Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuce,
da to Husna ta amsata suka wuce ciki,
abubuwan Badariyya sam basu dameta ba tunda tana samun sassauci a gurin Husna...




Yana gama nunawa plumber gurin dake zubar ruwa daga sama ya biyo ta kitchen dan duba ko akwai inda ke toshe a makwarar,
tsaff yagama saurarar maganganunsu,
maganar Badariyya ta tsaya mishi a rai,
"wai yarinyar nan me ta dauki kanta ne,
danne bacin ranshi yayi yakoma ya shiga ta parlonshi,
a gurin dining ya samu Mummy tana hada plates din da suka ci abinci shi da bakinshi,
gyaran murya yayi yace
"Zainab wani class Nadeeyah take?
Tunani Mummy ta farayi tace "mate din su Husna ce nasan class dinsu daya,
zama yayi akan kujera yace "ki fada mata gobe su shirya tare da su Husna zan kaita makarantarsu ta karasa acan,
duk da taji ba dadin yadda yakeson hada Nadeeya da ya'yanta baisa ta nuna mishi ba saboda yadda take taka tsantsan da zamansu,
amsa mishi tayi da "to Allah ya saka da alkhairi, bai amsa mata ba ya cigaba da kallon tv....




Shiryawa tayi cikin wata koriyar atamfa mai ratsin ja,
dinkin zamani riga da straight skirt mai tsagu,
rigar kuma matsatstsa mai budadden hannu,
tayi kyau sosai,
Husnah ce ta bata a cikin kayanta da suka dan kamata dan tafi Nadeeya fadi kadan,
dankwali ta daura ta kunshe kanta ta dauko hijab zata sa,
fisgewa Husna tayi tace "u are a joker,
wa zaki bi da wannan hijab din,
gyale ta miko mata tace "dankwalin ma cireshi zakiyi,
kallon Husna tayi tace "da wannan matsatsun kayan zan fita babu hijab?
gyada mata kai tayi tace "hango kanki har kin fita ma,
zatayi magana Husnah ta kwacee dan dankwali ta turasu cikin drawer ta rufe,
shiryawa tayi tana waka tana rawa tana ma Nadeeyah gwalo,
ita abin dariya ma ya bata ta sake kallon kanta a jikin madubi,
babu ta inda kayan nan basu bayyana surorin ta ba,
marairecewa tayi tace "kiyi hakuri Husna ko dankwali ne in daura,
bata saurereta ba ta fara shafa mata powder tana fadin "ki cigaba da butulcewa Allah,
dan dai So ba samu bane,
wallahi da nice tsirara ne kadai bazanyi yawo ba,
lallausan gashinta ta taje mata tayi mata parking da katon ribon,
light janbaki ja ta bata tace "ki dan sa kadan kiga yadda zakiyi, amsa tayi tadan goga a bakinta, gurin madubin Husna ta jata tace "dan Allah kalla, kamar a bakinki aka halicceshi,
mtsww taja tsaki hade da cije lips tana hango inama akai Nadeeyah school dinsu tayi ma gayu iskanci, ta nunawa *SABRINAH BILAL* ba ita kadai aka halitto da kyau da sura ba,
gyale ta daura ma Nadeeyah a kanta irin yadda tayi tace "muje ko,
a kunyace Nadeeyah ta bi bayanta tana tunanin yadda zata fita da kayan nan ba hijab,

Fitowarsu tayi daidai da mikewar Badariyya, hade da fitowar mummy daga parlon Daddy,
fassara yadda idon Badar ke nuna tsantsan tsana da kishin Nadeeyah mai wuyar fadi ne a alkalami,
bata ankara ba taji Mummy ta sake furto maganar da taji ta kamar saukar Aradu,
"yawwa Nadeeyah gobe ki shirya da wuri zaku je makaranta tare dasu Husnah,
wani irin tsalle Husna tayi tace "so quick Ya Allah, lallai luck is on her side today,

kallon Badariyya Mummy tayi tace "ke bazaki kitson bane? dauke kanta tayi tace "umm bazanje school ba gobe,
tana kaiwa nan tayi hanyar daki, dakatar da ita Mummy tayi tace "saboda me?
Kafin ta bata amsa Musaddiq ya shigo parlon yana hamma, tsayawa yayi daga nesa yana kallon Nadeeyah daga sama har kasa..


