Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan mutumi yayi da sarki Kuffuru." Wannan badakare ya
ɗago kai ya dubi Marganu ya ce, "Bayanan da muka karanto a cikin wannan wasiƙa
sunyi daidai da kai, don haka ka miƙo kanka." Badakaren ya koma kan dokinsa ya zauna.
Yarima Marganu ya fusata ya dakawa dakarun nan tsawa ya ce, "Ƙaryarku ta sha ƙarya
baku isa ku iya kamani ba, na rantse da kaifin takobina yau ɗinnan sai na tarwatsa ku."
Koda waɗannan dakaru suka ji kalaman Marganu sai suka fusata suka zazzaro kulaken
dukansu suka afka masa da yaƙi, aka garƙame da mugun yaƙi.
Yarima Marganu ya wanzu a tsakiyar dakarun yana ta kai musu sara da suka da
takobinsa, su kuma suka wanzu suna ta kawo masa duka da kulakensu. Ba'a shafe
lokaci mai tsaho ba, yarima Marganu ya fuskanci cewa waɗannan dakaru suna da
tsananin horon yaƙi wanda yafi nasa, tsananin zafin nama da juriyarsa ne kawai yake
ƙwatarsa.
A duk sa'adda suka kawo masa duka da kulkin dake hannunsu, da zarar yasa takobinsa
ya tare sai yaji tamkar ƙaton dutse aka kwaɗa masa. Kafin a jima kaifin takobinsa ta
fara dakushewa, lamarin da ya sake ɗugunzuma hankalinsa kenan. Yarima Marganu ya
taƙarƙare iya iyawarsa ya sari ƙirjin ɗaya daga cikin dakarun, take ƙirjin ya tsage jini mai
yawa yayi feshi. Badakaren ya kwarara uban ihu ya kaiwa Marganu wawan duka da
kulkinsa, Marganu ya kauce kulkin ya doki wani ƙaramin dutse dake gefe guda, take
dutsen ya tarwatse.
Sauran dakarun kuwa koda suka ga an sari ɗan-uwansu sai suka fusata, suka rufarwa
Marganu da duka gaba ɗayansu tamkar zasu cinƴe shi. Da yake sarkin yawa yafi sarkin
ƙarfi. Wannan karon suka fara samun nasarar dukan jikin Marganu da waɗannan kulake
nasu. Tuni hankalin yarima Marganu ya ɗugunzuma saboda a wannan karo sun hana shi
sakat. Kafin ya ankara wani sadauki ya gabza masa duka a wuya da kulkinsa saboda
ƙarfin dukan, yarima Marganu ya yi sama ya faɗo a sume. Waɗannan dakaru suka saka
sarƙoƙi suka ɗaɗɗaure shi gaba ɗaya, tun daga kansa har ƙafafuwansa a ɗaure suke.
Badakaren da yarima Marganu ya jiwa rauni akan ƙirji, yazo gaban Marganu ya watsa
masa ruwa, Marganu ya buɗe idanunsa ya tsinci kansa a ɗaure cikin sarƙoƙi. Yana shirin
yunƙurin tsitstsinka sarƙoƙi wannan badakare ya ɗaga kulkinsa ya yiwa Marganu wani
ƙwaƙwƙwaran duka a ka, take kan Marganu ya fashe jini ya fara zubowa yana wanke
masa fuska. Badakaren ya bushe da dariya ya sa hannunsa guda ya mangare Marganu
a wuya, take Marganu ya sake sumewa. Dakarun nan suka ɗauke shi bisa dawakansu
sannan suka juya suka nufi hanƴar da zata kaisu kurkukun mutuwa.
