Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata lokaci ba aka soma gabatar da bikin gunin sha'awa wanda ya tsaida dukk wasu ayyukan garin ko ina celebration akeyi..



Bayan an gama naďin *Yareemah Magajin Agadez* masu rawa nayi, fulani masu dukan jikinsu sunayi, anata cashewa tun da aka gama har washe gari..




Hafeez da Nadeeyah da duk wani makusancinsu sunyi kukan tunawa da iyayensu wadanda basu tsinci komai a cikin duniyar nan ba sai tarin wahalhalu,

Allah baya barin wani rai dan wani ran yaji daďi,
babu mamaki tanadin da yayi musu a lahira na musamman ne.....





Duk sauran yan uwa sun koma nigeria,
Nadeeyah da Hafeez da iyalanshi ne kaďai suke zaune a agadez saboda yanzu rabin zaman Hafeez zai dawo nan agadez din ne,

Kayattacen gida Sarki ya bashi shi da iyalinshi da masu yi musu hidima ta ko ina,
Sannan a kullum sai an koyar dashi yanayin tsarin mulkin sarauta wanda sam bai sanshi ba dan bai taba tunanin ya gajeta ba....




A ranar da suka cika sati uku suka fara shirin komawa gida saboda karatun su Nour sannan Hafeez zaiyi resigning daga aikinshi,

Tsaraba kuwa sun shata kamar zasu kwashe kayan garin su tafi dashi,
wasu abubuwan ma basu san amfaninsu ba haka akayi mota guda wacce ta rigasu yin gaba su kuma suka wuce airport....
[02/07 9:55 am] Anty aisha ya'u kura: ************
*CONTINUATION*



Mun samu toka way dari biyu hajiya,
Ladi mai musu ta fadi cike da girmamawa...

Dariya Anty Saude tayi suka tafa da Mummy tace

"To Mummyn yara kinji mun samu Toka way ďari biyu,
za'a kara ne ko kuwa za'a barsu haka ne..

Cike da mutuntawa Mummy tace "Ai sai yadda kika ce Antyn yara, ni kinga kitchen din nan yayi min zafi,
duk yadda kikayi daidai ne...


Kallon Ladi tayi wacce ke murmushin turancinta tace
"Kice wa Laminu yaje ya shirya almajiran sai a fara rabo,
in ma bai isa ba sai a haďa musu da kuďi wani satin sai a kara hannu..
Jirani mu tafi Mummyn yara ta karashe tana mai mikewa hade da gyara hijab dinta...


Sadakar da ta zamewa gidan sabo duk jumma'a tun bayan tarewarsu wanda hakan ya kara musu haďin kai saboda kowa zata fito daga sashinta ta zo general kitchen ayi aikin tare...



Bayan an idar da Sallah jumm'a kuma kowacce sai ta cabo ado su iso parlon mai gidan inda za'aci abinci ayi wasa da dariya..


Yau ma kamar Kullum bayan sun gama cin abincin tare da Raudha da Nadeeyah sai Junior..

Sallamar Radiya da mijinta Shamsu wanda Allah ya taimaketa aka maida auren yana dawowa ita ta sanya dukkaninsu washe baki,
yaranta da na Fatima na shigowa suka nufi gurin junior wanda yake game da ipad dinshi..

Su kuwa iyayen gaishesu sukayi sannan suka zauna aka cigaba da hira dasu gunin ban sha'awa.

Suna gab da tafiya Raliya ta shigo itama aka ďan taba hira da ita sannan suka rakasu har gurin mota...

Shamsu na shiga mota ya kalli Raudha yace

"Abbati ya shigo gari,
jiya mukayi waya dashi yace in shaa Allah next week zaije katsina daga can zaizo nan..

Dariya tayi tace
"Kai dai Abban Raees kullum haka kake cemin dan hankalina ya kwanta,
karka damu in lokaci yayi zaizo da kafarshi,


"Allah ba wasa ba,
a gabana sukayi magana.
Radiya ta faďa mata cike da jaddadawa,


"To Allah yasa cewar Raliya wacce har ta fara farin cikin jin hakan....






