Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take jininsu ya fara tsiri izuwa sararin
samaniya suka fara yin wani irin ihu, wadda yasa wani baƙin hayaƙi ya fara fita daga
cikin bakinsu.
Da ƙyar da siɗin goshi yarima Marganu ya kashe su gaba ɗaya, a lokacin da suka yi
masa muggan raunika guda bakwai masu zurfi. A iya rayuwar Marganu bai taɓa ganin
bala'i irin na wannan rana ba, yana gama kashe su ya sulale ƙasa sumamme. Bai
farfaɗo ba sai bayan rabin sa'a a lokacin da wata irin iska mai sanƴin gaske ta fara
kaɗawa, yarima Marganu yana buɗe idanunsa yaji wani mugun zogi da raɗaɗi na shiga
jikinsa tamkar ana zuƙar jinin jikinsa. Duk da tsananin juriya da jarumta irinta tasa sai da
idanunsa suka ciko da ƙwalla, cikin tsananin ƙarfin hali ya fiddo wani magani daga cikin
jakar guzurinsa mai kama da daskararren mai ya dinga shafawa akan waɗannan raunika
nasa, take jini ya daina zubowa daga cikinsu. Marganu ya sake fiddo wani garin magani
ya baɗawa raunikan, saboda tsananin zogi da raɗaɗin da ya shige shi sai da ya sake
sumewa. Haka dai yarima Marganu ya ci gaba da yiwa kansa magani har tsahon sa'a
biyu, sannan ya daina jin wannan zogi sosai, amma koda ya miƙe da niyyar komawa
inda ya baro aljani Gulzab sai ya kasa tafiya sakamakon wani lafcecen rauni dake kan
cinƴarsa.
Nan fa hankalinsa ya ɗugunzuma ya fara tunanin abinda ya kamata yayi, sai da ya sake
shafe daƙiƙu masu yawan gaske sannan dabara ta sake faɗo masa. Kai tsaye yaje
gindin wata ƙaramar bishiya, ya karyo rassan bishiyar guda biyu masu gwafa. Ya fara
tafiya a hankali yana dogara waɗannan sanduna guda biyu ya tunkari inda ya baro aljani
Gulzab.
Aljani Gulzab na kishingiɗe a jikin bishiya yana gyangyaɗi domin ya gama ayyanawa a
ransa cewa, babu yadda za'ayi wannan yaron ya sami nasara a wannan daji domin
kafun yazo manƴansa sunzo. Kwatsam! Ba zato sai ya hango alamun mutum tafe yana
dogara sanduna tamkar gurgu, aljani Gulzab ya miƙe zumbur ya ƙurawa mutumin ido, a
hankali yayi ta matsowa har aljani Gulzab yaga yarima Marganu ya bayyana. Cikin
tsananin mamaki ya dubi yarima Marganu ya ce, "Ya kai wannan ɗan sarki ya ya akayi ka
kashe aljanun dake tsaron hanƴar nan?" Koda jin wannan tambaya sai yarima Marganu
ya harari aljani Gulzab ya ce, "Tambaya ma kake akan yadda na kashe su? Ba ka ga
yadda suka jikkata ni ba?" Aljani Gulzab ya dubi raunikan dake jikin yarima Marganu sai
ya sake cika da tsananin mamaki yadda yarima Marganu ya iya jure waɗannan raunika
har ma yake iya tafiya da kansa. "Tabbas jure irin waɗannan raunika sai jarumin da ya
amsa sunansa, na jinjina maka bisa wannan gagarumar jarumtaka da kayi." Yarima
Marganu ya yi murmushi ya ce, "Tukunna dai, bari muje dajin Shiwazu da tsaunin
Barzasa idan na tsallake su sai kayi min jinjina." Yana gama faɗin haka ya ɗare bayan
aljani Gulzab, suka kama hanƴa.
Yarima Marganu ya sunkuyo da kansa ƙasa yaga yadda gawarwakin waɗannan fararen
aljanu ta cika ko'ina a cikin dajin, ya yi mamakin yadda aka yi shi ɗaya jal ya gama dasu
gaba ɗaya. Ya jinjina kai ya ce a ransa, "Ko ya ya sharrin ɗaya hanƴar dake kudu zai
kasance? Na tabbata sai ta ninka wannar sau goma, idan kuwa haka ne lallai duk
jarumin da zai ratsa ta wannan hanƴa akwai aiki a gabansa." Yana cikin wannan zancen
zuci ya juya wurin da Hajriya ke kwance yaga raunikan jikinta sun daina zubar da jini,
wasunsu ma har sun fara bushewa al'amarin da ya bashi mamaki kenan. Ya tambayi
aljani Gulzab, "Shin akwai maganin da ka sanƴawa wannar matar ne a raunikanta?"