****Ruhin Jarumtaka!
*
Babi na 17: *Horo*
*
*
Umar Sangaru
*
Lokacin da sarkin ɓarayi Barban ya gama yiwa Aymanul Faris bayanai akan satar da
zasu je suyi a birnin Askandariyya sai Aymanul Faris ya tashi ya koma cikin wannan ɗaki
inda jaruma Riya ke kula da mahaifiyarsa, tun daga nesa ya hango jaruma Riya tana
baiwa mahaifiyar tasa abinci a baki, tana ci kaɗan-kaɗan. Wani irin hawaye mai nuna
tsantsar tausayi ya zubo daga cikin idanun Aymanul Faris ya gagara ƙarisawa inda
mahaifiyar tasa take, har jaruma Riya ta gama bata abinci sannan ta taso ta nufo inda
yake tsaye. Tana zuwa ta dube shi ta ce, "Lafiya ka tsaya anan?" Aymanul Faris ya goge
hawayen idanunsa ya ce, "Ba komai bane yasa kika ga na tsaya anan ina ta zubar da
hawaye face tausayin halin da mahaifiyata take ciki, tabbas duk wanda ya jefata cikin
wannan hali sai na hukunta shi. Sannan kuma ina so na baki haƙuri gami da sanar dake
cewa, ranar sha-tara ga watan Disamba zamuje birnin Askandariyya domin yin wani
gagarumin aiki, Barban ya ce min aikin yana da haɗari sosai. Don haka daga yau zan
soma ƙara baiwa kaina horon yaƙi, ki ci gaba da kula da mahaifiyata har izuwa lokacin
da zamu dawo daga wannan aiki." Jaruma Riya tayi murmushi mai taushi ta ce, "In dai
nice baka da damuwa. Mahaifiyarka mahaifiyata ce." Tabbas Aymanul Faris yaji daɗin
wannan kalami nata, bai san sa'adda ya sumbaci goshinta ba sannan ya wuce inda
mahaifiyarsa ke kwance, ya zauna a gefenta. Har wannan lokaci idanuwanta a rufe
suke, ya ɗora hannunsa akan hannunta, ya ce, "Sannu umma." Bisa mamaki sai yaga
tayi murmushi amma bata buɗe idanunta ba, wani farin ciki ya lulluɓe Aymanul Faris ya
sumbaci hannunta sannan ya fice daga cikin ɗakin. Jaruma Riya ta bishi da wani kallo
irin na ma'abota bege.
Aymanul Faris na fitowa daga cikin wannan ɗaki ya wuce kai tsaye izuwa wani ƙaton fili,
wanda aka cika da abubuwan motsa jiki da kuma kayan yaƙi. Waɗansu zabga-zabgan
takubba guda biyu Aymanul Faris ya ɗauka ya yi ta kaiwa iska sara da su, idan kaga
yadda Aymanul Faris ke wasa da waɗannan takubba sai ka cika da tsananin mamaki.
Yana cikin wasan ne yaga jaruma Riya ta shigo cikin wannan fili tana murmushi,
Aymanul Faris ya dubeta ya ce, "Meyasa kika biyoni nan?" Jaruma Riya ta taho inda yake
tsaye ta ɗauki wata zabgegiyar takobi ta dube shi ta ce, "Shin ka manta matsayina ne?
Ni ce fa ƴar sadauki Jarata mai bayar da horo kuma na gaje shi. Yanzu sai ka faɗa min
wanne kalan salon yaƙi kake so a koya maka?" Aymanul Faris ya yi murmushi ya ce,
"Tun da nake a rayuwata ban taɓa yin gumurzu da zaki ba, ina so ki koya min yadda ake
faɗa da zaki." Ba don komai ya faɗa mata haka ba, sai don yana so ya fara shirin yaƙi da
waɗannan dakaru masu siffa biyu da maigida Barban ya bashi labari, tun da ance rabin
jikinsu na zaki ne, rabi kuma na mutum. To tabbas zasu yi ƙarfi kamar zaki sannan
yanayin faɗansu zai iya kasancewa kamar na zaki ne.
"Shi zaki makaman faɗansa sune; fiƙaƙƙun haƙoransa, faratan hannunsa da kuma ƙarfin
ƙirjinsa. Mafi yawancin lokuta zaki tsalle yake ya tsirga akan mutum sannan ya turmushe
mutum a ƙasa daga nan sai ya kafa haƙoransa a wuyan mutum har mutum ya mutu.
