Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

san
cewa baza mu iya shiga wancan kurkuku ba saboda tsaronta shiyasa muka yi shiri
muka zo gidan sarautar muka saceki, mun tabbatar da cewa indai kina hannunmu, sarki
zaiyi duk abinda mukeso. Kiyi hakuri akan abinda Riya tayi miki, kinsan zafin rabuwar ɗa
da ubansa." Koda Aymanul Faris yazo nan a jawabinsa sai gimbiya Jaanu ta fashe da
kuka saboda tsananin tausayi. "Ya ku waɗannan 'yan uwa, kuyi hakuri bisa rashi da kuka
yi na masoyanku da 'yan uwanku. Tabbas mahaifina ya cika azzalumi mara tausayi,
amma nayi alkawarin da sannu zan sauya shi matuƙar zai sauyu. Ya kai wannan jarumi
hakika nikam na kamu da tsananin kaunarka tun sa'adda nayi arba da kai a cikin
turakata. Haƙiƙa kana da kyawawan halaye irin wanda kowacce mace take burin samu.
Nagode da kulawar da kake nunawa a gareni." Jaanu ta karasa maganarta tana mai
goge hawayen dake zuba a idanunta. Aymanul Faris rike hannayenta biyu yayi cikin
tsananin so da kauna ya ce, "Nima ina tsananin kaunarki kamar yadda kike kaunata,
amma da akwai matsala." Cikin hanzari gimbiya Jaanu ta dago kai ta kalleshi ta ce,
"Matsalar me kuma?" Aymanul Faris ya daga kai ya kalli inda jaruma Riya ke tsaye
sannan ya fice daga ɗakin, ba tare da ya bata amsar tambayar da tayi masa ba.
****
A can birnin Damashkar dai, al'amura sun dada caɓewa sarki Ayubul Zairiy. A ranar
wuni guda yayi cir bai sa komai a bakinsa ba, kuma yadda yaga rana haka yaga dare
wato bai rintsa ba. Mutanen birnin Damashkar dai su ma a ɗimauce suke saboda yadda
suke tsananin kaunar gimbiya Jaanu saboda adalcinta, ace ta ɓata ai akwai matsala.
Sarki Ratanam da ɗansa Marganu kuma a ɗakinsu raba dare suka yi suna hira akan
al'amarin suna mamakin hatsabibancin da ya shigo har cikin gidan sarautar kasar
Damashkar ya sace 'yar sarki guda ba tare da asirinsa ya tonu ba.
"A'a naji ance an sami hatimi mai zanen wasu bakaken rubutu masu kama da na
mutanen birnin Sin a inda aka shaƙawa dakarun dake tsaron lafiyar gimbiya banju, na
taba kallon zanen wannan hatimi a birnin Sin, shaida ce ta wani gawurtaccen barawo
wanda ya talautar da sarki Kim Sam a dare ɗaya." Inji sarki Ratanam, ya bawa ɗansa
Marganu amsa akan ko akwai alamar da ɓarawon ya bari.
Yarima Marganu ya yi ajiyar zuciya ya ce, "Lallai ko waye wannan ɓarawo ya cika
hatsabibi kuma abin tsoro tunda har zaizo yayi sata kuma ba'a kama shi ba a wurin da
yafi ko'ina tsaro a birnin Damashkar. Amma meyasa zai sace gimbiya Jaanu maimakon
ya saci dukiya kamar yadda ya saba?" Koda jin haka sai sarki Ratanam ya numfasha ya
ce, "Wannan tambaya taka abar dubawa ce. Watakila niyyarsa akan satan dukiya ne
amma da yayi arba da kyawun gimbiya Jaanu sai ya canja shawara. Watakila kuma
dama shirinsa akan satan gimbiyar ne domin yaje yayi ta amfani da ita, ko kuma aljanun
da suke taimaka masa ne suka buƙaci ya kawo musu kyakkyawar 'yar sarki." Yarima
Marganu ya cije baki. "Ai kuwa idan ya kuskura ya shafa koda kyakkyawan jan gashin
dake kanta ne sai na hukunta shi, idan ya shiga hannuna. Saboda Jaanu tawa ce ni
kadai." Sarki Ratanam ya yi murmushi ya ce, "Da wuya. Mutumin da ya gallabi manyan
sarakunan duniya da sata, me zaiyi da ƙaramar yarinƴa kamar Jaanu? Mu jira kawai
zuwa wani ɗan lokaci na tabbata zai bayyana bukatarsa." Haka dai sarki Ratanam da
ɗansa Marganu suka ci gaba da hira, har barci ya sace su.