Aljani Gulzab ya ce, "Kwarai ma kuwa sai dai maganin irin namu na aljanu ne, yana
warkar ciwukan bil'adama da wuri. Amma idan bai karɓi jinin mutum yana yi masa illa,
shiyasa naji tsoron sanar da kai kada a samu matsala." Yarima Marganu ya ce, "Kawo
na saka akan waɗannan raunikan nawa, tun da ya karɓi jinin wannar matar nima zai
karɓi jinina." Aljani Gulzab ya sa hannu a cikin aljihun rigarsa ya fiddo wani garin magani
ya baiwa yarima Marganu. Marganu ya karɓi maganin ya sanƴa akan raunin dake kan
cinƴarsa, bisa mamaki sai yaga jini ya daina zuba, rauni ya haɗe. Ya dubi aljani Gulzab
ya ce, "Godiya a gareka ya kai wannan aljani tabbas ka bani babbar gudunmuwa a
wannan tafiya tawa." Nan take yarima Marganu ya bi duk sauran raunikan dake jikinsa
ya barbaɗe su da wannan garin magani, ai kuwa take suka haɗe. Aljani Gulzab ya dubi
yarima Marganu magana, "Abinda yasa waɗannan raunika naka suke warkewa farat
daya shi ne, aljanu ne suka yi maka raunikan. Wannan magani kuma domin sharrin
aljanu irin waɗannan aka yi sa, ka san mahaifina likita ne." Yarima Marganu yayi
murmushi ya ce, "Jinjina ga shugaban likitocin aljanu na duniya."
Haka dai suka ci gaba da tafiya suna hira har tsahon sa'a goma sha huɗu sannan dare
ya riskesu bisa dole suka yada zango a bakin Shiwazu, cikin wani tafkeken daji.
***Ruhin Jarumtaka!
*
Babi na 11: *Alwashin sarauniya Rauziyya (1)*
*
*
✍️✍️ Umar Sangaru ✍️✍️
*
Kashe gari tunda duƙu-duƙun safiya yarima Marganu ya farka, ya ɗauki takobinsa ya kunna kai izuwa cikin dajin Shiwazu. A wannan lokaci raunikan jikinsa sun bushe gaba ɗayansu wasu har sun kame ma saura sauƙi kawai, ko riga babu a jikinsa daga shi sai wani dogon wando na fatar damisa, yana tafiya a cikin dajin yana nazarin kowanne irin motsi.
Dajin Shiwazu ƙaton daji ne wanda waɗansu irin manƴan duwatsu suka cika ta ko'ina, kana shigowa cikin dajin zaka fara jin rugugin gudun ruwa dake ƙwaranya daga saman duwatsu. Dajin a cike yake da manƴa-manƴan koguna da koramu, sai dai kaga murgujejen kifi ya yiwo sama daga ƙarƙashin kogi sannan ya sake afkawa cikin ruwa. Yarima Marganu ya ci gaba da tafiya a hankali a cikin wannan daji yana kaucewa ƙananun koguna da koramai ba tare da ya shiga cikinsu ba, yana cikin tafiya har ya iso bakin wani tafkeken kogi wanda ya tare hanƴa gaba daya. A bakin wannan kogi an ajiye wata ƙaramar kwale-kwale da aka ɗaure a jikin wani itace, yarima Marganu ya ƙarasa bakin kogin gurin wannan kwale-kwale. Ya ƙarewa kogin nan kallo yaga ai duk faɗin dajin babu wacce ta kaita girma, daga inda yake tsaye yana hango wani abu mai kama da akwati tsaye cikin iska acan tsakiyar wannan kogin. Yarima Marganu ya mayar da takobinsa cikin kufe sannan ya shiga cikin wannan kwale-kwale ya kwance igiyar da ta ɗaure kwale-kwalen sannan ya fara tuƙata ya nufi tsakiyar kogin inda yake hango wannan abu mai kama da akwati, tafiya yake yana dube-dube ta gefe da gefensa don tabbatar da tsaro. Koda ya shafe daƙiƙa ɗari biyu da ashirin yana tafiya, ba tare da ya ci karo mugun abu ba, sai ya saki ransa hankalinsa ya kwanta don gani yake da wuya a sami mugun abu a cikin wannan kogi saboda amincinta.