Karasowa yayi ya kewayeta yana kallon fuskarta da ta sunkuyar kasa,
murmushi yayi yace "tsarki ya tabbata ga ubangijin da halicci kyawawan mata a cikin gidan mu,
ina zaku je da irin wannan kwalliyar,
Kusa dashi Husna ta matso tace "saloon, ko zaka kaimu ne?
bata fuska yayi yace "na kwaso rana,
bacci nakeji amma bazan iya refusing daukar kyawawan kannena a mota ba,
kallonshi Mummy tayi tace "kyalesu su tafi Diku,
jeka ka huta abinka,
girgiza kanshi yayi yace "bari in kaisu Mummy, zanyi aski nima,

jin haka ya sa Badariyya sakin ranta tace "Mummy su jirani nima zanje kitson,
bata rai Husna tayi tace "wallahi Mummy Badar bata mana lokaci zatayi,
harara mummy ta sakar mata tace "in ma zata kai la'asar sai kun jirata,
turo baki Husnah tayi suka dawo parlon suka zauna,


Wayarshi kirar iPhone x max ya ciro a aljihu ya kalli Husnah yace "meye zai bata ran autarmu,
tashi muje waje inyi miki hoto da portrait camera,
sanin halinta nasan hoto yasa shi fadin haka dan ya kwantar mata da hankali,
da sauri ta bi bayanshi tana kiran Nadeeyah da tazo suyi tare,
kin fitowa Nadeeya tayi saboda yadda mummy ta kafa mata ido,
kyawunta da ta gani na yau da yafi na ko yaushe shi ya daga hankalinta,
bata so samm Musaddiq ya fada tarkon kyawun nan,
taci buri akan nema mishi 'yayan abokan Daddy ministoci dan samun karin girma a idon kawayenta,
dole ta san abin yi akan irin wannan kwalliyar da Nadeeya ta fara yi,
dawowa Husna tayi taja hannunta suka fita dan yin hoton..



Hotuna sukayi masu matukar kyau kamar an wankesu,
wanda sukayi su biyu shi yafi komai yi mishi kyau,
suna gama hotunan ya gyarasu ya daurasu akan status dinshi da instagram,
bai rage ko daya cikin goman da suka dauka ba,
yana gama daurasu ya sauka dan ganin fitowar Badariyya,
gaba Badariyya ta bude da sauri ta shiga ta zauna,
kallonta yayi ya kasa cewa komai yashiga ya waigo ya kalli su Husna a baya,
tada motar yayi suka wuce,
ta gefen ido Badar ke satar kallonshi, shi kuwa hankalinshi na kan titi yana tambayar inda zasu, cikin doki Husnah tace *MEENA'S TOUCH* Sabon saloon din da Anty Amina ta bude,
ta madubi ya harereta yace "inada Allahn misirun sanin shagon kenan,
kafin Husnah ta bashi amsa Badar tayi saurin cewa " *Kura plaza* bai sake magana ba ya dauki hanyar Yakubu gawon way..


Yana saukesu ya bawa Husna dubu shidda yace "bani da enough ku kara,
kinsan nima sammin akeyi babu aikin yi,
dariya tayi tace aiki kam zaka samu yaya, kaima kasani, lokaci ne, dariya yayi ya wuce yana dagawa Nadeeyah hannu...




Wayarshi ya dauko a inda ya ajiyeta, yana bude ta kiran *Haidar Galadanci* ya shigo..