Kashe gari tun daga ketowar alfijir sarki Ayubul Zairiy ya fita izuwa fadarsa ya zauna
akan karagarsa yana mai jiran bayyanar boka Ruguzan domin yaji inda 'yarsa Jaanu
take.
Sai da gari ya gama wayewa sosai aka kawowa sarki abincin kalaci, amma ko kallon
abincin baiyi ba saboda ba shine a gabansa ba. Jim kaɗan kuma sai ga sarki Ratanam
tare da ɗansa Marganu sun shigo cikin fadar sanye da kaya masu tsadar gaske, nan
take suka zazzauna akan kujerun da suke zama kullum. Bayan sun gama gaisawa da
sarki Ayubul Zairiy sai sarki Ratanam ya dube shi ya ce, "Ya kai abokina shin akwai wani
labari kuwa akan inda gimbiya take?" Koda jin wannan tambaya sai sarki Ayubul Zairiy
ya ce, "A'a ban samu wani labari ba amma ina jiran zuwan shugaban bokayen ƙasata
domin na san halin da ake ciki. Yanzu haka shi nake ta jira tun ɗazu amma bai ƙariso
ba." Ayubul Zairiy na rufe bakinsa, wani dunkulen haske ya faɗo cikin fadar kamar curin
nakiya. A hankali hasken ya dinga tarwatsewa yana zamowa hoda, siffar boka Ruguzan
ta dinga bayyana dishi-dishi a cikin wannan hoda. Ba'a jima ba ya gama bayyana
tsulum, a wannan lokaci ma baƙaƙen kaya ne a jikinsa.
Fuskar boka Ruguzan na dauke da tashin hankali da jimamin abinda ya gani, lamarin da
yasa jikin sarki Ayubul Zairiy yayi sanyi kenan. Ya taso da sauri ya zo gaban boka
Ruguzan ya kama kafaɗunsa ya ce, "Ya kai wannan boka, shin ka gano inda gimbiya
take?" Boka Ruguzan ya dube shi cikin nutsuwa ya ce, "Akwai matsala. Shugaban
ɓarayin duniya ne ya sace 'yarka. Ya kai shugabana kayi sani cewa nayi iya bakin
ƙoƙarina wajen gano inda wannan ɓarawo ya kai 'yarka amma na gagara ganowa
saboda ya fini karfin nesa ba kusa ba. Tabbas rayuwar gimbiya na cikin mugun haɗari,
domin a binciken da nayi na gano cewa wannan ɓarawo ya ninka dukkanin attajiran
dake wannan birni namu a yawan dukiya sau dubu, wato gawurtaccen attajiri ne da
babu kamarsa a duniya. Haka kuma gawurtaccen boka wanda yafi kowa ƙarfin sihiri a
duniya tunda gaba ɗaya bokayen duniya sun gagara gano ko waye shi, tsawon shekara
da shekaru. Idan kayi la'akari da haka, kaga kenan ba dukiya yake so ba. Ba kuma wani
sihiri zaiyi da ita saboda ya cika ya tumbatsa da ƙarfin sihiri. Dole cikin biyu za'a yi
ɗaya. Ko dai wannan ɓarawo ya aure wannan 'ya taka ko kuma wata bukata mai karfi
zai nema a wajenka wacce ya tabbatar da cewa kaine kaɗai ne zaka iya biya masa ita.
Yanzu dole mu jira mu ga meye yunƙurinsa na gaba, idan har yana da wata bukata to
tabbas zai aiko da wasiƙa. Idan kuma mu kaga kwanaki uku sun shuɗe bai nememu to
tabbas akwai matsala sai dai mu shiga duniya muyi ta nema" Koda boka Ruguzan yazo
nan a zancensa sai sarki Ayubul Zairiy ya sake kwarara uban ihu ya dubi Ruguzan ya ce,
"Kana ganin nan da kwanakin ukun zai iya aiko mana da wasiƙa, yana bukatar wani
abu?" Ruguzan ya ce, "Ina kyautata zaton haka." Sarki Ayubul Zairiy ya ce, "Allah dai
yasa ya aiko ɗin."