Kwatsam! Sai ya ga ruwa ya fara jan kwale-kwalensa da gudu ya nufi cikin wani ƙaton rami dake tsakiyar kogin, yarima Marganu yayi iya yinsa wajen ganin ya tsayar da kwale-kwalen amma ya kasa bisa dole ya daka tsalle, ya faɗa cikin kogin nan ya fara iyo. Yana ji yana gani kwale-kwalen nan taje ta faɗa cikin wannan rami, abinda ya gani na gaba shine yayi matukar ɗugunzuma masa hankali. Ba wani abu ya gani ba face rufewar wannan rami, ashe ba rami bane wani ƙaton kifi ne ya buɗe bakinsa yake shan ruwa. Yarima Marganu ya haɗe gira ya fara iyo a cikin kogi, ya nufi inda yake hango gaɓar kogin. Sai da ya shafe rabin sa'a yana iyo amma sai yaga tamkar a guri ɗaya yake, al'amarin da ya ɗugunzuma hankalinsa kenan domin ya fara gajiya.
Ba zato! Sai ya ga ruwan dake gabansa ya fara juyawa tamkar ana gauraya shi, wani irin murgujejen kada ya taso saman ruwan yana ƙoƙarin haɗiye shi. Yarima Marganu ya zaro takobinsa ya kaiwa wannan ƙaton kada sara a wuya, takobin ta haɗu da wuyan kadan ta haifar da wata ƙara tamkar an sari dutsen wuta. Al'amarin da ya sake ɗugunzuma hankalin yarima Marganu kenan a karo na biyu, ya tabbatar da cewa wannan kada sihirtacce ne. Koda fahimtar hakan sai ya juya da baya ya fara iyo da sauri domin ya gujewa kadan, ai kuwa sai wannan kada ya saka shi a gaba suka fara tsere a cikin wannan kogi da gudu. Yarima Marganu ya wanzu yana mai yin iyo da sauri kuma yana zille-zille domin ya gujewa hare-haren wannan kada, shikuma kadan ya wanzu yana mai wangame ƙaton bakinsa domin ya haɗiye Marganu gaba ɗaya. Nan fa suka tashi hankalin wannan kogi, ruwa ya soma yin tsiri yana haustinewa. Ba'a jima ana wannan gumurzu ba yarima Marganu ya soma gajiya saboda bai iya iyo sosai a cikin ruwa ba, shi kuma wannan kada jinsa yake tamkar a cikin gidansa, gudu kawai yake iya son ransa. Lamarin da ya sake ɗugunzuma hankalin yarima Marganu kenan, ya waigo da kansa baya yaga wannan kada ya wangame ƙaton bakinsa tamkar zai haɗiye dukkanin abinda ke cikin kogin. Marganu ya yi nutso izuwa ƙarƙashin kogin domin hakan ne kawai zai ƙwace shi daga haɗiyar kadan, yana nutsewa ƙarƙashin kogin yayi arba da waɗansu kifaye kyawawan gaske waɗanda suka burge shi matuƙa. Adadin kifayen zai kusan ɗari da doriya, suna da launin jiki kala uku, ja, kore da shuɗi.
Kai tsaye yarima Marganu ya tunkari inda waɗannan kifaye suke domin ya kama su, ya manta da batun wannan kada gaba ɗaya. Kwatsam! Sai yaga waɗannan kifaye gaba ɗayansu sun tarwatse, suka saka shi a tsakiya wato suka kewaye shi. Cikin matsanancin gudu suka taho gaba ɗayansu, suna wangame ƙananun bakunansu zasu cije shi. Yarima Marganu ya tabbatar da cewa lallai indai ya kuskura ya bari waɗannan kifaye suka riske shi to tashi ta ƙare, tuni ya gane manufarsu wato so suke suyi abincin kalaci da shi. Koda fuskantar sai ya sake yin ninkaya ya taso saman kogin nan, amma dukda haka sai yaji wasu daga cikin kifayen sun cije shi a ƙafarsa wani irin azababben zogi ya shige shi. Yarima Marganu ya sake yin arba da wannan akwati dake tsaye a cikin a tsakiyar kogin ta sake bayyana, a lokacin da irin wannan murgujejen kada guda uku suka sake tasowa suka saka shi a tsakiya.