********


*What comes easy won’t last long, and what lasts long won’t come easy..*



Cike da kosawa ya dubi agogon hannunshi a karo na uku bayan farkawarshi daga bacci,
gani yakeyi jirgin ma kamar tafiyar hawainiya yakeyi,
ga wani sururun sanyi da ya turnuke cikinshi,
sake dukunkuna yayi cikin bakar suwaitar dake jikinshi yaja hular kanshi ya rufe kunnuwanshi.
Murya can kasa yace

"Zubair na gaji walhy,
sau uku fa bacci na daukata ina farkawa amma har yanzu bamu sauka ba.


Dariya Zubair yayi cikin muryar bacci yace
"To sarkin raki,
ko zakaje ka karbi control din a hannunka ne,
suma ai zasu fimu san su sauka su huta,
dan Allah karka sake tashina nafison ina farkawa in jini a matakalar jirgi..


Mtsww...

Musaddiq yaja tsaki haďe da juyar da kanshi yana kallon duniyar sama ta window..


Duk wannan kaguwar yayi ta ne saboda kosawar da yayi ya isa gurin ahalinshi waďanda a kullum yake jinsu cikin farin ciki idan suna waya,
ga kuma matarshi wacce tun dawowarta basuyi maganar minti biyu kwakwara da ita ba,
ko waya akeyi dashi a gidan bata sanya kanta koda kuwa Anty saude ta matsa, tana karbar wayar take kasheta saita dade da wayar kamar tana yin wayar dashi kafin ta kawo mata..

A yanzu dai ya gama hakuri, domin koma meye takeson yi mishi na horo tayi,
bazai iya jurar wani daga gareta ba,
tunanin kiran Maleekah ya faďo mishi,
nan fa kaguwarshi ta karu ya kosa jirgin ya sauka ya kirata dan yasan ita kaďai ce zata taimaka mishi....




Karfe huďu na asuba jirgin su ya sauka a airport ďin Lagos.

Ajiyar zuciya ya saki haďe da mika yace
"Dan da kyar,
tattara kayanshi yayi yana adduoi a fili yana hararar Zubair dake faďin


"Kai kaga dan da kyar,
kaidai kosawarka ce tayi yawa, amma jirgi ya sauka at the right time,
tazarar minti uku zuwa hudu ne..


"Ashe dai kasan sunyi latti. Musaddiq ya faďi yana rataya jakarshi,


"Muje dallah can,
nasan matsalarka,
yanzu zan kira Nadeeyah ince mata ta shirya komawa Agadez garin buzaye..



"Haaaa..
Musaddiq yace cike da dariya,
"karka fasa,
ai ko bangon duniya ta tafi binta zanyi,
ďan bakin ciki..

Nan fa suka bi layin sauka suna barkwanci suna dariya abokan tafiyarsu na tayasu....





Jirgin shida na safe ya hau daga lagos zuwa Abuja,
ko gida bai je ba dan yasan yanzu duk wasu gyare gyaren da ya bari ayi kafin tafiyar ta taso mishi an gamashi,
yasan Faidah bazatayi mishi wasa ba domin ta iya gyaran gida sosai...



Jirginsu na sauka yayi hamdalah ya ďauki drop har gida,
a hanya ya kira Hilal suka ďan taba hirarsu sannan ya bawa Maleekah wacce ke tsokanarshi yana daďa jaddada mata tayi gaggawar gyara abun da ta bata tun farko, dan duk influence dinta ne, ita ta zuga Nadeeyah,
saida ta gama tsokanarshi sannan ta tabbatar mishi da cewa zaiga canji....





Babu wanda yasan da isowarshi garin domin safiyar tayi yawa..

Malam Ali ya kira gab da shiga unguwar, shi yayi mishi iso har cikin gidan bangaren Mummy..


Da Raudha ya fara cin karo ta fito dan shiga kitchen,
da murnarta ta tareshi tana dariya tace

"Saukar yaushe?

A gajiye ya saki karamar jakar hannunshi kan manyan yace "Yanzu Anty, Ina kwana?
Lafiya kalau muje in kaika bangarenku sai ka huta dan duk basu tashi ba, nima fitinar ďanka ta tada ni..


Dariya yayi yace
"Haba Anty ko me zaiyi yanzu ai dole ayi hakuri ya fanshe rashin mu na tsawon lokaci,

"Ay ka dawo sai ku karata can,, iyawa rigimar nan sai Taheer shi da ya fara,


"Nima zan iya fiye da Taheer..
ya bata amsa yana yaken da tasan na kishi ne..