*****
Dakin a haskake yake da manya-manyan fitilu masu tsananin haske, mutum uku zaune
ne a cikin ɗakin bisa kujeru na tagulla. Ɗaya daga cikin mutanen saurayi ne kyakkyawa
wanda ba shi da sura ta jarumta amma yana ɗaure da kambun tsafi a damtsen
hannunsa na hagu, idan ka san sarkin ɓarayi Barban to shine. Ɗayan kuma yaro ne ɗan
kimanin shekaru goma sha tara amma idan kaga murdewar jikinsa sai kayi zaton ya
baiwa shekaru ashirin baya saboda tsabar murɗewa da tarin kwanji, idan mutum ya san
Aymanul Faris to zai gane cewa shi ne ba wani ba. Na ukun ne wani dogon saurayi mai
doguwar fuska wadda take ɗauke da wani ɗan gajeran gemu, idan ka duba bayansa
zaka ga fuka-fuki guda biyu masu kauri hakan ne zai tabbatar maka da cewa aljani ne
ba mutum ba.
Kujerun da Barban da Aymanul Faris suke a haɗe suke suna fuskantar kujerar aljani
Ranganu. Muryar Ranganu ta fara bada sauti mai kama da kukan kosasshen jaki, "Na
gama rubuta muku wannan wasika, yanzu take nake so kai Barban ka baiwa daya daga
cikin aljanunka ya kaiwa boka Ruguzan wannan wasiƙa. Na zana taswirar gimbiya Jaanu
a jikin wannan wasika sannan na zana taswirar mahaifiyar Aymanul Faris a jikin wasikar.
Idan yana bukatar 'yarsa to dole ne ya dauki Mahaifiyar Aymanul Faris ya kaita dajin
Marsas dake karshen birnin Sin, sannan mu kuma mu bashi 'yarsa. Acan zamu karbi
Hajriya sannan mu bashi 'yarsa.
"Wancan daji na Marsas asalinsa mallakin babana ne, babu yadda za'ayi sihirin tsafinsu
yayi tasiri a cikin dajin."
Aljani Ranganu na zuwa nan a zancensa ya fiddo wata takarda nannadaddiya wacce aka
yiwa ado da ruwan zinari ya baiwa Barban, sannan ya ɓace ɓat! Barban ya shafi kambun
dake ɗaure a hannunsa take waɗannan gabza-gabzan aljanu guda uku suka bayyana,
suka fadi ƙasa suka ce, "Me kake bukata ya shugabanmu?" Sarkin barayi Barban ya
basu wannan wasika ya ce, "Su kaiwa boka Ruguzan dake birnin Damashkar." Aljanun
nan suka ce an gama sannan suka ɓace ɓat.
Aymanul Faris yazo gaban Barban ya zube ƙasa yana godiya bisa taimakonsa da yayi.
Barban ya taso shi tsaye ya ce, "Kwantar da hankalinka babban jarumi, wannan ai yiwa
kaine. Ina fatan dai har yanzu baka manta cewa ban fada maka aikin da zaka min ba."
Aymanul Faris ya ce, "Wanne aiki kenan?" Barban ya ce, "Zan faɗa maka amma sai
bayan hankali ya gama kwanciya wato mun kuɓutar da mahaifiyarka daga hannun su
sarki Kuffuru." Yana gama fadin haka ya fice daga dakin.
*******RUHIN JARUMTAKA!
*
Babi na 6: *Sarki Kuffuru*
*
*
Umar Sangaru
*
Sarki Ayubul Zairiy bai jira lokacin tashi daga fada yayi ba, ya tashi ya shige cikin gidan
sarautarsa. Kai tsaye ya wuce cikin turakarsa ya kulle kansa a cikin turakar, sannan ya
durƙushe bisa gwiwowinsa ya fashe da kuka. Yana cewa a ransa, "Me na yiwa sarkin
ɓarayin duniya har zai sace ƴata? Shin me zai buƙata a wajena maimakon wannan ƴa
tawa?" Da ya rasa wanda zai bashi amsar waɗannan tambayoyi sai ya sake fashewa da
sabon kuka. A daidai wannan lokaci ne yaji wata azababbiyar ƴunwa ta rufe shi, wani
mugun jiri ya ɗebe shi baisan sa'adda ya faɗi ƙasa ba, ya fara juye-juye kamar wanda
zai mutu.
