"Nadiya Adam"
muje mu rage Miki hanya mana,

yamutsa fuska Nadiya tayi cikin damuwa tace bari kawai Rukky, zan samu napep in tafi,

Kallonta rukky tayi cike da mamaki dan dai tasan bata da ko Naira biyar a jikinta,
hannu tasa ta fara daukar kayanta tace zan kai miki kayan, ki taho a mashin ma wannan ke ta dama,

bin ta Nadiya tayi da kallo tace
"Haske dan Allah ki barshi kar in matsa muku Kinga hanyar mu ba daya bace,

  "ke kika rokeni? Rukayya ta fadi fuska a hade,,
Girgiza kai Nadiya tayi tace "a'a amma--- amma me Haske tayi saurin katse ta, tace "zo mu tafi dan Allah,

kwashe sauran kayan tayi ta bi bayan Rukayya Haske ranta duk a jagule,

A gatance ta fara makaranta,
tun daga shigarta har Zuwa ss1 third term,
tunda ta dawo first term din nan ko sau daya babu wanda ya ziyarce ta,
zuciyarta cike take da fargabar abin da yake faruwa da Yan gidansu,
number yaya Hafiz Sam bata shiga haka ta mamma,
tunda ta shiga motar take addu'ar Allah yasa kowa na nan lafiya,

dai dai kofar gida suka sauketa suka wuce cike da kewar makaranta,

Jakarta ta dauka ta fara tafiya domin karasawa cikin gidan,

A can bakin murhu ta hangi mahaifiyarta idonta yayi jawur hanci duk ruwa saboda wahalar hura wuta,
ajiye Jakarta tayi ta karasa kusa da ita,
idonta cike da kwalla take kallon mahaifiyarta dake mata murmushi,

hannunta Nadiya ta kama zata fara magana suka jiyo tari me karfi babu kakkauci daga cikin dakin,

da gudu mamma ta nufi dakin tana fadin subhanallah!! sannu,

bin bayanta Nadiya tayi da sauri, ta tarar da abin da ya daga hankalinta matuka,
mahaifinta ne kwance cikin bargo kamar jaririn goye,
ya rame ainun, idanuwanshi sun zurma sai tari yakeyi hade da kakin jini,

kuka mai karfi Nadiya ta saki tana fadin meya sameka Baba?,
mamma me ya sameshi,?

mamma dake tare jinin da wata tsumma tayi kokarin boye idonta da ya ciko tace "bashi da lafiya ne amma da sauki,

wani irin sauki mamma, Ina saukin yake anan?,

dan Allah ki kira yaya Hafiz mu kaishi asibiti,

nan kukan da mamma ke boyewa ya bayyana,

Take Nadiya ta rikice, dan ita dai tun tasowarta bata taba ganin bacin ran mahaifiyarta ba bare har takai ga zubar ruwan hawaye,
Durkushewa Nadiya tayi tace "mamma me nayi,? Dan Allah kiyi hakuri,
Wai me yake faruwa ne?

kuka mamma takeyi iya karfinta gunin ban tausayi,

kallonta Malam Adamu keyi hawaye na zuba ta gefen idonshi a ranshi yana mai Jin dadin kukanta domin ko ba komai zata samu saukin nauyin dake cikin ranta,

sai da tayi mai isarta ta share hawayenta, ta kalli Nadiya dake kuka tana share hawayen idon mahaifinta tace
"tashi maza kije kiyi wanka kiyi sallah,
bari in nemo miki abin da zaki ci,

Nadiya ta share hawayenta tace "ki barshi kawai, bari nayi wanka in daura mana, zauna ki kula da baba,

Gyada kai mamma tayi kawai, dan bata son tasan abinda ke faruwa,

Nadiya na shiga bayi mamma ta fita shagon Tasi da ya kara cika ba kamar da ba,
Indomie da Kwai ta ce ya bata,
dakyar ya bata dan yana bin ta bashin kusan dubu daya da dari hudu,

da sauri tayi cikin gidan, ta hado yayi, ta sauke ruwan dumin da ta daura ma mijinta, ta iza wutar ta daura Indomien cikin karamar tukunya..