Kai Little kar dai kishi ne,? ta karashe tana mishi kallon gefen ido,

"Allah ya kyauta,
ai Taheer ďan uwa ne,
ya wuce ayi kishi dashi.. ya faďi yana mai danne wani ďan halittar kishi da ya motsa mishi..


Hira ta shiga yi mishi har suka isa sashen shi,
a gyare yake tass saidai kura da ya danyi,
windows din ta buďe tace "Bari in kira Najume ya sake gyara maka..


"Noo barshi kawai, baiyi wani kura ba,
i will manage..




Tana fita ya faďa bayi yayi wanka ya fito ya sanya jallabiya dake cikin karamar jakar hannunshi..
janyo manyan akwatinan gefenshi yayi dan a bakin kofa wadanda suka kawo suka barshi..


Saida ya tabbatar ya gama kimtsawa sannan ya kakkabe gadon da yasha gyara da zanin gado mai taushi,
kwanciya yayi yana lumshe ido sanyin Acn na ratsashi,
bacci ne mai dadi yayi gaba dashi wanda ya dade bai samu ba saboda wahalar aikin da suka je koya.....




Karfe tara da wani abu suka gama haďa miyar waina a kitchen ďin Anty Saude,
suna gamawa Nadeeyah ta fara shirin damawa Daddy kunun gyaďa,
Tana kammalawa ta zuba a flask, tana shirin ajiye kwanon damun Anty Raudha ta miko mata wani flask ďin tace ta zuba mata a ciki,

Ba musu ta zuba mata suka karashe farfesun zabin da ke wuta wanda yasha kayan kamshi..

A cikin coolers masu kyau suka kammala kayan har Wainar da aka gama tuyanta a general kitchen...



Har kun gama?
Anty Saude ta tambaya tana buďe coolers din..

"Eh mun gama Anty,
ga na bakonki nan na gama haďawa Raudha ta faďi tana kashe mata ido,


"Auhoo to madallah,
Allah yayi muku albarka,
bari inje gurin Daddynku in dawo sai in kai mishi,
ko Raudha zaki taimaka min?


"Kashh Anty..
walhy Junior na can yana jirana ban mishi wanka ba,
in dai zai jira bakon to dan sai na gama ma ďana hidima,


Da sauri cikin nuna alamar ba daďi Nadeeyah tace
"Gani Anty,
haba ai bako bazai jira abinci ba saidai abinci ya jirashi,
bari in wanke hannu in kai mishi..


'A'a je kiyi wanka ma,
nasan bai tashi ba,
kinga in kika kai sai ki dawo a karya baki ďaya ko Anty?


Kwarai Raudha kinyi gaskiya..
Dan Allah Nadeeyah ki haďasu cikin tray mai kyau, in sun miki nauyi Sai in kira Ladi ta tayaki..

"Ba nauyi Anty bari inyi wankan da sauri sai inkai ta karashe tana fita daga kitchen ďin..


Dariya sukayi Anty Saude tace

"In shaa Allahu bazan biye ta Daddynku ba,
wai shi dole bai so a matsa ma Nadeeyah akan Musaddiq,
gobe ko jibi zasu tattara su koma can gidansu suma suyi rayuwar aurensu kamar kowa,
kema akwai surprise din da zan miki, sai gobe zaki sani,

Dariya Raudha tayi ta kwashi kayan abincinsu tace
"Allah ya kaimu Anty,
kuma Allah ya biyaki da Aljanna..


Ya biyamu baki ďaya yar kwarai, nagode da yadda kuka daukeni tamkar uwa....


A haka suka jera abincin a gurin da zasu karya kowa na yabon ďan uwanshi....





A gaggauce tayi wanka dan kar bakon Anty Saude ya farka ya gaji da jiran abinci,
Mai da powder kaďai ta shafa sai ta zizara bakin kwalli a cikin idonta,
doguwar riga ta sanya ta ďaura hijab da ďan turare mai sanyin kamshi..

Tana gamawa ta nufi kitchen ta haďa kayan cikin babban tray,
a kofar kitchen ta iske Anty Saude wacce ta kureta da ido..