Muryarsa na rawa ya ƙwalawa wani hadimi kira, take hadimin ya rugo cikin turakar.
Koda yaga halin da sarki ke ciki sai ya ɗimauce, ya ruga zai tallafo shi. Sarki Ayubul
Zairiy ya daka masa tsawa ya ce, "Kai Muzaffar je ka kawo min abincin kalaci, amma
ƴaƴan itatuwa zaka kawo." Hadimin ya risina sannan ya fice, jim kaɗan ya dawo ɗauke
da farantin kayan marmari, ya ajiyewa sarki a gabansa. Da ƙyar sarki Ayubul Zairiy ya
miƙe zaune sannan ya fara cin wannan kayan marmari, bai gushe ba yana ci sai da ya
ƙoshi taf.
Gama cin wannan abinci keda wuya sarki Ayubul Zairiy yaga hadimi Muzaffar ya sake
shigowa cikin turakar, ya zube a gaban sarki. "Ya shugabana boka Ruguzan ya dawo ya
ce, a kirawo masa kai." Sarki Ayubul Zairiy ya ja dogon numfashi ya ce, "Shin fadar ta
watse ne? Ko har yanzu akwai jama'a?" Muzaffar ya ce, "Kwarai har yanzu akwai jama'a
birjik a fadar." Sarki ya ce, "Je ka yiwa boka Ruguzan jagora izuwa wannan fada tawa,
tare da su sarki Ratanam da ɗansa." Hadimi Muzaffar ya sake risinawa sannan ya fice
daga cikin turakar.
Jim kaɗan aka sake buɗe wannan ƙofa, boka Ruguzan, sarki Ratanam da ɗansa yarima
Marganu suka shigo cikin turakar. Sarki Ayubul Zairiy ya ja su gefe guda inda aka tanadi
wadansu kujeru masu yawan gaske suka zazzauna. "Ya kai shugaban bokaye meke tafe
da kai?" Sarki Ayubul Zairiy ya tambayi Ruguzan. Maimakon boka Ruguzan ya bashi
amsa kawai sai ya sanƴa hannu a cikin aljihun rigarsa ya fiddo wata nannaɗaɗɗiyar
takarda, koda sarki Ayubul Zairiy ya yi arba da wannan takarda sai gabansa ya faɗi.
Ruguzan ya miƙa masa wannan takarda. Hannun sarki Ayubul Zairiy na karkarwa ya
karɓi wannan takarda, ya buɗeta amma sai ya gagara karanta abinda ke ciki. "Ya
shugabana ka kwantar da hankalinka, ka karanta abinda ke cikin wannan takarda
saboda ita ce kawai mafitar mu." Inji boka Ruguzan tamkar ya san abinda ke cikin
takardan.
Sarki Ayubul Zairiy ya yi ajiyar zuciya ya kwantar da hankalinsa, ya sake buɗe takardar ya
fara karanta ta a fili kamar haka:
"Wasiƙa daga shugaban ɓarayi, sarkin talakawa na duniya. Zuwa ga sarkin Damashkar,
sarki Ayubul Zairiy. Ya kai wannan sarki da fatan kana lafiya. Ba don komai na aiko
maka wannan wasiƙa ba sai domin na shaida maka cewa ƴarka gimbiya Jaanu tana
hannuna, ma'ana ni ne wanda ya saceta. Ba don komai na sace wannan ƴa taka ba sai
domin kuɓutar da ƴar uwata, mahaifiyar Aymanul Faris daga kurkukun daka tsareta.
Idan kana buƙatar ƴarka, to ya zama dole ka aiko mana wannan mata ko kuma ka
kawota da kanka izuwa dajin Marsas dake ƙarshen birnin Sin nan da cikar kwanaki
talatin, idan ba haka ba kuwa. Zan yanko kan ƴarka na aiko maka da shi. Ƴarka tana
cikin ƙoshin lafiya, ka tabbatar da cewa an kawo mana wannan mata a cikin ƙoshin
lafiya idan ba haka ba kuwa, ka san sauran... Za mu kasance masu jiran zuwanku a
dajin Marsas ranar ashirin da tara ga watan Nuwamba. Idan kana so ka ceci ƴarka, sai
ka kawo wannan mata a wannan rana. Kahuta."