Wanka da sallah Nadiya tayi,
ta saka doguwar rigar deep blue material mai gajeren hannu ta shan iska,,
ko mai bata shafa ba ta daura jar hula a kanta,

kyawu mai sirri da cikar budurci suka bayyana a tare da ita,

wani irin kyau Nadiya ke dashi marar hayaniya, wanda ya kara fitowa saboda dan hutu da kuma rufin asirin da suka samu,,

kusa da Mamma ta tsaya tace "sannu da aiki mamma,
ina Zainab?
"Tana  islamiyya,, mamma ta bata amsa tana tura leda cikin murhun,

Tambayoyi ne cure cikin zuciyar Nadiya,
ta rasa wanda zata tambaya ya bata amsarsu,
ko zata mutu tana tambayar mamma bazata amsa koda tambaya daya cikin tambayoyin da take dasu ba,,

Daki ta shige gurin mahaifinta da ya fara bacci numfashin shi na fita dakyar,
Kure shi tayi da ido tana addu'a tana tofa mishi,

Mamma na kwashe Indomien zainab ta shigo gida da gudu jikinta yayi futu futu,

"mamma yunwa nake ji, zainab ta fadi murya a sarke saboda tsabar gajiya..
kallon Indomien mamma tayi tace to bari kiyi wanka ko? ,

noke wuya tayi kamar zatayi kuka tace cikina na murda min,

je ki wanke hannu kizo muci, Nadiya ta fadi tana fitowa daga daki,

rungumeta zainab tayi tace "yaushe kika dawo anty?

Dazu kina islamiyya,
da fatan kina karatu a makaranta, Nadiya ta tambayeta tana shafa kanta,,
gyada kai zainab tayi tace Sosai ma,
kin kawo min chocolates,
Kumatunta Nadiya taja tace "eh yana jaka ta,
maza wanko hannu muje muci abinci..

Mamma kinci abincin ne?
Nadiya ta tambaya idonta kyar akan mahaifiyarta,
mamma dake kofar daki tace "eh munci sosai, bansan zaki dawo ba da na ajiye miki,
zainab da ta kai Loma kamar zata shake tace "mamma yaushe kika ci abinci?, bayan tafiya ta makaranta,
shine kika cinye baki ajiye min ba,

mamma ta saci kallon Nadiya,
tayi saurin maida kallonta gurin zainab tace ba gashi kina ci ba,
maza kici karki kware,

Nadiya dai hannu kawai take juyawa cikin abincin har zainab ta kai karshen shi harda sid'e kwanon,

meya ke faruwa mamma???

Tambayar ta fito a bakin Nadiya cikin rashin sanin fitowarta,

me kika gani?
Mamma ta amsa ta cike da fargaba,

rarrafowa Nadiya tayi ta dafa cinyarta tace "mamma boyemin abin da ke damunki bashi da amfani, nasan bani da maganin shi amma atleast zaki ji sauki in kin fada min.....

    **********

Ohh ni!!!
"wacce iriyar rayuwa ce wannan? d'aki kaca kaca sai kace ba na mata ba, mummy ke mitar tana tafe tana tsintar kayayyaki a kasa da takalma,