Idan mutum yana so ya kaucewa hare-haren zaki dole ne mutum ya koyi tsalle mai nisan
gaske domin idan yaga zaki yayi tsalle zai faɗo kansa sai yayi tsalle ya faɗi a gefe guda,
sannan kuma dole ne mutum ya iya sarrafa takobi da kuma tale sawaye a ƙasa. Yadda
da zarar zaki yayi tsalle kafin ya tsirga akan mutum zai iya tale sawayensa yayi ƙasa
sannan yayi amfani da kaifin takobinsa ya farke tumbin zakin. Inaga idan ka koyi
waɗannan dabarun yaƙin zaka iya cin nasara akan zaki, amma meyasa kayi tambaya
akan zaki kaɗai?" Aymanul Faris ya yi murmushi ya ce, "Saboda maigida Barban ya ce
min dakarun dake tsaron abinda zamuje mu sato siffa biyu gare su - rabi zaki, rabi
mutum." Jaruma Riya ta cika da tsananin mamaki ta ce, "Siffa biyu fa kace?" Aymanul
Faris ya amsa mata da cewa, "Kwarai ma kuwa amma ance asalinsu waɗansu mayun
aljanu ne dake rayuwa bisa wani ƙaton tsauni." Jaruma Riya ta ce, "Tabɗijam. Yanzu dai
zo a fara baka horon ko?"
Aymanul Faris ya yi murmushi sannan ya matso kusa da ita. Jaruma Riya ta daka wani
wawan tsalle sama ta dira a can gefen guda nisan kamu sha biyar. Aymanul Faris ya
cika da tsananin mamaki, ta dube shi ta ce yayi abinda tayi. Aymanul Faris ya gama iya
tsallensa amma ko nisan kamu goma bai kai ba, ta ce ya dage iya yinsa. Ai kuwa yayi ta
gwadawa amma daƙyar ya samu ya yi tsalle mai nisan kamu goma. Jaruma Riya ta
dube shi ta ce, "Idan kazo yin tsalle ɗauke numfashinka zaka rinƙa yi sannan idanunka
su kasance akan inda kake so ka tsirga." Koda Aymanul Faris ya gwada yin hakan sai
yayi tsalle ta kusan kamu goma sha huɗu, al'amarin da yasa ya cika da tsananin farin
ciki kenan.
Cikin kallo mai cike da jinjina jaruma Riya ta dube shi ta ce, "Tabbas ka kasance mai
hazaƙa kuma ƙwaƙwalwarka na aiki sosai..." Haka dai jaruma Riya da Aymanul Faris
suka ci gaba da baiwa kansu horo a cikin wannan fili har tsahon sa'a bakwai a lokacin
da rana ta faɗi. Aymanul Faris ya yiwa jaruma Riya bankwana sannan ya juya ya fice
daga filin horon, jaruma Riya ta ji kamar ta kamo hannun Aymanul Faris domin ta
bayyana masa abinda ke cikin ranta amma sai ta fasa sakamakon tuno wani abu.
****
Sauƙowa suke daga saman wani ƙaton tsauni sanƴe cikin baƙaƙen tufafi masu ratsin ja,
sadaukai ne majiya ƙarfi masu yawan gaske don baka isa ka irga su daga kallo ɗaya ba.
Dukkaninsu suna zazzaune bisa waɗansu irin ingarmun dawakai ƙosassu, farare masu
baƙi-baƙi ta wuya. Sadaukan sun kasance a jere a sahu guda, a yayin da wata
kyakkyawar sarauniya ke zaune a gabansu bisa wani jan doki. Idan mutum ya ƙarewa
wannan sarauniya kallo zai fuskanci ba wata bace illa RAUZIYYA mai mulkin tsaunin
Barzasa.
Sarauniya Rauziyya tayi shiga ta kayan yaƙi mai ban tsoro, gaba ɗaya jikinta a lulluɓe
yake da sulke mai launin shuɗi. A gadon bayanta ta ratayo waɗansu zabga-zabgan
takubba guda biyu masu tsananin kaifi da tsini, a ƙwibin cinƴoƴinta kuma waɗansu
ƙananun wuƙaƙe ne guda huɗu. Ta rufe kanta da hular ƙarfe, gashin kanta kuma an
ɗaure shi a waje guda. Kana kallonta kaga MACE MAI KAMAR MAZA, kuma
BASADAUKIYA.