Lokacin da sarki Ayubul Zairiy yazo nan a karatun wasiƙar sai hankalinsa yayi
mummunan tashi, idanuwansa suka kaɗa suka yi jawur. Kamar yadda sarki Ayubul Zairiy
ya tsinci kansa a cikin wannan hali haka shima sarki Ratanam ya kasance, al'amarin da
yayi matuƙar baiwa Marganu mamaki kenan. Ya dube su ya ce, "Ya ku shuwagabanina
me yake damunku ne, naga duk kun sauya? Shin wannan fursuna da za'a sake tana da
haɗari ne, wanda zai sa ku ji tsoron sakinta? Ai ni a gani na rayuwar gimbiya Jaanu tafi
ta wannan fursuna muhimmanci a gare mu!" Sarki Ayubul Zairiy ya ɗago kai ya dubi
yarima Marganu ya ce, "Wannar fursuna da muka tsare, ba ni ne wanda ya kamota ba.
Mai gidanmu ne nida mahaifinka. Kayi sani cewa wannan kurkuku wanda aka tsare
wannan fursuna, ƙasashe huɗu ne keda mallakinta. Mai gidanmu ya horemu sosai akan
kada mu kuskura mu yarda a kuɓutar da wannan fursuna, saboda haka har sojojin haya
ya kawo daga ƙasar Hindu wanda zasu ƙarawa wannan kurkuku tsaro. Kayi sani cewa
duk zaluncinmu da rashin imaninmu, ba mu kama farcen mai gidanmu ba. Haka ma
sadaukantaka da jarumta ko rabinsa bamu yi ba. Ni kaina bansan dalilin da yasa mai
gidanmu ya kamo wannan mata ba, amma dai ya ce mu tsareta kamar yadda zamu
tsare lafiyarmu. Tabbas idan mai gidanmu yaji wannan labari na sace ƴata da abinda
ɓarawon ya buƙata ba lallai bane ya amince, mu yi masaƴa da ɓarayin ba. Tabbas
rayuwar ƴata guda ɗaya jal a duniya, tana cikin mugun haɗari." Sarki Ayubul Zairiy na
zuwa nan a zancensa ƙwalla ta cika masa idanu.
"Wai shin waye ne wannan mai gidan naku?" Yarima Marganu ya tambaya cikin ƙarfin
zuciya, tamkar shi kaɗai zai iya yaƙar wannan mai gida nasu. Sarki Ratanam ya dubi
yarima Marganu ya ce, "Kai yaro! Da sanin wannan mai gida namu gwara kullum a yi ta
gana maka azaba kala dubu har ka mutu. Da sanin mai gidanmu gwara ace baka wanzu
a wannan duniya ba. Ina tabbatar maka da cewa SARKI KUFFURU ɗan FARHAMA mai
mulkin Kufa shi ne wannan mai gida namu. Idan ban manta ba mun taɓa zuwa birnin
Kufa da kai, tun kana ɗan shekara goma. Kaga kyawun birnin da kuma yadda aka tsara
shi, duk kyawun birninmu baiyi rabin birnin Kufa ba. Sarki Kuffuru baya son wargi ko
kuma magana ta rainin hankali yanzun sai yasa takobinsa ya sare mutum ko shi waye,
don haka lallai samun wanda zai je wa sarki Kuffuru da buƙatar nan zaiyi wahala saboda
yadda ake tsananin tsoronsa. Mu kanmu da muka kasance abokansa tun na yarinta
baya raga mana."