Dauka yayi yana dariya yace "Head Boy how far, ya kake,
daga daya bangaren Haidar yace "fine kyari, kana ina ne?
Taka birki yayi da karfi saboda mai mashin din da shigo mishi, tsakii yaja yace "ina gurin Leventis zanje waff road any probs?
Kwantar da murya yayi yace "Kyari naga bebs din story dinka, plss farar fa,
kanwarka ce?,
nasan Husna, ban dai gane farar bane,
dariya sosai Musaddiq yayi yace "kanwata ce Galadanci,
kafin ya karashe maganar yaji kiran Hilal ya shigo wayarshi a karo na uku,
hakuri ya bashi ya katse wayar dan ya dauki ta Hilal, kafin ya dauka ma ta katse,
duba missed calls yayi sunfi hamsin,
Hilal kadai talatin da uku yayi mishi,
sai sauran daga abokanshi,
kafin ya kira Hilal wayarshi ta shigo,
bai jira jin kalmar Hello ba saboda baya cikin nutsuwa da hankalinshi yace "dis is madness Kyari,
in banda rashin hankali ya zaka sanya hoton yarinyar nan a ig,
a story is understandable, but ig is very bad, duk inda ka zaga su arewa cuties nd co hotonta ne ke trending,
ya zakayi exposing dinta haka, wat is the need of all dis,
kuma baka ma duba kayan jikinta ba kawai ka tashi ka sata a social media,
idon mazan duniya su gama ganeta,
am very angry with u wallahi,
tunda ya fara masifar musaddiq yayi parking, saida ya gama zazzaga masifar yace "ka gama?

Tsaki Hilal yayi yace "ban gama ba, ka hau kaga banzayen comments din da akeyi maka,
na rokeka ka hau ka cire hotunan nan, cikin fada musaddiq yace "Bazan cire ba,
nace bazan cire ba,
hoton ta ita kadai nasaka,
au su sauran matan da suke saka hotonsu ba mata bane,
a fusace Hilal yace "ba irin su bace kyari,
ka kasa fahimtar ba irin matan da za'a dinga exposing bace,
yawo kalmar ta dingayi cikin kwakwalwar musaddiq yace
"wat do u mean, kana nufin bata kai matsayin da zata hau instagram ba,
ko kuwa tana da makusar da--- katse shi Hilal yayi yana share zufar da ta addabashi tun ganin hotunan da comments din abokan musaddiq yace "bazaka gane ba Kyari,
taushi yayi da muryarshi ya cigaba da cewa "rayuwarta zaka duba, marainiya ce, a yanzu gatanta shine ilimi,
wannan gayun ba nata bane, ilimin shine zai zamo gatanta gaba da baya,
yanzu wannan hoton baka san abubuwan da zai janyo mata ba,
samari zasu fara kawo mata hari, daga nan shikenan zasu zo su--- runtse idonshi yayi kafin ya furta kalman *aureta*, at end of the day kuma rayuwarta zata kare a bauta,
wasu kuma will come su yaudareta, wasu su lalata ta,
plss Musaddiq ka cire hoton nan,

cike da gamsuwa Musaddiq yace "very true, kamar kasan yanzu *Galadanci* ya kirani akanta and lots more, gara da ka fahimtar dani,
bari inyi maza in cire...



Safa da marwah ya dinga yi a cikin dakinshi,
pencil din da yake zane dashi yayi dagaga a bakinshi saboda tauna,
hoton ya sake kallo kashi na ba adadi yace "ya Allah ka cire idon duk wani namiji akan hoton nan,
yana cikin haka yaji karar notification din story a ig, *Husnah_kyari is live on instagram* da sauri ya hau,
yana budewa ya zauna dabass, *what is dis, ya ilahi!!
Ya fadi yana rike kanshi,
video Husna tayi musu da kai a bude,
gashin Nadeeyah ya sakko har baya,
a juye take tana parking din kanta, bata san Husna na mata video ba,
tsaki yaja sannan ya lalubi number wayarta, a zuciyarshi yace "kasheshi suke so suyi,