"Anty yana Bq ko?

Gyaďa kai tayi tace

"Ke dai ba ruwanki da tunanin mijinki ko?

Kauda fuskarta tayi gabanta yayi matukar faďuwa,

*Tunani*..
faďinshi ma bata baki ne,
Allah ya sani tana tsananin begen son ganinshi,
amma ya zatayi, tana jin kunyarsu,
ga Daddy da a ganinshi har yanzu tana cikin alhinin son Taheer ne shi ya sa yace kar wanda ya matsa mata,
a barta hankalinta ya gama kwanciya..



Dafa kafaďunta da taji anyi ne yasata dawowa daga wata duniyar da ta shiga,


"Kin bar mijinki shi kaďai,
bakya tunanin halin da yake ciki,
aure daraja ne dashi Nadeeyah, iyayenshi sun fifita farin cikinki akan ďansu,

Dan Allah Nadeeyah in mijinki ya dawo ki bishi kuje kar wani mummunan abu ya sake giftawa a tsakaninku wanda zai janyo muku rabuwa...

Anty Saude na ďiga aya Raudha ta karbe da cewa


"To jiya nan Faidah ta kirani wai wasu mata yaran ogansu Haneefah da Halisa suna can suna faďa akan shi,
har gidanta suke zuwa,
yanzu in sukayi nasara ya auri ďaya daga cikinsu ai kinga aurensu zai raurawa,
yadda ta karashe maganar kamar da gaske yasa Anty saude gimtse dariyarta..


Ita kuwa Nadeeyah da sauri tayi gaba har tana yin tuntube da kofar fita daga corridor din da zai sadata da waje,
wasu zafafan kwalla ne suka taru a idonta tayi saurin shanyesu sukayi mata tsaye a makoshinta,
babu abin da imaginations dinta bai kawo mata ba,
har ta hango ma ya gama zabar ďaya daga cikinsu,
kara sauri tayi dan taje ta ajiye abincin ta dawo ta kunna wayarta da ta daďe a kashe bisa ga umurnin yar uwarta Maleekah wacce a yanzu take ji kamar cutarta tayi...




Tun kafin ta karasa take duban hanya ko zata ga daya daga cikin almajirai ma'aikata gidan ta haďasu da abincin su kai,
saidai har ta kai kofar bq din bata ga kowa a cikinsu ba...


Tana taba kofar parlon taji wani daďin faďuwar gaban,

"Shi kenan wani abu na shirin faruwa da ita,
nan fa tayi rau rau da ido tana kokarin dasashe kukan da makoshinta ya kasa rikewa.

Dakyar ta iya daurewa ta murďa kofar ta shiga,
kamshin parlon shi ya sanyata sakin ajiyar zuciya hade da dan samun nutsuwa a cikin ranta,
wannan kamshin tayi mugun sabo dashi domin yana matukar sanyata nutsuwa..

Bayan rabuwa da ma'abocinshi takan tsinci kanta cikin tashin hankali a duk lokacin data gitta wani mai irin kamshin...


Ajiye abincin tayi a center table din dake parlon ta juya ta fara tafiya da niyyar fita,
tana taba murfin kofar taji karar kofar ďakin haďe da faďin
"Hey.....


Tsaye tayi faďuwar gabanta ya karu matuka,

Hamma taji yayi haďe da mika da salati yana faďin

"Wacece??

Samm kafarta ta gaza yin koda taku ďaya ne bare har ta fita daga ďakin da gaggawa kamar yadda take niyya,
jin takun karasowarshi ne yasata runtse idanuwanta hawayen dake kwance a idonta ya fara saukowa da sauri sauri...



Ganin taki motsawa kuma taki waigowa jikinshi ya bashi ita ce,
kara sauri yayi dan ya isa gareta kafin ta fita,
yasan tsaff zata iya...


Yana gab da isa kuwa ta fara kokarin buďe kofar domin tuno kalaman Raudha,
samn ta rasa da wani ido zata kalleshi,
bazata iya controlling kanta ba, kuma bazata taba barinshi ya gano lagonta ba..


Tana murďa kofar yayi saurin rike hannun haďe da tura kofar, bazai taba yarda ta sake kubuce mishi ba,
tayi matukar wahalar da rayuwarshi wanda har hakan ya kusa zama nakasu ga zuciyarshi...