Koda sarki Ratanam yazo nan a jawabinsa sai sarki Ayubul Zairiy ya tari numfashinsa ya
ce, "Ai babu abinda zai hanani zuwa gare shi face bana numfashi a doron ƙasa. Kai
yanzun nan ma nakeson tafiya gurin wannan sarki, Ruguzan kirawo mini hadiminka na
aljani ya kaini." Boka Ruguzan yayi ajiyar numfashi sannan ya ce, "Ya shugabana. Zuwa
wurin sarki Kuffuru ba shine damuwar ba, damuwar ita ce dazuzzuka da tsaunukan da
za'a ratsa kafin a je dajin Marsas. Kuyi sani cewa wannan daji na Marsas yana da nisa
sosai daga birnin Sin, kafun mutum yaje wannan daji sai ya ratsa ta cikin waɗansu
muggan dazuzzuka guda biyu haka kuma sai ya bi ta kan wani makeken tsauni. Daji na
farko ana kiransa da suna Djinn, babu komai a wannan daji face ayarin waɗansu fararen
aljanu masu zuƙan jinin bil'adama, fiye da shekaru goma sha bakwai baya aka
ƙauracewa wucewa ta cikin wannan daji saboda duk wanda ya shiga cikin dajin, ba ya
fitowa a raye. Komai hatsabibancin mutum da ƙarfin sihirin tsafinsa da zarar yayi arba
da waɗannan fararen aljanu ta sa ta ƙare. Ba kowa bane ya ajiye waɗannan aljanu
domin su yi gadi ba, sai sarkin sadaukai Samudul Ansari, sai mun samu lokaci zanyi
muku bayanin waye ne sarki Samudul Ansari.
"Daji na biyu kuma wanda ke kan hanƴar zuwa dajin Marsas shi ne dajin Shiwazu, babu
komai a wannan daji sai tafka-tafkan koguna da koramu masu ɗauke da muggan kadoji
da manƴan kifaye wadanda suke iya kifar da jirgin ruwa komai girmansa. Wani abun
al'ajabi dangane da waɗannan dazuzzuka guda biyu shi ne abu mai fuka-fuki bai isa ya
ƙetare ta samansu ba, walau tsuntsu ko aljani. Duk gangancin da ya kai aljani waɗannan
dazuzzuka guda biyu to tasa ta ƙare sai dai uwarsa ta haifi wani, saboda ƙonewa zaiyi
ƙurmus ya zama toka.
"Idan mutum ya ƙetare waɗannan dazuzzuka guda biyu zaiyi kiciɓis da wani katon
tsauni wanda ya tare hanya, babu yadda za'ayi mutum ya wuce ba tare da hau wannan
tsauni ba. Matsalar ita ce a saman wannan tsauni gari ne guda na waɗansu muggan
arnan daji, manya-manya kamar mutanen farko haka zaka gansu. Waɗannan arnan daji
sun kware matuka wajen iya ɗana muggan tarkuna, su ɗinga kama mutane suna
yankawa gunkinsu. Ya shugabana wannan shi ne taƙaitaccen bayani akan haɗarin dake
kan hanƴar zuwa dajin Marsas, haƙiƙa wannan ɓarawo ba shi da niyyar bayar da
wannan ƴa taka. Saboda ya san da wuya a iya tsallake masifun dake cikin waɗannn
dazuzzuka da wannan tsauni. Dangane da batun neman buƙata a wajen sarki Kuffuru ni
nasan abinda za'a faɗa masa ya yadda a sake wannan fursuna amma ba zan faɗa
muku a nan ba, sai kun yanke shawarar wanda zaije gare shi. Shi wannan shi kaɗai zan
faɗawa."
Lokacin da boka Ruguzan yazo nan a jawabinsa sai hankalin Ayubul Zairiy da na sarki
Ratanam yayi mummunan tashi, saboda sun gama tsorata da batun waɗannan
dazuzzuka guda biyu da kuma tsaunin nan na arnan daji. A ɓangaren yarima Marganu
murmushi kawai yake, saboda a ganinsa ya samu babbar dama wacce zai sadaukar da
rayuwarsa ya ceto rayuwar gimbiya Jaanu wataƙila ta kamu da tsananin sonsa itama.
Sarki Ayubul Zairiy da sarki Ratanam na tsaye cikin jimami kawai sai suka ga yarima
Marganu ya durkusa bisa gwiwowinsa ya ce, "Ya ku shuwagabanina, alfarma ɗaya nake
nema a wajenku. Dukkaninku kunsan cewa na kamu da tsananin son gimbiya Jaanu, so
ba na wasa ba. Saboda haka nake son ku amince min, na sallama rayuwata naje birnin
Kufa wajen sarki Kuffuru na nemi izinin ɗaukar wannan fursuna. Daga nan na wuce kai
tsaye izuwa dajin Marsas don amso abar begena, madubin zuciyata gimbiya Jaanu.