Koda Marganu yaga haka sai ransa ya ɓaci, ya fara iyo ya tunkari ɗaya daga cikin kadojin nan. A wannan lokaci a hankali yake iyon saboda yadda ya gaji, waɗannan kadoji guda uku kawai sai suka zuba masa idanu suna ganin abinda zaiyi. Marganu na zuwa daidai inda ɗayansu ke tsaye, ya zaro takobinsa cikin baƙin zafin nama da shammace ya cakata a tsakiyar idon kadan. Take jini mai yawa yayi feshi daga cikin idon tamkar teku ta ɓalle, kadan yayi wani uban ruri sannan ya birkice ya fara wutsil-wutsil a cikin ruwa. Koda ƴan uwansa suka ga abinda ya faru sai suka wangame bakunansu a tare suka kawowa yarima Marganu haɗiya cikin ɓakin zafin nama ya sake nutsewa a cikin ruwan nan, take kowanne daga cikin kadojin ya ciji ɗan uwansa a kafaɗa, jini yayi feshi su ma suka wutsil-wutsil suna gudu a cikin ruwan.
Yarima Marganu na nutsewa ya sake yin arba da gungun waɗansu irin kifaye masu yawan gaske a tare a guri ɗaya suna ta iyo, kifaye ne masu dogon baki mai tsini kamar tsinin mashi. Koda suka yi arba da yarima Marganu sai suka taho da gudu suna saita shi da wannan dogon baki nasu mai kama da mashi, yarima Marganu baisan sa'adda ya juya da baya ba ya fara tsala wani azababben gudu wanda shi kansa sai da ya cika da tsananin mamakin yadda yake wannan gudu. Nan fa suka kasa mugun tsere, koda wasa yarima Marganu bai yi yunƙurin tasowa daga ƙarƙashin wannan ruwa domin gani yake yana tasowa zaiyi karo da waɗannan manƴan kadoji guda uku. A duk lokacin da yarima Marganu ya waigo bayansa sai yaga tazarar dake tsakaninsa da waɗannan kifaye bata wuce taku biyar ba, nan take hankalinsa yayi mugun tashi domin ya tabbatar da cewa yana cikin TSAKA MAI WUYA. Kafun a sake ɓata wani lokaci tuni waɗannan kifaye sun fara cimmasa, suna ƙoƙarin caka masa wannan dogon baki nasu. Marganu na ta iyo kawai yaji wani mugun zogi ya ratsa cikin cinƴarsa tamkar da mashi aka tsire shi, dukda cewa a ƙarƙashin ruwa amma sai da ya kwarara uban ihu, ihun nasa bai yi ƙara ba sai ma ruwa da ya cika masa baki.
A daidai lokacin ne kuma yaji numfashinsa ya fara ɗaukewa sakamakon tsahon lokacin da ya ɗauka a ƙarƙashin ruwa, ya juyo ya dubi inda ke masa zogin nan sai yaga ɗaya daga cikin kifayen ne, ya soke shi da dogon bakinsa. Nan take Marganu ya fusata saboda ganin wai yau ace jarumi kamarsa yana gudun wasu halittu da basu kasance manƴan masu cutarwa ba, cikin tsananin ƙunar rai ya zaro takobinsa ya tsaya cak, a inda yake. Koda ganin haka sai kifayen nan suka ƙara azama wajen ganin sun isa inda yake tsaye, suna isowa yarima Marganu ya kai musu wani wawan sara a tsakiyarsu, da yake a wuri ɗaya suke cure take wannan takobi ta raba fiye da rabinsu gida biyu. Sauran na ganin haka suka tarwatse kowannensu ya kama gabansa, Marganu yayi murmushi ya fara iyo ya taso saman ruwan, nan ma sai yaga gawar waɗannan kadoji na ta yawo akan ruwa har ungulu ta fara tsatstsagarsu.