"My Personal person ta fadi da karfi,
bai amsa ba yace "tarbiyyar musulmi ne daura video babu dankwali,
come on je ki cire shi,
dariya tayi tace "done my PP, yanzu zan cire,
ajiyar zuciya yayi yace "hope kuna nan lafiya,
amsawa tayi da cewa lafiya kalau kowa yake,
"Good yace hade da cewa ku kula sosai fa,
kunsan samarin yanzu basu da kirki,
is hardly su soku tsakani da Allah, ku kama kanku ku daina kwalliya kuyi focusing akan karatunku kinji,
gyada kai tayi tace "in shaa Allah my pp,
murmushin jindadi yayi yace "bani Nadeeyah,
saida yaji kunya da ya fada,
cire wayar yayi a kunnenshi ya kalleta hade da jin haushin kanshi,
to me zaice mata?
, sansanyar muryata yaji tana fadin "Assalamu alaikum,
"kara wayar yayi a kunnenshi yace "Alaiki salam, ya kk
, lafiya lau ina wuni ta fadi darare,
lafiya lau,
kinada abubuwa a gabanki kike kwalliya harda wani possing ayi hoto ko?,
murya na rawa tace "a'a yau ne kawai,
kuma munje saloon ne,
dadi yaji har cikin ranshi yace "to ya zama na karshe,
karatunki yanzu shi kadai zaki sa a gaba,
ko powder ki daina shafawa,
u are very ok a haka,
ki daure kiyi karatu sosai ki zama independent woman kinji ko?
Gyada kanta tayi kamar tana gabanshi tace "in shaa Allah zan kiyaye,
"yauwa kanwata take care ya fadi hade da kashe wayar ba tare da ya barta ta bashi amsa ba.......



Tun dare Daddy ya kira principal din makarantar,
da yake suna ganin girmanshi shiyasa basuyi rejecting ba suka ce gobe a zo da ita a mata interview,
godiya yayi mishi sukayi sallama, a waya ya kira Musaddiq yace gobe ya shirya ya kaisu school yayi mata registration,
amsawa yayi yace "Allah ya kaimu Daddy...




Kallo ne ya koma kan su Husna lokacin da suka fito a cikin motar, jar jallabiya Husna ta zabowa Nadeeya tace ta saka, saboda tayi bagu a makaranta,
ai kuwa sun kawo kallo,
har a registrar office duk staff din da ya shigo sai ya kalli Nadeeyah,
bayan an gama mata komai suka mata interview,
dakyar ta wuce saboda karatunsu yayi mata tsauri,
Ss3 Art 1 suka kaita saboda Art take a makarantar da ta baro..

Sallama Musaddiq yayi musu ya wuce yana jaddada musu muhimmacin karatu,
commerce class Husna take,
saida taja ta suka je class dinsu kafin teacher ya shigo,

zagayesu akayi ana tambayar Husna sunan sistern ta,
murmushi tayi kanta yayi girma tace "She is my cousin,
Nadeeyah Adam,
wow nice name suka hada baki suka fadi, *Jameelah Aja* ce tace "a sit dina zata zauna,
nan fa class din ya kaure kowa na a gurinshi zata zauna harda mazan class din,
Dariya sosai Husna tayi tace "to a Art take,
tsaki sukayi sukace 1 or 2, one ofcourse Salmah Habeeb ta fadi hade da cewa "wai halan uncle Kamal zabar kyawawa yakeyi ya kaisu art da kanshi badan suna so ba,
dariya duka class din suka kece dashi suka ce very true,
duk taron kyawawa ne a art,
halan gani yayi duk sunfi dacewa da art gidan da babu Maths,

Hango Economics teachernsu sukayi kowa ya nemi gurin zama ya nutsu,
hannunta Husna taja suka hau sama inda class dinsu yake, daukar excuse tayi gurin Uncle Tahir literature teacher tace
"new comer ce sir,
uncle Kamal yace a kawota nan class din, kuma yace a bata special treatment,
hararta yayi cikin slangs turancin shi yace go to your class,
da sauri ta fita tana dariya,

kallon Nadeeyah yayi yace "welcome, what is your Name?
Gyara baki tayi cike da kunyar kallon da yan ajin suke mata tace "Nadeeyah Adam from Fgc malali, "Good ya fadi yana kare mata kallo,
seat din Sabrinah ya kalla yaga ita kadaice bata barin kowa ya zauna,
nuni yayi mata da sit din yace "go and sit down der,
bata rai Sabrinah tayi fuska da alamar shagwaba tace "sir,
Hararta yayi ya cigaba da abin da yakeyi,
tana zama tace "sannu,
ko kallonta Sabrinah bata yi ba tace ciwo nakeyi?
Nadeeyah bata sake kulata ba ta maida hankalinta kan allo...