Kuyi sani cewa a wannan karon idan gimbiya Jaanu bata amince da buƙata ta ba, zan
kashe kaina kamar yadda mazajen jiya suka kashe kansu domin banga amfanin
rayuwata a duniya ba. Ina haɗaku da girman ababen dogaronku kuyi min izini, ni kuma
na rantse da ƙaunar da nake yiwa gimbiya sai naje har dajin Marsas na dawo da ita."
Koda jin haka sai sarki Ratanam ya sake gigicewa ya dakawa yarima tsawa ya ce, "Baka
da hankali ne?! Ka san waye Kuffuru kuwa? Idan barci kake ka farka, idan wasa kake ka
daina. Na rantse da karagar mulkina, babu wani sadauki a wannan nahiya tamu da yayi
rabin ƙarfin damtsen sarki Kuffuru. Sarki Kuffuru azzalumi ne na gaban kwatance,
baisan wani abu wai shi tausayi ba. Masu hasashe da kiyasi sun tabbatar da cewa a
duk shekara ana yankewa mutane dubu ɗari da arba'in hukuncin kisa a birnin sarki
Kuffuru. Zaluncin Kuffuru bai tsaya iya kan talakawa ba, hatta sarakuna ƴan uwansa
zaluntarsu yake. Ya ya kake tsammanin zai amince da buƙatarka ta kuɓutar da wannan
mata? To in baka sani ba ka sani, wannan mata da ya tsare a kurkuku tana daga cikin
tsatson sarki Deher ɗan sarki Al-Khamis da ya shuɗe. Sai mun samu zama zan baka
tarihin yadda aka yi Deher ya tarwatsa zuri'ar kakannin sarki Kuffuru har mahaifiyasa tayi
gudun hijira ta haifeshi a birnin Kufa, da ya girma yayi hankali ya kashe sarkin garin
sannan ya haye karagarsa. Ya kai ɗana kada soyayya ta ruɗeka kazo kayi dana sani
daga baya, ka bari kawai mubi abin a hankali har a samu a ƙwato gimbiya."
"Idan ka amince masa zaiyi wannan tafiya nikuma nayi alƙawarin zan sanar dashi wani
sirri wanda indai ya faɗawa sarki Kuffuru zai amince da buƙatarsa. Sannan zan ba shi
taimako sosai wajen ganin ya ƙetare waɗannan manyan dazuzzuka guda biyu masu
mugun haɗari." Inji boka Ruguzan cikin tsantsar nutsuwa da yarda abinda yake cewa.
"Ka tuna ya kai wannan sarki, wannan ɗa shi kaɗai gareka. Kana ƙaunarsa kamar yadda
kake ƙaunar mahaifiyarsa da ta mutu. Ka tuna cewa sau bakwai yana yunƙurin hallaka
kansa akan wannan gimbiya tamu wato Jaanu, na san baka so ka rasa wannan ɗa naka.
Wannan babbar dama ce ya samu da zai nunawa gimbiya yana ƙaunarta fiye da yadda
yake ƙaunar rayuwarsa, tabbas wannan zai kashe mata jiki ta kamu da tsananin
ƙaunarsa itama. Ya ya kake tsammanin yarima Marganu zai kasance idan aka ce yau an
ɗaura masa aure da gimbiya Jaanu?" Koda boka Ruguzan yazo nan a zancensa sai jikin
sarki Ratanam yayi sanyi ya faɗa kogin tunani mai zurfi. Daga can sai hawaye ya soma
tsiyayowa daga cikin idanunsa ya fara kuka. Marganu ya riƙo hannayensa biyu ya ce,
"Abba? Lafiya kake kuka?" Sarki Ratanam ya ce, "Ya kai ɗana na tuno tsohon tarihin
matata ce, gimbiya Sharlisa. Ka sani cewa muna tsakiyar soyayya da ita, mahaifinta
sarki yace ba zai aura min ita ba face naje birnin Duma na saro kan sarkinsu na kawo
masa a matsayin sadaki. Sarkin Duma a wancan zamani wani gawurtaccen tsohon
sadauki ne kuma shine babban abokin gabar mahaifin Sharlisa, saboda tsananin ƙaunar
da nake yiwa Sharlisa yasa na sayar da raina naje birnin Duma, muka gwabza yaƙi da
sarkinsu na kashe shi da ƙyar na saro kansa, na kawowa sarki sannan aka ɗaura min
aure da Sharlisa. Sai da nayi jiƴƴa ta tsahon shekaru bakwai sakamakon mugun artabun
da nayi da sarkin Duma. Tabbas nayi babban rashi na masoyiyata Sharlisa. Saboda haka
na amince ka sayar da rayuwarka domin cikar burinka." Hawaye ya kwacewa sarki
Ratanam daƙyar su Ayubul Zairiy suka bashi baki sannan ya daina kukan.