Kai tsaye ya ƙarasa tsakiyar kogin inda wannan akwati take, ya kai hannu ya cafeta sannan ya budeta inda yayi arba da wata ƴar ƙaramar takarda mai ɗauke da rubutu na ɗalasimab tsafi. Marganu ya sa hannayensa biyu ya yage wannan takarda sannan ya ci gaba da iyo har iso gaɓar kogin nan ta inda ya shigo, yana fita daga kogin ya gagara ɗaga kafarsa guda domin yayi tafiya. Koda ya kalli ƙafar sai hankalinsa ya ɗugunzuma domin a kumbure take suntum sakamakon sukarta da wannan kifi yayi, Marganu yayi iya yinsa domin ya ɗaga ƙafar amma ya kasa. Bisa dole ya ja cikinsa yaje gindin wata ƙaramar bishiya ya karyo reshe guda ya ɗinga dogara shi yana tafiya, ya nufi inda aljani Gulzab.
Aljani Gulzab na ganinsa ya sake cika da tsananin mamakin yadda ya kuɓuta daga sharrin dajin Shiwazu. "Kaga ba surutu ya kawoni ba, maza ka ɗauke ni mu ƙarisa tsaunin Barzasa domin na karya sihirin dake hana aljanu wucewa ta cikin wannan daji." Inji yarima Marganu. Aljani Gulzab ya sake ranƙwafawa yarima Marganu ya ɗare bayansa suka ci gaba da tafiya, aljani Gulzab ya sake baiwa yarima Marganu irin wannan magani wanda ya bashi daga farko.
Sai da suka shafe tafiyar kwana biyu da rabi sannan suka fara hango wani ƙaton tsauni acan nesa, aljani Gulzab ya saki fuka-fukinsa ya dira ƙasa a tsakiyar wani daji wanda ba shi da nisa sosai zuwa wannan tsauni. Yarima Marganu ya yi sallama da aljani Gulzab sannan ya falfala da azababben gudu ya tasar ma wannan tsauni, zuciyarsa cike da farin ciki domin ganin irin nasarorin da yake samu a wannan tafiya. Koda ya shafe sa'a ɗaya da rabi yana wannan gudu sai ya iso gindin wannan tsauni. Tsauni ne dogo wanda ba'a hango ƙarshensa daga ƙasa, a jikin tsaunin akwai ƙananan bishiyoyi da ciyawi wato ba zallar dutse bane akwai ƙasa a jikinsa.
Yarima Marganu ya tsaya a gindin tsaunin yana tunanin yadda zai hau kansa, inda ace yana tare da aljani Gulzab da sai ya buɗe fuka-fukinsa ya hawar dashi saman tsaunin, amma ya tuno cewa ai babu yadda za'ayi Gulzab ya shigo cikin wannan daji ba tare da ya ƙone ba. Nan dai ya sake ɓata wata rabin sa'ar yana tunani sannan wata dabara ta faɗo masa, kawai ya juya da baya ya falfala da gudu ya nufi inda ya baro aljani Gulzab. Koda aljani Gulzab ya gan shi sai ya ce lafiya ya dawo? Yarima Marganu ya yi farat ya ce, "Shin akwai wani makami a wajenka ne? Takobi ko mashi?" Aljani Gulzab ya ce, "Kwarai ma kuwa." Ya zaro wata sharɓeɓiyar takobi dake ɗaure a gadon bayansa ya miƙowa ita Marganu.
Marganu na karɓar takobin ya juya da baya ya sake falfalawa da azababben gudu ya koma gindin tsaunin, yana zuwa ya daka wawan tsalle ya caka ɗaya daga cikin takubban a jikin tsaunin. Kafin ya zareta ya sake caka ɗayar, haka ya ci gaba da caka waɗannan takubba yana hawa kan tsaunin a hankali. Sai da ya shafe sa'a biyu cir sannan ya iso ƙarshe tsaunin, a lokacin da hannayensa suka ɗura ruwa gaba ɗayansu sakamakon yawan damƙar ƙarfen takobi. Yana hawowa saman tsaunin ya nemi gindin wata bishiya ya zauna ya huta, ya fiddo salkar ruwansa ya sha.
A can gabansa ne ya hango katangar wani ƙaton birni mai tsawon gaske, ba katangar bane ta bashi tsoro ba, dakarun da ya gani suna shigewa cikin birnin sune suka razana shi. Waɗansu irin mutane ne gajeru masu ƙira ta ƙarfi, suna riƙe da makaman yaƙi masu mugun haɗari. Suna gama shigewa cikin birnin aka mayar da ƙofa aka rufe, yarima Marganu na gama ganin haka ya miƙe tsaye ya ruga da gudu ya nufi wannan ƙofa ta garin arnan daji. Rashin sani yafi dare duhu.