*Gombe state university*

9:34am
Monday 17th july,




Assalamu alaikum..

Waigowa gungun samarin sukayi suka amsa da "wa alaikum salam hade da mika mashi hannu suka gaisa,
dan Allah ina ne Acadamic planning? Hafeez ya tambaya yana gyara jakarshi,
kwatance suka mishi yayi musu godiya ya koma motarshi,
hanyar da suka nuna mishi yabi, yana zuwa gurin yaga sunan a manne,
fitowa yayi da takardunshi ya karasa kofar shiga,
layin students ya gani suna turereniya suna mika takardu, wani ya samu a gurin yace "dan Allah ina ne office din Director academic planing,
nuna mishi office din yayi ya juya ya kutsa cikin layin,

Da sallama ya shiga ya tarar da secertary dinshi,
bayan sun gaisa ya tambayeshi ko lafiya,
takardu ya mika mishi yace "nazo registration din D.E ne,
karbar takardun yayi ya duba yace
"kaje waje daga lungu zaka ga wani office ka tambayi ina Hajiya farida, ka bata,
amsan takardun yayi hade da yi mishi godiya,
yana kokarin fita daga office din yaji an murda kofar wani office dake kusa da kofar fita,
dan saurayi ne ya fito fari kyakykyawa,
kallonshi yayi ya miko mishi hannu suka gaisa,
kallon sani Hafeez yayi mishi, tunanin inda ya sanshi ya shiga yi,

"Kai Jamal, ka dauki key din motar ne,
waigowa sukayi tare da Hafeez yace "yes Papy, kai fa ka miko min,
a wannan karan ba kallan sani Hafeez yayi wa dattijon ba,
kallon kamannin da yayi da mukusancin shi yayi mishi,
Allah mai halitta,
tabbas badan wannan fari bane tass babu abinda zai hanashi cewa shi bane......




Mrs Tijjani Shattimah......
[11/03 4:41 PM] Aysha Kura: •• *ZUMUNCINMU A YAU* •• 3⃣4⃣
By *Aysha Ya'u kurah*





Har kasa Hafiz ya tsuguna ya gaida dattijon,
bai kalli inda yake ba ya amsa yana magana secretary dinshi, Mikewa Hafeez yayi har lokacin idonshi nakan dattijon,
waigowar da zaiyi idanuwansu suka sarkafu cikin na juna,
nan take wani abu ya tsarga a jikin dattijon,
bai dauke idonshi akan Hafeez ba ya karaso kusa dashi yace "your face looks familiar,
wani level kake?,
cikin girmamawa Hafeez yace "yau na fara zuwa,
nazo registration ne, "Good, ya sunanka and wane course? dattijon ya tambaya har lokacin bai fasa kallon Hafeez yana nazarin inda yasanshi ba, "sunana Hafeez Adam, daga kaduna, computer science ne sir!
kauda tunanin inda yasanshi yayi dan ya kasa tunowa,
shi dai yasan yaron ya shiga ranshi daga ganin farko,
kuma a dan fisge idonshi na yanayi da Jamal,
kafadunshi ya dafa yace "All the best, Allah yasa ka fara a sa'a, Ameen.. Hafeez ya fadi ya bishi da kallo har ya fita daga office din....




Rashin nutsuwar da bai samu ba saboda registration shiyasa bai koma gurin directorn ba,
saida yayi sati uku ya samu nutsuwa har ya fara shiga lectures, a sannan ne ya fara tunanin konawa gurin mutumin dan jin ko yana da wani dan uwa, kamannin sunyi matukar yawa, badan tsufa da haske ba, babu abinda zai hanashi cewa su ba yan biyu bane,
saidai wannan ya fishi yarinta, da haske da kuma ilimi...