Wani abin mamaki shi ne duk irin tsananin wahalar da yarima Marganu ya sha wajen
hawa kan wannan tsauni, sarauniya Rauziyya da dakarunta tafiya suke cikin kwanciyar
hankali suna gangarowa daga kan tsaunin ba tare da sun faɗo ƙasa ba, kai kace akan
turɓaya suke tafiya.
Sarauniya Rauziyya na riƙe da kalar taswirar da aljani Barzasa ya basu wacce ke nuni da
duk wurin da yarima Marganu yake a faɗin duniya. A wannan lokaci hasken na tsakanin
birnin Hirtoliya da birnin Damashkar, kuma hasken na tafiya ya tunkari birnin
Damashkar. Wato hasken na nuni da yarima Marganu ya taso daga birnin Hirtoliya ya
nufi birnin Damashkar inda yayi mugun gamo da dakarun-masifa har suka kama shi.
Lokacin da sarauniya Rauziyya tare da dakarunta suka sauƙo daga kan wannan tsauni,
sai ta ɗaga hannunta sama, dakaru suka tsaitsaya kuma suka yi tsit tamkar mutuwa ta
gifta. Ta juyo ta dube su, sannan ta fiddo wannan taswira ta ɗagata sama ta nuna daidai
inda hasken yarima Marganu yake. A wannan lokaci tuni an isa da yarima Marganu cikin
kurkukun mutuwa.
"Wannar haske da kuke kallo," inji sarauniya Rauziyya cikin yarensu. "Shi ne daidai inda
tsinanne Marganu yake. Kamar yadda wannan taswira ta nuna wannan waje da yake
kurkuku ne, wataƙila akwai laifin da yai musu har suka kama shi. Koma dai ina ne
mukam bai shafe mu ba, abinda muka sani kawai shi ne sai mun kamo wannan
tsinanne mun gurfanar dashi a gaban mai girma Barzasa. Babu tsoro, babu gudu, babu
ja... da baya. Lallai sai mun kama wannan shaiɗanin. Daga wannan waje zuwa wannar
kurkuku tafiya ce ta kusan wata guda, don haka dole ne mu zage dantse muyi ta tafiya
babu dare ba rana, babu batun yada zango sai ta kama dole. Dole ne mu kamo
Marganu..." Sarauniya Rauziyya na gama faɗin haka ta zaburi dokinta da gudu, ta nufi
cikin ƙungurmin daji dakarunta na take mata baya, suna yi mata kirari gami da wasata.
Duk wanda ya hango wannan runduna ta sarauniya Rauziyya daga nesa walau aljanu,
dabbobin daji ko dodanni sai kaga sun arce saboda tsananin kwarjinin rundunar da
kuma ƙarfin sihirin dake tashi daga jikin sarauniya Rauziyya mai sanƴa razana gami da
tsoro a zuƙatan masu kallonta.
*****
Tun daga wannan rana Aymanul Faris da jaruma Riya suka ci da baiwa kansu horo a
cikin wannan ƙaton fili har tsahon kwanaki goma sha-bakwai. Saura kwana biyu rak,
ranar zuwa birnin Askandariyya tazo. Aymanul Faris ya ƙware matuƙa wajen daka
wawan tsalle da kuma talewa. A wannan rana da yammaci ne sarkin ɓarayi Barban ya
keɓe da Aymanul Faris a cikin wani ɗaki domin ya ƙara nuna masa yadda shirinsu zai
gudana. Taswirar birnin Askandariyya maigida Barban ya shimfiɗe akan wani teburi mai
faɗin gaske, shi da Aymanul Faris suka zauna akan wasu kujeru biyu da suka kewaye
teburin.