Zuciyoyi aka bari kawai da aikinsu domin dukkaninsu gangar jikinsu ya gaza motsawa sai shi da ya zuba mata idon da ruwa ya taru yana jin kamar mafarki yakeyi,
yana ganin ya tsallake siraďin rayuwa ďan da dakyar...


A hankali ya dago fuskarta wacce ruwan hawaye ya jikata,
samm taki yarda ta buďe idonta sai kukan da take karayi mai ďan sauti..

Jiki na rawa ya shiga share mata hawaye da harcenshi nashi wanda ya gaza rikesu na ďiga yana gauraya da nata..


Wani irin kuka ta fashe dashi haďe da shigewa jikinshi ta kankameshi...

*Sab'anin masoya Hutu ne a garesu wanda ke daďa tsuma zuciyoyinsu su gane muhimmancin juna*...


Sun kai minti uku suna kukan zuci hade da na idaniya,
sai daga bisani Musaddiq ya ďauketa cikin kirjinshi ya nufi cikin daki yana mai bata hakuri da tattausan kalamai a cikin kunnuwanta..




A hankali ya kwantota jikinshi ya sake kankameta yana aika mata sakwanni masu wayar fassaruwa a gareta,

Ita kanta ta manta a duniyar da take bare tayi tunanin wasu sun ga zuwanta gurinshi,
gani takeyi kamar su biyu Allah ya halittawa duniyar baki ďayanta..

Ajiyar Zuciya kaďai suke saki a haka har bacci mai daďi ya ďauketa,
yana ganin tayi bacci ya kwantar da ita sai a sannan tunanin cire mata hijab yazo ranshi,

A hankali ya zare mata sannan ya maida ita cikin jikinshi yana yi mata wani irin kallo kamar zai haďiyeta,
ji yakeyi kamar in ta bar gefenshi bazai sake ganinta ba sai an dauki wasu lokutan,
kaii gaskiya bazai iya ba,
gobe zai dauki iyalinshi su tafi can kusa dashi..
Da wannan tunanin ya soma shafa lallausan gashin kanta har shima ya koma baccin.....




*****

Karin hularshi ta gyara ta ďaura mishi a kai ta bashi amsar tambayarshi cike da son yaji kunya ya tattara yaran su tafi gidan aurensu..


"Diyarka tana can gurin mijinta, yazo gari kuma a wani dalili zata zauna ta karya damu,
ai ni bana fata ta dawo yanzu,
zan faďa mata kace tayi zamanta har ranar da zai koma....



"Ya salam ya faďi yana dariya, "wallahi Saude sai a barki,
to yaushe mara kunyar yazo gidan har yasan ya kirata taje?


"A'a itace dai mara kunyar da ta je gurinshi,
shi ko cikin gidan ma baizo ba,
to yarinya ta gaji tana son kasancewa da mijinta,
amma surukai sun hana suna ta yi mata hannunka mai sanda..


Matsowa tayi cikin jikinshi tana kakkabe mishi riga haďe da rage murya,
yanzu kai dan Allah zaka iya yin kwana biyu ba tare da matanka ba?



Tsaki yayi mai haďe da dariya dan yasan sarai so takeyi sai yaji kunya,


"Saude goben nan Nadeeyah zata koma gidan ta,
duk wasu shirye shiryen da zakuyi kuyi su a yau,
nasan halinki kina iya bani kunya gaban 'ya'yana...


Dariya sosai ta kyalkyale dashi haďe da sumbatar kuncinshi tace "Kasan fa shiyasa nake mutuwar sonka,
bana ma tunanin yin minti ďaya ba tare da kai ba..

Kalaman kauna shima ya mayar mata wanda yasata rungumeshi tana zubo mishi nata salon da ke kara mishi kaunarta a cikin ranshi.....





Anty Raudha da kanta ta kai abincin rana sashin Musaddiq gurin daya da rabi, har lokacin basu tashi ba..,

A inda ta samu abincin safe nan ta ajiye na ranan tana dariyar plan ďinsu da Anty Saude yayi aiki,
komawa tayi tasake dauko juice ta sanya cikin fridge ďin parlon sannan ta rufe kofar ta wuce cikin gida dan zasu fita yi ma Nadeeyah yan siyayyar da zata tafi dasu....