Lokacin da yarima Marganu ya kusa isowa bakin wannan ƙofa sai ya yi tuntuɓe da wani dutse, take yayi sama ya faɗo a bakin ƙofar. Kafin ya miƙe tsaye yaga an jeho masa wata raga daga sama ta kanannaɗe shi gaba ɗaya, Marganu ya yi, ya yi ya tsitstsinka ragar amma ya kasa saboda da zallar ƙarfe aka yi ta. Irin waɗannan gajerun dakaru ya gani suna ta firfitowa daga maɓoyarsu, kowannensu na riƙe da kaifaffen gatari irin wanda ake fille kan shanu da shi. Dakarun suka kewaye ragar da ta kanannaɗe yarima Marganu, mutum goma daga cikinsu suka fiddo waɗansu irin sandunan duka, suka rufe yarima Marganu da duka. Ji kake tim, tim, tim tamkar ana bugun dawa, kafin a jima sun yiwa yarima Marganu lilis sun haɗa masa jini da majina. Ko'ina a jikinsa sai da ya kumbura saboda ƙarfin dukan da ya sha, idanuwansa sun kumbura sun yi ɓulu-ɓulu. Ƙasusuwan jikinsa sai amsawa suke tamkar zasu ɓaɓɓalle, bakinsa da hancinsa sai yoyon jini suke. Nan take yarima Marganu yaji nadama ta sake zuwa masa a karo na biyu bisa wannan sayar da rayuwarsa da yayi domin ya mallaki gimbiya Jaanu.
Nan take waɗannan arnan daji suka fiddo shi daga cikin wannan raga suka ɗaɗɗaure shi a jikin wani dogon itace, aka buɗe wannan ƙatuwar ƙofa suka kunna kai izuwa cikin birnin. Dukda cewa yarima Marganu ba'a cikin hayyacinsa yake ba, amma sai ya ɗinga yin arba da gine-ginen arnan dajin, ya rinƙa ganin yara da tsofaffi suna ta fitowa daga cikin gidajensu suna kallonsa. Al'amarin da ya sake ɗugunzuma hankalin Marganu kenan saboda ya fuskanci cewa gari ne guda na irin waɗannan arnan daji. Haka dai aka ci gaba da tafiya da shi a ɗaure a jikin itace tamkar dabbar da aka yanka, har suka iso fadar garin. Suna zuwa aka kwance yarima Marganu daga jikin wannan itace aka kaishi wurin wata shugabarsu dake zaune bisa karagar mulki. Koda wannan sarauniya taga dakarunta sun yi nasarar kamo abinda za'a yankawa gunki Barzasa sai ta cika da tsananin farin ciki, ta dubi dakarun ta ce, "Yau Talata, ku kai wannan fursuna izuwa cikin keji sai gobe da yamma zamu yankawa mai girma Barzasa jininsa." Dakarun suka sunkuyar da kansu ƙasa gami da dafe ƙirji alamun sunyi biyayya ga umarnin sarauniya, nan take mutum goma suka ɗauki yarima Marganu tamkar sun ɗau tsintsiya suka nufi wani ƙaton keji dake ajiye a gefen fadar. Suna zuwa suka wurga yarima Marganu cikin kejin tamkar sunyi jifa da shara.