Akan wannan taswira akwai zanen ƙaton gari, mai ɗauke da zane-zanen gidaje, koguna,
duwatsu, bishiyoyi da sauransu. A tsakiyar taswirar akwai zanen wani ƙaton gidan
sarauta mai ƙofar shiga guda ɗaya jal, sannan akwai zanen dakarun tsaro masu yawan
gaske a bakin wannan ƙofa. Gidan sarautar na da girma da faɗin gaske, kuma an raba
shi wajen kashi huɗu ne. Kashi na farko shi ne inda ɗakunan dakaru da masu hidima na
gidan sarautar yake. Kashi na biyu kuma shi ne inda aka yi zanen wata doguwar
husumiya guda ɗaya jal, wadda aka zana dakarun tsaro masu yawan gaske a kewaye da
ita. Kashi na uku kuma zanen waɗansu irin ɗakuna ne da aka gina akan tsaunika da aka
samar a cikin gidan sarautar. Kashi na huɗu shi ne yankin sarki Darwazu da iyalansa.
Babu yadda za'a yi mutum yaje yankin sarki Darwazu ba tare da ya ketare kashi na
farko, na biyu da na uku ba.
"Jiya-jiyan nan mai girma Ranganu ya kawo min wannan taswira." Inji sarkin ɓarayi
Barban. "Taswirar birnin Askandariyya ce inda zamuje bayan-gobe domin fara aikinmu
na farko da kai."
Mai gida Barban ya gyara zama sannan ya nuna ƙofar shiga gidan sarautar ya ce, "Idan
baka manta ba, sa'adda nake maka bayanin wannan aiki namu ban sanar da kai hanƴar
da zamu bi mu shiga gidan sarautar nan ba. Dama ba don komai yasa na ƙi faɗa maka
ba sai domin jiran zuwan wannan taswira. To, kamar yadda ka gani ƙofar shiga cikin
wannan gidan sarauta guda ɗaya ce, tunda ko guda ɗaya ce tabbas ka san zatayi
mugun tsaro da hatsari. Da yake ranar sha-tara ga wata zamuje shiga cikin wannan
gidan sarauta ba zaiyi mana wahala ba, indai abinda bincike ya tabbatar min gaskiya
ne. Wato a wannan rana sarki Darwazu ke barin mutanen ƙasar domin su shiga cikin
gidan sarautar, suna zuwa gurin wani ƙaton gunki suna neman tubarraki. Kaga kenan
zamu iya sajewa a cikin mutanen gari mu shige cikin gidan sarautar." Maigida Barban
ya sake ɗora hannunsa akan yankin farko na gidan sarautar inda aka zana hoton wani
ƙaton gunki. "Iyakacin inda mutane ke zuwa kenan, wato yankin farko inda gunki
Sairamas yake." Ya ci gaba da bayani, yana mai ɗora hannunsa akan yanki na biyu.
"Duk wanda aka gani a wannan yanki na biyu, to tabbas ya aikata babban laifi. Dakaru
zasu kamashi su kaishi wurin sarki. Kamar yadda na faɗa maka wannan wuri shi ne inda
sarki Darwazu ya ajiye wannar farar lu'u-lu'u." Maigida Barban ya sake ɗora hannunsa
akan ɓangare na uku ya ce, "Wannan wuri da kake kallo, ba tsaunikan asali bane. Sarki
Darwazu ya samar da su da ƙarfin sihirin tsafi, a nan dakaru masu siffa biyun nan ke
kwana. Babu yadda za'ayi mutum ya isa yankin sarki Darwazu ba tare da ya kawar da
waɗannan dakaru ba."
Haka dai maigida Barban ya ci gaba da yiwa Aymanul Faris bayanan zanen dake jikin
taswirar har dare ya soma rabawa sannan suka yi bankwana yaje ya kwanta.
Aymanul Faris na kwanciya bisa gadonsa ya gagara barci, tunani kala-kala suka ɗinga
faɗowa ƙwaƙwalwarsa. Abu na farko da ya fara tunowa shi ne gimbiya Jaanu. Nan take
ya shiga cikin wani shauƙi, ya ɗinga tunanin abubuwan da suka faru tsakaninsa da ita a
baya. Aymanul Faris ya ji ina ma ace zai sake yin arba da kyakkyawar fuskar gimbiya
Jaanu koda kuwa sau ɗaya ne, da ya kasance cikin farin ciki. "Ko wanne hali take ciki,
oho? Wataƙila ma ta manta dani, Marganu ya aureta!" Ya faɗa a cikin ransa. Zuciyarsa
ne ta daka masa tsawa ta ce, "Wannan ai ba zai yiwu ba, in dai har soyayya ta kasance
gaskiya. Tabbas gimbiya Jaanu tana ƙaunarka fiye da komai a duniya." Murmushi kawai
Aymanul Faris yayi, ya canja tunaninsa domin gani yake soyayya ba tashi bace a yanzu.