Yana gama cin abinci a cafeteria ya wuce masallaci yayi sallah, yana idarwa ya kama hanyar Academic planing,
meeting ya samu suna yi sai ya fita harabar gurin dan ya jirasu, saida yayi jiran awa 3 basu gama ba sannan ne ya hakura ya tafi gida,
zuwa academic planing ya zamewa Hafeez kullum,
wata rana har yaje sau biyu duk ba sa'a,
ko ace suna meeting ko kuma ace yana office din VC..


Ranar friday karfe 11 suke da lectures din Maths method,
tun tara na safe ya shiga school ya wuce office din,
zama yayi a gurin yana jiran ganin ta inda zai bullo,
daga can nesa ya hangoshi yana tafiya sauri sauri secretary dinshi yana binshi a baya da jaka,
mikewa Hafeez yayi ya iso gurinshi ya tsugana ya gaishe shi,
dafa kanshi yayi hade da mishi alama da ya dago,
sannan ya amsa, yace "malam Hafeez har ka gama settling ko?
Cike da mamakin rike sunanshi da yayi yace "eh ranka ya dade, kullum sai nazo bana cika samun ganinka,
tafiya ya fara yi yace "Allah sarki, schedules din nawa ne are very tight, muje in baka card dina kazo gida ka sameni......



*Kaduna*

Cikin ikon Allah Nadeeyah ta fara sabawa da yan ajinsu mata,
bata saki jiki dasu a farko ba saboda gudun wulakancin masu kudi,
da taga kowa na shige mata sai ta fara sakin jiki dasu musamman *Haifa* da *Amal* su biyun nan su suka zama kawayenta,
tun da suka fahimci Sabrinah na jin haushin shigowar Nadeeyah cikinsu sai suka dauke Nadeeya a sit dinta suka maida ita gabansu,
duk jan ajin Sabrinah saboda ganin tana da kyau ta saukeshi saboda ganin yanzu duk yan ajin sun raja'a akan Nadeeyah....



" *Badariyyah Kyari* sisternki tana da kyau sosai,
Rukky Mama ta cabe da cewar bari kedai Aliya,
in muna tsaye a assembly kallonta kawai nakeyi,
na rasa cikin jinsin da ta fito, fatarta kadai abar kallo ce,
uwa uba yatsun hannu,
kamar sun sokawa Badariyya Mashi tayi saurin cewa "ba sister na bace dalla,
she is an orphan, kawota gidanmu akayi dan ta dinga tayamu aiki,
u knw Daddy is very generous, kawai yaga tunda mate dinmu ce why nt ya sata a school tunda dama ss3 zata,
she is our helper kun gane ko!!

Kallonta Rukky tayi tace "kaii amma tayi sa'a, ga kyau, gashi ta dace gidan ruko,
wallahi in tana wucewa gaban staff room malamai har leke sukeyi,
uncle Tahir ne kadai bai wannan saboda class dinshi,
shi duk yadda ake koda sabrinah bata gabanshi,
shiyasa wannan ma bata d'ad'ashi ba,
gajiya Badar tayi da jin maganganu akan Nadeeyah tayi saurin mikewa ta wuce hade da ja musu tsaki...
bayanta suka bi da sauri saboda duk yan koranta ne.....




Tsaye yake gaban class yana kallonsu daya bayan daya,
cikin harcen turanci yace "Ba tambayarku nakeyi ba,
kun shirya ma presentation and drama?,
groups biyu suka mike suka ce sun shirya,
sauran kuwa sukayi kwala kwala da ido,
group 3 and group 6 meye topics dinku, ya tambaya fuska a murtuke, "*PLAGIARISM* "Khalifa ya fadi hade da mika mishi printed papers din da suka hada,
kallon dayan group din yayi yace and you?
Cike da rawar jiki Sabrinah tace *DRAMA, FICTION AND IMITATION*,
hannu ya mika ya karbi nasu takardar sannan ya kalli sauran yan class din yace "Kowa yasan dis is your first CA test,
to yanzu saboda kun nuna you are not serious na maida shi first nd second and is over 40 no attendance marks,
yana kaiwa nan yace duk class din su tafi school Hall su jirashi yazo su fara presenting,
cike da tsoro sauran suka fara ihu suna fadin sorry sir,
wasu a cikinsu kuma suka tafi cafe dan shirya nasu ko baiyi yawan na sauran ba....