Marganu ya dubi Ayubul Zairiy cikin girmamawa ya ce, "Ya kai sirikina, na hutassheka.
Zan je har dajin Marsas sannan na dawo maka da ƴarka, abu ɗaya da nake buƙata daga
wajenka shi ne. Ina son idan muka dawo a ɗaura min da ita, ko tana so ko bata so.
Saboda hakan shi ne zai dauwamar da zumunci tsakanin birninmu da naku. Ka sani
cewa duk abinda nasa a gabana sai nayi nasara, ina son wannan ƴa taka fiye da yadda
kake tsammani. Da ace na rasa gimbiya Jaanu kwara ace anyi gunduwa-gunduwa da
sassan jikina don hakan zai fiye min alheri. Shin ka ɗauki alkawari, idan na dawo tare da
gimbiya zaka ɗaura mana aure, ko tana so ko bata so?" Sarki Ayubul Zairiy ya harari
yarima Marganu ya ce, "Baka da hankali ne? Ya ya kake tsammanin zan so abinda ƴata
bata sonsa? Idan kana tunanin don kuɓutar da ƴata ce zaisa nayi mata auren dole to ka
sake tunani. Kai nima fa zan iya zuwa dajin Marsas ɗinnan kawai dai don ina kunƴar
abokina Ratanam ne shiyasa zan barka kaje. Tsahon shekarun nan kasan nikam babu
wanda nakeso ƴata ta aure, idan ba kai ba. Ita ce bata sonka. Shawarar da zan baka ita
ce kayi amfani da wannan dama, ka shawo kanta ta amince da kai. Kaga kenan kuna
dawowa sai mu sha shagali." Yarima Marganu ya bushe da dariya ya ce, "Da yaddar mai
girma Nurutu za'a yi hakan!"
Ba tare da ɓata wani lokaci ba, yarima Marganu yayi bankwana da mahaifinsa yana
kuka don basu taɓa rabuwa ba na tsahon wuni guda. Boka Ruguzan ya dafa kansa suka
ɓace ɓat, daga cikin turakar suka bar sarki Ayubul Zairiy da sarki Ratanam. "Wai shin
wannan yaro naka sadauki ne?" Ayubul Zairiy ya tambayi Ratanam cikin raha. Sarki
Ratanam ya riƙe baki ya ce, "Ka taɓa ganin an samu ɗan ƙabilar Jenher rago?" Ayubul
Zairiy ya ce, na sani?! Ratanam ya ƙara da cewa, "Ɗana fitaccen sadauki ne, kuma
jarumin jarumai. Shi ne ya saro min kan ɗan fashi Bajaru na dajin Kajhar dake ƙasata."
*****
Yarima Marganu na bude idanunsa ya tsinci kansa a tsakiyar wata fada madaidaiciya,
wacce aka yiwa da ado da fatun manƴan dabbobin daji da ƙoƙon kawunansu. Kallo
ɗaya zaka yiwa fadar ka tabbatar da cewa, fadar mashahurin boka ne. Shi dai Marganu
a zaune ya tsinci kansa bisa wata lumtsetsiyar kujera. Boka Ruguzan ya hango zaune
akan wata karaga mai siffar kan zaki wanda ya wangame baki.
Boka Ruguzan ya ce, "Ya kai babban jarumi kuma yarima. Dangane da bayanan da suka
zo mini na sirri daga aljanu, sun shaida min cewa jarumi Aymanul Faris ɗan Hasanul
Jalwar da jaruma Riya ƴar sadauki

Please Login or Register in order to submit comment