Yana cikin wannan hali barci yayi gaba da shi.
Washe gari bayan ya farka, ya yi wanka kuma ya yi kalaci. Maigida Barban da kansa
yazo ya kira shi, suka nufi cikin wannan ɗakin. Da shigarsu cikin ɗakin Aymanul Faris ya
yi arba da kayan sawa kala daban-daban, mafi yawa daga cikin kayan irin kayan ɓarayi
ne masu ɓoye siffa. Maigida Barban ya nunawa Aymanul Faris waɗansu kaya baƙaƙe
masu sheƙi, ya ce ya saka su. Ba tare da gardamar komai ba Aymanul Faris ya ɗauki
waɗannan kaya ya shiga cikin kewaye, ya saka su sannan ya fito. Kayan sun kasance
ƙaramar riga da dogon wando wanda yazo har idon sawu, sai kuma hula wadda ta rufe
dukkan fuskarsa, iya idanunsa kaɗai ake kallo. Haƙiƙa waɗannan kaya ba ƙaramin kyau
suka yiwa Aymanul Faris kuma duk sanin da mutum yayi masa ba zai iya shaida shi a
cikin waɗannan kaya ba. Maigida Barban ma ya zaɓi kalar waɗannan kaya su ma
baƙaƙe shima ya sanƴa kamar yadda Aymanul Faris yasa.
Suna gama kimtsawa maigida Barban ya shafi kayan jikin Aymanul Faris take suka ɓace
ɓat, ya dawo cikin waɗansu sutura daban. Farar riga doguwa mai ratsin ja, da wando
kore sharr. Maigida Barban ya sake yin tsafi shima kayan jikinsa suka ɓace ya bayyana a
cikin wata malun-malun fara sol daga sama har ƙasa saboda tsayin rigar, mutum baya
ganin kalar wandon da ya sanƴa.
"Ya kai Ayman, lokacin tafiya yayi," inji maigida Barban. "Je kayi bankwana da
mahaifiyarka Hajriya, da kuma mai ƙaunarka Riya." Koda Aymanul Faris yaji abinda
maigida Barban ya faɗa sai ya cika da tsananin mamaki amma bai ce komai ba, ya fice
daga cikin ɗakin.
Bayan kamar rabin sa'a sai ya sake dawowa cikin ɗakin, ya cewa maigida Barban ya
shirya.
Maigida Barban ya shafi kambun dake ɗaure a hannunsa na hagu, take waɗannan
gabza-gabzan aljanu guda uku suka bayyana a gabansa suna masu risinawa. Barban ya
ce, su ɗauke su su kaisu dajin Ras. Aljanun suka risina sannan suka suri Barban da
Aymanul Faris suka aza bisa gadon bayansu suka lulluka cikin gajimare, suka nufi
ɓangaren birnin Askandariyya suna tsala azababben gudu.
"Waɗannan kaya da suke jikinka sune kayan ɗaliban addinin Dayyarish," inji Barban.
"Kayan da suke jikina kuma su ne na shaihunan addinin ne, tabbas idan aka ganmu a
cikin wannan shiga, za'a barmu mu shige cikin birnin Askandariyya ba tare da mun
fuskanci matsalar komai ba. Shin kana da tambaya ko kuma neman ƙarin bayani kafun
mu isa birnin Askandariyya?"
Aymanul Faris ya yi caraf ya ce, "Tabbas ina da tambaya. Naga ka shafi waɗannan
baƙaƙen kaya da suke jikina sun ɓace, shin idan muka shiga birnin Askandariyya a ina
zamu same su? Tsahon wanne lokaci zamu ɗauka kafun wannan aiki ya kammala?"