Shi ya fara farkawa ya sake sanyawa baccinta ido yana mai godiya da Allah da ya sake bashi damar samunta a karo na biyu..


Saida yayi minti biyar da tashi sannan ta soma buďe idonta daga nannauyan bacci mai cike da mafarkai masu daďi..


Sauke idanuwan da tayi cikin nashi ya sanyata saurin runtsesu tana tunano abin da ya kawota ďakin..


Cike da fargaba ta sake buďe idon, har lokacin bai ďauke nashi a kanta ba,
hannuwanta tasa ta rufe fuskarta haďe da yunkurin mikewa..

Maida ita yayi da kanshi yaje saitin kunnenta yace
"Ina zaki?
Kin biyo mijinki kuma zaki gudu ki barni..


"Ni ba gurinka nazo ba,
aiko ni akayi,
dan Allah ka kyaleni kar a zargeni,


Shafa fuskarshi akan kuncinta yayi yana dariya cikin nishaďi yace
"Waye zai zargeki,
kowa yasan kina gurin mijinki, kuma yanzu karfe biyu har da minti biyar,
kinga yanzu kowa yasan zaki amince ki daina wahalar dani tunda sun lura so na yayi miki yawa..


Ture kanshi tayi..
tayi saurin mikewa zaune tace

"Ni bana sonka,
kaje can gurin masu sonka,
suyi ta faďa akanka bai dameni ba..


Wow ashe kin ji Labarin su Rumaisah su Lantana, suna da yawa fa,
ni kuma gashi nan ana bani wahala.... ya karashe a shagwabe...


Turo baki tayi idonta ya ciko da ruwa tace
"Rumaisah, Haneefah, Halisa, suna ma da yawa ko...
ta faďi a can kasan makoshi....


"Dariya yayi wacce da gani kasan ta jin daďi ce ya sake matsowa kusa da ita yace

"To ya zanyi,
ko ban kula su ba suna zuwa office,
suna yawan damuna,
dan Allah ki tayani korarsu...


Kuka sosai ta fashe dashi wanda kishi yayi sanadiyyar fitowarsu haďe da ayyano abubuwa da dama...


"Rungumeta yayi yana faďin "Wasa nake miki, Sorry plss,
babu face ďin da wata zata min magana bare har ta samu damar mallakar amsata har ta kiyasta wani abu a ranta,
Ke kaďai ke dani Nadeeyah,
babu wacce zata iya shiga rayuwata,
i just can't imagine loving sm1 else,
i love yhu alot, nd i will love u until i breath my last breath...


"Ba wani ai Anty Raudha ta faďa min.. ta faďi tana kokarin kwace kanta daga rikon da yayi mata...




"Wasa take miki.. ya faďi a kasalance dan ya fara rasa hakurinshi,
itama tasan bani da kowa,
ita kaďai ce tasan na dawo kuma ta turo min ke saboda tasan nasha wahalar rashinki,
Plss don't live me.. plss..


Sai a lokacin taji nutsuwa na saukar mata tayi lamoo a jikinshi tana ajiyar zuciya...


Daurewa yayi ya ďagata dan suje suci abinci daga nan sai ya shiga cikin gidan gaisawa da iyayenshi da danshi da yake mararin gani....




Kunun kaďai Nadeeyah tasha sai romon farfesu saboda bazata iya cin Biskin da sukayi da rana da rana ba..



Saida ta tabbatar ya cika cikinshi sannan ta mike ta sanya hijab dinta ta fara kokarin barin ďakin dan bazata yarda su jera tare ba...


Riketa yayi har saida ya gama abun da yakeyi dan a cewarshi gara a gansu tare dan kowa yasan tana son komawa gidan mijinta. haka nan ba dan taso ba ta tsaya har ya gama suka fita suka nufi sashin Mummy....




Tariyar Nadeeyah ta tabbata a washe gari saboda Daddy yace bazasu kara kwana mishi a gida ba,
su shirya tafiya komin dare tunda ba'a kafa ko mota zasu tafi ba..
kuma babu wanda zai yi musu rakiya tunda dama ba yau sukayi auren ba..