Karfe goma daidai group 3 suka fara presenting nasu,
cike da kwarewar turancinsu mai dadi na butters suka gabatar dashi,
saida suka gama tsaff kowa ya tafa musu harda observers,
Shirye shiryen na dramar group 6 suka fara,
saida suka kammala komai sannan suka fara presenting, definition din drama sukayi sai dan short fiction story of Beggars da illolin da irin wulakancin da mabarata ke fuskanta,
a karshen labarin ne suka ce "Yanzu zamu yi muku drama akan labarin da muka gabatar...



Nan jikin Nadeeyah ya fara rawa saboda tsoron turancinta ba irin nasu bane,

Sabrinah da Ishaq sune masu kudi,
sai Nadeeyah, Haifa, da Abdulhameed sune maroka,

Nadeeyah itace Makauniya tana rike da sanda,
sai Haifah kurmah,
Abdulhameed kuma gurgu,
cike da burgewa suka fara dramar akan stage,
da fari Nadeeya taji tsoro,
sai da Haifa tayi mata wuzuwuzu ta tunasar da ita marks din da zasu samu sannan ta saki jikinta,
da sanda take shafa kasa tana fadin "a taimaki almajira saboda Allah da Annabi,
cikin harshen turanci take magana ta karasa daidai inda Sabrinah da Ishaq suke zaune kan dadduma suna shan fruits ta tsaya,
"Hajiya a taimaka min da sadaka saboda Allah..
tsaki sabrinah tayi hade da daukar ayaba tace "Mabaratan nan sunyi yawa a kasar nan honey,
kuma mostly hausawa, kallon Nadeeyah tayi hade da watsa mata bawon ayaba ta cigaba da cewa "ku ko kunya ma bakwaji, da wannan barar da kukeyi ba gara kuje ku zauna a gida ku jira ranar mutuwarku ba tunda baku da amfani,
katseta Ishaq yayi yana murmushi ya daga malunmalun ya fito da dari biyar yace "sweetie,
in ba irinsu ta yaya zamu samu kudin,
Allah na bamu kudin ne dan ya turo su suzo su amsa,
yana mika mata kudin Abdulhameed da Haifa suka fito daga mabanbantan guri suna kokawar kwacewa,
ana haka har suka tura Nadeeyah jikin Sabrinah kamar yadda suka tsara a labarin,
Sabrinah na ganin haka ta mike hade da manta drama sukeyi ta tura Nadeeyah da iya karfinta,

ihu Nadeeya ta saki saboda kafarta daya ta sauka akan stage ta rinjayi dayar,
ga tsakanin stage da kasa akwai yar tazara,
runtse idonta tayi ta sadakar ko kafarta ta karye ko kuma ta samu mummunan rauni,

Bude idonta tayi da sauri saboda jinta hannun mutum da kuma jin bugun zuciyarshi alamar tsoro,

kallonshi tayi ta hango manyan idanuwanshi cikin farin glass sunki daukewa a kanta,
ajiyar zuciya tayi ta fara kokarin raba jikinta da nashi,
sai a sannan ya sauketa ya koma gurin da yake tsaye har lokacin zuciyarshi bugawa takeyi,

Husnah da Haifa ne sukayi saurin isowa gurinta suna mata sannu hade da hawa kan stage din inda Abdulhameed da Ishaq suke ta ma Sabrinah masifa,
itama jikinta yayi sanyi dan bata taba tunanin Nadeeyah zata fadi kasa ba,
hakuri Nadeeyah tabawa su Ishaq tace "mistake aka samu kun sani, kuma faduwar is part of the drama dan a nuna yadda mabaraci ke wulakanta,
in Allah yayi muna da rabon marks zamu samu koda 30 ne,

kalaman Nadeeyah sunyi matukar yin tasiri a zuciyar sabrinah,
nan take taji ta shiga ranta,
a zuciyarta tana auno da ita akayi wa haka da sai ta kusa yi ma mutum illa,
nan dai sauran groups din suka fara presenting nasu..

Kallonsu

Please Login or Register in order to submit comment