Maigida Barban ya yi murmushi ya ce, "Ai shan ruwa yafi wahala akan dawo maka da
waɗannan kaya. Tsahon lokacin da wannan aiki zai ɗauka? Ya danganci yadda muka
tafiyar da aikin ne. Kai dai ka zage dantse kawai, zamu yi nasara."
Maigida Barban na rufe bakinsa, waɗannan aljanu guda suka dira a tsakiyar wani ƙaton
daji. Suka ce mun iso, maigida Barban ya sallamesu.
Daga wannan daji idan suka ɗaga kawunansu suna iya hango ƙofar birnin Askandariyya,
wacce ke cike maƙil da dakarun tsaro.
***RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 18: *Shiga birnin Askandariyya*

*
✍️✍️✍️ Umar Sangaru ✍️✍️✍️
*
Ba tare da ɓata lokacin komai ba maigida Barban da Aymanul Faris suka tunkari ƙofar shiga cikin birnin Askandariyya, idan ka gansu zaka yi tsammanin malami ne da ɗalibinsa. Aymanul Faris na bisa gaba rataye da wata ƙatuwar jaka wacce aka cika da litattafa, shi kuma Barban na biye da shi, riƙe da wani irin carbi. Fuskar Aymanul Faris ta sauya matuƙa domin kalar ƙwayar idanunsa ta sauya daga baƙa wuliƙ zuwa shuɗi, gashin kansa ya rine ya koma jajawur. Shi kansa bai san hakan ba sakamakon ƙarfin sihirin tsafin Barban. Fuskar maigida Barban na nan yadda take amma wani siririn gashin baki ya bayyana a fuskarsa wanda ya kewaye bakinsa.
Ƙofar birnin Askandariyya ƙatotuwa ce sosai, da zallar baƙin ƙarfe mai kauri aka ƙerata. Akwai dakaru gabza-gabza aƙalla guda dubu tsaitsaye a bakin ƙofar, suna riƙe da zabga-zabgan takubba kuma suna ta muzurai tamkar zasu ci babu. A bakin ƙofar shiga akwai mutane a jere layi, suna zuwa da ɗaiɗaiya ana cajesu sannan su wuce cikin birnin. Barban da Aymanul Faris ma cikin jerin waɗannan mutanen suka shiga suka tsaya, suna jiran layi yazo kansu.
Sannu-a-hankali layi ya ci gaba da tafiya har aka zo kan wani mutum, tsoho ne tukuf daƙyar ma yake tafiya. Daga wannan mutumi sai su maigida Barban.
"Kai tsoho! Waye kai daga ina kake?" Wani badakare dake tsaye a bakin ƙofar shiga ya dakawa tsohon tsawa.
"Sunana Saihar al-Aswàd. Daga birnin Kisra nake, abinda ya kawo ni wannan birni shi ne nazo ne domin yin bara da neman abinda zan ci." Inji tsohon.
Koda maigida Barban yaji muryar wannan tsoho sai tsikar jikinsa ta mimmiƙe, idanuwansa suka cicciko da ƙwalla domin shi kaɗai ne yasan mai wannar murya.
"Barka da zuwa, Askandariyya. Tabbas kazo inda za'a taimaka maka." Wannan badakare ya amsawa wannan tsoho, sannan yasa aka buɗe masa ƙofa ya shige cikin birnin yana tafiya a hankali da sandarsa, kamar zai faɗi. Maigida Barban ya bi wannan tsoho da kallo kawai, idanuwansa suna ta zubar da hawaye.
"Malam, meyasa kake kuka? Yaushe ka fita daga cikin birnin nan har ka dawo bamu sani ba?" Badakaren nan ya tambayi Barban. Maigida Barban ya share hawayensa ya ce, "Abinda yasa kaga nake kuka shi ne yanzu dama akwai irin waɗannan mutane masu neman taimako amma bamu sani ba. Taimakon gajiyayyu wajibi ne inji maigirma Haiƙàn. Yaushe na fita daga cikin birnin nan? Shin ka manta lokacin da shaihunai suka je dajin Ras domin addu'a akan masifar da dodo Dodras ya sauƙe, gaba ɗaya shaihunai sun dawo amma ni ban bar dajin ba, sai da na tabbatar da cewa maigida Haiƙàn ya karɓi addu'ata. Tabbas wannan cuta ta yaye yanzu."