Hakan ba karamin dadi yayi wa Musaddiq da su Mummy ba,
dan dama tun jiya sun gama shirinsu...




Jirgin karfe ďaya na rana zasu bi dan haka suka tafi kaisu airport tun karfe 12 saboda gudun latti
duk yadda sukaso tafiya da Junior Anty Saude taki dan a cewarta bazasu taba bashi kula ba a yanzu da suke amarci,
haka nan suka hakura suka tafi Nadeeyah na cike da kewarsu kamar bazata barsu ba.....






Nadeeyah tayi mamakin ganin yadda tsarin gidan nata ya koma kamar ba'a kasar nan ba...
Furnitures da curtains din kaďai sun isa su sanya mutum gigita.
wai itace Nadeeyah mai dinka atamfar dubu daya a matsayin kayan Sallah a wannan katafaren gidan haďe da tsadaddun kaya..

Alhamdulillahi ala kulli halin hakan ta faďi tana mai kewaye ko ina na gidan...


Tana shiga kicin taji sallamar Su Faidah wacce ko a mafarki bazata mance muryar ba..
Saida gabanta ya faďi kafin daga baya ta daidaita kanta ta fito ta gansu gurin dining ita da yaranta suna jera abinci,

Zubair kuma yana tsaye a bayansu yana kwala kiran Musaddiq cikin shakiyanci,


Gyara gyalenta tayi tace "Sannunku da zuwa,
da sauri Faidah ta juyo suka haďa ido kowanne da murmushi akan fuskarshi.

Ya salam Faida ta faďi tana mai karasowa da ita,
Nadeeyah kece haka,
kinga yadda kika zama classy diva...


Dariya Nadeeyah tayi ta kamo hannun yaran haďe da gaida Zubair..


Cike da fara'a ya amsa yana mata congrat haďe da yi musu adduar zaman lafiya..


Zama sukayi Faida na bawa Nadeeyah hakuri hade da yi mata shakiyanci akan wahalar da Musaddiq din yasha da bata nan..


Sakkowar Musaddiq ne ya sake tado wata hirar wacce ta kaisu har magrib,
a tare suka ci abincin da suka kawo dan mai yawa ne sannan sukayi sallama suka nufi gidansu.....




A masallaci yayi sallar isha'i sannan ya tsaya wani gurin saida nama ya siyo hade da juice da wasu abubuwan da zasu bukata da safe..



Ko da ya shiga gidan waya samesu sunayi su uku suka hada conference Hinad, Husna sai Nadeeyah,
hira sosai sukeyi suna ma Husna shakiyanci suna faďin tuba muke ranki shi daďe....


Shigowar wayar Anty Saude ne ya katse wayar ta dauka taji muryar gudan jininta suka dinga hira harda Musaddiq ďin.


Karbar wayar Anty Saude tayi tace
"Kai rabani da iyayen nan naka, maza jeka gurin Daddy yana kiranka..


"Ohh Anty ki barshi plss, Musaddiq ya faďi kamar yaro karami,


"Allah ya shiryeka wallahi,
a halinka kaďan Junior ya rage,
ni sai da safenku...


Dariya sukayi dukkaninsu sannan Nadeeyah ta ajiye wayar tana mishi sannu da zuwa...





Dan Allah ka barni da wannan kallon,
ni duk sai in jini wani iri,
Yaushe zakaje Agadez?,

Mamma Sharee ta kira tanata faďa wai maji daďin Agadez yaki zuwa gaishesu..

"Au har sun naďa min sarauta,
karki damu so nakeyi sai mun samu sabon sarki mai sunan Baba sai muje mu gaishesu..

Rufe fuskarta tayi tana dariya tace
"Wai dan Allah yaushe zaka girma?


"Sai ranar da na samu me cemin Daddy,
kina dai jin Babana Twinny yake cemin..

Dariya tayi har tana kyakyatawa tace
"Rainon uncle ne,
sai ka samo rainonka,
anan zan gane wanda yafi tabara da wanda yafi iya raino...




Daukarta yayi cakk yace
"A yau kuwa zan samo me cemin Daddy..



Dan Allah kayi hakuri ka saukeni..
ko sauraronta baiyi ba

Please Login or Register in order to submit comment