Husna dake kwance tana duba littafi tace
"kema kin San ko aikin waye mummy,
"ni gaskiya na gaji wallhy, canza min daki za'ayi, bazan iya wannan rayuwar ba,

kwance take cikin matsatstsiyar jar riga da yellow mini skirt,
Gashinta Parke a tsakiya da yellow ribon,
kunnenta dauke da earpiece alamun bata ma San me sukeyi ba,
kada kanta kawai takeyi tana bin wakar hade mutstsuka santala santalan kyawawan kafafuwan ta,

kafarta mummy taja a hankali,
juyowa tayi tana cire earpiece din kunnenta cike da rashin da'a tace
"ya akayi ne mum"
  mummy ta ajiye kayan makarantar ta a gefen gado tace "babu komai baby na, kinci abinci dai ko?
gyada kai Badar tayi alamar eh sannan ta juya ta mayar da kanta kan pilo tana cigaba da jin waka hade da chatting,,
"hmmmm" kawai Husna tace ta sakko daga kan gado tace
"mummy zanje gidan Anty Raudha,
"me akeyi??
mummy ta tambaya tana gyara ma Badar skirt dinta,
"birthday din Amal diyar Anty Laura, Husna ta bata amsa,
gyada kai mummy tayi tace "too jira Badar ta shirya ku tafi tare,

hanyar bayi husna ta nufa tace "bata San me muke fadi ba sai ki fada mata dan gaskiya ina shiryawa zan tafi,

Badar da ke saurarensu da kunne daya tace
"kifi ruwa gudu,
ke kika damu da local partys,
duk inda kika ji sha'ani jiki na rawa kin tafi,
'anyways baki yar a kasa ba,

maida earpiece dinta tayi ba tare da ta kalli mummy ba ta cigaba da danne dannen waya,

Husna kuwa bayi ta shige cike da bacin ran irin rainin da Badar ke ma mummy,
abin da ke kara bata ranta bai wuce yadda mummyn ko a jikinta ba,

duk rainin da badar ke mata sai dai tace "yarinta ke damun ta,

ita kuwa komin kankantar abu in tayi mummy ta dinga masifa kenan kamar zata ari baki,

watsa ruwa tayi cike da takaici da tunani iri iri....

Mrs Tijjani Shattima...
[04/12 09:47] Meela Adeel: ZUMUNCINMU A YAU
By Aysha Ya'u Kurah
1⃣2⃣

A hankali take maimaita kalmar "innalillahi wa Inna ilaihir rajiun" ruwan hawaye na tsere akan kumatunta,

kirjinshi take dannawa tana share kumfar jinin dake fita a bakinshi, nishi yakeyi Sama Sama yana kakari da karfi,

magana yake fisgowa daga can kasan makoshinshi,
muryarshi ta kara karfi tamkar amsa kuwwar loud speaker,

"kiyi Hakuri suwaiba! ,
kiyi Hakuri da rayuwa,
nasani ban jiyar dake dadin duniya ba saboda talauci na,

gashi zan tafi in barki cikin rayuwar talaucin da babu mataimaki,

kiyi hakuri suwaiba, Allah kadai yasan tanadin da yayi mana a lahira,
ki cigaba da hakuri da duk yadda kika tsinci kanki,
nasani kin iya kanki,

ki rike yaran nan,, basu da kowa a duniya sai ke,

ki fadawa Hafizu in ya dawo
na yafe mishi,!
na yafe mishi,!
na yafe mishi,!!!

Idonshi da yake lumshewa ya daga Sama,
ga azabar zafin fitar rai ga kuma radadin barin iyalanshi cikin yanayi na rashin garkuwa,

Ya Allah! ka iya ma zuri'ata abin da bazasu iya yi ma kansu ba,
LA' ILAHAILLALLAH----- kukan mamma ya karu saboda tsabar firgici,


A gigice Nadiya ta farka daga gajeren baccin da ya dauketa saboda jiyo kukan mahaifiyarta,
fitowa tayi daga daki da sauri har tana turgude kafa ta karasa dakin baban su,

kasa shiga tayi saboda hangoshi da tayi  damke da karfen gadon dakin hade da hannun mamma, yana haki da sauri sauri.

Juyawa tayi ta fita a gigice, 

"wake ta takalmi ko mayafi a wannan lokacin",
gudu takeyi da iya karfinta, ita dai tasan jefa kafafuwan ta kawai takeyi, bata ma San akan abinda suke

Please Login or Register in order to submit comment