Koda wannan badakare yaji batun maigida Barban sai jikinsa yayi sanƴi amma dukda haka baice a buɗewa Barban ƙofa ba. "A sanina dai shaihunai basa taɓa rabuwa da ƴan uwansu a yayin addu'a," wannan badakare ya fara bayani. "Meyasa zasu dawo su bar ka kai kaɗai a dajin Ras, alhalin nasan cewa da wuya su yarda su bar ka kai kaɗai don kada dodo Dodras ya hallaka ka." Fuskar Barban ta sauya launi ya murtuƙeta ya ce, "Kai Kuffan, ka san da wa kake magana kuwa. Ni ne fa shugaban shaihunnan birnin Askandariyya gaba ɗaya mabiya addinin Dayyarish. Meyasa kake neman kawo min matsala, shin ka fini sanin addinina ne. Addininmu ba ɗaya ba don haka ka buɗe min ƙofa kafun fushin maigirma Haiƙàn ya sauƙa akan ka." Koda badakare Kuffan yaji wannan batu sai ya zare idanu ya ce, "Idan kaga na buɗe maka ƙofa, ka tabbatar ka shaida min cewa kai asalin shehun addinin Dayyarish ne kuma ɗan asalin birnin Askandariyya."
Barban ya yamutse fuska, "Tayaya zan tabbatar ma?" Ya ce. Badakare Kuffan ya ƙwalawa wani mutum kira dake cikin wani tanti acan gefe guda. Nan take wani saurayi dogo mai hasken fata ya fito daga cikin tantin, ya nufo inda suke tsaye.
"Wani abu ne?" Saurayin ya tambaya. Kuffan ya dube shi ya ce, "Ya kai Buddusu, masanin addinai dubu ina so ka yiwa wannan mutum tambayoyi akan addinin Dayyarish, don naga kamar ban taɓa kallonsa a cikin shaihunai ba." Buddusu ya kalli Barban suka yi kallon kallo, Barban ya yi masa murmushi mai nuna a shirye nake.
"Waye ne Dayya? A wacce shekara aka sauƙe littafin kitabul Dayyan? Waye ne ya kashe Hushun? Idan ka amsa waɗannan tambayoyi dai-dai babu inda-inda tabbas ka zamo asalin shehun addinin Dayyarish kuma ɗan birnin Askandariyya." Inji Buddusu.
"Dayya? Shi ne wanda ya kwana bakwai a gaban gunki Rash yana sujjada, ba tare da ya ɗago kai ba balle yaci ko ya sha wani abu. Dayya shi ne wanda ya yiwa gunki Rash ado da zinariyar Gazwar kuma shi ne wanda ya yanki jinin hannunsa ya zubawa gunkin a idanunsa.
"A wacce shekara aka sauƙe littafin kitabul Dayyan? A shekarar Rash. Lokacin da gunki Rash ya bayyana a ɗakin bauta kimanin shekaru ɗari huɗu da suka shuɗe.
"Kashe Hushun ba shi da wata alaƙa da addinin Dayyarish domin kuwa mahaifin sarki Darwazu ne ya fille kansa, akan ya shiga gonar Laiham. Wannan ai ba wata tambaya ce mai wahala." Barban ya ƙare bayaninsa.
Buddusu ya ja Kuffan gefe suka yi ƙus-ƙus sannan ya koma cikin wannan tanti da ya fito. Kuffan ya dawo bakin ƙofa ya ce a buɗewa su Barban su shige ciki. Nan take kuwa aka buɗe ƙofar suka danna kai izuwa cikin birnin Askandariyya.
Birnin Askandariyya ƙaton gari ne mai cike da manƴa-manƴan gine-gine, shaguna, ɗakunan bauta da sauransu. A wannan birni ana ƙwatanta aƙalla addinai ɗari ba ɗaya, kasancewar sarki Darwazu babu ruwansa

Please Login or Register in order to submit comment