Yarima Marganu ya faɗo ƙasa a cikin kejin a lokacin da yaji jikinsa nayi masa wani irin ciwo saboda ɗan karen dukan da yasha a hannun arnan dajin, nan fa yayi ta juye-juye a cikin kogon idanuwansa na gudun hawaye. Ko wahalar da yasha a hannun fararen aljanun nan ba tayi rabin wacce yake sha ba yanzu, yarima Marganu ya tuna duk fa wannan wahalar da yake sha akan mace yake shanta, macen da ba shi da tabbacin cewa zata karɓi soyayyarsa. "Na rantse da darajar mahaifina idan har bata amince dani ba, wannan karon sai na kasheta sannan na kashe kaina." Yarima Marganu ya faɗa a cikin wata irin murya ƙasa-ƙasa. Yarima Marganu ya ƙarewa ƙarafunan da aka yi wannan keji dasu kallo, sai yayi murmushi kawai don ya tabbatar da cewa zai iya ɓalla su. Ya dubi wajen kejin inda yayi arba da gungun dakaru a zube birjik suna ta tsaro, kowanne lokaci sai kallon cikin kejin suke suna ta muzurai. Yarima Marganu ya miƙe zaune daƙyar ya laluɓa inda jakar guzurinsa take, ai kuwa sai ya jita. Nan take ya cika da tsananin farin ciki ya fiddo wannan garin magani ya barbaɗa ko'ina da ina a jikinsa, wani sabon zogi da ya shige sai da ya sume. Bai farfaɗo ba daga wannan suma da yayi ba, sai da rana ta faɗi. Ya na buɗe idanunsa ya laluɓi inda takobinsa take amma bai ji taba, ya yi ajiyar numfashi sannan ya koma ya kwanta yana jira dare yayi.
Dare na soma rabawa yarima Marganu ya buɗe idanuwansa dama lamo yayi ba barci yake ba, yaje jikin ƙarafunan da aka yi kejin nan dasu yasa hannayensa biyu a tsakanin ƙarafun yana ƙoƙarin buɗa su. Nan fa jijiyoyin jikinsa suka kumbura suka yi burdin-burdin, idanuwansa suka kaɗa suka yi jawur, yaji tamkar za'a yayyaga shi bisa dole ya saki ƙarafunan kejin ya koma gefe guda yana haki. Sai da ya shafe rabin sa'a yana hutawa sannan ya dawo ya daɗa jarrabawa, a wannan karon sai ya ayyana a ransa ko mutuwa zaiyi sai ya buɗa waɗannan karafuna domin ya fita. Yana zuwa ya sake sanƴa hannayensa a tsakanin waɗannan ƙarafuna ya shiga ƙoƙarin buɗasu da ƙarfin tsiya, nan take jijiyoyin jikinsa suka sake kumbura suka yi burɗin-burɗin, fuskarsa ta fara gatsinewa, idanunsa suka yi jawur, sawayensa suka fara karkarwa. Daƙyar da siɗin goshi ya samu ya buɗa karafunan a lokacin da yaji tamkar ransa zai fita saboda tsabar wahala, ai kuwa yana buɗa ƙarafunan ya zube ƙasa wanwar yana ta haki. Koda ya miƙe zaune sai ya tofar da jini daga cikin bakinsa, ya sunkuyar da kansa ya huta sosai, sannan ya tashi ya karkata jikinsa ya fice daga cikin wannan keji ta tsakankanin ƙarafunan nan da ya buɗa.
***$RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 12: *Alwashin Sarauniya Rauziyya (2)*
*
*
Umar Sangaru
*
Lokacin da Marganu ya fito daga cikin wannan keji sai ya rakaɓe a cikin duhun keji yana
kallon yadda dakaru keta kaiwa da komowa ta harabar wurin, ya ƙarewa dakarun kallo
yaga sun kasance gajeru masu tsananin ƙarfi. Ɗaya daga cikin dakarun ya gani ya
tunkaro inda yake tsaye, a lokacin da ƙirjin Marganu ya fara dukan uku-uku saboda
tsananin razana, babban abinda yafi ɗaga masa hankali shi ne babu makami a
hannunsa. Badakaren ya ƙaraso ya wuce kai tsaye izuwa bakin keji yana haska cikinsa
da icen wuta dake hannunsa, bisa mamaki sai yaga kejin wayam babu kowa a ciki.
Al'amarin da ya bashi mamaki kenan kuma ya ɗaure masa kai, ya juyo da nufin ya
bayyananawa ƴan uwansa abinda ke faruwa kawai sai yaji an shaƙo shi ta baya, an
murɗe masa wuya aka jefar da gawarsa gefe guda. Ba wani bane ya aikata masa hakan
ba face Marganu. Cikin baƙin zafin nama Marganu ya kashe wutar jikin wannan itace
sannan ya sunkuya ya ɗauki takobin wannan badakare, ya sake laɓewa a gefe guda.
Har alfijir ta fara ketowa babu badakaren da ya sake zuwa inda Marganu ke tsaye, koda
Marganu yaga gari ya fara wayewa sai hankalinsa yayi mugun tashi domin ya tabbatar
da cewa indai gari ya waye sai

Please Login or Register in order to submit comment